Uncategorized

Wace Ce Ita Chapter 39 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

   THIRTY-NINE📍

          A hankali ta bude gate din ta fita, da sauri tayi gefe jin kamar motsi daga cikin gidan, saida taji shiru baa tawo ba sannan ta fara tafiya, tana tafe tana dialing number khaleel a wayar Umm data fito dashi, ringing wayar ta dingayi baa daga ba, bata hakura ba ta cigaba da dialing number, tana cikin wannan hali taji takun takalmi a bayanta, kirjin tane ya bada sautin rass, ko baa fadamata ba tasan waye balle ba wani nisa da gidan tayi ba, wata zuciyar ce tace ta zura a guje kawai, zatasa gudu kenan taji an kamo tsintsiyar hannunta, kin juyo tayi dan tasan bazasu kwashe ta dadi ba……..

      “Wifey ina kuma zaki?”…..

Da sauri ta juyo jin muryar wanda batayi expecting ba……..

  “Why’re are you not picking your calls khaleel?”…

Ta fada tana janye hannunta at the same time tana sauke ajiyar zuciya me karfi…..

    “I’m not with my phone”…..

    “Ok, muyi sauri mubar street dinnan, ze iya fitowa anytime”……

      “My car is close by, muje”…..

Basuyi tafiyar 10 inches ba suka isa inda khaleel yayi parking dan nesa da gidan, shiga motar sukayi yaja suka fara tafiya in silence…….

Wani ajiyar zuciya fatima zainab ta sauke ganin dagaske sun bar unguwar, sai a lokacin ta samu nitsuwa taji hankalinta ya kwanta, ta kuma kudirta a ranta bazasu kara haduwa ba har abada ita da Deen….

KARANTA>> Cututtukan Dake Hana Mace Jin Dadin Jima’i

Duk uban gudun da Deen yake khaleel be hakura ba haka yayita binsu shima ana kauce masa har yaga gidan da Deen yashiga, suna shigewa shima yayi yunkurin shiga saidai kememe securities din gidan suka hanasa dan baa san da zuwansa ba, sukace in ya matsu ya kira wani a gidan shikuma bashi da wanda ze kira, haka ya dawo yayi parking dan nesa da gidan ya cigaba da zama a cikin mota hoping fatima zainab zata fito anytime soon, ko damuwa da jinin dake fita daga goshinsa bayayi burinsa kawai yaga fitowarta dan yasan tinda tace zata bishi su gudu toh tabbas zata fito dan bata taba cewa zatayi abu batayi ba……. Sai yayi using time din wajan neman musu ticket din country din da zasuje, booking hotel da sauransu…..

Yana zaune cikin ikon Allah ya hangota tana fitowa daga gate din baya, barin wayarsa yayi a mota dan yaje ya sameta shiyasa tayita kira baa dagawa…….

       

        “Menene tsakaninki dashi?”……..

Khaleel ya tambaya yana daukar hanyar airport…..

      “Nothing!”……

    “Ki fadamin gsky wifey?”…….

     “Na taba maka karyane?”……

    “No, I am just wondering why you stop me from shooting him”…….

      “So kake nabarka kayi kisa khal? Moreover I like him, I mean I like his family”…..

      “Did I just here you say you like him? For real?”..

    “Kunnanka na maka ciwo ne? I said I like his family not him!”……

    “Hmmm I have a lot of questions, ya akayi ya daukeki ranar har daddy yace a bishi a kasheshi, I’m starting to suspect daddy akan gaskiya yake”…..

     “Tsaya in sauka if you’re here to interrogate me!”…..

    “Sorry wifey, I don’t mean it”……

Amma zuciyarsa taki aminta da babu wani abu tsakaninta da Deen, da zata amsa masa duka tambayoyinsa kila da komai yazo masa da sauki, ko ranar daya gansu a garden din ya akayi yasan suna chan? Ya akayi kuma ya dauketa a gidan daddy?, daya kawota gidansu kuma me yake nufi? Sai yaji gabadaya lissafinsa ya hargitse he needs more light on the issue…….

Wayar Umm dake hannunta ne ya fara vibrating alamun shigowar call, sosai hankalinta ya tashi har hakan yaso bayyana a fuskarta, tabe baki khaleel yayi yace;

    “Wayar waye?”….

    “His mom!”….

  “Who?”…..

   “Saif!”…..

  “Who is saif?”……

   “That guy!”…..

   “Who is that guy?”….

    “Would you stop this nonsense! Kasan fa wanda nake nufi”….. 

Shiru khaleel yayi dan yasan wanda take nufi dagaske, kishi ne kawai ke damunsa shiyasa yake mata tambayoyi, yanaso ya cire Deen a zuciyarsa amma ya kasa, gani yake kamar there’s something between them….. Chan kuma sai yace;

     “Where are your phones?”….

    “Duk na batar!”….

   “Ai da kin gayamin, dana siyomiki wani, why taking someone else’s phone?”…..

     “Ban bukata!, stop the car khaleel! I said stop the car!”……..

Kin tsaida motar yayi, cikin marairaice murya ya shiga bata hakuri…….

     “I’m sorry wifey bazan kara ba wallahi, you know I love you so much ko? Sanki ne yajawo duk wannan abun da nake, but I promise to stop”…….

Bata kulashi ba ta kashe wayar Umm dake hannunta…..

So yake yace tabashi wayar ya boye ya cillar amma ganin ta hada rai ya sashi kasa cewa komai……

         “Wifey we’re heading to the airport now”….

Kai kawai ta daga dan har lokacin bataji tayi wucewar da zata kulashi ba………

Haka sukaje sukayi boarding basu tafi da komai ba dama jirgin 6pm ne, yace in sunje sa siya……

      Karfe shida Deen ya tashi, yana tashi ta fado masa arai, hankalinsa ne yayi gurinta sosai musamman yanda yasan bataci abincin kirki ba ranar, yasan kuma tsap zata iya kin fitowa daga dakin saidai kuma su mami na nan….

Ruwa ya fara wasawa yazo yayi sallolinshi sannan ya bar part din gudu gudu………

Sama ya fara haurawa gurinsu mami ganin yamma tayi sosai yasan kuma dole sun dubata by then…..

Tambayarsu ita yayi sukace ai sun dauka tana tare dashi, bece komai ba ya juya ya sauka kasa..

A bakin kofar dakin data kulle kanta ya tsaya, knocking ya shigayi a hankali amma shiru baa budeba…… 

Murmushi yayi gane fishi takeyi har lokacin sannan cikin kwantar da murya yace;

      “Hey baby girl! Zo ki bude pls”….

Shiru har lokacin baa bude ba, Girgiza kai yayi aransa yana fadin yasan sai yayi dagaske kanta bude yarinya karama da ita sai zuciya, sake kwantar da muryarsa yayi yace;

      “Kince baki gama dukana ba shine nazo ki karasa, so pls open the door”……

      “Bazan kara miki ihu ba, kizo ki bude kofar pls, kinga bakici abinci ba tin safe”……..

     “Oya let’s make a deal, open the door and punish me the way you want, I promise to be loyal”…….

     “Has anybody ever told you how beautiful you are? Har kanki yayi kato ko? Toh you’re not even beautiful hhhh”……

Ya kuma fada cikin sigar tsokana……

      “Fatima ko zainab, whichever is your name open this door!!”…….

Duk wannan maganganun da yake bata kulashi ba har yaji ransa ya fara baci, controlling kansa ya sakeyi, ya sake kasa da murya yace;

     “You don’t know what you mean to me, da zaki dena bani wahala da bani da matsalar komai a duniya baby girl”….

Hannunsa ne ya murda kofar by mistake kawai yaji kofa ta bude, da mamaki ya shiga ciki yana kalle kallen ta inda ze hangota, wayam yagani babu kowa a dakin, toilet yayi knocking a tinaninsa ko tana ciki, saidai shiru baa amsa ba hakan yasa ya murda kofar ya shiga, ga mamakinsa nan ma ba kowa, a hargitse ya fito parlor ya shiga duba dakunan parlourn daya bayan daya ko Allah zesa tana ciki amma babu ita babu alamarta, a birkice yashiga duba ko ina na kasa, su kitchen hardasu store, saida ya duba ko ina be ganta ba sannan ya koma sama, a hargitse ya shiga duba ko ina su Umm na tambayarsa ya kasa basu amsa…….

     “Wai me kake nema ne saif, ka nitsu mana”….

   “Bazan iya nistuwaba Umm banganta ba, I left her in one of the rooms downstairs, yanzu ba inda ban duba ba batanan”…….

Umm da lokaci daya taji hankalinta ya tashi itama tace;

     “Amma ya zakayi haka saif? Shine bazaka zo ka fadamana ka barta ba, da kanka fa kace guduwa suke son yi”……..

      “Kulle kanta tayi Umm, kulle kanta fa tayi, wallahi indai tabi shegen yaron chan sun gudu saina kasheshi, shit ina take!!!”……

Sai ya sauka kasa da sauri, su mami suka bi bayansa….

Direct gate ya nufa mai gadi na zaune akan kujerarsa, shakosa yayi a kausashe yace;

      “Ina take?! Ubanwa yace ka bude mata kofa ta fita”….

     “Sakeshi! Sakeshi nace!”…..

Mami ta fada tana janye hannun Deen daga wuyar me gadi, wurgar dashi yayi ya daka masa sawa yace;

     “Ina take?!”….

Murya na rawa ya bashi amsa da;

      “Ba wanda ya fita yau yallabai tun bayan da kuka dawo”….

Juyawa yayi ya nufi gate din baya da sauri, yana zuwa ko yaga keys zube a kasa ga gate a bude, kanshi ya buga a jikin kofar yace;

     “Damn it! Ta gudu!!!”……

    “Saif dan Allah ka nitsu”….

Ya juyo muryar Umm da suke tsaye a bayanshi, suna ganin ya juya sukabi bayanshi dama……..

      “Why is she so sane Umm? Why?!”……

     “Kayi hakuri yarinta ke damunta”….

   “Yarinta fa kikace? Shine zata dinga dagamin hankali in the name of yarinta? Amma ba lefinta bane it’s mine, nina jawowa kaina komai dana shiga sabgarta, amma ku rubuta ku ajye daga rana me kamar ta yau na fita sabgarta na har abada!! She should go to hell, I don’t care any longer!!!”…….

Be jira ta sake cewa komai ba yabar wajan da sauri, part dinsa ya koma ya rufe kofa……..

       

KA KARANTA>> Gyaran Nono A Mahangar Ilimi

         A lokacin da suka fito daga filin jirgin ana sallahr asuba, a Nigeria kuma befi karfe biyun dare ba lokacin, fresh suke jinsu gabadaya kamar wa’yenda aka yayewa damuwa, kallonta khaleel yayi murmushi kwance akan kyakkyawar fuskarsa yace;

      “Habibty welcome to dubai!”……

Murmushin ta maida masa itama, bata iya tayi magana ba saboda gajiyan jirgi dan sunyi kusan 8hrs a sama, a haka ma babu transit direct flight ne…… 

Cab suka tsaida khaleel ya mishi bayanin inda ze kaisu…..

Daidai Burj Al Arab Jumeirah yayi parking inda khaleel ya musu reserving, hotel ne nagani na fada da ake ji dashi a duniya gabadaya ba iya dubai ba….. 

Wani hadadden room of two reserved area aka kaisu, sai katon parlor dayaji kayan alatu, sai wani garden me dauke da swimming pool da zakabi ta wani glass door da yake parlorn ka shiga, sosai gurin yayiwa fatima zainab kyau har tadinga sakin murmushi batasani ba, she has been to some countries amma bata taba zuwa dubai ba, khaleel ma yana sane ya kawota nan dan yasan bata taba zuwa ba, zaban room din datakeso tayi shi kuma ya dauki dayan, suna tsaye suna kara kallon gurin akayi knocking, khaleel ne yaje ya duba yaga pajamas da yayi ordering aka kawo musu, karba yayi ya mika mata nata ta shige ciki……..

After an hour ya mata knocking ta fito suci abinci, idar da sallolinta kenan ta fito da hijabi har kasa ta samesa a zaune akan dining yana jiranta……

     “Come and eat pls, bakici komai a plane ba wifey”……

Zama tayi ta dau mug din tea daya hadamata ta shiga sha…….

      “Abincin fah?”….

   “Maybe later!”……

    “Kina wasa da abinci wifey! Why?”……

     “Because I’m not used to!”…….

      “Bangane ba?”……

Basar da zancen tayi da fadin;

      “Khal I need something!”……

      “What?”…..

     “Take me out, let me go get it myself”…..

     “You’re exhausted, bari na siyo miki, me kike so?”…….

     “Akwai club a hotel dinnan?”……

    “Kuma? Mezakiyi a club?”……

     “Tambaya kawai nake, akwai?”……

   “Eh akwai”…..

   “Ohk, zaa iya samun abinda nakeso achan!”…..

    “Haryanzu baki dena shayeshayen nan ba wifey?”..

Khaleel ya fada dan ya riga ya gama gane kwalo kwalon da takeyi, yayi mamaki ma da bata fadi abinda takeso straightforward ba…….

     “Bandena ba!”……..

     “Haka zamuyi aure yaranmu suga mamansu na shayeshaye?”…….

      “Khaleel don’t even go there! Ba ruwanka!”…..

     “Naji, yanzu ya kikeso ayi?”……

      “Bansani ba”…..

Ta fada tana harararsa……

Murmushi yayi yana mikewa tsaye yace;

      “Toh yi hakuri wifey, kinsan bana san bacin ranki”……

Dauke kai tayi ta mishi banza…..

Kama kunnensa yayi cikin rarrashi yace;

      “I’m so sorry my love, fadamin kome kikeso in siyo miki”….,,

Dan jimm tayi sai kuma tace;

      “You know what?”…..

     “Sai kin fada wifey”….

    “I am getting resistance to codeine, sai nasha dayawa yake min abinda nakeso, how do you see if I try alcohol?”…….

      “A’a karki sha giya dan Allah, gwara codeine din, let me go get it for you”……

      “Ok, ka siyomin dayawa”……

         “Your wish is my command love”…..

     Karfe bakwai na safe suka iso house kamar yanda daddy yace su hadu achan…..

Su biyar suka tarar dasu zaune parlour, bayan daddy akwai alhaji habibu sai sauran mutanen…..

Gaisawa sukayi sannan ogansu ya fara bayani;

      “Alhaji gsky duk inda kace muje munje bamuga yaronnan ba”……

      “Bangane ba? Khaleel din da muka rabu dashi jiya, sannan me gadi ya tabbatarmin da be fita ba tin jiya sai yau da asuba, be isa ace yabar garinnan ba”….

      “Alhaji kasan dai iya aikinmu ko? Saidai in mutum baya garinnan amma babu inda bazamu nemoshi ba, toh mun dubashi a ko ina bamu ganshi ba!”……….

     “This is impossible! Dole ku nemo khaleel duk inda yake dan shima barazana ne a garemu yanzu, na baku nan da kwana uku a nemoshi ko ina yake a fadin kasarnan, sannan zan zuba ido ta gurina idan ya dawo gida”…….

       “Karkaji komai alhaji, kasa a ranka anyi kidnapping khaleel angama!”……..

   Tinda yashiga ciki ya rasa abinda ke masa dadi, yariga yayiwa kansa alkawari ya fita sabgarta gabadaya amma daze ga khaleel yanzu sai ya masa jina jina, idansa ne ya sauka akan wayarta daya dauka wani lokaci data sume masa, dauka yayi ya shiga gallery ko Allah zesa yaga hotonta, deep down bayasan sake ganinta, a hakan kuma yanajin ganin hotonta zesa yaji sanyi a ransa, saidai me? Yana shiga yaga pictures din khaleel birjik babu nata ko guda daya kai ka dauka wayar khaleel dinne, buga i14 pro max din yayi a jikin bango ta fashe tass, dukda haka beji sanyi a ransa ba ya cigaba da tattakawa a kasa, wata zuciyar ce ta shiga zugashi akan yanzu fa suna tare da khaleel, kilama tana kwance a jikinshi yanda ta kware akan seducing din mutane, kila shi kuma yana chan yana kissing lips dinta……

DUBA WANNAN>> Yadda Zaki Magance Kaikayin Nono

      “Nooooooooooooooooooooo”

Ya fada da karfi yanajin zuciyarsa kamar zata fado daya tina khaleel zeji abinda yaji shima, what if sunje an daura musu auren da gaske kamar yanda suka shirya? Mere thought dinnan ya sasa fara fasa duk abinda ya samu a dakin, dama ya saba indai yana fushi saiya fasa wani abu yakejin dadi shiyasa lokacin daya batawa fatima zainab rai yace ze kaita biggest mansion dinshi tayi fashe fashen da taga dama tinda irinsa ce……..

Knocking din daya faraji a parlor ne ya sashi dan dawowa hayyacinsa, sai kuma ya cigaba da sanbatu yana fadin “bazeyiwu ba! Bazeyiwu ba, wallahi bazaka aureta ba!”……

Chan kuma sai yaji knocking din ya kara karfi, cikin fitar hayyaci yaje ya bude, Umm ya gani tsaye a bakin kofa Allah ya taimakeshi iya daki yayi fashe fashe…..

      “Son lafiya? Yana ganka haka? Kalli hannunka ya akayi kaji ciwo?”…..

      “It’s nothing serious Umm, me kikeso”…..

Ya fada yana kokarin boyemata yanayin dayake ciki..

     “You’re not alright, tell me what’s your problem?”..

     “Trust me bakomai Umm, ya akayi”…..

     “I still don’t believe bakomai, well wayata nake nema”…….

     “Wace wayar?”…..

   “My office phone”…..

   “A ina kika ajye?”….

    “A parlor, sama da kasa mun nemeta mun rasa yanzu, and it’s so important you know”…..

Murmushi me ciwo yayi yace;

     “Ta tafi da wayarki! Ta gudu bata tsira ba Umm, zan nemota a duk inda take kodan wayarki!!”…….

     “Anya zata daukanmin waya kuwa saif?”……

      “Ku kuke mata kallon innocent, wannan ba abinda bazata iya ba, let me trace the phone now!!!!”….

    

~Uniquebarakancy~

Back to top button