Uncategorized

Abdul Jalal Chapter 2 Complete Hausa Novel

 

“Shigomana ya kika tsaya anan”.

Dagewa tayi ta boye tsoronta ta dai dai ta nutsuwarta, tashiga cikin dakin

“Kanwata ga Abokina kuma Dan uwana wato Jalal dukda kin sanshi amma nasan bazaki tunashi ba lokacin kina Karama sosai “

Download>>> Jiddertul Khair Complete Document

K

Jalal tayi taga mugun kallon dayake mata amma ta basar 

“Sannu” 

abinda tafada kenan ta maida kallonta kan Jawwad

“Yaya naga kanada bako in kungama na dawo karka manta da kiran Abba”

Ta juya tafita tana godewa Allah a zuciyarta da Jalal bemata komai ba

“Wannan ce kanwartaka?”

“Yeah ya kaganta so gentle and innocent”

“Good” 

shine abinda yafada kawai

Mikewa yayi tsaye zetafi

“Bros yazaka tafi muna magana”

“Inada abunyi ne”

Ya fice wato ma kanwar Jawwad ce tabdijan yanzu ta zagi banza kenan anya kuwa ze kyaleta ko dai yagaywa Jawwad yaja kunnen kanwarsa tafita a harkarsa, to meye amfanin hakan,

Tana ganin Jalal yafita ta koma gurin Jawwad tasameshi inda tabarshi be tashi ba, shiga tayi ta zauna tace 

“Yaya Jawwad magana nakeson muyi”

“Am all ears sisyna ina jinki fadi abinda kikeso” 

ta Dan gyara zamanta tana fuskantarsa Wanda bayan kujerar dayake ya kasance window ne

  Zancen zuci yacigaba gsky y zama dole ya dau mataki inma ya kyaleta taci bulus kenan yana cikin wannan tunaninne se jeje yafado masa bari ya kirashi yaji wani shawaran ze bashi ne, 

hannunsa ya zura a aljihu da niyyan ya dauka wayan se yaji babu yadan yi shiru seya tuna tana kan kujerar da ya zauna a dakin Jawwad

“Yaya Jawwad meye hadinka da mutumin nan ne?”

“Kina nufin Jalal?”

“Eh shi nake nufi”

“Abokina ne kuma Dan uwana”

“Ta Yaya yazama Dan uwanka Yaya Jawwad wannan ba aminin arziki bane halinku Sam ba daya bane kallafa sigari yake shamaka a daki da ganin idonsa kasan tarbiyya ba ta wadace shi ba, kalli askin kansa, daganin bakinsa wannan yana shaye²

Zamanka tare da shi mutane zasu zata halinku daya Sam bashi da tarbiyya” 

ta daga kanta wazata gani  kawai taga Jalal a tsaye a bakin window yana kallonta da jajayen idanuwansa

Wanda hakan ya tabbatar mata yaji abinda tace

Ras! Ras!! Ras!!! Gabanta yafadi

     cikin palourn ya shigo ya dauki wayarsa bece komai ba ya fice

   Jawwad be kawo komai a ransa ba Dan yasan halayen Jalal shiyasa bekawo yaji wani abuba kuma yabawa window baya Dan haka besan yazo wajen ba.

“Kinaji kanwata Jalal mutumin arziki ne ba yadda kike tunaniba inayimasa addu a in Allah ya yadda wataran zakiga ya dena ze wuce kaman ba ayiba kema kisashi cikin adduo’inki kidinga masa fatan shiriya”

“Yayana ka kula da kanka Dan Allah karka bari dabi’unsa su rinjayeka wataran Dan Allah”

“Karki damu kanwata ba abinda ze faru mun Dade tare da Jalal da zan zama irinsa da tuni na zama shima abinda kikaga yanayi kaddara ce babu abinda ze faru da yaddar Allah”

Download>>> Budurwar Mijina Complete Document

“To shikenan” ta fada tana mikewa 

“Karka manta da kiran Abba 

“to shikenan zanje insha Allah “

Jalal kam Shiru yayi yana tunanin wani mataki yakamata ya dauka akan yarinyar nan gata kanwar amininsa kanwarma kuma wadda yakeso ta yaze hukunta yarinyar nan ya bakanta mata  ba tare da Jawwad ya gane ba baya son batawa abokinsa rai Dan tabbas in yayi mata wani abun Jawwad bazeji dadi ba,

Ko in kira Jeje yabani shawara idan na kirashima mezemin? wata zuciyar taba shi amsa 

Mara tarbiyya!!! Wai nine bani da tarbiyya mtseeww yaja tsaki zakiga rashin tarbiyya ganin idonki.

(Kai JALAL bafa karya tayiba )

Jalila kuwa Cikin gida ta koma tunda ta shigo maama ta bita da wani irin kallo na zanyi maganinki ita kuwa Jalila bata san tanayi ba,

Gurin Abba nufa ta durkusa tace

“Abba nagaya masa yace yana zuwa”

“To shikenan diyata”

Wucewa tayi dakin su ta je ta tarar da Nana tana ninkin kaya taje ta zauna kusa da ita

“Nana kinsan me yafaru?”

Nana ta juyo ta bata dukkan attention dinta 

“A’a sekin fada”

“Ingaya miki Jalal nagani adakin Yaya Jawwad yana ta shan sigari”

“Hmmm to ai bakiga komai ba Dan dai sigari kawai karewa har giya yake sha masa a daki wataran in yaje yasha yana tambelansa Yaya Jawwad ne yake nemo shi a club yakawo shi dakinsa ya kwantar da shi har giyar ta sake shi

Ke baki San komai bane shiyasa nace miki rabashi da Jalal ba abune me sauki ba” Nana ta karashe zancen jikinta a sanyaye

“Tabdijan kice abun babba ne ai in gaya miki dana ganshi a dakin bayan ya fita nakoma gurin Yaya Jawwad nai masa magana akan ya rabu da Jalal bashi da tarbiyya Ashe yadawo  daukar wayarsa  yaji duk abinda nafada bakiga kallon da yayi min ba”

Dan zaro ido Nana tayi

“Are u serious”

“Wlh dagaske nake yaji me nace bakiga mugun kallon da ya dingamin ba”

“Tabdijan Jalila garin Yaya haka tafaru aikuwa kinci sa a Yaya Jawwad yana gurin da wallahi inaga seya kusa sumar dake”

“To dai Allah ya rufamin asiri 

Bari in Dan kwanta in huta”

“Sarkin bacci ko gajiya ba kyayi Allah ya kiyaye haduwarki dashi”

“Shi wa?”

“Kinfini Sani”

Murmushi kawai tayi ta hau gadon ta kwanta.

Nana kuma tacigaba da ninke kayanta, 

Befi 10 minutes da kwanciyar Jalila ba 

Ilham tayi sallama 

“Mutuniyar kinji gori kenan yau se gashi kinzo anya makuwa bawani abun yakawoki ba” Nana tafada cikeda zolaya 

“Hmmm ke dai bari Nana akwai magana ne,

sister dinki bacci takene?”

Download>>> Macijine Complete Document

“Eh bacci takeyi meyafaru”

Cike da damuwa ta kalli Nana 

“Nana Yaya Jalal ne”

“Wani abunne yasameshi?”

Nana ta tambaya

“Aa Nana kin San dai zancen, ta tsuniyar gizo bata wuce koki hankalin yaya Jalal Sam baya kaina wlh ko kallo ban isheshi ba komai nayi bana birgeshi ke mukwana gida daya mu tashi amma semu shafe kwanaki ko kallon inda nake beba

Abun yana damuna Nana ina matukar kaunarshi amma shiko a jikinsa ni ban San meyake damun saba kaman ba mutum ba” 

  Nana ta dan dafata da sigar rarrashi

“Ilham inso cutane hakuri maganine kicigaba da hakuri kina addu’a insha Allah komai zezo karshe”

“Nana in ba ya Jalal na aura ba bazan iya zaman aure ba, dashi nake so na rayu yazama uban yayana ,

nifa ko karatu bazan iya cigaba ba sonake munayin SSCE ya aureni narasa yadda zanyi gashi mummy ma ba jin maganarta yake ba itama tayi kokarinta amma yaki saurarona

Dama daddy ba a maganarsa don baze taba tursasa shi ba Ina cikin damuwa”

  Daga inda Jalila take kwance ta tashi zaune Dan taji hirar dasuke ba bacci take ba, dannan waya take,

“Aikuwa kina tattare da nasani a rayuwarki damuwa yanzu kikafara muddun kika zabi dan giya a matsayin uban yayanki karki biyewa son zuciya ki cutar da yayan dazaki Haifa a nan gaba auren Jalal babu abinda zaki kwasa bayan bacin rai da dunbin danasani”

Kallonta Ilham tayi tana nanata Kalmar Dan giya aranta lallai Jalila bata da mutunci a gabanta take kiran Jalal Dan giya banda shishshigi da munafurci wayasakota a ciki 

Lallai bata sanniba akan Yaya Jalal banki imbata da kowace ce ba 

Ta kalli Jalila rai a bace

“Kekuma wayasa dake a gabana kike cin zarafin Dan uwana kuma masoyina Dan giya wannan ba magana bace at least yana abokin yayanki ya cancan ci ki mutuntashi”

“Taya kike tunanin in girmama Wanda be girmama mahaifiyarsa ba, Sam Jalal ba abin girmamawa bane, kema zuciya yace take rudarki, kokuma akwai wani sirri a ranki da kike boyewa, Wanda bakowa yasani ba

in bahakaba babu macen dazatayi sha’awar rayuwar aure da Wanda bayajin maganar iyayensa inba kema irinsa bace fitinanniya””

Da sauri Ilham ta kalli Jalila,

Jalila ta Dan daga mata gira

“Nayi karyane”

Gaban Ilham ne yafadi akwai wani abu danake boyewa da bakowa yasani ba ya akai tasan hakan???

“Ba abin mamaki ko tuhuma  a maganata, shawarace kawai tun wuri kisake tunani kinemi hanya me bullewa wannan shshashan be cancanci zama miji ba balle uba in bahakaba seyasaki kukan da kekanki bazaki iya hana kanki ba” cewar Jalila

“Enough please meyasa baki da ta ido kinacin zarafin dan uwana kina kiransa da dan giya agabana!!” Ilham tafada cikin shouting

“Hold on madam ba ayimin shouting” Jalila ta katseta

“Haba mene haka kukeyine bafa yarane kuba wannan be kamata ba we are all sisters”

Tabe baki Jalila tayi tace

“Ilham nasan zakiji ba dadi amma gaskiya nagaya miki”

Bari inje waje in Baku guri ina bukatar recharge card zani insiyo ta dau hijabinta tasaka tafice

Gajiya yayi da kwanciya ga bacin rai yana fama a banza akan wannan shedaniyar yarinyar yafito kofar Gida da sigarinsa a hannu kaman kullum 

Download>>> Yaro Ne Complete Document

Bari yaje Jawwad yazo yarakashi su Dan zaga gari koze rage takaici ya sha sigari kusan kara 7 amma har yanzu ransa a bace yake 

Cikin gidansu Jawwad yakoma yanufi bangaren Jawwad wayarsa tafara ringing tsayawa yayi ya dakko wayar Cwt dad ne ke kiransa murmushi yadanyi yadaga wayar.

   Tazo fita taganshi tsaye bangaren Yaya Jawwad yana amsa waya yana murmushi

Kai amma wannan akwai nacin bala’i wai dama yana murmushi

Dogon tsaki taja Wanda yasashi waigowa 

” dubeshi dan Allah kalli askin kanka daganin wannan askin bana mutanene kirki bane kullum baki cikin fidda hayaki kaman salansan tifa ko gajiya bakayi, kuma kazo ka likewa Dan uwana mutumin kirki kana nema ka lalata shi,

Kai dashi akwai banbanci shi yana da tarbiyya yana girmama iyayensa sabanin kai kaga kunada banbanci!!!””.

(Turkashi kindebota da zafi Jalila mekuke tunani zefaru keep following aakwai cakwakiya fa!!!!!!!!!)

Haka ta tsaya daga inda take ta dinga caccaka masa maganganu son ranta maganganu masu ciwo ciki harda Kalmar dayafi tsana Mara tarbiyya sabida tasan baze iya cinmata ba

“Inda zuciya kadena shaye shaye kazama mutumin kirki kacigaba da abota da yayana in ba zuciya kuma kacigaba da zuwa kana like masa cingam ko kuma ince 

Salansa sarkin hayaki “”

Ta juya takoma cikin Gida abinta kaman batayi komai ba

Maama ta tarar a palour tana tsifa 

“Maama kawo in tayaki naga tsifar dayawa “

“To karbi kibiyar”

Hmm yarinyar nan akwai shiga rai ba ruwanta dukda tasan abinda ke tsakanina da mahaifiyarta amma ko a fuskarta ban taba ganiba,

inma dai salon wani makircinne duk zan iya daku d’a na ne dai ba a isa a hada min zuri a da wadda take da raunin nasaba ba, tayi wannan zancen a zuciyarta.

     Shikam tsayawa yai cak kaman an dasa shi, yama rasa wani mataki ze dauka, fasa zuwa gurin Jawwad yayi ya koma gida ya shige dakinsa, ya dinga tuttulawa cikinsa giya seda yayi mankas sannan ya zube a gurin yana bacci.

    “Nana gaskiya abinda Yar uwarki tamin ya mugun bata min rai, ya dace tafadamin haka agabana taci zarafin Dan uwana, wallahi taci albarkacinki dasena shukamata rashin mutunci wallahi”

Itakuma tsayawa zatayi tana kallonki ba bakisan wannan uwarkice a fitsara ba kina ganinta haka shi kansa uban gayyar ina tsoron randa ze danketa (Jalal)Nana tayi maganar a zuciyarta a fili kuma Se cewa tayi

“Nasani Ilham bata kyauta ba amma zanmata magana haka halinta yake bata boye abu a ranta komene ne zata fada a gabanka amma kiyi hakuri insha Allah hakan baze kuma faruwa ba”

“Kinga ni tafiya zanyi bansamu biyan bukatana sema karamin takaici da kukayi”

“Naface kiyi hakuri Dan Allah ki gaida mommy”

Banza tayi mata tai tafiyarta 

a palour taga Jalila nayiwa Maama tsifa harara ta wurgawa Jalila  amma me ita seta maida mata da murmushi

“Kigaida Gida sister Ilham agaida mummy da yayanmu” tafada dauke da murmushi a fuskarta

Maama CE 

“Ilham kicewa mummynku in ankawo lesunan tamin magana zan turosu su zaba”

“To zangaya mata” 

shine abinda ta iya fada saboda Jalila takawota iya wuya.

Tana zuwa Gida dakinta ta wuce ta nemi guri ta kwanta maganganu Jalila suka shiga dawo mata

{“Sedai in akwai wani sirri da kike

boyewa Wanda bakowa yasani ba”!!}

To ya akayi tasani, taga a iya tunaninta babu Wanda ta taba wannan zancen dashi balle ya gayawa Jalila 

To ya akayi tagane akwai wani abu a ranta haka taita tunane²

Har bacci yayi awon gaba da ita

   Se banyan  isha’i sannan giyar  da yasaha tasake shi ya farka daga nannauyan baccin da yayi, ji.yayi kansa yayi mugun nauyi kaman ba a jikinsa yake ba haka ya tashi yana rarraba hanya ya shiga toilet yayo wanka tare da alwala

Download>>> Bakar Inuwa Complete Document

Ya fito palour ya shimfida sallaya yayi azhar yayi la’asar ya dauke sallayar 

(Nikam nace magariba da ishan fa?)

Cikin gida ya shiga ya tarar mummy na waya, ya kai minti biyar yana jira amma wayar taki karewa har ya kosa yagaji da zama yafara tsaki 

“To Dan sarkin Mara kunya tsakin me kake” mummy tafada bayan ta kammala wayar

“Tun dazu na shigo kina kallo amma kin tsaya kina surutu a waya kin barni ina zaman jiranki kuma kinsam gurinki Nazo”

“Wayar da nake ne surutun JALAL?” 

Tafada tana kallonsa

“Munyi waya da megidan nan dazu yace in gaya miki  yana dawowa jibi” 

yafada a takaice batare daya bata amsan tambayrta ba, inba hakaba yanzu zata fara masa fada Takara masa wani takaicin, kuma shi a rayuwarsa ya tasani fada.

Ilham datake kitchen taga shigowarsa Dan haka ta aje abinda takeyi ta dakko juice da cup ta dorosu a tray ta fito palour tana yauki ta nufi India Jalal yake

Cikin iyayi tafara magana

“Yayana ga juice na kawo maka”

Bece komai ba sema Kafeta da yayi da ido ko kiftawa ba yayi 

Nan ta sha jinin jikinta saboda kallon da yakemata

“Mtsewwwww” yaja wani dogon tsaki ya mike ze bar palourn 

“Haba Jalal meyasa kake hakane? Ilham fa kanwarkace koba komai ai yakamata ka karba kasha” mummy tayi maganar adan hasale

Ko takansu be biba seda yaje bakin kofa ya tsaya batare da ya waiwayo ba

“Yace in gayamiki jirgin karfe hudu ze biyo” (yana nufin mahaifinsa)

Yayi gaba abinsa

“Na shiga uku mummy meyasa Yaya Jalal yakemin haka kwata² bana gabansa mommy kiyi wani abu Dan Allah wallahi ina son Yayana amma ni meyasa baya sona” 

Ilham takarasa maganar cikin sheshsheka kuka

Rungumota mommy tayi tana rarrashi

“kiyi hakuri Ilham ina iya kokarina ni kaina fama nake Jalal kinagani ina mahaifiyarshi amma ban isheshi komai ba 

Amma in dai ina raye Jalal bashi da wata matar inba keba insha Allah”

Aikuwa daga ranar da burina yacika kingama yawo mummy dan sekinyi kuka da hawayenki Dan ba lefi bane in anmaka abinda kayi tafada a ranta amma a zahiri kuma secewa tayi

“Allah yasa mummy kitemaka min burina yacika in mallakeshi Dan Allah wallahi in ba shiba bazan iya auren kowaba”

“Karki damu Ilham keda Jalal duk abu dayane a gurina insha Allah zanyi duk meyiwuwa inga kin auri Jalal”

“Nagode sosai mommyna inkikamin haka kingamamin komai”

     Wai ni Jalal  yarinyar nan take cewa innayi zuciya indena kula yayanta saboda muna da banbancin tarbiyya

Zanyi maganinta ai rana dubu ta barawo daya tak itace tame kaya zan kamata a hannu

Haka yayi ta wannan zancen zucin

Bayan kwana daya

Gidansu Jalal suka tashi da aikace² saboda shirin dawowar magidan,

 sedai aikin yayiwa mummyn da Ilham yawa saboda me aikinta ta tafi kauyensu za ai bikin yayarta ga Ilham da shegen son jiki.

Dan haka mummy ta Yanke shawarar kiran maama a waya tace Dan Allah tabata Aron su Jalila su tayata aikin dan yayi musu yawa,

  kimanin wata hudu kenan rabon mahaifin Jalal da Nigeria Dan haka dole ayi shiri na mussaman domin tarbarsa.

A waya ta kira maama ta sanarda ita Dan Allah inba abinda su Jalila suke ta turo su tayata aiki ayyukan dayawa

Itakuma tace zata turomatasu 

Dakinsu mama taje ta sanar dasu sakon mummyn Jalal 

Nanace tace 

“To maama zamuje insha Allah”

Itakuwa Jalila cikinta ne yayi wata kara me sauti kuuuuuuuu!!!

“Na shiga uku ni Jalila !!?

” me yafaru ne Jalila?” Nana ta fada tana kallon Jalila 

“Au tambayata ma kikeyi yanzu in Jalal ya ganni fa? Yanzu ni yazanyi”

“Tab yanzu meye abunyi ainamanta da kinmasa rashin M,

shiyasa nace miki ba ruwanki dashi Jalila yanzu ga irinta nan”

(Nikuwa nace hmm danma bakomai kikasani ba jiyama tamasa rashin kunya” Jalila sarkin rawar kai da shishshigi)

“Kinga ni ba wannan ba ko ince kawai bani da lafiya? Se in zamana base naje ba”

“Kai Jalila wannan ba shawara bace yanzu fa Maama ta shigo ta ganki ras dake sannan kice baki da lafiya wannan ba shawara bace Sam”

“To ya zanyi? Inkuma muka hadu fa ?” 

“Bazaku haduba insha Allah kitsaya a waje in leka in baya nan seki shigo”

“To amma nikam ina jin tsoro Nana”

“Ba abinda ze faru insha Allah, kwantar da hankalinki taso mu tafi”

A kofar Gida Jalila ta tsaya tana  waige² itakuma Nana ta shiga domin dubawa in Jalal yana nan minti uku Sega Nana ta fito ta kalli JALILA ta girgizamata kai

“Shigo baya nan”

“Kin tabbata”? 

“eh na tabbata banganshi a ciki ba,

Hmm waike dama kinsan kina jin tsoro amma kika tsokano shi”

“Ke ni matsa in wuce tun kafin ya dawo ya ganni anan” Jalila tafada a gaggauce

Tare suka shiga cikin gidan Jalila tana ta faman  rarraba ido 

 A palour suka ci karo da Ilham rike kwanuka zata shiga kitchen, bata kula suba tai shigewarta batace musu komaiba ta shige kitchen ta ajiye kwanukan sannan ta fito sewani shan kanshi take tana hura hanci

“Waike Ilham har yanzu abinda yafaru be wuceba a gurinki kike ta wani kallonmu kina hade rai 

Indai Jalila CE ita tamanta ma kunyi kiyi hakuri Dan Allah”

Jalila kuwa a ranta cewa tayi

Tab lallai aiki yaganki indai nice bana gani inyi shiru

“Hmm bakomai ya wuce kuzo mukarasa mummyn tana ciki”

Suka bita gaba daya wani part suka nufa Wanda tunda Jalila tazo a rufe take ganinsa tana kyautata zaton shine part din mahaifin Jalal

      Shigarsu yayi dai² da fitowar mummyn dauke da labulaye a hannunta, Nana daga inda suke ta Dan rusuna ta gaisheta ita Kuwa Jalila seda ta durkusa har kaasa, sannan ta gaisheta, fuskarta a sake ta amsamusu

Har cikin ranta taji inama Jalal din tane haka yake girmamata

Karasawa Jalila tayi gurin mummy ta karbi kayan hannunta 

“mummy kawo ina za akaisu?”

“Dama wasu za a canza wannan zan badasu wanki biyoni seki karbo wasu a canza tace to”

Juyowar nan dazatayi taganshi zaune akan kujera, alamu ya dade a gurin itace bata lura dashi ba

Nana kuwa tun shigowarsu taganshi a zaune amma ta lura JALILA ba ta Ganshi ba,

Be dago ya kalleta ba seda mummy tayi gaba tabiyo bayanta, sannan yayi mata kallon zamu gauraya dake

  Itakuwa kallon up and down tayi masa hada murguda baki tayi sauri tabi bayan mummy 

Akajima Jalila ta dawo da labulaye a hannunta suka fara gyaran part din yana zaune beje ko ina ba 

” mummy tace Nana da Ilham suzo su siyo abinda babu saboda girki tunda taga Jalila tafisu rashin son jiki”

“Mummy indai Jalilace intaga dama batajin aiki “

“Ainima naga alama Nana”

ILHAM da Nana suka tafi cefane yai saura Jalal, Mummy, se Jalila

Mummy ce take kokarin Jan wata durowa na litattafai amma takasa,

Jalila tazo ta tayata amma suka kasa,

Takaici ya ishi Jalila ganin ga JALAL a zaune amma yakasa temakawa tsaki taja

“Mtsewww mummy wannan Dan naki bashi da amfani Sam wallahi yana kallo muna fama amma ko a jikinsa”

“India JALAL ne kadan kika gani bari in dakko bagco a rage litattafan mugani ko zamu iya janye durowan”

Ita Jalila a hankali tayi maganar batai zaton yajiba,

Sedai kawai gani tai yana kallonta

Mummy na Barin dakin,

ya tashi ya tako har gabanta yana muzurai yana mata wani irin kallo, yana zuwa gabanta yatsaya yadan kura mata ido

Nan da nan jikinta ya dau rawa 

“Mara tarbiyya, Mara amfani, mutumin banza, mekama da yan daba, Dan shaye² Niko?” Yanuna kansa da yatsansa

“To bari ingaya miki wani abu ba tsoronki nakeji ba Dana kkyaleki ban  kakkaryaki ba,

bana son in batawa Dan uwana rai sedai kawai zan maidake Irina ne, shize tabbatar miki bani da tarbiyya kinga in mukazama mu biyu semunfi dadin kwatance

Sha³ Jahila kawai dakikiya na tsani ganin ko fuskarki”

Ya juya da nufin yafita yabar dakin

” duk jahilcina nasan girman iyayenaa kuma inazuwa makarantar islamiyya,

a islamiyyarmu ma nasan akwai ukuba game sabawa iyaye tundaga duniya, dukda Jahilcina bana zuwa mashaya ina girmama manyana, kaga sekanemi waye jahili”

Yana jinta kalamanta suna dukan zuciyarsa amma ya fice ya kyaleta da sannu ze maganinta.

      Haka sukayita aiki har yamma tayi suka shirya girke² suka gyara ko ina Wanda yakasance Jalila ce karfin aikin

      “Karfe hudu da rabi dai² Jawwad da Jalal sukaje airport suka dakko Alhaji Habib Kamal,

mahaifin Jalal ya karaso gidansa cike da farincikin ganin tilon dansa cikin koshin lafiya, dukda yawan korafin da mahaifiyar D`an nasa kanyi masa game da miyagun halayen yaron nasu.

  Gaba daya sukashiga cikin gidan kowa se fara a yakeyi ana mass sannu dazuwa

Daka ganinshi kasan mahaifin Jalal ne saboda  tsabar kamar dasukeyi,

kaman yadda yake dabi’ar  Jalila, har kasa ta durkusa ta gaisheshi,

Da sakin fuska ya amsa mata tareda cewa

” wannan fa?”

“Ai Yar wajen marigayi ce kanin babansu Jawwad” mummy tabashi amsa

“Allah sarki, Ashe takwarar Jalalce ta girma haka, tubarkallah 

gata nutsatsiya

Allah yaraya ma naku gaba daya”

Suka amsa da “Ameen” gaba daya

Banda Jalal dayake ta cin magani a ransa yace “wai wannance nutsatsiya munafuka Mara kunya yarinya”

Watsewa suka farayi a hankali domin Barin daddy ya huta 

Ilham ta tafi dakinta tashiga wanka saboda tagaji,

Jawwad yakoma Gida

Shikuma Jalal yatafi part dinsa

Jalila da Nana Suma suka nufi hanyar Gida har sun fito Jalila ta tuna wayarta tana gidansu Jalal inda ta kwaso labulaye daga Shanta

“Au Nana wayata rakani in dakko please”

“Gaskiya nagaji bazan koma b”

“Dan Allah ki rakani, inkuma Jalal yakamani fa?”

“A gabanki fa Yakoma part dinsa baya cikin gidan inajiranki anan jeki dakko”

“To bari inje”

Tashiga ba kowa a palourn Dan haka da sauri tashiga ta dakko wayar,

 tana zuwa corridor din daze sadata da waje taganshi a tsaye yabawa inda take baya yana waya na Shiga uku inya kamani na shiga uku, wata dabara ta fado mata

Ta tako da gudu zata wuce tabayansa caraf ya riketa

“Haba karamar Mara kunya kinzaci bansan da shigarki bane yau babu me kwatarki zanga karyar rashin kunya”,

” meye haka dalla malam cikani”

Tafada tana kiciniyar kwace kanta

“Ooh har kin manta da maganar mune

Zan maidake Irina ne kawai in samu abokiyar shaye²”

“Dalla ka cikani ni ba Yar iska bace “

“Nima ba Dan iska bane kawai Mara tarbiyane, kema kuma hka nakeso kizama,

yanzu sigari kawai zaki sha kema kizama salansa kaman ni kullum bakinki cikin hayaki”

Wani mugun kallo tayi masa

“Allah ya kiyaye in zama irinka kai halinka har wani abun sone  mara………..

Bata karasaba yasaka sigarinsa a baki ya zuka hayakin a bakinsa

Ya rikota yasa hannunsa daya ya toshe mata hanci, yasa bakinsa a nata ya dure mata hayakin nan tas a bakinta,

aikuwa take numfashinta ya sarke,

Yakuma zuka ya dura mata sau uku

Sannan yasaketa ta zube tana wani irin tari tana Jan numfashi da kyar, idanun ta sukayi jawur, numfashinta yana sama yana kasa kaman me asthma.

“Gobe ma in kikaga Jalal kikuma zaginsa useless creature kawai”

Yayi tafiyarsa ya barta a gurin tana ta mimmikewa tana fama da numfashi ta galabaita har a tafara fita hayyacinta.

  Mummy ce tafito daga sashen daddy zata shiga kitchen ta dinga jin kakari da nishi, dawowa tayi da baya a Dan tsorace, tana duba meke wannan nishin,

Jalila tagani a zube a gurin tafita hayyacinta numfashinta nata fita da sauri

(Lallai JALILA ta sha hayaki)

” subhanallah ke Jalila meyafaru meke damunki??”

Tazo tana taba ta 

“Ohh ni khadija meke damun ta kodama tanada athma ne

” Ilham!,  Ilham!!,  Ilham!!!,”

Tashiga kwala mata kira

“Ke Ilham kifito da sauri”

    Itakam Nana gajiya tayi da jiran Jalila Dan haka kawai tayi tafiyarta ta shige Gida,kai tsaye taje dakin mummy

“Mummy mun dawo “

“To sannunku ina Jalilan?”

“Wayarta ta manta ta koma dakkowa shine na taho”

Kai inkuma Yaya Jalal ne yamata wani abunfa tai wannan tunanin a ranta

da sauri tafito ta nufi gidansu Jalal

   Shikuwa Jalal gurin Jawwad yatafi abunsa, kaman be aikata komai ba hankalinsa kwance

Amma lokaci2 in ya tuna maganganun Jalila se ransa yabaci .

Da gudu Ilham tafito

“Mummy lafiya kuwa?

” zo kiga Ilham dama tanada asthma ne ko wani cutan?”

Ilham ta Dan zaro ido 

“Mummy ya za ayi in Sani”?

” maza jeki gidansu kifada suzo akaita Asibiti kar ta mace min a Gida”

“To bari in je”

Mayafi Ilaham ta dauka ta fito da sauri a bakin gate taci karo da Nana

” yawwa Nana Jalila dama tanada asthma ne kowani cutan?”

A firgice Nana ta kalleta

“Asthma kuma? Bata da wani asthma, me yasameta?”

“Zo muje kyagani”

Ilham tafada tana janyo hannunta zuwa cikin gidan 

“Subhanallah Jalila meya sameki?”

Nana tafada tana jijjiga Jalila amma Jalila bata San me akeba tafita hayyacinta

Da gudu Nana ta tafi gida domin sanar dasu abinda yake faruwa,

tana shiga gida a harabar gidan ta ci karo da su Jawwad

“Ke Nana lafiyarki kike gudu haka? sekace wata karamar yarinya mene haka”

Jawwad ne yayi maganar a Dan fusace

“Yaya Jalila CE”

“Me yafaru da ita?”

Yafada hankalinsa a tashe

Nima bansaniba  yaya tana gidansu Yaya Jalal yanzu muke tare da ita takoma dakko wayarta yanzu kuma  ta suma bata iya numfashi sosai

“Suma kuma”

  Ai bejira tagama bayanin ba yayi hanyar waje da sauri

Wani Dan guntun murmushi Jalal yayi sannan yabi bayan Jawwad

  Itama Ilham ta karasa cikin Gida dan ta sanar da maama abinda yake faruwa 

Suna zuwa suka tarar da Jalila kwance akan cinyar mummy bata numfashi, se kadan²

“Subhanallah Jalal bani key din motarka mu kaita Asibiti” Jawwad yafada da sauri

  Key din ya danka masa

memakon ya raka Jawwad sema ta shi da yayi yai ficewarsa

Jawwad beyi wata² ba ya dauki Jalila yayi waje da ita yasaka ta a mota ya tada motar kenan 

Nana ta shigo  gidan ya tsaya ta Shiga motar 

“Yaya maama tace muyi gaba zata taho in Abba ya dawo”

Be amsa mata ba yaja motar

“Ilham ki bisu mana kirakasu ko Asibitinne kinga ni badamar in fita yau babanku ya dawo” maama tayi maganar tana duban Ilham

“Ba inda zani wallahi Allah ya bata lafiya in nabisu ai bani zan bata lafiya ba”

“Haba Ilham amma ai a gidanmu abun yasameta”

“Ni wallahi mummy a gajiye nake ba inda zan iya zuwa yadda nagajin nan  hutawa nake sonyi”

Ta wuce daki abunta 

“Ohh ni hadiza yaran nan se a hankali kowanne da halinsa  

    Suna zuwa Asibitin aka karbesu aka shiga da Jalila emergency don ceto rayuwarta 

  Wajen karfe Tara na dare Maama sukazo asibitin ita da Abba 

Wanda yai dai²Da fito da Jalila daga emergency aka basu daki 

Alhamdilillah numfashinta ya dawo dai² se dai tanata bacci ga drip da aka saka mata 

” Allah sarki diyata Allah yabaki lafiya, Amma nayi mamaki iya sanina bata da wani ciwo makamancin haka”

Abba yafada cike da damuwa yana kallon maama

Dan tabe baki maama tayi

“A’a to ai ba dolene kasaniba watakila tana dashi mune bamu saniba kasan uwatta bakomai zata gaya mana ba tunda….”

“Ya isa haka Zainab..” Abba ya katse maama

“Yanzu lafiyarta muke fata ba wani surutu ba”

Likitan ne ya shigo domin kara dubata

Jawwad ne yayi gyaran murya

“doctor meyake damunta ne?”

“Eh blockage ne akasamu a airways dinta maybe ta kwarene ko kuma ta shide da wani abun,

Zatasamu lafiya insha Allah munyi mata allurai zatayi bacci karku damu Allah yabata lafiya” suka amsa da Ameen

Guraren sha daya na dare 

Abba da Jawwad suka tafi Gida akabar Nana da da maama suka kwana a gurin Jalila

   Washe gari da sassafe Jawwad ya tashi ya shirya da nufin ya koma Asibiti, dayake motar Jalal a hannunsa ta kwana kafin ya wuce ya maida motar gidansu Jalal,

Jawwad ya tsaya  suka gaisa dame Gadi yayai masa yame jiki dayake yasan meyafaru,

ya” amsa da sauki,”

Jawwad ya juya zefita se yadawo da baya ya kalli me gadin 

“Jalal yana nan ne”

“Eh yana nan yana bangarensa”

“Nagode”

Jawwad ya juya ya nufi part din Jalal Lamar kullum ya na kwance yayi dai² yana bacci babu alamar yayi salla 

Jawwad ya daddaki pillown da Jalal yake kwance 

A hankali Jalal ya bude ido 

“Tashi kayi sallah Dan nasan bakayi ba”

Seda yadan ja seconds sannan ya tashi zaune yana hamma bece masa komai ba ya mike yaje

Yai alwala yagabatar da sallar asuba karfe 7:30am 

“Jalal fushi nake da kai”

Jawwad yafada tare da Dan hade rai

Jalal ya kalleshi 

“Why”

“Kanwata ba lafiya rai a hannun Allah amma ko ka tambayeni ya jikinta talk less of kace zaka min kara ka dubota to ni na roki arziki ka rakani Asibiti”

Dabeyi niyyar zuwa ba amma yaga in yai haka be kyautawa amininsa ba wato Jawwad Dan haka yace 

“Sorry bross karkayi fushi dani bari in shirya muje”

“Seda na roka?” Jawwad yafada yana Dan hada rai

Murmushi Jalal yayi “to koma mene ai nace zani in kuma bakasone in koma baccina”

“Kai ka isa ni yi Sauri karmu makara ni sonake tana farkawa tafara tozali da fuskata”

Girgiza kai kawai Jalal yai a ransa yace ka dorawa kanka wahala saboda wannan banzar yarinyar Mara kunya

   Kafin Jalal yagama shiryawa Jawwad yakira maama

A waya bugu seda ta kusa tsinkewa sannan ta daga 

” salami alaikum maama barka da safiya “

“Yawwa barka ya daddynaka”?

“Muna lafiya dama tahowa zanyi nace ko kuna bukatar wani abun?

” a’a bama bukatar komai ka hanzarta dai inaso indawo Gida in huta nibana son zaman Asibiti “

“To maama yanzu zan iso insha Allah, nace ya kuwa Jalilan ta farka ne”

“Ban saniba in kazo kaganewa idonka kaita wani rawar kai akan yarinyar nan ka kiyayeni wallahi”

Ta kashe wayarta 

Shidai a iya tunaninsa beyi wani abu dabe daceba amma meyasa maama ta dau zafi haka yayi ta zancen zuci har Jalal yagama shiryawa suka tafi 

Sun isa asibitin dukda Jalal ya Dan bata musu lokaci 

room din da aka kai Jalila suka nufa

Jawwad ne ya bude kofan tare da sallama

Maama ce ta amsa dayi musu sannu da zuwa,

yawwa tunda kunzo bari mu je Gida dama ruwa zasu karasa mata da allurai kawai su sallameta,

Ninazata tun dazu zakazo Abbanku yazo ya dubata yanzu ya tafi.

shikam gogan kujera ya janyo ya zauna abinsai be kula kowa ba

Alhamdilillah jikin Jalila yayi kyau sun sameta tana rama sallolin dabatayiba

“In ta idar Jawwad ka kira nurse din suzo su karasa mata abinda zasuyi mata seku taho Gida” Maama tafada tana shirin tafiya

Sukagama abinda zasuyi maama da Nana suka tafi Gida.

“Yaya ina kwana”

Jalila ta gaisheshi

“Lafiya qalau ya jikinnaki?”

Jawwad yafada cike da kulawa

da sauki Yaya

“Waime yafaru dakene? Ya akai haka tafaru”?

seda ta kalli inda Jalal yake suka hada ido, tai sauri ta dauke kanta 

Ta maida kallonta ga Jawwad

“Kwarewa nayi” tafada a takaice 

“Kwarewa kawai numfashi ya dauke ko kinada asthma ne?”

“A’a Yaya banida asthma”

Duk abun nan Jalal danne² wayarsa kawai yake, ba Wanda ya kula a cikinsu 

“To tunda kin idar bari inje inkira nurse suzo su miki alluran dafatan kinci abincin?”

“Eh naci abinci, amma ban idar da sallah ba zanyi walhane”

“Kai sisyna bakida lafiya fa ai Allah yaga zuciyarki”

Jawwad ya danyi maganar a shagwabe

Jalal ji yayi kaman ya shake Jawwad yaga yanata wani lallabata hada yiwa mace shagwaba saboda shirme

(Niko nace a ganinka ba)

Itama a shagwaben tafada maganar

“Nifa zan iya Yayana kasan sallah haske ce me girrma kuma tana hana mutum aikata wasu laifukan,

Yayana abune mawuyaci kaga Wanda ya tsaida sallah yana aikata wasu miyagun laifuka da baya kunyar yinsu agaban mutane,

Koda ze aikata yana kunyar mutane suganshi

Kaga inka tsaida salloli biyar seka kara da nafila bakasan abinda Allah ze duba a ayyukanka ba yai maka rahama”

“Nice one sisyna proud of you

Allah yasa iliminki ya amfaneki ya amfani al Umma” 

Jawwad tafada yana murmushi

“Proud of u too bros”

Jalal yasan da biyu tayi wannan maganar amma yai kaman besan me sukeba 

Seda ta idar da sallah takoma kan gadon sannan 

Jawwad ya kalli Jalal 

“yace brother zomuje induba nurse din suzo susa mata ayi ai sallamemu”

“Jeka dawo ina nan” abinda Jalal yace kenan

“OK to bari inje”

Gaban Jalila ne yafadi ta kalli Jalal idonsa yana kan wayarsa ba ita yake kallo ba 

To in yayi min wani abun fa

Jawwad nafita Jalal ya kalleta

Kina tsoron in kumayi miki wani abun ne?”ya mike daga inda yake yadawo kujerar gaban gadonta 

“Meyasa baki gaya musu gaskiya cewa taba kika shaba,

rashin sabone kawai, in bahakaba daga shan sigari seki suma kikusa shekawa lahira?”

yafada yana murmushin mugunta

Banza taymasa taki kallon sa

“Yanzu sauranki giya da kwayoyi tunda ina sha kema sekin sha,

Kwanan nan kema zaki fara zuwa mashaya”

Yafada yana hade rai

“Allah ya kiyaye ya tsareni, dazama irinka bazan taba zama irinka ba Mara tarbiyya…

” ohoh wait ashefa Ke kin tsaida sallolinki biyar a rana hada nafila nikuma banayi shiyasa Ke ba irirna bace,”

Nima bani na saiwa kaina ba amma zanyi meyuwuwa inga kinzama Irina tunda jiya kinfara ki rubuta ki aje sauraanki giya da kwayoyi zaki zamaa abar kwatance kaman ABDULJALAL sha³ jahila, I hate u”

“God forbid, over my death body kwatance in dai bana Alkhairiba indai irinnaka ne Allah ya kiyaye kuma niba Jahila bace wallahi”

Hannu yasaka a aljihunsa ya dakko taba da lighter

“naga kaman ta jiya bata isheki ba sokike in kara miki wata”

girgiza kai tashigayi tana zare ido

“Mara kunyar karya kawai” 

Yafada tare da maidasu aljihunsa

Ya mike ze koma kujerar da ya taso kawai yaji muryarta tana fading

“Kuma wallahi Allah ya isa abinda kamin jiya kodayake bakasan ma’anarta ba kona maka bazaka damu ba amma ban yafe wallahi azzalumi kawai me kama da yan daba”

Ohh God yarinyar nan ba zata canza ba,

Dawowa yayi inda take har gaban gadonta yasa yatsunsa biyu a side din kumatunta ya matsa da karfi

Wani uban ihu tasaka saboda zafi jitayi kaman ze Huda mata kumatu da yatsunsa nan da nan hawaye ya shigo zubowa daga idonta wani nabin wani sedayaga fuskarta tayi jawur hawaye na ambaliya a fuskarta

Sannan ya cikata Yakoma inda yake zaune da farko yana danna waya

Jawwad ne yayi sallama tare da nurse

Kallonta  Jawwad yayi 

“lafiya kuwa sisy kukan me kikeyi?”

Seda ta kalli inda Jalal yake amma ba ita yake kallo ba

“Ni Kaduna zankoma gurin Ummi'”

Tai maganar tanakuma fashewa da kuka

Se da Jalal yayi murmushi mugunta

“Haba Jalila dama hayanzu kina wannan rikicin naki kiyi hakuri in muka koma Gida mayi wannan maganar”

Kai kawai ta gyada masa

Nurse din takarasa mata abinda yakamata aka sallemesu.

Har suka Shiga mota suka kama hanyar Gida kuka takeyi shikuma

Jawwad se aikin rarrashi yake

Shikam Jalal Jawwad yafi bashi haushi se wani lallabata yake

Itakuwa ita kadai tasan zugin da fuskarta takeyi ga kirjinta hayanzu ba dadi saboda wahalar yin numfashi da tayi

(Nikam nace in rashin kunya abinyine gobe maki kara)

Maama da Nana suka iso Gida Nana wanka tayi ta kwanta saboda batasamu tayi bacci sosai ba Daren jiya

Maama kam datayi wanka seta shiga kitchen da niyyar Dora sanwar rana

Sallama taji a parlour Dan haka ta aje abinda take ta domin ganin me sallamar 

Wata matace mekama da maama sekuma wata budurwa da batafi sa’ar su Nana ba

“Yaya mairo sannu da zuwa yanzu kuke Tafe da ranar nan”

Wadda takira da Yaya mairo tace 

“eh mune ai munzo tunsafe bakowa a gidan narasa INA kuka tafi da safe haka gashi ni ba waya a hannuna tasamu matsala,

Kukuma makota kowa gate a rufe sekace marasa gaskiya”

“Wallahi kinga Jalila ce tazo mana hutu se kuma ta yanke jiki tafadi jiya,

A Asibiti muka kwana sedazu muka dawo, mun baro za a sallamata Jawwad ze taho da ita”

Wani mugun kallo Yaya mairo tayi mata

Sun iso gida lafiya sukayi parking

Jalila fuska duk hawaye amma se cewa tayi “Yaya JAWWAD an kira azahar ka tsaya a masallaci kai salla 

Kasan sallar jam’i tafi lada akan sallar mutum daya kodayake garama Wanda yakeyi shika dai wanima bayayi”

Jawwad ne ya kalleta da mamaki  da nufin yayi magana

Ta bude kofa tafice da Sauri

Shiko Jalal yasan dashi take sarai haka halinta yake bazata canza ba  amma seyayi kaman beji me tace ba shi dariya ma taso bashi ganin fuskarta duk hawaye amma Neman magana take

Ta nufi cikin gida abinta har yanzu jikinta babu kwari sosai, tana shiga ta nufi dakin maama domin ta Sanar da ita ta dawo an sallameta 

takama handle din kofar da nufin ta shiga

amma maganganun datajine  

Suka Sa ta daskare a tsaye zuciyarta ta fara bugawa da karfi

“Gaskiya zainabu baki da hankali yanzu har asibiti kikaje jiyyarta kika barota da danki, dangin arna ababen kyama kika bari tana mu’amala da yayanki hartazo miki Gida Hutu koda take musulma ai daga tsatson arna tafito!!!”””

Tirkashi wasa farin girki

Domin Sauke Cikakken Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Please share

More comments more typing……

Back to top button