Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 12 Complete Hausa Novel

Tun amsa ɗaya da Aziza ta bama zainab ba ta sake magana ba

Har zainab ta gaji da surutun ta tayi shiru.

Gaba ɗaya Abdul be san a inda kan shi yake ba, 

Nannauyan bacci ne yayi awon gaba da shi, 

Da ƙyar Zainab ta iya jan shi ta gyara mishi kwanciyar shi.

Ta jima a zaune tana tunanin rayuwa, labarin Abdul ya taɓa ta matuƙa, sannan ita aljanar ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar Abdul ɗin.

Nan taita saƙe-saƙen ta, daga baya ta tashi ta shiga kitchen dan ta samar musu abinda zasu ci, tunda akwai komi a gidan.

Har ta shiga kitchen ɗin ta fito, ɗakko maganin da Abie ya bata tayi ta sake kunna shi tukun ta koma ta fara ƙoƙarin haɗa girki, ƴar baƙa na nan biye da ita duk in da taje.

Sosai Zainab ta nutsu ta shirya lafiyayyen abincin ta da ya cika ko’ina da ƙamshi, 

Tsaf ta gama sannan ta ɗakko komi ta shirya shi a dining.

Kallon Abdul tayi taga yarda yake haɗa zufa kamar ba’a kunna Ac a palon ba, 

Har ta juya da niyar tashin shi, ta fasa.

Haurawa tayi sama da niyar watsa ruwa kafin shima ta tashe shi.

Ta ɗauki kusa awa ɗaya kafin ta sakko.

sanye take da blue atamfa, ɗinkin bubu da ya fito da zallar ƙuruciyar ta da kuma hasken fatar ta, ta kashe ɗauri ya zauna ɗas a kanta.

Ba wani kwalliya ce can me yawa a fuskar ta ba, daga powder se kwalli da man baki, amma kar kuso kuga yarda ta fito a amaryar ta cas, sedai idon ta ne da har yanzu be koma normal daga kukan da sha ɗazu ba.

Ƙaurin maganin da ta saka duk yabi ya gauraye da ƙamshin girkin ta, se ƙamshin ya yi ba ɗaɗi.

Komawa sama tayi ta ɗakko turaren wutar da ba’a kai ga jera mata su ba ta sakko da su.

Haɗaɗɗen turaren kajiji da yaji haɗi na musamman ta ɗauki ƙwaya uku ta saka a bunner, sannan ta rufe ta bar wajen.

A hankali ƙamshin shi yake game palon, seda taji ƙamshin shi ya fara tashi tukun ta ƙarasa inda Abdul ke ta faman juyi.

Ta jima sosai a kanshi kafin a hankali ta ɗan bubbuga gefen kumatun shi tana tashin shi.

Can cikin bacci Abdul yaji tattausan hannun ta a kumatun shi, ji yayi wani sanyi-sanyi na ratsa shi, kamar tana mishi waiwayi haka yake ji.

Kaɗan kaɗan ya fara buɗe idon shi, da sauri ya maida su ya kulle, sannan ya sake ɗan ƙyallaro su.

Kamar wawa haka ya saki baki yana kallon Zainab da yaune farkon ganin shi da ita a hakan.

Can cikin zuciyar shi yace “Allah kai ne abun godiya”

Yunƙurawa yayi ya tashi duk jikin shi yayi tsami yace.

“Saura ƙiris wannan kwalliyar taki tasa na kwasa da gudu, duk a tunani na a wani gidan nake ba a wannan ba”

A tare sukai dariya, can tace

“Da zaka dawo da kanka ai”

sake kallon shi tayi tace

“kaje kayi wanka se muci abinci kafin lokacin sallah yayi”

Da mamaki Abdul ya sake kallon ta,

“Wai girki kika yi?”

Gira ɗaya ta ɗaga mishi, can dai fuskar ta takoma zuwa tausayi tace

“Wai Amaryar kwana ɗaya ce ke girki”

Da damuwa shima yace

“Ban san bacci ya ɗauke ni ba wallahi, amma ina da niyar inyi mana order” 

Ganin yarda yayi magana yasa da sauri tace

“wasa fa nake maka malam, amma ai girki yana ɗaya daga cikin abinda nake so”

Murmushi yayi ya tashi ya haura sama yana cewa “minti shabiyar yayi yawa na dawo, inzo in kwashi girkin amarya ta”

Seda taga ya ƙarashe haurawa sannan ta ce

“Ka jini da gulma “wai girki na ɗaya daga abinda nake so”

ƙyalƙyalewa da dariya tayi, ta ɗora da “Ba abinda nafi so sama da kwanciya in huta yasin”

Ita kaɗai taita ma kanta dariya, “wai ita me miji”

Can ta ƙara cewa “wallahi na wani gaji da kame kaina tun jiya, haka nan an saka ni yin wani iyayi da kisisina,” 

Ƙwata tayi sannan tace “Na kusa komawa ainihin zainab ɗina wallahi”.

Remote ta ɗauka ta maida shi tashar Suunah TV ta ci gaba da kallon tana tunanin abubuwa sama-sama.

Abdul da yace minti shabiyar, se gashi yana dosar awa be sakko ba

Tun zainab na kallon agogo har ta gaji ta tashi itama ta haura saman.

Ɗakin da aka fara kaita ta shiga, wayam bata ji motsin shi a ciki ba ta janyo ta wuce ɗayan kai tsaye.

Tana tura ɗakin taga Abdul zaune ya miƙe ƙafa yana kwasar girkin da ta san ba ita ta dafa shi ba.

Sororo ta tsaya tana kallon Abdul da ya ɗago kan shi yana murmushi, 

Fuskar shi cike da annuri yace

“Halan baki ga inda na aje su ba?”

Zainab da gaba ɗaya idon ta ya ciko da ƙwalla ta kalle shi da alamun tambaya tace

“Me kake nufi wai?”

Tissue ɗin gefen shi ya zara ya goge bakin shi sannan yace

“wayoyin da nace ki ɗakko min mana”

Ta mai-maita wayoyi yafi a ƙirga, idon a cikin na shi tace

“Ni baka aike ni ko’ina ba, ina ƙasa ina jiran ka ashe shanya ni kayi, kai kana nan kana cin kashin aljanu baka sani ba”

Ta ƙarashe maganar hawaye na sakko mata 

Jiki a sanyaye Abdul ya tashi ya kamota suka zauna a gefen gado, 

Murya a sanyaye yace

“Wallahi har na fito zan sakko muka ci karo da ke kin biyo ni da abincin, kuma fa a tare muka zauna mukaci, seda kika gama ci sannan  nace kije ki dakko min wayoyi na fa”

Ture shi tayi daga jikin ta sannan tace

“ka dena haɗa ni da ita, ni wallahi bani ka gani ba, ni ina can zaune ina jiran ka, kuma ni white rice na dafa ba fried rice ba”

Seda ta kai ƙofa, sannan ta waigo tace

“Ka cika tumbin ka da kashin aljanu wallahi, dan duk wanda aljani ya kawo ma abinci yaci, to ya tabbatar da ƙazantar su ya ci”

Tana gama faɗar hakan ta janyo mishi ɗakin ta sauka ƙasa a zuciye, 

Duk yunwar da take ji haka ta zauna tana jiran shi, ashe shi yana can yana kwasar gara

Dining ta zauna, ta janyo flask ɗin white rice ɗin ta zuba a plate sannan ta zuba sauran kayayyakin a kai

Tana kai lomar farko bakin ta tayi saurin dawo da ita,

 a guje ta janyo robar ruwa ta buɗe ta kafa bakin ta akai

Dai-dai nan Abdul ya biyo bayan ta, akan idon shi ta dawo da abincin

Ido waje ya dafa ta yana tambayar ta “lafiyar ki kuwa”

Kuka zainab ta fashe da shi tace

“wallahi bazan yar da ba, ni ba haka nayi girki na ba, ni sam ban saka gishiri a girkin ba amma yanzu na zuba naji kamar an juye min buhun gishiri a cikin miyar”

Shiru Abdul yayi, can ƙasan ranshi yake cewa 

“zata aikata fiye da hakan ma”

Jin shirun da yayi ne zainab ta saka hannu ta mintsine shi, firgigit ya dawo daga tunanin da ya tafi

A hankali ya ɗauki spoon ɗin data aje ya saka a plate ɗin ya ɗebi abincin, har ya kai baki ze ci, aka kaɓar da cokalin daga hannun shi.

Seda yayi hakan so kusan uku ana kaɓarwa, daga baya dai ya haƙura da ci,

Kujera ya ja ya zauna ya zuba mata idanu ganin yarda take kukan ta bilhaƙƙi da gaskiya, abin se ya sosa mishi rai

Nan da nan idanun shi suka kaɗa sukai jajir saboda zuciyar shi dake tafasa

Murya a sanyaye yace

“Ɗakko hijabin ki muje na kai ki kici abinci”

Tana sharar ƙwallar ta taje sama ta ɗakko sannan ta sakko, ƴar baƙa na biye da ita a baya

Seda ta kashe komi tukun ta fito ta same shi zaune a cikin mota ya kifa kanshi, har ta shigo be san ta shigo ba seda ta yi magana tukun ya ɗago kan shi.

Murya a sanyaye Zainab tace

“kar ka saka damuwa a ranka, Allah yana tare da mu, yasan komi kuma da ikon shi komi ke faruwa, sannu a hankali ze mana maganin komi”

Kamo hannun ta yayi ya saka a nashi, yace

“Nagode da tunatarwar ki, kuma ina me baki haƙuri akan duk wani abu da zaki ci karo da shi dan Allah”

Hannun ta ta ɗora akan bakin shi, sannan tace

“Ka dena bani haƙuri akan laifin da ba naka ba, ubangijin mu baya taɓa ɗora mana abunda yasan ba zamu iya ba, Allah kawai ya bamu ikon cin wannan jarabawar yasa tazo ƙarshe dan soyayyar da Allah ke ma annabi muhammad”

A tare suka amsa da “Sallallahu alaihu wasallam”

Ya jima yana rungume da ita, jin ta yake tana ratsa duk wani jijiya dake jikin shi, 

Seda ta fara mutsumutsun gajiya tukun ya sake ta sannan ya fita ya buɗe gate, ya dawo ya fitar da motar, tukun ya sake fita ya kulle ƙofar.

A hanya ba wanda ke magana a cikin su, kowa da duniyar da ya tafi

Zainab kam labarin rayuwar Abdul ne yaƙi barin zuciyar ta, 

Gani take kamar baza’a samu masu zuciya irin wannan ba na ƙin kula

Ajiyar zuciya me nauyi ta sauke tana faɗin “Allah ka iya mana da iyawar ka”

Ɗan kallon ta yayi, jin numfashin da ta sauke, hannun ta ya kama da ɗayan hannun shi, hankalin shi rabi na ga hanya rabi na gare ta yace

“Me kike tunani?”

Murya a sanyaye tace

“Har yanzu ina mamakin labarin ɗazu ne,

A yanayin zuciya ta ni kam ba zan iya aikata ma ɗan kowa hakan ba, 

Gani nake in har Allah yasa abu ya shigo rayuwar ka, to tabbas akwai abinda Allah yake nufi da hakan, kuma ka haifi ɗa ne baka san wanda ze kula da shi ba, tunda har kaga ɗannan ya shigo ƙarƙashin kulawar ka, to tabbas akwai abinda Allah ke nufi da hakan”

Sosai Abdul ke mamakin kalaman zainab, magana ce da ko wani babban me shekaru da dama baze yi wannan tunanin ba

Ɗan matsa hannun ta yayi kaɗan yace

“Na jima da yafe ma ummie duk wani abu da tai min fa, ita kanta tun a lokacin ta gane kuskuren ta sosai wallahi, 

Abinda na sani shine ba zaka taɓa sauya wa mutum wani abu da ya zamana halin shi ne.

Ummie tana da kirkin ta dai-dai ita fa, karki sa wani abu a ranki ya dame ki, yarda da kuma son da nake miki ne yasa har na iya baki labarin ma”

Jin kalmar “so” da Abdul ya faɗa ya sa zainab ɗaga ido ta kalle shi, dai-dai shima yana kallon ta a ido

Gira ɗaya ya ɗaga mata yace

“da gaske nake Zainab, ina son ki tun a ranar farko da na fara tozali da ke”

Kunya ce ta lulluɓe zainab, tai saurin juyawa ta maida kanta gefe,

Murmushi shima yayi, dai-dai sun karyo kwana zasu shiga resturant.

BAYAN WASU KWANAKI.

*****Yauma ta sake zuwa, ta gargaɗe ni akan zainab, ban san ta inda zan fara sanar da Abdul ba gaskiya, gashi har suna dosan wata da aure kuma abu yaƙi ci yaƙi cinyewa.

Shiru mama tayi tana tuna wayar da sukai da zainab ɗin a jiya, 

Murya a sanyaye tace

“Zainab na da ƙarfin zuciya ƙwarai malam, jiya data kirani tana bani labarin yanayin da suke ciki abun sam ba daɗin ji, nidai nace kawai taci gaba da addu’a muma muna taya ta”

“Addu’a mafita ce, amma abu ɗaya zasuyi ta tafi ta barsu har abada”

Dawowa kusa da shi mama tayi, tace

“ka faɗa min ai, kuma ga dukkan alamun yarda muke waya da ita ban jin wani abu ya shiga tsakanin su ba, amma ga shawara malam”

Gyara zama sosai Abie yayi yace

“ina jin ki”

Mama tace “me ze hana ka kira mahaifin shi Abdul ɗin, ka sanar da shi komi, in yaso se ya kira ɗan shi yayi mishi bayani”

Shiru Abie yayi yana nazarin maganar mama, 

Can dai ya numfasa yace

“shawara me kyau, inshaAllah zuwa anjima zan neme shi da zancen”

Kafin mama ta yi magana suka jiyo muryar IYA na ƙwala mata kira

Tun ranar da aka ɗaura ma zainab aure IYA taƙi yarda ta koma gidan ta sabida tsabagen tsoro.

Amsawa mama tayi ta yunƙura ta fito daga wajen Abie.

“gani IYA”

Kamo hannun mama IYA tayi suka zagaya ta can bayan tsohon ɗakin zainab, tace

“Ga mushen dake mana wari nan ashe”

Da mamaki IYA ta sake cewa

“wai Binta in tambaye ki?”

Mama data toshe hanci tace

“inaji iya”

IYA Ta gyara tsayuwa tace

“wai zainabu na ta maido da ƴar baƙar ta ne dama?”

Mama tace “a’a Iya, ai dama ban bari ankai mata ba”

Wani danƙareren salati IYA ta buga tana ja baya da sauri, ido waje take nuna ƴar baƙa data kumbura tai dam, ƙudaje nata binta, 

Kasa magana tayi ta juya a sukwane ta bar wajen tana ci gaba da salatin data fara, 

Ɗakin da a yanzu shine ya zama nata ta shiga

Janyo jakar kayan ta tayi ta fara tusa kayan ta dake ajiye a gefe

Abie da mama a tare suka shigo ɗakin suna tambayar ta me yafaru

Ba wanda taba amsa a cikin su sema share ƙwalla da take ta aikin yi.

A nutse Abie ya tsugunna a kusa da ita yace

“Haba IYA, duk kin sa hankalin mu ya tashi, dan Allah me ya faru?”

Tsayawa tayi da haɗa kayan data ke ta fashe da kuka, sannan tace

“Abun ya fara wuce gona da iri, ya za’ayi ace in ɗauki ƴar baƙar zainabu na da kaina in saka ta a mota kamar yarda kowa ke shiga, nace akai mata, yanzu kuma inga mushen ta a gidan nan sannan ace dama ba inda aka kaita tana nan alhalin ni na san da hannu na na bayar da ita akai mata

To gara na nisanci jama’a kafin na fara cutar da su, tunda nima naga alamar na fara rikiɗewa gaskiya.

Da mamaki Abie yace “Da kanki fa kika ce IYA?”

Baki ta sake ɓarewa tace “shiyasa nace maka na fara rikiɗewa nima, 

Haka nan muna zaman zaman mu kaje ka jawo mana danƙara danƙaran lukutar masifu bamu san hawa ba bamu san sauka ba

Lukutar masifar da zainabu na ke a cikin ta Allah ne kaɗai ya sani,”

Ba wanda ya ce uffan, IYA taci gaba “eh mana ai baku da bakin magana wallahi,  yo ni ko labari aka bani ace ba wai da idona na gani ba, wallahi gida arba’in gefe da gefen gidan zainabu na ba zan shiga ba, 

Itama Allah ya fito da ita lafia, wa ya sani ko tana can itama ta gama rikiɗewar bamu sani ba muna nan tunda ga alamu nan sun fara nunawa”

Tunda Iya tace ta saka ƴar baƙa a mota, jikin Abie yayi sanyi, ae yanzu yake gane a inda matsalar take da ta ƙi ci taƙi cinyewa.

Tashi yayi ya fito ya barsu a ɗakin yayi hanyar nashi ɗakin, wayar zainab Abie yayi ta kira amma se a  ce mishi a kashe take, sauya aƙalar kiran yayi zuwa wayar Abdul, shima a kashe

Su kuma a dai-dai lokacin suna tsaye suna kallon ikon Allah, basu san ta yarda akai wayoyin sun suka tarwatse suka yi ratsa ratsa, kamar irin an saka dutsen nan an kwankwatsa su

Zainab ta kalli Abdul, shima ya kalle ta, dukkan su ba baka se kunne, 

ga ƴar baƙa nan a gefe itama tayi wuƙi-wuƙi da idanu kamar yarda taga suma sun yi.

Abdul ne yayi ƙarfin cewa

“Ta ya hakan ta kasance?”

Ɓata rai zainab tayi, tace

“ai ba se an ɓata baki ba wajen tambaya, kowa ya san waye ai, wallahi Allah ya saka min”.

Juyawa tayi ta ɗauki ƴar baƙa a hannun ta da niyar komawa sama, 

Takurewa tayi ta yakushe ta, da sauri zainab ta sake ta tana duba gefen hannun ta inda har sheda yayi

 

Ƙwata zainab tayi, ranta duk ba daɗi tace

“kin dena sona kwata-kwata ƴar baƙa, tunda muka zo gidan nan kika sauya”

Zainab bata kawo komi a ranta ba, ta juya tayi wucewar ta, 

Kamar jira take zainab ɗin ta juya, aikuwa ta ɗare jikin Abdul tana lasar shi tana kaɗa bindi, shi kuma ya hau shafa bayan ta yana jin yana hucewa daga fushin da yayi na fasa musu wayoyi.

Littattafan ta kwaso ta dawo ƙasan inda ta bar Abdul da ƴar baƙa

Zama tayi a kusa da su, tana bitar littafin data ɗauka, can Abdul yace

“Baki lura da yanzu ƴar baƙa ta fi son zaman a jiki na ba?”

Murmushi kawai zainab tayi tace

“Ga alamu nan ina gani, da bata yarda ko kaɗan nayi nesa da ita, amma yanzu ko dani ko ba ni, be dameta ba”.

ƙara matsowa kusa da shi zainab tayi tace

“Yamma tayi, matso muyi azkar”

Sum,sum ƴar baƙa da sauka daga jikin Abdul tayi hanyar kitchen

Ɗan kallon ta tayi tana nazartar ta, can dai ta ɗauke tunanin dake bijiro mata a zuciya suka fara karanto azkar ɗin safe da yamma wanda yazo daga bakin manzon Allah.

ƊANƊANO! ƊANƊANO!!

DAGA BOOK ƊIN

 “MAKIRCI” 

NA MRS SULAIMAN(ZAINAB FALALU)

Da ƙyar da jan ƙafa ta sakko daga kan gadon ta,

A hankali ta fara lalubar bangon ɗakin, inda makunnin wutar yake ta kunna

Haske ne ya gauraye ɗakin

A hankali, cikin jan ƙafa ta sake komawa gefen gadon ta inda Mardiya ke kwance tana bacci.

Hannun ta na karkarwa ta fara tashin mardiya dake kwance, 

Murya a raunane tace

“Mardiya, mardiya, tashi”

Warda aka kira da mardiya, ta tashi da sauri tana ƙoƙarin sakkowa daga kan gadon

Da sauri mardiya ta dafa ta tace

“Ummu, badai jikin bane ya tashi?”

Ummu da ta kai ga durƙushe wa ƙasa tace

“Yi sauri ki je ki kira min Alhaji, ya daure ko asibiti ne ya kaini, na kasa jurewa mardiya”

Nan da nan idanun mardiya suka kawo ruwa, 

Da sauri, har tana cin tuntuɓe ta buɗe ƙofa ta fice

Duk girman gidan nan haka ta ratsa ta wuce ba ko alamun tsoro a tattare da ita.

Saitin babbar ƙofar da zata sadaka da ainihin cikin gidan mardiya ta ja ta tsaya ta hau danna door bell  a hankali, 

tsoro shimfiɗe a fuskar ta.

Kamar a mafarki taji ƙarar ƙofar,  agogo ta kalla taga uku saura na dare

Wani wawan tsaki ta ja ta dire tukun ta sakko daga kan gadon

Fitowa tayi, dan dama tun da wannan watan ya kama take tsumayin su

Ba tai wata-wata ba ta buɗe ƙofar tana ƙare wa mardiya kallo

Da sauri mardiya ta tsugunna, jikin ta na ɗaukar rawa tace

“Dama Ummu ce tace inzo in duba ko Daddy yana nan”

Ta ƙarashe maganar tana inda-inda

Wani wawan kallo ta watsa mata, murya ba mutumci yace

“Uban me Daddyn ze mata da tsakiyar daren nan banda jaraba irin na uwarki?”

Kafin Mardiya ta bata amsa, suka jiyo tafiyar  shi zuwa wajen su

Ko kallon inda mardiya ke a tsugunne beyi ba yace

“Gimbiya, lafiya naji muryar ki a sama da tsohon daren nan?”

Juyawa tayi saitin inda yake tsaye, ta nuna mardiya dake durƙushe kanta a ƙasa tana sharar hawaye, tace

“Saƙo ne aka bata wai”

A ɗan tsawace yace

“Ke, menene?”

Murya na rawa mardiya tace

“Ummu ce tace dan Allah ka daure kazo ka kaita asibiti, ta kasa jurewa wai”

A hankali ya maida idon shi ga Mummy dake tsaye tayi folding hannun ta a ƙirji,

Bece komi ba kuma bashi da niyar cewa komi

Cike da izza mummy ta kalli mardiya tace

“Kije gani nan zuwa”

A tsorace mardiya ta miƙe ta juya inda ta fito.

Kallon shi tayi taga yarda ya tsaya ƙiƙam bashi da niyar komawa ciki tace

“ka je ka kwanta ne, zan je na kula da komi”

Ba dan ranshi ya so ba ya juya ya koma ciki

Tana ganin shigewar sa tai hanyar ɗakin ta da gudu, minti kaɗan ta fito ta rufo ƙofar sannan tabi hanyar da mardiya ta bi itama.

Sanda mardiya ta koma ɗakin ummu ta gama jigata tai luɓus gunin ban tausayi

Mardiya na riƙe da ummu, mummy ta banko ƙofar ɗakin ta shigo hannun ta ɗauke da reza me tsatsa da kuma robar yaji da kaskon me ɗauke da rushi a ciki.

Da ƙyar mama ta lallashi IYA ta haƙura da tafiyar data ce, suka zauna sukai jigum-jigum kamar wanda akai ma mutuwa.

Abie kam tunda ya koma ɗaki ya sauya akalar kiran shi ga Abbah dake office zaune yana ɗan taɓa aiyukan da ba’a rasa ba

Da sauri Abbah ya ɗaga wayar ganin sunan wanda ke kiran shi, ya kara a kunne haɗe da sallama

Bayan gaisuwa da suka gabatar Abie ya ɗora da maganar da ya kira shi domin ta

Shiru Abbah yayi yana sauraren Abie da abinda yake cewa.

Seda Abie ya kai har ƙarshe tukun Abbah yace

“Insha Allah zan sanar mishi, duk da dai maganar tana da ɗan tsauri hakan, nagode ƙwarai da kulawar ka malam”

Seda suka ɗan taɓa barkwanci tukun suka aje wayar, kowa da abinda yake saƙawa a cikin zuciyar shi.

Abbah yayi yunƙurin kiran Abdul be san adadi ba se ya fasa ya aje wayar,

Ya jima yana taunar maganar da ze faɗa mishi kafin daga baya ya daure ya danna mishi kira

Runtse idon shi yayi yana jiran yaji Abdul ɗin ya ɗauka, amma se yaji ance mishi wayar a kashe take.

Ajiyar zuciya me nauyi ya sauke, kafin daga baya ya miƙe ya hau zagaye ɗan madedecin office ɗin nashi, yana nazarin ta yarda ze fara.

Ta ɓangaren Abie kuwa, ko da ya kira Abbah be gaya mishi abinda ze ɗaga hankalin shi ba, 

A gurguje ya shiga wanka ya fito, be wani tsaya ɓata lokaci ba ya shi

Yana cikin shirin ne ya kira Abubakar yace “ka same ni yanzu-yanzu”

Da “to” yaya Abubakar ya amsa, barowar shi kenan daga wajen yaya Abida, itama tun da ta sha dukan Aziza bata sake lafia ba, har seda ta dangane ta da komawa gaban iyayen ta.

Be wuce min ashirin ma ya kawo shi gidan Abie

Kafin ya ƙaraso duk yabi ya ƙosa, 

Mama kawai ya faɗa ma inda zashi, kuma yace kar ta sanar ma Iya

Fatan dawowa lafia tayi mishi, gaba ɗaya jikin ta a sanyaye.

Yana fita ya buɗe gaban motar ya shiga,   yaya Abubakar yace

“Ina zamu je Abie?”

Kai tsaye Abie yace

“Gidan Auta zamu je”

Yaya Abubakar bece komi ba, dan yasan ko a musulunce in uba ya kai ma ƴarsa ziyara ba laifi bane

(SUNNAH CE BABBA! MANZON ALLAH S.A.W, YANA KAIMA NANA FAƊIMA ZIYARA A DUK LOKACIN DA YAKE DA DAMA)

Sun ɗau hanya suna tafia motar tai shiru, baka jin komi se sautin radio

A hankali Abie ya waigo ya kalli yaya Abubakar yace

“Da gaske lokacin auren zainab, Iya ta baku magen ta ku kai mata?”

Ɗan shiru yayi na ƴan daƙiƙu, can yace

“eh, ta sakota a mota, bamuyi nisa ba ta fara tsalle-tsalle na son ta fita, shine na jiyo na sauke ta a ƙofar gida ta shige da kanta, amma bamu kai mata ba”

Ajiyar zuciya me haɗe da hamdala Abie yayi, can ya bashi labarin darun da Iya tayi musu ɗazu.

Dariya yaya Abubakar yayi ta kwasa, yace 

“Ai Iya ta firgita ƙwarai”

Abie yace “dalilin da yasa zanje gidan kenan, amma tun da dai nayi niya muje mu gaisa se mu dawo.”

Sama-sama suke taɓa hira, itama duk akan zainab ɗin ne, da kuma abubuwan da suke faruwa daki-daki.

A ƙofar gidan Abdul yayi parcking, suka fito

Tsayawa suka yi, sake kiran wayar zainab Abie yayi amma shiru

Bari a buga musu kawai, cewar yaya Abubakar da shima ya  kira wayar Abdul ɗin a mma akashe.

Zainab na zaune tana takaicin, tana tsaka da wanka kawai aka kashe mata ruwa, gashi duk ta mulka kumfa a jikin ta,

 kuma tayi-tayi ta gwada famfon wani ɗakin amma suma duk sun ƙi y,

 ga kuma Abdul ya fara wannan baccin na shi tun kafin ta shiga wanka ya kwanta, tashin duniyar nan tayi mishi amma kamar mushe.

Haka nan ta haƙura ta ɗaura zani akan kumfar ta fito palo tai zaman ta, 

Ga takaicin ba wanda ta sani a unguwar, ka takaicin rashin waya, ga kuma takaicin ba wanda ke zuwa inda suke

Tsaɓar takaici da ya isheta kawai fashewa da kuka tayi.

Tana tsaka da kukan ne taji ana buga ƙofar gidan, 

Seda tai tsamm ta saurara da kyau sannan ta tabbatar da nan ɗin ne ake bugawa abunda tunda aka kawo ta gidan ba’a taɓa yi ba

Da sauri ta ɗauki hijabin ta dake aje gefen ta tasaka ta fita.

Ko tambayar waye bata yi ba, kawai ta buɗe ƙofar

Tana buɗewa taga wanda bata yi tsammanin gani ba, ai da gudu ta faɗa jikin Abie ta fashe da kuka me taɓa zuciya

Daga Abie har yaya Abubakar sororo suka yi suna kallon ta da mamaki

Tunda ta kifa kanta a jikin Abie taƙi yarda ta ɗago balle har ta yi musu iso zuwa cikin gidan.

Ɗa da mahaifi se Allah, nan da nan jikin Abie yayi sanyi, dariyar da ke fuskar shi ta fara raguwa a hankali a hankali, a ranshi yake jin kukan zainab, duk da yasan ta sarai da kuka mara dalili, amma jin wannan kukan datake yana zuwa ne daga ƙasan zuciyar ta.

Yaya Abubakar yace “Abie mu shiga daga ciki ne, duk wanda yazo wucewa se ya kalle mu, kuma fuskar ka ba ɓoyayyiya bace”

Hannun zainab Abie ya kama, yace “ka rufe motar ka shigo” sannan suka shiga shi da ita.

Seda ya barta ta gama kukan ta tsab bece mata komi ba be kuma hana ta ba, 

Dan kanta tayi shiru, se faman aikin sauke ajiyar zuciya da take.

Ganin tayi shiru, sannan Abie yace

“Oh zainabu na ta zama raguwa” ya yi maganar cikin zolaya

Ɗan murmushi kawai zainab tayi me haɗe da guntun hawaye, tukun tace

“sannu da zuwa Abie, bari in kawo muku ruwa”

Duk da ranshi ba daɗi amma seda suka murmusa shi da yaya Abubakar.

Ko da ta dawo, bayan ta aje musu ruwa da ɗan lemo me sanyi, kusa da Abie ta koma ta zauna, kanta a ƙasa tana ta murza hannu

Kusan zamuce ɗabi’ar zainab ce in har tana son yin magana.

Abie na lura da hakan yace

“uhum, ina jinki auta”

Bayan hannu zainab ta saka ta sake share hawayen da ya zubo mata, murya na ɗan rawa tace

“Abie ni gaskiya na gaji da zama a gidan nan”

Ɗari bisa ɗari ya mayar da hankalin shi kanta, ba ko ɗar a ranshi yace

“menene hujjar ki?”

Cikin kuka zainab ta cire hijabin jikin ta, tace

“kalle ni Abie, wallahi nafi awa uku zaune a hakan, wulaƙancin da nake gani kullum gaba yake Abie, ina wanka ɗazu, seda ta bari na saka kumfa a ko’ina ta je ta hana ruwan gidan zuwa gaba ɗaya, da ƙyar na samu na goge idona na fito zuwa sauran ɗakunan, amma suma duka babu, haka nan na haƙura na zo na zauna”

Abie yace “ina mijin naki yake?”

Zumɓuro baki zainab tayi sannan tace, “ai kullum be da aiki se bacci me nauyi Abie,

Ɗazun nan fa shima muka sakko muka ga wayoyin mu duk an fasasu, kuma wallahi Abie tunda aka kawoni gidan nan ban taɓa yin girki ya ciyu ba, 

kullum innayi sedai a zubar, wani lokacin a zuba sugar, ko gishiri me yawa, wallahi rannan ma warin kwata naji a girkin, kuma dan mugun ta se ta ware shi ta bashi abinci lafiyayye ni kuma sedai muje waje mu siya”

Zainab bata tsaya ba taci gaba

“Ko shekaran jiya da yaje office, ina fitowa sedai na koma, saboda ko ina ya cika da kiyasai wasu akan wasu, wallahi sema ka gani Abie, haka nan dole na haƙura na koma ɗakin da yunwa ta har se sanda ya dawo,

Kuma yana dawowa ya fara tuhumata wai me yasa na fita ba tare da sanin shi ba”

Da sauri Abie ya katseta yace 

“Meyasa kika fita ba tare da sanin shi ba?”

Ɓata rai zainab tayi tace “wallahi Abie duk sharrin ta ne, ko ƙasa ban sakko ba seda ya dawo gidan nan, shima da kan shi ai ya gane daga baya ba ni ɗin bace”

Shiru Abie yayi, yaya Abubakar kam tunda zainab ta fara magana ya zuba tagumi yana kallon ta, can Abie yace

“Maganin da na baki ya ƙare ne?”

kanta a ƙasa tace

“Ban san yarda akai ƴar baƙa ta zaƙulo shi ba, sedai nazo na iske ta tai kaca-kaca da shi a ƙasa, kuma tayi fitsari a kai”

A razane Abie ya kalli zainab jin ta ambaci ƴar baƙa

Har ya so ya taune harshe wajen saurin yayi magana

“kina nufin ƴar baƙa na nan?”

The way yayi magana abun se ya ɗan ba zainab mamaki ko ma ince tsoro

Kallonta ta mayar kan yaya Abubakar tace

“ba kaine ka kawo ta ba ranar? mu lokacin muna can family house ɗin su?”

kaɗa kanshi yayi, yace 

“Bani na kawo ta ba”

Jin maganar tayi banbaraƙwai, da mamaki ta miƙe ta haura sama dan ta tabbatar musu da ƴar baƙa na gidan nan, amma lungu da saƙo na gidan nan ta duba bata gani ba, har ta haƙura ta sakko ƙasa inda Abie su ke zaune

Da mamaki a fuskar ta tace

“Ban san inda ta shiga ba, kuma ɗazu fa muna tare da ita a cikin ɗaki na”

Kafin Abie ya bata amsa ta juya da gudu, tana tafe tana cewa

“Ban duba ɗakin shi ba, in na nemeta na rasa can nake gano ta”

Abie na jin haka ya miƙe yabi bayan ta, yaya Abubakar ma ya mara mishi baya

A hankali zainab ta tura ƙofar ɗakin da Abdul

Tana saka kanta ta buga wani razanannen salati haɗe da ihu a lokaci ɗaya

Dai-dai Abie da yaya Abubakar sun ƙaraso

Da baya da baya zainab ta fara matsawa ganin yarda shimfiɗeɗiyar baƙar macijiya ta nannaɗe Abdul dake bacci,  ta fito da harshen ta tana ta lashe ko’ina na jikin shi

Su kansu su Abie tsiga jikin su tashi take ganin wannan masifa

Tsayawa sukai dukan su suna kallon yarda Abdul ke bacci cikin nutsuwa, kuma ga dukkan alamu yana matuƙar jin daɗin baccin.

Suna nan a tsayen, kan macijiyar ya fara rikiɗewa yana zama kan ƴar baƙa, jikin macijiya amma kan mage

Nan Abie ya sake gasgata lallai sharrin aljana Aziza da yawa yake, 

Ta rikiɗe ta zama ƴar baƙa dan ta shiga jikin su ta cutar da su ne kenan.

A hankali kuma kan ya koma na mujiya, jikin macijiya fuskar mujiya

Da bisimillah Abie ya saka kan shi cikin ɗakin, ba wani ɗar ko ɗaya a ranshi,

Direct kan gadon ya nufa, 

Tana ganin Abie ya tunkaro ta tasake rikiɗewa ta zama macijiyar gaba ɗaya,  har wani kumbura take tana ƙara girma

Cikin hukuncin ubangiji Abie ya samu ya damƙi kan macijiyar da sunan Allah

Yarda ya shaƙeta taji azaba, kawai ta koma suffar ƴar baƙa, haka Abie ya sake damƙe ta da iya ƙarfin shi, 

Ganin hakan baze mata ba, ta sake rikiɗa ta koma mujiya, duk da haka Abie be sake ta ba dan riƙon da yayi mata ba na wasa bane.

Yana riƙe da mujiyar tai wani jijjiga se gashi ta koma ɗan ƙaramin malam buɗa mana littafi(butterfly) 

Abie be ankara ba ta ƙwace, firr ta tashi sama tana neman hanyar ficewa daga ɗakin

Ya yunƙura ze kamota, tabi ta saman zainab da gudu zata fice

Cikin dakiya, zainab tai bisimillah ta kaɓota da ƙarfi, se ga butterfly a ƙasa ya kasa tashi

Da sauri zainab taja da baya ganin wannan butterfly ɗin ya ɓace ɓat daga wajen.

Abie bece komi ba, fitowa ya yi daga ƙofa ya ciro wayar shi, kai tsaye Abbah ya kira, sun ɗau lokaci haka suna magana kafin daga baya sukai sallama

Maida wayar yayi a aljihun shi, sannan ya kalli zainab da tai tsuru-tsuru, yace

“Je ki ƙarasa wankan, sannan ki haɗa duk wani abu da zaki iya ammafani da su na kwana biyu

Ba musu zainab ta juya ta koma ɗakin ta

Kallon shi ya maida ga yaya Abubakar shima da yake tsaye yace

Mu kama shi a saka mishi riga.

Da ƙyar suka iya saka ma Abdul riga, saboda yarda jikin shi ke a sake yayi nauyi

Suna a haka Abbah ya ƙaraso gidan, da ka ganshi zaka san lallai shima ba cikin nutsuwar shi yake ba

Dukan su ukun suka kamo shi suka sakko da shi ƙasa.

Zainab kam tun da ta shiga ta kunna ruwa taga yanayi ta shige tayi wankan ta, a ranta tana tsine ma wannan jarababbiyar Azizar

Tasan ana jiran ta, bata wani ɓata lokaci ba tayi ta gama, sannan ta shirya a gurguje ya ɗauki abinda zata iya ɗauka ta fito.

Sanda ta sakko har an saka Abdul a motar Abbah

Har ƙasa zainab ta tsugunna ta gaishe shi, kanta a ƙasa

Da fara’a sosai Abbah ya amsa mata, sannan ya ɗora da

“Kiyi haƙuri kinji ko zainab, Allah yayi maki albarka, kuma inshaAllahu komi ya kusa zuwa ƙarshe,”

Kanta a ƙasa tace “Amin Abbah, nagode”

Taso ta ɗan leƙa Abdul  kafin Abbah ya wuce da shi, duk da bata san me Abie ya shirya ba, amma can cikin ranta tana jin kewar shi tun yanzu.

Tana ji tana gani Abbah yaja motar shi ya tafi, 

Abie da kanshi ya karɓi mukullan gidan ya rufe, sannan ya saka keys ɗin a cikin aljihu.

Ganin ta tsaya yasa Abie ya kamata ya saka ta a mota, sannan ya aje mata jakar ta a kusa da ita

shima ya shiga, dan har yaya Abubakar ya kunna motar ma.

Shiru motar ta ɗauka, kowa da abinda ke ranshi.

Zainab kam tun ba’aje ko ina ba ta fara kewar fuskar Abdul.

Sannu a hankali suke tafiya har suka kai gida, sannan yaya Abubakar ya samu waje yayi parcking

Kafin su fito, zainab ta sungumi jakar ta tayi cikin gida cike da ɗokin ganin mama da kuma Iya.

****Tunda Abbah suka kama hanya yayi amfani fa shawarar Abie na kunna karatun  alƙur’ani a cikin motar,

Abu kaɗan ya waigo ya kalli Abdul dake kwance, banbancin shi da mara rai numfashi ne kawai 

Wani nannauyan abu ne ya danne mishi ƙirji, shi da yake tunanin auren shine mafita, gashi anyin amma abu yaƙi ci yaƙi cinyewa

Yana wannan tunanin ne maganar Abie ta faɗo mishi a rai

Shafa kanshi yayi yace “Ya subhanallah, ta ya hakan zata kasance bayan mutum kullum cikin bacci yake?”

Duk dauriya irin ta Abbah, seda yayi parcking a bakin hanya saboda yarda idon shi ya rufe gaba ɗaya ba ya gani, tsabar hawayen da suka cika mishi idanun shi

Yana tsayawa ya fashe da wani kuka me cin zuciya, 

Yayi kukan da rabon shi da yin shi tun rasuwar murjanatu, 

A hankali ya fara maimaita kalmar “LA’ILAHA’ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!”

Yana maimaita addu’ar nan yana jin zuciyar shi na sanyi da sauka

(ƳAN’UWA NA, MU YAWAITA LAZUMTAR WANNAN ADDU’AR, TANA TAFIYAR DA ƘUNCI DA KUMA DAMUWA”

Seda ya samu nutsuwa tukun ya ci gaba da tafiya.

Har gaban palon shi yayi parcking motar, sannan ya fara kici-kicin fito da shi

Amal ce ta fara ganin Abbah, da sauri ta ƙaraso inda yake tace “sannu da zuwa Abbah, me ya sami yaya Abdul?”

Se nishi Abbah yake, da ƙyar yace

“Zagayo ki riƙe min murfin motar”

Da sauri Amal ta zagaya tare da ƙwala ma ummie dake kitchen kira

Da sauri ummie ta fito jin yarfa Amal ta kwaɗa mata kira, birki ta jaa kiii, tana tambayar Abbah da “lafia?”

Be ce komi ba, se cewa da yayi “kuzo ku taya ni shigar da shi”

Ba musu ummie ta ajiye ludayin hannun ta itama tazo aka kama shi da ita.

Da ƙyar suka kaishi palon Abbah suka kwantar da shi, kowa nata zuba nishi.

***Zainab na shiga da IYA ta fara cin karo duƙe gaban famfo tana ɗaura alwala

A hankali ta aje jakar hannun ta, ta saɗaɗa taje ta bayanta ta mamutse ta da iyakacin ƙarfin ta

A razane IYA ta ƙanƙame idanun ta haɗe da rafka salati da iyakacin muryar ta

Duk da salatin da IYA ke zabgawa haɗe da yarda jikin ta ke rawa be hana zainab ƙara riƙe taba

Da gudu mama ta fito, dan itama yanzu zuciyar ta tsinkewa take da al’amarin nan gaba ɗaya

Da mamaki mama taja burki tana baza idanu tace

“Zainab! daga ina?”

Jin an ambaci Zainab yasa Iya ƙara rikicewa, ba abinda ya faɗo mata a rai se ranar da suka kai zainab ɗin,

Kuma akan idonta ta rikiɗe ta koma mujiya

Nan da nan Iya ta sassanƙame  tana faɗin

“Binta kuzo ku rabani da ita a jikina, wallahi ba zainabu na bace, wannan riƙon da tayi min bana bil’adama bane sam,”

Dariya kamar ta kashe zainab, duk da yarda take jin ranta babu daɗi sam, amma kalaman IYA sun yi mugun bata daria,

Sakin ta tayi taja da baya tace

“Kai IYA, a ina kika taɓa jin riƙon aljani ke kam?”

Tun da dai IYA ta samu zainab ta sake ta tayi bayan mama da sauri tana maida numfashin wahalar da ta sha, sannan tace

“Ai kuwa nice na shaida hakan, mu da aka ratso damu ta bango, in ba aikin jinsin ku ba to su uban waye zasuyi hakan?”

Murya ƙasa-ƙasa IYA tace

“Kalle ta da kyau Binta, naga ku kuna saurin gane wanda ba mutum ba, anya zainabu na ce kuwa?”

Murmushi mama tayi tace “kai IYA”

Taɓe baki IYA tayi tace

“Hummm, nayi danasanin da baki ga irin lukutar masifar da muka shiga ba a gidan ta, amma ai akwai wata rana, tunda har nace ki duba, kawai ki duba, ni kaɗai nasan abunda na sani Binta”

Zainab na tsaye tana kallon su, taga iya gudun ruwan su, ganin kamar tsoro-tsoro a tattare da mama yasa zainab ta sauya idanun ta tayi sama dasu tana jujjuya su

A hankali ta fara matsosu tana dalalo da harshe waje

Haba ƙafa me naci ban baki ba, mama da IYA suka danƙara a guje suka shige palon Abie da yake yafi kusa da ƙofar shigowa

Sanin mama ne ba wani aljani da ya isa ya shiga palon nan yasa tayi can, amma ga mamakin ta se taga itama tana biyo su,

Ganin sun faɗa da yawa yasa zainab, buɗe murya tace

“Zainab ce ta aiko ni, tace inzo in kaimata ke tunda ni da ita mun shirya kizo kisa albarka, taso tazo da kanta, shine nace ta bari in hutashshe ta ni nazo da kaina”

Rufda ciki IYA ta kwanta ta fashe da kuka, tace

“Zainabu bata kyauta min ba wallahi, kuyi haƙuri ku barni na sarara dan Allah, wallahi ban shirya hawa iska ba yanzu da magaribar nan,” ta ɗora da kalmar shahada da falaƙi da nasi

Kwanciya zainab tayi ta rinƙa kwasar dariya, dama tunda tayi maganar farko mama ta gane zainab ɗin ce, ita kanta dariya ta hauyi, kwata-kwata ta kasa riƙe dariyar

Ta ɓangaren IYA kuwa, ita a nata tunanin dariyar aljanu kawai take ji bata muta ne ba, tashin hankalin da take ciki ya kasa barinta ta gane sam.

Suna a haka Abie yayi sallama, yana tambayar hayaniyar me yake ji, be ƙarasa magana ba ya hango IYA kwance rufda ciki tana ta zuba magiyar kar a hau iska da ita, zata je da ƙafafun ta wallahi

Kallon tuhuma ya ke ma zainab sannan ya ƙarasa kusa  IYA ya ɗagota yace

“Kin manta shaƙiyancin zainab ne iya, ba wanda ya isa ya hau iska dake ina nan”

Tashi Iya tayi zaune fuska jaga-jaga, tace

“ka tabbatar dai ɗannan, ni ba yarda nayi ba gaskiya”

Juyawar da Abie zeyi yaga zainab na wurwurga idanu tana zaro harshe, da gudu ya ɗauki pilon gefen shi ya wurga mata, shima dariya nacin shi yace

“Kin manta haramunne tsoratar da mutum ko Auta?”

Dariya sosai zainab keyi har tana riƙe ciki, kamar ba itace ta gama kuka ba ɗazu, 

Da ƙyar tace

“wallahi Abie su suka tsorata kan su bani ba, shine na ƙarasa kaisu fa”

A hankali Iya ta miƙe tsaye tana goge fuskar ta da ta jiƙe sharkaf, 

Tunda ɗanta yace zainab ce, yanzu ta yarda, ƙanƙance idanu tayi tace

“Ja’ira, halan halin ki kika nuna musu aka sako ki?”

Dariya zainab ta sake kwashewa da shi tace

“Bikon ki nazo yi IYA ta”

Taɓe baki Iya tayi tace “ƙarya haram wallahi”

Mama da Abie har da zainab ɗin ma dariya suke ma Iya, ganin lokaci ɗaya ta maze ta dake kamar ba ita bace a ƙasa kwance tan  magiya.

Ƙofa Iya ta nufa, har tasa ƙafa zata fita ta kai ma zainab ranƙwashi a kai, tace

“muje ki rakani in kasayar da abinda ciki na ya ɗura”

Ɓata rai zainab tayi tana sosa inda iya ta ranƙwashe ta, sannan tace

“yasin hannun ki ne ma kamar wanda ba na bil’adama ba Iya”

Banza da ita IYA tayi, ta nemi bayi ta shige dan sauke nauyi.

GASHI NAN NA JIYA DA NA YAU😎

MASU CEWA NA RIKIƊE, BAN KAI GA RIKIƊEWA BA TUKUN🤣🤣

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU🤲

TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!”

INA MATA ƳAN ƘWALISA?

A.A.G COMPLEX YA ZO MUKU DA NAGARTATTUN KAYA, WRAPPERS, LACES, SHADDA, SHOES, BAGS, KAYAN KITCHEN, ROBOBI PLASTIC AND MORE.

A FARASHI MAI SAUƘI DA RAHUSA, MUNA MARABA DA KOWA DA KOWA

DOMIN ƘARIN BAYANI, ZAKU IYA TUNTUƁAR MU TA WANNAN NUMBER

07035046805.

Back to top button