Uncategorized

Tubali Book 1 Chapter 1 hausa Novel

 

*Bismillahi rahmanirahim. Alhamdulillah Allah na gode maka da ka bani rai da lfy da damar fara rubuta wannan littafin nawa mai suna. TUBALI* *Ya Allah ka bani aron rai da lfy da konciyar hankali ka bani ikon rubutashi har ƙarshe bisa, lfy al’farmar Annabi da al’ƙur’ani. Allah kayi min tsari da abin hani, ka tsare min hannuna, tunanina, idanuna, al’ƙalamina, yatsuna, da rubuta wani abu da zai zamewa al’ummar Annabi sharri ko ya zama cutarwa ga tarbiyarmu.*

GEMBU MEMBILA Taraba State.

Wani irin hadari mai masifar ƙarfi da duhu ne, ya yiwa illahirin yankin Gembu Membila ƙawanya tako wani sashi, gabas da yamma kudu da arewa yake ta gangami.

Yayinda Ya haɗe da duhun dare mai gauraye da duhun damina.

Hakan yasa babu abunda ke tashi a yankin sai wasu irin tsawa da rugugin da aketa yi babu ƙaƙƙautawa, kana kuma wata iriyar iska mai ɗan karen ƙarfi da sanyi ne ke ci gaba da  kaɗawa da ƙarfi.

A dai-dai ya irin wannan lokacin  kuma gaba ɗaya bani Adam mazauna cikin gidaje, sunyi nisan bacci kasan cewar ƙarfe ɗaya na dare ta gota.

Wata kyakkyawar mota ce mai masifar kyau da tsadar gaske, wanda take nuni da mamalakinta wani  ne ko wane,  ta faso kai.

Gudu yake shararawa cikin motar tamkar zai tashi sama. 

Ma’ana gudu irin na ceton rai, shiyasa shi kansa bai san irin tuƙin da yakeyi ba.

Gaba ɗaya jikinsa kyarma yakeyi, duk da azabebben sanyin yanayin wurin, da kuma sanyin A/C’n dake cikin motar, amma hakan bai hanashi haɗa fitinanniyar zufa ta fargabar ganin alamun rabuwa da rayuwar duniya ba.

Tuƙi yakeyi yana juyowa yana kallon wata zungureriyar tirela dake biye dashi a baya, haikan-ƙadaran. 

Da nufin bi ta kanshi ya takeshi, ya gane hakane ganin duk inda yayi binshi tirelar takeyi tana binshi.

Cikin tsananin tashin hankali yasa hannunshin ya sharce zufan goshinsa, kana yasa hannunshi ɗaya ya ruggume yaron dake bisa cinyarsa, yana karkarwa ganin irin azabebben gudun da sukeyi.

Dai-dai lokacin kuma suka iso, kan babban tsaunin dake saman zuzzurfan kwazazzaɓan kogin Gembu wanda yake haɗe da kogin. Numan Adamawa. Dadin Kowa Gombe. kana da binuye.

Sannan hanyar tana nan tamkar tafiyar macijiya ziz-za.

Wayarshi ya zaro a cikin kiɗima ya fara magana da wanda ya kira ɗin, yana maganar muryarshi na rawa, magana irin ta ban kwana da duniya da barin wasiyya da bada amana.

Sun zo gab da Rugar Rumo dake ƙasan hanyar can gefen kwazazzaɓan.

Dai-dai lokacin kuma, tirelar nan ta cim mishi.

Cikin tsananin mugunta ya danna motar da ƙarfi, ya ingizata, cikin ramin dake haɗe da manyan Koguna wanda zurfinsa ya zarta zaton mai zato.

Ji kakeyi k’uuuuuuhhhh, motar ta bada wani irin gigitaccen sauti.

Sai kuma ta ɗan tsaya daga gangarawar sabida karon da tayi da wata bishiya hakan yasa bata faɗa ciki kai tsaye ba.

Da ƙarfi ya kuma matsowa ganin  bishiyar ta ƙare ƙaramar motar.

Ingizata yayi ta tafi cikin ramin.

Ji kakeyi fuuuuuuhhh zinɗim! Ta faɗa cikin ruwa.

Wanda sautin faɗawan yasa mafi akasarin mutanen Rugar Rumo farkawa.

Suna al’hini da tausayin sanin duk wanda ya faɗa ciki ya faɗa ƙabarinsa kenan…

Shi kuwa mai tirelar wani irin masifeffen dariya mara daɗin amo, yayi kana ya wuce cikin garin dan babu damar yin kwana a wannan wurin.

 Tuƙin yakeyi wayarshi saƙale a kunne shi yana cewa.

“Sir na gama dashi, babushi a duniya.

Yayi ban kwana da duniya yanzu zan wuce cikin Gembu kuma zamuje mu kashe matarsa da yaranshi kab”.

Ɗan jim yayi jin yadda Sir ɗin ke dariyar cin nasara tare da cewa.

“kuna kashesu.

Sauran cikon 2 million din ku zai shigo hannunku.”

Cikin zaƙuwa matuk’in tirelan yace.

“Yanzu kuwa”.

Kana ya katse kiran, ya nufi cikin Gembu a cikin daren da wannan duhun damunar.

            ***************

Bayan wasu shekaru A kamar Ashirin da biyu 22.

             Kano state.

Shiru hall ɗin taron ma’aikatan tashar Arewa 24 TV dake birnin Kanon Dabo yake, yayinda ma’aikatan ke zaune bisa kyawawan kujerun dake zagaye da babban table mai kujeru sama da hamsin.

Yayinda gaban kowa goran ruwan Faro mai sanyi ne da kuma Nutrimilk sai maltina da chii exotic, baya ga haka kuma glass cheers cups ne a gefe-gefe.

Kana sai abun sautin magana dake gaban kowa, mai ɗan tsawo.

Gefen dama duk manyan ma’aikata ne.

Kana gefen hagu mabiyansa.

Can baya kuma ƙananun ma’aikata.

Babban ogansu ne ke musu bayanin canje-canje tsarin aikin da suke shirin kafawa na forkon shekarar.

Gyara zamanshi yayi tare da kallon gefen damanshi.

Murya ya ɗan gyara tare da cewa.

“Ina mai Shirin baƙon mako?.”

Cikin nutsuwa Jannart Idris Saleh Dakata. Ta ɗago kanta cikin tattausan muryarta mai cike da nitsuwa tace.

“I’m here Sir”.

Sautin daddad’an muryarta ne kuma yasa, mafi akasarin mutanen dake wajen suka juyo suna kallonta.

Tabbas Nitsuwarta na daya daga cikin dalilan da suka sa aka bata ragamar wannan shirin.

Kasan cewar manyan mutane masu kamala da shahara ake gayyatowa, so ana buƙatar mai nitsuwar da zata martaba musu manyan baƙin su.

Cikin kula. Uban gidan nasu yaci gaba da cewa.

“Shirin baƙon mako, yana da manufa mai girma, ta samo manyan mutane ta tattauna dasu, su sanarwa duniya nasarorin su da kuma irin ƙalubalen da suka fuskanta domin.

Su kasan cewa matasanmu masu tasowa, Maduban gina TUBALIn rayuwarsu ta yadda zata inganta su, tsare kansu da lalatacciyar tarbiya suyi karatun da sana’a domin watan-wata rana su zama abun koyi abun so wa yan baya.”

Shiru ya ɗanyi tare da kurɓar ruwan Lemun exotic din dake gabansa.

Ita kuwa Jannart na’urar maganar dake gabanta take ɗan sa fararen yatsunta wanda sukaji red henna tana sama tana ƙasa dasu a hankali.

Yayinda duk saura kuma sukayi shiru.

A nitse yaci gaba da cewa.

“But now I’m sorry to say Jannart, shirin ya raunata sosai. Yananin tsaron da kike ciki yasa bakya sakewa ki samu ki gayyato mana manyan mutane, shahararrun masu nagartan da zasu burge mutane.

 Shiyasa shirin yayi rauni mafi akasarin ranaku sai dai aita maimaita program ɗin daya gabata.

Wannan dalilin yasa muka samu umarni daga sama.

Aka bamu zaɓi biyu.”

Da sauri Jannart ta lumshe idanunta kana tayi ƙasa da kanta, saboda fahimtar inda kalamanshi suka dosa.

In ta gane ana gab da  sallamarta daga aikin. Wanda nanne kaɗai duniyar farin cikin ta, in ta shiga cikine kadai take samun ta sake, tayi raha tajita mai eanci babu Escort, ba Yah Junaidu a kusa.

A hankali tasa yatsarta ta ɗan ƙara saƙala na’urar dake saƙale a kunnenta wanda shike ƙarawa jinta ƙarfi, yadda take ɗan taune lips ɗin ta na ƙasane ya bawa kyakkyawan Dimple ɗin ta damar lotsawa, yayinda jajayen lips din nata suke sheƙi dan lasarsu da ta ɗanyi.

A hankali A’isha Lawal dake gefenta tasa hannunta ta kama nata tana ɗan murzawa alamun bada ƙarfin guiwa.

Salman kuwa dake fuskantar ta, idonshi ya rumtse.

Da sauri ta buɗe idonta jin shugaban nasu yaci gaba da cewa.

“Umarni na forko wannan karon an bamu sunan mutumin da ake son mu gayyato, yazo ayi hira dashi.

Domin shi kadai ne zai ɗaga darajar shiri.

Sai kuma  cewa in har bazaki iya samun dama da lokacin sakewa ki nemishi ba, to dole a sauƙeki kan shirin. 

A nemo wata ko wani da zasu iya.”

Cikin nitsuwa ta ɗan kalleshi kana a hankali cikin tsoron rasa aikinta tace.

“In sha Allah zan iya”.

Da sauri ya kalleta.

Kai ta jinjina alaman.

“Yess zan iya”.

Kai ya jinjina kana yaci gaba da cewa.

“Sai umarni na karshe, dole a nemishi, ya zama next 2 week’s dashi za’ayi hira. Kinga kenan yau saura kwana goma kenan.”.

Asiya ce dake masifar son amsar ragamar program ɗin daga hannun Jannart.

 Ta gyara zamanta tare da cewa.

“Sir waye ne shi? A ina yake?”.

Cikin ɗan ɗaga sauti yace.

*”Dr Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara ne”*

Da sauri duk suka fara kallon juna, cikin kaɗuwa Aisha Lawal tace.

“Sir Rayyern Bashir Muhammad Mai-nasara, shifa…”

Hannunshi ya ɗaga mata tare da cewa.

“Na sani, shi ba mutum ne kamar kowaba, ra’ayin shi da banne.

Ko BBC bata taba samun nasarar yin hira dashi bako!?”.

Da sauri kab suka amsa da.

Yess! Yesssss!!”.

Ajiyan numfashin ya sauƙe tare da cewa.

“Toh wannan itace nasararmu in har an samoshi.

Zai zama mujallar Arewa ce zata taɓa fidda hirarshi da hoton fuskarshi kana, Arewa 24 TV ce zata taɓa haska fuskarshi da surar jikinshi bayan sunanshi daya zama sananne a Africa baki ɗaya.

Wannan shine zai ƙara ɗaga darajar shirin. 

Shin Jannart zaki iya? Ko dai kai tsaye asa Asiya?”.

Da sauri Asiya tace.

“Sir Ni zan iya, tunda bani da wani tsaron nuna isar cewa ni ƴar wanice, aikina shine isata”.

Mafi akasarin mutanen wurin ido suka zuba mata ganin yadda take mgna tana watsawa Jannart harara.

Ita kuwa Jannart glass din idonta ta gyara tare da ɗagowa jin shugaban nasu na cewa.

“Jannart zaki iya ko dai yanayin tsaron da mafahifinki ke baki bazai barkiba?”.

Cikin sanyi da danne fargabarta tace.

“Sir zan iya  in Sha Allah. A bani kundin bayaninshi”.

Ajiyan zuciya Salman ya sauƙe jin cewa ta amsa zata iya, baya son rasa abokiyar aikinsa sabida yana jin daɗin aiki da ita.

A’isha Lawal kuma ajiyan zuciya ta sauƙe.

Shi kuwa MD’n su, wani file mara girma ya tura gaban Jannart tare da cewa.

“Gashi sai dai babu komai nashi a ciki, sai sunanshi, da sunan Company’s ɗinshi, da garuruwan da suke. Da Hospital’s ɗinshi. Da kuma foundation ɗin sa, mai suna Mainasara Foundation.”

Jin yayi shiru ne yasa ta ɗan kalleshi kana a hankali tace.

“Ba phone number ɗinsane, ba picture dinsa? Ba address ɗin sane?”.

MD ne ya ɗan gyara zamanshi tare da cewa.

“Toh Jannart ai da akwai waɗannan abubuwan a ciki, toh da bazaiyi wuyar samuwa ba kuma da bazai zama mutum na musamman ba, kunsa duk abinda yake killace shine special.”

Sai kuma ta juyo ta kalli mai kula da shirin nasu dake cewa.

“Babu number sa, ba hotonsa ba adireshinsa. Kana ko akwai number sa, ko sau 1000 zaki kira da layuka 1000 ma-ban-ban-ta bazata shigaba,  sabida yana amfani da App ɗin nan da in dai bawai yayi saving number ki a wayarsa bane, kiran bazai taba shigaba.

Kuma koda ya ajiye ya shiga, zaki kira a ƙalla sau goma bazai amsaba, sai dai ace mikin ki  ajiye mishi voicemail.

  Sabida yawan aiyuka da uzurrukan da mahaifinshi ya ɗaura masa yasa bashi da isashen lokacin kansa ma, da yawan mutane suna matuƙar jinjina masa da mmakin kwazonsa, sabida aiyukan sun mishi yawa, kana matashine a tsakiyar dattijai.

To shiyasa bai cika samun lokacin amsa kiraba.

Sai dai a ajiye mishi saƙo, so nanne zakiji muryarsa, idan abinda ke tafe dake mai mahimmanci ne, kuma kinyi hikimar faɗa mishi number ki to shida kanshi zai kira”.

Mafi akasarin su ajiyan zuciya mai nauyi suka sauƙe.

Cikin karaya Jannart tace.

“My Aunty to Ina kikaji duk wannan bayanin?”.

Dariya Hajia Rabi’ah tayi tare da cewa.

“Jannart yar jaridar gaske wato, tuni har kin fara binciken tun yanzu a kuma kaina”.

Murmushi tayi tare da gyaɗa kai.

MD kuma kai ya jinjina sabida gamsuwa da hikimarta da nitsuwarta wurin aikinta.

Cikin girma Hajia Rabi’ah tace.

“Toh gsky nima wurin  PA’nsa na samu wannan bayanin.

 Ba kuma wurin PA din kai tsaye ba.

Akwai ɗan yayata, abokin ƙanin PA’n nashi ne, so nan naji wannan.”

Cikin sauri ta miƙawa Hajia Rabi’ah wayarta tare da cewa.

“Samin number ɗan yayar taki”.

Murmushi tayi ta amsa tasa mata number.

Kana tace.

“Sunanshi, Mahmoud”.

“To” tace kana ta adana number.

Shi kuwa MD’n gyara zamanshi yayi yaci gaba da tsara musu sauye-sauyen programs ɗin nasu.

Sai kusan ƙarfe shida saura suka tashi a taron.

Suna fitowa, mafi akasari suka kama hanyar parking lot ɗinsu dan daukan ababen hawansu.

Wani irin kallo mai cike da tsana Asiya ke bin Jannart dashi lokacin da suka fito, a take Escort ɗin ta suka miƙe suka mara mata baya.

A hankali ta ɗan juyo jin Aisha Lawal na kiranta.

“Jannart! Jannart!!”.

Juyowa tayi tare da bin tsakiyar hanyar da suka buɗa matan.

Da sauri A’isha Lawal ta iso, cikin sanyi tace.

“Zaki iya?.”

Cikin jin tsoron rasa aikinta, ya zama dole taita zaman gidan da yafi na kurkuku muni da zafi.

Tace.

“Na’am A’isha zan iya, in sha Allah. In ban iyaba naci gaba da zaman gida, Yah Junaid zai k’arasa kurmatani da marukan da yake yayyarfa min a cikin ko wani mintuna, wurin aikin nan shine duniyata, shine TUBALIn ɗan y’ancina, ya zanyi sakacin  rasa aikina”.

Cikin rauni da ƙara yin ƙasa da murya Aisha tace.

“Okay Salman yace ince miki in sha Allah zaku iya, kuma zai roƙi a baku cikekken dama, da zai biyoki sai ya tuna waɗannan kattin dake zagaye dake wanda suke shirye da ilkata duk wani na miji in yazo kusa dake”.

Kai ta jinnina kana sukayi sai anjima.

Wasu dalla-dallan motoci ne guda, uku.

Ta tsakiya itace a baya.

Ta baya kuma ƴan tsaronta, hakama na gaba.

Tana baya a zaune.

Yayinda driver’n ta ke janta.

A haka suka nufi gida tana mai jin tsoron me zata riska a gida, kasan cewar ta wuce lokacin dawowarta.

Anguwa ce mai zaman kanta Janbulo tsit anguwar ba hargitsi, da hayaniya, da kwata kamar ba cikin kano ba, sabida manya-manyan gidaje ba irin gidajen kanawa mitsi-mitsin nan ba.

A bakin wani tamfatsetsen gida mai ɗan karen girma da kyau, suka tsaya tare da danna hon.

Jiki na rawa mai gadi ya buɗe musu.

Nan suka ratsa cikin gidan.

Suna isa parking space ana kiran sallan magriba.

Wanda yayi dai-dai da fitowar Alhaji Idi Sale Dakata daga cikin gidansa tare da zaratan samari uku Junaid Azeez Abdul a bayanshi.

Da wani mutum wanda suke kama da juna Barrister Kabir Saleh Dakata kaninsa kenan.

Wata iriyar sassayar ajiyar zuciya mai nauyi ta sauƙe fahimtar Yah Azeez zai koma wurin aikinsa dan taga ana sa kayansa a mota, alamun ana idar da salla zasu wuce Airport dashi.

Murmushi Barrister Kabir yayi tare da cewa.

“Masha Allah, Ammina kin dawo kenan”.

Da sauri ta matso kusa dashi tare da kaucewa mugun kallon da Yah Junaid ke watsa mata, cikin sanyi tace.

“Eh Abba na dawo, ina  Aunty Dija”.

Ta k’are mgnar tana kallon fuskar Yah Azeez d’in da yakeyi mata kallon mai cike da tausayawa,

Barrister Kabir kuwa wanda ta kira da Abba Cikin kula da tsananin tausayinta da danne wani abu can ƙasan zuciyarsa yace.

“Suna ciki shiga bari muje masallacin”.

Da sauri tace to. 

Kana tayi cikin gida su kuma suka nufi masallaci…

   *Ethiopia Addis Ababa.*

Wani kyakkyawan matashine mai wani irin tsabtaceccen kyau mai masifar ɗaukar hankali, matashine mai jini a jika. 

 Wani irin kimtsestsen taku mai cike da nagarta, nitsuwa, kamala, haiba, yakeyi, yana mai fitowa  habarar wani kyakkyawan Asibitin.

(Tikur Ambess Teaching hospital Addis.) 

Yayinda wasu manyan likitocin da ƙasar Ethiopia ke ji dasu ke biye dashi a baya, kana da Nurses.

 Taku yakeyi cikin kamala da haiba, a hankali yake motsa lips ɗinshi bisa dukkan alamu, gajiya ce ta sashi hakan ɗin.

 Fari ne mai masifar kyau irin farin mutanen ƙasar Ethiopia sai dai fatarsa tana da haske fiye data sauran dake biye dashi a baya bi’ma’ana ya ɗan fisu fari.

 Yana da wani irin hanci mai ɗan karen kyau, da tsini, idanunsa masakaita masu masifar kyau da fari, irin idanun nan ne da in sun cicciko da hawaye in akwai abu a gabansu kalar idon kan iya komawa haka, wani irin kekkyawan saje ne mai masifar kyau ne kwance lib a fuskarsa yayi mishi ƙawanya, lips ɗinshi ƴan sirara jajaye masu kyau, sai girarsa masu kyau.

Wani irin askine mai ɗan karen kyau bisa kansa.

Sosai kamanninsa da Dheeraj-Dhoopar suka fito ras hatta tsawonsa da ɗan jikinsa kamar na Dheeraj-Dhoopar ne komansa dai-dai misali.

Daga shigarsa zata nuna wanene shi.

Wani irin masifeffen  Suit ne a jikinsa mai ɗan karen tsada, red colour mai maiƙo, riga da wondo sai ɗigon fari-fari, kana necktei ɗin wuyanshi shima fari sai ɗigon ja-ja’n.

Haka takalmanta sau ciki, toms farare ƙira company’n Italy sai harafin R-M da akayi da red color. irin ta matasa. Masu kima da daraja sai agogon hannunsa ƙirar Gucci shima da harafin R.M a gefe da gefe. Shigar tayi masifar mishi kyau da kamala.

Taku yakeyi suna biye dashi a baya.

Har suka iso inda motocinsu ke jere.

*DR. Rayyern Bashir Muhammad  Mai-nasara kenan.*

Cikin nitsuwa ya juyo yana mai miƙa wa  Dr Adeym hannu cikin nitsuwa suka ɗan yi mgna, kana duk sauran ma suka bashi hannu.

Kana ya shiga mota, Driver’n’shi dake ciki yaja.

 Suka fita cikin asibitin.

Kai tsaye.

  Hera Addis hotel Ethiopian, suka nufa.

A kan hanyarsu ne, suka bi kusa da wani babban masallacin.

Cikin sauƙe numfashi ya cewa, Driver’n’shi.

“Tsaya”. A taƙaice

Da sauri yace to.

Kana suka tsaya ganin ya nufi cikin masallacin ne suka fahimci me zaiyu.

Nan suka mara mishi baya, dan yin sallan isha’i kasan cewar lokacin ta yayi daga nan kuma suka wuce.

A hankali ya maida kanshi ya jingine jikin kujerar idonshi ya lumshe tare da motsa lips ɗinshi a hankali yana sauke numfashin gajiys.

Yana jin wayarshi na ringing Amman ko idonsa bai buɗeba sabida tsananin gajiya, kayan jikinsa kansu nauyi sukeyi mishi, bacci yakeji da  kuma yunwa.

Shiyasa bai amsa kiranba.

 Sai dai cikin zuciyarsa yace.

“Sulaiman!!!”. 

Sai kuma ya ɗan mirgina kanshi gefe.

Ganin sun iso.

Da sauri mutanen dake cikin motar dake biye dasu a baya suka fito ɗaya daga cikin sune ya matso.

Buɗe mishi marfin motar yayi kana ya matsa gefe.

A hankali yace.

“Bismillahi”. 

Numfashin gajiya ya ɗan fesar.

Kana ya zuro ƙafarsa woje.

Sai kuma ya ɗan kalli Usman PA’nshi dake tattaro System ɗin shi da wayoyinshi.

Kana a hankali yace.

“Ɗauko small bag ɗin can.”

Da sauri Usman yace. To.

Kana ya ɗauko ɗan jakar leda mai ɗauke da tambarin Edna Mall Addis Ababa Ethiopian. yabi bayanshi suka nufi cikin HOTEL ɗin.

Kai tsaye inda masauƙinsu yake suka nufa.

Suna shiga ya juyo ya kalli Usman daya ajiye mishi kayyakin nasa bisa kujera.

“Sai da safe, bazanci komai ba, kada Sulaiman ya dameka kace zaka zo ka dameni”. Yayi mgnar cikin gajiya.

Cikin sauri yace.

“Okay Sir”.

Yana mai kunce net ɗinshi yace.

“Toh jeka”.

Toh yace tare da juyawa zai fita.

 Sai kuma ya ɗan juyo yana kallonshi jin yana cewa.

“Ramadan ya kira ɗazu”.

Kai ya gyaɗa mishi kawai.

Ganin haka Usman ya juya ya fita.

Yana ganin ya fita, ya matso ya rufe ƙofar.

Yana juyowa yana cire Suit ɗin, bisa kujera ya cillata, kana ya cire ta cikin.

Sunkuyowa ya ɗanyi yana kunce belt ɗin ƙugunshi.

Yana daga tsaye ya zare wando .

Yana son sakewa shiyasa yake jin daɗin rayuwar kaɗaici.

Sabida yana masifar kunya da suturce surar jikinsa.

Ko dan yanayin halittar jikinsa mai gargasa ne, baya son koda Ramadan ne yaga koda damtsen hannunshi bare sharaɓarsa bare aje ga cinyarsa, da tattausan gargasa yayi masu ƙawanya. 

So Amman in shi  kaɗaine yana sakewa, wasu lokutan daga falo yake fatali da kayyakinsa kafin ya shiga bedroom ma daga shi sai boxes zai shiga.

Tattare kayan yayi ya wuce dasu Bedroom, bisa gado ya ajiyesu.

Kana ya wuce Bathroom.

Bayan ya fitone ya kimtsa cikin wasu tattausan riga da wondo iya guiwa farare ƙal.

Turare ya ɗan fesa, kana ya ƙara gudun A’C sannan ya koma parlon ya ɗauko ƴar jakar da yasa Usman ya ɗauko mishi wanda yake cike da chocolates kala daban-daban.

Masu sanyi a daskare.

Sosai ya ci Galaxy Chocolate mai ɗan karen daɗi kamar yadda ya saba ta’ammali da kayan zaƙi.

Bayan ya gama ne, kuma yasha tea mara haɗi, wato coffee. Bayan ya kammala ne kuma  ya dawo Bedroom riƙe da system a hannunshi.

Kashe wutan ɗakin yayi, kana ya kwanta.

tare dasa l system ɗinnasa a gaba.

Ajiyan zuciya ya sauƙe, Allah ya sani yana jin wani irin nishadi da sanyi na musamman in yana jin wa’azin Dattijon nan, Malam Mai-nasara, yana son tafsir din shi.

Baya gajiya da kallon fuskar tsohon.

Wannan yasa yake bibiyar shafin shi na You tube inda yake saka tafsiransa.

Lallatsa system ɗin yayi.

Jim kaɗan sai ga hoton ya bayyana.

Fuskar dattijon ya zubawa idanu.

Har bai jin abinda ake magana a kai.

Sai da yaji iska na ɗan cika mishi ido ne, ya ɗan lumshe idanun tare da sauƙe numfashi, kana ya buɗe su.

Kan rubutun dake ƙasan hoton Dattijo ya kuma kalla. Malam Mai-nasara”.

Cikin sanyi can ƙasan zuciyarsa yake magana.

“Ƙarshen sunanmu iri ɗaya. Ni dai nasan Tubalin nawa sunan. Toh shi kuma menene TUBALIn nashi sunan Mai-nasara,  menene asalin sunan?”.

Wa zai amsa mishi waɗannan tambayoyin da zuciyarsa taƙi dena mishi su?

Numfashin gajiya ya sauƙe kana ya kauda tunanin yaci gaba da jin tafsir ɗin nashi.

Jin bacci zai kwashesa ne yasa ya rufe na’urar ya kwanta yana mai buɗe tafin fararen hannunshi yana addu’o’in. 

Yana idawa ya shafa ya kwanta.

              Kano Nigeria. 

Sulaiman ne zaune bisa kujera matarsa, Sumayya na gefenshi.

Da sauri yace.

“Ikon Allah”.

Juyowa Sumayya tayi tana cewa.

“Lfy?”.

Da sauri ya matsota tare da cewa.

“Kiji ikon Allah wai Riyyam-nsra, wannan ɗan Ethiopia da nake ce miki yana masifar kama da Rayyern wai zaizo Nigeria”.

Leƙowa tayi ta kalli fuskar wayarshi, inda yake TIKTOK yana bisa shafin Riyyam-nsra.

“Kai gsky kam Ni kaina ina ta’ajjudin kamanni Rayyern da yaron nan, kamar ta ƙazanta”.

“Uhumm ni kaina na gaza daina mmakin kamanninsu.

To amman kin kuma ji wai zaizo Nigeria”.

Riƙon da tayiwa yarsu ta gyara tare da cewa.

“Abban Nihal me abun mamaki don zai zo Nigeria, kasan celebrity’s da yawo kamar jirage”.

Kanshi ya jinjina tare da cewa.

“Sumayyah ba zuwansa Nigeria bane abin mamaki.”

“Toh menene abin mamakin”.

Ta tambayeshi cikin kulawa.

Juyo mata fuskar wayar yayi.

Da sauri ta zsro idonta waje cike da mamaki tace.

“Dama H…!

“Hausa ya keyi fa ko?”. Cike da kaɗuwa Sulaiman yace.

“Eh abinda ya ban mamaki kenan.” 

Sai kuma ya kalleta jin tana cewa.

“Koda yake ba mamaki  wani ne ya rubuta mishi, tunda kaga ai yace.

Ethiopia Addis Ababa to Nigeria kano State. Kanawa zan zo muku.

Wata ƙil wani ne ya rubuta mishi”.

Komawa yayi da baya ya jingina bayanshi da jikin kujera. 

Numfashi ya ɗan fesar tare da cewa.

“Kai Sumayyah gsky da mamaki fa.

 Kalli Comments ɗin mutane fa da amsar da yake basu.”

Ya ƙare maganar yana shiga  comments section ɗin ƙasan video’n da ya saka a shafin nasa.

Inda wani Abis Fulani yake cewa.

“Eyyeh Riyyam-nsra a Nigeria, kanawa nama fatan isa lfy”.

Cike da mamaki Sumayyah ta kalli amsar da ya baiwa Abis Fulani.

“Ngd aboki na”.  da alamun musabaha.

Sai kuma tayi ƙasa ganin inda wani.

Ahmad MG ya fara mgn da zaro ido alamun mamaki tare da cewa.

“Riyyam-nsra da yin Hausa, ko mafarki nakeyi”.

Dariya yayi tare da bashi amsa.

“Noh Ahmad zahiri ne”.

Tofa wannan abun yasa comments ɗin mutane zubowa kamar ruwan sama domin shi dai ɗan ƙasar Ethiopia ne, kalarsa, harshensa, cimarsa, rayuwarsa, komai na canne, bai taɓa koda maganar Nigeria a shafinsa ba, sai gashi yau kuma yayi video cewa zaizo Nigeria, kuma yana rubutu da hausa yana kuma karantawa.

Cikin kaɗuwa Sumayyah taci gaba da bin comments ɗin mutane na farko-farko da ya iya basu amsa sabida yawan mutanen.

Cikin mamaki tace.

“Lah kalli tambayar da wani ya mishi.”

Amsar wayar Sulaiman yayi.

Ya fara duba saƙon da Imran yayi mishi.

“Riyyam-nsra kasan Nigeria ne? Ko Ka taɓa zuwane? Ko wannan ne zuwan da zakayi na forko?”.

Alaman murmushi yasa tare da cewa.

“Nasan abu da yawa kan Nigeria”.

“Da sauri yace gaya min kaɗan daga ci.”

“Ok kamar me kake son in gaya maka”.

Da sauri yace.

“Ka iya taken ƙasa. Ko rantsuwar al’ƙawarin ƙasa.”

Cikin lumshe ido, Riyyam-nsra dake kwance a ɗakinsa.

Ya rubuta mishi amsa, da bari in baka amsar a video.”

Take kuwa ya tashi zaune yayi taken ƙasarmu Nigeria ƙasarmu ta gado kana da rantsuwar al’ƙawarin ƙasa.

Wannan video da ya saki 

Yayi matuƙar jan hankali al’ummar Hausawa duniya baki ɗayansu more Especially ƴan Nigeria bama ya kanawa.

Da sauri Sulaiman ya fara rubutu.

A karo na forko a rayuwarsa da zaiyiwa wani comment a TIKTOK.

Rubutu yayi cikin harshen nasara.

“Hey Riyyam-nsra you knew much about Nigeria you are a patriot”.

Yayi mgnar da gayya ne dan ya gano ko dai ɗan Nigeria ne basaja ne da karya yasa yake ciwa ɗan Ethiopia ne, wata ƙil karatune ya kaishi can.

Murmushi yayi tare da rubuta mishi amsa.

“Baƙon Nigeria dai mai kishin Nigeria amman ni ɗan Ethiopia ne.

Sai dai Nigeria ƙasar babban abokina ne da mukayi karatu tare a US.”

So daga ganin wannan video, akai ta cewa.

“Haba shi yasa mana.

Nasir Ahmad ne wanda shine abokin nashi ya fito, yanata mishi tsiya a nashi shafin. Nanfa aka gane sanadin zuwansa da kuma inda ya koyi Hausa ras.

Ɗan gajeren tsaki Sulaiman yayi tare da cewa.

“Wadannan yaran gaba ɗaya TIKTOK ta haukata mana matasa wanda sune TUBALIn al’umma sai gashi kuma muɗin ma suna shirin haukatamu”.

Dariya Sumayyah tayi tare da cewa.

“Dama haka ai Rayyern ɗin ke ce maka, in baka dena biyewa social media ba, zaka rasa lokacin kanka”.

Kwaffa yayi tare da rufe datarsa kana yace.

“Nima fa Ibrahim ne ya sani fara wannan abun sabida, kamannin Rayyern da wannan yaron.”

Daga nan sukaci gaba da hira kan kamanninsu.

Washe gari da safe ranar talata.

Gidan Alhaji Idi Sale Dakata.

Su kusan shida ne cikin falonshi.

Wanda huɗu daga cikin manyan yan kasuwane masu faɗa a ji masu juya sule ta koma million ɗaya ko tako wanne irin halin ƙaƙama ko talaka zaiji daɗi haka ko bazai jiba.

Biyu daga ciki kuma ƙusoshin gwamnati ne masu ƙarfin iko daga ta jiha zuwa ta ƙasa.

Alhaji Yawale ne ya gyara zamanshi tare da cewa.

“Yaron nan fa yanayi mana illa ba tare da mun ankare ba.

Gaba ɗaya ya rarake tubalin da mukayi tsawon shekaru muna ginawa muna samun wuri na jawo mana wuri.”

Cikin tsananin takaici Alhaji Abdu Tababa ne yace.

“Tun-tuni nake gaya muku haka.

Mu kauda yaron nan a doron ƙasa shine kawai mafi sauƙin mu.

Kunaga yadda kasuwan cinsa ke haɓaka,  kamfanonin sa suna bunƙasa daga Arewacin Nigeria har ya koma kudanci ya kafu.

Uwa uba yanzu duk ƙasashen  Afrika yanada rassai.

 Ya maida kayan abinci da araha tamkar ruwan sama cikin damuna.

Duk inda ka shiga a kasuwannin Mai-nasara race, ke cike.

A farashi mai sauƙi ta yaya za’ayi a saurari kayan kamfanonin mu”.

Ɗaya daga cikinsu ne ya miƙe tsaye tare da cewa.

“Ni tambaya ta a kullum ma shine

menene Tubalin kasuwancin yaron nan?

Yaushema aka haifeshi? Sa’an yaran cikin mune fa!

Ta ina ya samu Wannan tarin dukiyar da har ya samu damar razana mana kasuwanci ya raunata mana Company’s.

Yaushe yayi ginin duk a lokacin ɗaya menene Tubalin dukiyarsa da matakan ikonsa!?.”

Ya ƙare maganar yana kallon Bala Tambari wanda shine shugaban tsare-tsaren ginin masana’antu a gwamnatance, dole sai yasa hannu za’ayi gini  ya za’ayi ka bashi izini da damar yin gini a duk inda yake so a ƙasar nan”.

Cikin takaici Bala Tambari ya fesar da numfashi tare da cewa.

“Tsohon yarjejeniya ne, yana da dukkan abin buƙata, yanada sa hannun da suka gabaceni kuma kan tsari suke.

Naso in ƙalu balanceshi.

Tun shekaru biyar baya lokacin da ya fara gina babban campany dake Nan birnin Kano wanda yanzu yake gab da kammalashi so naga komai da hujja yakeyi.

Yaron shegen taurin kai ne dashi, gashi da ɗan banzan tsaurin ido.

Kana mgna zai tsira maka waɗannan siraran idanun nashi masu kama da soyayyan gujjiya, tsakar idon ka ya baka amsa da hujjar da baka isa kayi mgna ba”.

Dr.Lukman ne ya fesar da iska a baki tare da cewa.

“Ni ta ko ina ya tosheni

A fannin likitancin gaba ɗaya yana bi yana rarake privet Hospitals.

Ɗan banzan komai na asibitinsa mai sauƙi kuma ga kula ya za’ayi aje irin namu asibitocin.”

Alhaji idi Sale Dakatane ya miƙe a fusacen shina kana yace.

“Nifa gaba ɗaya ya ta’azzara min campany na na shinkafa.

Sannan kafin kace ka motsa sai ka samu ya toshe ko ina.

Hegen yaro mai jajayen kunnuwa.

Yana nan tamkar Wahainiya, samun ganinshi ma ya zamewa mutun aiki.”

Dr Lukman ne ya ɗan sauƙe numfashi tare da cewa.

“Cikin satin nan zai dawo Nigeria yanzu haka yana Ethiopia yaje, shugaban kasar can da kanshi da manyan likitocin sune, suka karrama shi.

Sabida taimakon da yayiwa wasu daga cikin mutanen ƙasar Ethiopia cikin Airport kan hanyarsa ta zuwa US, dan karramashi a matsayin ɗan kasuwan da yafi ko wanne sauƙin farashin kayan masarufi.

Kaga yana tafi kuma yazo wai kuma Ethiopia zasuyi mishi wata karramawar.

Yaro kamar ɗan ruwa, komai yasa kai sai Nasara”.

Bala Tambari ne, ya kalleshi tare da cewa.

Toh yanzu dole kai zaka nema mana zama dashi.

Yana dawowa muna buƙatar shi mu gwada sayan farashinsa.

Muyi mishi tayin harƙallarmu yasan irin ribar da muke shigarwa, wata ƙil zai amince mu haɗa hannu in kuma yaƙi tabbas zamu gina mishi gadar zare.”.

Da sauri Alhaji Idi Sale Dakata yace.

“Uhumm ai In Kuma yaƙi amincewa mu haɗa hannu.

Toh lokacin wasan zai fara, dan in taurin kaine da gsky da samun ƙarfin iko bai kai.

Mai-gaskiya da wasu ba, da muka gama dasu shekaru ashirin da biyu baya ba, danni cinnaka ne ban bar na gida Bama, bare shi baare.”

Haka dai suka tashi a taron nasu.

A nufin sai ya dawo su zauna dashi.

A cikin gidan kuwa. Jannart ce ke 

Tsaye a kitchen, inda take sanye da wani half gown mai masifar kyau wanda ya d’an bayyana fararen legs d’inta, rigar irin mai kauri da kama fatar jiki dinnan ne, wanda hakanne kuma yasa had’add’iyar Surar jikinta dan bayyana, kasancewarta y’ar gayu, Tabbas Jannart macece mai matuk’ar son fashion, shiyasa hatta suturun da take sawa ya banbanta da sauran na y’an Nigeria, saboda sometimes tafi yin shiga irin na wasu daga cikin larabawa, ko kuma shigar mutanen turkey🇹🇷.

Tsaye take a kitchine din cikin kuma nutsuwa take aikinta.

Yayinda Mom ke tsaye a gefenta.

Cikin kula Mom ta kalleta tare da cewa.

“Jannart kamar Yayanki ne ke kiranki”.

Cikin bugawar zuciya tace.

“Yah Junaid!?.”

Da sauri tace.

“Eh shi dai”.

Bugawa zuciyarta ya kumayi, tare dajin wani iri acikin jikinta, saidai kuma babu yanda ta iya, haka ta juya cikin sanyi ta nufi falon.

Can tsakar falon ta hangoshi tsaye,  saurayi ne, mai murd’addiyar Surar jiki da kuma tarin gashi akansa irin busu-sun nan, duk da cewar kyawun nasa bawani na zarce hankali bane amma baza’a tab’a k’iransa da mummuna ba, wata riga

marar hannuce ajikinsa, sai kuma wondon dake jikinsa wanda ya tsaya masa iya guywa.

Bisa alamu kuma yanzu ya tashi daga bacci.

saboda yanda idanunsa sukayi jazir.

Kallonta yayi, tare kuma da d’an cije labb’ansa, still Cikin binta da wani irin mayataccen kallo yace.

“Kije ki share min ɗakina”.

Fuskarta ta d’an b’ata cikin kuma tsanar shiga ɗakin nashi tace.

“Yah Junaid breakfast nake haɗa mana”.

A fusace ya juyo kanta cikin takaicin abubuwan dake haɗe mishi a kanta ya yarfa mata wani irin gigitaccen mari a kan kunneta na dama, saida ya bada wani irin sauti ƙauuuuu! Da ɗan karen ƙarfi.

A gigice tasa tafin hannunta ta tallabe ƙuncin ta.

Yayinda wasu taurari suka fara gilma mata a gani.

In da sabo yaci ace fuskarta ta saba da marukan Yah Junaid Wanda tun tana yarinya take shansu gashi sanadin su, kunnuwanta sun samu matsala jinta ya raunata.

Wasu irin hawaye ne masu masifar zafine suka silalo mata.

Ba tare da tace komaiba ta juya ta nufi ɗakin shi.

Ta yaya zuciyarta zata samu sauƙin ɗan uwanta da take bata da wani sama dashi tunda shine suke uwa ɗaya uba ɗaya amman yafi kowa tsanarta a duniya.

Ba shaƙuwa ko tausayawa a tsakaninsu.

Sannan mahaifinsu babu ruwanshi ko a gabanshi Junaid zai daketa babu ruwanshi sai yayi kamar baya wurin ma.

In Mom tayi mgna ya gwatsaleta yace babu ruwanta sunfi kusa.

Wannan ne ya ƙara tsananta zubda hawayen ta.

A haka ta fara tattara mishi falon da gaba ɗaya ya birkitashi.

Shigowa yayi ya zauna yana mai Binta da ido, duk inda tayi.

Wani irin abu yakeji a kanta.

A hankali ya miƙe yabi bayanta lokacin da ta shiga Bedroom.

Da sauri ta juyo jin shigowarsa.

Gefenta ya matso fuska a murtuke hakan ne yasa bugun zuciyarta ya ƙara tsananta.

Har kana iya ganin yadda numfashin ta ke fita da yanayin tsoro.

Fuska ya kuma murtukewa.

Kana yace.

“Munafuka, sai kace da gaske haka kike tsoron maza, ji yadda kike tafiya ba bra kina wani karkakaɗa ƙirji irin ke gaki ƴar iska mai son maza ko?.”

Idanunta ta rumtse da k’arfi cikin kuma ƙunan ran ƙazafin da Yah Junaid ke jifarta dashi murya na rawa tace.

“A’a”.

Cikin haɗe fuska ya daka mata tsawa tare da cewa.

“Toh meya hanaki sa bra?”.

Murya na rawa tace.

“Dr. Lukman ne yace in daina sa bra, sabida matsalar numfashin da Athsman ɗina ke jamin. In nasa ya matse min ƙirji sai numfashina yayi ta shaƙewa”.

Wani irin dogon tsaki yaja tare da cewa.

“Ubanki zanci in baki dena raina min hankali ba, matse ƙirjin da ƙatti keyi bai shaƙe numfashin ba sai saka bra ne zai cushe miki numfashin.”

Fice min da gani!!”. Ya k’are maganar a tsawace.

Jin hakanne kuma yasa da sauri ta juya ta fita, hawaye na zubo mata sabida raɗaɗin marin daya yarfa mata da zafin kalaman zargi da yake binta dasu.

A falo ta samu Mom da sauri ta faɗa jikinta.

Cikin sakin sassayan kuka tace.

“Mom ki gaya musu wlh ni ba yar iska bace, Meyasa Mom Meyasa Ya Junaid ke jifana da mugayen maganganu, shifa yaya nane..” 

Jawo hannunta Mom tayi suka zauna bisa kujera, a hankali tasa tafin hannunta tana share mata hawaye cikin yin ƙasa da murya tace.

“Na sani Jannart kuma Allah ya sani, ke ba ƴar iska bace. Yaushe ma kika samu sakewar rayuwar duniya kullum kina cikin takunkumi.

 Ko ina zakije da masu gadinki.

Na rasa wannan masifar tsaron na menene kina girma ana ƙara killaceki kamar abun rashin gsky.”

Cikin shessheƙan kuka tace.

“Mom shi Yah Junaid gani yake, su masu tsaron nawa dasu nake iskanci.

Daddy Kuma gani yake in ya cire masu tsaron da wasu zanyi iskanci.

Wlh na sani Mom bawai dan tsaron lfyata bane yasa Daddy ware min masu tsaro.

Shima zargina yakeyi ko Mom?”.

Jin yadda numfashin ta ke fitane yasa mom gyara zamanta kana ta fuskanceta da kyau.

Allah ya sani tana son Jannart tamkar ƴar cikinta.

Amman duk yadda zatayi bata burge Alhaji Idi da Junaid, gani suke kamar so take Jannart ta lalace ne don ba ita ta haifeta ba.

Cikin kula da tausasawa uƙubar da suke shayar da ita tace.

“A’a Jannart Daddynku baya zarginki, shi ya bada masu tsaronkine sabida larurar ciwonki, kina buƙatar makusanci a koda yaushe, tunda abu kaɗan ke tada miki athsman ɗin wanda kinga tun da yana nimoniya, kina girma yana canzawa ya riƙa har ya zama asman shiyasa yake tsananta kulawa a kanki.

Sabida abu kaɗan ke tada miki shi.

Kuma Yah Junaid ɗinki yana sonki.

Ɗan uwa, uwa ɗaya uba ɗaya ya wuce wasa.

Sun haɗa da son da Mamanki zatayi mikine da tana raye”.

Cikin zubda hawaye tace.

“Mom kin bani son da ya kamata uwa ta bawa ƴarta, ni banyi maraicin kyakkyawan tarbiyar uwa ta gari ba.

Kawai dai basa so nane”.

Cikin kafeta da ido Mom tace.

“Jannart ki yarda dani, tashi muje kici abinci”.

Cikin nitsuwa tasa hannunta ta share hawayenta kana ta miƙe.

Dinning area suka nufa.

Suna zama Daddy ya fito da hakama Junaid da Abdul.

Nan suka zauna sukayi breakfast.

A hankali ta sauke numfashi ganin Junaid ya miƙe ya bar wurin.

Sai kuma ta ɗan kalli Alhaji Idi Saleh Dakata.

Cikin takatsantsan da girmamawa tace.

“Daddy Ina son zanje gidan Aunty Rabi’ah akwai wani aikin da zamuyi a can”.

Ido ya ɗan zuba mata.

Ita kuwa da sauri tayi ƙasa da kanta.

Tana tasbihi cikin ranta, da addu’ar Allah ya ɗaurata a kanshi.

Juyawa yayi ya fara sauƙa kan steps ɗin tare da cewa.

“Kada ki daɗe.

Kuma ƙafarki ƙafarsu Sunday.”

Cikin sabo da hakan tace.

“Toh”.

Kana ta miƙe ta nufi ɗakinta. Mom kuma ta fara tattara kan table ɗin.

Wanka tayi cikin nitsuwa da kuma sauri-sauri.

Tana fitowa, ta zauna ta tsane jikinta kana ta busar da tattausan suman kanta.

Ta shafa mishi mayuka, sannan ta tubkeshi.

Mai ta ɗan shafa kana ta Murja farar hoda, tare dasa man baki.

Sosai tayi kyau duk da bata cika kwalliya a fuskarta ba.

Wasu tattausan riga da wondo pallazo farare ƙal ta zaro,

Sai wata doguwar riga budaddiya mai igiya a tsakiya.

 pantie tasa, kana ta zira dogon wondon daya kasance yayi tightin fatar jikinta.

Dole sa bra baya cikin jadawalin rayuwarta sabida larurar ciwonta.

Sai dai takan sa rigunan su ɗan matseta.

Rigar ta zura irin mai wuyanan nane wato, high neck, naɗe wuyan tayi ta gyarashi.

Cib-cib rigar tayi mata a jikinta gwanin burgewa ƙirjinta yayi cas a tsaye babu alamun ronƙofowa bare zubewa.

Lafaffen cikinta ya taimaka kwarai wurin bayyana tsayeyyun breast ɗinta.

Doguwar rigar kimono blue color mai ɗigon fari-fari’n ta ɗaura saman riga da wondon, cib kuwa kimonon yayi mata ajikinta, inda kuma har ƙasa yazo mata.

Igiyoyin dake sarƙafe tsakiyan rigar ta kama ta ɗaure.

Hakan ya bawa tsakiyar rigar haɗewa, sama can kan ƙirirjin ta kuma gefe da gefen ya rufu har ya samu damar rufe nimples ɗin ta.

Sai kuma tsakiyan bai ida rufuwa ba.

Sai kuma can ƙasa ta nan zaka gane riga da wondone a ƙasan doguwar rigar farin mayafi rigar ta dauko tayi Rolling kanta fuskarta ta fito a ciki kamar sifili (0) a ciki.

Sosai shigar tayi masifar mata kyau.

Wanda kuma sune suturunta na yau da kullum wanda tafi so da jin daɗin sawa, kasan cewar rigunan cikin masu taushine suna buɗuwa dai-dai jikinta.

Turare mai sauƙin ƙamshi ta  fesa, sanin sa mai tsananin ƙamshin yana da illa ga baliga in zata fita da kuma lfyarta.

Wasu fararen takalma sau ciki masu taushi tasa.

Kana ta zari babbar wayarta kiran iphone11promax ta fito.

A bakin ƙofar shigowa falon tayi kiciɓis da Mom cikin.

Yanayin sakin fuska Mom tace.

“Kai masha Allah ɗiyata kinyi kyau”.

Cikin yanayin jin daɗi tace.

“Ngd Mom bari inje da wuri in samu in dawo da wuri”.

“Toh hamzarta ɗiyata, sai kin dawo”.

Toh tace kana ta fita ta tafi.

Tana fitowa harabar gidan

Wadannan garadan marasa kan gado suka miƙe baki ɗayansu.

A hankali ta matso kusa da Driver’n’.

Cikin kula yace.

“Jannart yau kuma ina zamu je, naga yau ba ranar aiki bane?”.

Cikin jin daɗin yadda dattijon ke mata mgn ta mutuntaka tace.

“Baba Ado, gidan Hajia Rabi’ah zamuje”.

Marfin motar ya kama da nufin buɗe mata, da sauri tace.

“Baba Ado ka bari zan buɗe”.

Murmushi yayi kana ya bude mata,  ta shiga.

Suma sauran suka shiga sauran motocin suka tafi.

Suna isa gidan Hajia Rabi’ah.

Bayan sunyi parking ta nufi cikin gida su kuma suka zauna a waje.

Da sallama a bakinta ta tura ƙofar.

Da sauri taja da baya ganin Asiya dake fitowa.

Sai kuma ta shigo ganin taja gefe tana hararanta.

Da sauri tayi ciki jin Hajia Rabi’ah na cewa.

“A a Jannart kin iso ko.

Maza shigo daga ciki”.

Cikin jin daɗi ta shigo.

Ta zauna inda Hajia Rabi’ah ke nuna mata.

Cikin girmamawa tace.

“My Aunty Ina kwana”.

Murmushi tayi tare da cewa.

“Lfy lau Alhamdulillah ya ƴan  tsaron ki”.

Cikin yin gajeren murmushi tace.

“Gasu can a tsaye a bakin gate tamkar dogaran sarki”.

Dariya ta ɗanyi kana ta kalli wani ɗan matashi dake zaune can bisa kujarar Dinning area tace.

“Toh Mahmoud ga Jannart ɗin ta iso.

Tunda kaƙi bawa Asiya amsa ko ɗaya”.

Da sauri ta juyo ta kalli inda aka kira Mahmoud.

Shi kuwa tasowa yayi ya nufo cikin falon yana mai cewa.

“Aunty naga kamar hasadace ke cinta, kuma ma bada ita nai wayaba.

Ita kuma wanna sai saiɓi.

Kin san tun safe ina nan kin ajiyeni kamar mara aikin yi”.

Cikin nitsuwarta tace.

“I’m so sorry. Ina kwana”.

Gefe ya zauna kana yace.

“Wuni dai tunda 12 tayi”.

Nan suka gaisa kana Jannart ta fuskanceshu da kyau.

Cikin sani makamar aiki tace.

“Yaushe jirgin Ethiopia zai diro Nigeria a wanne gari ɗaya Abuja ko Lagos ne?”.

Murmushi Mahmoud yayi tare da cewa.

“Wato zaki nuna min ke yar jaridace, tuni kin fara tambaya da wayo.

Jirgi zaki tambaya ko shi?”.

Kwaɓe fuska tayi tare da kallon Hajia Rabi’ah kana a hankali tace.

“My Aunty menene ma sunan nashi?”.

Cikin zuba mata ido Hajia Rabi’ah tace.

“Iyeh wato ma har kin mance sunan nashi. Kin manta cewa sunan nashi ne kawai makaminki.”

Cewar Hajia Rabi’ah.

Ita kuma Jannart takwara kanta tayi bisa kafaɗa kana tace.

“Please my Aunty gaya min zan riƙe”.

“Rayyern”.  Ta bata amsa a takaice.

Ita kuwa ido ta lumshe tare da fesar da numfashi can cikin zuciyarta tace.

*”RAYYERN! RAYYERN!! RAYYERN!!!* Ta maimaita sunan sau uku kana ta juyo ta kalli Mahmoud cikin nitsuwa tace.

“Mahmoud ranar yaushe zai dawo? Da wanne lokacin jirginsu zai iso daga Abuja ko Lagos zuwa Kano?”.

Gyara zamanshi yayi kana yace.

“J….!

Back to top button