Hausa novels

Haihuwa Da Hanji Page 31 Hausa Novel

A hankali kwanaki ke ja har ranar da Uncle Musa ya yanke da za su tafi Dutsen-wai su samu kawu, shi da yaranshi manya biyu sai Driver suka ɗauki hanyar, tafiyan awanni kaɗan ya sada su da kauyen, kusan abin da ya faru da ‘yan uwan Sulaiman hakan ce ta faru amma dayake ya riga ya sani suma kuma sun sani so basu wani damu ba.A kofar gidan Labaran suka yi parking motar su biyu suka fito suka bar uncle ɗin cikin mota, gidan da rabin shi a zube a ƙasa suka ɗan zubawa idanu suna mamakin me ya kawo Rayyan har nan neman aure? Daga ka ga gidan zaka san suna fama da masifar talauci, buhuhuna ne da suka zama jajazir aka kare ɓangare guda na gidan dashi, ga yara nan dukunkun rabin su tsirara suna ta wasa a kofar gidan, daga gefe wasu matasa ne suna shaye-shayensu ko a jikinsu, ɗayan na shirin turawa a kira musu mai gidan sai ga kawu Labaran ya fito a zuburen shi ganin mota ya sa ya taka birki “Lafiya?””Ƙalau sai Alheri, Malam Labaran muke nema”Kanshi ya nuna “Ga ni”Girgiza kai babban da sunanshi Mansur yayi wani abu sai bakauye Dukda wasu kauyukan mutanen cikinshi akwai kara da girmama baƙo haka kuma mutane suna suka tara, amma babu gaisuwa babu komai bare iso ko ruwa kawai a yi abinda ake so.”Mun zo ne akan maganar ‘yar wajenka Afeefah”Uncle Sanusi ya faɗa, tun ma kafin ya gama kaiwa aya Kawu ya katse shi “Wace Afeefah? Ai mu bamu da Afeefah a zuri’ar mu kap”Uncle Mansur yace “Afeefah ‘yar wajen ƙaninka?””Ah Annoba zaka ce sai na fi ganewa, ai na jima da sallamar wa duniya ita ko a chan ne tayi muku wani abin ba wurina za ku zo ba ita za ku kama babu ruwan Labaran Ah to””Malam ka natsu mana ka ji bayanin da muke tafe dashi”Uncle Mansur ya faɗa da ɗan zafi don yana da faɗa shi, Buɗe kofan da Mahaifinsu yayi ya fito ne ya sa suka yi shiru, uncle Musa ya miƙa mishi hannu suka gaisa ya ce “Ba wani abu bane ya kawo mu illa nemawa jikana, ɗan wajen su auren ‘yarka Afeefah, mun zo ne da batun na gani ina so idan babu damuwa zaka iya ba mu rana sai mu zo a ɗaura aure””aure??”Ya faɗa yana sake kallonsu Dukda sun yi zubin masu hankali kuma kaman suna da kuɗi amma wani gida ne zasu yadda dansu ya auri Afeefah? Kila dai basu san wace ita ba, zayyano musu wace ita da mutanen da ta kashe ya shiga yi har abinda ya sa ta bar garin “Duk mun san da hakan”Uncle Sanusi ya faɗa.”Kuma kuka yarda ɗan ku ya aureta?””Eh a haka yake sonta, bama buƙatar komai daga gareka ita ɗin ma ba sai ta dawo nan ba auren kawai muke so ka bamu da kanka kuma mutanen garin nan su shida zaman aure zata cigaba da yi ba dadiro ba kaman yadda kuke ta faɗa”Numfashi ya sauƙe ai tunda babu abinda suke so shikenan kila ma suma manyan mayun ne don waenda basu ji tsoro ba bayan jin labarinta ai basu da maraba da mayun, kuɗi har dubu hamsin suka bashi a cewar na gani ina so ne. Ya hangame baki yana kallon uban kuɗin kaman faɗa ya karɓa yace tunda sune zasu zo su gaya mishi kawai randa suke so a daura, suna ta mamaki shi ba ruwanshi da bincike ko wani abu tunda ya ga kudi kawai ya ruɗe, suka tsayar da nan da wata guda a haka suka yi komai daga tsaye suka shiga mota suka juya suna mamakin ƙarantar mutumin.A chan wurin kawu kuwa kaman zai kifa ya shiga gidan “Asabe, larai ku fito ku ji abin mamaki wai na kwance ya faɗi”Duk waje suka yo larai ta kasa shiru “Wannan uban kudin fa malam daga ina haka?””Nima duk kaina ya kulle, wasu ne suka zo yanzu a mota wai sun zo neman auren Afeefah wannan kudin na gani ina so ne suka bayar””Afeefah dai???? A mota?? Wannan uban kudin kawai na na gani ina so ne? Kuma ka amince musu??”Duk a jere suka jero tambayoyin cike da tashin hankalin hassada.”Toh ko ban basu ba ai zasu iya auren tunda ba gabanmu take ba tunda suka ba da wannan a na gani ina so ki yi lissafin nawa zasu bayar sadaki?””Amma malam Afeefah annoba Mayyar taya zata yi aure ta bar yaranmu zaune? A dandi fa take basu sani bane?””Sai da na basu labarinta tsaff kuma sun ce sun ji sun gani”Wani irin abu ne ya taso ya tsayawa inna larai a makogoro Ah ba zai yiwu ba, sam Afeefah bata chanchanci auren mai kuɗi ba dole ta san yadda zata yi zama bai ganta ba.Ko ta kan bayanin da kawun ke tayi bata bi ba shi lissafin zuwan kuɗin shi yake don ya ce sai ya bi Afeefar ya ga inda zata zauna in gidan kudi ne yayi ta zuwa ana bashi kasonshi ai ta zauna gidanshi sama da shekaru goma yana ciyar da ita a banza.Inna larai gyale ta saɓa ta fita afujajan ko auren ya lalace ko kuma ya dawo kan daya daga cikin ‘ya’yanta ba zai yiwu tana ji tana gani Afeefah ta yi aure inda zata je ta huta ba su suna nan suna cin wuya, har ita a wa? Daji sossai ta shiga sau ɗaya ta taɓa rako wata kawarta wurin bokan don bata taɓa zuwa ba amma ganin aikinshi yayi a kan kawarta ya sa ta gamsu zai iya wargaza auren Afeefah ya dawo dashi kan ‘yarta, ɓacewa tayi tayi ta zagaye a garin neman inda zata kulla sharrin ta maciji ya sare ta, wani irin ihu take da kururuwa tana neman taimako Allah ya taimaketa akwai wasu mutane a gona suka zo suka fara taimakonta kan aka ɗauko ta mutu kwaikwai rai kwaikwai aka dawo da ita cikin dutsen wai, abu kaman wasa kafa ya fara zama wani abu daban kaman ba macijin gaske ba don duk maganin da ake yi na macizai an yi mata sai zabura take ga zazzabi tayi sharkar da gumi tana surutai…****Afeefah na zaune tana azkar na bayan Magrib Abeeha ta shigo tana shigowa ta rangada guda “Ahayye matar babban yaya bi’izinillahi nan da wata guda za mu sha shagali”Gaban Afeefah ne yayi wani irin faɗuwa, kenan wata daya suka saka auren? Jikinta yayi wani irin sanyi ta fara jin hawaye na zuba mata dukda ta amince har ranta da auren sai dai tana jin wani irin ciwo a ƙasan ranta na auren wanda baya sonta bai ma dauketa mace ba, kila ma ko sunanta bai sani ba don bata taɓa ji ya ambata ba, Abeeha ce ta tsuguna tana tsokanarta har ta fara kukan auren kenan? Da kyar tayi shiru.Bayan isha Mammi ta aiko aka ƙirata bayani ta mata akan kwanakin da aka sa auren, bata ce komai ba Mammi ta ce zata iya tafiya a Washegarin aka fara zuwa yi mata gyaran jiki don mammi sossai ta tashi tsaye Dukda ciwo dake nukurkusarta amma auren ɗan farinta babu batun zama, shi dai kam ma a satin aka tura shi wani assignment Zamfara ya wuce kuma zai yi akallah sati uku.****Ta ɓangaren su mommy fa rayuwar ya juye musu, a hankali suka fara fahimtar abin da rayuwa ya kunsa barin ma da ta mayar da sunna Tv da kuma Africa tv3 abin sauraro, suna takure sai dai basu rasa ci da sha ba kuma duka yaran suna zuwa makarantar su sai dai hankalinsu ba’a kwance yake ba, ga ayyukan su da suka manta yadda ake su wanki, guga, shara wanke wanke da girki duk su suke yi idan basa nan suna school haka mommyn ce ke yi dole, ko wani dare karfe uku baccinta ya ƙare don ciwo ne sossai a ranta na abin da aka yi wa saleem, tana roƙon mishi waraka kuma tana roƙon Allah kar ya kama shi da laifi don ba laifinshi bane nata ne. Yau da ta ji tana matuƙar kewanshi ta tura Sameera da Samha gidan akan su duba shi, ko da suka je kaman baƙi haka suka tsaya jikin kofan suna knocking kusan mintuna biyar tukuna Gaje ta zo ta buɗe ganinsu ya sa tayi murmushi “Ah ashe su Sameera ne sannunku da zuwa bismillah”Sai suka ji wani iri a gidansu ne ake musu iso? Shiga suka yi suka samu Yaya zaune cikin kujera relaxed irin gidan shin nan, zama suka yi suka gaishe shi ya amsa kan Samha tace “Wurin Yaya ne muka zo yana nan?””Eh yana nan bari na dubo Sabrina ta turo muku shi. Talatuwa..! Talatuwa…!! Kawo musu ruwa”Su dai banda ikon Allah babu abinda suke gani wai in faɗa ya fi karfinka sai ka mayar da shi wasa ba kuma baki sai kunne murmushin dole kawai suke yi har Talatuwa ta fito, da tausayi take kallon su amma ya zata yi dole ta cigaba da aiki da mutanen da suke gidan in tana bukatar abin rufa wa kai asiri, ruwan ta kawo musu ta gaishe su suka amsa a sanyaye.Sun fi mintuna talatin kan ya fito ya zauna yana kallon su itama Sabrina ta zauna gefenshi don su Gajen duk sun tashi sun yi wuraren da nan ne ɗakunan Mommy da nasu suke a baya, gaisheshi suka yi ya amsa “Lafiya?”Ya tambaya sai Samha ta fara zubar da hawaye, wai yaya saleem ne ya zama musu baƙo? Yaya saleem dai da yake matuƙar kaunarsu ne wannan zaune? “Rashin kunyar taku ne kuka zo har nan ku cigaba ko? Duk wanda kuka dinga yi mata a baya bai ishe ku ba?”Shiru suka yi don basu san me suka yi ba wani irin tsawa ya daka musu “Ba Za ku gaishe ta ba??”A ɗan razane suka shiga gaisheta tayi murmushi tana amsawa har da tambayar su mommy na lafiya? Suka amsa da lafiya lau.”Me kuke so? Ba na ce zan neme ku ba?”Ya faɗa har yanzu babu walwala a fuskarshi “Dama mommy ce tace mu zo mu duba kana lafiya?””Jinjiri ne ni? Ko idan banda lafiya ku nake jira ku kaini asibiti?”Shiru suka yi sai Sabrina ce tace “My S ka daina fushi ai ba laifi bane don sun ji lafiyarka, ku je ku ce mata yana lafiya yana miƙa saƙon gaisuwa kuma bai manta da ita ba zai zo idan ya shirya shikenan?”Sameera ta miƙe ta kama hannun Samha “Za ta ji, sai anjima”Ta jata suka fice sai kuka samhar ke yi har suka shiga napep hannun Sameera ta rike”Sameera har da laifina a mayar da yaya saleem haka, duk ni ce da ban kiraku ɗakin Afeefah ba da bamu san suna soyayya har mu raba su mommy ta aura mishi wannan fitsararriyar mai ido a tsakar ka ba””Samha ki daina wannan kukan, komai ya wuce dukkanmu muna da laifi… Ki yi shiru bana so mu je wurin Mommy kina cigaba da wannan kukan kar hankalinta ya sake tashi, Yaya Adu’a yake bukata ba kuka ba”Dukda itama hawaye take sharewa lallai ta yarda duk soyayyar Uwa ga ɗa tana iya zama mummunar kaddararshi ko da sanin ta ko akasin hakan, mommy ta zamewa salim mummunar kaddara sai dai Allah ya bashi ikon hayewa ya bashi ƙwarin zuciyar ɗauka kar ya halaka a haka.****A sati uku da suka biyo baya idan ka ga Afeefah za ka rantse da Allah ba itan ba ce, Caramel skin ɗinta wani irin daukar ido da sheki yake, tayi wani irin kyau har ta gaji, ba gyaran jiki kaɗai ake yi mata ba sessions ne daban daban a satukan ga karatu, ana koya mata dressing irin na wayyayyun matan aure, ana koya mata girke girke na zamani da bata kware ba ana kuma koyar da ita rayuwar auren da ma auren karan kanshi haɗe da dabarun zama da miji, ta ɗan rame saboda stress amma ta wani irin cikowa tayi kyau masha Allah, ba kananun kudi Mammi ke bararwa ba Dukda ba buki za su yi ba sam.Ko da su Umman Sulaiman suka ji labari su ma ba’a bar su a baya ba, Baaba jummai ta kan zo ta yini bata shawarari kuma tsaff take ɗauka wasu dai sai dai tayi murmushi don ta san ba dai Rayyan za ta yiwa ba don wani abin bata tunanin har abada ma zata yi amfani da shawarar, mixed emotions take ji akan auren. Wai ita ce Afeefah za ta yi aure? Ita da ta fara sallamar da zancen aure a rayuwarta saboda mummunar Taɓonta, ko da a da ta yi tunanin auren tayi tunanin aure zai zo mata a kaskance cikin rashin galihu da gata, auren da zata iya zuwa ta cigaba da shan wahala kaman yadda ta faro a rayuwarta sai gashi ta samu gatan da bata taɓa tunani ba, gatan da ko iyayenta suna raye karshen abin da za su yi mata kenan, ta kan raba dare tana kuka tana miƙa godiyar ta ga Allah tana kuma roƙon shi da kar ya nuna mata ranar da za tayiwa waennan bayin Allahn butulci.Yau Asabar da wuri ta tashi don sun yi class da mai koya mata girki, gasashen kifi suka yi talapia ya ji onion sauce sai irish da aka gasa aka yi ganishing a gefen kifin, a gefe wani hot beef stir fry jollof Rice ne, a dining suka shirya don ita da Abeeha suna ci Mammi ce dai ba zata ci ba, bayan sun gama taje tayi wanka yadda aka nuna mata sabon method na yi har da dauraye jiki da ruwan turare ta fito tana zuba uban kamshi, gaban wardrobe ta tsaya tana tunanin kayan da zata saka, a hankali ta zaro wani dogon riga mai yanayi da silk material ta zura yayi mata kyau sossai don A line ne rigar bai kai ƙasa sosai ba kuma ƙasan ba a zagaye ba ana iya ganin idanun sawunta, hula mai butterfly a gaban Goshi ta saka ta ɗan tsaya gaban madubi sai taga kaman kayan ya mata yawa bata fita classy ba, komawa tayi ta nemi belt ta ɗaura a daidai cikinta sai ya bata wani kyaun na musamman murmushi ta saki ta ɗauki wayanta ta fito, daidai Abeeha ma ta fito daga nata ɗakin.”Ku ne kyau amare”Ta tsokani Afeefar da kullum aikinta kenan, murmushi Afeefah tayi don tun tana rigima har ta gaji ta shiga kyale Abeehar.”Wlh Afeefah kina da kyau, kaman fa wata model haka kika fita, duk kayan da zaki sa yanzu kin san irin adon da zaki musu su fita daban”Suna shiga cikin parlorn suke zancen, Afeefah na cewa “Addah Abee ai ina ga zan saka fashion design cikin mafarkaina don gaskiya abin na burgeni bana rabo da kallon fashion show””Toh ke madam komai ma kina so? Ke fa kika ce business woman kike son zama na inna naha don kina son yin kuɗi”Ta faɗa da dariya.”Ai duk mace tana bukatar waennan a gani na fa, kin ga girki ya zama favorite thing ɗina saboda wajibi ne a gidan aure, dressing ma wajibi ne in kana so ka burge masoyinka duk ba laifi bane business kuma shine asalin abin da nake so, ina so nayi kuɗi na samu na kashewa marayu da bayin Allah, ina so nayi kudi na tallafi rayuwar yaran da suke wahala a duk sadda suka rasa iyaye, gidauniyoyi nake mafarkin buɗewa na wayar da kan mata akan mecece rayuwa da kuma yakar jahilci a yankunanmu”Abeeha na dariya take cewa “Su burge masoyi, a’a ka ga Masoyiyar Ya Ra…”Katse wa maganar yayi suka tsaya chak idanunsu a kan Rayyan dake zaune dining yana karyawa hankali kwance, kuma tsaf ya ji su don daskare wa da suka yi ya sa ya ɗago firgitattun idanunshi ya zuba musu yana aika musu da kallo mai kama da gargaɗi….

Back to top button