Uncategorized

Maciji ne Page 61-62 Hausa Novel

Na mammy kabeer

Elegant online writers📚📚

Free book 

page 61/62

________________Ficewa sukayi daga part ɗin ammi zuwa na Adeeb, haka kawai gaban sarauniya Nazli ke faduwa,sam ta kasa gane kan wannan faɗuwar gaban nata,saidai kawai ta alaƙa ta hakan da tunanin halin da zata ga yarinyar data sanya tausayi ta cikin zuciyarta.

Su zayyad ma biyo ta sukayi,dan sunce suma son gannin marar lafiyar ,kuma zasuyi   wasa agurin uncle Adeeb ɗin.

Suna zuwa Adeeb ya dannan lambobin securityn daya sanya lokacin da zai fice,nan take ƙofar ta bude suka shiga.

“Tana cikin daki” Adeeb ya faɗa yana kallon sarauniya suhaimat wacce ke tsaye cikin faduwar gaba.

Kallonsa tayi cikin tausayawa, tare da jinjina kai .

sam zuciyarsa  Adeeb da jikinsa basa masa daɗi, yana cikin matsananciyar damuwa ,abubuwa sunyi masa yawan da har yana rasa me Yakamata yayi.

 

” Ku zauna anan maza kafin na fito kunji” ta faɗa tana shafa kan yaran nata,kafin tabi bayan Adeeb zuwa cikin dakin.

Tana kwance kamar yadda ya barta,ruwan daya ɗaura mata ya kusan karewa.

Jiki asanyaye sarauniya suhaimat ta karasa bakin gadon da fattu ke kwance .sosai bugun zuciyar sarauniya suhaimat ya tsananta.

Zama tayi tare da ƙurawa fattu idanu,lokaci guda taji wata masifaffiyar kaunar yarinyar tana ratsa dukkan sannan jikinta,ji take kamar bata taɓa son abu makamancin yadda take jin son yarinyar na shiga lungu da sako na jikinta ba.

Hannun fattu ta kamo tare da riƙewa gam-gam cikin nata,wani sanyi taji yana ratsata  lokacin data kama hannun fattun,batare da saninta ba kawai ta rungume hannun fattu aƙirjinta ,tare da runtse idonta.wani irin shauƙi takeji yana shiga jikinta irin na ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa.haƙika takamu da matsananciyar kaunar yarinyar lokaci guda.

Download>>> Yaro Ne Complete Novel Document


Kallon fuskar fattu take bata ko ƙifta idanunta,Adeeb na tsaye agefe guda yana kallonta ,mamakin yadda yaga fuskarta ta nuna so da kaunar fattu yake,koda yake haka Allah ke al’amarinsa.ganin ta kasa cewa komai kawai tana rungume da hannun fattu ta kura mata ido yasa shi sauke ajiyar zuciya yana mai faɗin”anty  lafiya kuwa naga kinyi shiru “ya faɗa yana mai kallon fuskar sarauniya suhaimat.

Sai lokacin tadanyi firgigit ta ɗago kai tana kallon Adeeb,ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi kafin tace “wllh Prince haka kawai naji ina kaunar yarinyar har cikin raina ,sosai nake jin tausayinta, yanzu ka dan bamu guri inason na dubawa”ta fada ta na mai shafa kan fattu.

Kallon fattu Adeeb yayi cike da tausayawa,zuciyarsa na masa wani irin ɗaci ,kafin ya sauke ajiyar zuciya kana yayi falo gurin su zayyad da yazeed.

Sosai sarauniya suhaimat taji mugun daɗi lokacin data gane fattu period ma take,kuma babu alamun Rashad yayi mata wani abu,hamdala tayi ga Allah tana jin zuciyarta wasai, murmushi kwance kan fuskarta take kallon fattu,wacce ta fara dan motsi tana yamutsa fuska.

Hannunta sarauniya suhaimat ta kara riƙewa da kyau tana mai faɗin”princess buɗe idonki ki ,kalleni kinji” tana faɗin haka tana ɗan buga kumatun fattu.

Ahankali fattu ke buɗe idanunta da suka yi wani irin jaaaa kamar jini ya taru a cikinsu,har ta bude idon fess,tare da  kafe silin da ido,bata ko ƙiftawa.da alama tana son tuno wani abune, shiru sarauniya suhaimat tayi tana bin idanun fattu da kallo.

Kusan minti ɗaya fattu tana kallon silin ,kafin ta zabura tare da kwalla kara tana kokarin tashi,da sauri sarauniya suhaimat ta cire mata karin ruwan dan dama ya kare .

Download>>> Budurwar Mijina Complete Novel Document

“Wayyo Allah na ,wayyo hammana kazo ka ceceni,zai lalamin rayuwa,wayyo baffana,wayyo innata kizo ,dan Allah ka bari wllh niba yar iska bace karkamin bana so banaso wayyoooooo!!!” Abinda fattu ke faɗa kenan tana fizge -fizge ,dan gani take kamar lokacin Rashad ke ƙoƙarin yi mata fyade,janyota sarauniya suhaimat tayi da sauri ta rungumeta tsam-tsam ajikinta ,cikin mugun tausayinta,tana faɗin”ki nutsu princess ba kowa buɗe idonki ki gani,nice ba Rashad bane ya tafi kiyi shiru ya isa”abinda take faɗi kenan tana shafa kan fattu ,wacce ilahirin jikinta ke rawa ,ta rufe idanunta ƙam -ƙam taƙi budewa.

Da hanzari Adeeb ya ƙaraso cikin dakinz su zayyad ma bishi sukayi da gudu ,jin ihu da fattu ta kwalla,har neman faduwa  Adeeb yake tsabar sauri,yana zuwa ya zauna abakin gadon tare da kamo hannun fattu ,da sauri ta fizge hannunta tana mai sakin ƙara ,”ahhhhhh,wayyo ni kasakeni banaso ,wayyo hammana kana ina? wayyo Hamma kazo ka taimakeni” fattu ta faɗa tana kokarin zamewa daga jikin sarauniya suhaimat.

Cike da damuwa Adeeb ya ƙara kamo hannunta ya rike cikin nashi ,duk yadda take ta ƙoƙarin kwace hannun nata,amma yaƙi saki,

“Hulwa ki nutsu kinji ,nine hammanki,buɗe ido ki kalleni ,ba Rashad bane nine Hamma” Adeeb ya faɗa cikin sanyin murya yana mai shafa kan fattu.

Jin muryarsa da fattu tayi yasata saurin buɗe  kunburarrrun idantuna ,ta sauke akan fuskar Adeeb,ɗan kafeshi tayi da ido,gabanta na faɗuwa kamar zai fado kasa.

“Nine ,hammanki ne Hulwa kalleni ki gani ,nine Hamma Adeeb ” ya faɗa yana ɗan matso da fuskarsa saitin Tata.

Ahankali tace “hammana”

“Na’am Hulwa is me “Adeeb ya faɗa yana mika mata hannu.

Da sauri ta fada ƙirjinsa tare da fashewa da wani irin kuka,mai matukar ban tausayi,kukane irin na wanda ke cikin tashin hankali kuma ya sami mai taimakonsa.

“Hamma ina kaje ka barni?wannan mai kama da kai ɗinne yazo zaiyi min fyade,Hamma dan baki yarda shine yayi ta dukana,ya fasamin baki,ya bugamin kaina ajikin katanga,Hamma bana sonshi,bana son ganinsa ,dan Allah Hamma ka fitar dani daga gidan nan bana so”fattu ta faɗa cikin matsanancin kuka muryarta har wani yankewa take kamar numfashinta zai dauke.

Download>>> Jiddertul Khairi Complete Novel Document

Ƙamm ƙamm,Adeeb ya rungumeta ajikinsa,yana jin wani irin zafi akirjinsa, mugun tausayinta ne yake zaga dukkan wata kofa dake jikinsa,haushin kansa ma yake ji,wai me yasa ma ya tafi gurin taron ya barta anan?me yasa bai tafi tare da itaba?

Ahankali yake shafa kanta,yana mai faɗin”am sorry Hulwa,kiyi haƙuri laifinane,dana tafi na barki,na miki alkawarin ba wanda zai sake ƙoda miki kallon banza ne bare hakan ta kara kasancewa,ki yafemin hulwata ,an sorry “ya faɗa yana kara ruƙunkumeta ajikinsa,wasu hawaye Masu zafi suna zirarowa daga idanunsa.

 Zuru su zayyad sukayi suna kallon fattu,dan yazeed ma tuni ya fara kuka ,dan shi yana da mugun tausayi.

Sarauniya suhaimat na zaune ta kura musu ido,cikin tausayi take zubda kwalla itama,ji take kamar yarta akayiwa wannan zalumcin ,Allah Sarki Adeeb ya cika dan halak dan ga dukkan alamu yana kula da yarinyar nan,duk da kasancewarta ma aikaciya agidansu,kuma tabbas taga zallar kaunar yarinyar cikin idanun Adeeb.

Sun jima cikin wannan yanayin,har saida Adeeb ya tabbatar Hulwa ta sami nutsuwa ta hanyar daidaiton da yaji bugun zuciyarta yayi,sannan ya rabata da jikinsa.

“Sannu princess hulwar Adeeb”sarauniya suhaimat ta fada ,fuskarta ɗauke da murmushi.

Sai lokacin fattu ta juya tana kallonta .rassa!rassa!!rassa!!! gaban fattu ya yanke ya fadi,ƙurrr ,ta kure sarauniya suhaimat da ido,lokaci guda taji ƙaunar matar na ratsata fiye da yadda tayi tunani,duk kunya irin ta fattu,da bata yarda kuyi ta haɗa ido da ita,amma yau kam ta kafe sarauniya suhaimat da ido bata ko ƙiftawa.

Murmushi sarauniya suhaimat take sakarwa fattu,kafin tace” baki sanni ba ko?

Ta fada cikin yanayi na murmushi.

Kamar wata doluwa haka fattu ta daga kai idonta akan fuskar sarauniya suhaimat.

“Daga yau nice innarki ,danaji kina faɗi kinji “ta faɗa tana mai shafa kan fattu.

Ahankali fattu ta matsa kusa da ita tare da ɗora kanta akan cinyar sarauniya suhaimat tana mai faɗin “innata”ahankali tare da lumshe idonta.

Kallonsu kawai Adeeb keyi,zuciyarsa na darsa masa abubuwa da dama,wannan wane irin shakuwace ta lokaci ɗaya?gaba ɗayansu sun kamu da  kaunar juna daga haduwar farko,anya ba wani al’amarine mai ƙarfi atsakinsu ba ?.

Hammmmm mudaije zuwa.

“Sannu  anty “zayyad ya faɗa cikin tausayawa.

Ahankali fattu ta ɗago kai tana kallon yaran masu tsananin kama, 

Lokaci guda yaran suka shiga ranta.

Masha Allah kyawawa dasu.

Jinjina kai tayi tana kallonsu cike da kauna.

Download>>> Gamo Complete Novel Document

“Maza kuje falo ko anty zatayi wanka” cewar suhaimat.

Kama hannunsu Adeeb yayi suka fice zuwa falon.

Saida Sarauniya suhaimat ta taimakawa fattu tayi wanka ta gyara mata jikinta sosai,ta bata abinci taci ta sha magunguna sannan ta kwanta barci .kafin ta bar ɗakin akan zata kara dawowa ta duba ta.har ta kai bakin ƙofa fattu ta ce”innata” da sauri sarauniya suhaimat ta juyo ,dan har cikin ranta taji sunan ya shigeta.

“Zaki dawo “fattu ta faɗa tana kallonta .

Jinjina kai tayi tana mai yiwa fattu murmushi tace “tabbas zan dawo ƴata”murmushi fattu tayi  cikin karfin hali tare da rufe idanunta.ba ɓata lokaci  barci yayi gaba da ita.dan kuwa harda maganin barci acikin wanda ta sha.

Koda sarauniya suhaimat ta koma bangaren ammi,zaune ta tarar da ammin ta buga uban tagumi,duk sallamar da take sam ammin bata jiba,dan tayi nisa cikin duniyar tunani,saida ta tabata kafin ta san da zuwanta gurin.

“Suhaimat ina kikaje ?na duba baki afalon?

Ammi ta faɗa da kokarin kawar da samuwar dake kan fuskarta.

Zama suhaimat tayi susa da ammi tace ,wllh yarinyar nan da abin nan ya faru da ita naje na gani,dan kuwa sosai lamarinta ya tsayamin araina ji nake kamar inada wata alaƙa da yarinyar” suhaimat ta fada tana mai lumshe idonta.

Azabure ammi ta kalli sarauniya suhaimat tana mai dafe ƙirji”na shiga ukuna ,suhaimat gurin yarinyar kikaje?me kika gani?da wa kikaga tana miki kama?ammi ta faɗa cikin rudewa da tashin hankali,dan bata taba tsammanin suhaimat zataje gurin fattu ba.

Kallon mamaki suhaimat ɗin ke bin ammi dashi ,kafin tace  “uktee ,yanaga kin rude haka?daga jin cewar naje gurinta?kuma dawa kike tsammanin zanga tana kamar?ta fada cikin mamaki tana kallon ammi,da sai lokacin ta fahimci tayi baran -barama kuma tana son bada kanta.

Cikin sauri ta saita kanta,kafin tace “ai nayi mamakin yadda kika damu da 

 baiwane,har kikaje dan ganinta”ammi ta faɗa cikin basarwa.

Murmushin suhaimat tayi kafin tace “wllh yadda nake jin yarinyar nan cikin raina ,ko su zayyad bana jinsu haka”ta faɗa cike da shauki akan fuskarta.

Wani shegen kallon ammi ta jefa mata ,tana mai faɗin ,aikuwa saidai kiyi ta jin wannan shaukin cikin ranki,amma keda ƴarki har abada,bazan ƙara bari ki ganta ba,dan kuwa  kashe shegiya zanyi kowa ya huta.ammi ta fada cikin ranta.

Amma afili saitayi murmushi tana faɗin,”ke dai suhaimat kina nan da son jama’a har yanzu,sukuwa mutane ba abin yarda bane ,Gara ki kula” 

Jinjina kai suhaimat tayi kafin tace “ai idan har kana abu tsakaninka da Allah ,to tabbas Allah zai zama gatanka, kuma bazai taba ba maƙiya Sa’a akanka ba,kuma kinsan shi sharri dan aikene,idan ka cutar da wani to kana zaune zakaga sakayyar Allah”cewar sarauniya suhaimat kenan cikin murmushi take bayaninta.

Kallonta ammi keyi,cike da sanyin jiki,sai take ganin kamar magana suhaimat ke faɗa mata afakaice,amma ai tasan suhaimat bata san komai game da halayyar ta ba ,bare tayi mata shagube.dan haka ta Badar da maganar sukaci gaba da hira.

Download>>> Tubabbiya Complete Novel Document

“Ranka ya dade ,hakika al’amarin Adeeb babban abune,wanda Allah shine kadai zai iya kareshi,domin kuwa sihirin da akaiwa yaron nan,badan ƙarfin addu’ar dake tare dashiba, to tabbas mutuwa zaiyi,domin kuwa sihirin anyi shine badan ya rayu ba,saidai akasheshi. Dan haka ba abinda zamuyi face addu’a domin Allah ya kareshi da duk wani mai nemansa da sharri” Shaikh lateef ya faɗa ,yana mai kallon mai martaba ,

Shiru abie yayi cike da tsantsar mamakin waye yayiwa ɗansa wannan aika aikar,kallon ƙaninsa waziri yayi cikin damuwa yace “ɗan uwana kanaji? Kana jin abinda Shaikh ke faɗi, me Adeeb ya tsarewa jama’a ?yaro mai hakuri,hankali da hangen nesa,ba ruwansa da kowa bai tsarewa kowa komai ba,amma ana neman ganin bayansa,Allah ka karemin ɗana ,ka raba shi da sharrin makiya,yanzu Shaikh menene abinyi.

?”abie ya faɗa cikin damuwa yana jin kamar ya zubda hawaye.

Jinjina kai Shaikh lateef yayi yana Jan carbinsa dake maƙale adan yatsansa.

“Ranka ya dade ba abinda zamuyi masa daya wuce addu’oi,sannan zan hada masa maganin karya sihiri wanda zai sha yayi wanka dashi,amma fa kasancewar samutum akoda yaushe abune  mai matukar wahala,dan kuwa Aduk lokacin da ya shiga yanayi na ɓacin rai mai tsanani to tabbas akwai yuwuwar komawarsa macijin ” Shaikh ya faɗa yana mai kallon abie.

Wazirine ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Shaikh cikin damuwa kafin yace “yanzu  ba wata  hanya da Ya kamata abi,Dan arabashi da wannan iftila’in?ta yaya za’ace mutum yana komawa wata halittar? Shaikh aduba dai “waziri ya faɗa yana kallon Shaikh.

Murmushi Shaikh yayi yana mai girgiza kai,kafin yace ,tabbas da ‘ace akwai hanyar da zanbi dan ganin na raba yaron nan da wannan al’amarin ,to danabi ,kamar yadda na faɗa muku, anyi amfani da mugayen aljanu waɗanda suka samo macizan da ba irinsu afadin duniyar nan,kafin aka hada lakanin da akayi masa sihirin dashi, dan haka addu’a itace kadai mafitarmu” 

Ajiyar zuciya abie ya sauke ,zuciyarsa kamar zata fashe tsabar damuwa da ɓacin rai,sosai yake jin tausayin Adeeb,waye wanda ke son ganin bayan Adeeb? Me ya tsarewa mutane haka?

Dole ya tsaya sosai ya kula da rayuwar dansa ,ta hanyar bashi kariya ta kowace sigar.

“Shikenan Shaikh Allah ya shige mana gaba ,ya bamu Sa’a akan abinda muke nema”cewar abie yana mai lumshe idonsa lokaci guda damuwarsa ta baya ta dawo masa ,yana tuna abinda ya faru shekarun baya,sam baya son abu makamancin abinda ya faru a baya ya sake faruwa.

“Yanzu  ranka shi dade,ina son aturomin yarima zuwa anjima dan akwai abubuwan da zamu tattauna dashi”Shaikh lateef ya faɗa yana mai mikewa dan barin dakin.

Bayan fitarsa waziri ya kalli abie wanda yayi shiru fuskarsa gaba ɗaya ta sauya ,ta koma kalar damuwa sosai,

“Ranka ya dade ka kwantar da hankalinka,In Sha Allahu komai yazo ƙarshe,ba abinda zai sake samun yarima”waziri ya faɗa cikin kwantar da murya aƙokarinsa na kwantarwa da abie hankali.

Download>>> Ni Da Yaya Habeeb Complete Novel Document

“Allah yasa waziri,amma abin yana damuna ,kasan yadda nake son Adeeb ,bana son abinda zai tabashi komai ƙanƙantarsa,domin shine magajina”

“Ba komai ranka ya dade mubar komai hannun allah.”cewar waziri. 

Jinjina kai abie yayi kafin yace ,sai kuma wannan matsalar ta Rashad,Dole in ɗauki mataki mai ƙarfi akansa,jira nake kawai ya sami lafiya”

“Haka ne yaya dole ahukunta Rashad ,Dan yana don bata mana  suna” cewar waziri cikin damuwa.nan dai sukaci gaba da tattaunawa akan matsalar.

Rashad yana nan har yanzu kwance kamar gawa ,ko motsi bayayi, gaba ɗaya kamanninsa sun sauya ,abin tausayi,kullum amma cikin kuka take tana tausayawa halin da ɗan nata ke ciki,

Gimbiya Zulaihat ma tun daga wannan ranar bata kuma ganin Adeeb ba,dan tsoronsa take ji sosai,amma har lokacin tana nan akan bakanta na son aurensa.

Adeeb kuwa yana dakin da fattu ke kwance tana barci,kallonta yake cike da tausayi,gefe guda kuma wayar da ammi tayi gaba ɗaya ta tsaye masa arai,ga maganar da nanny ta fada masa,shi gaba ɗaya ma ya shiga ruɗu baisan me Yakamata yayi ba,yanzu gurin wa zai je neman shawara?waye zai sanarwa da damuwarsa?yanzu tsoron mutanen fadar nan yake ,dan kuwa cike take da mutane marasa amana da gaskiya.

Ahankali ya shafa gefen fuskar fattu tare da sumbatar goshin ta kafin ya mike tare da ficewa daga ɗakin.

Kai tsaye amma ta fito daga part ɗin Rashad bayan ta gama kukanta ta koshi,tunani tayi kan cewar ya kamata akawo karshen wannan al’amarin dake dukunkune cikin fadar nan,dan haka tana da bukatar magana da  nanny Dole taje tayi magana da ita yanzu .

Dan haka can ta nufa ,cikin sa’a ta tarar da nanny zaune afalo, kallo ɗaya zakayi mata kasan tana cikin damuwa da alhini.tana ganin amma ta mike tana mata maraba cikin girmamawa.

Zama amma tayi tare da kallon nanny tace”zauna nanny inason muyi magana dake . “ta fada tana mai kallon nanny ,wacce itama kallonta take.zama nanny tayi jikinta asanyaye kafin tace “wace magana kike son yi dani ranki ya dade?inaga da kin aiko ankirani nazo gurinki dan gudun zargi ,idan aka ganki anan”nanny ta fada cikin damuwa.

“Ajiyar zuciya amma tayi kafin tace ,ya kamata mu daina boye-boye nanny akan abinda muka san menene gaskiyarsa,ki duba halin da ɗana yake ciki ?kuma duk akan wannan makirar matar ,nasan cewa kome ya faru shirinta ne,meyasa zamu zauna mu zuba mata ido tana aikata abinda taga dama?dan haka dole mu kawo ƙarshen zalunci ta”amma ta faɗa cikin ɓacin rai da damuwa.

Ajiyar zuciya nanny ta sauke mai ƙarfi kafin tace “ranki ya dade wannan abun fa  abune mai matukar hadari ,dakuma tarin ƙalubale,domin nayiwa magajin fada maganar hadarin sarauniya Nazli, na sanar dashi wanda ke da hannu akan hadarin, amma sam bai yarda dani ba yayi fushi mai tsanani.tunda ya fita bai sake dawowa ba.dan haka ina ganin mudan jinkirta zuwa wani lokaci,har wannan abinda ya faru yayi sanyi”

Jinjina kai amma tayi cike da gamsu,tace “wannan gaskiya ne ,dan kuwa nasan mai martaba ma jira yake Rashad ya farfaɗo ,kafin ya yanke hukunci akan abinda ya aikata .Allah shine kawai zai fitar damu ” ta fada kwalla na cika idonta.

Download>>> Jinin Sarauta Complete Novel Document

“Kiyi haƙuri ranki ya dade ,komai yayi farko, yana da karshe ina sha Allah muke da nasara”cewar nanny cike da damuwa akan fuskarta.

“Shikenan nanny Bari na koma can gurin Rashad din”Amma ta faɗa tana mikewa.

Biyota nanny tayi tana mata sallama ,har farfajiyar gidan suka fito nanny na kara kwantarwa da amma hankali.

Daidai lokacin kuma Adeeb ya fito daga part ɗinsa ,idonsa ne ya sauka akan nanny tsaye tare da amma.

Kallonsu yayi cike da tsantsar mamaki,da kara tabbatar da zarginsa akansu.

Suma kallonsa suke cikin yanayi na damuwa da rashin jin dadin ganinsu da yayi .

Tafiya amma tayi daga gurin ,ganin irin kallon da Adeeb ke mata.

Nanny kuwa jikinta ne yayi sanyi sosai.da hanzari ta nufi gurin da Adeeb ke tsaye……..

Hmmmmm masu karatu muhaɗe next page .

Takuce anty mammy 

Mrs babi💘💘

Share and comment fisabilillah.

More comment

More typing.

Back to top button