Hausa novels

Halysaah Page 64 By Khaleesat Haydar

Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido ganin ya nufi kofa, sai kuma ta juya tana kallonsa, fita ta ga zai yi daga parlon, da sauri tace “Ka jira in dauko maka wayar yana sama” Tuni ya fice daga parlon without looking at her, tafi minti biyu tsaye tana kallon kofar da mamaki, does this min yaji haushin abinda ta fada kenan? To ai ita ba da wata manufa ta fadi hakan ba, tana ta tsaye parlorn with surprise, can dai ta taɓe baki ta karasa ta zauna kan kujera ta bude handbag dinta ta ciro wayarta tana duba pdf da aka mata sending a school na wani course dinsu, after a while ta mike ta tafi sama don yin sallah ta canza kayan jikinta sannan ta dawo downstairs ta girka abinda zata ci, Khaleesat bata sauko downstairs din ba sai kusan karfe biyar da rabi na yamma don tana sallah bacci ya dauketa saboda sanyin garin, tana gyara hulan kanta bayan ta sauko kasa zata shiga kitchen taji anyi knocking kofar parlor at the same time aka murda kofar, juyawa tayi da sauri after realizing ashe a bude ta bar kofar bayan Ajay ya fita daxu, kallonsa ta dinga yi babu ko kiftawa kuma ko kwakkwaran motsi bata yi a inda take tsaye tsabar yanda ta tsorata, ya kullo kofar yana tsaye daga nan bakin kofar yana kallonta yana murmushi with calm yace “Good evening Khaleesat” Khaleesat ta sauke idonta gabanta na wani mugun faduwa, her common sense didn’t give her the go Ahead to be rude or anything of such to him, can dai ta kallesa with calm in her voice tace “Why will you badge into my House just like this?” Ya ɗan yi murmushi yana sauke hulan jacket din jikinsa yace “That was because u left the door open…” Cikin kwantar da murya tace “But that doesn’t warrant you to badge in” Ya daga hannu sama yace “My bad, sorry about that beautiful Khaleesat” Zaunawa tayi kan kujera bata sake cewa komai ba faduwar gabanta ya tsananta, yana bin apartment din da kallo keenly yace “Such a nice apartment, Communal living kike, ko ke kadai ce a duk apartment din nan?” Ba tare da ta kallesa ba calmly tace “Co-living” Ya karaso cikin parlon tayi masa kallon gefen ido gabanta na faduwa sosai, zaunawa yayi gefenta yana kallonta yace “Sorry i came unannounced, banyi tunanin kina da fahimta haka ba, na zo gidanki ba tare da izinin ki ba and u are not mad at me, i even badged in but u are still calm….” Khaleesat tayi murmushin karfin hali tace “It’s fine… How did you get to know my apartment?” Yana gyara zama yana wani murmushi yace “Gane apartment din ki har wani wahala zai min a Baltimore ni da na damu dake?” Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, tasan babu tantama bayan ta fito school ne daxu ta hau Lyft shi ne ya biyota without her knowledge, bin parlon ya dinga yi da kallo yace “But seriously i really love this ur apartment, it’s big and fine, ko ke da Safiyyah ku ke sharing?” Ta girgiza masa kai, can kasan zuciyarta kuwa tunanin next move din da zata dauka take yi, yana kallon sauran gashinta da basu gama shiga hulan kanta ba tunda tana cikin saka hulan ya shigo parlon, ya kai hannu zai taɓa gashin da mamaki yace “Are all this ur hair??” Da sauri ta matsa gefe tace “Noo, i won’t welcome that” Ya buda ido yace “I am sorry Dear, you’ve got a beautiful soft black hair” Ita dai bata ce komai ba, Yana kallonta speaking calmly yace “Tell me more about ur self pls Khaleesat” Ta kirki murmushi tace “Kaga yanxu fita zanyi zan tafi supermarket in yi shopping, and it’s almost late” Yayi er dariya yana kallonta da kyau yace “Duk salon korana ne wannan dear?” Tace “Not at all, assuming zan kore ka ai kana shigowa zance ka fitar min a gida, kawai zan je in yi siyayya ne yanxu don gobe ba da wuri zan dawo gida daga schl ba” A hankali yace “Alright, dress up sai mu je shopping din” Tayi karfin halin mikewa tsaye sai kuma ta kallesa tace “But plss respect my privacy, ka jira ni in sauko” Yayi wani murmushi yace “Baki da matsala my dear” Bata sake cewa komai ba ta nufi stairs har sannan gabanta na faduwa sosai, ga wani takaici da take ji a ranta don wata er doguwar riga ne kawai a jikinta that is not even cloth enough, a haka dai ta haura sama yana bin ta da kallo, tana shiga dakinta ta kulle dakin da makulli hawaye ya cika idonta ta tafi ta dau wayarta da sauri, number Housemate dinta tayi dialing bayan few seconds ya fara ring amma har ya katse bai daga ba, zaunawa tayi gefen gado tana goge hawayen dake sauka idonta tana tunanin yanda zata yi, bata sake dialing number Housemate dinta ba instead tayi dialing number Ajay, a cikin daya daga jakunkunan da take fita school taji vibration din wayar tasa, ajiye wayarta tayi ta daura kanta kan pillow ta fashe da kukan takaici, after some minutes ta mike tana goge hawayen da yaki tsaya mata, ta dau handbag din da wayar Ajay ke ciki, ta ciro wayar tana dubawa taga ya ma kusa shut down, cikin jakar da ta dawo da shi daga school ta saka wayar sannan ta dau nata wayar tayi ordering Uber, ta saka wayarta ma cikin jakar, ta canza kayan jikinta sannan ta saka hijab ta fito daga dakin ta kulle ta sauka downstairs, yana tsaye parlorn hannunsa rike da can drink da ya shiga kitchen dinta ya dauko a fridge yana sha, ya bi ta da kallo yace “The weather is cold outside dear, ina jacket din ki?” Without looking at him tace “I will be fine” Yace “Ohk then, mu tafi?” Tace “A’a zan ɗan yi abu a kitchen in fito tukunna” Yace “Ohk, take ur time” Kitchen dinta ta nufa ya bi ta da kallo har ta shiga ciki, kulle kofar tayi ta tsaya a kitchen din tana jiran Uber dinta at the same time zuciyarta na tafarfasa tana goge hawayen takaicin dake sauka idonta, after a while ta fito daga kitchen din without looking at him tace “Na gama” Mikewa yayi yana gyara jacket dinsa yace “You look cute dear, ko dai in baki jacket dina, its freaking cold outside fa” Tace “Kar ka damu” Daga haka ta nufi kofa ta fita, shi ma ya fito sannan ta kulle kofar da makulli, motarsa da yayi parking ya nufa yana nuna mata yace “There is my car” Ta kallesa tace “Ga Uber da nayi order can” Ya juya ya kalleta yace “Why? Cancel the order, da mota na zo ae” Tace “I can’t cancel it” Bata sake sauraronsa ba ta nufi uber din without looking at him, ya bi ta da kallo with astonishment, dariya yayi yace “Whatt? Like seriously…. this little girl played me” jingina yayi da motarsa ya rufe baki yana murmushi yana kallonta yana gyada kai har ta shiga uber din, wato shi zata yi ma wayo, gaskiya tana da wayo, gyada kai yayi ya shiga motarsa ya tada sannan ya bi bayan uber din da ta shiga…. Khaleesat na lura da yanda yake bin uber din da ta shiga a baya, sai kusan karfe bakwai ta isa gidan, ta bude Uber din ta sauka ta nufi cikin gidan da sauri, sai gashi shima yayi parking, ko kashe motar bai yi ba ya sauka ya bi ta yana kiranta, amma tuni ta shiga gidan zuciyarta na bugawa, hakan yasa ya tsaya ya bi ta da kallo har sannan yana murmushi yana gyada kai, sai da ya kare ma babban gidan kallo sannan ya juya ya koma motarsa, Khaleesat tana hardewa ta isa har kofar shiga gidan tana jin gabanta na faduwa sosai don gani take kamar ya biyota har cikin gidan tunda ba juyawa tayi ba balle ta gani, bubbuga babban kofar parlon ta dinga yi hawaye cike idonta, amma shiru ba a bude ba, sai a sannan ta lura da madannin kararrawan gidan, ta danna da sauri hannunta na rawa, sau uku tana danna bell din kafin aka bude kofar after almost 5 minutes, ta fashe masa da matsanancin kuka tana kallonsa, Da mamaki yake kallonta daga sama har kasa yace “Me ya faru?” Taki ce masa komai tana rusa masa kuka, bai san sanda yayi mata tsawa ba sounding so apprehensive yace “Can’t u speak out? Tell me what is it? Me ya faru?” Cikin kuka tace “He followed me to my apartment” Ya bude ido sosai yace “Who?” Tace “Wannan mutumin nan” Da mamaki yake kallonta babu ko kiftawa yace “Ur apartment?” Ta gyada masa kai hawaye na zuba idonta tace “Ya biyoni har nan gidan ma a cikin motarsa” Yace “Nan gidan??” Tace “Eh, yana waje ban san ko ya shigo ba ma….” Ya cire takalman kafarsa ya saka wasu dake bakin kofar sannan ya fito daga parlon ta bi sa da kallo tana goge hawayen idonta ta jingina da bango, Ajay na fita can waje ya dinga bin Neighborhood din nasu da kallo don babu alamar ko mota daya a waje, sannan kuma babu kowa cause the weather is sooo cold kuma gari yayi duhu, ya juya ya koma cikin gida, har ya iso entrance din shiga parlon kallonsa take, ya hade rai yace “Shiga ciki” A hankali ta juya ta shiga cikin parlon ta cire takalmanta ta karasa ciki ta zauna kan kujera har sannan gabanta bai dena faduwa ba, shi dai Ajay na tsaye bakin kofar parlon gaba daya mamakin Aymaan ya gama cikasa, har ya fara tunanin irin matakin da zai dauka kansa, lkci lkci Khaleesat take kallonsa, after some minutes ya karaso cikin parlon yana kallonta fuska daure yace “Ta yaya ya san apartment din ki har ya je?” Muryarta na rawa tace “Nima wallahi ban sani ba” Ya wani hade rai yace “Kee, kar ki kuskura ki min kuka a nan, don’t stress me with your silly cry….” Ita dai bata ce komai ba, yace “Da ya je apartment din naki sai aka yi yaya?” A hankali tace “Ni na manta ban kulle kofar ba da ka tafi daxu, kawai da yayi knocking sau daya shine ya bude kofar ya shigo da yaji sa a bude, and i told him i am going out for shopping yace to zai kai ni, bayan mun fito sai naki shiga motarsa dama nayi ordering Uber, shi ne ya biyo bayan motar da na shiga har muka zo gidan nan” Ajay yace “Da ya je apartment din naki ur common sense bai gaya maki ki kira masa cops ba immediately, ni ranan saboda rashin kunya ba cewa kika yi zaki kira min 911 ba??” A hankali tace “To ba wayar yana sama ba, kuma ai mantawa nayi da cops, i was confuse” Jinginar da kanta tayi jikin kujera bata sake cewa komai ba cause she is already tired, a hankali ta jawo handbag dinta ta bude ta ciro wayarsa ta mika masa tana kallonsa, taga direction din da yake kallo daban yana nazari, ajiye wayar tayi a gefenta, after a while ya juya yana kallonta a takaice yace “Go upstairs” Ta ɗan bude ido tana kallonsa tace “Upstairs?” Ya mata wani kallo yace “Gidan za ki koma yaje ya same ki a can?” A hankali tace “A’a i tot za mu koma gidan tare” Yace “Sai ki zo ki daukeni mu tafi” Daga haka ya nufi stairs, ta wani bi sa da kallo, shi dai komai masifa, sai kuma ta zumburo baki ta kauda kai, har bayan awa daya Khaleesat bata ga ya sauko downstairs ba, tayi ta zama a parlon har ta gaji gashi bata yi sallah ba, bata ji alamar da workers ko daya a gidan ba cause everywhere is so silent, jinginar da kanta tayi da kujera don ta gaji ga wani ciwo da kanta yake mata and she is very hungry, ta lumshe ido tana zaune a haka bacci ya dauketa, cikin bacci taji muryarsa ta bude ido da sauri ta gyara zama, yana kallonta yace “Oh baki tafi saman ba?” Ta hade rai tace “To ni nasan inda zan je a saman?” Yace “Baki san inda Jay ya saba ajiye ki ba?” Kin cewa komai tayi, after some seconds ta daga kai ta kallesa taga hararanta yake, ta mike ta dau handbag dinta ta bar masa wayarsa a kan kujeran, juyawa yayi ya koma sama ta bi bayansa tana tafiya a hankali, tsaye ta gansa a corridor fuskarsa babu yabo babu fallasa, sau daya ta kallesa har zata tafi dakin da ta taba zama a gidan sai kuma ta saci kallonsa tace “Ina zan je?” Yace “Ban sani ba” Juyawa tayi ta dau hanyar bangarensa, ya bude baki da mamaki yana kallonta yace “Kee” kasa daurewa tayi har sai da tayi dariya don ba karamin dariya abun ya bata ba, ta dake tace “To ba kace inda Housemate dina ya ajiyeni ba, ae can zan je” Shi tsabar mamaki ma rasa abinda zai ce mata yayi, can yace “To tafi ki ga ikon Allah” Ta wani kallesa ta juya ta nufi dakin da ta zauna sanda take exam, tana shiga dakin ta kulle kofar, the room was neat amma kana gani kasan an dade ba a zauna a ciki ba, sosai dakin yayi sanyi kamar kankara, tayi dusting gefen gadon sannan ta zauna tana takurewa waje daya, bayan wani ɗan lokaci ta mike da sauri bayan ta tuna bata yi sallah ba, ta shiga bandaki ta dauro alwala ta fito, Heater din dakin ta kunna amma yaki yayi function, a haka dai ta tada sallah bayan ta idar tana zaune saman darduman taji knocking a kofar dakin, tana ta kallon kofar sai kuma ta mike ta tafi ta bude kofar tana kallonsa, a takaice yace “The workers in the house are yet to resume, you can go to the kitchen and sort ur self out, this is the only help i can render” Daga haka ya juya ya bar bakin kofar ta bi sa da kallo, sai kuma ta kulle kofar ta koma ta zauna ta takure waje daya don sanyi take ji sosai gashi bata zo da Jacket ba, duk da yunwan da take ji ta gwammace ta hakura don bazata iya zuwa kitchen ba, har ta kagu gari ya waye a san yanda za ayi da Aymaan ta koma gidanta, amma duk da haka ita dai ta tsorata da wannan apartment din ita kadai a cikinsa, mikewa tayi ta kwanta saman gadon bayan ta kakkabe, ta lulluba da second of the bedsheet don biyu ne a kai amma duk da haka sanyi ta dinga ji kamar bata rufa ba, a haka bacci ya dauketa, wajen karfe goma Ajay yayi knocking kofar dakin, ta bude idonta a hankali don restlessly take baccin saboda sanyi, still dai bata juya ba, ya shiga cikin dakin, ya nufi gun room heater din shi ma ya kunna yaga bai yi ba, ya fi minti daya tsaye dakin, sai kuma ya juya ya fita, dakin Jay ya nufa ya bude ya shiga ya dauko white duvet dinsa, sannan ya fito ya koma dakin da Khaleesat take, sai da ya fara duba tagogin dakin to be sure they are locked, sannan ya rufa mata duvet ya juya ya fita ya kullo kofar, kamshin turaren Jay ya cikata gaba daya, nan da nan ta nemi baccin da take yi ta rasa, and she felt so warm, a hankali ta jawo wayarta tana kallon call logs dinta don har sannan Jay bai biyo kiran da tayi masa ba a apartment dinta, ta kunna data dinta ta duba WhatsApp taga nan ma bai ajiye mata message ba, and she even saw him online, sauke idonta tayi, nan da nan taji hawaye na taruwa idonta ta fita daga WhatsApp din ta shiga contact dinta ta goge numbersa da tayi saving daga wayarta, sannan ta ajiye wayar ta rufe har kanta da duvet din tana kuka a hankali, wajen karfe sha daya saura ta zamo kasa a hankali ta dalilin sharp pain da take ji a abdomen dinta, tana durkushe for almost 10 mins daga karshe ta mike da kyar ta shiga bandaki, sosai gabanta ya fadi ganin period dinta ne, ta kasa fitowa daga bandakin, at last dai ta jawo kafa ta fito tana tafiya a hankali, to yanxu ya za ta yi, ta kalli white bedsheet da duvet din Jay dake saman gadon, ba wai ta fara flow sosai bane amma tasan dai hakan zai iya faruwa ko zuwa anjima, a hankali ta durkusa kasan dakin, bata ma damu da sanyin da take ji ba, ta jawo wayarta tana tunanin yanda zata yi, ko dai tayi order din Uber zuwa apartment din nata, amma dai tsoron komawa gidan kuma take, tana jin alamar saukan period din ta mike a hankali, duk jikinta a sanyaye ta nufi kofa ta bude ta fita, ta dade tsaye corridor kamar mara gaskiya daga karshe dai tayi gathering courage ta karasa har bangaren Ajay, tsaye tayi jikin kofarsa kamar tana tausayin kofar tayi knocking gently, Ajay dake danna wayarsa ya juya yana kallon kofar, ta sake knocking a hankali, ya mike zaune ya jingina da gadonsa ya ajiye wayarsa ya rungume hannu yana kallon kofar, idan yace bai gaji da yarinyar nan ba yayi ma Allah karya, daukar wayarsa yayi, yayi dialing number Jay fuska daure, after some seconds Jay ya daga, Ajay yace “Wai yaushe ma kace zaka dawo ne?” Jay yace “Gobe zan tafi Nigeria” Ajay yace “Na gaji da wannan brat din da ka bar ni da ita a kasar nan, you know i have anger issues, I can’t tolerate her anymore wallahi…” Jay dake ta sauraronsa yace “To ka iya ajiyar ribbon for more than 2 months, me ribbon din ce baza ka iya ajiyewa under your watch ba?” Shiru Ajay yayi, Jay yace “Hang up pls, Mami tana kirana” Ajay ya kalli screen din wayarsa don daga can bangaren Jay ya katse wayar, ajiye wayar Ajay yayi idonsa akan screen din ko kiftawa baya yi, after almost a minute yace “What is he talking about, meye ma ribbon?” A hankali ya dau wayarsa ya shiga Google yayi typing ribbon…..*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda*07087865788

Back to top button