Uncategorized

Shawarwari akan yadda mace mai juna biyu zata kula da shi

Hakika mata da yawa musamman wadanda suka ɗauki cikin fari suna yin musakurai wanda wasu ka iya rasa cikin gabaɗaya, wannan yaja hankalina na yi wannan rubutu 

1- SHAWARA GAME DA ABINCI

Idan mace ɗauki ciki yaron da yake cikinta yana zukan jininta saboda shine abincinsa wannan dalilin yasa mata masu ciki suke yawan samun karancin jini. Yana da kyau mace mai juna biyu ta dinga cin abinci iri iri musamman abinci mai gina jiki kamar su:

– Wake

– Kifi

– Nama

– kwai da sauransu

Da kuma ganye da kayan itatuwa kamar su :

– Salat

– Kabeji

– Alayyafu

– Zogole

– Lemu

– Kankana

– Apple da sauransu .

Wanda cin abinci lafiyayya yana karawa mata jini, lafiya, sannan ya ƙarawa yaron da yake cikin ta lafiya da kaifin basira.

2- SHAWARA GAME DA ZAMAN MAI JUNA BIYU

I- Mace mai juna biyu bai kamata ta dinga aikin wahala sosai ba, yana da kyau ta dinga hutu ko wacce rana.

II- Idan mace mai ciki bata da lafiya yana da kyau taje asibiti domin gudun kada tayi amfani da maganin da zai zama mata matsala, ko zai kawo matsala ga yaron dake cikinta.

III- Tsaftar muhalli da tsaftar jiki yana da amfani sosai ga mace mai juna domin kare kanta da yaron cikinta daga kamuwa da cututtuka.

IV- Maccen da take yawan amai yana da kyau tayi amfani da busheshshen abinci wanda hakan zai rage yawan amai ko kuma ya tsayar da aman baki daya ma.

3- SHAWARA GAME DA AMFANI DA MAGANIN KARIN JINI

Mafi yawan mata idan aka basu maganin karin jini mai makon suyi amfani da shi kullum, amma basa amfani da shi, da sunan basa son warin maganin, wanda wannan baya daya daga cikin dalilin da zai sa a hana mutum shan wannan maganin.

Asali dama can magani ba dan daɗi ake shansa ba, illa dan neman lafiya da neman kariya daga cututtuka.

4- SHAWARA GAME DA ALLURAR TETANUS 

Wannan wata allura ce da ake yiwa mata lokocin awon ciki,

amma mafi yawa mata basa son wannan allurar saboda rashin sanin amfaninta.

Gaskiya wannan allurar tana da amfani sosai wanda yana daga cikin amfaninta shine kare yaro daga kamuwa da wannan cutar mai hatsarin gaske wato (Tetanus).

5- SHAWARA GAME DA ZUWA AWUN CIKI

Zuwa awo yana da amfani sosai wanda alokocin awo za a auna aga yadda yaro ya kwanta a ciki. Kuma ana aunawa aga wasu matsaloli masu kashe uwa da jaririnta domin a magance su, kamar su:

1- Hawan jini

2- Ciwon sugar na masu juna biyu

3- Cutan kanjamau

4- Yawan Jini

5- Zazzabin cizon sauro da dai sauransu.

6- Alamar Eclampsia.

Allah Ya sa mu dace, Ya kuma sauki duk wata mace mai juna biyu lafiya. Amin

Back to top button