Karfe A Wuta Chapter 31 By Ayshercool
Tunani ya fara yi, ko tana da aljanu ne.Ganin idan ya ƙyaleta, fashe-fashe za ta yi, ya sanya shi takawa ya riƙo hannunta, amma sai ƙoƙarin fizgewa take yi.Kasancewar ba ta yi masa wahalar ɗauka, ya sanya ya danƙota kamar kazar cikin akurki, aikuwa ta cigaba da fizge-fizge da ƙoƙarin ƙwacewa, falo ya shiga da ita, ya tattara hannayenta ya riƙe, hakan ya sanya ta kasa cigaba da ƙoƙarin ƙwacewar.”Meye haka ki ke yi? Kanki ɗaya kuwa?”Kallonta yake yi, har ta fara kuka, shi bai ma san me yayi mata ta aikata hakan ba.”Me nayi miki ki ke jifana?”Cikin takaici ta kalleshi ta ce “Meye ma baka yi mini ba, ni bani da wani amfani a wurinka, bani da ikon roƙon alfarmarka, komai ma yi mini ka ke yi, ko yayi mini daɗi ko akasin haka, ba ka tausaya mini dama ka tsane ni, so kake yi na mutu ka huta”.”To yanzu kuma me nayi miki?””Wuƙa fa ka ɗauka zaka fita, idan aka yi maka wani abun ko ka yi wani laifin nikaɗai nake fama, sai su yaya walid da suke taimaka mini, amma kai gaba ɗaya baka tausayina, ba ka tausayin maraicina saboda da ma ba so na ka ke yi ba. Kodayeke ba laifinka bane, tun da sama ta ka aka aura maka ni, bayan an gama ɓata ni a wurinka. Ko hira ba ka yi da ni, in tayi maka magana kayi mini shiru, idan aka ga na mutu kai ne, sai ma na rubuta na bar wasiyya, idan na mutu kai ka ƙarasa ni da takaici”Yayi shiru ta din ga yi, tana faɗa tana kuka, sai da ta gama tsaf, sannan ya miƙe ya ce “Ki kula da abun da na gaya miki, kar ki fita kar ki bar gida a buɗe, idan na yi dare ki kwanta zan hauro”.Ta ɗaga idanunta da suka yi ja ta ce “Sai ka fita ko?””Ai na ce idan ba zaki iya ba, ki koma gidanku ko ban gaya miki ba?” Tayi shiru ranta na yi mata wani irin zafi, ya fita ya kwashe kwanukan da ta watso waje ya fice.Unguwar su ya nufa, faɗa ya haɗa ɗan unguwarsu, da ɗan unguwar su madaki, yaron ya kwaso ‘yan daba yaran madaki, sun shiga unguwar su Al’amin su na ta faɗace-faɗace.Yana zuwa chamber su, ya ɗaukko wuƙaƙensa, ya fita, sai dai da ya je, yaran suka din ga darewa, saboda wanda suka taɓa karo da shi, sun san irin ƙarfin da Allah ya yi masa.Wani yaron madaki ne, da yake ji da tashen balaga da rashin mutunci, ya sha gaban Al’amin yayi yana zage-zage yana ƙoƙarin saran Al’amin.Ya jefar da wuƙarsa, ya nufi yaron, wanda suka san Al’amin suka din ga ce masa ya gudu, kar ya bari ya kama shi, amma kasancewar ya yi wa wiwinsa haɗin kauri da wata ƙwaya da suke yi wa laƙabi da ‘yar fara, ya sanya yake jin kansa a sama, ko barikin sojoji zai iya shiga yayi rashin mutunci.Duk iya ƙoƙarin sa ya kasa saran Al’amin, saboda yadda yake da zafin nama, wurin kare saran, wanda idan ba professional athlete ne ba, babu lallai ya iya.Ya shammaci yaron, ya soka masa iraƙi a cinyarsa, a take ya kurma wani uban ihu, liti ne ya karyo kwanar, riƙe da nasa makamin yana ɗigar da jini, “Mai zamani yi haƙuri, kar ka karya yaron nan” sai dai bai rufe bakinsa ba, ya ga Al’amin ya fito da dogon harshensa, ya lashi laɓɓansa na ƙasa da su, idan har yayi haka sai aiwatar da muguntar da yayi niyya, kan liti yayi wani yinƙuri ya karya ƙafar yaron ya watsar da shi yana kururuwa.”Mai zamani, yanzu zaka sake janyo mana faɗa, madaki zai ce sai ya ɗauki fansa, da baka karya shi ba”Ya ɗago jajayen idanunsa a slow, yayi wa liti wani irin kallo ya ce “Ya zo ya ɗauki fansar a kaina, idan ya isa” ya wulwula iraƙinsa, ya cafe ya yi gaba.Kai tsaye gidan su ya tafi, da wannan wuƙar tana ɗigar da jinin da ya soki yaron nan.Yana shiga ya wuce falo, sai ganinsa suka yi a tsaye a kansu da makami tsirarsa.Salati suka fara yi da kururuwa, ya kalle su ɗaya bayan ɗaya, “Me ya kai ku gidana?” Yayi maganar yana kallon shahida.Cikin tashin hankali ta ce “Abbu ne ya ce Mu je mu duba matarka”.”Shi ya ce ku je ku gaya mata cewar kangarewa ce ta sanya aka yi aurena da ita? Ku je ku ci zarafinta?”Cikin tashin hankali shahida ta ce “Ba ni na faɗa ba Amira ce wallahi”.Rahila kuwa hankalinta ya dugunzuma, ta ce “Ka yi wa Allah da ma’aikinsa ka yi haƙuri, dan Allah kar ka yi musu wani abu”Ai kamar ta tunzura shi, ya saka wuƙa a wuyan Amira, “Ya zama na farko ya zama na ƙarshe, ayi duk cin kashin da za ayi a kaina, ban da ‘yar mutane da ki ka haɗa kai ku ka cutar, idan aka kuma zan yi ɓarna, wallahi sai na saka wa mutum ƙarfe”Shahida ce ta iya cewa “In sha Allah ba za a sake ba” yayi ƙwafa ya fita.”Amira kin ga abun da ki ka ja mana ko? Da ya illatamu, da kin cuce mu”Amira kam kasa magana tayi, sai dafe ƙirji tana hakin tsoro.Al’amin wuni yayi ranar, yana partrol da yaransa a unguwar, saboda kar yaran madaki su zo su afkawa wanda bai ji ba bai gani ba.Cikin ikon Allah, har dare yaran madakin ba su sake shiga unguwar su Al’amin ba, duk da sun yi artabu sosai da wasu, dan sai da aka yi masa rauni a cikinsa, ya kama hanyar tafiya gida.Jauhar na falo tana karatun exam, duk da sun kusa kammala jarrabawa.Ta katangar ya diro kamar ɓarawo,s an samu cigaba, yanzu idan ya ga dama ya kan yi salama.Sallamarsa kawai ta amsa, ba ta sake kula shi ba, ya wuce ɗakinsa, mintuna goma amma ba ta biyo shi ba, ya fito ya ce “A kawo mini ruwan zafi zan yi wanka”Ta tashi ba ta ce komai ba, ta ɗaukki flask, aurensa da ita ta saba masa da wanka da ruwan ɗumi, saɓanin da da har a kuddudufi wankansa yake yi ya ƙara gaba.Yanzu kuwa kusan kullum, da an kawo wuta, take dafa ruwan a heater, ta saka a flask.Ta zo ta haɗa masa ruwan, sai dai ta ga kamar yana ɓoye wani abu.Kawai ta leƙa ta ga me yake ɓoyewa, yanka ne a gefen cikinsa, ya saka rigarsa yana ƙara goge jinin kasancewar ba mai zurfi bane ba.”Ka gani ko? Sai da ka je aka yanko ka ko? Abun da nake ta gudu, sai da ka zubar da jini ko, ba za kai daina zuwa wurin da za a cutar da kai ba ko master? Kodayake ma ni abun yake damu, kai ko a jikinka”.”Na ce ya dame ki ne? Ba jikina bane?” Idan ba gizo idonsa yayi masa ba, hararsa ta yi ta fice.Shi mamaki ma take bashi, tun da ta yi rashin lafiyar nan, take rigima kuma kamar ta rage tsoron sa.Ya shiga ya yi wanka, ya fito ya tarar da ita da ɗan ƙaramin kwanon abinci, sai kuma kayan dressing, tun na lokacin da aka yi masa wancan raunin.Bai kulata ba, ya ja kwanon abincinsa ya cinye, awara ce da miya, ya sha ruwa.Ita ma ba ta kula shin ba, ta saka auduga da spirit tana goge, kan ciwon, tana gogewa tsigar jikinta na tashi, kamar jikinta take gogewa, shi kuwa kamar dutse latsa wayarsa ma yake yi.Haushi ya isheta, ta kalleshi ta ce “Wai ba zafi ne?””Eh babu, idan ma dirzawa ki ke da ƙarfi, dan na ji zafi, ba na ji” ta tashi ta fice fuuu, tana yi masa fatan shiriya a ranta.Kusan awa ɗaya da rabi, ya shigo mata ɗaki, ta yi sauri ta tashi zaune, saboda ta san tsiyar da ta aikata masa.Ya kunna fitila ya hau yi mata bincike a ɗaki.”Me ka ke nema?”Ya tashi ya nufo ta, ya miƙa mata hannu ya ce “Bani kayana da ki ka sace mini yanzu””Ni ba na sata”Ya ce “To baki nayi ki ka ɗauka? Ko kema kin fara sha ne ban sani ba? Kodayeke biri yayi kama da mutum, da ki ka iya kallona ki ka din ga jifana nan gaba ina ga swizaland zaki saka mini ina ga””Ni ba na shan komai, kuma ban ɗau komai ba”.”Ba ki ɗauka ba ya aka yi ki ka san a kan me nake magana?” Tayi shiru ba ta ce komai ba.Hankaɗata yayi, ya janyo ledar kayan shaye-shayen sa a cikin bargonta.”Na gaya miki idan kin gaji ba zaki iya zama ba, ban ɗaure ki ba, ki ƙara gaba”A ƙule ta ce “Ka ɗaure ni mana, zan tafi ba ka sallame ni bane, ka rubuta ka gani idan ban tafi ba. Tun da baka da tausayi idan ba mutuwa na yi ba hankalinka ba zai kwanta ba” tayi maganar tana sheshsheƙar kuka.Ya kalleta, gaba ɗaya ko faɗan ba ta iya ba, voice ɗin ta sam ba na masu faɗa bane, shagwaɓa kawai take yi.Ya ce “Kin yanke hukunci kenan? Ai da kin gaya mini da duk ba a zo nan ba, zan rubuta na baki, dama na gaji”.”Kuma wallahi idan ka yi shaye-shaye kai da Allah”Bai kulata ba, ya jefo mata kwalin sabuwar waya gal, ya ce “Gashi nan, akwai layi a ciki na yi rijista, idan kuma na yi wani laifin na gudu ke za a kama”.”Bana so” ta faɗa tana kwanciya, duk da ƙasan zuciyarta tayi mamakin wayar.Ya saka hannu ya ɗauka ya ce “To kin huta” ya fice ya bar ɗakin.Ta kwanta ta yi shiru, sai ta fara tunanin ya aka yi ya ɗaga mata ƙafa ya ƙyaleta, sai kuma ta ga rashin kyautuwar abubuwan da ta yi masa.Bayan sallar asuba bacci ta koma, ƙarfe takwas da rabi ta farka, tana ƙoƙarin saukkowa daga kan gadon, tayi tozali da farar takarda da biro. Gabanta ya faɗi ta ce “Na shiga uku sakin nawa ya yi?” Ba ta taɓa takardar ba, ta saukko a sukwane ta tafi ɗakinsa sai dai baya nan ya fice.Gaba daya jikinta yayi sanyi, sai yanzu ta ƙara jinjina girman wauta da aikata.Yau rahila har gidan su jauhar ta je, suka ƙule a ɗaka ita da Anty Zakiyya suna ta surutu da shewa.”Zakiyya ina ga ‘yar ku fa an gamu laulayi take yi””Kai haba dan Allah””Wallahi da gaske, ke ‘ya mace shu’uma komai ƙanƙantarta, kin san yaron nan har gida ya zo da wuƙa ya gama ta’addancin sa tana zubar da jini, zai yi mini hauka a gida wai su Amira sun je masa gida sun yi matarsa ko me oho musu, na ga tashin hankali na ce iyee yanzu har ta samu wannan matsayin. Wallahi mamaki nake yadda ta iya zama da yaron nan”Zakiyya ta ce “Ba ki ganta ba kamar sokuwa, kafin ki ga ta yi fushi, ko tayi zuciya da abu za a jima, ko kuma kawai tsabar ƙarfin hali ne da ƙi faɗi ba”Rahila ta ce “Sai ta yiwu, ya ake ciki da maganar hafsa?””Mu na nan ana ta murginawa, ana shirin kawo kuɗin aure, na ce lallai ta ce masa a haɗo da kayan lefe, ana sallacewa ayi auren, duk da wannan matar ta nuna bakomai na san tsohuwar muguwa ce, wataƙila wani abun zata kitsa, dan haka kan tayi wani yinƙuri ayi a wuce wurin”.”Yauwwa kar ki kuskura ki sakankance ko ki yadda da ita, ni ban zaci lamarin ma zai zo da sauƙi haka ba, ku cigaba da tatsarsa kuna tarin kayan aure”Zakiyya ta ce “Ke kin ga hidima, ai ni dai Allah ya kashe ya bani, da yanzu sai dai mu ga ana yi wa waccan yarinyar jauhar”Rahila ta kwashe da dariya ta ce “Ga mijinta can suna fama, amma wallahi ya fara son yarinyar nan, kai amma ba ƙaramin haƙuri take yi ba bala’i Allah ya kyauta” suka cigaba da hirarrakinsu, da shirin biki.Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, suka fito daga taron meeting, daga ofishin jam’iyya, sakamakon gabatowar manyan zaɓuka da za a gudanar a cikin Nigeria.Yau bai san iya adadin meetings ɗin da ya yi attending ba, suka jero da shi da mataimakin firaministan jam’iyya na jiha, ya ɗan yi miƙa ya ce “Kai, yau na gaji over””Kai honorable, da an yi babban zaɓe an wuce wurin, haka ne, ka san ban yi sati da shigowa daga Abuja ba, can ma wasu tarurrukan ne, abun duk babu sauƙi, ina ta ƙoƙari in sha Allah sai na kawowa excellency yankina, ina nan a satin nan zan yi empowerment na matasa, kuɗina duk sun tafi a campaign ɗin nan””Kar ka damu honorable, hannun jari ka saya, da an wuce wurin sama zaka din ga kwashe ribarka, ka mayar da uwar da ribar ka ɓace ba zasu sake ganinka ba, sai bayan shekara huɗu” suka kwashe da dariya.Suka yi sallama, kowa ya nufi motarsa, ko da ya je gida, matarsa tuni tayi bacci, yayi wanka ya nemi wuri ya kwanta, dama ba yunwa yake ji ba, sai dai bacci ya gagare shi, ya din ga juyi a kan gadon, ga gajiya ga baccin yana ji, amma ya kasa ya ɓuge da lissafe-lissafe abubuwan da yake son yi idan ya dace ya samu ya ci zaɓen nan.Ji yayi kamar kansa zai fashe, saboda stress kawai ya tashi ya ɗauki mukulli, ko direba bai nema ba ya hau motarsa ya fice.Yamma da gari yayi, ya hau kan titin gwarzo road kasancewar dare ne, titin babu ababen hawa, ya sauke glas ɗin motar kaɗan, yana tafe a hankali yana shaƙa wani abu a hancinsa. Sai d yayi nesa da cikin gari sosai, sannan ya yi parking a gefen hanya, ya rufe glasan motar, ya cigaba da shaƙa abun nan, kusan mintuna talatin, sannan ya juyo kan motar ya nufi dawowa yana tafe iskar kan titin nan na ratsowa cikin motar, sannu a hankali har ya koma gida.Jauhar kuwa tun da tayi tozali da takardar nan ta kasa nutsuwa, ta kasa zaune ta kasa tsaye, kuma taƙi buɗe takardar, da ta leƙa ta hangota ma, sai ta yi sauri ta fito daga ɗakin, ta din ga lissafa irin halin da za ta shiga idan ta koma gida, da irin dariyar da za su yi mata.Kuma yaƙi dawowa, har dare ba ta ganshi ba, hakan ya ƙara sanyata cikin tashin hankali, ba irin tunanin da ba ta yi ba, har ta fara tunanin ko da ya saketa, barin gidan yayi gaba ɗaya, sai dai kayansa suna nan, dan ita ta gyara ɗakin ya watso da komai ya bar mata a wurin.Sai sha biyu saura ya dawo, idonta biyu ya dawo ba ta yi bacci ba, sai da ta tabattar ya shiga ɗakinsa, sannan ta ɗauki takardar ta bishi ɗakinsa.Yana kwance a kan katifarsa, ya cika ɗakin da warin taba.Yanayinsa ya nuna a buge yake, saboda fitilar ɗakinsa a kunne take, ya haye katifa ya mimmiƙe idanunsa sun yi ƙanana da ƙyar yake ɗaga su, kallo ɗaya ya yi mata ya mayar da idonsa ya lumshe.”Master sai da ka rubuta takardar nan hankalinka ya kwanta ko?”Bai buɗe idonsa ba ya ce “Ke ki ka ce na rubuta””Kuma sai ka rubuta ɗin ko? Saboda ina fargabar kar ka sake ni, bakomai maraici ne ya janyo mini, Allah ya gani na yi iya yi na, na yi biyayyar aure, amma kullum kallona ka ke yi wadda ta takura rayuwarka, ga takardarka nan, ban ma buɗe ba balle na san meye a ciki, kuma wallahi ban saku ba” ta dire masa takardar a jikinsa, ya ziro harshensa tare da naɗe shi ya mayar, ya gyara kwanciyar sa, har ta gama surutanta, bai kuma motsawa ba.Kasa bacci tayi, ta ɗaura alwala ta tayar da salla, ta din ga addu’a Allah ya sa ya fasa sakinta, saboda ita a ganinta gara ƙalubalen gidan Al’amin a kan na gidansu.Duk rintsi ba zai daketa ko ya ci mutuncin ta ba, ko yi mata sharri ba, sai dai miskilancinsa da gaya mata baƙar magana wasu lokutan da har daɗi take ji ya kulata, ciyar da su kuma da take yi mafi yawan lokuta baya damunta, sai ma yi wa Allah godiya da take yi da ko yaya ba ya hanata abun da zata sarrafa su ci, ko yaya ta kasa abun sayarwa za a saya dan ma ana yi mata mugunta.Bayan sallar asuba tayi shiru tana tunani, ta ga sam ba ta kyauta ba, wasu abubuwan da ta yi masa, tun daga jifansa da kwanuka, har zuwa tsiwar da ta yi masa, ita tayi mamaki ma da ya ƙyaleta.Yau ba ta iya komawa bacci ba, ta fito aikace-aikacen ta, tana yi tana leƙawa ko ta gani ko ya tashi.Tana falo ta jiyo motsinsa, ta tashi ta shiga ɗakin da sallama.Ya amsa mata, ba tare da ya kalleta ba.Jiki a sanyaye ta durƙusa ta ce “Master ina kwana?””Lafiya ƙalau””Ka tashi lafiya, ya ciwonka?” Sai a wannan karon ya kalleta sai dai bai ce komai ba.”Master dan Allah dan Annabi ka yi haƙuri ka yafe mini, abubuwan da na yi maka kwanan nan ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba, wallahi ni ba mara kunya ba ce, kawai na rasa ya zan yi da wasu abubuwan ne, damuwa tayi mini yawa, dan Allah ka yi haƙuri idan ka sakenin ma, ka yi haƙuri ka mayar da ni” tayi maganar cikin rauni.Ya lumshe idanunsa ya ce “Bani wuri zan kunna hayaƙi”Ta marairaice ta ce “Dan Allah ka yi haƙuri master, ka yafe wa ‘yar madara ɓacin rai ne ba zan sake ba, na san ban kyauta ba, dan Allah ka yi haƙuri””Sai fa kin tafi, kin isheni ne kawai takura mini ki ke yi””Dan Allah ka yi haƙuri, na daina takura maka, har cincin na yi maka jiya, in kawo maka?””Eh ki kawo mini, sai fa kintafi””Da ka san abun da hakan ka iya haifar wa rayuwata, da baka sake ni ba, dan ka ga ina ta roƙonka shikenan, duk ranar da ka bari na bar rayuwarka na bar ta har abada lokacin da zaka so ka ganni da kuɗi ba zaka ganni ba”.”Eh na ji, kafin ki fara ɗaukar makami, gara mu rabu, ungo takardarki tafi da ita” yayi maganar yana danƙa mata takardar da ya warware. Ta rintse idanunta, tuni ta fara kuka, ta buɗe idanunta ta sauke a kan kyakkyawan rubutunsa, dan ganin saki nawa ya yi mata.*Ba zan dawo da wuri ba, na bar kuɗi a kan katifata ki sai wani abun ki ci*Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, ta ce “Shi ne ka yi ta wahalar da ni? Dama ba sakina ka yi ba, ka sakani kuka?”Hamma yayi, yayi shiru ta ce “A’uzibillah” duk gurbin da ya yi wani abu, yakamata ya yi addu’a bai yi ba, sai tayi masa.Ta ce “Aishikenan amma dan Allah ka yi haƙuri abubuwan da na yi maka ka yafe mini””To, ki bani wuri zan sha abu”Ta ce “To bani wayar da ka bani jiya” gefen katifarsa ya nuna mata, ta tashi ta ɗaukkota a kwali.Ta kalleshi ta ce “Yanzu dan Allah wannan ta wa ce master? To kai ina taka?” Ya nuna mata keypad ɗin sa.”Wallahi ko a mafarki ban taɓa tunanin riƙe waya ba, yaya saifu ya taɓa bani keypad mama ta ƙwace, Allah ya saka maka da alkhairi ya saka ka a aljanna, Allah ya nuna mini ranar da zaka daina shan komai, ka zama limami saboda salihancinka, Na gode master na gode sosai da sosai” tayi maganar tana tattaɓa wayar.”To excuse me, ina son yin caji””To yi mana”Ya ce “Ki fita ki bani wuri dai, kar ki sume mini yau bani da kuɗin zuwa asibiti”Maƙale kafaɗa tayi, ta ce “Master, wai yaushe zaka kai ni na gaida mama ne? Da wurin hajiya ma?”.”Wace maman?””Mamanka mana, bamu taɓa zuwa ba, na san wadda na gani a gidanku ba ita ce mamanka ba””In ji wa?”Jauhar ta ce “Babu uwar da zata zauna hankalinta a kwance, alhali an yi wa ɗanta sharri an tsare shi”.”Mama ta mutu” ji tayi kamar ya soka mata mashi, ta kalleshi ta ce “Kai ma ka san pain ɗin master? Ka girma da ita ka santa?” Ya jinjina mata kai alamar eh.Jiki a sanyaye ta ce “Ni ban ma santa ba, ina yawan takura ƙwaƙwalwata, dan na tunota, da rayuwar da muka yi tare, amma bana iyawa, baba ne yake da hotonta, nayi-nayi ya bani, ya hanani, idan na shiga ɗakinsa zan gyara masa, sai na ɗauki hoton in yi ta kallo ina jin daɗi, duk da ina jin kewarta, ina son in san yaya take ya halinta yake, yadda su mama suke faɗa ne ko akasin haka? Kawai saboda Baba ya saka hoton a cikin wallet ɗin sa, ya ce zai kai a wanko wani ya saka a yi enlarging ɗin sa ya bani, mama ta ɗauki hoton ta yayyaga, ta watsar wallahi ji na yi kamar ta yaga zuciyata, bana riƙo idan an yi mini laifi mantawa nake yi, ana yawan cewa bani da zuciya amma haryanzu a raina, na kasa jin cewa na yafe wa mama abun da ta yi mini.Da farko da na taso, na zata mama ce ta haife ni, daga baya na gane ba ita haife ni ba, sai na fara tunanin ko kawai faɗowa na yi ko tsinto ni aka yi, kowa yana da uwa ban da ni, wataƙila a haka aka haifeni, daga baya na yi tunanin ko kawai ‘yar aiki ce ni, na zata ‘yan aiki duk ba su da iyaye. Daga baya na gane baba ne babana, uwa ce bani da ita, sannu a hankali kuma na gane ina da uwa amma bata duniyar.Sai dai ba na jin daɗin irin yadda su mama ke aibata mamana, duk da ba ta raye ban san ta ba, har suna cewa mayya ce ta taɓa kama su ma, amma baba yana faɗar cewa mamana mutuniyar kirki ce, irin halina ɗaya da ita, haka yaya saifu ma yana faɗa.Mama ce mariƙiyata, na so in tashi kamar ita ce wadda ta haife ni, amma ƙiriƙiri sai ta nuna mini banbanci ba ita ta haife ni ba. Ta saka aka cire ni daga makarantar kuɗi, aka mayar da ni ta gwamnati wai ba na gane karatu ni daƙiƙiya ce, kuma ni babu mai kula da ni, ko koya mini assignment komai ni nake yi wa kaina gashi baba ba ya iya magana a kan abun da ake yi mini.Ita kuma anty Zakiyya cin zali na zahiri, na daku a wurinta, duk ba wannan ba ni ya riga ya wuce, kawai haryanzu ina jin zafin yaga mini hoton uwata da mama tayi, da ƙazafin nan da suka yi mini, na fanɗarewa, na san zan yafe musu wataran amma ba yanzu ba.Ina son in ga mutum yana hira da mamansa, ko suna wasa irin na ɗa da uwa, abun yana burgeni, ko mutum ya din ga gaya wa mamansa damuwarsa da daɗi master, wataƙila kai ka samu wannan damar ni kuwa ban samu ba, maybe da mamanka ta yi tsawon rai wannan rayuwar za ta zo maka da sauƙi”. Tana gaya masa raɗaɗin abun da take ji a zuciyarta yana raguwa, duk da kuka take yi.Ya ce “You are missing her?” Yayi maganar yana kallonta.Ta jinjina masa kai ta ce “So badly””Ki yi mata addu’a” ta jinjina masa kai tana goge hawayenta, a take shi kuma ya tuna irin tasa rayuwar, duk da lokuta da dama idan ka haɗu da wanda ku ke da irin matsala ɗaya ku ka yi sharing ana samun releif, amma yanzu shi ba ya son doguwar magana idan ya fara ma gajiya zai yi, duk da kwanan nan jauhar na isarsa da saka shi magana, kuma muddin ya gaya mata shi nasa labarin, zata shiga damuwa dan haka ya ƙyaleta.Duk da kuka take yi, ta fara ɗaukarsa a hoto tana murmushi ta ce “Kai zan fara yi wa hoto da wayar nan, haryanzu mamaki nake yi, wai master ne ya saya mini waya, Allah dai ya sanya mini kai a cikin aljanna ya jiƙan mama, ya ja da ran wanda suka rage mana, Allah ya goyi bayanka ya yi maka jagora a cikin lamuranka. Kai master na rasa wace addu’ar ma zan yi maka, na rasa wace irin godiya zan yi maka ma”Har cikin ransa ya ji daɗin Addu’ar da take yi masa.Ya kuma amsa da Amin.”To mun gama ki tafi””To me na yi maka ka ke korata?”Ya ce “Sigari zan sha”Ta ɓata fuska ta ce “Da sassafen nan ba ka ci komai ba, sai ka fara da hayaƙi, haba mai babban suna, idan a baya babu wanda ya damu da lafiyarka, ni ina son ka yi lafiya, ka rayu saboda ka ajiye ‘yar madara, yau dai ɗaya ayi haƙuri dan Allah a ɗaga ƙafa kar a sha da sassafen nan” kamar shashasha haka yake bin ta da kallo, ta karɓe lighter da sigarin hannunsa, har da ta gefe ta cikin kwali ta tattaresu.”Bari na dafa mana shayi, cincin na yi jiya, amma na kasa ci saboda damuwa, ka yi brush sai ka fito ka karya, kuma zan din ga leƙowa saura na ga mutum ya sha wani abu”Sunkuyar da kai ya yi, yana murmushi da gefen bakinsa.Jauhar ta samu na yi, lambar baba ta kira, yana ɗagawa ko gaisawa ba su yi ba ta ce “Baba na yi waya”Baba ya ce “Masha Allah Alhamdilillah, ina tayaki murna waliyya””Ka hau what’s app mu yi video call”Baba ya ce “To shikenan waliyya” Al’amin ya kalleta ya maimaita waliyya a ransa, lallai ta ci sunan da mahaifinta ya kirata da shi.”Master, nan ne wurin video call ɗin ko?” Ya jinjina mata kai alamar eh.Tana kira baba ya ɗaga fuskarsa ta Bayyana a screen ɗin wayar.”Baba wayata touch screen ce mai kyau”.Baba yayi dariya ya ce “Masha Allah, Allah ya sanya alkhairi.””Amin, ina su yaya saifu su mama da Anty?””Duk suna nan lafiya, baba dan Allah kowa da kowa a turo mini lambarsa, duk zan yi musu magana ta what’s app, zan din ga kiran su kuma a waya””To shikenan, a ina ki ka samu waya ne?””Master ne ya saya mini” sai kuma ta ce “Au amm maigidan ne ya sai mini”Wani irin sanyi ya ratsa zuciyar baba, ya ce “Allah ya saka masa da alkhairi, ya yi muku albarka baki ɗaya””Amin baba” ta kaste wayar.”Master ” ya ɗago ya kalleta.”Na gode sosai” ya ɗan tsuke fuska ya ce “Kin faɗa kin sake, ya isa haka””Bar ni na yi yabon gwani ya zama dole”.Tana cikin maganar hankalinta ya kai kan labarin da ake yi a radio, wata mata ce take kuka, take roƙon gwamna, sarki da kuma jami’an tsaro su kama Aminu mai dogon zamani bisa karya mata ɗa da yayi, ya soke shi da wuƙa, an kai shi asibiti rai a hannun Allah gashi ba ta da ƙarfi, tana neman a bi wa ɗanta hakkinsa.Cikin tsananin tashin hankali, jauhar ta kalli Al’amin, tamkar bai ji me aka faɗa a radiyon ba, sai tauna cin-cin yake yi ƙururus ƙurus ko a jikinsa an mari dutse.
Ayshercool 08081012143
