Gargadar So Chapter 110 By M Shakur
Chak ta tsaya yanda ya kirata har cikin ranta taji muryansa gabobin jikinta na amamsawa, amman bata amsaba bakuma tajuyoba, ahankali Khaleel yana gyara voice nashi dan baiso tagane wani abu gamedashi yace “change and come down we are going out” batare data kalleshi ba tace “I’m not going anywhere with you Ibrahim Khaleel!” Saikuma tajuyo zuciya na debanta fuuu tadawo gaban kujeran dayake zaune ta tsaya tareda bude jakan hannunta duk yana kallonta envelope na court taciro ta ijiye kan hannun kujeran dayake kai yabi sammacin da kallo tajuya tawuce fuuu tafara hawa staircase, ahankali kaman baisan metayi ba yace “hurry up Moonshine, I kept something on your bed shizaki saka” juyowa Hawwa tayi cikeda fada kaman wata zakanya tace “nace ba inda zani dakai so also I’m not gonna wear anything from you” kallonta yayi shima cikin ido yace “Baba ke neman mu wajenshi zamu, the clothes shiya aiko dasu plus this one I’m wearing” chak Hawwa ta tsaya tana kallonshi, karanta yakai wajen Baba saikuma ta juya zata wuce Khaleel yace “after magrib” dakinta tawuce tana shiga taga wani mahaukacin designer abaya sabo fil ajikin hanger irin wanda take gani a IG na 20M dinnan black ga duwatsu ya Allah kaman ka lashe abayan saiga wani takalmi dan heel na Dior pink sai wani bottega hand purse pink ya Allah sunyi kyau, note tagani dasauri takalla handwriting din Khaleel ne hannu tasa tadauka yace “can you please do makeup? Banso Baba yasan we are fighting” ijiye note din tayi da sauri sai kawai tafada bayi toh idan Baba baisan suna fada a maisa yake nemansu? Dawani kudi yasainusu kayan nan, bataso asan sunyi fada za’a hanata shigar da karan kotu.Wanka tayi tafito tazauna kawai tafara makeup gabanta na faduwa, foundation ta shafa da hoda tai carving eyebrows nata tasa concealer ta tai highlighting yau pink lipstick tasa sabida takalmi da jakan taga pink ne, ta tashi tai salla sannan tawuce tasaka inner tafito tasa abayan tunda take bata taba saka abaya daya mata kyau like this ba heel din tasa tai wani irin kyau kaman aljana, tadauki purse din wlh kaman balarabiya tana fesa turaruka, kallon kanta tayi kyan yamayi yawa kaman taje ta goge makeup din daidai anyi knockin tareda bude kofan, chak breath na Khaleel ya tsaya sabida yanda Hawwa tayi kyau dauke kanta tayi from kallonshi sabida yamata kyau dayawa a idanu hakan yasa shima ya iya daidaita kanshi yace “let’s go” yajuya yayi gaba itama tafito gashi ta iya tafiya da heel tundaga staircase take kallon sammacin data bashi dake inda ta ijiye daga gani ko tabawa baimayiba, kofa yabude mata yajuyo yana kallonta yana jiranta tazo tana zuwa tafita kamshin datake yawani shaka yabiyota abaya taga wata sabuwan Maybach pink ke jiransu bude mata yayi tazo tashiga batare data kalleshi ba shima ya shiga ciki ya zauna, aka rufo musu kofa aka ja motan kamshin datakeyi da kamshin dayakeyi sun hadu sun gauraye motan, ahankali Khaleel yake kai hannunshi zuwa nata dake kan kujeran gabanshi har faduwa yake but he just wanna touch her ko kadan ne, tun safe bai riketa ba not yayi feeling skin nata, even if it’s just for a moment he wants to touch her, hannunshi yadaura saman nata ahankali dasauri Hawwa tajuyo takalleshi suka hada idanu tamai wani kallon fitinan bala’i ta fizge hannunta, dan ijiyan zuciya Khaleel yasauke yakoma ya jingina da bango kujeran.Gaban wani babban teaching hospital yaga sunyi parking already saitaga ma’aikatan Khaleel dasu bodyguards duk tsaye wajen kaman ansan da zuwansu, ga CMac na asibitin da wata HOD da couples of Doctors and metrons, budu musu akayi Khaleel yasauko yakalleta yace “come” adan tsorace tace “something happened to Baba ne?” Girgixamai kai yayi yace “No” sakkowa tayi ahankali suka fara tafiya looking elegantly cute together sai kawai yarike mata hannu akwai mutane awajen kuma kallonsu ake ga ma’aikatan sa hakan yasa bata karbe hannun ba, CMac din yakaraso da sauri yana bama Khaleel hannu yace “welcome Sir and Ma” gyadamusu kai yayi suka babbama Khaleel hannu sauran likitoci kafin Cmac yayi gaba suka shiga cikin hospital din gaban wani newly built abi renovated ICU taga sunyi Khaleel na rike da hannunta sai kawai aka bata tray da scissors akai jama’a ma taruwa awajen harda patient, CMac yace “Ma please”Khaleel yasaki hannunta da idanu yace mata tabude looking confuse tadauki scissor da ake bata ta yanke ribbon din aka shiga sabon ward din da gadaje daban daban keciki ga machines, devices, har chairs komi sabi da laptops and desktop, an rubuta renovated by Hawwa in some space haka, ana gama shigowa kawai sai Cmac yace “adakata akwai statement da ake fadi honor who honors you” sai kawai yafara tafi yana kallon Hawwa da Khaleel yace “Happy birthday day to you” haba kowa yadauki wakan ana kallon Hawwa ana clapping akace “Happy birthday Dear Mrs Hawwa, Happy Birthday to youuu” dasauri Hawwa takalli Khaleel dake mata murmushi sosai shima yana clapping yana singing dasu for a moment Hawwa was confuse saikuma dasauri tafito wayanta daga wallet ta taba tana kallon todays date no wonder taga banks nata sun mata message but bata duba ba, today is her birthday, daidai lokacin sukace. “Happy birthday Mrs Ibrahim Khaleel, hip hip hop hip” akace “hurray” Cmac yakarbi flowers da aka kawomai yace “Ma thank you for what you did to our hospital, thank you for the donation, we will never forget this, komi na dakin nan is embedded da name naki duk wanda yazo dakin nan kinada ladansa, there’s no better way to celebrate birthday than this Ma, thank you Ma’am and thank you Sir, our entire hospital is saying what” jama’a akace “Thank you Mrs Hawwa”sauran Doctors sukai shouting “once again Happy Birthday Ma” akai tafi Hawwa tai shiru tana kallon Khaleel dake mata murmushi sosai shima yana clapping yana kallonta with so much admiration and love zuciyan Hawwa kawai taji ya tsumu tanajin goosebumps ajikinta, sai kawai Khaleel yakama hannunta sukaje O&G ward bangaren Female surgical, Ma’aikatan Khaleel su Salman na shigowa da envelops dayawa masu kiba, dawasu manya manyan bags na goodies, ya karbi envelops din yakama hannun Hawwa yasaka aciki murya chan ciki yace “share it’s your birthday” Khaleel yakalli mutanen ward din da duk suka mike anga goodies yace “it’s my wife birthday” Ya Allah zokaji yanda akema Hawwa addu’a suka shiga raba abubuwan bed by bed wata mata data bude envelop nata taga kudin dake ciki kawai saitazo tai kneeeling gaban Hawwa ta rungumeta tana kuka security Khaleel zasu dakatar da ita Hawwa ta hana, ahankali ta duka tace “Mama ya isa dena kuka, menene”?Matan tace “kinga y’ata raping nata akayi ciki yaki fita haihuwa yazo operation bamu da kosisi, da karo karo muka iya biyan kudin aiki, abinci saidai yan nan ward su tsammana, wannan kudi jinake kaman kin bani duniya da lahira Hajiya, Allah ya barki da mijinki, Allah yabaku yara masu tausayi da imani da kirki irinku” yan ward sukace Ameen, tace “nagode nagode nagode yallabai nagode nagode nagode” yarinyar itama tana kokarin saukowa daga gado dasauri Hawwa takamata tace “no karki tashi” yarinyar tace “nagode Anty kinji, ki taimakeni ni da Mamana” kuka Hawwa taji yazo mata idanunta sukai jaaa yarinyar is so small, ahankali Khaleel yazo kusada ita ganin tana shirin kuka and baiso tai kuka yace “do you want to help them”? Gyadama Khaleel kai tayi ahankali anatse yace “okay we will sponsor her treatment and help them financially agida” gyadamai kai Hawwa tayi yariketa sukai komi suka wuce ward uku sukaje sunsha addu’a sannan suka wuce mota suka tafi.Wani fancy restaurant sukaje da babu kowa aciki kaman yayi reserving gabaki daya an gyara anyi decoration na love kuma ba haske sosai wajen wani kujera yaje yajamata yana kallonta cikeda so wani iri kirjin Hawwa keyi, no one has ever done abubuwan da Khaleel yamata har samarin datayi a da like babu wanda ma yataba attempt din nan, all of them behave da ita kaman they’re doing her a favor na cewa ma suna sonta, kaman kartazo ta tsaya tana kallon Khaleel dake kallonta amman saitazo ta zauna ahankali daidai an kunna wani kalan wuta wajen yayi mahaukacin kyau saiga ma’aikatan sun taho rike da cake da aka kunna fireworks masu kyau ajiki anyi playing wakan happy birthday akazo aka ijiye agabanta ma’aikatan na waka tareda Khaleel yana mata murmushi sosai Hawwa na kallonshi ko kyafta idanu batayi, he should be angry! They had a serious fight this morning, bata gida tun safe, takawomai letter from court seeking for divorce but he’s celebrating her birthday with her smiling from cheek to cheek yana mata kallon that screams i love you! What is going on? Why is she feeling kaman tana nadaman kaishi court? Why is she feeling kaman bata kyauta ba? Why is she feeling bad all of a sudden?? Tun shekaran jiya yake cemata kartai girki they’re going on a date, from the look of things yadade yana planning all of this, no one has ever celebrated her like this! This is the best birthday of her entire life! Cikin very very beautiful voice Khaleel yana kallonta right in the eye yace “Happy birthday Hauwa’u!”.



