Hausa novels

Halysaah Page 46 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 46…Washegari da safe bayan Khaleesat ta shirya cikin tsadadden Abayan da Momy ta bata, Momy ta gama hada mata shayin da take yi cikin cup tace “To zo kiyi breakfast din kar ya huce Mamana” Khaleesat bata ce komai ba ta karasa ta zauna kan darduman da aka jera mata breakfast din, Momy tayi murmushi tace “Idan farfesun bai isheki ba sai ki bude warmer ki ƙara, dankalin ma akwai saura a warmer in bai ishe ki ba” Ita dai Khaleesat kai kawai ta gyada mata, tana juya shayin gabanta a hankali da spoon din ciki, Momy ta koma kan kujera ta zauna tana kallonta tace “Duk da ma ina lura jiya baki wani ci abincin da aka kawo maki da yawa ba, ko maganin cin abinci zan sa a samo maki mamana” Khaleesat tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba ta dau shayin tana kallon ciki, sai tayi tunanin lipton din ne kilan ya fashe a cikin ruwan shayin, sipping din shayin tayi kadan ta ajiye sannan ta fara cin irish din, Momy dai kallonta kawai take kasa kasa, Bude kofar dakin aka yi Momy ta juya, ganin Abdul tace “Sai yanxu ka tashi Babana” Bai ce mata komai ba ya karasa ya zauna saman kujera, Khaleesat ta ɗan kallesa taga kallonta yake, sauke idonta tayi a hankali tace “Ina kwana” Ya kauda kai yace “Lafiya” Momy tace “Ka tashi kaje kayi breakfast din ka” Yace “Momy za mu je shopping ne, bata zo da kaya ko daya ba” Momy na kallonsa tace “To wanda ka gani a jikinta yanxu kai ka siyo mata?” Shiru Abdul yayi yana kallon Momy, Momy tace “To har na tura ma Meemah kudi su je su yi mata siyayya ita da Karima tunda kai baka da ƙara” Mikewa Abdul yayi ya nufi kofa ya fice daga dakin, Momy ta bi sa da kallon gefen ido, sai da Momy taga Khaleesat ta gama cin abinda zata ci na breakfast din sannan ta mike ta fita ta kira mai aikinta ta fitar da sauran abubuwan da Khaleesat ta rage, bayan mai aikin ta fita Momy ta bude bayan labulenta ta dauko wani karamin jarka ta kawo ma Khaleesat tace “Wannan tsumi ne Mamana, daga yanxu har zuwa dare nake son ki shanyesa gaba daya” Ita dai Khaleesat kallon jarkan take, Momy tace “Kin ji ai ko?” Khaleesat ta gyada mata kai tace “Toh Momy” Momy ta dauka ta mayar bayan labule sannan tace “In zaki yi kallo sai ki kunna TV abun ki, bari in je zanyi bakuwa ban san ko ta iso ba” Khaleesat tace “Toh” Momy ta fita daga dakin ta kulle da makulli tana rike da makullin ta sauka downstairs don aminiyarta godiya ta kirata ta sanar mata tana hanya, tana shigowa parlor taga Abdul zaune dinning area da breakfast din da Khaleesat ta rage a gabansa, da karfi Momy ta kwala masa kira, ya juya yana kallonta, ta karasa wajen da mugun sauri tace “Banda abun ka ba ga naka a kitchen ba Abdul me zaka yi da wanda aka rage? Ko har kaci wannan din ne?” Abdul dake kallonta yace “Ban ci ba, amma menene idan na ci?” Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da sauri Momy ta kunduma mata wani ashar tace “Nan nace ki ajiye sauran abincin er iska kawai er neman jidali? Me yasa ke dakikiya ce? Wallahi zan kore ki fa a gidana na gaji da maganar da kike sa ni kamar kanwar uwarki, yau ga shegiyar mata kawai” Abdul ya kalli Momy yace “Ni fa nace ta kawo min nan, beside what is wrong with the food da bazan ci ba?” Momy ta mata tsawa tace “Dauka ki wuce ki ban waje guntuwar banza kawai” Mai aikin na ba Momy hakuri ta dauke jiki na rawa ta tafi kitchen da breakfast din, Momy ta kalli Abdul dake kallonta, yace “I want to understand meye da abincin da bazan ci ba Momy?” A takaice Momy tace “Kayan gyaran mata mana? Ko kai na mace ne?” Bata jira cewarsa ba ta bar wajen ta shige kitchen ya bi ta da kallo, Tuttular da shayin tayi a sink sannan ta juye sauran irish din da kwai da farfesun duk ta cakudesu waje daya tace “Gasu nan ki kai ma karnuka, in kuma kwadayin ki ya ja ki kika ci ke kika jiyo” Mai aikin ta risina ta amsa tace “Toh Hajiya” Sai da Momy ta jirata har ta dawo bayan ta kai ma karnukan can cage dinsu sannan Momy ta dau breakfast din Abdul ta kai masa kan dining din tace “Ga naka nan” Daga haka ta juya ta bar wajen, dai dai shigowar Godiya gidan, da fara’a Momy ke mata sannu da zuwa Abdul ya dauke kai kamar bai ganta ba don ya tsani matar with passion, tun asali dama baya gaida ta, Haka Momy ta ja ta zuwa sama tana cewa “Mu je ki ga surkar tawa ku gaisa” Da ido Abdul ya bi su har suka haura sama, Momy na isa kofar dakinta ta bude da makulli suka shiga, Khaleesat dake gyara gadon Momy ta mike tsaye tana kallonsu, Momy na murmushi ta kalli godiya tace “Kin ganta” Da fara’a sosai Godiya tace “Maa sha Allah, ai ko ga ta kamar balarabiya Maa sha Allah, sannu amarya, ya sunanki?” Momy na murmushi tace “Sunan Baabata gareta, Hauwa sunanta” Khaleesat ta zame kasa ta sauke idonta ta gaida Godiya, Godiya ta karasa kusa da ita ta dafata tare da ɗagota ta zaunar da ita gefen gadon Momy tace “Lafiya lau diyata, ya bakunta?” Khaleesat bata ce komai ba kuma bata dago kanta ba, Momy na kallon Khaleesat tace “Kin sha tsumin da nace ki sha kuwa?” Khaleesat ta gyada mata kai tace “Na sha” Momy tace “To maa sha Allah, Allah ya maki albarka Mamana, zuwa anjima sai ki kara sha kin ji” Khaleesat tace “To” Bayan few minutes Momy da Godiya suka fita dakin, Momy ta sake kulle kofar da makulli sannan ta cire makullin suka tafi wani daki dake sama, bayan sun shiga Momy ta kulle kofar tana kallon Godiya tayi murmushi tace “Duk tayi amfani da abubuwan babu gardama godiya, iya na jarkan nan ne kawai ya rage yanzu” Godiya ta zauna gefen gado tace “To madallah, shi ma Abdul din duk kinyi yanda aka ce kiyi da na sa?” Momy tace “Kwarai kuwa” Godiya tayi wani murmushi ta bude handbag dinta ta ciro wani babban laya bakikirin da shi ga er karamar kwado a jiki ta mika ma Momy tace “To aikin karshe kenan wannan Hajiya, Malam ya ce ki samu inda kika san baza a taɓa tono sa ba ki binne a cikin gidan nan” Momy ta zauna gefenta tana murmushi ta amshi layan tace “To laya nawa na binne gidan nan ba a tono ba godiya, ai wannan karamin aiki ne a wajena don ba sabon abu bane” Godiya tace “Yauwa, bayan kin binne Malam yace ki basa yarinyar kawai, wallahi yace min in har ta wuce sati biyu Abdul bai rabu da ita ba to bazata wuce sati biyar ba a gidansa” Fara’ar fuskar Momy ya bace tace “Har sati biyar Godiya? Ni da yace min sati daya kacal a waya” Godiya tace “Halan bai gaya maki irin abubuwan dake ƙan dan ki bane? Da yaya ma aka samo kansa har asirin nan yayi tasiri? Ai abubuwan ƙan Abdul sun fi karfin wani asirin wallahi kiji in gaya maki” Momy ta sauke ajiyar zuciya tace “An taɓa gaya min haka da dadewa wallahi, don ni akwai malamin da yace min ma yanda asiri ke cin ubansa shi sai an wahala asiri zai ci sa” Godiya tace “To wallahi Malam sai da ya tura masa aljanu don ma ki ji Hajiya, aikin nan sai da Malam ya hada da wasu malaman don aiki ne me wahalan gaske yace min wallahi” Momy tace “To ni fargabana kada fa in mika masa yarinya ace asirin nan bai ci ba abinda muke gudu ya afku mu shiga uku Godiya” Godiya tace “Sai kace yau Malam ya fara maki aiki? Ai da aikin bai yi ba kinsan bazai boye mana ba, sai dai ya kara mana lokaci yayi wani sabon aikin fa, dama yace in na yarinyar ya ci shine zai sa na Abdul din ma yayi tasiri sosai” Momy tace “Haka ya ce kam” Godiya tace “Don haka zuwa gobe ki basa ita kawai su tafi an gama aiki sai jiran result, kuma ina me tabbatar maki zaki sha mamaki” Momy na murmushi tace “Toh shikenan godiya, nagode sosai, zan tura masa cikon dubu dari biyar dinsa anjima” Da yammacin ranan bayan Momy taga Abdul ya fita gidan tayi maza ta aiki mai aikinta kasuwa saboda tayi amfani da daman ta haƙa rami a garden din gidan ta binne layan da Godiya ta kawo mata, bayan mai aikin ta tafi Momy ta zaga zuwa garden din gidan ta samu spot me kyau ta fara haƙa rami da wuka, bayan ta haka yayi zurfi yanda take so sannan ta jefa layan ta mayar da ƙasan wajen ta dau wani dutse ta dora dai dai wajen don kada a ga alamar an tono kasa, tap ta bude don wanke hannunta da wuƙan da tayi using, Khaleesat ta karasa bakin window din dakin Momy jin ƙaran bude ruwan pampo, in ta gaji da zaman dakin dama jikin window take zuwa ta tsaya tana kallon waje, ta tsaya jikin window din tana ta kallon Momy dake ta wanke hannunta bayan ta wanke wuƙan, bayan ta gama ta kara komawa kusa da dutsen tana seta sa da kyau ta yanda ko da wasa baza a ga tonannen ƙasa ba, sai kuma ta mike ta fara tsinko doddoya dake Garden din, sannan tayi using wuƙan hannunta ta yanki pumpkin leaves isasshe bayan ta gama ta bar garden din tana rike da ganyayyakin hannunta, babu abinda Khaleesat ta kawo a kai don tunaninta ganye Momy taje diba a garden din, Momy na kai ganyayyakin kitchen sai ga su Meemah sun dawo daga shopping din da ta aikesu su yi ma Khaleesat, dariya Momy ta dinga yi a parlor ganin wasu shegun abayoyi masu saukin kudi da suka kwaso ma Khaleesat irin wanda ake dinkawa a kano, ga wasu shegun dogayen riguna su ma masu arha, hatta inner wears da suka siyo duk very low quality ones ne, babu wani abu na arziki da suka siyo ma Khaleesat, Momy na ci gaba da dariya tace “Duk maida su cikin ledojin kawai na yafe ganin wannan tarkace haka karima, amma baku da kirki yaran nan” Aunty Karima na dariya ta maida kayan cikin leda ta kulle tace “Su ne dai dai er talakawa ai Momy, da so kika yi ki ga abayan dubu hamsin zuwa sama? Ai ita Meemah ma en gwanjo ta so mu je muyi selecting mata kawai” Dariya kawai Momy take, ita kuwa Meemah danna wayarta kawai take don duk wani abu da ya shafi Khaleesat ko kadan baya bata dariya, she just can’t wait taga irin rabuwan da Abdul zai yi da Khaleesat don shine babban abinda ke gabanta yanxu. Wajen karfe takwas da rabi Momy na zaune parlor da Abdul tana ta yi masa hira, shi dai wayarsa kawai yake dannawa baya responding kamar ma bai san me take cewa ba, Momy ta kwalo ma mai aikinta kira, Mai aikin ta taho da gudu tace “Na’am Hajiya?” Momy tace “Zaki ga Kankana da na yanka a kitchen ki dauko ki kai ma Mamata a sama” Mai aikin tace “To Hajiya” Juyawa tayi ta koma kitchen sai ga ta ta dawo rike da bowl din kankanan tana kallon Momy cikin ladabi tace “Amma Hajiya dakin a kulle yake” Momy tace “A’a a bude yake tun daxu, ki je ki kai mata” Bayan mai aikin ta tafi ta kai water melon din ta dawo ta tafi kitchen ta ci gaba da aikin da take, Momy ta dau wayarta tace “Bari in inyi waya da Alhaji, daxu na ga kiransa ina kitchen wallahi” Shi dai Abdul bai ce mata komai ba har ta shiga dakin dake downstairs ya bi ta da kallo… Bayan minti biyu ya mike ya nufi stairs direct ya tafi bangaren Momy, yana bude kofar dakin Khaleesat dake zaune saman darduma bayan ta idar da sallah ta gama duk addu’o’in da zata yi ta juya ta kalli kofar, sosai gabanta ya fadi bayan sun hada ido da Abdul, ya karasa cikin dakin babu yabo babu fallasa yace “Ta shi mu je shopping….” Khaleesat da gabanta ke faduwa ta nuna masa ledan da Momy ta kawo mata daxu duk da bata duba kayan ciki ba cikin sanyin murya tace “Ai Momy ta sa an min shopping din, ka gan su can ma” Ya hade rai yace “Kee… Get up nace, i am not asking for ur opinion” Ta sauke idonta ta mike tsaye da kyar ta dauke darduman tana linkewa, sosai taji hankalinta ya tashi, a ranta ta dinga addu’an Allah ya kawo Momy dakin immediately, fixge darduman hannunta yayi ganin it’s taking her a whole eternity to fold, ya ajiyesa saman kujera sannan ya kama hannunta suka nufi kofa fuskarsa a daure suka fita daga dakin, Khaleesat dai bin sa kawai take a tsorace, downstairs suka sauka har sannan yana rike da hannunta, babu kowa a parlorn sai mai aiki dake goge goge a dining area, ya dau makullin motarsa da ya bari kan center table, Khaleesat ta marairaice masa cikin rawan murya tace “Ya Abdul Momy fa bata sani ba, kar ta shiga dakinta taga bana nan, kaga babu dadi haka” Wani kallon da yayi mata yasa tayi shiru zuciyarta na bugawa, bata sake gigin ce masa komai ba har suka fita parlorn gidan zuwa parking space, Khaleesat taji hawaye ya cika idonta bayan ya sa ta shiga motarsa ya shiga driver seat, mai gadi ya bude masa gate ya fice gidan da motar. Momy ta fito parlor tana kallon Mai aikinta tace “Naji kamar fitar mota, waye ya fita?” mai aikin tace “Alhaji karami ne ya fita” Momy tace “Shi da wa?” Mai aikin tace “Shi da matarsa” Shiru Momy tayi don bata yi tunanin zai ce zai tafi da Khaleesat yau ba, don so tayi taga yanda za su kwashe, shi yasa ma ta basa hint din dakinta a bude yake, ta zata can din kawai zai bi ta ko kuma ya kai ta dakinsa, Momy ta sauke ajiyar zuciya, ganin mai aikinta sai kallonta take ta hade rai tace “Lafiya kike kallona haka munafuka?” Da sauri mai aikin ta juya ta bar wajen, Momy ta juya ta koma daki amma fa zuciyarta ya kasa nutsuwa sam sam, gani take kamar Abdul zai yi tarayya da Khaleesat, duk da malaminta bai taɓa mata aiki bata ga result me kyau ba amma a wnn case din sai take ɗari ɗari kada abinda suke gudu yaje ya afku dama ga Godiya tace aikin me wahala ne, ai kuwa da ta shiga uku ta lalace, number Godiya tayi dialing ta zauna gefen gado tana jiran tayi picking. Hawaye kawai Khaleesat take tana dafa shayin da Abdul ya sa ta dafo masa a kitchen, ita ta ma riga tayi give up yau don bata da wani dubaran da ya rage mata in ba so take ta fusata Abdul ya doketa ba, she will just accept her kadr with good faith, gwara tayi accepting dinsa kawai a mijinta tunda haka Allah ya kaddara mata, goge hawayenta tayi tana tafiya a hankali ta tafi kai masa lipton din dakinsa, tana bude kofar ya ajiye wayar hannunsa yana kallonta, kanta a kasa ta karasa har inda yake ta duka ta ajiye masa black tea din, ta mike zata bar wajen ya jawota ya zaunar da ita gefensa yana kallonta, ita dai bata bari sun hada ido ba zuciyarta na wani irin bugawa, ya dago kanta suka hada ido, sauke rigar baccin jikinta yayi slowly yana kallonta babu ko kiftawa, ta sunkuyar da kanta bugun zuciyarta ya tsananta sosai, tana ji tana gani ya cire duk abinda ke jikinta yana kare ma each and every part of her body kallo, bata sake yarda sun hada ido ba, a hankali ya kwantar da ita, ta runtse idonta da sauri jikinta na rawa ganin inda yake kokarin kai bakinsa, after some seconds Khaleesat ta bude idonta a hankali tana kallonsa jin bai yi abinda yayi niyya ba, taga wani wajen daban yake kallo babu ko kiftawa, after some seconds ta ga ya mike ya nufi kofa ya bude, fuska daure yake kallonta babu yabo babu fallasa yace “I need my privacy…..” Khaleesat ta mike zaune da kyar tana kallonsa, lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta jawo Hijab dinta da ya cire tun zuwansu gidan ta saka sannan ta dau kayan baccinta ta nufi kofa, bata bari ta hada ido da shi ba ta fita daga dakin taji ya kulle kofar da makulli, juyawa Khaleesat tayi tana kallon kofar…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button