Mijin Marigayiya Page 53 Hausa Novel
Tun ranar da ta koma gida take lissafi, duk da dai tana jini a lokacin amma dai sai da ta lissafa jini uku, kuma jiya ne ranar da ta fita daga jini na uku bayan rabuwarsu da Mustafa.Tana zaune a gefen karamin gadonta wanda shine dai gadonta tun kafin ta auri Mustapha, ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana tunanin yanda rayuwarta zata cigaba; tabbas ta ji dadin rabuwa da Mustapha, bata yi nadama ba kuma ba zata koma ba. Domin ko babu komai yanzu ne ta tabbatar tana cikin nutsuwa. Duk wani abu na kulawa da Hammad yake bukata zata iya yi masa don haka ba zama ta nemi Mustaphan da maganar Hammad din ba saboda ma kada yace ta bashi yaronsa. Fatan ta daya Allah ya tabbatar mata da alkahiri a cikin rayuwarta ta nan gaba; duk da bata tunanin akwai namijin da zata sake aure. Ba zata yarda a sake yi mata yanda Mustapha yai mata ba kuma bata fatan ta zama dalilin da zai saka wani namijin ya mayar da matarsa kamar yanda Mustapha ya mayar da ita bayan ya kara aure.A hankali ta mike ta fito daga dakin. Ta ji dadi da ta sami Baffa da Mommy a parlor suna zaune suna cin abinci. Bayan ta gaishesu ta dubi Baffa tace ‘Baffa ian so a debo min kayana na gidansu Hammad.’Ya ajiye cokalinsa yace ‘Ikon Allah, bai nemeki ba kenan?’‘Eh Baffa, duk da ma ko ya neme nin ba zan koma ba. Jiya ne na gama iddata ka ga auren ma ya kare kenan.’‘Hakane, Allah ya sa haka ne ya fiye muku alkhairi gaba dayanku. Gobe sai kaninki ya shirya suje a kwaso miki kayan, kiyi masa bayanin abubuwan da zasu kwaso.’‘To Baffa.’Mommy tace ‘To ya za ayi da Hammad? Ai dai ya kamata ayi magana da Mustaphan ya dinga turo abinda za a kula masa da yaron ko?’Tace ‘Eh bamu dai yi magana da shi ba, amma da bari nayi sai zai shiga makaranta tukunna.’Baffa yace ‘A’a tun yanzu zai dauki nauyin dan sa, ni zan nemeshi in sha Allahu.’Mommy tace ‘Hakane kam, ba sai daga baya ba azo ana sa toka sa katsi.’Suka karasa hirarrakinsu sanna Khadeeja tayi musu sallama ta tafi office.……….A mota suke tafe yana tukasu, zai sauke Naja a wajen aikinta sannan ya wuce. Wayarsace ta fara ringing, kusan a lokaci guda suka kalli screen din wayar “Babe” shine sunan da yayi saving lambar Khadeeja da shi tun kafin aurensu kuma rabuwarsu ma bata saka ya goge ba. To me ya manatar da shi Khadeeja ma da bai ko da kirawota a waya ba tun bayan dawowarsa daga aikin Hajji? Ko da yake ba mantawa yayi ba jira yake ta kirawoshi ta bashi hakuri idan ba haka ba ma ya kyaleta ta dandana zawarcin daga baya ya koma a sake daura musu aure idan ta gane shayi ruwa ne. to menene take kiransa yanzun? Ko har zawarcin ya isheta ne? Watakila kuma ta ga taba daf da gama idda ne bai nemeta ba shine ita take nemansa ya zo a daidaita.Ya dauki wayar ya amsa sannan ya kara a kunnensa a daidai lokacin da ya kaucewa hada ido da Naja wadda take ta faman binshi da kallo saboda ta san lambar wacece yayi saving da sunan Babe.Babu wata alamar nadama ko kuma damuwa a muryarta, cike da walwalarta suka gaisa kamar babu wani abu na rashin dadi da ya taba hadasu. Bayan sun gaisa tace ‘Na gama idda jiya, so in sha Allahu idan babu damuwa gobe zan turo Ahmada zasu zo su debar min kaya na. kayan da suke bedroom din kawai za a dauka tunda dama duk na sabon gida ne ka saka, amma akwai food flasks dina a kitchen guda uku da kuma tea flask da zasu hado min da su shikenan. Ina fatan babu wata damuwa.’Sai da ya bude baki da niyyar bata amsa sannan ya gane yawun bakinsa ya riga ya kafe, ya kifta ido ya dan lalubo yawun bakin nasa sannan ya kalli Naja wadda take ta faman binsa da kallo kamar wata mayunwaciyar kura a yayin da ta hango nama yace ‘Ehhm, babu matsala. Um kin gama idda kenan?’‘Eh, na gama jini uku a jiya. Idan ma an hada da jinin barin da nayi jini hudu kenan duka da shi kwana biyu yayi ya dauke tun kafin sakin.’‘Oh hakane, Alah ya kai mu, sai sun zo din.’ Ya amsa.‘Da yake ranar aiki ce zasu zo da wuri domin su sameka a gidan in sha Allahu.’ Ta fada sannan tayi masa sallama ta ajiye wayarta.Ya mayar da tashi wayar ya ajiye a inda ya dauka ya mayar da hankalinsa ga hanya.Naja wadda take ta kallonsa tana jiran ya bata labarin abinda aka fada wayar ta gaji da kallonsa kuma bai yi alamar zai yi magana ba tace ‘Maman Hammad ce?’A gajarce yace ‘Eh.’Ba iya wannan amsar take son ni ba don haka tace ‘Wai menene?’Cikin yanayi na kosawa yace ‘Ta gama idda ne take so gobe da safe za a zo a kwasar mata kayanta.’Ta gyara zama ta bata rai tana cewa ‘Ai na zata furnitures din naka ne?’A fusace yace ‘Eh, iya nata za a kwasar mata ai ko akwai naki a ciki ne kuma.’Ta tabe baki tace ‘A’a, me yayi zafi.’Daga haka har suka karasa ya sauketa babu wanda ya sake magana.Duk yanda ya so ya mayar da hankali a kan aikinsa hakan bai samu ba; zai iya cewa baya nadamar rabuwa da Khadeeja amma tabbas yau da ta gaya masa ta gama idda jikinsa yayi sanyi. Zai yi kewarta, kuma yaba ji a jikinsa kamar a gutsure wata tsoka daga jikinsa.Bai ma taba tunanin zai yi kewar Khadeeja haka ba amma gashi kayanta kawai aka ce za a kwasa amma ya ji babu dadi. Bai dade da shiga office din ba ya lalubo wayarsa ya danna mata kira, kamar dazu yanzu ma muryarta cike take da walwala. Sosai ya kasa kunne yana kokarin ko gano wata alama ta damuwa a muryarta amma ji yake kamar ma an karawa muryarta zaki.Bayan ta amsa sallamarsa tace ‘Um kayi mantuwa ne?’Kamar wanda aka farkar daga barci yace ‘No. Umm! Hammad fa? Ya kamata ya dawo cikin ‘yan uwanasa ai ko?’A nutse tace ‘Eh haka ne, amma ka ga bai karasa shekaru hudu ba ma. Ina ganin nan da zuwa ya gama primary in sha Allahu sai ya dawo cikin ‘yan uwansa tunda tabbasa ni na san kula da yaro akwai wahala, musamman da yake ka ga Antinsu ba zama take ba tana aikinta. Ina ganin ka bar min shi duk wani abu da yake bukata in sha Allahu zan sanar maka, idan ya iya kula da kansa sai ya dawo gida.’So yake ya ce mata hakan ba zai yiwu ba ko don ma ya bata mata rai, amma ya kasa. Tabbas yana son ganin yaronsa a kusa da shi cikin ‘yanuwansa amma kuma idan ya karbeshi baya jin Naja zata iya hadawa da shi ta rike, don yanzun ma kullum cikin korafi take a kan yara suna gajiyar da ita. Gara ma ya bari ta rike shi in Allah yayi da ragowar zaman sa koma tare. ‘Um hakane, to babu damuwa. Sai goben kenan.’‘Ok, Allah ya kai mu goben.’……….Bata taba tsammanin Mustapha zai bar mata Hammad da sauki ba, don haka ma da yayi saurin amincewa da maganarta sai ta ji wani dadi marar misaltuwa; domin ta hango wahalar da zai sha idan ya koma gidan; zama zai yi kamar maraya. Tunda su Shukra su hudu ne, Rukayya kuma uwarta tana gidan sai shi kadai wanda ba shi da uwa bashi da dan uwa a gidan.A hankali ta mayar da wayar tata ta ajiye a kan teburinta. Ta sunkuyar da kanta ta share kwallar da ta taru a kwarmin idonta sannan ta zuba fuskarta a tafukan hannunta; ta tuno lokacin da suna soyayya da Mustapha kafin suyi aure. Wai ina soyayyar nan ta tafi ne? ya barta ita kadai tana ta dakon soyayyarsa har tsawon shekaru takwas?PAGE 221MIJIN MARIGAYIYAA Hausa Novel by Sakina Yazid (Innar su Amal)Tabbas ta sha wahala a gidan Mustapha; ba wai wahalar jiki ba don wahalar jiki ta san abinda ta yi bai wuce abinda matar aure zata yi ba. Sai dai wahalar zuciya da ta sha; kulawa da tausaya tare da kauna da zuciyarta take bukata daga wajen Mustapha sune bata samu ba. Ko su din ma ta hakura da su tana zama haka tunda ko babu komai tana kallonsa a matsayin mijinta kuma suna kwana tare. Amma daga lokacin da ya auro wata kuma ya ke bata kulawa da kauna wanda ita ya kasa bata daga lokacin ta yanke kauna daga zaman gidan Mustapha.Ba zata ce bata jin zafin rabuwa da shi ba domin tabbas ta san ko babu kauna akwai sabo, amma tabbas ba zata sake komawa gidan Mustapha ba. Domin tayi sujjada ta roki Allah kada ya sake hadata zaman aure da Mustapha. Da farko ta fara jin haushnsa amma daga baya sai taga jin haushin babu wani amfani; ko babu komai dole ta yiwa Hammad kara ta girmama mahaifinsa.Ta sake share kwallar da ta taru a kwarmin idonta, ta kalli ruwan hawayen da ta lakata a hannun nata; to kukan me take a halin yanzu? Ta zata ta gama kuka a kan Mustapha. Tayi murmushi ta sake goge kwallarta; ta san ba zata iya goge Mustapha daga cikin tarihin rayuwarta ba amma tabbas bata fatan sake rayuwa irin wadda tayi a gidansa. Ta goge fuskarta ta fice ta nufi cikin studio inda zata gabatar da labarai…….
