Sirrin Rike Miji

Hanyoyin Da Mata Masu Bushewar Gaba Za Subi Domin Karin Ni’ima Cikin Kankanin Lokaci

Wannan Hadin Yana karawa Ruwa ga mace da Namiji Gaba daya.

 

1. Kankana 🍉

 

2. Kokumba 🥒

 

3. Tumatir 🍅

 

4 Mazarkwaila 🌰

 

5. Madara Peak 🥛

 

6. Dabino.🌴

 

A yanka kankana Duka a hada da ‘ya’yanta, ita ma kokunban duka za’a yankan harda bayan, kada a cire ‘ya’yan, a yanka tumatir shima kada a matse ruwan cikin sa sai ki daka kanunfari ki jika dabinon, ki cire kwallayen ki hade su wuri daya, ki marka da A Blander, sai ki juye ki saka mazar kwailan ta narke ki zuba zuma sai ki juye madaran peak daya.

 

Ki rinka Sha Safe da Yamma Zaki sha Mamaki Uwargida.

 

Wadannan Abubuwan suna da kyau mata su rika Amfani da su domin Karin Ni’ima da kuma samun Isasshiyar lafiya a jikinsu.

 

Karanta>>> Amfanin Hulba A Jikin Yan Mata Dama Matan Aure.

 

1. Ruwan Abarba: Yana da kyau mace ta rinka markadawa tana tacewa tana sha da sugar ko zuma, wannan hadin yana karawa mata Ni’ima sosai da sosai.

 

2. Rakke: ita ma tana karawa mace ni’ima kuma tana da amfani matuka a jiki, domin tana karawa Macce Ruwa.

 

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Kanki Kafin Aure Da Bayan Aure

 

3. Aya: ita ma duk tafiyar su daya da rake, ayar anaso irin bula-bulanan tana da matukar muhimmanci gurin mace tana da ni’ima sosai, kuma za’a iya samun kunun aya a hada shi da madarar peak ta ruwa.

 

4. Zaitun: Man zaitun yana magunguna da yawa to anaso macce ta ringa shafashi ajikinta yana gyara fata da saka santsi jiki, hakama yanada kyau macce ta dinga shafawa a gabanta, yana saka laushi.

 

Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi

 

5. Bawon bagaruwa: ita kuma wani sirri ne wanda idan mace na son ta zama kullum a tsuke ta dinga dafa bawon ta na shiga kamar yanda ake shiga ruwan dumi idan an haihu.

 

6. Ga kuma wani hadi a nemi sasaken baure, kananfari, zuma, citta, mazarkwaila. Za ki tafasa sasaken baure ya dahu sosai sai ki daka kanumfari me yawa da citta yar kadan ki zuba akai, ki saka mazarkwailan da zuma amma zaki cire icen kafin ki zuba hadin, sai ki sauke ki dinga sha daidai kima idan ya huce, wannan hadin kadai ya ishi macce, ba sai ta wahalda kanta neman boka ko wani asiri tana raba kanta da Allah ba.

 

Karanta>>> Maganin Kowacce Irin Cuta Da Izinin Allah.

 

7. A samu zogale a wanke shi a nika shi tare da dabino da kuma kwakwa sai a tace a saka zuma tare da madara sai a saka ya yi sanyi a rika sha bayan mangariba.

 

8. Wannan hadin yana kara ruwa, ruwan kwakwa ,nikakken rid,gari dabino,madara ta ruwa a ha su guri guda a dama miji zai sha mace ma zata sha.

 

9. Ina mata masu fama da matsalar bushewar gaba? ki samu man ridi ki rinka zubawa cikin ruwan dumi ki zauna a ciki, sannan ki rika matsi da Albabunaj ko Hulba.

 

Karanta>>> Karin Ni’ima Ga Mata Da Kuma Yadda Zaki Zama Kamar Famfo Saboda Ruwa.

 

Back to top button