Matar Hariji Page 20 Romantic Hausa Novel
Ajiyar zuciya tayi tace “dama dolene kake daukata mahaukaciya mana dolene kake daukata bansan abinda nakeyi ba”Shidai bai bari mgnr tayi qarfi ba ya tashi ya fice yace “zance gurin wani me magani a Doguwa don Allah ki kula da Hauwah yarinya ce Koda yake nasan Zulaiha ma zatazo.Ficewa yayi ya sake komawa bangaren Hauwah ya zauna a gefenta ya kamo hannunta yace “zanje Doguwa insha Allahu bazan dadeba magani zan karbo gurin wani mutum da Salees ya samomin lbrnsa, bata jaba tayi masa addu’ar dawowa lfy yayi kissing nata ya fice yana daga mata hannu.Daqyar ta tashi saboda ciwon da jikinta yakeyi ta dan gyara parlourn sama sama duk da dama ya riga ya gyara ta dauki mayafinta ta yafa ta sauka qasan a wahalce tayi saa sun dawo parlourn qasa ta zauna suka gaisa da kaka Fadwah ta taho gurinta.Daukarta tayi ta dubi Mubaraka ta gaisheta daqyar ta amsa ta miqa hannu zata dauki jaririn tayi saurin riqe abinta tace “ah haba yarinya ki jira lkcnki yazo kema ki dauki naki ai naga ya dage so yake sai yayi miki cikin Koda yake na gaba ai yariga yayi gaba banza dake”Itadai jiddah bata iya kulata ba saboda zazzabin da takeji a jikinta sunanan zaune zaman kurame sai Hauwah da Kaka suke Dan taba Hira lkc zuwa lkc Kaka tana mamakin mugun halin jikar tata ita bataga laifin namiji ba idan yanada halin ajiye mace sama da daya ba don ya ajiye amma Mubaraka ta dauki qunci ta dorawa kanta.Sai wajen 11:00am Hajiya ta iso gdan ita da autanta tunda taji tsayawar motarsu gabanta ya fadi, hakadai ta zauna har suka iso anata gaisawa shikuwa hankalinsa yanakan matar yayan nasa da kullum yake kwana da tunaninta.Zamewa Hauwah tayi daga kujerar ta gaida Hajiya ta kalleta a qasqance tace “me kuma wannan takeyi anan?” Tabe baki Mubaraka tayi tace “uhm inaji zaman sa ido tazo” dariya Hajiya tayi Zainab tace “lallai fah sa ido to atashi abamu guri tunda ba fadar tsoho bace.Jikin Hauwah yayi matuqar sanyi ta miqe a gajiye idanunta ya ciko da qwallah ta nufi qofar da zata shigar da ita bangarenta sukaja tsaki a tare tare da qwashewa da dariya Hajiya tace “don Allah jibi yanda take tafiya a wani tattale wai ita miji ya kwanta da ita ko uban waye baiji abinda tajiba”Duk da haushinta da muneef yakeji Saida yaji babu dadi akan abinda akayi Mata yace “haba Hajiya kullum sai ki rinqa abu kamar wata yarinya wannan bafa girmanki bane zaki zubarwa da kanki mutunci ne a banza kisa yarinya qarama ta rainaki inama ruwanki da tsakaninta da mijinta ne wai don Allah”Daquwa ta watsa masa tace “kaima saina sallama mata tunda duk sallamammu na haifawa duniya nifa kawai tsanar yarinyar nan a jinina take bazan taba sonta ba har abada” Itakuwa Jiddoh dakinta ta shiga ta fada saman gadon ta fashe da kuka sosai kalaman na surukarta suka kashe Mata jiki ta rasa meye yasa kullum Hajiyan Lameer bata fadan alkhairi akanta kullum cikin jifanta da mugayen kalamai take.Yini tayi surr a kwance zazzabinta ya tsananta har wajen magrib tana kwance, daqyar ta iya miqewa tayi sallah sannan ta dawo parlourn ta kwanta ta rufe jikinta da hijjab dinta tanajin sanyi yana ratsata bude qofarsa taji ta sauke numfashi tare da dagowa ya tako da sauri yace “lfy meye kuma Babe?” Fashewa tayi da kuka tace “tun tunda ka tafi kaina da cikina yake ciwo inajin kamar zan mutu” A gigice yace “amma bakida lfy gidan nan cike da dangina a rasa wanda zai kirani ya fadamin” fita yayi yana masifa ya sauka qasan ransa bai taba baci irin na yau ba ya rinqa qwala musu kira yana bala’i fadi yake “saboda tsabar an rainani an mayar dani dan iska ban isa na kafa doka a gdana a bita ba to wlh anyi kadan ayimin wannan iskancin a gdana, itama fa matatace kuma sonta nake fiye da yanda kuke zato da kowa zan iya keta riga akan lamarin daya shafi Hauwah tsabar wulaqanci jiya batada lfy bata fito ba kun rinqa kirana Kuna fadamin matata munafuka ce taqi fitowa cikin dangina ayi Hira da ita, yau taji dama dama ta fito kun koreta har kuna caccaba mata magana, kuma a rasa wanda zai bita yaganemin lfyrta hardake Hajiya bayan kinsan yarinyar nan amanace a gurina to wlh bazan dauki wannan iskancin ba daga yau kada wanda ya qara takomin gidana tunda zuwa kuke domin ku rabamin kan matana kun zabi wacce kukeso a ciki, saboda haka ku dauketa ku tafi da ita bana buqata wannan din da bakwaso ni ita nakeso” Duk wani wanda yake gurin saida cikinsa ya karta lallai ran maza ya baci yau ankai Lameer bango, miqewa sukayi sumsum suka fara ficewa bai jima ba ya dawo da gudu gudu ya haura saman ya daukota cak sai rawar sanyi takeyi ya fito da ita yasata a mota hajiya tabisa jikin motar ta Kira sunansa yayi saurin daga mata hannu yace “kiyi hqr Hajiya wlh bazan saurareki ba kece kike sabbabamin duk wani Abu da yake damuna a matsayinki na uwa kin dauki lalurata abar yayatawa a duniya kamar kaina aka fara nasani bantaba cemiki komai ba sannan kin fifita matar da take qarqashin ikona ni danki fiye dani still kina daure Mata gindi abinda takeso shi takeyi kin nuna mata banada wata daraja a gurinta haka qanne na saboda haka ki dauketa ku tafi da ita wlh a yau dai bazata kwana a gidana ba kiyi Mata daki a gidanki ki kula da ita samada wacce nakeyi mata” yana gama fadin haka ya figi motarsa a guje ya fice daga gdan……….. Yana fita asibitin su Salees ya nufa yakaita aka shiga da ita aka fara bata taimakon gaggawa cikin ikon Allah ta fara samun sauqi ranar anan suka kwana yana jinyarta tun a daren ya gama shirya musu komawarsu Lagos saboda ya fahimci sai yayi da gaske akan lamarin Mubaraka da Hajiyarsa.Washegari sai goma aka sallameta suka tafi gida dayake sunsan tujararsa idan aka kaishi qarshe bai tarar da kowa ba hakan ya bashi damar sakewa sosai da matarsa ya rinqa bata kulawa sai washegari da yaga taji sauki sannan suka wucce Lagos.Tunda suka koma Lagos yake riritata babu abinda ya sake shiga tsakaninsu yana maganinsa a hankali saida sukayi sati biyu sannan ya sake nemanta da kukanta da komai haka ya rinqa lallabata suka raya daren bai wani dadeba kamar karonsu na farko dana biyu gaba daya baifi minti uku ba yayi release.Baiso hakan ba amma hakan ma yaji dadi sosai yana ganin alamun nasara haka rayuwar taci gaba da tafiya a hankali Hauwah ta fara sabawa da yanayin mijinta itama bata wani damu ba idan yazo miji idan baizoba salamun sukanyi sati biyu uku har wata wani abu bai shiga tsakaninsu ba duk ranar da zai nemeta kuwa to yini yakeyi a kwance da zazzabi da ciwon mara.Shekararsu daya da rabi da aure soyayya babu irin wacce bata gani a gurinsa duk wani burinsa akan iyalansa yake, zuwa lkcn daqyar Alhajinsu yasa ya komar da Mubaraka dakinta hakan yasa ta dan nutsu bata nuna zafin kishinta akan Hauwah.Ko dawowa sukayi bata fiye shiga harkarta ba saidai habaici da take jefar mawa da Hauwan ita kuma wata nutsuwa ta shigeta bata biyewa suyi saidai tayi murmushi, Abu daya da yake damunta shine gorin da dangin mijin sukeyi Mata wai baayi kyau ayi yado ba.Akwai lkcn da ya matsa mata sukaje gaida Hajiya ya shiga gurin Alhnsa yabarsu itama Hajiya ta tashi ta shiga kitchen saboda ita har cikin ranta bata qaunad Hauwah hakan yabawa Muneef dake zaune a gefe damar tasowa ita bata ankara dashi ba ta miqe ta cire hijjab dinta ta ajiye ta fara gogewa Hajiya kayan da take gogewa ta tashi.Batayi aune ba saijin hannu tayi a saman qirjinta da suka qara cika suke daukar ido, bin hannun tayi da kallo gabanta ya bada wani rass ganin farar fata sabanin ta mijinta chocolate, hannunta tasa ta janye hannunsa da sauri.Miqewa tayi shima ya miqe kafin yayi aune ta daukeshi da mari bai dago ba ta sake sauke masa wani a daya kuncin jikinta na rawa ta nunashi da yatsa daidai lkcn da Hajiya take fitowa tace “Allah ya isa tsakanina dakai dan iska fasiqi maci aman…..” Itama Marin taji an dauketa dashi daya sanyata faduwa cikin bala’i Hajiya tace “lallai kinzo birni kinci shinkafa kinsha madara har dana Zaki mara ki kalla a gabana kicewa fasiqi ubanki yayi miki….” Dagowa tayi ta zari dankwalinta daya fadi tace “au yanzu Hajiya bakiga abinda yayimin ba saini kikaga abinda nayi masa wannan zindiqin fasiqin har dane da zaayi alfahari dash…..”Dauketa taji an sakeyi da mari tana dagowa taga Muneef dinne, hannunta ta dora akanta ta rusa ihu tace “Allah ya isana wlh bazan yafe muku ba” fitowar Lameer da Alh tayi daidai da miqewarta ta zari hijjab dinta tana kuka mecin rai.Nufota yayi da sauri ya riqota cikin tashin hankali yace “menene me sukayi miki” fadawa tayi jikinsa ta rushe da kuka me tsuma zuciya tana girgiza kai tana cewa dashi “mu tafi babe mu tafi bazan qara zuwa gidannan ba har abada wlh na tsaneshi na tsani Muneef Allah ya isana ya cuceni” Dagota yayi cikin tashin hankali yace “me yayi miki Hauwah fadamin meye ya hadaku?” Ita dama ba isasshiyar lfy ba dan ta kusa sati tana fama da zazzabin dare da amai, nandanan numfashinta ya fara daukewa, hankalinsa fa ya tashi yayi qasa da ita yana jijjigata yana Kiran sunanta.Itama Hajiya tsuru tayi gabanta yana faduwa don batasan asalin rigimar ba taka haye tayi shikuwa Alh kafe Muneef da ido, miqewa Lameer yayi gashin jikinsa duk sun miqe saboda tashin hankali idonsa ya kada yayi jajir ya kalli Muneef da Hajiya ya girgiza kai ya dauki matarsa ya fice da sauri.Asibiti yakaita suka fara bata kulawa sannan suka binciketa gwajin farko sakamako ya fito tana dauke da ciki na sati bakwai, farin ciki kamar anyi masa albishir da Aljannah nandanan ya nemi damuwarsa ya rasa abinda ya dade yana addu’ar zuwansa yazo ji yakeyi kamar baa taba samun ciki a gdansa ba.Sai Tara na dare ta farfado Koda ta farfado da kukan ta tashi tanajan zuciya ya matsa da sauri yace “don Allah ki fadamin menene Babe wlh kinsayani cikin damuwa me Muneef yayi miki?” Kukanta ta qarawa qarfi tace “nidai kawai ka mayar dani gurin iyayena na gaji Babe nagaji da zama da zuri’ar da basa qaunata meye laifina meye aibina da mahaifiyarka bata sona laifin me nayi Mata?”………..……….



