Sirrin Rike Miji

Maganin Kaikayin Nono (Breast Itching)

KAIKAYIN NONO (BREAST ITCHING)

Kaikayin Nono walau a budurwa ko ga me aure, kokuma wacce ta ta6a haihuwa ko kuwa sabanin hakan abune dake faruwa.Nono dai bangare ne na jiki da ya kunshi mahimman kwayoyin halittu daban-daban gami da kitse da lallausar tsoka mai raga-raga tattare cikinsa da kuma acan kansa (nipple) wadanda duk ke taimaka masa ya zamo yana jin ta6i da samar da wadataccen ruwan nono don jin dadin shayar wa idan lokacin bukatar hakan tataso.

Karanta>>> Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

Kaikayin nono yakan zamo abu marar dadi gami da takura ga mace musamman budurwa, sannan hakan a wani bangaren kan iya kasancewa alama dake nuna samuwar wata matsala amma de yawanci abunda ke jawo hakan sun hada da:-

Karanta>>> Dalilan Dake Sawa Nonuwa Suke Zama Kanana

1- Shigar ko hawan kwayoyin cuta (infection) kan fatar nono, wannan kan jawo kaikayi a wasu lokutan susar ta jawo kuraje inda gurin kan iya dadewa ko yayi jah.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

2- Sai inya kasance ana wanke rigar nono da wani sinadarin omo ko sabulu da fatar macen bataso hakan kan iya sa idan mace tai zufa irritant din ya naso bra din tafara jin kaikayin.

Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam

3- ko Kuma sabulun wankan mace ya kasance allergies ga jikinta. Ko kuma Shanya irin Wannan kaya arana bayan wankesu ciki harda pant. – Anfi so ake shanyasu adaki ko cikin Toilt me rufi.

Karanta>>> Tusar Gaba Da Abinda Ke Kawota Yana Da Kyau Ku Karanta Wannan Bayanin

4- Sannan kan iya kasancewa alama dake nuna akwai wani nau’i da kan iya haddasa sankarar nono (breast cancer) a jikin nonon wato bayyanar Kari ko ince lump acikin breast.

Karanta>>> Yadda Ake Matsi Da Tafarnuwa

5- Akwai Kuma yanayin reaction na tafiyar sinadaran hormones na glands din cikin nono irinsu prolactin hakan ma nasa wasu suke jin kaikayi musamman a mata masu karfin sha’awa..

Karanta>>> Yadda Zaki Hada Sabulun Da Zai Sa Ki Dinga Kyalli, Santsi, Kamshi Da Kuma Maganin Kuraje

6- Zufa a mata masu kiba da yawan zufa akai-akai wannan ma na sa in gumin ya ratsa fata suji duk sun takura inda in ba canza wata bra din sukai ba ko suka cire kaya suka sha iska wannan na jawo kaikayin.

Karanta>>> Domin Dawo Da Martabar Nonuwanki Cikin Sauki.

SHAWARA

Akan yi kokari a gano a inda matsalar take a magance walau shawarwari ko magungunan rage radadi.

Sannan a san irin sabulu ko Omo da za’a ke wanke irin wadannan inner wear👙 din.

In an wanke su ake shanyasu inda hali a inuwa Koma cikin daki Saboda in iska na kadawa zata iya dauko abubuwa masu kaikai ko kwayoyin cuta ta budesu wannan ko ya harma da pant ba iya bra kadai ba.

Sannan shanyasu a inuwa zai sa rana baza tai musu dukan da zasu iya zama allergic ga fata ba.

Sannan a koyi breast checkup duk bayan wata uku ki tsaya ki duba shape Sannan ki daddanna ciki ki ji ko akwai kullutu wato lump dan daukar mataki. ko na nuna alamun da ake gani idan cancer tana neman kama nono wata ko da budurwa ce zata iya ganin inta matsa Kän nonon ruwa na fitowa sai a dauki mataki.

Karanta>>> Matsi Ga Sabbin Amare Kafin Kije Gidan Miji.

MAGANIN KAIKAYIN NONO

A nemi Ma’ul khal a wanke wajen ko a goge wajen ta gabyar Dangwalar Ma’ul-khal din da auduga a shafa ko a goga a wajen, In ya bushe sai a shafa Man Hulbah Dan Misrah a gun, haka za a dinga yi safe da yamma zai dena InshaaAllahu.

ALLAH YASA MU DACE. YA BAMU LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA

Back to top button