WACECE ITA
WHO IS SHI ?
Unique Barakancy🌹
FIFTY-SEVEN
Farkawa kawai tayi taganta a kwance akan gado, bude idonta tayi kadan batareda sun lura da hakan ba sai taga mutane kusan goma zagaye da ita, su mami kawai ta sheda sai uncle A da matarsa, motsa hannun hagunta tayi taji ta taba hannun mutum, Deen dake zaune akan bedside drawer abun duniya ya ishe shi yaji ta taba hannunsa, ba karamin shiga tashin hankali yayi ba da mami ta kirashi tace an aika yarinya ta kirashi be zoba to yazo yanzu ta suma, ko kafin yaje umm na kanta tana bata taimakon gaggawa, sosai hankalinsa ya kara tashi ganin yanda umm ke kokarin ganin ta daidaita numfashinta dan ta farfado amma kwata kwata numfashinta baya fita yadda ya kamata, duk a tunaninsa kuma dannetan dayayi ne, dama tace masa kirjinta ze fashe shi kuma yaki ji saboda yanaso ta shiga hankalinta gashi yanzu ta sume, hakan sai ya taru ya dagula masa lissafi, daurewa yayi yasawa umm hannu suka cigaba da kokarin ganin numfashinta ya daidaita, sun sha wahala sosai kafin Allah yasa komai ya daidaita, shi ya bada shawarar a mata allirar bacci saboda ta samu nitsuwa sosai, allurar umm ta mata kuwa, bayan sun gama suka zauna suna tattaunawa akan health condition dinta da yanda ya kamata su shawo kan al’amarin gabadaya…
Suna cikin wannan hali su bappa suka karaso, nan fa gida ya zama ba masaka tsinke saboda jama’a, wai a hakanma wasu na dayan building din na umm wanda ya kasance exactly irin na mami, dinner din da akayi niyar yi a tare na yaushe gamo sai fasawa akayi saboda baby tee dake kwance, karshe ma taruwa akayi a dakin da baby tee ke kwance ana jajantawa, anna harda kuka wai tana farincikin zuwa taga jikarta sai kuma rashin lafiya, deen kuwa dayaga mutane sunyi yawa a dakin ya fatattakesu yace duk su tafi su bawa mutane guri, karshe duk wanda ya shigo sai yace ya dubata ya fita bappa kuma ya goyamasa baya da fadin be kamata a taru akanta ba dama, sai ya zamana iya manyan iyaye ne kawai suka saura a dakin sai shi, twins ma babu irin magiyar da basu masa ba akan ya barsu su zauna amma yaki, matasan su sudais kuma dama basu zo gidan ba hotel suka wuce direct, Deen na sane ya ziga bappa akan kar a bari mazan su sauka a cikin part din gidan ba tsari bane shi kuma gaskiya baze zauna da kowa ba, bappa kuma ya biyemasa yace haka za’ayi……
Motsin hannunta ya sakeji a kusa da hannunsa, hakan ya tabbatar masa da ta farka, mantawa da mutanen dake dakin yayi ya ruka hannunta dake kusa dashi ya sunkuyo kusa da ita a hankali yace;
“Zahrah kin tashi?”….
A tsorace ta juyo jin muryarsa akanta tana zare ido…..
Wani guilty feelings ne ya kamasa har ya kasa hakuri yace;
“Zahrah nine nasa kika suma ko?”….
Sakin bakin yan dakin sukayi suna kallo da sauraron ikon Allah….
Da sauri ta girgiza masa kai batareda tayi magana ba…..
“Toh meya sumar dake? Gayamin kinji ko?”…..
Kamar tace masa ga abinda ta gani amma sai ta kasa fada, kawai tace;
“Cikina ne yakemin ciwo”…..
Sai a lokacin ya juyo yaga irin kallon da suke musu, mazewa yayi ya cewa umm;
“Umm baki bata maganin nan bane?”….
Gyada kai umm tayi tace;
“Na bata fa, saidai in bata sha ba dan karba tayi ta wuce”…..
Dawo da kallonsa kan baby tee yayi yace;
“Kinsha ko baki sha ba? Gayamin gaskiya bazan miki fada ba”….
Tabbas ta sha maganin amma kuma masu iya magana sunce ta inda aka hau tana ake sauka, so gwara tace batasha ba tinda tin farko ciwon ciki tace yana damunta, sunkuyar da kai tayi a hankali tace;
“Ban sha ba”….
A bazata cikin rarrashi taji yace;
“Dan Allah in aka baki magani kinasha kinji zahraty?”….
“Naji yaya”…
Ta bashi amsa cike da ladabi itama…..
Kallon juna umm da mami sukayi dan basu taba ganin magana me dadi ta shiga tsakaninsu ba sai yau, basu taba tinanin ze iya lallabata haka ba ma, sannan basu tabaji tace masa yaya ba dan ko rannan sai da umm ta mata fada akan yanda take ce mishi saif kai tsaye kamar wani sa’anta….. Tabe baki mami tayi tace;
“Meyafaru naji kace ko kai ka sumar da ita, hala ka mata wani abu ne daga zuwa kiranka, dama naga ta dade”…..
A dabure yace;
“Bari ta min shine na mata fada, na tambayane ko saboda fadan dana mata ta suma”….
Sai kuma ya kalli baby tee yace;
“Ko na miki wani abun bayan wannan ne zahrah?”…..
Kada kai tayi tace;
“A,a”….
Aranta kuma tana tsine masa tana kuma jinjina karyarsa….
Tafi anna ta hau yi tana nufar su baby tee, baki har kunne da farinciki dauke akan fuskarta tace;
“Saifu baka gayamana yar gida za’ayi ba”…..
Deen zeyi magana kenan bappa shima yace;
“Gaskiya ka munafurceni aboki, shine baka gayamin kana ciki ba tun kafin nazo”…..
Kallon rashin fahimta Deen ya musu sai kuma yace;
“Tsofaffin nan wai me kuke nufi ne, anna gaskiya ki dena cemin saifu kamar a kauye”….
Dakuwa umm ta masa tace;
“Kaniyarka iyayen namune tsofaffi”….
Dariya bappa yayi yace;
“Kyaleshi, ni yanzu ta amaryata da yake san kwacemin nake”….
“Bappa wai me kake nufi ne?”….
“Me muke nufi banda kaga fatimatu kana so”…
Zaro ido yayi yace;
“Ni yaushe nace muku ina sonta?”….
Rankwashi anna ta masa tace;
“Yanzu mana, yana ga kana wani kaucewa?, tsaleliyar budurwa kamar kishiyata ai sai dace”..
“Toh ni banaso, kawai daga zuwanku zaku wani zo da wani zance, gaskiya ku dena min irin haka”….
Karap mami tace;
“Itama me zatayi da kai, bappa da anna ku dena bata bakinku dan tana da wanda takeso, mahaifinta ma ya bada ita”…
“Bangane mahaifinta ya bada ita ba, har yaushe aka ganta da har ze bada ita, inace a labarin da kuka bani ta sanadin saifu aka ganta? Ina shi muhammadun yake, it’s too early”…..
Bappa ya fada ba alamun wasa…..
Kamar jira deen yake yace;
“Nima dai haka nace bappa, daga ganin yarinya wai aurar da ita zasuyi, wannan meta sani da zata iya zaman aure”…..
Baby tee da tinda suka fara maganganun taketa bata rai, ganin anzo gejin da bazata iya shiru ba ya sata turo baki tace;
“Toh ai ni ina sonsa”…..
Buge mata baki yayi niyaryi tayi saurin kaucewa ta boye a bayan anna dake kusa da ita, kwafa yayi yace;
“Idan manya suna magana kinasa baki saina fasa miki baki”…..
Harararshi mami tayi tace;
“Kai ai ka iya sa naka bakin, harda bada shawara, toh ka barta ta fada ai tana sonsa, kai da kace baka sonta waya buge maka baki”……
Haderai yayi yace;
“Amma mami ai ita tayi karama bare ta san wani soyayya, anna kinga yanda take dinnan toh wallahi haka take yau lafiya gobe ba lafiya, a haka suke san aurar da ita, hakan ya dace dan Allah?”…..
Jan hannun mami umm tayi suka fita daga dakin dan bazata iya tsayawa sauraron gurmin da deen yake san hadawa ba…..
“Sam be dace ba, gwara a batta ta samu nitsuwa sosai, kafinnan ma kila ku daidaita, bansan meyasa ga abu a cikin gida kuke haka ba, kai in kafita ina zaka samo irinta, kema idan kika bari ya wuce ki ina zaki samu kamarsa?”…
Cewar anna tana kamo hannun baby tee…..
Bata fuska baby tee tayi tace;
“Ni wallahi bana son shi, ni khaleel nake so”…..
Bugemata baki ya karayi wannan karan akaci sa’a ya sameta, sannan cikin bacin rai yace;
“Ni sa’anki ne da zakice bakya sona? Sai ki kallemu kice kina son wani? Saboda gaki mara kunya fitsararriya?”……
“Kai Kai Kai, saifu banasan haka fa, bazeyiwu ka takurawa jikata ba, karka kara bigemata baki dama”…..
Cewar anna tana janyo baby tee jikinta….
Deen zeyi magana bappa ya nuna masa hanyar kofa yace;
“Jeka abunka”….
Dan yasan yanzu sai abu ya zama babba indai Deen ne musamman yanda yaga ransa ya baci..
Kwafa yayi ya dunguremata kai sannan ya fice…
Murmushi bappa yayi yace;
“Kyale yayannan naki kinji ko amaryata? Khaleel din kekeso ko?”…
Turo baki tayi tace;
“Ehh”….
“Toh shikenan karki damu kinji ko?”….
“Toh”….
“Rabu dashi ki saki ranki muyi hira, tukanna ma ya jikin naki? Cikin ya daina ciwo?”…..
Anna ta kara da fadin haka….
Sannu da jiki sauran yan dakin suka mata sannan suka fita suka barta da bappa da anna da suka sata a tsakiya suna bata tarihin familyn shuwa, babu wanda basu bata labarinsa ba tindaga kan iyaye, jikoki da kakanni harda tattaba kunne duka… Nan da nan suka shiga ranta saboda yanda suketa nan nan da ita, sunata mata wasan jika da kaka, har kwallar farinciki ta zubar a boye saboda bata taba tinanin zata sadu da familynta ba bare har kowa yana nuna mata kauna irin haka banda mutum daya😏…….
Around 10am umm tashigo dakin da sallama, suna zaune ita da anna, tana bata abinci a baki sai shagwapa take, anna kuma sai lallabata take wai ta karaci ko kadan ne, barka da wutawa umm tayiwa anna sannan ta kalli baby tee tace;
“How’re you feeling now?”…..
“Naji sauki umm”….
“Masha Allah, cikin ya dena miki ciwo?”….
“Eh ya dena, bana jin komai yanzu”…..
“Alhamdulillah, ungo”…
Umm ta fada tana mikawa baby tee wayarta…..
Karba tayi tana sauraron maganar da umm ta cigaba dayi….
“Gashinan nasa miki number eesha, itama ta karbi taki, call her and invite her for your welcoming party tomorrow”….
“Okay umm”…..
“And kartazo ki wulakantata dama, idan saif yace meyasa tazo kuma kice masa ke kikayi inviting dinta”…
“Toh umm”….
“Call her while I’m still here”…
“Okay”….
Baby tee ta fada tana kallon screen din wayar, sai taga wayar na kan number ma har saving umm ta mata da friend eesha, dialing number tayi tasa a kunne…..
Eesha na zaune akan gadonta ta kurawa side daya ido abun duniya ya isheta, idar da sallanta kenan ta dawo ta zauna bayan tayi karantun qur’ani, tinda suka dawo daga gidan mami jiya mommynta ta daina kulata, bata dai fadawa babanta ba kamar yanda tayiwa umm alkawari amma wani silent treatment me cin rai take bawa eesha, ga deen data kasa cirewa aranta, kamar kar abunnan ya faru taji ita fa in bashi ba zata iya mutuwa, tana cikin wannan hali taga kiran baby tee, abinda bata taba tinanin gani ba, atleast not this soon, tayiwa baby tee bayani kamar yanda umm tace ta mata, amma sai taga kamar baby tee bata wani gamsu ba dan ta ki sakar mata fuska ko kadan, da murna ta dauki wayar tasa a kunne……
“Hi eesha”…
Baby tee ta fada daga daya barin….
“Hello dear, ya kke? Ya jiki?”…..
Cewar eesha cike da farinciki….
“I’m good, you?”….
“I’m good too, ya su umm, mami and my yaya saif”…..
Dan jimm baby tee tayi tana maimaita my yaya saif din a ranta, sai kuma ta tabe baki tace;
“All good, I’m inviting you for a party tomorrow if you would be available”……
Tashi zaune eesha tayi cikin muryar dake nuna zallar farinciki tace;
“Of course I will, ai ni yanzu ke kadai mommy ta yarda inyi kawance da ita, nasan zata barni nazo, where’s the party holding?”….
“A gida”….
Ta bata amsa a takaice…..
“Whaaat? Ai dole ma inzo, friend bansan meyasa bakya sona ba, wallahi I’m not like billy, I even need a big help from you amma bakya san kulani”……
“I never hated you eesha, what help do you need?”…..
Kamar me tsoron magana eesha tace;
“Ki taimakamin in shawo kan yaya saif ya soni ko kadanne dan Allah, ina son shi sosai wallahi”….
Rasa me zatace mata tayi kawai tace;
“We’ll talk when you come”….
“Okay dear, can’t wait”…,
Eesha ta fada fuskarta cike da annuri tinda taga baby tee ta fara sakar mata fuska tasan komai ze zo mata da sauki, yanda taga saif ya rikice akan abinda billy tayiwa baby tee ta san ba karamin sonta yake ba, soyayya irinta ya da kanwa dan tasan da da wani abu a tsakaninsu da mami bazataso tarayyarsa da ita ba, shiyasa takeso tayi using baby tee ko Allah zesa ya sota ko yaya ne……
“Alright bye”….
Baby tee ta fada tana kashe wayar, kamar jiya tana kashe wayar taga message yayi popping ta notification dinta da wata number da bata sani ba, wani irin bugawa kirjinta yayi sai da ta nemi guri ta zauna, taso taki budewa amma sai zuciyarta ta kasa daurewa, kawai tashiga inbox dinta, tafi minti biyu tana kallon number kafin tayi bismillah ta bude content din…
“Idan har bakya jin irin yadda nake ji a kan ki a yanzu, to tabbas na san zaki ji irin hakan bayan na mace. Da in mace ni kadai wani ya aureki kuma gwara in kasheki in kashe kaina kowa ya hakura!”……
Rintse ido tayi bayan ta gama karanta sakon, tanajin anna na tambayar umm wacece eesha ita kuma umm na mata bayani amma bazata iya cewa ga abinda suke cewa ba, gabadaya hankalinta ya tafi wani gurin, tayi lalube tayi lalube ta rasa waze iya turo mata da wannan message din, haka kawai kuma message din ke balakin daga mata hankali, gashi ba number jiya bace dan saida ta haddace number kafin ta goge, haka tayita maimaita message din batasan so nawa tayi ba, karshe kuma tayi blocking number kamar jiya amma bata goge message din ba, sai ma maimatawa data cigaba dayi, sai da umm tace taje ta gaisa da yan uwanta yan matan da sukazo sannan ta dawo hayyacinta, ajye wayar tayi ta fita….
Tin kafin ta karasa parlourn takejin muryar mutane na tashi sai shafta akeyi, nufosu ta cigaba dayi a hankali feeling so nervous dan rabon ta da shiga cikin hayaniyar mutane bazata iya tinawa ba shiyasa abun yake affecting dinta yanzu dan bata iya sakewa da mutane… Suna hangota sukayi kanta suka rungumeta suna mata sannu da jiki, yan mata guda tara ne including twins, wasu sa’anninta ne wasu kuma zasu girme ta da kadan, so duk clique dinsu daya, introducing kansu suka mata daya bayan daya dukda anna ta gayamata sunayensu dama, akwai siyama, asma’u, ilham, fahima, safiyaa, raihan, khairat, sai sun twins, daga nan kuma aka dora daga inda aka tsaya a hirar, duk yanda suka so ta sake dasu kuma ta kasa, saidai kawai ta zuba musu ido tana sauraronsu……
Kamar yanda deen ya fada tin kafin ayi nisa ta fara ganin mabanbantan halayye a gurin wasu daga cikin yan matan a iya magana kawai, saidai batasa musu baki ba ta cigaba da observing kowannensu…..
Da taga hirarsu ta isheta tace musu zataje ta kwanta, basu mata musu ba dan sun san bata da lafiya even though sun so ta sake tasa baki a hirar itama….. Gurin anna ta koma ta tarar dasu har lokacin suna magana saidai mami tayi joining, ya jiki suka sake mata, ta dauki wayarta ta fita..
Bedroom dinta ta koma tayi wanka tayi shirin kwanciya, har zata kwanta khaleel ya fado mata arai, ta tuna bata sanar dashi welcoming party din da zaa mata gobe ba tasan kuma yanata kiranta yaji shiru gashi wayarta a silent take dama, sai da ta fara duba call log dinta taga calls din khaleel rutututu kamar yanda tayi tinani harda na dazu dazu sannan tayi dialing numbersa tana zama akan gado…. Rejecting call din yayi ya kirata back a take, tana picking yasa mata kuka yana fadin;
“Where have you been wifey? Daga fita tun safe sai in kasa samunki a waya? You have no idea how I have been bothered, I was so scared Allah”…..
Murmushin da bata shirya bane ya kubuce mata tace;
“Shine kake kuka? Karka ba da maza mana darling khal”……
“In dai akanki ne in bada kowa ma I don’t care, wifey kuka kawai nakeyi inji sanyi a raina, please where have you been? Ki taimaki zuciyata ki dena nesa da ita please”…..
“Insha Allah honey, nima inata kewarka, it’s just that I forgot my phone at home, da muka dawo kuma banajin dadi shine umm ta min allura, bandade da tashi, I’m sorry for making you scared”….
Wani ajiyar zuciya ya sauke yace;
“You don’t have to be sorry dear, dama burina kawai inji kina lafiya wifey, toh how’re you feeling now? Ya jikin?”…..
“Naji sauki sosai, especially after hearing your melodious voice sai naji na warke gabadaya”…..
“Dagaske? Harkinsa ina blushing wallahi, you’re so sweet wifey”…..
Dariya tayi tace;
“Dama kira nayi to invite you for a party tomorrow, I hope zaka zo?”…..
“Ni na isa inki amsa kiranki? Ban isa ba, where is the party holding?”…..
“A gida ne, come early, I want to introduce you to my family”…
Zaro ido yayi yana daga kwance, sai kuma ya mike yace;
“Me kikace wifey? Did I hear you clear?”….
Murmushi me sauti tayi tace;
“You heard me right, I want to introduce you to all my family members as the love of my life”……
Ai besan sanda ya koma ya zube akan gado yana dafe zuciyarsa ba, sai ga hawayen farinciki na zubo masa, jiki na rawa yace;
“Am I dreaming? Kina so na haka dama wifey? Innalillahi me zan baki tukuici? Name anything please? Gosh inaji kamar na janyo gobe”…..
Kyalkyalewa tayi da dariya tace;
“Ni banason komai, and of course you’re so special honey, ni dai kadena kuka please”….
“Toh na daina babyna, but seriously you really made my day, why won’t I keep falling and falling and falling for you again and again and again after you gave me the reason to?”…
Kankame pillow dake kusa da ita tayi maganganunsa na ratsata, rasa abinda zatace tayi kawai tace;
“Sai da safe, I love you!”….
Murmushi jindadi yayi yace;
“I love you too wife, Allah ya tashemu lafiya”…..
Kashe wayar tayi tana wani blushing, haka ta cigaba da tinanin khaleel har bacci barawo ya saceta bata sani ba……
Tafe take cikin shiga ta alfarma me kayatarwa, sosai tayi kyau a cikin tsadaddan lace din datasa maroon, karyane a fada maka shekarunta ka yarda saboda yanda jindadi da gyara ya zauna a jikinta, mace ce me kyan gaske ga diri masha Allah, shiyasa ko yaushe cikin shigar mutunci take bare ayi tinanin bata da aure a kawo mata shirme, a haka sai ka dauka she’s in her early 30s in baa fadamaka ba, da safe ne gurin karfe bakwai da wani abu ta fito, tana sane ta fito da sassafe saboda ta samu tayi magana dashi kafin a taru dan sunyi inviting family friends da sauransu, murda kofar parlourn kawai tayi tashiga dan tasan a bude yake barinsa a irin wannan lokacin, yana yin hakanne kuma saboda ze koma bacci, so in akayi knocking ba lallai ya ji ba saboda distance din dake tsakanin parlourn da bedroom dinsa amma in ya barshi a bude sai a shigo azo ayi knocking a kofar bedroom dinsa…….
So daya tayi knocking ya farka kasancewarsa mutum mara nauyin bacci da kaifin ji dama kuma be dade da kwanciya ba, amsawa yayi da fadin;
“waye?”
“Umm ce”….
Da sauri ya tashi yaje ya bude kofar, yana budewa fuskarsa ta wadatu da murmushi saboda ganin shigar da tayi…..
“Umm dina ni kadai kinyi kyau sosai”….
Deen ya fada yana murmushi…..
Bata bashi amsa ba sai kafe guri daya datayi da ido tana screening wani abu da take hangowa..
“Bani hanya in wuce!”…..
Matsa mata yayi ta shiga ciki, direct inda take hango wani dan karamin pack ta nufa, tana zuwa ta dauka ta shiga jujjuyashi a hannunta sai ga syringe din allura ya fado daga ciki alamun ba’a dade da amfani dashi ba……
Juyowa deen yayi dan yaga abinda takeyi kawai yaga kwalin allurar daya gama yiwa kansa dazu a hannunta, wani irin sarawa yaji kansa yayi yayi saurin juya baya yana sunkuyar da kai, sai yaji dama mami ce tashigo ta gani da hankalinsa kwance dan bazata taba gane menene ba, amma umm manyan likitoci taga wannan abun ai ya shiga uku…….
Dagowa tayi taga ya juya baya, hada rai tayi strictly tace;
“Saifuddeen turn!”….
Sai da yaji gabansa ya wani mugun faduwa amma ya dake ya juyo yana sunkuyar da kai….
Takowa gabansa tayi rai a bace tace;
“Yanzu abinda kakeyi ya dace? Kashe kanka kakesan yi? Kana da hankali kuwa?”…..
Kara sunkuyar da kai yayi a sanyaye yace;
“I’m sorry umm”…..
“Sorry for yourself! Ka sani amma kake take sani? Wani irin nonsense Doctor ne kai?”….
Cikin kame kame yace;
“Umm kiyi hakuri bansan yanda zanyi bane”…..
“Bakasan yanda zakayi ba? Tin yaushe muke binka kayi aure ka ki? Nace tin yaushe? And you’re here injecting yourself with cyproterone imagine!”…..
“Umm wallahi…”…
“My friend shut up!”…
Tayi saurin dakatar dashi cikin tsawa….
“Har kanada bakin kare kanka saif? Wallahi I’m really disappointed in you, ina lefin small subsidizers haka? Toh waya sani ma ko duk kayi amfani dasu sun dena maka aiki yanzu shine ka tafi extreme stage, dama zuwa nayi muyi magana ta fahimta da kai but after seeing this wallahi wallahi sai ka auri eesha as soon as possible, kaji na rantse and I’m not going back on my words!”….
Tsugunawa yayi ze fara bata hakuri ta sake daka masa tsawar data fi ta farko tace;
“Dalla bani hanya in wuce, shashasha kawai mara tinani”….
Ba shiri ya matsa mata ta fita kamar yayi kuka…
Har ta kai bakin kofa kuma ta dawo tace;
“Dama ka fara shiri tin yanzu, idan kaga dama kuma ka cigaba da injecting kanka, anytime the side effect affected you just make sure ba’a kirani ba! Fool kawai!”….
Zubewa yayi a kan gado bayan ta fita yana hargitsa gashin kansa, yasan umm batada saurin fushi kuma tanada saukin kai sosai, a hakan kuma idan ta nuna tayi fushi yana fara bata hakuri take saukowa, amma wannan bacin ran daya gani a idonta be taba ganin irinsa ba, if only she knew abinda yayi triggering dinshi har ya kasa jurewa hmmm, it’s all started with lallen baby tee, daganan kamar wanda akayi ma casting spell yaji komai ya kwance masa, koda aka aikota ta kirasa shi kadai yasan irin yakin da yayi da zuciyarsa lokacin daya danneta da abun bazeyi kyau ba, haka ya kasa bacci saboda ciwon mara, babu irin dauriyar da beyiba, lemon tsami da thick lipton ko besan adadin nawa yasha ba, karshe kawai yaga abin na nema yafi karfinsa shine yayi ma kansa allura dazu, unfortunately kuma be saka kwalin injection din a shara ba kawai ya saka syringe din ya ajyeshi a kasa shine tazo tagani, a yanzu babu abinda yafi daga masa hankali ma irin rantsuwar da tayi akan sai ya auri eesha and he knows she mean it, shi gabadaya ma bayasan kara hada ido da umm yanzu……
“Lafiya kake ya mutsa kanka haka, in ya isheka kaje kayi sanko mana”….
Yaji muryar sudais akansa cikin tsokana…..
dagowa yayi yace;
“Kai yaushe ka shigo?”….
“Ka tafi duniyar tinani ta ina zaka san nashigo, meyake damunka bro?”….
Mutum ne shi me tsananin zurfinciki amma haka kawai yau yaji yanaso ya gayawa wani damuwarsa especially sudais da yasan mutum ne me amana, hannunsa ya kara turawa a cikin gashinsa yace;
“Wata ake san chusa min sudais, wai dole sai na aureta and I don’t love her”…..
Shekewa da dariya sudais yayi kasancewarsa mutum me barkwanci da tsokana yace;
“Gaskiya ka bani kunya smart, meye wani abun damuwa in dai tana da kayan more rayuwa? Ka godewa Allah an taimaka maka da wata tinda kowa ka gani kace bata maka ba”….
Naushi ya kaiwa sudais a baki yace;
“Matsalata da kai bakada hankali wallahi, uban me zanyi da kayanta toh? You thought I can be intimate with someone I don’t love?”…
Kaucewa sudais yayi yana dariya yace;
“Kai ko kake da abunyi da kayanta, sanda zaka haikewa yar mutane ma wayasani? Wuyarta fa kawai ace an shafa fatiha nasan wallahi hakurinka ya kare”…..
Wani mugun kallo yayiwa sudais sannan a zafafe yace;
“Fita min daga daki dan ubanka! Ka dauka kowa ne mara class irinka! Wallahi mace ko tafi duka matan duniya kyawun sura da kyawun fuska wallahi bata isheni kallo ba you know that”….
Dariya sudais yayi yana tashi zaune yace;
“Mai da wukar mutumina, Insha Allah zamu san yanda za’ayi, ni yanzu zuwa nayi ka rakani in gaisa da mutanen gidan in kuma ga jikar anna da aka samu zuwa dominta”……