Halysaah Page 210 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 210all this?” Ajay da hankalinsa yayi mugun tashi yace “Pls tell me what’s happening Jay? Did anything go wrong with her? Pls tell me” Jay na kallonsa yace “Sai da na ce maka ka bi ta a hankali saboda condition dinta, l told u this severally, to yanxu da ta yi miscarrying cikin hankalin ka ya kwanta ai ko?” Sai da Ajay yaji kansa ya wani sara masa jin abinda Jay yace, everywhere became blurr to him at first, abinda Jay yace ya dinga yi masa yawo a kai, a hankali ya jinginar da kansa da kujeran motar ya runtse ido yace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un” Bai ma san hakan da ya fada ya fito fili ba, Jay yayi masa wani kallo, after a while ya ja tsaki don har cikin ransa bai ji dadin wannan abu ba kuma duk laifin Ajay ya gani ba nata ba, ya dau wayarsa yana tunanin wanda zai kira a gaya masu wani hospital ne don yasan in dai ya sake kiran Nenne bayani zata tsaya yi masa tana koke koke, banda dare yayi da sai su tafi can Tudun Yola yasan a gidan baza a rasa wanda zai masu rakiya zuwa asibitin ba, but it’s very late now, number Aunty Farida ya kira don ita ce ta fara kiransu bayan da Nenne ta kirata ta daga mata hankali ita kanta tayi tunanin ko wani abu ne ya samu Ajay, tunda kowa yasan akan Ajay ne kadai za a ga Khaleesat a halin da ta shigo gida yau, har kiran ya katse Aunty Fa bata daga ba, Jay bai sake kiranta ba, can ya tuna yana da number Umma, duba number yayi ya kira, ba a dau lokaci ba Umma ta daga, gaisawa suka yi sannan yace “Umma kiyi hakuri na kira ki a wannan lokaci” Umma tace “Ayya ba komai Ahmad, ya mai dakin taka?” Jay yace “Tana lafiya, dama Umma asibitin da aka kwantar da Halysaah nake tambaya, yanxu muka iso Kanon za mu je asibitin” Umma tace “Ae kam ban san asibitin ba, amma bari a tambayo yanxu” Yace “To Umma” Katse wayar tayi tana kallon Islam dake dakin ita ma bata yi bacci ba, tace “Islam je ki duba ko Mama Shatu bata yi bacci ba ki tambayo ta wani asibiti ne” Islam ta mike ta fita daga dakin, babu bata lokaci sai gata ta dawo ta gaya ma Umma asibitin da Mama Shatu ta ce, Umma ta mika mata wayar tace “To kirasa ki gaya masa” Islam tayi dialing number Jay, bayan ya daga ta gaya masa sunan asıbitin…. Har Jay ya isa hospital din babu abinda Ajay yace a gaban motar, kamar ma baya cikin motar, gaba daya a sanyaye yake ba kadan ba, he looks so despondent at this point, Jay ya bude motar ya sauka, da kyar ya dake shi ma ya sauka daga cikin motar, a haka suka shiga cikin asibitin with Ajay feeling so weak, gun Nurses dake reception suka nufa, bayan sun gaisa Jay yace anyi admitting patient dinsu ne daxu shi ne suka zo dubata, wata nurse tace “Wata warce kawo tare da kakarta?” Jay yace “Yeah” Nurse tace “Sai da safe ne za ku iya ganinta, yanxu ta samu bacci” Nenne dake zaune a can wani gefe a reception din bayan likitoci sun koro ta daga ward din Khaleesat, ta mike da sauri ganin su Jay ta nufe su tace “Ashe asibitin yan iska kawai Haiydar ya kawo mu Ahamad, tun daxu suka koroni waje ban san halin da jikata take ciki ba yanxu haka, kowa ya ki kulani balle in san me ke faruwa, na kira Parida tace gobe da safe zata taho don Sarki ma yace ta taho gobe” Jay ya sauke ajiyar zuciya don duk ta cika asibitin da magana, he wish bata ma hango su ba, A hankali yace “Amma kaka ai da baki kira Aunty ba tunda nace maki muna hanya” Nenne tace “Ai zubewan cikin ne ya gigita ni Jawwal, na fito ina ihu shine mutanen nan suka kulle kofar dakin suka ki barin in kara shiga har yanxu da nake maka magana, kuma sun ki gaya min halin da take ciki” Ajay ya nemi waje ya zauna a reception din don ji yake tsayuwar na neman gagaran sa, Jay na kallon Nenne yace “Bari mu shiga Office din likitan mu yi magana da shi kaka” Nurse din tace “Sorry, but Dr is not on seat now, sai da safe” Nenne ta kankance ido tace “Sai da sate za ayi me? Ban gane sai da safe ba bamu san halin da yarinya ke ciki ba, gaskiya Haiydar ya ja mana babban matsala wannan asibitin gantalallu da ya kawo mu, haba sai kace ba dan boko ba kawai ya kinkimo mu ya kawo mu asibiti babu bincike akan wani irin asibiti ne” Jay wish zai disappearing daga reception din, har yaji kansı fara ciwo a wajen, yaki ce ma Nenne komai, Dai dai nan wani likita ya shigo reception din, Nurse din na kallon sa tace “Sir, wajen patient din ka suka zo….” Nenne ta dinga hararan likitan don shi ya koreta kuma yaki mata bayanin komai har yanxu, Likitan na kallon Jay suka gaisa sannan yace “Are you related to the patient?” Jay yace “Certainly…” Likitan yace “To mu je office” Jay ya juya ya kalli Ajay da ya mike jin abinda likitan yace, likitan na fara tafiya suka bi bayan sa, sai da likitan yayi nisa ya juya ya ga Nenne ma na biye da su, tsayawa yayi yace “A’a Mama, ban da ke, ki koma reception kiyi zaman ki kawai” Nenne tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, ko dai baka da kai ne likitan nan, ni fa na haifi ubanta, me yasa zaka dinga min katanga da abinda ya shafi jikata, wannan wani irin asibiti ne Haiydar din Zaliha ya kawo mu” Jay ya juya ya kalli Nenne calmly yace “Kaka kiyi hakuri, duk bayanin da yayi mana za mu maki ai idan muka fito in sha Allah” Likitan dai tuni ya ci gaba da tafiyarsa Ajay na biye da shi, Nenne tace “Ni Wallahi Jawwal ban taba ganin dan iskan likita kamar wannan mutumi ba, amma ba komai ku je kawai, duk Haiydar ne ya ja mana wannan tsiyar, bai yi bincike ba ya kawo mu asibitin nan, ni ina masa kallon wayayyen yaro” Jay dai ya lallaba Nenne ta koma reception sannan ya bi bayan su Ajay. Likitan na kallon Jay dake zaune office dinsa yace “Babu wa yayi ma Mama maganar Miscarriage ko makamancin sa, bamu san inda ta samu news din ba gaskiya” Ajay ya mike tsaye yana kallon likitan jin abinda yace amma ya kasa cewa komai, Jay na kallon likitan da sauri yace “Dr kana nufin cikin na nan lafiya?” Likitan yace “Cikin ta na nan babu abinda ya samesa, kawai tana bukatar bed rest ne…” Jay yace “Za mu iya ganinta yanxu?” Likitan yace “She is asleep now….” Jay yayi kasa da murya yace “Yeah, ba tashin ta za mu yi ba Dr….” Jay ya nuna ma likitan Ajay yace “He is her husband, and i am his brother” Likitan ya daga kai ya kalli Ajay da ya kasa cewa komai a office din, likitan yace “Alright, to naga yayi shiru nayi tunanin rako ka yayi ai” Jay yayi murmushi yace “He is worried ne Dr, shi idan yana damuwa baya magana” Likitan yace “To gaskiya zai yi magana don ina da tambayoyin da zan masa da Mama ta kasa amsa mana su” Ajay dai ya sauke idonsa bai ce komai ba, Likitan yace “What happened to her in particular har tayi pass out? Menene ya faru, ko kuma ta saba yin haka dama with or without pregnancy?” Jay ya sauke ajiyar zuciya, at first ya rasa me zai ce ma likitan, can kuma yace “Ba ma gari Dr, dawowar mu Kano kenan saboda wannan abun da ya faru, or probably she is stressed, cause ita ma tayi tafiya, she arrived Kano today also” Likitan yace “To amma akwai abinda dameta ne, ko yake damunta cause ni naga da damuwa sosai, sannan mun samu information din tana da record din miscarriage a baya, so ya kamata da ta samu cikin nan ace an kawota asibiti an dubata to be sure everything is okay at this stage which we call the embryonic stage, probably ba a san dalilin miscarriage dinta na farko ba, da basu kawota hospital ba definitely cikin nan zai iya fita with the look of things, You both look learned, nake ga ai ba sai an karanto maku abinda ya dace da mai ciki ba….” Jay na kallon likitan calmly yace “Sir, her husband is Gynecologist nasan duk yana da niyyar yin abubuwan nan da ka lissafo, we’ve been away for some time now, har da ita aka yi tafiyar kuma, kawai dai ta riga ma isowa Kano ne..!.” Likitan yace “Maa sha Allah, mu je to ku ganta” Mikewa yayi, Ajay ya juya ya fita daga ward din. Tun da suka shiga ward din da Khaleesat ke kwance Ajay yake kallonta, bacci take da drip a hannunta, Jay ya karasa har kusa da gadon yana kallonta shi ma, sannan ya kalli drip din hannunta, hannu ya kai forehead dinta yaji alamar temperature dinta sauka yayi don it was high before, after few more seconds ya juya ya fita daga ward din likitan na biye da shi, sai a sannan Ajay ya samu courage din karasawa kusa da gadon ya zauna gefenta yana kallonta, a hankali ya saka hannunsa cikin nata, yajı hannun da dumi sosai, sun fi minti biyar a haka, ita dai bacci kawai take, daga karshe saketa gently ya mike yana kallon drip din ya gudunsa kadan, after standing for another 5 minutes yana kallonta ya juya ya fita daga ward din, ya tarar da Jay a corridor din ward din a zaune, nan duk avoiding komawa reception yake kar Nenne ta cika sa da magana, Jay ya mike yana kallon Ajay yace “Ka ga ko zagin ka Halysaah take yanxu kawai sai dai kayi hakuri ka zuba mata ido har ta haifi cikin nan lafiya, i wish kaji irin fadan da Mai martaba ya dinga yi a waya daxu, a haka ma bai san abinda ya faru ba har ta tafi gida ita kadai da daddare” Ajay ya sauke ajiyar zuciya, a hankali yace “Amma waye ya kira su?” Jay yace Warce ta ce mana cikin ya zube mana, ai har Bauchi sai da ta kira duk a daren nan, Hajiya Kaka kenan kake ji, ashe ma babu wanda ya ce mata ciki ya zube ita ta tsara kayanta, yanxu dai ka tanadi me zaka gaya ma sarki don yana son sanin dalilin da yasa ta tafi gida ita kadai da daddare, ní dai nace masa ban san komai ba” Ajay bai ma san me zai ce ba ya dinga kallon Jay, can yace “To amma dai baka ce masa she travelled all the way to Kano ita kadai ba?” Jay yace “A’a duk kai zaka yi wannan explanation din ba ni ba, don ni na ce ban san komai ba, kuma bazan nuna nasan komai ba, wai ka zata Mai martaba na wasa da batun Halysaah ne? I won’t even be surprise to see him in Kano tomorrow….” Ajay ya nemi waje ya zauna a corridor din, shi kansa yasan Mai martaba won’t take it likely with him ko da bashi da laifi, Jay “And i will advise you to go home kar ma tayi arba da kai ta tona mana asiri a asibitin nan, shekaru biyu da suka wuce tashin hankalin abinda ya same ka yasa tayi miscarrying cikin a lokacin, I told you this but may be not as seriously as i was suppose to tell you, i wish kaga wahalan da Halysaah ta sha during that phase of miscarrying ur twins, but rashin ka ya doke wannan wahalan a wajenta, kuma wannan cikin ma ace bacin ran da ka kuntsa mata ne zai yi sanadin lalacewan sa?” Ajay yace “| don’t understand, what are you talking about Jay, is it an offense don na je wajen mutanen da suka taimakeni, mutanen da tunda na baro garin ban koma ba sai yanxu, don’t forget i left without even saying a thank you to them” Jay yace “To tunda me ciki ta nuna hakan offense ne sai ka bi ta a haka, beside na lura rungume mata miji da aka yi ne kawai matsalar ta, kaga next time idan zaka koma wajen su ae ba wani ne zai sa ka ki gaya mata inda zaka je ba, sai da nace kar aje da ita amma kana shakka da tsoron yi mata magana, you weren’t man enough to stop her from following us, to sai da muka je Benue ta fara misbehaving ne zaka nuna mata kai namiji ne, ai aikin banza kenan tunda ka kasa stopping dinta from following us, so why acting like a man all of a sudden, ai da ta fara maka bori kawai da lallabata zaka yi har mu baro garin tunda ka saba tolerating, any way, duk ma me Halysaah zata yi maka she deserve to pampered and tolerated, may be idan an zal da kai an baka full lectures din halin da love ones dinka suka shiga during the period you were away da duk ma me Halysaah zata yi maka shanye….” Shi dai Ajay was quiet, a haka suka koma reception daga karshe, Nenne ta taso da sauri ta nufo su tace “Kun samu ganinta kuwa?” Jay yace “Mun ganta kaka, tana bukatar hutu ne shi yasa basa son a shiga dakin, sannan juna biyun dake jikinta yana nan babu abinda ya samesa” Nenne ta saki baki tace “To me yasa suka ce min cikin ya zube? Kai wa ennan likitoci dai anyi barbadaddun likitoci, kuma yanda suka daga min hankali Allah bazai bar su ba, gashi har Parida na kira na daga mata hankali ita ma” Ajay dai ya nemi waje ya zauna yana tunanin me zai ce ma Mai martaba ya sami Khaleesat, where is he going to start explaining from, Washegari Jay bai bar Ajay ya shiga wajen Khaleesat ba duk da yana asibitin don duk a nan suka kwana, karte tara da kusan rabi na safe Hadiyah ta iso asibitin da breakfast da tayi ma Khaleesat, Jay na zaune cikin ward din sai Islam da tun karfe bakwai na safe suka zo asibitin da basket din breakfast ita da Mama Zubaida, Haiydar ne ya kawo su asibitin sannan ya dau Nenne ya maidata gida, Jay ya daga kai yana kallon Hadiyah da ta shigo ward din da sallama, ta ajiye abincin hannunta tana amsa gaisuwan Islam, ta nufi kusa da Khaleesat dake zaune kan gado an cire mata drip ga cup din te hannunta ko quarter bata sha ba, zaun gefenta Hadiyah tayi tana kallonta da damuwa tace “Sannu Halysaah, ya jikin?” A hankali Khaleesat tace “Da sauki” Hadiyah ta juya Jay tace “Ya Junaid fa?” Ya gyara zama yace “Ina kwana Madam” Ta wani kallesa tana murmushi tace “Sau nawa za mu gaisa yau din, ni dai ina Ya Junaid?” Yace “Who brought you?” Tace “Driver ne ya kawo ni” Yace “Ohk, to ki zuba mata abincin may be she will like what you brought, tunda ta ki cin wanda aka kawo daxu” Hadiyah ta mike zata dibar ma Khaleesat abincin da ta kawo, Khaleesat dake kallonta a hankali tace “Bazan ci ba Hadiyah….” Jay yace “To me kika ci?” Taki kallonsa kawai ta nuna cup din hannunta, wayar Umma dake hannun Islam ya fara ringing, mikewa tayi ta fita don Haiydar ne ke kiran wayar sanin yana hannunta, Hadiyah tayi kasa da murya tace “Wai kin riga su dawowa ne daga Benue din Halysaah?” Jay ya daga kai ya kalli Hadiyah yace “She needs rest Hadiyah….” Hadiyah bata sake cewa komai ba, Jay ya duba wayarsa dake vibrating ya daga kiran ganin Mami ke kiransa, bayan sun gaisa ta tambayesa jikin Khaleesat sannan tace ya bata waya, Khaleesat ta amshi wayar da Jay ke mika mata suka yi magana da Mami sannan ta maida masa wayarsa, fita yayı daga dakin bayan ya maida wayar kunne, Khaleesat ta daga kai ta kalli Hadiyah muryarta na rawa tace “Sai yanxu na kara sanin waye na wallahi nayi da na sanin duk sacrifice dina” S ta fashe da kuka, Hadiyah ta dinga kallonta da mamaki jin abinda tace, to matsala kenan suka samu da Ajay?? But how? a yanda dai jay da Khaleesat har za su iya samun matsala kuwa, ko dai wani namijin daban take nufi ba dai mijinta ba, don ita dai tasan Ajay will be the least person to hurt her duba da yanda yake bi da ita kamar kwai, after some seconds Hadiyah ta kamo hannunta ganin yanda take kuka ta girgiza mata kai tace “Consider your condition pls Halysaah, ko ma menene ki sa ma ranki hakuri, this is not the right time to speak, kiyi hakuri ki bar maganar nan yanxu” Cikin kuka Khaleesat tace “Walakanta ni fa yayi a Benue din” Hadiyah ta kasa daurewa tace “Walakanci kuma? How? Waye ya walakanta ki?” Ita dai kawai ta tambayeta waye ya walakanta ta ne don zuciyarta bai amince cewar Ajay take nufi ba har sannan, Kuka kawai Khaleesat take ta kasa bata amsa tana kokarin sauka daga kan gadon amma taji kamar jiri zai dibeta idan ta sauka, hakan yasa ta fasa saukan ta koma ta zauna tana ci gaba da kukanta, a sanyaye Hadiyah tace “Ni dai don Allah kiyi hakuri ki bar kukan nan Halysaah, koma menene kiyi hakuri kiyi ta innalillahi wa Inna llaihi raji’un a zuciyar ki, you will feel relieve in sha Allah” Da kyar Khaleesat tace “Wallahi bazan zauna da shi ba, na gama aurensa har abada, ya je can ya auri er Benue su zauna, idan na haifi cikin ma zan basa dan ya kai mata rike masa” Tsabar mamaki Hadiyah speechles zama a wajen ta saki baki tana kallon Khaleesat.Ajay na zaune tare da Jay a reception, wajen karfe sha daya, tun da Jay yace masa an taho daga Emirate hankalinsa yaki kwanciya, ya daga kai ya kalli Jay yace “Nasan Mai martaba ma bazai ce zai bar fada ya taho har Kano because of just this ba, kawai Aunty Farida ce take hanya alone I guess” Jay ya wani kalli Ajay yace “Wato just ne ma issue din nan a wajen ka ko?” Ajay yace “Just ne mana, since she didn’t miscarry the pregnancy, you just have to tell her that she shouldn’t say anything to anyone about this, this is something we can resolve without involving anyone, dama ita ce ta dauka da zafi ai, but there is, nothing wrong don na je Benue” Jay yace “I Finally give up on ur matter Ajay, kawai ka tashi kayi tafiyar ka gida kaje kayi bacci” Yana fadin haka ya mike ya koma wani wajen ya zauna don ba karamin haushi Ajay ya basa ba, may be don yaga cikin bai zube bane ya samu bakin magana, Haiydar ne ya shigo reception din tare da Abdul da Islam, tun da Ajay ya kalli Abdul sau daya nan da nan mood dinsa ya canza ya dauke idonsa ya ciro wayarsa yana dannawa, Jay ya mike suka gaisa da Abdul da fara’a, Abdul yace “Ya me jiki?” Jay yace “Jiki Alhamdulillah” Abdul ya karasa ya ba Ajay.


