Mijin Marigayiya Page 44 Hausa Novel
Bayan ya mike duka suka mike gaba daya, a nan yayi sallama da Khadeeja yace ta koma ciki. Suka fice shi da Mustapha wanda yayi masa rakiya har wajen motarsa sannan yayi masa sallama ya tafi.Ya san ko da ya koma wajenta a yanzu ba zata saurareshi ba sai dai ma ta gaya masa maganganun da baya son ji, don haka ya wuce wajen Naja tunda dama kwananta ne.……….Har turiri take ji yana taso mata a kirjinta saboda tsabar yanda zuciyarta take tafasa; sai da tayi da gaske sannan ta kai kanta dakinta ba tare da tarushe da kuka ba. Ya za ayi ace ta karbarwa naja girki saboda kawai tana da ciki? Bayan ita a lokacin da tana da nata cikin hakaya dinga barinta da duk wata hidima yana hana yaranshi su tayata. Sannan kuma idan tayi magana ya dinga nuna mata cewa laulayi ba komai bane kamar ma dai itace take son nuna raki. Yanzu kenan haka zata kwashe wata takwas ko tara tana kula da yara yayinda Naja take kwana da miji tunda laulayin bai hana idan ta sameshi shi kadai a dakin ta kai masa kanta ba?Tana shiga ta murza mukulli ta rufe kofar, sai da karasa kan daddumar da ta tashi sannan ta zube da gwiwoyinta tarushe da kuka. Shikenan ita ta zama baiwar Mustapha ne? ya iya nunawa kowa kauna da tausayi a duniya amma banda ita? Anya zata iya wannan rayuwar a gidan Mustapha kuwa? Amma ta san dole ne ta bi umarnin Baffanta, musamman da yake a gaban Mustapha ya bata umarnin. Ta kifa goshinta a kasa ta sake rushewa da kuka.…..Ya so kwarai kamar yanda ya saba lekawa da daddare ya yiwa wadda bata da kwana sai da safe ya leka wajen Khadeeja, amma da yake bai shirya rigimarta ba sai kawai ya kyaleta suka shige daki shi da Naja suka yi kwanciyarsu.Ba karamin dadi ya ji ba da ya dawo daga masallaci sallar asuba ya jiyo motsinta a kitchen, tabbas ya san ta ji maganar Baffanta. Ba tare da bata lokaci ba ta shiryasu sannan ya fito ya kaisu makarantar.Kafin ya dawo daga kaisu makaranta ta gama nata shirin, a zaune ya sameta a parlor dinta tana karyawa. Babu yabo babu fallasa suka gaisa, sai dai daga gaisuwar bata sake ko da kallon inda yake ba.Jimawa kadan ya mike zai fice, tace ‘Idan na tsahi daga aiki zan je gidan Mommy.’Ya dan tsaya yana kallonta yana kokarin su hada ido ko zai karanto wani abu a fuskarta, sai dai bata bashi damar ba. Daga tsayen yace ‘Ki gaishe min da mutanen gidan.’Ya fice ita kuma ta cigaba da cin abincinta ba tare da ko da ta kalli inda ya wuce ba; gaba daya ma a halin yanzu ko son kallonsa bata son yi.……….Tun wajen 12pm ta nemi izini a wajen aikin nata ta fice, kai tsaye gidansu ta nufa. Ta ci sa’a ta sami Mommy da Yaya Mama suna zaune a parlor suna hirarrakinsu. Bayan sun gaisa Khadeeja ta dubi Yaya Mama tace ‘A nan kika kwana Yaya.’Tayi dariya tace ‘Ga jakata a kusa dani kina kallo amma kike min wannan tambayar, to ni yanzu ma zan tashi saboda 2pm zan dauko yara a makaranta sannan mu wuce gidan.’Itama tayi dariyyar, ta umurci Hafsa da ta shida dakin Nabila ko taje kitchen wajen masu aikin gidan ta zauna.Tun kafin tace wani abu Mommy ta dubeta tace ‘Lafiya dai na ganki kamar a fusace, sarkin rigima.’Ta zumbura baki ta sunkyar da kai tana kallon hannunta kamar me kunkuni, sai da ta gama zumbura bakin sannan cike da takaici tana kokarin danne hawayen da ya taso mata tace ‘Mommy ni Mustapha zai mayar ‘yar aiki, kuma Baffa ya goya masa baya.’Mommy ta gyara zama ta fuskanceta sosai tana kallon fuskarta da mamaki sannan tace ‘Ban gane ba, kuma me kawo Baffanki a cikin mayar dake ‘yar aiki? Shi Mustaphan me yayi miki?’Tana bude baki zata yi magana hawaye ya kwace mata, ta sa bayan hannunta ta goge sannan ta labartawa Mommy abinda ya faru. Zuwa lokacin hawayenta ya gama kwacewa yana zuba kamar ana zubar da ruwan famfo, Mommy ce ma take kokarin goge mata. Tace ‘Mommy yanzu shikenan haka zan yi wata tara ina mata hidimar gida tana kwana da miji, bayan ni haka nayi nawa laulayin ko tausayina baya ji. Ko haihuwar Hammad fa ana gama suna dole na mike na koma hidimar gidan saboda ban ma ga fuskar cewa ba zan iya ba. Amma yanzu saboda ya auro ‘yar gwal shine zan karbar mata aiki ita kuma tayi laulayi.’Yaya Mama tace ‘Nifa gaba daya ban gane. To ke me yasa bakya zuwa dakin kike barinta taje, ai da sai kije ki yi wanciyarki a can kiga ta inda marasa kunya zasu kwana tare.’Kafin tayi magana Mommy tace ‘Gaskiya nima dai ban gane dabarar yin hakan ba, ai dakin ya kamata ki gyara ki tare har sai kin gama kwananki.’Ta sa bayan hannunta ta goge hawayenta sannan tace ‘Mommy ba zan iya ba, ya kwana da wata matar a kan gadon sannan nima ya kwana dani a kan wannan gadon. Watakila ma da yayi aurensa ba tare da ya ci min mutunci ba abubuwa da dama zau zo min da sauki, ama gaskiya ba zan iya ba. Tunda ko bayan ta tare ranar da zan karbi girki bayan da ta gama kwana takwas dinta na shirya tsaf zan shiga dakin, amma har magriba bata fito daga ciki ba. Lokacin shi kuma ya riga ya fita. Don haka na kyaleta na shirya masa abincin dare tunda na gama kintsawa. Amma yana dawowa ko kallon abincin bai yi ba ya sameni wai tunda ina jego na bashi kwanakin ya kaiwa amaryarsa in ya so idan nayi arba’in sai a fara rabon kwanan. Kinga kenan ita ta riga ta san ba zai bani kwnan ba shi yasa ta ki fita ma daga dakinsa. Daga wannan lokacin dakin da me dakin suka karasa fice min daga rai gaskiya. Idan yana bukatata ya sameni a dakina, kuma yana zuwa din.’Mommy wadda take binta da kallo tana jijjiga kai tace ‘Lallai Mustapha, ni na rasa ma me zan ce. Ni fa mamakin da nake Baffanki ko gaya min bai yi zai je ba balle da ya dawo ya gaya min, watakila jiya bayan ya fita da magriba Mustaphan yayi sa’a ya sameshi a gate suka gama magana.’Yaya Mama tace ‘Hmm! Ai komai dadinki da miji idan dai wata macen ta gifta to sai abinda kika gani. Watan hakurinki ne ya kama har ya gama yayinta.’Mommy tace ‘To yanzu ya za a yi? Kinga Baffanki ya riga ya sa baki a maganar ba tare da kin gaya masa ainahin abinda yake faruwa ba..’‘To Mommy ya za ayi nayi masa duk wannan bayanin ya gane, ai ban ga alamar zai ma gane ba tunda ko a lokacin ma yace amfanin mta biyu kenan daya ta taimakwa daya. Kuma ya za ayi na zauna ina gaya masa Mustapha yana satar min kwana saboda na ki zuwa dakinsa?’‘Umm, hakane kuma. To Allah ya kyauta. Yanzu kam sai dai kiyi hakuri a ga abinda hali zai yi tunda dai babu wanda zai je ya kwance maganar baffanki. Ina ga kula dayarn wanda kika yi a baya bai kashe ki ba bana jin na wata tara nan gaba zai dameki.’Haka suka zauna suka yi ta bata hakuri; sai daga karshe Yaya Mama tace ‘Kuma kema idan kin gaji kawai kiyi pretending ki kwanta masa, wallahi da kaina zan zo na taho dake na kawowa Mommy tayi jinyarki idan kin huta kya koma.’Mommy ta kai mata duka tana cewa ‘Allah ya shiryeki yayar kwabo.’Suna nan zaune wajen 1:30pm Baffa ya shigo gidan da sallama, bayan ya amsa gaisuwarsu da sannu da zuwa ya dubi Mommy tana zaune a tsakiyar su Khadeeja yace ‘Gulmar wa kuke yi suka saka ki a tsakiya haka.’Itama dariyar tayi tace ‘Ba dai gulmarka muke yi ba.’Yaya Mama tayi musu sallama ta fice yayinda Khadeeja ta mike ta nufi dakin Mommy ba tare da tace komai ba.Baffa ya bi bayanta da kallo sannan yayi dariya ya dubi Mommy yace ‘Wannan iya rigimar karata ta kawo ko?’Ta harareshi tace ‘Ashe ka san kayi mata laifi?’Yayi dariya yace ‘Rabu da ita da-Allah, ya za ayi ace mutum yana da mata biyu ace daya ba zata karbi daya aiki ba idan bata da lafiya? Ai itama bata so a zauna lafiya ba.’Nan ta kara yi masa bayanin yanda zaman nasu yake, sai dai ta kasa gaya masa cewa Mustaphan yana bawa Naja kwanan Khadeeja saboda Khadeejan bata yarda taje dakinsa. Yanda ta san shi ta san tabbas ba zai dauki wanna ba, tunda shima tashi uwar har ta koma ga Allah turaka take zuwa ranar kwananta.………
