Hausa novels

Kurkukun Kaddara Takun Farko Chapter 56 By Hafsat Bature

💋KURKUKUN ƘADDARA💋

56

Wani irin mugun bugu zuciyoyinsu su ka yi bakomai ne ya faɗo musu aransu ba, fa ce Ƴar uwarsu batool, haƙiƙa Gabriel Yayi wata magana da su ba suyi tinaninta ba, lokacin da suke 6atawa na rashin ta6uka komai akan adawo musu da ƴar uwa, kamar suna ƙara jefa ta cikin matsala ne, idan ma mutuwa ce ae yanzu ya isa ace batul ta mutu saboda azabtarwar da su ke yi musu idan su ka ɗauke su.

Shessheƙar kukan su Azeeza ne ya karaɗe cikin ɗakin, Jikin su yae mugun sanyi, ita kanta angel hawaye ne suka cicciko mata acikin idanuwanta, a marairaice take kallon Danish.

kukan su parveen ya ƙara dasa tsoro da firgici acikin zuciyar Gabriel, Yana ƙoƙarin Tambayarsu meyasa su ke ku ka, Danish yae saurin dakatar dashi ta hanyar yi mishi magana

“Gabriel, is enough! Maganarka bata da amsa, kamar yarda ka tsinci kanka acikin kurkukun nan ba tare da kasan komai dangane dashi ba, mu ma haka muka tsainci kan mu, Ƴar uwarka da aka É—auka ba’a ita kaÉ—ai ba ce, ka tuna su goma ne aka juya dasu, so ka kwantar da hankalin ka, Su ma suna acikin kurkukun nan kuma suna rayuwa kamar yarda muke yi”. Cikin karyayyiyar murya gabriel yace”Bana tunanin haka, Saboda ina ji acikin zuciyata wani abu yana faruwa da ita, ya za’ae na tabbatar da cewa tana Lafi…….” bai Æ™arasa maganar ba, sakamakon ganin angel da ya yi ta miÆ™e da gudu ta nufi sashen toilet É—insu tana kuka,

Da sauri gabriel Ya janye unaiza daga jikin shi ya miÆ™e Ya nufi hanyar shiga sashen toilet É—in da niyar yabi bayan angel, sai dai kafin yakai ga Æ™arasawa Danish yasha gabanshi, damÆ™ar damtsen hannun shi yae tare da cewa”Kada ka yi gigin cewa zaka bi bayanta, Ka koma ka lallashi waÉ—anda ka fama ma ciwon dake acikin zuciyarsu, har sai sun yi shiru,” Kamar wani ubanshi haka ya bashi umarni, ku ma abin mamaki gabriel bai musa mishi ba, Ya amsa mishi da toh, kafin ya juya ya nufi su azeeza, É—aya bayan É—aya ya dinga zuwa bakin gadonsu yana lallashin su, Har sai da ya samu su ka yi tsit Sannan Ya koma bakin nashi gadon ya zauna, Jikin shi duk ba daÉ—i kewar Æ´ar uwarshi ta addabe shi, tuni unaiza ta koma saman gadonta, chinonsa ma ya hau nashi gadon.

Sam bata ji alamar shigowar shi cikin toilet ɗin ba, tana zuƙunne gaban tukunyar furennin nan, Sai kuka take yi kamar marainiyar da ta rasa gata a duniya, Furen batool ya ƙara tayar mata da hankalin ta, ganin yadda Jikin shi ya bushe Ƙamas, Ganyayyakin jikinsa duk sun tsamure, Alamar babu lafiya atattare da mamallakin furen, A gefen ta Danish ya zuƙunna Tare da ambaton sunanta, Angel kusan sau uku Yana kiranta bata ɗago ba, sai da ya ɗaura hannun shi ɗaya asaman kafaɗarta tukunna ta ɗago ta kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu, fuskar tai jaga jaga da hawaye wasu nabin wasu

Cikin shessheÆ™ar kuka tace”Me zaka faÉ—a mini? Kai idan ma lallashina zaka yi to banso! Ko ka yi abanza tun da ba iya dawo min da batool za ka yi ba, Ku ma wlh rantsuwar É—an musulmi, zanje na dawo da Æ´ar uwata ne, ko da zan rasa raina ne akan hanyar zuwa wurin ta….” bata Æ™arasa maganar ba, Ta daura kanta saman gwiwowinta, gaba É—aya ta kashe mishi baki, Ya rasa me zaice mata, don ya lura babu sassauci akan fuskarta, shiyasa tun farko bai so Gabriel Ya fara maganar Æ´ar uwarshi ba. Ga shi yanzu yaja mishi masifa,

Jim ya É—an yi kafin cikin cool voice ya furta”Angel, nasan bazan iya dawo maki da ita ba, kamar yarda kika faÉ—a, ku ma kema haka koda ace kin Æ™ara dura tagar nan da niyar kije neman ta, ba lallai bane Ki iya tsira, ko kin manta abunda Ya faru dake ne a rana ta farko da kika haura…..”? DaÆ™yar ya Æ™arasa maganar saboda yadda ta É—ago tana wurga mishi harara gwanin ban tsoro launin idanuwanta kamar na zombie, masifa ta soma zazzaga mishi

“Bana son ganinka, sai iya daÉ—in baki, Danish idan har ni bazan iya shiga prison ba, kai zaka Iya, tun da har ka iya zuwa ka É—auko ni, dan haka inaso kaje ka dawo mana da batul É—in mu, Danish ka taimaki rayuwar batul, tsawon wata É—aya da weeks babu ita, ka duba ka gani fa, ko su deeja 2 weeks ne aka dawo mana su, amma Jibi kaga yarda aka canza musu halittarsu to inaga ita da ta jima a hannunsu”

Baisan ya zaiyi ya fahimtar da angel ba, ya san koya lallashe ta abanza don ba jin shi zatayi ba, hakan ya sa shi miƙewa Ya fuce daga Cikin toilet din tabi bayan shi da kallo, Zuciyarta akarye ta miƙe, Tana sharar kwalla, Bata fito daga Cikin toilet din ba, Sai da ta goge bankinta, Tayi wanka,

Lokacin da ta fito, su hanna ta taras A cikin sashen toilet ɗin nasu, suna jiran wanda ke aciki su fito suma su shiga, kallon su kawai tai batare da tayi musu magana ba tasa kai ta fuce daga wurin, shigarta ɗaki keda Wuya, Sai ga Giants sunzo kawo musu abinci, nan take ta ɗaure fuskarta, su uku hannayensu ɗauke ta farantan kayan abincin su, ciki suka shiga tare da sauke trays ɗin saman dining carpet ɗin su, Atare suka ja baya kamar yadda suka sa6a ƙame wa,

Kaitsaye angel ta nufi inda suke, Danish na jin takun tafiyarta ya É—an É—ago daga kishingiÉ—an da yake saman gadon shi, Hatta haris da Gabriel da suke acikin É—akin hankalinsu na akanta

“Har yaushe ne zaku kammala amfani da ita ku dawo mata da ita? Nasan kun gane akan wa nake magana, Ƴar uwar mu batul tana ina”? Ranta a6ace take yi musu magana, babu wanda ya motsa, tsawa ta daka musu tare da cewa”Da ku fa nake magana? Nasan kuna ji na, mugaye kawai……” jiki na 6ari danish Ya sauko daga saman gadon shi ya nufi angel ya ruÆ™o hannunta yana Æ™oÆ™arin janyeta baya, gudun kada su cutar da ita, fashewa tayi da matsancin kuka, Tana bugun Danish akan ya saketa, wlh sai sun fito musu da Æ´ar uwarsu, Wannan maganar tayi matuÆ™ar É—aure ma Gabriel, da Unaiza kai, don tuni ta miÆ™e zaune saman gadonta, idanuwanta luhu luhu take kallonsu, Saboda sautin kukan Angel har na cikin sashen toilet dinsu saida suka fito, hankalinsu yayi matuÆ™ar tashi ganin yadda take kuka tana Æ™oÆ™arin kwace kanta daga hannun danish donta kaima Giants hari, A Æ™arshe da ta ga dagaske Danish bazai Ƙyale ba, ta daddage ta gartsa mishi ciwo a damtsen hannun shi tare da sanya hannayenta biyu ta ingije shi gefe É—aya, taku É—aya zuwa biyu takai ga farantan kayan abincin da aka kawo musu, Robar ruwa ta É—auko ta buÉ—e murfin, Cikin zafin nama ta watsa ma giants ruwan ajikinsu kaf ta zazzage musu shi.

waro ido waje su Parveen su ka yi ganin irin bala’en da take so taja musu, kowa yasha jinin jikin shi, Tana haki tace”Dama nasan bazaku motsa ba, saboda ku É—in dabbo bi ne, Marasa imani, Allah dai yana ganin ku mugaye, Wlh rantsuwar É—an musulmi, idan har wani abu ya sami batul sai kun gane ba ku da wayau, domin kuwa saina addabi rayuwarku, inyaso ku kashe ni, kai bazan ma mutu ba bi’iznillahi har sai na ga bayan ku…” Bata kai Æ™arshen maganar ba, Danish Ya sake damÆ™ota, kamar Æ´ar dambe sai harba Æ™afarta take yi, ahaka yaja ta har zuwa saman gadonta, Ya jefar da ita, Kafin ya juya ya kalli Sauran yace dasu su je su ci abinci,” da sauri suka nufi kayan abincin nasu kowa ya zauna banda Gabriel da Unaiza, kalaman angel sun yi matuÆ™ar É—aga musu hankali, tunani suke yi wacece batul? Meyasa aka É—auke ta?

A gefen gadon Angel Danish ya zauna yana gadinta, gudun kada ta ƙara zuwa ta 6allo musu aiki, Shi kaɗai yasan me yae mata, da har tagaza ɗagowa, hawaye sai bin fuskarta suke yi, ta ɗaura kanta saman pillow,

Bayan sun kammala cin abinci sauran da suka rage ma waɗanda basu samun damar xuwa suci ba, acikin kwando suka adana mu su nasu, Giants na fita daga Cikin dakin, Gabriel ya soma tambayarsu wacece batul? su azeeza suka bashi amsa da cewa ƴar uwarsu da aka ɗauka, yaso ya ƙara tambayarsu dalilin dayasa aka ɗauke ta amma Danish Ya hana shi, ta hanyar
Ƙura mishi ido yana kallon shi, nan take yaji maganar ta fita aranshi, bai ƙara tada ta ba.

Yinin ranar babu daÉ—i suka yi shi, Saboda halin da suka shiga na tunawa da Æ´ar uwarsu, Kowa jikin shi yae sanyi, Har marece ya yi babu wanda ya motsa acikin su, majnun ne kaÉ—ai yake ta tsalle tsalle shi kaÉ—ai atsakiyar É—akin su.

Lokacin da marece ya nutsa, Gabriel ya bukaci yin wanka, Saukowa Yae daga saman gadon shi, Ya nufi toilet ɗinsu Ya shiga, bayan yasanya jamlock ya datse ƙopar Ya dan jingina bayanshi Jikin ƙopar, yayin da zuciyarshi ke acunkushe da tunanin abubuwan da suka faru ayau, Tabbas ya razana sosai da gidan kurkukun nan, duk da baisan komai adangane dashi ba amma yana ji aranshi cewa wani abu yana faruwa badai badai ba, Shi bakomai yafi jimawa ba face ƴar uwar shi Gabriella, maganganun da angel tayi ɗazu akan tasu ƴar uwar sun tsara mishi aranshi.

A Æ™alla ya É—auki kusan minti talatin Yana tunani acikin toilet É—in ba tare daya ta 6uka komai ba, Sai daga bisani ne ya soma Æ™oÆ™arin cire rigarshi, Kwatsam idanuwanshi suka sauka akan Glass window É—in nan, A wani slow yake kallonta sai yake ganin kamar glass É—in jikinta bai zauna dakyau ba, nan take ranshi ya bashi cewar Yaje ya duba ya gani, wata’kil ma ya samu hanyar shiga Cikin kurkukun ko dan yaje ya É—auko Æ´ar uwarshi, ba tare da yayi shawara da zuciyarshi ba, Ya fasa cire rigar ya nufi tagar, Yakai hannu ya tatta6a jikin glass É—in Yaji yana girgiÉ—i, ya daddage ya zame shi daga jikin tagar ya sauke shi Æ™asa, wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyarci, bakomai yake hange ba face fuskar sister É—inshi.

Rashin sani yafi dare duhu, cike da Æ™warin gwiwa Gabriel ya dura tagar ya faÉ—o ta cikin wannan hanyar da angel ta tsinci kanta lokacin da ta ta6a durawa, hada saurin shi wurin miÆ™ar hanyar, babu wadataccen haske, amma yana iya gani dakyau, yana kaiwa Æ™arshenta, Ya faÉ—o cikin wannan babban filin mai É—auke da dogayen benayen nan, A hankali yake Æ™arewa ginin kallo, bai ta6a ganin wuri mai matuÆ™ar ruÉ—arwa ba irin wannan wurin, hakanan ya dinga jin faÉ—uwar gaba, tun daga kan hauwa na farko har zuwa na biyu, a Æ™arshe ya tsayar da idanuwanshi kan hawa na uku, ba zato ba tsammani idanuwanshi suka hango mashi kyakkyawar matashiyar budurwa tana gudun ceton rai saman hawa na uku, fara fat kamar fatalwa, Jikinta sanye da riga ja, wadda bata kai gwiwarta ba, fararen cinyoyinta santala santala, daga gani babu hankali atattare da ita, tana gudu tana waiwayon bayanta, ga uban gashin kanta dake yarfowa harta saman idanuwanta, hakan yasa ta dinga faÉ—uwa Æ™asa tana miÆ™ewa saboda bata ganin gabanta dakyau, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyar Gabriel, Ganin tana saukowa daga saman benan mai hawa talatin, Girgiza kanshi ya dinga yi, zufa tako ina saman fuskarshi, Ya rasa gane shin mutunce ita ko aljan, ko kuma fatalwa ce, Idanuwanshi ne suka dinga nuna mashi kamar sister É—inshi ce, sai dai akwai banbanci sosai, Ƴar uwarshi ba fara bace, kuma bata da tsayin sumar kai da yawa irin na wannan yarinyar, ‘ A tsorace ya juya zai koma hanyar daya fito, A lokacin harta Æ™arasa saukowa saman benan, sai miÆ™a mishi hannu ta ke Yi, tana magana sautin muryarta sam baya fita, ranshi ne ya bashi cewar Ya juya ya kalle ta, ya É—an dakata ya waiwayo baya yana kallonta, sai jan Æ™afarta take yi, saboda nauyin da tayi mata, Taya zai iya yarda cewa mutunce ita? Bai gama yanke shawara da zuciyarshi ba, yaga ta faÉ—i Æ™asa kanta ya bugu, ‘ Gaba É—aya sumar kanta ta rufe mata fuskarta, Tsananin tausayinta ne ya kama gabriel, koma dai aljana ce wannan ba Æ™aramin jiki taji ba, sai motsi take yi alamar tana son É—agowa da kanta amma ta kasa, kuma duk da tana kwance Æ™asa hakan baisa ta fasa miÆ™a mishi hannunta ba, yayi niyar yaje wurinta amma sai yaga Benayen dake awurin sun soma motsi suna yin sama da Æ™asa, Ya zazaro ido ganin suna tunkaro shi, aiko da gudu ya juya ya bi ta hanyar daya fito Ko waiwaye babu ya koma bakin tagar nan, Allah ne ya taimake shi bai 6ace hanyar ba, Jiki na kerma ya haura tagar Ya dura Cikin toilet É—insu Yana ta haki, Sai da ya samu natsuwa tukunna yakai hannu ya É—auki glass É—in daya jingine jikin bango ya maida shi jikin tagar kamar yadda ya ganshi,

Kamar amafarki yake tariyo abubuwan da suka faru Cikin Æ™anÆ™anin lokaci, zuciyarshi cike fal da tunanin matashiyar yarinyar nan daya gani ……….

Masu so karanta middle Step book 2 whatsapp suyi min magana 08103884440 masu son facebook paid group Ga link ku danna shi za kaiku ga wadda zaku yi ma msgana👇

 

 

Click Here To Download Kurkukun Kaddara Takun Farko Complete

 

 

( mu hadu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya, masu yi mun ya jiki ina godiya)

Back to top button