Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 33 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN KADDARA💋

E33

By Boss Bature

Tabbas kuwa tana hasashen Jinin daga Jikinta yake, bubbuga Æ™afar azeeza tayi da hannunta tare da ambaton sunanta”Azeeza”! Har cikin kunnan ta tajiyo kiran da angel ke yi mata, rai a6ace ta farka tana faman mutsustuke idanuwanta, muryarta adisashe tace”Wai lafiya? Wanene ke kirana, Hakanan mutun na yin baccin shi an wani katse mishi” angel na yunÆ™urin buÉ—e baki tayi mata magana tajiyo muryar hanna tana fadin”Nashiga Uku, Jini A jikina! Wanene Ya goga mini jini” afirgice angel ta juya tana kallon hannah dake zaune saman gadonta, Bata gama ruÉ—ewa ba, Suka juyo muryar Eve tana fadin itama Jini ajikinta, hankalin fa angel yayi mugun tashi ganin kusan mutun huÉ—u acikinsu sun fara Jinin al’ada, da ace tana da halin da zata dakatar da jinin da tayi hakan saboda ta fuskanci ba Æ™aramin barazana bane Yin Jinin Agidan kurkukun Æ™addara

Sai kuka suke ta Yi sunga Jini Ajikinsu, Da yake basu da ilmi akan Jinin, Ita kuma angel É—in Tagaza buÉ—e baki tayi musu bayani saboda ruÉ—un da kwakwalwarta ta shiga, koke koken da suke Yi ne ya farkar da Batool daga bacci, aruÉ—e ta sauko daga saman gadonta tana tambayarsu lafiya koda itama tayi tozali da jinin daya 6ata wandonsu a firgice ta É—aura hannayenta asaman kanta tana faÉ—in mun shiga uku, hibba Hanna yasmin Jinin menene ajikin ku? kodai Ciwo kukaji wurin Wasan Ƴar 6oyen da mukayi Jiya”? har suna haÉ—a baki wurin bata amsa da cewa”Suma basu sani ba, kawai sun farka sun ganshi ajikinsu ne,” Lamarin ya É—aga musu hankali ba matan kaÉ—ai ba, hatta mazan da suka farka daga bacci suka ga abunda ke faruwa da Æ´an uwansu jikinsu duk Yayi sanyi, don sun san cewa huÉ—un É—in nan duka xa’a zo akwashe su da sunan za’a bincika lafiyar jikinsu daga nan kuma su da ganinsu sai In Allah Ya nufa za’a dawo dasu Cikinsu, kafin su yanke shawarar zuwa su faÉ—a ma tsohuwa, sai ga giants sun shigo Cikin É—akin wannan karan ba Su uku suka zo ba, wani iko na Allah Su huÉ—u suka shigo giants É—in, Iya adadin marasa Lafiyan dake akwai, Abun ya basu mamaki matuÆ™a, ka rasa wake sanar dasu game da duk wani abu dake faru atsakaninsu,

Babu irin haukan da angel batayi musu ba akan bazasu ÆŠaukar musu Æ´an uwansu ba, Amma duk abanza, Ba ita kadai ba wannan karan hada su deeja suna kuka suna faÉ—in Kada su bari a É—auki Æ´an uwansu, Ba duba lafiyarsu xa’ayi ba Æ™ara musu Ciwon za’ayi, Wani abun ban tausayin ma. lokacin da giants suka É—auki su Hanna, Suka nufi kopa zasu fita dasu, Da gudu Azeexa da batool da su deeja suka bi bayan giants abunda basu ta6a yunÆ™urin Yi ba, Aikuwa sunyi danasanin Binsu da sukayi da niyar su Æ™waci Æ´an uwansu domin kuwa, Wurgi giants su kayi dasu, gaba É—aya suka kife saman benan kansu Ya bugu sosai, Kuka hada majina, danish bai ta6a sanya kokwanto akan Giants ba, Sai yau da suka jefar da su Angel yaga rashin Imani tsantsa atattare dasu, kuma ranshi yayi mugun 6aci, zuciyarshi ta hasala, bashi kaÉ—ai ba Hatta haris da naufal da mubeen Sun fusata sosai,

Saboda tsabar buguwar da su ka yi, ga6o6in jikinsu sun jigata sosai, Angel tana yashe saman last step na benan, Azeeza da batool sun yi gefen dama atare aka wurgar dasu kamar kayan wanki, Deeja da Parveen da rubina suna ata 6angaren hagu, kowa Ya tarwatse, Sun yi kuka har sun gaji ga takaicin ƴan uwansu da aka tafi dasu ta ƙarfi da yaji, ga kuma takaicin wurgin da akayi dasu kamar wasu dabbobi marasa Ƴanci, ita angel ma hancinta har ya fara bleeding sakamakon bugun ƙasan da yayi, hakan ba ƙaramin tayar masu danish da hankali Ya yi ba, haris Yana zuƙunne gabansu azeeza dake a kwance ƙasa sunata kuka Yana lallashin su, Mubeen da naufal suna a 6angaren da aka wurgar dasu deeja, suna ta aikin lallashi,

Danish ke a zuƙunne Inda angel take kwance ƙasa, ya rasa ya zaiyi da ita saboda sautin kukanta dake neman hargitsa mishi lissafi, yana so ya lallashe Amma ya kasa, Yanke shawarar ɗaukarta yayi zuwa toilet don ya samu ya wanke mata fuskarta ko jinin ya daina zuba, Hannayenshi Ya sanya duka biyun Ya ruƙo waist ɗinta Ya ɗago da ita zuwa saman kafaɗarshi, Ya yunƙura ya miƙe ɗauke da ita Ya nufi sashen toilet ɗinsu,

A bakin fanfo Ya sauketa, Ta zuÆ™unna saman Æ™afafuwanta, idanuwanta sunyi jawur launinsu Ya ciza sun koma kamar na zombie, hawaye duk sun wanke fuskarta sharkaf, Jikinta har kerma Yake yi, Giants bala’e ne, duk yadda suka ta6a mutun sai yaji jiki,

“Am sorry angel” ya furta hakan Yayin da idanuwanshi ke akan fuskarta, a raunace ta É—ago tana kallon shi without saying anything, ita kaÉ—ai tasan Azabar da take ji ajikinta, Zuciyarta ta hasala, har wani tafarfasa take yi,

Janye idanuwanshi yayi daga kan fuskarta, Yakai hannu saman tap ɗin ya kunna shi, Ruwa ya soma kwararowa, Da tafin hannayenshi Ya dinga tarbo ruwan yana wanke mata fuskarta, Ba ƙaramin sanyi taji ba lokacin daya watsa mata ruwan a fuskarta, har saida ta lumshe idanuwanta, Bayan ya kammala Ya kashe tap ɗin, Ya ɗan juyo yana kallonta,

Cikin sanyin murya yace”zaki sha ruwa? Girgiza mashi kai tayi dakyar ta iya buÉ—e baki tace”bana jin Æ™ishi, wanka nake so In yi, U can wait for me out side,” amsa mata Yae da okey, kafin ya miÆ™e Ya fito daga Cikin toilet É—in Ya tsaya Abakin Æ™opar Yana jira ta kammala, lalla6awa tayi ta miÆ™e taje bakin Æ™opar toilet É—in ta datse Æ™opar ta koma ciki, tsawon mintuna bata fara wankan ba, takaicin duniya ya isheta, tarasa ina zata tsoma ranta taji daÉ—i, yanzu shikenan an É—auke su hanna? Suma za’aje a cutar da rayuwarsu kamar yarda aka cutar da su parveen, Ya salam, fashewa tayi da wani sabon kukan mai cin rai, Tana jiyo cool voice É—in danish daga bakin door É—in yana yi mata magana,

“Angel stop crying, its hurting me, idan ba haka zan shigo daga ciki,” tana Jin yace haka da sauri ta taja baki tayi shiru don tasa halin shi, Yanzu ya faÉ—o mata Cikin toilet, MiÆ™ewa Tayi jiki duk ba Æ™wari ta zame kayan jikinta ta É—aura su saman igiya, Ta cika ruwa abokiti Ta soma Yin wankan,

Yana a tsaye Bakin door ɗin ya jingina bayanshi, fararen idanuwanshi na fuskantar ceilling, Yayin da zuciyar shi ta yi nisan kiwo Cikin tunanin Abunda Ya faru ɗazu Zuwansu Giants, tambayoyi ya shiga jefa ma kan shi wata irin lalura ce ke damunsu Hannah? Jinin menene Yake fita ajikinsu? And why tsohuwa bata nuna damuwa a kansu ba? Bakomai yafi ɗaure mashi kai ba, face yarda giants suka nuna rashin tausayi wurin yin wurgi dasu azeeza, don kawai suna ƙoƙarin hana atafi da ƴan uwansu,

Yayi zurfi acikin tunaninshi, kunnuwanshi suka soma Jiyo mashi muryar haris a kausashe yana magana daga Can Cikin ɗakinsu, Da sauri Ya bar ƙopar toilet ɗin Ya shigo ɗakin nasu, kaitsaye Eyes ɗinshi suka sauka akan tsohuwa dake A tsakiyar ɗakinsu Hannunta ruƙe da sanda haris ne agabanta Ya ruƙe qugu, Yana mata maganaTamkar zai rufe ta bugu,

“Saboda me zasu yi wurgi da su? Saboda rashin tausayi da mugunta suka jefar dasu, kamar wasu barguna, gasu nan kina gani da idanuwanki ko tashi sun gaza yi saboda raÉ—aÉ—in da jikinsu yake Yi musu, wai mu me aka maida mu ne eye? nifa nafara kokwanto akan kowa ma dake atare damu, ” Yana magana yana watsa hannayenshi kamar zai buge tsohuwa dama fa shi haris akwai zuciya, Idan ya fusata Ya isa masifa,

Tun da haris Ya soma magana, Tsohuwa ta zazzaro kwarkwararrun idanuwanta waje, Kwayar idon kamar zasu rubzo Æ™asa saboda tsabar zaro su da ta yi, Bakomai bane yasa tayin hakan face Mamaki da al’ajabin daya kamata, karo nafarko kenan da aka fara samun wani acikin su Ya É—aga mata murya, haÆ™ika tayi matuÆ™ar girgixa, sai da yakai karshen maganarshi Ya juya mata Æ™eya yana Æ™unÆ™uni,

RuÆ™e ha6arta tayi idonta akan keyarshi, Muryarta Na rawa tace”HARISU!! yau ni kake gaya ma magana babu tausasa harshe? A ina ka samu wannan Æ™warin gwiwar? Kamanta matsayina ne awurinku? Wato ina can ina tufka ana nan anayi mini warwara,” a wani sukwane Haris Ya juyo Yabi ta da wani irin kallo Yace”Indai akan Æ´an uwana ne fiye da haka ma zan Iya fada maki, Wannan matsayin da kike dashi awurin mu kina dab da rasa shi, Saboda Na fara zargin ba Æ™aunar mu kike Yi ba,” kasa karasa maganar haris yayi idanuwanshi cike tab da kwalla, tsohuwa sai faman gyaÉ—a kai take Yi kamar wata Æ™adangaruwa,

Ganin tana Æ™oÆ™arin juyawa ta koma Cikin dakinta Ne yasa Danish Yin saurin dakatar da ita, ta hanyar yi mata magana” meyasa a koda yaushe muka sanar dake agame da rashin lafiyar É—aya daga Cikin mu baki nuna damuwarki? jin muryar danish Yasa tayi saurin Juyowa tare da kallonshi, A tsanake Yake tafiya yana tunkarar inda take atsaye, Duk wannan abun dake faru Su azeeza sun natsu suna sauraronsu, a lokacin sun dakata da yin kukan sai dai har yanzu basu iya miÆ™ewa daga kwacen da suke a kasa ba,

A gefen haris Danish Ya tsaya tare da ɗaura hannunshi na hagu saman kafadar haris, still idanuwanshi akan tsohuwa Yana jiran Jin amsar da zata basu, Sai faman zare ƙwalaƙwalan idanuwanta take yi, Da alama zuciyarta ta shiga ruɗani,

Bata gama kiÉ—ima ba, zazzaÆ™ar muryar angel ta ratsa kunnuwanta da cewa”Ki basu amsar tambayarsu mana? Daga anyi magana kaÉ—an sai ki dogara sanda Ki koma É—aki, saboda rashin gaskiya, Meyasa kike 6oye mana gaskiya ne? Tun rana ta farko dana tsinci kaina acikin kurkukun nan raina ya bani cewa ba abun arziÆ™i ake aikatawa acikin shi ba, saboda bai kwanta mini araina ba, Kina yawan yi mana Æ™arya, wanda bani kaÉ—ai ba hatta su kansu yanzu sun fara kokwanto akanki, kince mana ana kaisu treatment room domin duba lafiyarsu, to meyasa ake dawo mana dasu a haukace? Maimakon Muga sauÆ™i ajikinsu saima dai muka ga tashin hankalin akan fuskokinsu, Da jikinsu, mutumin dake yin jinin al’ada meya haÉ—a shi da Æ™aiÆ™ayin gaba? Da kuma gwamewar Æ™afafuwa? Uwa uba da fashewar le6e, ga rama, Wannan wani irin treatment ne tsohuwa”! Tayi tambayar tana kallonta, Tsohuwa dai tarasa bakin magana, sai faman gyaÉ—a kanta take yi,
Angel taci gaba da cewa”Allah dai ba Azzalumin bawansa bane, idan ma cutar mu ku keyi, To ku sani Allah Yana kallonku, Kuma akwai ranar hisabi, ranar da duk wani abu da kuke taÆ™ama dashi aduniyar nan bazai ta6a taimakonku ba…….” Angel bata kai Æ™arshen maganarta ba, Tsohuwa ta buga sandar hannunta, Cikin nuna 6acin ranta, Da sauri danish ya dafe kanshi da hanneyenshi,

Ranta amatuÆ™ar 6ace tace”Kin manta abunda na faÉ—a maki? Nifa bakowa bace agidan kurkukun Æ™addarar nan? Don me zaki titsaye ni kina gaya mini magana yadda kika dama? Meyasa bazaki tuhumi Iyayenku da suka sadaukar daku ba sai ni? Da bani da wata alaÆ™a ta jini da ku? Ga dukkan alamu baki Ji gargaÉ—in da nayi maki ba, Ina matuÆ™ar Tausayawa rayuwarku! Domin kuwa duk ranar da kika kuskura Kika bari Ƴan uwanki prisoners suka gasgata maganarki akan tawa, to daga wannan ranar ba zaku Æ™ara Yin tozali da ni ba, Zan barki dasu ne, Kiga idan zaki iya taimakon rayuwarsu,” Tsohuwa Nakai karshen maganarta, Ta Juya fuu kamar zata tashi sama Ta nufi dakinta, Ta shige taja kopa ta rufe,

Sai lokacin danish Ya zame hannayenshi daga saman kanshi, Wato a lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, basu ƙara fahimtar me take cewa ba, tamkar ta wanke masu tunaninsu na tuhumar da su ke yi mata, ita kanta angel ta lura da hakan, Sai dai ko kaɗan hankalinta bai tashi ba, Domin kuwa tasan dole su cigaba da tuhumarta, da zarar an dawo musu da ƴan uwansu da aka ɗauka,

Kallon juna su kayi ita da danish, Kafin ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kansu Batool, tafiya tayi zuwa inda take a kwance, Ta zuƙunna tare da kai hannayenta saman kafaɗun batool ta ɗago da ita tare da kwantar da kanta saman kafaɗunta,

“Sister, yanzu Haka zamu zuba ido muna ji muna gani, Ana raba mu da Æ´an uwanmu”? Cikin shessheÆ™ar kuka batool ta yi maganar, kafin angel ta bata amsar tambayarta, Naufal ya rigata cewa”HaÆ™uri zamuyi, Giants sunfi Æ™arfin mu, Ni dai na roÆ™e ku nan gaba kada ku Æ™ara gigin shiga huruminsu, Ina gargaÉ—inku, Idan ku ka yi haÆ™uri za’a dawo mana da su ne, kamar yarda aka dawo mana dasu Parveena,

Mubeen yace”Nima abunda nake so naja musu kunne akai kenan, Mutanan nan Æ™arfi ne da su, They are extremely dangerous! Da ace tun farko baku Yi yunÆ™urin tunkararsu ba da duk hakan bata faru ba, kun riga da kunsan halinsu, Basa ji basa gani, duk wani koke koken da za ku yi musu abanza, ba saurarar ku zasu Yi ba”

Danish yace”pls let it be past, tunda sun riga sun tafi dasu, Koke koken Ya tsaya iya haka, ”

Jinjina kai Angel ta yi tare da binsu Azeeza da kallo tace”Ku daure ku tashi, ku je toilet ku wanke fuskokin ku,” amsa mata Su ka yi da toh, daÆ™yar suka iya miÆ™ewa tsaye a daddafe suka Nufi toilet,

“Batool kema kije Ki wanke fuskarki, koma Kiyi wanka” amsa mata tayi da toh, Ta É—ago da kanta daga saman kafaÉ—ar angel, Hannunta adafe da sumar kanta, ta miÆ™e ta wuce cikin toilet,

Ba Iya wanke fuska Su kayi ba, Hada wanka su Kayi, Time da suka fito, mazan gaba ɗaya sun koma saman gadajensu, Angel ma tana zaune daga gefen gadonta, Kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi,

Lokacin da giants suka zo kawo musu abinci, Fushi suka Yi, suka Æ™i zuwa su Ci, naufal yace”da rabon muyi ma kanmu asara, domin kuwa su basu san bihim ba, ko ajikinsu, Mu zamu Ji jiki,” wannan maganar da naufal yayi ce tasa parveen ta sauko daga saman gadonta, Ta nufi saman dining carpet ta samu wuri ta zauna, ÆŠaya bayan É—aya suma sauran suka sauko daga saman beds É—insu, Suka Nufi Carpet É—in suka zazzauna,

Lafiyayyan abinci aka kawo musu, ba don suna jin daÉ—inshi ba suke Cin shi, Kamar waÉ—anda aka Yi ma dole, In ka cire parveen dake ta zuba loma, dama ita bata wasa da abinci,

Abinci take Ci amma hankalinta na akan giants dake a tsaye sun ƙame, Harara ta dinga jefa musu tamkar ƙwayar idonta zata faɗo kasa, ita kaɗai take haukanta domin kuwa babu tabbacin ko suna kallonta, Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran daya rage Batool ta 6oye musu shi acikin kwandonsu, saboda su samu wanda zasu Ci da anjima,

Bayan tafiyar giants, Safa da marwa suka shiga Yi acikin É—akin duk babu daÉ—i saboda rashin Æ´an uwansu, an rairaye su yanzu sun koma su goma sha É—aya, Babu mutun HuÉ—u acikinsu, dole suyi maraicin rashinsu atare dasu, ga zullumin da suke Yi da fargabar ko awani hali suke Ciki?

Idan suka gaji da zagaye É—akin sai su koma saman gadajensu su zauna, a haka har dare ya rutsa dasu, ÆŠakin Ya yi duhu, Rubina ce ta kunna musu fitilun ÆŠakinsu Haske Ya gauraye ko’ina, Kowa Ya kishingiÉ—a saman gadonshi,

Ta yi tsammanin sunyi bacci Jin É—akin Yayi tsit, Juyawa tayi tare da fuskantar gadon danish, idonshi biyu Ya kwantar da kanshi saman pillow,

“Meya hana ka bacci”? Amsa ya bata da cewa”ke zan tambaya, me kike Yi har yanzu baki runtsa ba”? Ta6e baki ta É—anyi”Damuwace ta hana ni bacci, ina jin duk babu daÉ—i zuciyata”

Shiru baice mata komai ba, sai dai kallonta da yake yi, kamar yadda itama take kallonshi, Gani yayi ta miƙe ta sauko daga saman gadonta, a bakin gadonshi ta zuƙunna tare da ɗaura hannayenta saman mattress ɗinshi

Da É—an mamaki yace”lafiya”? Murmushi ta É—ansaki kafin tace”Bakomai kawai ina so Muyi fira ne,” mayar mata da martanin murmushin yayi, har dimples É—in shi ya lotsa,

“Ai ni ban Iya fira ba, in fact ko surutu ban iya ba, sai in ta kama dole,” tace” toh ka Æ™addara ta kama dolen ne, tambaya ce nake so In yi maka hope zaka amsa mini” É—aga mata gira yayi tare da cewa” Am all ears”

Kame kame ta shiga Yi, abun ma sai yaso ya ba shi dariya, hannun shi yakai saman sumar kanta ya ruÆ™o gashinta tare da cewa”FaÉ—a mini mana, indai nasan amsa zan baki,” tace”Dama nayi mafarki ne, kana da wuÆ™a, shin dagaske ne”? Da budar bakinshi sai ce mata yayi”you’re trying to be smart, tell me the truth waya faÉ—a maki cewa ina da wuÆ™a? Nasan ba mafarki ki kayi ba,”

Hararar shi Tayi jin ya ganota, taso tayi mishi wayau,

“Na ta6a tambayar batool, cewa Inaso zanyi amfani da wuÆ™a, shine take faÉ—a mini cewa Akwai wadda tsohuwa ta baka lokacin da kace mata kana so ka rage yawan sumar kanka,” Wani kallo taga yana binta dashi, Can kuma yace”me zakiyi da ita”? Dariya tayi tare da cewa”bafa kai zan kashe ba, Nasan abunda kake tunani kenan, ni kawai inaso In rage sumar kaina ne, bama ni kadai ba hada batool itama Gashin kanta yayi yawa yana takura mana” tayi maganar tana yamutsa fuska,

Ta6e mata baki yayi”Nima namanta inda na ajiye ta, ko na mayar mata da ita ko ban mayar mata ba, namanta, ”

A Æ™agare tace”pls ka daure ka tuna, Zata yi mana amfani,”

“Angel idan Kina son In rage maki gashin kanki ne, Ba buÆ™atar Yin amfani da knife, i can use my nails to cut it for u” zaro ido ta É—anyi da mamaki tace”taya zaka Iya amfani da akaifa wurin rage yawan gashin kaina, baka ga yawanshi ba ne”

“Idan kin bani dama zan Jaraba” girgiza mashi kai tayi”a’a, Ni dai nafi so Inyi amfani da wuÆ™ar, Idan Allah yasa ka tuna inda ka ajiyeta sai ka É—auko mini” ta faÉ—i hakanne saboda ba gashin take so ta rage ba, WuÆ™ar take buÆ™ata saboda tsaro,

“Its Okey, Kije ki kwanta, duk time dana tuna i will let u know” ya karasa maganar tashi tare da jan bargo ya lullu6e jikinshi har zuwa kanshi, MiÆ™ewa Ta yi tare da juya ta koma saman gadonta ta kwanta, A daren ranar saida ta roÆ™i Allah Akan Yasa itama ta fara Menstruation kodan saboda giants su É—auketa sukaita É—akin nan taga uban me suke aikatawa, Idan Allah yasa Hankalinta bai gushe ba kenan,

Wasa wasa Yau har tsawon One week kenan ba’a dawo dasu Hannah ba, Tun suna sanya damuwa aransu har suka haÆ™ura suna zaman jiran tammani, Tun daga ranar da aka É—aukesu Kullum sai ta roÆ™i Allah tsakar dare Akan Ya karesu aduk inda suke, Bayan haka kuma Tana yawan yin addu’ar akan Allah yasa ta fara jinin itama, duk don saboda da taga me ake yi musu,

Yanzu ta kaiga ko tsohuwa basu tambaya dangane da Æ´an uwansu, saboda sun fahimci cewa ita É—in bata da banbanci da totan masara awurinsu, bi ma’ana bata da amfani duk wani magiyar da zasu Yi mata bazata iya Sanyawa adawo masu da Æ´an uwansu ba, sai da ta gaya musu Æ™arairakinta,

Yau tsawon 3 weeks kenan Suna ta baza ido suga an dawo musu Da ƴan uwansu, Sai acikin satin karshe na watan da suka shiga, Aranar da daddare suna zaune saman carpet Suna fira sun kunna fitilun ɗakinsu, Ba zato ba tsammani sai ga giants Huɗu sun shigo cikin ɗakin nasu Kafaɗunsu Ɗauke dasu Hannah, A wani irin zabure suka miƙe suna kallonsu, wuce wa cikin ɗakin giants su ka yi adai dai bakin gadajensu hannah masu ɗauke da numbobinsu suka kwantar da kowannansu, Atare suka juya suka fuce daga cikin ɗakin,

Azeeza sai tsalleta take Yi tana murna an dawo musu da ƴan uwansu, Su batool kuwa Kallon Kallon suka shiga Yi atsakaninsu, sun rasa gane farin Ciki zasu Yi ko baƙin Ciki? Ga shi dai an dawo musu da ƴan uwansu da suka daɗe suna jimamin rashinsu, Sai dai ga dukkan alamu Basu acikin hayyacinshi, Har ƙwarama lokacin da aka dawo dasu parveen sunyi magana, Amma waɗannan bayin Allahn, Idanuwansu ne kaɗai suke motsi, Numfashin su da hucin zafi yake fita, ƙafafuwansu duk sun tale, Wani abun tashin hankalin ma, Hada Yakushin akaifa asaman wuyansu, fatar wurin tayi jawur, jini ya kwanta, La66ansu sun faffashe, Hankalinsu danish ba ƙaramin tashi yayi ba, Matan kuwa Sun sha kuka kamar ransu zai fita, Angel tace Yanzu babu buƙatar saita yi musu bayani game da cewar cutar dasu ake yi yau dai gashi nan zahiri idanuwansu sun gane masu, Sahun yakushin akaifar dake asaman wuyansu, Haƙiƙa sun yi matuƙar girgiza, hatta mazan saida suka zubar musu da hawaye saboda tsabar tausayinsu daya kama su, daren ranar basu Iya runtsawa ba, A gefen gadajensu Hanna suka zaune suna Jimami, har garin Allah Ya waye, Koda suka je bakin ƙopar ɗakin tsohuwa suka kwankwasa mata, Munafukar bata fito ba, Hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa Bata da gaskiya,

HaÆ™iÆ™a sunsha wahala wurin Yin jinyarsu Hannah, kamar bazasu Rayu ba, jikinsu yayi tsauri sosai, babu sauÆ™i saima abunda ya qara gaba, sai da takai ga Komai daga kwance suke yin shi, fitsari kashi, duka dai, a Æ™alla sun É—auki tsawon one month suna yin jinyarsu kafin Allah yasa suka samu sauÆ™i Jikinsu ya warware, Suka koma kamar yarda suke da, Sai dai babu wani walwala atattare dasu, Suna yawan firgita, Ko kiran sunansu Kayi sai kaga sun É—an zabura, Idan suna bacci kuma Sun dinga sambatu suna koke koke, Ahaka ahaka dai da taimakon Allah angel Tana yi musu addu’a duk rana ta Allah, Sai gashi sun wartsake, Sun dawo normal, Bayan sunji sauÆ™i, Sai ga tsohuwa ta shigo É—akinsu, Wani irin mugun kallo da suka dinga jefa mata, ba arziÆ™i taja sandarta ta koma Cikin É—akinta, Angel taso ace su hanna sun Iya tuna abunda ya faru dasu amma sun kasa, kwata kwata basu Iya tuna komai, Da ace sun tuna koda kaÉ—an ne to kuwa tabbas sauran Æ´an uwan nasu zasu Ƙara gasgata maganarta, duk da ayanzun ma ta fara cin nasara saboda kokwanton su Ya ninku akan gidan kurkukun, Sun sha jinin jikinsu, Sun fara tsorata da lamarin, Haris har alÆ™awari ya É—auka akan bazai Æ™ara bari giants su ta6a wani acikin su ba, Sai dai in bayan babu ranshi, danish dai bamu san matsayarshi ba, Shi dai baice komai ba, Iya nuna 6acin ranshi akan fuskarshi ne, Amma su naufal mubeen da javed duk sun É—auki wannan alÆ™awarin na hana atafi da Æ´an uwansu idan basu da lafiya! Kallonsu kawai angel take Yi domin kuwa tasan babu abunda zasu Iya yi, ba wani Æ™arfi gare su ba, balle suce zasu Iya ja da giants, Mutanan da take tunanin Ba cikakkun mutane bane, Ƙarfinsu bana jinsin bil’adama bane,

Bayan komai Ya lafa tsawon Watanni uku wani iko na Allah, cikin matan ba wanda ya ƙara Yin Menstruation, kamar an ɗauke musu da jinin, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma angel ba, Yanzu hakalinsu ya ɗan kwanta,

Ganin sun samu natsuwa yasa Ta fara jan hankalinsu zuwa ga addinin musulunci, Idan dare Yayi bata barinsu Yin bacci, Tarihin annabawa take basu tun daga kan tarihin Annabi Muhammad (SAW) Cikin hikma take Basu tarihin, Kuma ga dukkan alamu ba Æ™aramin daÉ—in shi suke Ji ba, domin kuwa idan ta fara basu tarihin, Ko fitsari mutun ke ji sai kaji yace a jira ya dawo sai acigaba, idan kuwa tace ta gaji abari gobe zata Æ™arasa musu kamar su yi mata hauka, Taci wahala sosai Wurin janyo hankalinsu duk da bata ci nasara ba saboda duhun jahilcin dake akansu, Suna Yi mata tambayoyin Æ™ural da suka fi Æ™arfinta musamman haris, Da yace idan har akwai Allah wanda ya halicce su to meyasa bai ta6a zuwa ya kawo musu ziyara ba? Ire iren irin waÉ—annan tambayoyin sune kesa tana karaya wani lokacin, Ita dai tayi iyakar bakin Æ™oÆ™arinta wurin sanar dasu gaskiya, Sauran kuma tabar ma Allah domin kuwa shi kaÉ—ai ne zai basu ikon musulunta idan yaso, mutun huÉ—u ne acikinsu ta lura da suna matuÆ™ar son Addinin, Batool, Azeeza da Javed, sai kuma parveen, sauran kuwa kokwanto ne Ya hana su yarda da ita saboda wasu tambayoyin su da ta gaza amsa musu, shi danish bama tasan a wata matsaya yake ba, Yana dai son tarihin annabawan da take basu, Sai dai Babu alamar yana da niyar kar6ar addinin nata, mutun huÉ—un nan da suka nuna suna da interest sune suka fara kar6ar addinin musulunci acikinsu, Ta biya musu kalmar shahada, Kusan Yini guda suka É—auka tana ta fama dasu akan su maimaita sun kasa furta ta, Sai cikin dare Wani iko na Allah tana sake biya musu sai gashi sun maimaita lafiya lou batare da inda inda ba, Tayi farin Ciki sosai kamar ta zuba ruwa a Æ™asa tasha, Duk da farin Cikin nata ragagge ne tun da sauran basu kar6a ba, Tafi damuwa akan danish saboda tana ji aranta idan har ya kar6i addinin zai taimaka ma sauran Æ´an uwan nashi saboda suna jin maganarshi sosai, duk da haka bata Æ™yale shi ba, ta addabi rayuwarshi ta hana shi sakat, Sai yana tsaka da yin bacci ya dinga jin muryarta acikin kunnanshi tana karanta mashi kalmatusshahada, wato da tsiya sai ya kar6i addinin, babu yarda batayi dashi ba, Amma YaÆ™i bata haÉ—in kai a Æ™arshe da ta gaji ta Æ™yale shi badan ta haÆ™ura ba, Ta dai bashi lokaci ne ya É—an sarara, duk da haka bata yi fushi dashi ba, Sai ma Æ™ara janshi da take yi ajikinta, saboda sanin mahimmanci da yake da shi, dole saida shi wasu abubuwan zasu tafi dai dai, a 6angaren su batool da suka musulunta, tafara Æ™oÆ™arin Koya musu addu’o’i da karatun kur’ani, sai dai wani abu dake É—aure mata kai, Wahalar da suke sha wurin furtawa, Ita parveen ma hada amai take Yi idan angel ta matsa mata akan ta furta karatun kur’ani, ita kuma azeeza daga anfara sai ta kama bacci, ba Æ™aramin takaici angel ke ji ba, daga bisani tayi wani zazzafan nazari, Acikin kwanakin kowani sati akwai wace rana da idan dare yayi tayi musu karatu suke amsawa lafiya lou batare da sun kakare ba, a irin ranar ne ta ta6a yi ma danish karatun kur’ani da daddare lokacin da giants suka dawo dashi kuma dai dai lokacin ne take basu tarihin annabawa batare da ta samu targaÉ—e ba, Kuma a irin lokacin ne su batool suka furta kalmatusshahada batare da sun yi inda inda ba, duk irin lissafin kwanakin da take yi Tun lokacin da daddynta Ya gudu da ita bata ta6a bari lissafin kwanakin wata sun ku6uce mata ba, Sai dai wannan karan ta kasa gane wace rana ce wannan mai tarin albarka? Meyasa take samun dama A ranar? Bata iya hasashen wace rana bace sai dai tana ganeta ne da alamominta, duk irin ranar ta zagayo bata bari ta tafi abanza, kusan kwana suke Yi da daddare tana Koya musu karatu tare da yi ma sauran Æ´an uwan nasu da’awa kota samu suma Su kar6i addinin, Allah mai yarda yaso, Sai gashi É—aya bayan É—aya suna zuwa wurinta suna cewa suma zasu musulunta, cikin waÉ—an da suka kar6i addinin musulunci akwai, batool, azeeza, Hannah, Hibba, deeja, parveen, Eve, yasmin, Angel, Batool, rubina, Cikin maza mutun uku, Javed, Naufal da Mubeen, yanxu mutun biyu ya rage mata acikinsu, Haris da danish, Su kaÉ—ai suka yi mata cikas, Duk da Tayi matuÆ™ar yin farin Ciki, Da Allah ya bata ikon musuluntar dasu Hanna, Ranar da suka kar6i shahadar ko bacci bata yi ba, A tsakiyar gadonta ta zauna tana kukan farin ciki tare da Yi ma Allah godiya, daya bata wannan damar, Nima dai Na matse kwallata kuma na tayasu murna koba komai sun tsira da imanin da su ka yi, Allah zaiji Æ™ansu,

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button