Uncategorized

Macijine Shi Page 3-4 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Page 3/4

________________Cikin tsoro take shafa dogon abun dan jin ko menene,tabbas MACIJINE dan kuwa har kansa ta taɓo.

Aikuwa da hanzari ta janye hannunta cikin kidima ta fara ja baya tare da fasa wani irin gigitaccen ƙara,

“Ahhhhhhhh wayyo Allah baffa maciji!maciji !!maciji!!!”gaba É—aya ta kidime abinda take iya faÉ—i kenan jikinta na rawa kamar É—an mazari.

Allah Sarki baffa dama ba wani barci yake yi ba ,dan yana kula da  É—akin fattu ,kasancewar É—akin yana gaf da Æ™ofane,dan haka jin ihunta da yayi ,yasa shi tashi agigice ya nufi É—akin nata.

Haskawa yayi da tocila can ya hangota jikin bangon ɗakin ta duƙunƙu ne tana ta ihu,da alama batama cikin hayyacinta.

Da sauri ya nufeta yana kiran sunanta”fadimatu !ke fadimatu menene ?ya isa haka gani akusa dake baffanki ne kinji daina ihun “baffa ya faÉ—a cikin Æ™asa Æ™asa da murya dan karya Æ™ara tsorata ta.

Ita kuwa gaba É—aya ta rikice kawai kira take “baffa maciji zai sareni baffa wayyo Allah na”

Ganin halin da take ciki ne yasa baffa ya fara tofa mata addu’a ,cikin minti biyu kuwa tayi shiru sai rawa da jikinta ke famanyi,ahankali ta daga kanta ta sauÆ™e kyawawan idanunta akan baffan nata,kawai saita saki kuka tana mai cewa”baffa MACIJINE yake son  sarina aradu da idonsa na ganshi anan”ta faÉ—a tana nuna masa gurin dataga macijin.

Kallon gurin baffa yayi ,shifa ba abinda ya gani agurin ,kawai yana tunanin ko mugun mafarki tayi,dan haka cikin Æ™okarin kwantar mata da hankali yace “shike nan fattu ya tafi maza koma ki kwonta kiyi addu’a ba abinda zai sameka kinji”ya faÉ—a cikin yanayin Hausar su ta Fulani.

Cikin kuka take girgiza masa kai “aradu baffa dawowa zaiyi tun daga rafi suke son cinyeni baffa ,bazan iya kwonshiya Ni kaÉ—ai ba”ta Æ™arasa tana mai matsowa kusa da baffan.

Shiru yayi yana tunanin mai ya kamata yayi,dan gaskiya yaga ta tsorata da yawa,dan haka cikin Æ™arfin hali yace “tashi muje gurin hansai saiki kwonta shan ko”ya faÉ—a cikin tausaya wa.

Ai kafin ma ya rufe bakinsa ta kai ƙofa,dan ita kam babban burinta ta bar ɗakin nan,tama manta da gurin wa baffan yace taje.

Ahankali baffa cikin É—an tsoro yake tura murfin É—akin na hansai harya buÉ—e shi duka.suna kwance abinsu kan gado ita da yaranta su uku,na miji É—aya sai mata biyu Dukansu basu kai fattu shekaruba, da alama na mijin zaiyi shekara sha uku,matan kuma basu fi sha daya ba.

Kuma dan rashin tsari irin na goggo hansai da ita da yaranta duka suke kan gadon ,har na mijin.

Ahankali baffa ya karasa yana dan bubbuga fillon da hansai ke kwance ,sai uban munshari take zabgawa,banda wari ba abinda dakin keyi.

“Hansai!hansai!!”baffa ya faÉ—a cikin Muryar tsoro,dan yasan idan ta farka saitayi masa bala’in ya tashe ta tana barci.

Juyi tayi tare da goge yawun barcin dake zuba abakinta taci gaba da barcinta.ahankali ya fara kiran sunanta da É—an karfi “Hansai ! Hansai!!” Har sau biyu.

BuÉ—e ido tayi ahankali ta sauke su akan baffa dake tsaye ,buÉ—e idon tayi sosai cikin bala’in ta tace “to jarabarce ta motsa haka da cikin dare zakazo ka dameni?to wllh garama ka koma inda ka fito dan ba abinda zaka samu agurina ,wannan jaraba dame tayi kama ,ko sati biyu bakayi da saukemin jarabarka ba shine yanzu ka Æ™ara jajiÉ“o jiki kazo ka sake ko ?to wllh banda lokacinka kaficemin daga É—aki”ta faÉ—a cikin masifa tana juya masa baya.

Girgiza kai yayi cikin jin kunyar fattu ,dan yasan taji abinda gwogwgo take faÉ—i ,kuma ai ita ba yarinya bace bare ace bata san me hakan ke nufi ba,tunda tana karatun addini.

Cikin sanyin murya yace “ashsha Hansai ba wannan ta kawoni ba ,dama ina neman alfarmar fattu ta kwana anan ne daku,dan  bazata iya kwana ita kadai ba ,atsorace take “ya faÉ—a cikin shakkun zata amince ko yaya.

“Kan ubannan yau kuma da wannan sabon munafurcin kuka zo ?fattu ta kwana aÉ—akina ,lallai in baka mutu ba zakaga ikon Allah,da can  da ubanwa take kwana? sai yau zakace ta kwana aÉ—akina?yarinyar mayya wato cikin dare ta lashemu ko?kai baka da asara,to ku ficemin aÉ—aki ,Allah yasa abinda yake tsoratatan ya cinyeta ta mutu kowa ya huta “tana gama faÉ—in haka ta juya taci gaba da barcinta.

Sosai maganganunta suka É“atawa baffa rai ,saidai bashi da damar magana ,kai kawai ya girgiza yace “muje fattu” 

Kuka sosai fattu keyi na tausayin su ita da baffanta ga wannan matsalar dake ƙoƙarin Kunno mata kai ,basu da gata sai Allah kawai.

Suna fita baffa yace “shiga É—akina ki kwanta fattu,Ni bari na je É—akin naki kinji”ya faÉ—a cikin sanyin murya.

Girgiza kai tayi tace “baffa Zan koma É—akin nawa In kwanta kaima kaje É—akinka ,idan gwagwgo tasan na kwana aÉ—akinka yanka Ni zata yi,dan ta hanani shiga É—akin”ta faÉ—a tana mai share hawayenta tare da nufar É—akin nata ,gabanta naci gaba da bugawa.

“Kiyi hakuri fattu komai yana da iyaka kinji,Allah zai miki sauyi Na alkairi”baffa ya faÉ—a yana mai mika mata tocila ya ce ki haska ki kwanta kinji ,kiyi addu’a”

Karba tayi tare da É—aga masa kai ta koma cikin É—akin.

Daga bakin Æ™ofa ta tsaya tare da haska É—akin ko ina ,ba abinda tagani aÉ—akin ,hakan yasa tayi zamanta bakin Æ™ofar É—akin da tocilan É—in ta ko yaya taji motsi saita zabura ta  haska .

Sam awannan daren bata sami damar runtsawa ba ,ga sanyi da garin ya É—auka sakamakon ruwan da aka zabga jiya.

Sai gabannin asuba sannan barci É“arawo ya saceta. 

Wani irin azababben sanyi daya ratsa Æ™asusuwan tane  sakamakon ruwan sanyin da gwagwgo ta kwara mata ,shine ya sanyata zabura ta miÆ™e da sauri tana haki,kafin ta gama dawowa cikin hayyacinta kuma taji duka yana sauÆ™a ajikinta ta ko ina ,ihu ta fara tana neman taimako amma ba wanda yazo dan taimakon nata,dan baffa yana masallaci kasancewar shine limamin rugar,

“Wayyo Allah na gwogwgo kiyi haÆ™uri wllh bazan Æ™ara ba ,tsautsayine yasa na fashe miki bokati, dan Allah kiyi haÆ™uri gwogwgo”abinda fattu ke daÉ—i kenan cikin azaba dan ko ina na jikinta ciwo yake mata barin ma hannunta daya kumbura sosai ,alamun tayi targaÉ—e a  hannun kenan.

“Wllh yau saina kasheni Shegiyar yarinya muguwa, kafin baÆ™in cikinki ya kasheni ,na Tsaneki fattu bana Æ™aunar ganinki arayuwata, kinsan nawa nasai bokatin nawa?kika je kika fashemin shi? Murtala huÉ—u da nairagoma fa na siya,wllh saina daki

ina kuma  kije duk inda zaki samo min kuÉ—in bokatina ki samomin dan bazan É—auki asarar ba”gwogwgo ta faÉ—a tana haki,kuma bata daina jibgar fattu ba ,kamar ta sami jaka.

“Wayyo gwogwgo dan Allah kimin rai hannuna zai karye, wllh bada gangan na fashe miki bokati ba,macizaine suka biyo ni zasu cinyeni shine na gudu amma bada gangan nayi ba wllh”ta faÉ—a cikin azaba dan tuni Æ™arfinta ya kare ko iya É—aga hannunta bat.

“Allah ya tsine muku keda mashizan shegen yaro karuwa ,ina ruwana da macizai ?dama sun cinyeki kowa ya huta mai baÆ™in hali marar farin jini har yanzu kin kasa auruwa ,dama shegun macizan sun…….kasa Æ™arasa magannarta tayi  sakamakon wani Æ™aton abu dataji ya faÉ—o kanta jifff !!!kamar buhun hatsi.

“Wayyo Ni Hansai menene wannan É—in yake zagayemin jiki?ta faÉ—a cikin firgici da tashin hankali tana mai jefar da iccen hannunta.aikuwa carab idanunta suka sauka akan Æ™aton macijin daya nannaÉ—eta ko motsi bata iya yi,kuma ya fasa kai a saitin fuskarta sai huci yake yana Filato da harshe.

“Wayyo Allah na Ni hansai yau me zan gani ?na shiga ukuna malam kazo fattu ta min ture maciji zai kasheni ka taimakeni, handi É—in bonu lalashewa ni yar nan wayyo malam”ta faÉ—a cin tsantsar tsoro da razani da Æ™yar take magana dan ba Æ™aramin shaÆ™ar mata jiki macijin yayi ba har wuyanta.

Tsoro,fargaba da tashin hankali sune suka daɗa kashewa Fattu jiki ,dan faɗuwa tayi ƙasa warwas ko motsin kirki bata iya yi,shikenan Tata ta ƙare yana gamawa da gwogwgo tasan kanta zaiyo ,Allah Sarki innarta ,yanzu shikenan zata mutu bataga innarta ba,batasan ya fuskarta take ba ?bare tasan dangin innarta?,amma Gara ta mutumma ta huta da wannan baƙar azabar da take sha agurin gwogwgo.

Shikuwa macijin nan ƙara matse gwogwgo yake sosai ,gaba ɗaya ta fice daga hayyacinta,dan ko magana ma ta kasa ,idanunta sunyi jajur sai nishi take numfashinta na ƙoƙarin ɗauke wa.

Saida macijin nan yaga gwogwgo bata motsi alamun ta suma,kafin ya sake ta  ta hanyar janye jikinsa daga gareta.

Da gudu kuma yayi kan fattu wacce ke kwance cikin tashin hankali ganin yadda macijin nan ya kashe gwogwgo.runtse ido tayi da mugun Æ™arfi tana salati da sallama da duniya,ko motsin kirki batayi ,dan  da kyar take iya jan numfashi ma.

Shikuwa macijin nan yana zuwa gareta ya tsaya saitin fuskarta ya fasa kai yana huci,sai kuma ya fara zagayeta cikin sauri da sassarfa, kafin kuma ya fara hayewa kan ruwan cikinta……..

Masu karatu mezai faru da fattu ?

Me macijin nan yake nufi da ita ne?

Anya ma macijin ne shi?

Saimun haÉ—e next page in Sha Allah taku har kullum anty mammy

Mrs babi💘💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment 

More typing.

Back to top button