Hausa novels

Halysaah Page 11 By Khaleesat Haydar

Tun da gari ya waye Khaleesat ta kira Safiyyah tace mata bazata shigo school ba don tana son tayi bacci, Safiyyah tasan sarai bata yi baccin kirki ba kenan daren jiya, har mamakin yanda Khaleesat ta iya saka abu a rai ya dameta take, Safiyyah tace “Shikenan kawata, after our classes zan zo ko da yamma ne in sha Allah” a hankali Khaleesat tace “To Allah ya kai mu, Nagode” Daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar ta koma ta kwanta. Wajen karfe hudu na yamma Khaleesat ta tashi daga baccin da take, bandaki ta shiga ta wanke baki sannan tayi wanka ta dauro alwala ta fito, tun wayewar gari babu abinda ta ci har zuwa sannan, rabonta da abincin kirki zae yi kwana uku yau tun dai faruwar incident din few days ago, bayan ta idar da sallah ta shirya cikin kaya marasu nauyi ta fito parlor ta tafi kitchen ta hada shayi kawai sannan ta koma dakinta, laptop dinta ta jawo ta kunna zata saka movie ko zata ɗan samu nutsuwar abubuwan dake damun ta a rai ta hanyar kallon film, daga karshe ma ta fasa kallon ta dauko takardunta ta fara karatu, nan ma taji bata fahimtar komai a karatun, rufe takardan tayi ta kwantar da kanta gefen gado ta lumshe ido with different thoughts running her mind, it’s not as if she is disturb don Abdul bai daga kiranta ba ko bai kirata ba, kawai dai bata ma san abinda ke damunta bane in particular, bayan lokaci me tsawo ta sauke ajiyar zuciya ta bude idonta ta jawo wayarta ta bude WhatsApp, status taga Abdul yayi updating few hours ago, ta bude hoton da yasa taga har ya ma koma Nigeria cause a field din kwallo yayi hoton da abokansa dukkansu sanye da jersey, ko kadan bata yi mamakin komawarsa Nigeria ba don zai ma iya abinda yafi hakan, da taji shiru har kwana uku dama ta zargi ya koma, dai dai nan taji an bude dakin that is opposite her’s, sosai gabanta ya fadi don tun ranan sae yau Housemate din nata ya zo gidan, ta kalli agogon wayarta taga karfe biyar har ya gota, ta ajiye wayar ta dago kanta, tana ta zaune har bayan 15 mins da shigarsa daki sai kuma ta mike tsaye tana jin jikinta ba karfi ta dau gyalenta tana tafiya a hankali ta nufi kofarta ta bude ta fito corridor, sai kallon kofar dakin nasa take gabanta na faduwa, ta rasa courage din karasawa bakin kofar, she stood der for some minutes daga karshe ta lumshe ido ta bude tana tafiya slowly ta isa bakin kofar nasa ta tsaya, ta kai hannu tayi knocking a hankali kamar tana tsoron kofar, komawa gefe tayi kamar mara gaskiya waiting for his response, jin shiru bai amsa ba ta sake knocking din a hankali, ta jira for like a minute again taga dai ba a amsa ba, babu abinda yayi crossing mind dinta sai ko yana bacci ne, but bacci da yamma haka? handle din kofar ta kai hannu gently without thinking twice ta bude kofar tana kallon cikin dakin with throbbing heart, a edge din gadon dakin ta gansa a duke yana operating laptop dinsa da alamar abinda bai gama ba ranan da ya bar gidan yake karasawa, ya daga kai ya kalleta sai kuma ya ci gaba da abinda yake yi, she felt really really bad, ashe yana ma jin tana knocking din, da tasan yana ji ya kyaleta da bazata fara bude kofar dakin nasa ba, ya mike tsaye yace “Good evening Halysaah” Taki amsawa kuma taki yarda ta kallesa, da kyar tace “Dama kana ji kaki amsawa?” Har muryarta ya fara rawa, ya ɗan bude ido yace “To na sani ko saurayinki ne Halysaah?” Nan da nan hawaye ya cika idonta ta juya ta bar bakin kofar ta kullo masa dakin ta koma nata, dukawa yayi ya ci gaba da abinda yake yi a laptop, tana komawa daki ta fara kukan da bata san dalilinsa ba, she felt really hurt kuma tayi da ta sanin zuwa dakin nasa, tana nan a yanda take har shidda saura sannan taji yayi knocking kofar dakinta gently, daga kai tayi tana kallon kofar sai kuma ta hade rai, lkci daya ya bude kofar tare da sallama, sai dai daga nan bakin kofar ya tsaya yana kallonta yace “I was trying to finish a power point Housemate, how are you doing?” Ta sauke idonta a takaice tace “It’s fine” Yace “Baki je makaranta ba yau?” Ta gyada masa kai looking toward a different direction, yace “Why?” A takaice tace “Ba komai” Yace “Ok, hope everything is okay?” Sai a sannan ta daga kai ta kallesa sai kuma ta dauke kai don kar ma ta fara kukan dake taruwa idonta, bayan like 10 seconds yace “Saurayin da ke maki fada a waya ne guy din nan ko?” Ta kasa cewa komai at first, sai kuma muryarta na rawa tace “Kayi hakuri da abinda ya faru” Ya ɗan buda ido yace “No it’s fine Halysaah, ai ba ma abinda ya faru, but where did you know him from?” Tayi shiru ta kasa cewa komai tana share hawayen idonta, yace “I am intruding ko?” Ta girgiza masa kai kawai, yace “Ohk can we talk if you are comfortable Halysaah” She kept mute Kamar me nazari, can kuma a hankali tace “Ohk” yace “Then meet me at the parlor” Daga haka ya juya ya fita, ko da Khaleesat ta fito parlon bata tarda sa ba a ciki, ta zauna kan kujeran parlon tunani iri iri na yawo a kanta har ta rame a kwana ukun nan, bayan some minutes sae gashi ya fito daga kitchen with a cup of coffee, ya karaso cikin parlon ya zauna yana kallonta yace “You look pale Housemate, are you okay? Ko ya maki wani abun ne?” Khaleesat ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta girgiza masa kai a hankali tace “He left immediately u left too” Yace “Oh really? That’s weird” Ita dai tayi shiru, ya ɗan yi murmushi ya ajiye coffee din hannunsa yace “Amma baki ci abinci ba” Nan ma tayi shiru tana kallonsa, yace “Naga kamar its been a while da kika yi girki a kitchen, so me kike ci a gidan?” Ta sauke idonta, he could see tana cikin damuwa sosai, yace “Tun ranan da ya tafi bai dawo ba kenan?” Tace “Um” Ya kalli agogon wrist dinsa yace “Do u mind me taking u out for dinner?” Kallonsa Khaleesat take babu ko kiftawa kuma bata ce komai ba, ya mike yace “Get ready, let me get my car key” Yana fadin haka ya mike ya tafi dakinsa ta bi sa da ido, Khaleesat ta fi minti uku zaune parlon tana contemplating on weather to go out with him or not, what if Abdul bai bar kasan ba kawai old picture yayi uploading a status dinsa? The thought of this sent her quivers all over, Tana cikin wannan tunanin sai gashi ya fito daga dakinsa, yana shigowa parlor ta mike ba tare da ta bari sun hada ido ba ta wuce dakinta, canza kaya tayi ta dau veil dinta ta yafa sannan ta zauna gefen gado tana tunane tunane iri iri, bayan 15 mins da shigowarta dakin taji yayi knocking yace “Baki shirya ba Halysaah?” A hankali ta mike ta dau wayarta ta nufi kofa ta bude ta fita, ta samesa har ya koma parlor yana jiranta, tana isowa parlon yana kallonta yace “Where u contemplating inside the room?” Bata san sanda ta dan yi murmushi ba bata dai ce masa komai ba, yace “To mu je, this is after 6 already” Shi ya fara nufar kofar fita living room din sannan ta bi bayansa, yana tsaye bakin kofar bayan ya fita ya jira har ta fito daga parlon sannan ya kulle kofar yana kallonta yace “Why this much Deodorant Housemate?” Ta wani kallesa tace “Ni nace maka na sa?” Bai bata amsa ba ya nufi garage tana biye da shi a hankali, ita dai bata sa turare yanzu ba sai tun wanda ta saka da tayi wanka daxu, sai in ko kamshin kayanta yaji amma ba dai ita ba, bude mata motar yayi tun bata karaso ba sannan ya zaga ya shiga motar yana jiranta, bayan ta shiga suka bar Garage din, wani babban restaurant sananne ya kai ta a Baltimore, bayan yayi parking ta dinga kallon restaurant din da ta ga an rubuta The Capital Grille, sai da ya fara sauka daga motar sannan ita ma ta sauka, tana biye da shi suka shiga ciki, shi yayi offering dinta seat bayan ta zauna shi ma ya zauna ya dau food Menu dake saman table yana nuna mata na kusa da ita yace “Ki duba abinda za ki ci” Ita dai bata dau Menu din ba, yace “I am talking Halysaah” Without looking at him tace “Ko ma meye zan ci” Yace “Ohk” Tana danna wayarta yayi masu ordering abincin, mamaki Khaleesat ta dinga yi ganin amount of different type of foods that he ordered kamar za ayi karamin feast a wajen, abinci kuma masu tsadan gaske, da yawa cikin abincin da aka kawo masu sai a ranan ta fara ganinsu, duk da dai abincin turawa ne, drink ma ya kusa kala hudu ya siya masu, ta daga kai ta kallesa a karo na farko tace “Su waye za su cinye duk wannan?” Orange Crush ya dauka yana sha bai ce mata komai ba, after a while ganin bata fara cin abincin ba shi kuma sai cin abinda zai ci yake ya daga kai ya kalleta yace “Ko babu abinda kike so a nan ne?” A hankali ta dau Tacos daya, shi ko ya ci gaba da cin abincinsa, ƙasa ƙasa Khaleesat take kallonsa, ta lura yanda baya wasa da bacci haka baya wasa da abinci, because he didn’t even mind she was in front of him abincinsa kawai yake ci sosai, ganin ko kallonta baya yi ta abincin gabansa kawai yake yasa ta ɗan saki jiki kadan ta fara cin abincin duk da ba sosai ba, ta ci iya abinda zata iya ci ta dau drink tana sha a hankali, sai a sannan ya daga kai ya kalleta after almost finishing his food yace “Ko dai a maki packaging abincin ki ci a gida, naga kamar kina kunyan ki ci abinci cikin mutane, or should i give u privacy?” Tana kallonsa a hankali tace “Privacy in an open restaurant? Ni nace ina kunyan in ci abincin?” Ya ɗan bude ido yace “Naga u ate just the Tacos bayan ga abinci da yawa a gabanki” Ta sauke idonta tace “Nafi son sa ne” Yana goge lips dinsa da tissue alamar ya koshi yace “Ohk, so now can i talk to you?” Shiru tayi na few seconds, sai kuma ta kallesa a hankali tace “Ohk” Ya karasa shanye drink dinsa yace “A nan America kika hadu da saurayin naki ko a Nigeria?” Khaleesat was silent, sai kuma ta sauke idonta tace “Nigeria” Yace “Ohk, but me kike tunanin yake janyo maku matsala tsakaninku?” Ta girgiza kai tace “Nima ban sani ba” Yace “Saboda ke ya taho nan daga Nigeria or he have a business here?” Ta gyada masa kai tace “Saboda ni ya zo” ya gyara zama yace “Kinga yana sonki kenan, sosai ma kuwa yake sonki, he left everything he was doing and came over just to see you, in na fahimta bai son kiyi sharing apartment da namiji a kasar nan ko?” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana wasa da gefen mayafinta, yace “Sure… yana da gaskiyarsa, don ko ni bazan bar budurwata tayi communal living ba” Khaleesat ta daga kai ta kallesa, Yace “Yanzu dai kiyi kokari ki basa hakuri ku dai daita kanku, ni kuma i will think of another alternative for peace to reign between u and ur boyfriend, sannan shawaran da zan baki shine try all possible best ki dinga nuna masa abinda baza ki yi tolerating ba tun kafin kuyi aure, ya kamata ace akwai mutual understanding tsakanin ku, he look cool though kawai yana da hot temper ne and i notice insecurity na daya daga cikin matsalarku da shi, but you can definitely change him gradually Halysaah, so last maganar da zan maki ina ga ba abinda ya shafeni bane, kawai dai zan tunatar da ke Do’s and don’t din addininki ta bangaren relationship tsakanin mace da namiji” Khaleesat dai sauraronsa kawai take without looking at him, kuma taki ce masa komai tana kokarin fahimtar abinda zancensa na karshe ke nufi, shirun da taji yayi yasa ta daga manyan idanuwanta ta kallesa, at the same time ta kalli wa enda yake kallo a cikin restaurant din, 3 Guys ne suka shigo restaurant din gaba dayansu yan Africa, amma daya ne ɗan Nigeria a cikin su, guys din da ba yan Nigeria ba suka daga ma Housemate din nata hannu alamar girmamawa, and he waved back at them with smile on his face, Khaleesat ta dinga kallon daya mutumin da ya nufo su don ta ma ganesa, su sauran biyun kuma suka tafi yin abinda ya kawo su restaurant din, Mutumin na isowa kusa da table dinsu yana kallon Housemate dinta yace “Done with the power point?” Tuni kamshin turarensa ya cika wajen, Housemate dinta ya daga kai ya kallesa yace “Yau kuma har da kai za a ci abinci a nan kenan….” Yace “Not at all, i am getting some Steak for legend, meanwhile ashe kana nan” Housemate dinta yace “Yea, i came with my friend for Dinner” Khaleesat dai danna wayarta kawai take don mutumin yi yayi kamar bai san da Allah yayi ruwanta a wajen ba, ita ma ko kallon direction dinsa bata yi ba, Housemate dinta ya nuna masa bill dinsu yace “Get the bill cleared” juyawa mutumin yayi ya bar wajen yana tafiya irin ta ƙasaita, Khaleesat ta bi sa da kallon gefen ido, he was wearing a Jogger and a white Polo, ta dai ci gaba da danna wayarta, muryar Housemate dinta taji yace “That’s my gee Halysaah, we share the same name with him….” Khaleesat ta daga kai without interest tace “Ohk” Yace “Sorry about his attitude, he isn’t friendly, but i promise you he is good” Khaleesat tace “Likewise myself” Murmushi housemate dinta yayi sannan yayi excusing kansa ya mike ya nufi gun wanda ya kira da gee dinsa, daga inda take zaune taji mutumin na cewa “Kai kuma ina ka samo waccan yarinyar dake zaune kamar gunki bata iya gaisuwa ba, duk wani harkar raini ka iya ja ma mutane, that was how the other day da ka kawota karfe ukun dare a mota ta dinga kallon mutane kamar statue da aka dasa a gaban motar” Definitely yayi maganar ne ta yanda zata ji, Housemate dinta dake kallonsa yace “Ban gane bata iya gaisuwa ba, ba kai ka sameta a wajen ba, kayi mata magana ne kaga bata amsa maka ba?” Maimakon ya ba Housemate dinta amsar abinda yace sai taji yace “Na kai Legend gun Veterinary daxu” Taji Housemate dinta yace “Hope he is better now?” Mutumin yace “Let me get the bill cleared mu tafi gidan Mike yanxu….” Housemate dinta yace “No kayi tafiyarka zan yi dropping frnd dina first” Taji mutumin yace “Like seriously kai ko wani irresponsible being sae kace friend dinka, why are you stooping your self soo low Jay” Taji Housemate dinta yace “C’mon Ajay, come off it, this is so harsh…” Mutumin da ya kira da Ajay ya tafi ya bar sa gun a tsaye, Dawowa Housemate din nata yayi inda take, tuni ta mike tana gyara gyalenta without looking at him tace “Thanks for the dinner, kawata na kirana zan tafi gida” Housemate dinta yace “Ke kika kawo kanki da za ki koma ke kadai?” Taki kallonsa tace “Ae naga ur responsible frnds are here, so let me get going” Yace “Halysaah” ta daga kai ta kallesa, yace “Jira ni inyi clearing bill dinmu in yi dropping dinki gida” Yana fadin haka daya daga masu aiki a restaurant din ya nufosa da ladabi ya sanar masa anyi clearing bill din su, ya bi A-jay da ya fita daga Restaurant din da kallo, wa enda suka shigo tare na biye da shi a baya. Khaleesat bata yarda ta hada ido da Housemate dinta ba har suka fito daga Restaurant din zuwa inda yayi parking motarsa, sai da ya shiga motar sannan ita ma ta shiga ta zauna tana danna wayarta, bai tada motar ba ya kalleta, speaking calmly yace “Hope you are not offended Halysaah?” Without looking at him tace “Offended at what?” Yace “I don’t really know” Ta kada baki tace “Ai ni ban yi kama da someone that isn’t responsible ba balle in zama Offended at what a random stranger spew out, out of his ignorance, shi dai da bashi da manner shi ne babban irresponsible being, ai da ya fada a gabana yaji abinda zan gaya masa” Housemate dinta ya bude baki yana kallonta da mamaki looking completely speechless, bai yi tunanin taji abinda Ajay din ya fada ba, bai kuma yi tunanin tana ma da baki haka ba, after few seconds yayi kasa da murya yace “Pls kiyi hakuri Halysaah, bana son wannan yasa ranki ya bace, i purposely brought you out to cheer you up and make you lively don naga kamar kina cikin damuwa, amma ba don a kara bata maki rai ba, plss ignore Ajay’s attitude, wani lkcn yana da problem i think today is one of those days” Khaleesat bata sake cewa komai ba but she is trying hard not to cry, ya ci sa’a ba yana tsaye gabanta ya fadi haka ba da tsaff zata mayar masa da baƙar magana dai dai da abinda ya gaya mata a wajen, Housemate dinta ya tada mota suka bar Restaurant din, hakuri ya dinga bata kamar shi ne yayi mata laifi har suka isa gida, direct dakinta kawai ta wuce, after like 40 mins ta fito wanka tana duba sleeping dress din da zata sa taji yayi knocking kofar dakinta, hijab din da tayi sallah ta dauka da sauri ta saka, bai bude kofar dakin ba har sai da taje ta bude tana kallonsa, yace “Sae da safe Halysaah, pls ki kwantar da hankalinki and get some rest, gobe kuma ki je school” ta sauke idonta bata ce komai ba, taji yace “Take care” Sai da ya juya ya bar wajen sannan ta daga kai ta bi sa da kallo cikin sanyin murya tace “Thank you so much, for…” Sai kuma tayi shiru, ya juya yace “For?” Ta langwabar da kai tace “The Dinner” Ya ɗan buda ido yace “My pleasure Halysaah” A hankali tace “But…. i don’t… know, ur name” Yace “Oh really, amma ranan da na fara zuwa gidan nan ai nayi introducing kaina sai dai in kin manta, I am Ahmad Jawwad Yusuf, my frnds call me Jayy” Kallonsa Khaleesat ta dinga yi without blinking, yace “Are you okay with that?” Ta sauke idonta tace “Alright, i really appreciate you” Ya sakar mata murmushi yace “See yah tomorrow” daga haka ya bar wajen ta bi sa da ido har ya fita daga gidan gaba daya sannan ta juya a hankali ta koma dakinta ta kulle kofar.*Make ur payment before the end of free pages, kar a ji shiru*07087865788✍🏻

Back to top button