Zafafa 2023

Cuta Ta Dau Cuta Chapter 43 By Billyn Abdull Complete Novel

*_Typing📲_*

   *_CUTA TA ƊAU CUTA_*
_(Ɓarawo ya saci akwatin maciji)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_Shafi na arba’in da uku_

*_NACE KIN MALLAKI NAKI👋??._*

*_NAKI NAKE NUFI KIN MALLAKA KUWA👋🏻👋??_*

*_TIKITIN SHIGA JIRGIN TAWAGAR ZAFAFAN LITTATAFAN NAN NA ZAFAFA BIYAR NAKE MAGANA SISTER KIN MALLAKA👋👋👋🤔??_*

*_KIN SAN KUWA A WANNAN SHEKARAR TA 2024 TA DABBANCE. IDAN NACE DABAN INA NUFIN DABAN A CIKIN DABAN_*

*_A 2024 ZAFAFA BIYAR ƊIN NAN NAKU SUN SAKE ZUWA MUKU DA WASU SABON SALO NA MUSAMMAN DA ƘAYATARWA AKAN FARASHI KAI SAUƘI DA RAHUSA. DAN HAKA INA GAYA MIKI ƳAR UWA KADA KI BARI AYI TAFIYAR NAN BABU KE_*

_Littatafan sune kamar haka 👇🏻_.

   *_KWANKWASON JIMINA….._*
_(NA MSS XOXO)_

*_GUDUN ƘADDARA_*
_( NA SAFIYYA HUGUMA)_

*_TSUSTAR NAMA….._*
_(NA BILYN ABDULL)_

*_AMEENATU_*
_(NA  MAMU GEE)_

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

_______________

………A watan da su Mimi ke cika bakwai cif da aure iyalan Alhaji Abaan suka nufi Kano halartar auren yaron Ni’ima da ƴar wajen Zuhrah. Harda amarya Mimi mai fama da ciki ɗan watanni biyar. Sai langaɓewa take a jikin Khadijah tana tureta da mata faɗa akan ta dinga ƙarfafa jikinta. Shiko Alhaji Abaan na faɗan ta bar damar masa yarinya ta barta da abinda ya dameta. Ita daga uban ma har ƴar dariya suke bata. Dan bataga ƙyau a makanta ba sam. Da taga zasu isheta ta ce aiba dole bane zata kira Yazeed ɗin yazo ya ɗauki matarsa basai taje bikin ba ai. Aiko ta sanya ma Daddynta kuka akan ita dai tana son zuwa dan ALLAH. Aiko ya ɗaure mata ƙugu dole Khadijah ta kawo ido ta saka musu.
Sun isa Kano ranar talata, inda suka tarar su ake jira da shirye-shirye musamman Khadijah da ayanzu itace matsayin uwa ga ƙannenta. Washe garin laraba suka shirya fita duba matar autansu da ke a asibiti sakamakon miscarriage data samu a daren jiya. Mota biyu sukayi, daka gansu kaga nagartaccen family na gogaggun ƴan boko da naira ta gama nuna kanta a jikinsu. Dan daga iyayen har ƴaƴan tsaf-tsaf suke kamar ka taɓa jin daɗi ya maka ihu. Koda suka shigo asibitin kwarjininsu yasa kowama ya haɗu da su sai ya kallesu ya sake kallo. Bayan sun duba matar ƙanin nasu da akama sallama suka ɗunguma suka fito. Autansun ne ya ja su akan su rakashi wani waje Please. Babu wanda yay musu sai ma Mimi dake faman masa rakin ita dai a koma gida barci take ji. Aunty Jamilah na riƙe da ita tana riritata kamar wata ƙwai. Yayinda Khadijah ke faman harararta.
A gaban gadon wani yamutsatsen tsoho da wahalar rayuwa ta gama nuna kanta a jikinsa suka tsaya. Yana kwance sai idanu luƙu-luƙu da haƙora daka gansa kaga wanda yunwa ta gama cinyema hanji.  A yanda yake kwance kuma zai baka tabbacin yana tare da lalurar shanyewar ɓarin jiki ne. Dan bakinsa har ya ɗan karkace. Da alama kuma idonsa ɗaya baya aiki sosai. A gefensa mace ce akan tsohon wheelchair irin na ƙarfen nan da akeyi a Nigeria. Itama duk ta fita hayyacinta fatar fuskarta tai wani faci-facin nan baƙi nan jaa nan brown. Itama dai a rame take sosai, sai haƙora gayau na gaba ma guda biyu sun fita sai uban gate kamar ƙofar gari. Babu ƙafa a tattare da ita sai dungulmi. Sai wani kalar tsamin dauɗa take ga kayan jikinta duk a ciccinye saboda tsufa da gajiyar da sukai suma. A kaf su Khadijah babu wanda ya gane su wanene, sai dai sun gaishesu da tambayar mai jiki. Amma abin mamaki daga matar har mijin da alama su sun shaidasu musamman ma Khadijah da Mimi da suka tsurama idanu. Dan atake hawaye suka fara bin kumatunsu. Khadijah dai ta ɓalle handbag dinta ta cire rafa na dubu guda biyu 200k ta ajiye musu dan haka kawai suka bata matuƙar tausayi. Tasan kuma tunda auta ya kawo su nan ya san mutanen. Ƙoƙarin tafiya suke saboda naci da shagwaɓar da Mimi take musu kan a tafi ita bata son warin asibitin.
Cikin rawar muryar yamutsaten mutumin da ke fita gururu ya ce, “Khadijah!”. Cak Khadijah ta tsaya tare da juyowa a firgice dan jin ya ambaci sunanta. Hawayen dake bin kumatunsa masu zafi suka sake ɓulɓulowa kamar yanda na matarsa ke ɓulbulowa. Batare da ya damu ba ya cigaba da faɗin, “Nasan baki ganeni ba. Dafeeq ne.”
Ba Khadijah ba kowa ma dake wajen sai da ya razana. Idan ka cire Mimi da sauran yaran da basu san komai ba. Sai auta da ya san wanene ɗin shi daman. Dafeeq dake kuka rurus ya cigaba da faɗin, “Kinga yanda ALLAH yay dani Khadijah. Kinga yanda Dafeeq ya koma. Tabbas nasan alhakinki dana iyayenki bazai barni ba Khadijah. Dan na zalunceku ƙwarai da gaske. Nayi wasa da zuciyar data soni don ALLAH. Na bar soyayya ta gaskiya da amana saboda kuɗi. Na ɓata miki suna da tunanin ni ɗin mai wayo ne. Amma wlhy a duk abinda ya faru ban taɓa jin rashin sonki kona daƙiƙa ɗaya ba. Dan ALLAH ne shaida ta son gaskiya ke kaɗai na taɓamawa bayan iyayena. Sai dai ban san wace wauta da son zuciya ne ya jagoranceni aikata miki dukkan abinda ya faru ba. Kaicona. Inama nayi haƙuri nabi shawarar Baba alokacin da yace na bari ki gama karatunki da kansa zai aura min ke. Inama nayi haƙuri da abinda yace. Da nasan har yanzu muna a tare cikin farin ciki da zuri’armu. Amma na biyema son zuciya da wauta na ɓata komai. Na zugaki, nai amfani da soyayyar da kikemin ta gaskiya na sakaki bijirema iyayenki. Na kuma dawo na shirya da nawa kika cigaba da zama cikin fushin naki iyayen. Hakan bai isheni ba na ɓata miki suna a wautata wai duk dan na samu damar nisantaki da kowa sai ni kawai. Kiji bazaki taɓa iya rabuwa dani ba. Duk da hakan kuma ban haƙura ba naje na kawo wannan ƙarfen ƙafar cikin rayuwar mu. Na ɗakkoma kaina CUTA da hannuna gashi nan na gagara warkewa daga gubarta, saima sake wargazani da tayi gaba ɗaya. Khadijah kamar yanda Kainaat ta bijirema iyayenta da ƙyamatarsu matsayin su na iyayenta ta ɗauki iyayen bariki tarihi ya sake maimaita kansa. Dan a yanzu haka muma tamu ƴar ta jima da jefar damu da nunama duniya mu ba iyayenta bane ba. Talauci baisa mun sakata a makaranta ba. Sai talla da suyar awara a bakin layi. A haka ta samu saurayi daya dinga jan ra’ayinta har ya sakata a makaranta. Bayan ta kammala karatu ya tsaya mata ta shiga jami’a. Acan ne ta haɗu da ƙawaye da sabbin samari. Shima ta butulce masa dan acewarta ta gama da ajinsa. A haka ta zama koda yaushe cikin ƴaƴan manya. Inda ta samu damar aure baban wani yaro da suke abota kasancewar baban babban ɗan siyasa ne. Babu zato sai ganin aurenta mukai ana nunawa a tv tare da wasu iyayen bamu ba. Munsha kuka matuƙa, dan a ranar na yanke jiki na faɗi na samu paralysis. Koda akaje aka sanar mata sai cewa tai bama ta sanmu ba. Dan bata da wata alaƙa damu bayan ta ni wai mai gadin gidansu ne mamanta gata nan mai aikinsu. Haka naita jiyya a gida bata taɓa ta waiwayemu ba. Sai dai mu ganta a tv tare da mijinta. A haka akaja wajen shekara guda, ranar kwatsam sai ga labarai an nuna wai ta kashe mijin nata a sakamakon ya gano sirrinta na ƙarya data masa da iyayen bogi. Rikici ya hargume tsakaninsu ta daɓa masa wuƙa. In dai takaice muku yanzu tana prison anata Shari’a. Munma ji ƙishin-ƙishin ɗin kasheta zasuyi, koda yake nasan kuma duk kun san wannan labarin, dan labarine daya zaga lungu da saƙo na ƙasar nan. Munsha wahala a rayuwa Khadijah, dukiyar da akaso tarawa bata tarun ba. Ƴa ɗaya tak da muka mallaka a duniya tace mu ba iyayenta bane. Shekarata kusan uku kenan a wannan halin na jiyya, Babu mai taimakonmu, sai a kwanan nan da ɗan uwanki ya samu labari yazo ya kawoni asibiti. Ita kanta Kainaat kinga yanda ta koma. Duka ƙafafu babu, ta rasa a sakamakon haɗari lokacin data nufi Niger neman iyayenta……”
Cikin Kuka Kainaat ta amshe da faɗin, “Tabbas alhakinku ke da Abaan dana iyayenmu bazai bari mu rayu cikin salama ba Khadijah. Dan bayan kun bamu kuɗin nan ke da Abaan na shirya zuwa na nema iyayena kamar yanda kowa ke bani shawara. A haukana ƙila idan nayi hakan zan samu sararin sake komawa cikin rayuwar Abaan. Sai dai kaicona na baro shiri tun ran tubani. Dan kuwa a randa na tafi Niger batare da jiran yardar Dafeeq ba a hanya muka gwabza babban haɗari muna gab da shiga maraɗi. Kasancewar jeho mai sunaki Khadijah da muke kira Banan da nayi ita bataji ciwo sosai ba. Niko ƙarfe ya dannemin ƙafafu dan ɗaya ma tun sanda aka zaroni tama rabu da jikina. Ɗayar kuwa sai daga baya aka yanke min ita. A dalilin wannan haɗari ƴan uwana suka ganni cikin wanda ake cigiyar danginsu dan ni bana iya magana ba saboda buguwa a tv. Nanfa suka rankayo suka saman a asibiti. Bayan na dawo hayyacinna na nuna farin cikin ganinsu. Sai dai koda na tambayi ina iyayenmu dan na nema gafararsu sai aka tabbatar min da duk sun rasu. Nayi kuka sosai Khadijah irin wanda bazai taɓa ya misaltu ba. Amma yaya na iya haka na haƙura ƴan uwana suka kwasheni zuwa gida kasancewar an kira Dafeeq amma baizo ba. Nasha fama matuƙa da jiyya ta kusan shekara huɗu babu Dafeeq babu alamarsa. Gani ina cikin tsangwamar mutane da habaici da zagi akan abinda na aikata. Kowa faɗi yake ai banga komai ba, domin kuwa a silata zuciyar mahaifiyata ta buga dare ɗaya tabar duniya. Hakama babana hawan jini ne ya kasheshi kuma duk akan baƙin cikina ne. Dama ƴan uwan nawa bawai kowa ke kulani ba sam. Tun ina iya jure abinda mutane suke faɗa harna gagara haka. Dan tsantsar ƙyara da tsangwama da izgilanci nake gani kala daban-daban ni da Banan. Har takai ni da fara shiga a wani halin da yasa ƴan uwana dake ɗan kulawa dani suma suka fara janyewa saboda zugar mutane. Ganin bazata haifar min da ɗa mai ido ba dole na tattaro na baro Niger zuwa nan Nigeria. Haka na dawo ga Dafeeq. Inda shima na tarar tasa mahaifiyar ta rasu. Rayuwa ta masa zafi sosai komai ya ƙwace masa. Da farko yace shi bazan zauna da shi ba, daga baya dai darajar Banan daya ɗauki son duniya ya ɗaurawa saboda sunanki ya haƙura mu zauna tare. Sai dai tsangwama da kyarar da yarinyar ke fuskanta yasa dole muka canja anguwa. Haka mukaita wahala akan Banan, mune bara mune aikatau domin mu saya mata sutura mu bata abinci. Amma a hakan bamu tsiraba, dan bayan ta girma tasan kanta saita bijire mana. A sakamakon hakan Dafeeq ya rasa ɓarin jikinsa shima. Shine muketa fama har zuwa yanzu amma dai ga’anan. Dan kullum sai nayi Bara muke samu ma muci abinci sau ɗaya a yini. Mun rasa komai, mun rasa kowa har ƴar da muka haifa Khadijah. Na tabbata alhaƙinku ne. Wlhy alhaƙinku ne ku da iyayena ke da Abaan. Kaicon haɗamammiyar rayuwa irin tamu. Nabar iyayena nabi son zuciyata. Yau ga su Nadwan dana ɗauka da muhimmanci sunci amanata kamar yanda naci ta Abaan da iyayena. Inda suma sukaje sakamakon dukiyar da suka ƙwata a hannun nawa basu mori komai ba. Dan Dr Giɗaɗon shima ya wankesu tass harda nasun ma ya gudu. Inda shima dai bai cin ba ya tararma ajalinsa yay accident a motar komai daya ƙwace a hannunsu ya ƙone ƙurmus dashi kansa sai tokarsa aka tattara aka binne. A yanzu haka suma suna can sabon gari sunama ƴan tuwo-tuwo wanke-wanke da girki ana tsammusu na abinci dana shan sigari. Gaskiyar Noor ƙanwar Abban da tace ni da Dafeeq CUTA TA ƊAU CUTA. ke da Abaan ALKAIRI YA ƊAU ALKAIRI. A yau kuwa ga amsar ta fito. Dan randa mukaga shagalin bikin ƴarku da kukayi a tv munsha kuka sosai muna masu tsinema kammu da ALLAH wadai. Kuma nasan bazamu gushe ba muna masu amsar wannan furucin ga jama’a har ƙarshen rayuwarmu. Fatanmu dai ALLAH yasa mu zama izina ga ƴan baya masu sha’awar irin rayuwarmu koma wanda suke kan aikatawa”……..✍️

Click Here To Read Cuta Ta Dau Cuta Chapter 44 By Billyn Abdull

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al’ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

🔥🔥🔥🔥🔥🔥💥💥💥💥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Back to top button