Fentin Zina Page 27 Hausa Novel
****** Gyara zama Abdul yayi yace wadannan ‘yan matan guda biyu da auka fita tareda nurses dinnan mai sanye da hijab ruwan kasa itace wacce na gani kuma nan take naji zuciyata ta aminta da ita domin soyayyace da kallon farko.Mr.man kai daga ganin sarkin pawa sai miya tayi zaki?. Mutumin bari kawai wallahi kallo daya na mata sai naji kamar domin ni aka halicce ta kuma ta yiwu matar da na jima ina nema ne ta iso gare ni.Hakane kana da gaskiya lamarin Allah babu ta yadda bata kasancewa amma fa a yadda na sanka wannan yarinyar da kake gani bazata yi daidai da tsarin ka ba.Meyasa ka fadi haka aboki?.Sauke numfashi Anas yayi kana ya cigaba, kana ji tun kamin ka kai ga fadawa ciki gara in fada maka wannan domin tana da yaro na miji wanda kaga sun fita rike dashi danta ne, kuma kaga kai mutumne da nasan yana da matukar kishi da wuya ka iya auren yarinyar da wani ya rigaka saninta mace wannan shine dalilin da kaji nace batayi daidai da tsarin rayuwar ka ba.Ya girgiza kai ya saki guntun murmushi yace Anas kenan! Bansan meyasa ba amma naji koma menene inason ta kuma da gaske aurenta zanyi, ina fatan zaka taimaka mun wajen sanin gidansu domin in isar da sako na tun da zafin sa.Da mamaki Anas ke kallon abokin nasa domin yafi kowa sanin waye Abdul da kuma akidarsa ta son auren budurwa gal a leda kamar yadda yake yawan fada a cewar shi mace indai wani ya rigashi saninta toh gareshi ta zama panko, amma yau wai shine mai cewa eh yaji ya gani yana son bazawara mai da. Abun da mamaki.mikewa Anas yayi yace sorry friend zanje in duba jikin yaronku kada suji shirun yayi yawa suji babu dadi.Shima mikewa yayi yace well muje tare mana sai in fara kafa gwamnatina tun yanzu.Tare Suka fita suka nufi dakin daya umurta a ajiyesu ya tura kofar ya shiga Abdul na bayan shi.Kuyi hakuri fa nayi bako ne shiyasa baku samu attention dina da wuri ba ya jikin yaron?. Fateema ce ta Amsa da cewar Alhamdulillah kaga ma bacci yake yi kuma jikin ya rage zafi sosai.Ok masha Allah! Malama Ameena lafiya dai ko? Naga kinyi shiru kamar bakya dakin duk da daman ke ba mai yawan surutu bace.Daidai sadda dada da mama rabi suka turo kofar suka shigo don dama fateema ta fada musu an basu gado ta kuma kwatanta musu inda suke.Dan dukawa Dr. Anas yayi yana gaida dada da mama rabi, suka amsa cikin fara’a, ya faki idonsu ya aikawa Abdul sako wanda nan take ya amshe shima ya gaishesu cike da girmamawa, suka amsa ya ciro wasu ‘yan kudi ya ajiye a gefen shureim yana fadin ga wannan babu yawa a siyawa yaro biscuits.Dada ta kama haba tana cewa kai kuma harda wani wahala haka? Toh an gode Allah ya saka da alkhairi.Kallon fateema Abdul yayi yace kanwata indan ganki a wake mana, daga haka yawa su dada sallama ya fita Anas ya bishi a baya.Fateema ta juya tana kallon mama rabi don neman izini sai tace kada ki wuce miti biyu kuma kada kiyi nisa da kofa.A dan gaba kadan da kofar ta ganshi tsaye ya harde hannayenshi a kirji ta karaso da sallama.Yauwa sannu har nayi shirin tafiya naga kamar bazaki fito ba.Ba haka bane.Toh shikenan! By the way naga ‘yar uwar ki kuma ina sonta, ni ban iya nuku nuku ba shiyasa ma na bukaci in ganki ki fara yimun jagora kafin na isa gareta, ina fatan ba wanda ya rigani.Duniyar tunani fateema ta fada tana tuna yadda samari suke kawo kansu gurin addanta tana korar su a cewarta ita da aure har abada ko jiyan nan ma saida ta kori wani yau kuma ga wani ya biyo ta hannun ta, yaya kenan zata yi.Saida ya tafa mata hannu a kusa da kunne kafin ta dawo hayyacinta tana inda inda tace eh..unn… Toh…..Ban gane ba kodai kina ganin ban dace da yayar ki bane.Girgiza kai tayi tace ba haka bane ko kadan, akwai dai wani abu ne wanda a yanzu addata bata taba aminta da kowa da nufin soyayya shiyasa ma kaga na rasa me zance amma ka gwada sa’ar ka mai yiwuwa sai kaga ka dace.Amma abu daya ya daure mun kai ko zan iya tambayar ki?.Kayi hakuri kada ka tambayeni domin bani da hurumin baka amsa.Shikenan am please samun number dinki anan.Ta karbi wayar tasa masa lambar ta mika masa ta masa sallama ta shige ciki.*****–Abdul gadan gadan ya ballo da maganar aure inda ya shiga neman auren Ameena, tun tana koranshi yana dawowa har dai su dada suka zaunar da ita suka fahimtar da ita dole ta amince ba don ranta na so ba saida ana saura wata biyu bikinsu ta sanar dashi komai gameda rayuwarta, hakika ya kadu kuma yaji kamar ya fasa auren nata saidai kuma yana sonta haka ya nuna mata ai babu komai kaddara babu ta yadda baya zuwarwa mutum.Taji dadin yadda ya dau kaddara ta dauka idan ta fada mishi zaice ya fasa auren ne sai taga sabanin haka daga lokacinne kuma ta dauki matsayi na musamman ta bashi a zuciyarta.Har i zuwa wannan lokacin kuma inna bawai ta sake bane, don lokaci zuwa lokaci inta dauro mata haka zatayi kiran Ameena a waya taci mutumcinta sosai ta kashe waya, tun Ameena na kukan abun har ya zama indai inna ta kirata zata amsa kiran ta gaisheta sai ta ajiye wayar a gefe tayi ta gama sababinta ta kashe, shiyasa ma Ameenar ta kosa tayi aure ko zata daidaita da mahaifiyarta.Sai bayan anyi biki da sati daya iyayen Abdul suka ji labarin cewar ai matar da Abdul din ya aura ba bazawara bace kamar yadda shi abdul din ya fada, ashe a yawon barikinta ne ta samo yaronta a yadda wasu suka juya labarin, ai kuwa mamar shi ta dau zafi da yawa daga ranar ta tsani Ameena.A gurin Abdul kuma sai yakejin gurbin wani abu tun ranar daya kusanceta wani bakin ciki ya ziyarci zuciyar shi take tsanar shureim da mahaifinshi suka dirar mai a zuciya sam ya fara canjawa yaron sai ya zamana idan yana falo yaron baya fitowa kuma shi ya sanyata taho dashi domin da a gurin mama rabi taso barin shi.Zuwa yanzu inna ta saduda ta fawwalawa Allah domin koda yaya abubakar ya dawo daga karatunsa daya kammala ya samu labarin komai don dama baba malam ne ya hana a fada masa, ya sasanta inna da ‘ya’yanta ya kuma kara jan kunnen Ameena sosai da kada ta sake aikata wannan rashin hankalin, toh daga nan ne inna tayi hakuri sai dai idan aka fama mikin saidai suyi hakuri amma yanzu sun koma kusan kamar da amma Ameena wata iriyar kunyar inna take ji sosai har bata hada ido da ita.Inna tana son shureim sosai wanda hakan saita kara girmama lamarin ubangiji domin idan ra’ayinta ne bazata kalli yaron bama amma ga yadda Allah ya casa Mata kaunar yaron a zuciyarta har mamaki take yi.A hankali rayuwa ta soma tafiya, Abdul ya kulla soyayya da seceteriyarsa wanda suna dan tabe tabe, tande tande, amma basu taba aikata zina ba domin yana matukar kyamar hakan.Bayan sunyi shekara da aure matsaltsalu suka fara bijirowa, Abdul fitinanne ne na masifa ga saurin fushi da rashin bincike, sanna mafi munin abun yana da zargi abu kadan zai faru sai ya rika jifanta da miyagun kalamai yana amfani da past din rayuwarta yana zubo mata har i zuwa yanzu da take zaman hakuri dashi din baya ya kara auren shi.WANNAN KENAN!!!*****–CIGABAN LABARI…..Ajiyar zuciya ta shiga jerowa bayan ta tunano rayuwarta ta baya, tana jin cewar zata iya barin ma Abdul gidan shi ba wani abu bane domin son da take masa a halin yanzu babu hakuri kawai take yi toh na meye zai rika neman wulakantata akan abunda ba ita ta kaddarawa kanta ba.Da haka barci ya dauke ta da kudururruka a ranta sosai.Washe gari ma data tashi kota kansu bata biba ta samawa kanta saukakakken abu ta ci ta koma daki ta dau wayarta ta ci gaba da latsawa don ta kudiri aniyyar koyawa Abdul hankali gara yasan fa ita ba baiwarsa bace.Maryam ce ta nufo dining ta tarar babu komai na nau’in abinci sai tahau kwallawa Abdul kira tana cewa ka fito da sauri ka kalli wani abu.Ai kuwa da saurin shi ya fito sanye da jallabiyya yana fadin menene baby?.Kaga fa inajin yunwa amma har yanzu ace ba’a kammala abinci ba a gidannan fisabilillahi ko so ake ace dagazuwana har na soma aiki ina amarya guda? Dan Allah kayi wani abu.Baice komaiba ya juya ya nufi dakin Ameena cikin sa’a ya samu ta manta bata rufe ba data shigo.Tsayuwa yayi ya rike kugu yana dubanta irin kallon rainin nan.Plate din jellof din taliya ce da irish potato ga lipton a gefe guda turirin shi sai tashi yake.Bata ma san ya shigo ba hankalinta naga cin abinci da kuma wayarta da take dannawa ta shiga Facebook group din “SIRRIN ‘YA MACE” na maijidda bello da jiddatulkhairi tijjani. Tayi nisa a karatunta wanda uwargida ke neman shawarar yadda zata karkato da hankalin mijinta gare ta bayan sun hade mata kai da amaryar sa.Wani razanannen tsawa ya buga mata da ambaton sunanta cikin kakkausan murya wanda saura kadan ta kone da shayin lipton dake gefenta tsabar yadda tatsorata.Ya tako har inda take zaune ganin haka yasa ta mike tsaye tana jada baya.Baiyi wata wata ba ya sauke mata maruka guda biyu kana ya nunata da yatsa cikin kumfan baki yace.Nan gida nane bana ubanki ba kuma ke baki isa insa doka ki take taba wawuya dake mara hankali wacce bata san darajar mijinta ba, dama me nake tsammani daga auren ballagazar ma……..Kasa karasawa yayi sakamakon marin daya ji ya sauka a kumatun shi, kafin ya farfado ta kara masa a dayan bangaren ta nuna shi da yatsa cikin huci da tsananin bacin rai………… *EESHERT ADAMU* *MATAR MAJEEDADI* ✍️



