Halysaah Page 182 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 182….Khaleesat na zaune parlon Mami da Dr dinta wajen karfe goma saura na safe, tagumi tayi tana kallon akwatin ta da Dr Maryam ta zabar mata kaya kala uku da zata je Abuja da shi don ranan lahadi Mami tace za su juyo, Hadiyah ce ta shigo parlon da trolley dinta karami, Dr Maryam na kallonta tace “Da ke za ayi tafiyan Hajiyah Hadiyah?” Hadiyah tayi murmushi tace “Inteesar ai kawata ce, mun yi Junior school tare lokacin muna Abuja kafin mu koma Lagos” Dr Maryam tace “Allah sarki, gaskiya kam ya kamata ki je” Mami ta fito daga dakinta cikin shiri ita ma, mai aikinta dake tsaye a parlon ta maza ta tafi ta amshi akwatin ta, Hadiyah tace “Mami ba kince jirgin karfe sha daya bane” Mami tace “To ina ma naga me kai mu airport din, na kirasa bai daga ba ko yana can yana bacci, kawai bari ayi ma driver magana….” Dai dai nan Jay ya bude kofar parlon, yayi tsaye bakin kofar yace “Kun shirya Mami?” Tace “Kai nake jira tun daxu” Yace “To ku fito” Daga haka ya juya ya bar bakin kofar, Mami na kallon Khaleesat da tayi nisa tunanin da take tace “Tashi mu je Halysaah” Sai a sannan Khaleesat ta daga kanta ta mike a hankali tana kallon Mami, Dr Maryam ta mike ta dau akwatin ta sannan suka nufi kofar fita parlon tare da Hadiyah da mai aikin Mami dake biye da su da akwatin Mami da na Hadiyah. Sai da Mami ta fara shiga wajensu Kilishi da Hajiya A’isha tayi masu sallama, Kilishi na tsokanar Khaleesat wai sai kace ita ce amaryar sai sheki take, Khaleesat that was standing absently a wajen ta ɗan yi murmushi, ita da babu abinda ta shafa a fuskarta, a haka suka fito compound suka tarar da Jay cikin motarsa yana jiran su, wani dogari ya bude ma Mami back seat da sauri yana jera mata kirari, Mami na kallon Khaleesat tace “Shiga Halysaah” Khaleesat ta shiga motar sannan Mami ta shiga dogarin ya kulle motar, Hadiyah ta zaga zuwa daya side din motar don wani dogari ya bude mata kofa ta can, ta madubi Jay ke kallonta bayan ta shiga motar, ko sanin yana yi bata yi ba, Dogarai biyu suka gama saka duk boxes dinsu a booth din motar suna masu Allah ya tsare hanya, Dr Maryam ma tayi masu Allah ya kiyaye hanya, Mami tace “Ameen Dr, idan mun dawo zan kira ki, amma kin yi ma drivern da zai yi dropping din ki magana?” Dr Maryam tace “Eh na masa magana, so nake in ga tafiyar ku tukun, ranki shi dade duk magungunan ta suna cikin zip ɗin farko na trolley dinta….” Mami tace “To ba damuwa Dr” Dr Maryam tace “Amma sai an sa mata ido ranki shi dade idan ba haka ba bazata sha ba….” Mami tace “Kar ki ji komai Dr zata sha” A haka Jay ya ja motar suka bar haraban masarautar, the ride was silent, after driving for almost 30 mins Jay ya ciro wayarsa a aljihu jin shigowar message for the second time, kiris ya rage ya buge motar dake gabansa har sai da Mami tace “Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un, lafiya Jawwad?” Yayi saurin controlling motar ya gangara gefen titi, Mami da Khaleesat da Hadiyah sai kallonsa suke, Mami ta dake tace “Me ya faru?” Bai bata amsa ba ya bude motar da sauri ya sauka yana rike da wayarsa yana kallo, Mami ta bi sa da kallon mamaki, ita ma ta bude motar ta sauka tana kallonsa tace “Jawwad” Yayi saurin daga kai ya kalleta in a state of confusion, sai kuma yace “Waya zan yi Mami” Daga haka ya bar wajen, walking a little distance away from the car, Mami ta kasa dena kallonsa, she wasn’t convince with what he just said, hakan yasa ta sake bin sa har inda ya tafi ya tsaya tace “Wai lafiyar ka kuwa Jawwad? Me ya faru?” Jay ya kalleta cikin wani yanayi yace “Mami debit alert na gani daga account din Ajay” Mami ta bude ido sosai tace “Debit alert kuma? Baka sauke sim din nasa daga wayarka bane har yanxu dama?” Ya girgiza kai da damuwa karara fuskarsa yace “Ban cire ba Mami” Da mamaki Mami tace “To ko wani ya samu Atm card dinsa ne ya cira kudin?” Jay yace “His ATM card is with me Mami, babu abinda ya dauka daga hotel room dinsa on that very day” Mami was speechless, after some seconds tace “To debit din har nawa ka gani?” Jay yace “500k” Mami tace “500k?? Then who is tampering with the account?” Jay ya girgiza kai looking so worried yace “I don’t know” Mami tace “To ko bankin zaka je? A ina aka cire kudin?” Jay yace “Bari inyi dropping din ku, i will call someone at the bank yayi min confirming….” Mami ta sauke ajiyar zuciya tace “To Allah ya kiyaye, amma dai ina ga gwara ka kira bank din yanxu kar a ci gaba da cire kudin?” Jay ya fuzar da iska yace “Bari in kai ku airport din tukun….” Juyawa Mami tayi ta koma motar ya bi bayanta, Mami na shiga motar Khaleesat na kallonta tace “Mami me ya faru?” Mami ta ɗan yi murmushi tace “Kiransa aka yi emergency daga asibiti” Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Jay ya shiga driver seat ya ci gaba da driving din, har ya kai airport baya tare da nutsuwar sa kwata kwata, a nan parking space din airport din ya bar su bayan ya fiddo masu da boxes din su daga cikin booth porters sun shiga da akwatunan cikin airport, Mami na kallonsa tace “Duk yanda ake ciki za mu yi magana” Jay ya gyada mata kai yayi masu Allah ya kiyaye sannan ya koma cikin mota ya ciro wayarsa yana kara kallon debit alert din, bude ido yayi sosai with another new shock bayan ya lura ashe an turo debit na sabon Atm card before the 500k debit alert, ya dinga kallon alert din babu ko kiftawa, yaji komai ya tsaya masa cak na wasu seconds, it took him some time to recover, barin airport din yayi within few minutes yaji gwara ma yaje bank din da kansa ya samu friend din nasa don gaba daya ya rikice… Ajay na zaune kan dakali a kusa da bank bayan sun fito yana sauke numfashi a hankali, Ozhi dake tsaye kansa sai sannu yake masa yana masa fifita da bugujejen rigar jikinsa, shi dai Ajay kansa na kasa sai nodding masa kai kawai yake, Ozhi ya tari wani me siyar da pure water ya amshi guda biyu ya mika ma Ajay daya yace “Ga ruwa nan ka sha, tafiya ne yayi yawa tun safe shi ne kake jin hajijiya, ka gaji sosai” Ajay ya amshi ruwan da kyar ya bude ya sha kadan, Ozhi ya amshi sauran ya zuba masa a kai ya shafa masa a fuska, suna nan for more than 15 mins idon Ajay a lumshe and he was breathing slowly, tun daga sanda suka hau kwale kwale daga Abinsi zuwa Makurdi ya dawo wani iri, and he started feeling nauseated and sick, all of a sudden kansa yayi ta juya masa sosai ga wani sanyi da ya dinga ji har sai da Ozhi ya rungumosa yana lulubesa da ƙatuwar rigar jikinsa, a wahale suka isa garin Makurdi, sai da suka yi kusan minti ashirin a bakin hanya karkashin wata bishiya sbda yanayin condition din Ajay, daga karshe kuma yayi karfin halin ce ma Ozhi zai iya su ci gaba da tafiya, nan suka fara neman banki, har dai suka samu abun hawan da ya kai su bankin, a cikin bank din ma cike da dauriya Ajay ya gama abinda ya kai sa, aka basa sabon Atm card, don ma anyi attending masa da wuri an kuma basa attention saboda condition dinsa, duk wanda ya kallesa yasan bashi da lafiya sosai kuma zai tausaya masa cause he is looking pale, haka nan ya samu yayi withdrawing kudi bayan sun fito daga bank din, shine ya zauna kan dakalin dake kusa da Atm machine din ya kasa tashi, after a while cikin karfin hali Ajay ya mike a hankali yana kallon Ozhi yace “Za mu iya tafiya yanxu” Ozhi yace “Ka yarda kana iya tafiyan ko de mu bari in ka huta sosai sosai?” Ajay ya gyada masa kai duk da karfin hali kawai yake, Ozhi yace “To mu je” Yana fara tafiyar yaji he can’t go further, ya kalli Ozhi yace “Ba wani hanya sai ta inda muka bi muka zo yanxu?” Ozhi yace “Kwale kwale ne kawai muke hawa zuwa village din mu, muyi sauri sauri mu tafi Dochu ya baka magani, ciwo kar ya dawo kuma” Ajay ya gyada masa kai kawai ya ci gaba da bin sa, ko minti biyar basu yi suna tafiya ba vision dinsa ya koma blur, both motoci da mutanen da ke hada hadar su a wajajen ya dinga ganinsu double, lokaci daya ya fara ganin duhu duhu, dafa Ozhi yayi ya fara yin baya, tun kan ya kai ƙasa Ozhi yayi saurin rikesa da taimakon wasu dake bayansu, gefen hanya suka zaunar da shi amma he is already passed out, Ozhi ya cire ƙatuwar rigar jikinsa da sauri yana masa fifita, wani mutumi ya karbi pure water daya ya bude yana yayyafa masa ruwan, wasu ne suka ce a tafi da shi asibiti kawai, Ozhi dai yayi saurin cire kudaden jikin Ajay ganin yanda aka taru kansa, haka nan aka daukesa zuwa asibitin dake nan wajajen, bayan ɗan lokaci kowa ya watse aka bar Ozhi kadai a reception din asibiti, ko kadan bai so asibiti da aka kawo Ajay ba, so yayi ya maida sa kauyensu a ci gaba da yi masa maganin sa, gashi sai mamakin kudin da Ajay ya ciro masu yawa a banki yake, wata nurse ta zo ta samesa a reception din tana sanar masa zai ajiye dubu ashirin kudin deposit, Ozhi na zare ido yace “A’a bai ce a taɓa masa kudinsa ba” Nurse din tace “To kuwa zai mutu tunda baza a taɓa kudinsa ba, kudin nasa yafi rayuwarsa ne?” Ozhi yayi shiru, sai kuma ya ciro kudin a aljihunsa ya kirga dubu ashirin ya ba Nurse din tace “Ai ba ni zaka ba ma ba, ga can inda ake biya kaje ka biya za su baka takarda” Wajen da ta nuna masa ya nufa da sauri zai kai kudin, har wajen karfe biyar na yamma Ozhi na ta zaune reception din asibitin sai gyangyadi yake yi, daga karshe wata nurse ta tashesa yaje office din likita yana son magana da shi, yana kankame da kudin Ajay dake jikinsa ya tafi office din da aka nuna masa, ya ga likitan na zaune yana ta rubuce rubuce a takarda, ganin Ozhi ya tsaya likitan ya nuna masa kujera alamar ya zauna sannan ya zauna, likitan yace “Wannan patient din ɗan uwanka ne ko ya kuke da shi?” Ozhi ya gyara zama yace “Eh dan uwana ne, muna tare shekara biyu kenan amma ni ban san shi ba” Likitan ya daga kai ya kallesa, sai kuma yace “Ɗan uwanka ne amma kuma baka san shi ba? Ban fahimce yaren ka ba” Ozhi yace “To ni dai ɗan uwana ne amma ban san wanene shi ba” Likitan that was getting pissed off yace “A ina ka san sa?” Ozhi ya kara gyara zama ya fara basa labarin abinda ya hadasa da Ajay har zuwa yau, likitan sai kallonsa yake babu ko kiftawa with much interest, can ya ajiye biro din hannunsa yace “Amma wanene ya cire masa bullet din jikinsa?” Ozhi yace “Native Dr din garinmu mana, Dochu sunansa” Likitan sai kallonsa yake, can yace “What if criminal ne shi, duk baku yi wannan tunanin ba?” Ozhi ya gyara zama yana girgiza kai with seriousness a maganarsa yace “Noo, ai wannan fuskarsa babu criminal, mutumin kirki ne, shi ba criminal ba” Likitan ya wani kallesa yace “Dama ana rubutawa a fuska? To kaga irin wannan case din dole sai mun yi involving yan sanda to avoid problem, tunda baku san wanene shi ba, baku san dalilin da yasa aka yi harbinsa ba, baku kuma san dalilin harbin nasa ba, mu ma kuma bamu san sa ba, so we have to involve the police in this case, har yanxu akwai fragments din bullets a jikinsa which has lead to some complications for him, yanxu dai kafin mu kara taɓa sa sai an sanar ma yan sanda wannan case din” Ozhi yayi shiru yana kallon likitan, can yace “Zan gansa ne yanxu Doctor?” Dr din yace “Yeah zaka iya ganinsa, mu je ka gansa” Mikewa Ozhi yayi ya bi bayan likitan zuwa ward din da Ajay yake, yana kwance idonsa a lumshe, although he is revived by the Doctors amma he was still weak, ciwon kansa ya karu akan na da duk da drip din da ake kara masa ji yake kamar ana sara masa kansa, bai yarda ya bude ido ba yayi kamar bacci yake bayan ya ji sun shigo, Dr din na kallon Ozhi yace “Kafin mu kara taɓasa sai idan yan sanda sun zo gaskiya, saboda ba a san wanene shi ba” Ozhi yace “To, to ai sai ku kira su su zo, ni dai nasan mutum na kirki ne shi” Dr din ya juya ya fita daga ward din, sai a sannan Ajay ya bude ido a hankali, Ozhi yayi kasa da murya yana tsaye kusa da shi yace “Abokina ka tashi muyi gudu wa rayuwarmu, za su je su kira mana yan sanda ne, ka tashi mu yi gudu mu koma village din mu Dochu yayi maka magani da yake maka, yan sandan garin nan babu kyau suna kashe mutane” Ajay yayi shiru yana kallon Ozhi, can yace “Ka fara siyo min ruwa na sha zan ji karfi sai mu tafi” Da sauri Ozhi ya ajiye kudaden hannunsa a gefen Ajay ya dau dubu daya a ciki sannan ya fita zai je nemo ruwa, Ajay ya laluba jikinsa yaji sabon Atm card din da yayi, kayansa ne a jikinsa don matar Ozhi ta wanke masa tayi stitching din inda bullet ya huda, ana ta ajiyar kayan tun da dadewa, har sai yau da za su taho banki ta dauko masa ya saka su, a hankali Ajay ya mike zaune ya zare drip din hannunsa sannan ya sauka daga kan gadon ya dau kudaden ya saka a aljihu ya fita daga ward din, kansa tsaye with confidence ya nufi kofar da yaga alamar na fita daga reception ne without looking at anybody har ya fita, sai da ya fita ya fara tafiya da sauri har ya fice daga asibitin gaba daya ya tare adaidaita sahu ya shiga, ya jinginar da kansa da kujeran adaidata sahun yana sauke numfashi, ɗan tafiyar nan da yayi jinsa yake kamar wanda ya yini yana gudu, he was so weak…. Mami na tafiya a hankali ta fito compound din gidan Ammi tana kallon Jay dake zaune kan kujera kusa da parking lot ya rike kansa, it was almost magrib time, tun karfe daya na rana suka sauka garin Abuja, tun daga sannan kuma take ta kiransa baya daga waya har hankalinta ya tashi sosai, ta kirasa ya fi a kirga amma shiru, kawai gangar jikinta ne ke Abuja amma zuciyarta na can Bauchi, har Kilishi ta kira ta tambaya ko Jay ya koma gida tace mata bai koma ba, and this almost caused her a heart attack kawai dauriya take tayi ga gida cike da yan biki, all of a sudden sai gashi yanxu ya kirata wai ya shigo gidan Ammi yana parking lot, duk da wani relieve da ya zo mata amma tayi mamakin zuwan nasa Abuja all of a sudden don basu yi da shi zai zo Abuja ba yau, har ta karasa kusa da shi bai sani ba yana rike da kansa, calmly tace “Jawwad” Mikewa yayi da sauri kamar wanda ya firgita ya tafi gabanta da wani expression yace “Mami….” She could see he was in a state of shock and confusion don duk a birkice yake, gashi yayi wani zuru zuru, hankali tashe tace “Me ya faru Jawwad? Me yasa ka biyo mu? What’s happening?” Jay na birkita gashin kansa yace “Mami na je banki daxu bayan nayi dropping din ku, Mami Atm aka yi da account din Ajay sannan aka yi withdrawing 500k from the account in Makurdi….” Yana kai wa nan yayi shiru yana kallon Mami zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri kamar wanda yayi tseren gudu, Mami dai kallonsa take babu ko kiftawa lokaci daya taji kanta ya kulle, a hankali tace “Then who is impersonating him Jawwad?” Da wani expression Jay yace “How Mami? How is that possible? Kin taɓa ganin wani yayi ma wani Atm card a duk tarihin banki?” Mami was completely short of words tana ta kallonsa without blinking ita ma dai tsoro ne ya bayyana a fuskarta, Lokaci daya idanuwan Jay suka kada voice dinsa na breaking ya kamo hannun Mami da kyar yace “Mami does this mean Ajay is alive?” Kasa controlling kansa yayi ya dora goshinsa a kan shoulder din Maminsa hawaye suka fara zuba idonsa, Mami ta kasa cewa komai, but not wanting to give her son a false hope da zai fama masa ciwon dake zuciyarsa da har yanxu bai gama healing ba ta kwantar da murya cike da karfin hali tace “Jawwad babu abinda fraudster din nan basa iya yi a wannan generation din da muke ciki, zai iya yiwuwa aikinsu ne wannan tunda da kudi sosai a account din, ko kuma wani a bankin ke impersonating dinsa barin da yaga shiru shiru shekara biyu babu motsi a account din, idan ba haka ba ka taɓa ganin wanda ya mutu ya dawo?” Hawaye kawai ke sauka idon Jay yana jin abinda Mami ke cewa, da kyar muryarsa na rawa yace “Zan tafi Makurdi din yanxu, i have the bank location and everything now, I don’t believe wani na iya yi ma wani Atm card, it must definitely be him Mami, Mami ina ji a jikina shi ne….”

