Sirrin Rike Miji

Hanyoyin Da Ya Kamata Matan Aure Subi Domin Kara Inganta Zaman Aurensu: Malama Juwairiyya

ABUNDA KE QARA INGANTA ZAMAN AURE

Kamar yadda Al’kurani ya karantar damu; abunda ke karawa aure inganci yai danko ya zauna shine: (ASHURU HUNNA BIL MA’ARUF)

Ashiru hunna bil ma’aruf…. Anason Namiji ko yaushe ya zama kwasai-kwasai kamar goron bakin sarki. Namiji kwas-kwas yai shar cikin tsafta, da adoo…. Bawai arika ganinsa Bargajaja ba.

Karanta>>> Ga Masu Neman Karin Kiba Ga Hanyar Da Zaku Bi

Sannan Namiji ya zamto yana wanka, duk wani guri ajikinsa da yake da loko… da gashi yake fitowa toh ya zama yana kawarwa, yana askewa ya gyara farcensa, ya goge kafarsa da sanya sutura mai kyau.

Sannan Namiji ya rika amfani da turare, sannan bakinsa ya rika asuwaki ko brush akai akai,…. Abunda ya shafi su albasa ko Tafarnuwa ka kiyayi cinsu saboda MU’AMALARKA da kusaci da zakayi da mai dakinka. Anaso Maigida ya kiyaye wannan.

Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata

Sannan kullum Asuba anaso ka jaddada niyyar zaka rike Matarka tsakani da Allah, kuma zakai Hakuri da ita.

Idan ya zamto kana ado kana gyara jikinka, kana kwalliya, gami da kamshi komi na tafiya daidai…. Toh abu na gaba shine kiyaye harshenka.

Karanta>>> Yadda Zaki Kula Da Nonuwanki Lokacin Da Kike Shayarwa 

Ka kiyaye harshenka, ka rika fadar kalmomi masu kyau, ka dinga samo suna wanda zai yima Matarka dadi ka ringa gayamata. Domin inka duba kissar Nana Aisha da Annabi (SAW) aikaga wani irin suna yake fadamata… Tarhimi yakemata sai yace: YAA AH’ISHUUU….. Tana jindadin baice mata Aisha ba, sai A’eishuuu

Tanajin dadin cewa wanda yafi kowa kaunarta aduniya shi yake fadamata wannan kalmar… Alaihis salam wassalat. Don haka kasa mata suna mai kyau.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

Sannan lokacin da zakasata yi maka wata hidima… karka sata da zummar gadara, da iko irin dole tayi dinnan…. A’ah, ba’a haka

Da lumana ake sa Mace aiki….Misali; wance…. atashi ayi kaza da kaza badon sa aiki ba. Ita kuma inta tashi sai kaji tace; Ai ka isane 😅

Karanta>>> Ko Kunsan Amfanin Shan Kunun Aya

Sai kace; A’ah wane ni ni, kurum nafadane badon sa aiki ba. Ina ni ina wannan…. 😅😅 shikenan sai kaga ta tashi cikin nishadi. Haka akeyi yan uwana Maza. Da Raha da komai, anayi ana wadangarci haka akeso, kaita samata farin ciki azuciyarta harta dinga jin Gidan Auren yafi Gidan da aka haifeta.

Daga sanda Matar mutum tafijin dadin gidansa akan gidan mahaifatan toh daga lokacin Mutum ya zama KARIMI. Ka kar6ota “BI AMANATULLAHI WASA’ALATU FARJIHA BI KALIMATULLAHI….” toh yi kokari ka kula da ita.

Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata

Sannan duk abunda zai kunatata mata toh yi kokari ka farantamata. Koda wani abunne can daban da bakaine sanadin 6acin ranta ba.

■ Bazai yiwu kanaso kaga matarka fes-fes ba amma kai kace bazakai tsafta ba. Itama haushi takeji taga ka ware wata riga ko jallabiya kullum da ita kake zaunemata agida. Addinin mu bai barmu a duhu ba.

Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata

Wajibi ne mui tsafta domin cikon addini ce.

Allah yasa mudace.

Back to top button