Uncategorized

Macijine Shi Page 5-6 Hausa Novel

Na mammy kabeer

(Anty mammy)

Elegant online writers📚📚

Free book 

Page 5/6

https://www.facebook.com/groups/2803452939899949/?ref=share

________________Hawa  macijin nan yayi kan ruwan cikin fattu ,daidai kan fuskarta ya tsaya tare da fasa kansa ,ya tsaya ƙuri yana kallon fuskar Tata, wacce tuni idanun fattu ke rufe tayi mutuwar kwance ko nunfashi ta kasa shaƙa cikin salama.

Shikuwa macijin nan ganin bata koda motsi saiya sauƙo daga ruwan cikinta ya tsaya saitin fuskar tata tare da fasa kansa yana huci ,.matsowa yayi sosai jikin fuskar tata yana hura mata iska daga bakinsa,sannan ya ɗan ja da baya ya tsaya yana kallon ta.

Ahankali fattu ta ɗan buɗe idanunta dan ganin shin me kuma macijin nan ke shiryawa ?ta yaya yake tsara kasheta itama,saidai tana buɗe idanta suka sauka akan na macijin nan ya ƙureta da idanunsa.

Cike da tsoro da fargaba fattu ta kafe shi da nata idanun,dan tsintar kanta tayi da kasa daina kallonsa,abubuwan mamaki take gani tare da macijin,sam kwayar idanunsa ba irin ta macizai bace,sak!irin ta mutane ce saidai gurin farin yayi wani irin kala kala , blue yellow pink ,Amma asalin kwayar baƙace ƙirin.

Sai kuma taga hawaye na zubowa daga idanun macijin kamar mutum yana kuka.

“Innalillahi wa’inna ilahirin raji’un, Allahumma ajirni fi musibati waaklifni kairan minha,la’ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin”shine abinda fattu ta fara karantawa cikin zuciyarta jikinta na wani irin tsuma da karkarwa, tunda take bata taɓa ganin irin wannan macijin ba sai yau,ya maciji zai kasance da idanun mutane? sannan kuma jikinsa akwai banbanci sosai dana macizai,dan shi yana da wani irin jiki mai ban mamaki yadda kalar idanunsa ta kasance haka shima jikinsa yake .sannan kuma bai kai girma irin na macijin jiyan nan ba amma yana da girma shima sosai,kuma dogone na gaske.

Kallon kallo kawai ake tsakanin fattu da macijin nan,inda ahankali ya fara hucewa daga kumbura da fasa kan da yayi ,fattu na kallonsu harya koma normal jikinsa ya daidaita ,sannan ya fara ƙoƙarin barin ɗakin ta wata yar hanya dake jikin katangar karan ,wacce ita fattu sam bama tasan da ita ba sai yau,da alama dai shi yayiwa kansa hanyar.

Saida yaje gab da hanyar tasa saikuma ya juyo da kansa yana kallon fattun,shi bai tafiya ba  kuma bai dawo ciki  ba.

Sosai jikin fattu ke rawa tana zubda hawaye ,dan yau kam lamarin ya kulle mata kai ,wai wannan wane irin MACIJINE ?shin macijin ne  ma kokuma wata halittar?sannan maiyasa yaƙi yi mata komai,sai dai  ƙoƙarin ceto ta da yake atsammaninsa na ko bata numfashi?haƙiƙa akwai abin dubawa dan gane da wannan macijin.

“Fattu ! fattu!!kin tashine kinyi sallar  lokaci yana ja fa”ta tsinkayo Muryar baffa daga wajen ɗakin yana mata magana .

Jin muryar baffa da fattu tayi sai hankalinta ya ɗan kwanta  cikin ɗaga murya tace “baffa kazo ka taimaka   min gwogwgo bata motsi”ta faɗa cikin Muryar kuka tana kallon macijin.

 Cikin sauri da azama baffa ya shigo ɗakin yana faɗin”subhanallah me kuma ya sami Hansai din?

Cikin kuka fattu ta kalli baffa sannan ta kalli inda macijin nan yake ,har lokacin yana tsaye yana kallon ta,

“Baffa bansani ba kawai ta shigo tana dukana sainaga ta faɗi ƙasa”abinda fattu ta tsinci kanta kenan da faɗa murya na rawa. 

Ahankali macijin nan ya juyar da kansa ya bi ta yar ƙofar nan ya fice.

Sai lokacin hankali fattu da nutsuwarta suka dawo jikinta ,cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta tashi zaune ,har lokacin akwai alamun tsoro da firgici akan fuskarta,dan jikinta sai rawa yake.

“Washhhh hannuna”ta faɗa ahankali tana mai runtse ido,dan sosai hannun ke mata mugun ciwo.

Ruwa baffa ya ɗebo mai sanyi wanda ya taru na sama,yana zuwa ya kwarawa gwogwgo ruwan cikin moɗa .aikuwa azabure ta tashi zaune tana ihu”wayyo Allah na maciji zai kasheni malam kawo ɗauki ,fattu tayiminn turen maciji,wayyo wuyana ,wayyo hannuna na shiga uku na lalace”abinda gwogwgo hansai ta farka dashi kenan,maimakon ambaton sunan Allah .

“Kayya hansai ki nutsu ba wani maciji ana fa nine bukar wannan kuma fattu ce ɗiyarki”cewar baffa kenan a ƙoƙarin sa na kwantar mata da hankali.buɗe ido gwogwgo tayi sosai ta kallesu kafin tace “kuturin bala’i Allah ya kiyaye wannan sheɗaniyar ta zama ƴata mayyace fa,wllh ture tayimin yanzun na wani maciji ya kusan hallakani,wllh sainaga bayan yarinyar nan Shegiya may…….wayyo Allah na ya dawo ya dawo”gwogwgo hansai ta faɗa sakamakon hango kan macijin nan da tayi ,ai da gudun gaske ta fice daga ɗakin tana ihu .

Girgiza kai baffa yayi yana Allah wadai da halin matar tasa ,sam baiyi dacen mata ba.kallon Fattu yayi wacce take riƙe da hannunta mai ciwon, hawaye na zuba a idanunta na azaba.

“Ashsha ashsha fattu kiyi haƙuri  kinji,komai yayi farko zaiyo ƙarshe ,Allah yana sane da halin da kike ciki in sha Allahu zakiyi dariya anan gaba”baffa ya faɗa cikin sanyin murya da ƙoƙarin kwantar mata da hankali.

Ahankali ta sanya hannu ta share hawaye idanunta ,kafin tace “baffa hannu na ciwo yake min”ta faɗa tana nuna masa hannun dayake mata ciwon.

Kallon hannun yayi yanda ya kumbura yayi suntum dashi ,cikin tausaya wa yace “ayya faɗimatu sannu. Kinji maza daure kiyi sallah saina duba miki hannu kiyi haƙuri, Allah yayi miji albarka”ya faɗa yana mai taimaka mata ta miki tsaye.

“Ameen baffa “ta faɗa tana ficewa daga ɗakin .bayi ta shiga ta kama ruwa sannan tayi alwala cikin dabara kafin ta fito ta koma ɗakin ,Sallah tayi tare da karatun alƙur’ani mai girma ,da ka take karatun dan da ahaka aka koya mata ,bayan ta idar ne baffa ya shigo ɗakin ɗauke da kwarya ahannunsa ,

” Sannu fattu karɓi wannan madarar Kisha kinji,saina duba miki hannun”baffa ya faɗa yana miƙa mata kwaryar.karɓa tayi ahankali tayi Bismillah ta kafa kanta,saida ta shanye kafin ta ajiye kwaryar .

Allah Sarki fattu tasha wahala sosai lokacin da baffa ke gyara mata hannun ,dan yayi tsami sosai ,kuka harda majina,haka baffa ya gyara mata yana mata sannu.bayan ya gama gyara mata ne yace ta kwanta ta huta kafin garin ya gama wayewa.haka ta kwanta tana ajiyar zuciya ,ba jimawa kuwa barci yayi gaba da ita ,abinka  da wanda bai sami barci ba dama.

Ficewa baffa yayi daga ɗakin ya nufi nashi cike da tausayin ƴar tashi dayake matuƙar ƙauna.

Ko minti talatin batayi ba tana barcin ta tsinkayo muryar gwogwgo tana kiranta “Ke gantalalliya mayya  fito dan ubanki ,ko uwarki ce zata miki aikin?Shegiyar yarinya aljana wllh bakici bulusba yadda kika sa macijin nan ya lagartamin jiki to wllh saina rama ,fito ki ɗebomin ruwa yanzun nan .

Afirgice fattu ta tashi daga barcin ta fito da gudu tazo tana rawar jiki ,Dan bala’in tsoron gwogwgo take kamar ranta.”gwogwgo dame zan ɗebo ruwan “ta faɗa kanta asunkuye.

Da ubanki zaki ɗebo ruwan  kinji ?kije ki nemomin kuɗin da zaki biyani bokatina inyaso ki ɗebomin ruwan aciki”gwogwgo ta faɗa tana daga ɗaki,dan taƙi fitowa waje kartaje macijin nan ko ajikin fattun yake.

Masu karatu har zuwa wannan lokacin fa yaran gwogwgo hansai suna kwance aɗaki suna barci.

Amma take ƙoƙarin tura fattu ɗiban ruwa da wannan safiya,alhalin bata da lafiya.dan lokacin da baffa ke gyara mata hannun tana jin ihunta.lokacin tana kwance akan gado tana hucin azabar da macijin nan ya gana mata,”Shegiyar yarinya Gara kemaki ɗandana azabar dana sha ,Allah yasa hannun ya karye ma kowa ya huta.

“Dan Allah gwogwgo kiyi haƙuri wllh bansan inda zan samo kuɗin ba kiyimin rai “fattu ta faɗa cikin kuka.

“Dan kan ubanki tashi ki ɓacemin da gani,wllh kome zakije kiyi bai dameni ba Indai zaki kawomin murtala uku da raina gomata.”ta faɗa tana rarumo wani busasshen kwanon tuwo aɗakin ta cillowa fattu shi.

Allah ne ya kare fattu da tuni kwanon ya sauƙa akanta ,tayi saurin ficewa da gudu daga gidan.

“Shegiya da kin tsaya ai”cewar gwogwgo tana mai kwanciya ba ko sallar safiya.

Koda fattu ta fita daga gidan kuka take sosai ,batasan inda zata nufa ba ,ina zata samo Murtala uku da Naira goma?waye zai bata waɗannan iyayen kuɗin?  Kodai gurin jauro zataje tace ya taimaka mata da Murtala uku da Naira goman?kai a’a bazataje ba, dan  jauro ba mutumin kirki bane ,ranar nan ma hannunta yake ƙoƙarin kamawa wai yana sonta,kuma baffa yace maiyin hakan ba mutumin kirki bane.

Kusan minti biyar tana saƙa da warwara,kafin ta yanke  shawarar kawai ta tafi bakin rafin ta zauna ko Allah zai sa  ta sami abun ɗiban ruwan.

Tafiya take ahankali ,wanda kallo ɗaya zaka mata kasan batajin daɗi,hannunta mai ciwon kuwa ta rikeshi da ɗayan hannun.haka ta nufi rafin dake can bayan gari cikin jeji.

“Hai jauro wai kuwa kaga Abinda nake gani”?

Cewar  haroji kenan wanda suke zaune akan wata bishiya shida jauro can kusa da rafin da fattu ta nufa.

“Wanda aka kira da jauron ne  ya ɗago kanshi dake duƙe yana zuƙar sigari yace “me ka gano mana”?

“Wllh fattu ce kuma ita kaɗai kaganta can ta nufi rafi”ya faɗa cikin ɗoki da zumuɗi.

Da sauri jauro ya kalli gurin da harojin ke nuna masa ,aikuwa fattu ya hango ,cikin hanzari ya fito daga kan bishiyar yace “wayyeee huuhuuu ,yau kam mun fito asa’a dan wllh saimun aikata mata ,wllh saina kusan cinye fattu yau “ya faɗa cikin murna da farin ciki yana mai bin hanyar da fattu ke tafiya,harta kusan ƙarasawa rafin.

Da sauri haroji yabiyo bayansa yana faɗin”ai wllh nima saina ɗana yau ɗinnan inka gama saika birmin siɗi”

Da sauri suke tafiya dan haka cikin ƙanƙanin lokaci suka cimma ta.kawai sai gani tayi sun sata atsakiya.

Kallonsu tayi cikin tsoro da fargaba,tace”meye hakan jauro ku bani hanya in wuce”ta faɗa cikin dakiya da nuna alamun bata tsoro su.

Dariya suka kyalkyale da ita ,kafin jauro yace “wllh fattu yau saina kusan shinyeki gaba ɗayanki Allah ne ya kawo mana ke dan haka maza kwanta “ya faɗa cikin jahilci da rashin imani.

Cikin tsoro da fargaba fattu ta fara ja baya tace”jauro me na maka zaka cinyeni?dan Allah kayi haƙuri wllh bana son mutuwa yanzu ina son ganin innarta”ta faɗa lokacin harta fara zubar da hawaye.

Dariya suka saka sakawa suna tafa hannu kafin haroji yace”jauro kawai kamata da shegen ƙarfi dan bazata kwanta ba ,kuma fa kamar bata san me kake nufi ba ” aikuwa jin haka sai jauro ya cakumo  fattu yana faɗin aikuwa yanzu zata san me nake nufi ,yarinya kin cika kin batse amma ba mai amfana dake” nan da nan suka fara kokawa,yana ƙoƙarin Kaita ƙasa ,ita kuma tana Turkewa da ƙoƙarin kwatar kanta. kasancewarsa namiji tuni yaci ƙarfinta dan har ya Kaita ƙasa,ga ciwon hannu.

Daram ya zauna akan ruwan cikinta yana ƙoƙarin cire mata riga.dan tuni shikan ya cire wandonsa daga shi sai wata yar Shara ajikinsa banda wari ba abinda yake yi .haroji kuwa yana tsaye ya juya baya yana gane musu koda me tahowa.

Ihu fattu take cikin tsantsar tsoro da tashin hankali ,tayi mugun razana da ganin abinda jauro ke ƙoƙarin tura mata a bakinta yana fadin”maza Kisha fattu haka ake mana lagus sha maza kiji akwai daɗi”ya faɗa yana ƙoƙarin tura mata jauronsa abakinta wacce ganinta kaɗai ya mugun tsorata fattu.dan bata taɓa ganin wannan ƙaton abun mai numfashi haka  ba sai yau.

“Wayyo Allah na shiga uku jauro menene wannan kake ƙoƙarin bani abakina ka bari bana so wayyo hannuna ,wayyo baffa zan mutu” ta faɗa tana wani irin kakkafewa jikinta na wani irin ɓari.

“Wllh yau ko zaki mutu fattu saina kusan cinyeki dan na jima da yunwarki araina, yau kuwa ba mai hanani yin…….wayyo Allah menene wannan haroji maza zoka taimakeni”jauro ya  faɗa lokacin da yaji wani gibgegen abu ya fado kansa ya duƙunƙune shi sannan yasa baki ya cafke aliyarsa.

Ihu  jauro ya kurma mai ƙarfin gaske ya daɗi can gefe guda……..

Masu karatu,menene wannan ya faɗowa jauro?

Me zai faru nan gaba?ku biyoni next page in Sha Allah,taku anty mammy

Mrs babi💘💘💘

Share and comment

Fisabilillah.

More comment 

More typing.

Back to top button