Hausa novels

Ajiya A Duhu Book 1 Page 8 Complete Novel

*_Typing📲_* *_💞AJIYA A DUHU….💞_* *_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_**_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._*_My TikTok account 👇_*https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1*_Instagram👇🏻_*https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv*_Arewabooks_*Read My Book “AJIYA A DUHU” on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_🅿️➖0️⃣8️⃣______________Assalamu alaikum Ina Neman mutane 20 dazasuyi register da company 52u a karkashin link Dina akan $21 wato 35k a kudin mu na Nigeria account din zaibude a cikin 5-6 weeks idan account din yabude nikuma nayi alkawarin zanbiya mutum 20 dinnan salary 10k kowani mutum na tsawon wata 5 kunga riba biyu kenan kuka samu ga ribar kudin ku yadawo harda riba ga account din kun na 52u zanbude a wata na shida sai kudin ga kwasa duk kudin ku duk wata 💃🏽💃🏽💃🏽mai ra,ayi yamin maganahttps://chat.whatsapp.com/K0ECLn6O3WS1fnfCggOeu508083531881______________…….Shirun da tai na kusan minti biyu batare data amsashi ba ya sashi ɗan kallonta. Kanta tai saurin kaudawa tana mai ƙoƙarin haɗiye ɗacin daya mamayeta. Shima sai ya ɗauke kansa bai sake magana ba. Babu jimawa suka iso gaban gidan da take zuwa gyaran jikin, wanda yasani ne tuni saboda yanda take ma’abociyar zuwa gidan kusan duk ƙarshen wata. Jikinta har tsuma yake nason ta fita a motar, dan bata so ya sake mata wata magana amma sai taji motar a ɓame alamar ya saka luck. Dole ta ɗan dakata tana rumtse idanunta. Sai kuma ta juyo ta dubesa, ganin shima ita yake kallo ta maida kan ta duƙar. Murmushin ya sake saki kaɗan da ɗauke idanunsa a kanta cikin son basar da yanayin ke bashi a jikinsa. “Ki tayani murna?”. Batare data sake kallonsa ba ciki-ciki ta ce, “Tami?”. “Akan albishir ɗin da akai min yanzu a waya. Mutumin nan kusan shekara guda kenan muna son haɗa Bussines dashi amma ko ganinsa ya gagara a gareni. Amma yau kinji har zan samu ganinsa, nasan Daddy zaiji daɗi akan hakan shima matuƙa”. Karo na farko tai ɗan murmushi. Sai kuma ta ce, “ALLAH ya tabbatar da alkairi a haɗuwar taku to”. “Amin ya rabbi dear. Ammafa nasha wahala sosai. Mutumin ya riga yayi nisa ne matuƙa saboda yanda yake huɗɗa da manyan mutane na wajen ƙasar nan dama cikin gida Nigeria. Nasan dai bazaki rasa jin Mawaad ba”. “Ina dai ganin sunan Companyn a jikin buhunan shinkafa, ban sani ba ko sune ko kuma da banbanci”. “Yes sune. Dan yana harkar noma yanzu matuƙa a ƙasar nan. Kuma Kinga wannan harkar ma bai wani jima da farata ba. Amma da yake ALLAH ALLAH ne cikin ƙanƙanin lokaci nan ma yayi zarra.” “ALLAH sarki”. Kawai Maanal tace dan bataga ma’anar bata wannan labari ba ita kam da dam bata da alaƙa da shi. Cikin marairaicewa ta ce, “Yaya bara naje kada na makara Ammie tace zamu rakata anguwa”. Amsa mata yay da “Okay bari na barki ki wuce. Inata baki labarin abinda bai shafeki ba, haka nake buƙatar rayuwata Manaal, wato iyalinna su dinga sanin komaina dan su kasance masu min addu’a. Dan haka sai ki shirya, dan zaki dinga raba farinciki da mijinki hakama akasinsa idan ya gitta” ya ƙare maganar yana miƙa mata atm card ɗinsa. Kanta ta girgiza masa da sauri. “A’a yaya ga Ammie ta bani nata zanyi amfani da shi. Hararta ya ɗan yi da zare atm ɗin Ammien ya ajiye mata nasa a cinyarta. “Kiyi amfani da na mijinki, dan nike da hakkin hakan ba Ammie ba. Idan kin kammala ki kirani dan ba nisa zanyi ba”. Yanda ya tsatstsareta da ido yasa ta kasa magana. Dole ta buɗe motar ta fita dan shi in baiso wasa ba dole kaji shakkarsa. Bai bar wajen ba har saida yaga ta shige. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali da jingina jikinsa da kujera yana mai lumshe idanunsa. Ya jima a hakan dan yaci kusan mintuna biyar kafin ya tada motar yabar wajen yana mai danne abinda ke tsikarar zuciyarsa game da ita….. ★★★ Yanda Maanal ta samu tarba a ciki zai tabbatar maka akwai shaƙuwa da sanayya sosai tsakaninta da mai gyaran. Dan duk miskilancintan nan sai murmushi take da ɗan maidama mai gyaran hiranta dan tana mata tambaya ne akan Jos. Basu wani jima ba aka fara gyaran saboda tun jiya ta sanar mata. Kafin tazo ta haɗa komai. Gyara sosai jikinta ya sha. Ga turarruka kamar wata amarya. Hatta kanta da ƙafafunta zuwa farce an musu ƙal. Haka Maanal take akwai son gyara jiki, ƴar gayuce sosai da son kwalliya, sai dai yanzu yanayi yasata ɓarar da kwalliyar gefe gyaran jikinta da tsafta ne dai tana nan da abinta akoda yaushe. Sun gama a ƙurarren lokaci, dan har Ammie na kiranta a waya ma. A gurguje ta bata ta cire kuɗin aikinta tare da amso kayan ƙamshin data haɗa mata suka fito zata mata rakkiya. Turus taja ta tsaya da ganin motar Yaya Yazeed a ƙofar gidan, kafin ma ta samu abin faɗa ya buɗe mata gefensa alamar ta shigo. Ganin fuskarsa babu wasa sam yasa batai magana ba ta shiga kawai. Sallama sukai da mai gyaran bayan ta gaida shi ya amsa mata ciki-ciki yaja motar suka wuce. Shiru motar har sun ɗan yi nisa a tafiyar cikin ƙarfin hali ta ce, “Yaya dama baka wuceba ne?”. “Mi kika gani?”. Ya faɗa cikin wata irin kasalliyar murya data bata mamaki. Gashi yaƙi kallonta sam a yanzu. Itama sai kawai ta ce, “Ba komai”. Bai sake magana ba, itama tai shiru har suka iso gida. Sai da ya gama parking ta miƙa masa atm ɗin tana godiya. Kansa kawai ya ɗaga mata batare daya kalleta ba ko tankawa yanzu ma. Itama sai kawai ta buɗe motar tai ficewarta. Da Hajiya Yaya dake daga can ƙofar sashensu da wata baƙuwa suka haɗa ido, ganin irin kallon da suke mata yasa duk ta tsargu, amma sai ta dake ta nufesu badan taso ba, sai dan mahaifiyarta ta mata tarbiyya na girmama duk wanda ke gaba da ita. Sannan kodan Yaya Yazeed dake iya ƙoƙarin sa na girmama Ammie zata iya shanye komai daga mahaifiyarsa itama. “Tofa, kice agola kafi ɗan masu gida an dawo kenan?”. Matar da suke tare da Hajiya Yayan ta faɗa cikin yamutse fuska idonta akan Maanal dai-dai tana isowa inda suke. Wani harbawa zuciyarta tayi har tsakkiyar kanta. Ba wai yau ne karo na farko da aka fara kiranta da sunan AGOLA gidan ba, amma har yanzu ta gagara sabawa. A duk sanda aka kirata da shi kuma tana jin matuƙar ɗaci da zafi a ranta. Har takanyi yunkurin son barin gidan, sai dai yinƙurin nata baya zuwa ko’ina take komawa tai laƙwas saboda wasu dalilai. Hawayen da suka cika mata idanu ta haɗiye, tare da dai-daita kanta sannan ta ɗan risina fuskarta da murmushi ta ce, “Barka da gida Mamma. Aunty ina yini”. Kafin Hajiya Yaya ta amsa wadda ta kira da aunty ɗin ta sauri ta cafe zancen cikin masifa, “Oh kaji wani ɗan iskan gaisuwa wai barka da gida sai kace wasu sa’oinki?”. Cikin sake hasala Hajiya Yaya ta ce, “Kinga da yawa ai, idan batai iyayi ba ai bata cika jinin Asiya ba, Amma wai a haka Alhaji ke neman ƙaƙabama jinina ita”. “Humm kar kiga laifinsa wlhy Yaya, tunda uwarta ta shanyesa kina ganin shima Yazeed ɗin zasu barsa ne. Balle suna ganinsa shine gidan da uban gaba ɗaya”. ta faɗa tana mai ballama Maanal wata shegiyar harara. Tsamm Maanal ta miƙe kafin Hajiya Yaya ta bama ƙanwar tata amsa. Cikin ɗan sassarfa tabar wajen tana mai jin ɗaci da ciwo sosai a zuciyarta game da cin mutuncinsu ga Ammien ta. Tarasa mi Ammie ta tsare musu a gidan da su duka basa ƙaunarta… Shikam Yazeed tana fita ya kife kansa a saman steering yana mai cije bakinsa da masifar ƙarfi. Kai bazai yiwu ba, dolene ya zigirgiɗi Daddy azo ayita ta ƙare a bashi matarsa. Dan gaskiya yana cikin tashin hankali, da yasan ma abinda gyaran jikin nan zai zame masa yanzun nan daya hana yarinyar nan yinsa ko kuma yaƙi komawa ɗakkota. Ɗan buga glass ɗin saitinsa da akai da ɗan ƙarfi ya sashi ɗagowa. Sai da ya ɗan saisaita kansa kafin ya sauke glass ɗin. Da Hajiya Yaya yaci karo, ai da sauri ya janye idanunsa da sukai wani irin kaɗawar da duk mai hankali idan ya kallesa zai fahimci halin da yake ciki. Ita kanta Hajiya Yayan sai da taji wani iri a ranta, amma ta dake cikin masifa ta ce, “Yazeed miye haɗinka da waccan yarinyar? A ina ka ɗakkota?”. Ɗan gyaran muryarsa data koma can ƙasa yayi, kafin ya furta, “Mamma anan ƙofar gida ne mai napep ya ajiyeta shine nace ta shigo na ƙaraso ciki da ita. Wani abu ne ya faru?”. Wata hararar bana son rainin wayo ta balla masa. Kafin cikin masifarta ta furta, “Yazeed! Yazeed wlhy ka kiyayen, ni zaka maida sakarai ko….” “No Mamma ba hak….”Hannu ta ɗaga masa cikin tsawa, “Bana son ji, ka sameni ciki yanzun nan”. Tana gama faɗa ta juya ta bar wajen. Iska mai kauri ya furzar daga bakinsa tare da sake maida kansa jikin steering yana mai lumshe idanunsa. Yafi mintuna biyar a haka sannan ya buɗe motar ya fita yana mai saka glass a idanunsa domin ɓoye abinda ke cikinsu. A falo ya sami mahaifiyar tasa da ƴar uwarta. Cikin girmamawa ya gaida innar tasa dake wani binsa da kallon ƙurilla kamar mai son gano halin da yake a ciki batare data amsa masa gaisuwarsa ba ta ce, “Yazeed! Anya kuwa kana son nemawa mahaifiyarka mutunci damu ƴan uwanta a gidan nan. Wai kai bazaka bar batun yarinyar nan ba ne shin ko yaya kake nufi?”. Sai da ya ɗan haɗiye abinda ke masa yawo a maƙoshi sannan ya furta, “Aunty Please mun wuce maganar nan fa tuni. Dan ALLAH a barta kawai”. “Anƙi a bari ɗin dan ubanka. Yazeed ni dai kake son cigaba da tozartawa ko? Ni dai mahaifiyarka dana sha baƙar wahalar rainon ciki ka da naƙudar haihuwarka da shayar da kai. Asiya dai ta fini muhimmanci a wajenka ko? Shike nan kaje kayi duk abinda kake ganin dai-dai ne agareka. Amma ka sani ko mutuwa nayi kurwata bazata barka zaman aure da yarinyar can ba. Dan na riga na maka mata kamar yanda na faɗa maka. Garama ka shirya tun kafin takaimu da bakanta a cikin gidan nan. Amma bari shi Alhajin dake ɗaure maka ƙugu ya dawo gidan ina dai-dai dashi wlhy”. Kasa iya furta komai Yazeed yayi, sai wani irin haɗiyar zuciya yake acan ƙasan ransa dan mutum ne mai zuciyar tsiya dama. Haka suka cigaba da masa masifa bai iya sake cemusu komai ba har sai da ALLAH ya taimakesa Daddy yay kiran wayarsa sannan ya tashi ya fita domin amsawa. Daga haka bai koma wajen su ba ya gudu sashensa dan ya shirya gashi har yana neman makara…. ________ A ɓangaren Manaal bata sanarma Ammie komai ba. Sai ma ƴan uwanta ne da suka zagayeta suna yaba irin ƙyawun da gyaran yay mata. Daga haka Ammie ta korata dan ta shirya kada su makara. Saboda tasanta da nauyin shiri. Aiko bata kammala shirin ba sai da Ammie tai mata tsiya-tsiya. Faɗan Ammien yasa ta fito ɗauko da ɗan box ɗin da take ajiye kayan ƴan kunne da makamantansu ciki a hannu tana neman agogon da zata saka da zobe. Su Amal ne dake musu dariya suka amsa suna duba mata. Dai-dai fitowar Ammie tana faɗin, “K muje ai ba dole sai kinsa wani agogo can ba bana son shiririta”. Jin hakan ya sata miƙewa dan tasan kaɗan daga aikin Ammien ta maketa ma saboda bata ƙaunar jira, da sauri Shahidah da takamo hannunta ta ɗaura mata wanda ta zaro kalar silba kawai ta shiga ɗaura mata batare da su duka sun maida hankali akansa ba. Daga haka suka fice hannunta riƙe da ƴar bag ɗinta sai gwangwanin maltina data ɗauka saboda yunwan da take ji kasancewar bawani break ɗin kirki tayi ba ta fita gyaran jikin, yanzu kuma Ammie tace bazata zauna cin abinci ba aiba itace ta hanata ci ɗazun ba sai dai ta bari idan sunje gidan bikin taci. Itako tasan bazata taɓa iyawa ba cin abinci a gidan biki koda na wanda ta sani ne balle wannan, duk da kamar gidane can ɗin ma saboda alaƙar dake tsakanin mai gidan da uban amaryar mai matuƙar ƙarfi ce, ta wani gefen ma za’a iya cewa akwai zuminci. Koda yake su sai dai suyi kara saboda Ammie kawai amatsayinsu na ƴaƴanta………..✍️✨ZAFAFAN DAI ✨1 ƘALBIM (Mamu gee)2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)3 DUNIYAR MU (Huguma)4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)Book 1:-500Book 2:-1000Book 3:-1500Book 4:-20000022419171Access bankMaryam Sani GumiShaida:- 09033181070Kati MTN:- 09032345899Ƴan NIGER 🇮🇷 1000CF89825722Nousaiba Lawali Maradi Shaida:-09033181070*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Ajiya A Duhu Complete Novel Document Txt

Back to top button