Kallonsa Jalila take kaman wata sokuwa, ya daga kai yaga su Jawwad da Abba suna tahowa, yakuma durkusowa yace mata “Allah ya kaiku lafiya”
Hanan tana kallon abunda yake faruwa harsuka karaso inda motar take, Abba yayi musu nasiha tareda fatan suje lafiya, Abdallah ya shiga ya kunna mota, yafito da ita daga cikin gidan, Nana tace “Jalila dan Allah inkin tafi karki dade, zanyi missing dinki sosai”
“Bazan dadeba Nana, nima zanyi missing dinki” suka rungume juna sannan Jalila ta karbi jakarta a hannun Nana.
Hanan tazo bayan Jawwad ta wajen kunnensa tace “I love you Haidar, i wish to see you soon” ta juya ta shiga mota, murmushi kawai Jawwad yayi, Jalila ta bude mota ta shiga amma hankalin ta yana kan Maganganun Jalal.
Jalal yazaga sukayi musabiha da Abdallah yace “Allah ya saukeku lafiya, ya kiyaye hanya”
Suka amsa da Ameen banda Jalila da taketa zancen zuci. Abdallah ya kunna mota yafara ja a hankali Jalila tanata waigawa tana kallon Jalal harsuka bar layin, Hanan ta daki cinyarta tace “To ai seki dena kallon nasa haka”
dan hade rai Jalila tai tace “kamarya indena kallonsa? Wakenan?”
“Jalal mana, aishi kike kallo tukuna ma meya gaya miki ne naga jikinki yayi sanyi?”
“Bansaniba, niba shinake kallo ba”
Hanan tai dariya tace “Queen ba dai taurin kai ba, bakyason gazgata zuciyarki, ga abu a zahiri amma kinata wani basarwa”
“Ke dan Allah ki kyaleni Hanan”
Hanan tace “Na kyaleki”
Abdallah yana jinsu yai murmushi yace “Hanan kokece sirikar tamu ne? Keda Jalal kuke boyewa”
“Tab Allah ya kiyaye, bawani sirika, wadda ze Aura tana gidansu cousin dinsa ce Ilham”
Hanan tace “karya kikeyi, kefa kikace bazaki bari ya Auri Ilham ba”
“to dan ban bari ya auri Ilham ba kuma ni seya Aureni?.
Abunnasu na nema yakoma fada dan haka Abdallah ya shiga yimusu hira aka manta da wannan zancen, Jalila ta rarraba hankalinta me Jalal ya ajiye mata a cikin Al’qur’ani tsawon wannan lokacin bata taba ganiba? Sannan mezesa yace ze bar kasar nan haka taita zancen zuci, Hanan ta fuskanci Jalila nacikin damuwa, Amma taurin kai ya hanata yadda.
Nana taji babu dadi sosai da Jalila ta tafi jinta take kaman marainiya, Naja taje ta samu Maama ta gayamata abunda yafaru, Maama taimata alkawarin tasan matakin dazata dauka, zata kawo dukkan karshen wannan yaran, zatayi wa Abbansu Jawwad magana.
Jalila se kusan takwas na dare suka isa garin bauchi, wani irin katon estate ne, dake dauke da gidaje dayawa a ciki, kuma kusan duk irinsu daya, tundaga farkon estate din suke cin karo da sojoji, da sunzo wucewa Abdallah yake daga musu Hannu, wani gida suka nufa, duk gidajen da Jalila ta gani a estate din wannan gidan yafi shi girma, shima akwai sojoji abakin gate din, bude musu akai Abdallah yashiga sunata daga masa hannu, Abdallah ya tsaya suna gaisawa, suna masa sannu da hanya, daya sojan cikin gurbatacciyar hausar sa yacewa Hanan “Madam ba magana? Ko gajiyar ce?”
Hannaan tace “kai ba’a magana nagaji kam” dubawa yayi yaga Jalila a motar, kafin yayi magana Abdallah yaja motar zuwa makekiyar harabar dake cikin gidan, Abun yabawa Jalila mamaki bayan sojojin dake bakin gate akwai wasu a cikin gidan, Hanan tafara fita sannan Jalila dukda magariba tayi, amma ko ina hasken fitulu ne, Jalila ta bude motar ta sakko, ga mamakin ta gaba daya idan mutanen dake harabar gurin yadawo kansu, harta dan fara tsarguwa, Abdallah ya bude motar yana janyo kayansu.
Abdallah ina kasamo wannan kuma? Ko dama Hanan tanada sister ne? Suka dinga jerowa Abdallah tambayoyi, Hanan ta kalli wani soja tace Phillips ga kaya nan shigo dasu upstairs taja hannun Jalila suka shige cikin gidan. Gidan shiru se kamshin turare da Abinci dake tashi, gidan shiruu wani tangamemen palour suka shiga, tundaga palourn Hanan take kiran “Anty fiddo, kina inane?” wata matashiyar mace ce wadda bazatafi shekaru Ashirin da biyar ba ta fito tana cewa “Hanan wane irin kirane haka, Salla nakeyi ai yau kinzo kowa se san kin iso wannan ba…. Bata karasa maganar ba tayi shiru, ganin Hanan tareda Jalila, matar tace
“Hanan menake gani haka, ina kika samo wannan me matukar kama dake?”
Jalila tai murmushi tace “ina wuni Anty”
Hanan tace “daga zuwanmu kin isheni da tambaya, ina mutan gidanne?”
“suntafi shirye shiryen biki, anjima maybe kiga sun shigo” ta kalli Jalila tace “Sannu da zuwa baiwar Allah, shigo”
Hanan tace “aiba gurinki tazo ba, innancy tana dakinta ne?”
“Hanan ko kara babu, tana daki tana salla” Hanan taja hannun Jalila zuwa wata kofa, dakine me dauke da katuwar katifa da tv da bandaki da komai a ciki, gefe wata dattijuwace sanye da hijjabinta tana salla, daga imda Jalila take tana iya ganin dattijuwar fara ce tas daganinta kasan tana hutawa amma Jalila gani take kaman ta taba ganinta amma ta manta a inane.
Hanan tace “Shugabaa Inna salla ake tayi ne? Jalila ga toilet nasan zakiyi Alwala bari in dawo” Jalila tace to, koda Jalila ta shiga cikin toilet din shima ya hadu, kaman ba na tsohuwa ba, Jalila tai alwala ta fito harta tada salla tsohuwar bata idar ba.
Koda Hanan ta fito se tambayoyi suke mata ina suka samo Jalila, Hanan tace “Anty fiddo kimfiye tambaya wallahi”
Abdallah yace “kusan shekarunsu takwas kenan a tare, yarinyar da daddy yake gaya muku ce yayi ya mekama da Hanan, itace yace zekawow Inna taganta”
Wadda suke cewa Anty fiddo tace “Masha Allah, sekace wadda taimana maganin Hanan ce, kai amma Abdallah bantaba ganin wanda ba yan uwa ba masu kama kaman Hanan da wannan yarinyar ba, bari in kaimata Abinci masha Allah ashe itace ‘yar daddy”
Jalila ta idar da salallolinta a lokacin tsohuwar ta kammala nata lazimin, kurii ta zurawa Jalila ido, Jalila ta idar tazo kusada tsohuwar ta zauna tace “inna barka da yamma” kasa amsawa tayi sedai kallon Jalila da takeyi, Anty fiddo ce tashigo tareda su Abdallah, Inna ta daga kai ta kalli Hanan ta kalli Jalila tace “Haba nifa imce, nasan Hanan bata da wannan nutsuwar, amma ko idona neke ganin ba daidai ba, kamar duk Hanan dince?” tsohuwar kana jin yadda take magana kasan bafulatana ce, hausarta bata fita sosai
Anty fiddo tace “daidai idonki ke gani, kinga me kama da Hanan ko? Ita daddy yake cewa ze kawo miki ki ganta ai”
Inna tariko Hannun Jalila tace “mairo ashe dama kina raye zankuma ganinki, baki ganeniba, hafsatunki cefa? Allah sarki mairo ina kika shiga tsawon lokaci bamganki ba” sosai tsohuwar ta rike Jalila tana kuka, saroro Jalila tayi tana kallon Inna, Hanan tace “kekam Inna wai har yanzu bazaki dena wannan abun ba dan Allah?”
Abdallah yace “Inna idan mairon takice haka zakiganta bata tsufa kamarki ba, wannan fa yarinya ce sosai, bakuwarmuce kamar da takeyi da Hanan dinki yasa Daddy yace ze kawo miki ita ya nemi alfarmar mahaifinta alfarmar mahaifinta ankawomiki ita amma kina kuka”
Goge hawayenta tayi tace “yi hakuri yarinyata, daga zuwanki zanmiki shirme, zauna kusada ni”
Anty fiddo tacewa “Inna bari muje taci Abinci se adawo miki da ita” inna tace “ita ya sunanta ne? Ko itama Hanan din ce” Abdallah yace “sunanta Jalila”
“Kai wannan sunan da wahalar fada, na dauka itama Hanan dince ko mairo” Anty fiddo tace “Jalila taho muje” Jalila ta mike suka fito,
Anty fiddo tace “Kiyi hakuri haka takeyi wani lokacin haka takewa Hanan ma, wani lokacin setayi ta kuka wai Hanan tana abu kaman kanwatta, kumafa mu bamu san kanwartata ba, bawanda yasan inda take wata kilama ta mutu, amma har yanzu inta tuna setaita kuka”
Jalila tace “Allah sarki, kinsan babu abunda yafi dan uwa dadi duk tsufansa duk yarintarsa”
“Hakane kam”
Sun karrama Jalila sosai sukayi dinner sannan Hanan takai Jalila masauki, Jalila tace “Hanan bari inwa Inna seda safe ko?”
Hanan tace “inkikaje bazatayi bacci ba kuka zata cigaba, ki kyaleta seda safe”
“to shikenan, amma Hanan meyasa duk gidan nan naku sojojine, koduk saboda babanane?”
“Aiba daddy ne kadai soja a estate din nan ba, sannan duk wanda kika gani a estate din duk family dinmune, kaso uku bisa biyu na mazan dake estate din naan sojoji ne shiyasa kikaga sojoji ko ina, yanzu gobe in Allah ya kaimu zan kaiki kigansu akwai yan mata kamanmu, amma basu san munzoba, da yanzu an cika part din nan, Inna itace tushen family din nan, duk yarantane da jikoki da yaran jikokinta, sekuma kanin mijinta shima ya rasu amma akwai yaransa shima da jikoki a cikin estate din nan, mijin inna ya rasu shekaru bakwai baya, amma bata tunanin sa kaman kanwar nan tata tanabamu labarin kanwar ta, babban dantane kawai ya san kanwartata, shima bashida wayo sosai lokacin amma haka wataran take birkicewa ta wuni kuka”
Jalila tai ajiyar zuciya tace “Allah sarki, tunda kika ga haka ba karamin shakuwa ne tsakanin ta da kanwar tata ba” sukayi ta hira sannan suka kwanta bacci, amma Jalila tana tunanin meyasa bata dakko Al’qur’anin nan ta taho dashi ba, tana son sanin me Jalal ya ajiye a ciki, ita tsawon lokacin da qur’ani yayi tareda ita bata tab ganin komai a ciki ba, to me Jalal yake nufi.
Nana duk gidan yamata ba dadi, se yanzu takejin akwai shakuwa sosai tsakanin ta da Jalila, Naja kam haushin kowa takeji musamman Nana, Nana tarasa mema zatayi taji dadi, ta dakko waya ta kira Jalila suka sha hira, bayan sungama waya da Jalila, wajen karfe shadaya Nana ta fara kwalemar dakinsu kaman yadda Jalila takanyi wani lokacin, ta hargitsa komai tana gyarawa, Ilham ce ta shigo dakin babu ko sallama Nana ta daga kai ta kalli Ilham tace “Ilham anya ba batan hanya kikayi ba yaukece a gidanmu haka, yaushe rabonki da gidan nan”
Ilham ta tabe baki tace “ba dole indena zuwa gidan nan ba na fuskaci anamin zagon kasa, dama mummy ce ta aikoni, tace ace tanason ganin Jawwad, naga bayanan, kuma bakowa a palour, kuma naji ance wannan yarinyar bata nan shiyasa nazo nan dakin, badan hakaba bazan shigoba”
Nana tace “nifa bangane mekike nufiba Ilham, wani irin zagon kasa akemiki hakane a gidan nan”?
“Haba Nana karki rainamin hankali mana, kema haushinki nakeji kun hada kai za’akwacemin Jalal”
“wai dawa kike ne haka kimin bayani dalla2, dawana hada kai za’a kwace miki Jalal din?”
“wannan tsinanniyar ‘yar uwar taki mana, Kun hade kai zata kwace min miji”
“Wai kina nufin Jalila ce takeson Jalal kokuma yaya”
A fusace Ilham tace
“Nana nifa wannan maganganun nan naki batamin rai suke karayi, ta yaya zakidinga rainamin hankali ne Nana, kina nufin bakisan kulla2 datakeyi na kokarin rabani da Jalal ba, son Jalal takeyi kuma nida ita tace seta rabamu akanme zan kaunaceta”
Naja ce ta shigo dakin ta kalli Ilham tace “to yanzu tsakanin nidake watake rainawa hankali, waini narasa wannan shedaniyar yarinya ya take? Ba’agane gabanta ba’a gane bayanta, kekince tanason yayanki, ni daza’ayiwa baiko da Jawwad yace ita yakeso, katsam sega wata jarabbabbiyar tazo wai itama shi take so, nibana gane kan wannan yarinyar sekace dan wake Allah kadai yasan gabanta”
Nana tace “Allah me iko, Allah gatan bawa, kowa ya kwaso tarkacen tsiyarsa seta jibge akan marainiyar Allah, yanzu ke Ilham keda Jalila tace miki tanason JALAL iya sanina ko shiri basayi dashi, tayay zakizo da wannan maganar kuma yanzu?”
“Nana ke kanki yanzu haushin ki nakje kina rainamin hankali, ninaga abunda baki ganiba, sonshi takeyi kuma wallahi bata isaba”
Naja tace “Ai daga ita har Nanan bakinsu daya, kedai kiyi iyayinki ki kwaci Saurayinki dan wallahi bata isa ta auri Jawwad ba daga ita har wannan kodaddiyar yarinyar, banda zalama ki hada maza kice kina so duk jarabarta ai daya zata Aura”
Ilham tace “Aikuwa ba dai Jalal ba sedai ta Auri Jawwad dan bata isaba”
Nana zuba musu ido tayi, dan tarasa mema zatayi kotace
Naja tace “Ayi mu gani ai tafi dacewa da wanann dan shaye2, ba Jawwad ba kema banda jaraba mezakiyi da mashayi, ki kyalesu taje ta aureshi suta haukan tare”
“ke gyara kalamanki ni dan shaye2 nakeso, kika fadi bakar magana akan Jalal zanmiki ba dadi wallahi”
Abu yanemi yakoma fada tsakanin Naja da Ilham, Har Ilham ta juya zata fita, ta dawo ta nufi gaban drower da Nana ta fito da komai amma banda wani Dan karamin redbox, gaban drower taje tasa hannu ta dakko Al’quranin ta kalli Nana tace “Nana ya akayi wannan Al’quranin yazo gidan nan?”
Nana tace “Na Jalila ne lafiya?”
“Wallahi Nana ke makaryaciya ce, to wannan Al’quranin Jalal ne, kakrsa ce ta fanso masa a saudiyya, yanzu gashi a gurin ta, nace miki suna soyayya amma kin karyatani”
Nana tace “kinga Ilham wannan Al’quranin fa tun wani zuwa datayi akabata shi daga gidanku, kekika kawo kayan amma kina wani zance daban”
Ilham tace “to tunda kince nina kawoshi, to yanzu zan dauka, bekamata Abunda yake na Jalal yaje hannunta ba, kinsan son dayakewa Al’quranin nan kuwa?”
“Ilham karmu yi haka dake, ki bani inta dawo sekuyi da ita”
“Inta dawo kice meshi tazo ta dauka, inta matsu ta biyoni ta karba”
Bayan Jalila tagama waya da Nana, sunyi waya da Jawwad yagaya mata yakira Abdallah yace masa sun sauka lafiya sukayi waya, ta kira Abba ma ta gasheshi, Hanan taja Jalila suka koma gurin Inna,
Suna zuwa takuma rungume Jalila ta shiga yimata hira da labarai irin nasu na tsofaffi, Inna tanada abun dariya sun dade auna hira, zuwa jimawa ‘yan mata da samarin gidan suka ding shigowa duk wanda yaga Jalila seyayi mamakin kamaninsu da Hanan kaman yan biyu, Hanan ta dinga zagawa da Jalila cikin estate din nan, suna da karamci kaman dama can sunsan Jalila tasamu kyakyawar karba, kwanan Jalila uku a garin daddyn su Hanan ya iso shida Mummynta, yaji dadin ganin irin karbar da’akayi wa Jalila, wannan karon sam Mummy bata nunawa Jalila tsana ba sema mamakin girman da Jalila tayi take.
Inna tacewa daddy “dan Allah dan nan kacewa baban yarinyar nan yabarmin ita, wallahi kamar mairona haka take, musamman intana dariya ko tafiya”
Daddy yace “haba inna, yazasu barmiki diyarsu, yanzunma sunyi kokari dasuka bari tazo nan” haka yaita lallaba Inna ta hakura.
Dukda kulawar dasuke bawa Jalila hankalin ta yana kan Jalal tanason sanin hali dayake ciki, amma bata san wazata tambaya ba.
Yau daddare Har sunyi shirin kwanciya Hanan tace “Jalila kina fama da damuwa a ranki, kuma nasan akan Jalal ne meyasa kika damu dashi haka, in ance kina sonsa kice karyane?”
“niba damu dashi ba, ni bantaba jin son Jalal a raina ba, ina tausayinsane kawai”
“karya kikeyi Jalila, kina son Jalal”
“Hanan keba wadda zan boyewa wani abubace ba, bantaba jin son Jalal ba”
“Naji bakyason Jalal, amma mekikeji akansa?”
“Ina tausayinsa ne kawai, dakuma kasancewarsa da Abu mafi soyiwa a gurina wato Jawwad, ina tausayinsa ne da son ganin yazama mutumin kirki saboda Jawwad Hanan koke kikaji labarin rayuwar Jalal zaki tausaya masa”
Nana Jalila tagayawa Hanan komai na labarin Jalal, har kokarin da tayi na ganin an kama oga KB da Jeje, dakuma abunda Jalal yagaya mata lokacin dazata taho
Hanan jikinta yayi sanyi matuka sannan takara jinjinawa Jalila da wannan namijin kokari datayi da sa kanta a hatsari a boye ba tareda kowa yasani ba
Hanan tace “gaskiya Jalal ya cancanci a tausaya masa, Amma kina ganin kowane ze iyayiwa Jalal abunda kikayi masa, Amma tsaya kinason sanin me Jalal ya ajiye miki a Alqur’ani”
“tunda muka taho nakeson Sani”
“yakamata musani, kira Nana a waya kiji in Alqur’anin yana nan ta duba mana”
“Ai in banda ke seshi Jalal ba wanda yasan me nayi”
“eh ai bazata gane ba”
Jalila ta amince ta kira Nana, seda suka gama hira da Nana, kafin Jalila ta tambaya Nana tace “Baby Ilham fa taga Alqur’anin ki wannan Jan, yau inayimana gyaran daki tazo, tace wai na Jalal ne, kakarsa ce tabashi ya akayi yazo gurinki tace inkin dawo kisameta ki karba”
A fusace Jalila tace “What!!!?
Jalila tace “Yasalam, Nana kiname Ilham zata shigo har cikin gidan nan ta daukarmin abu natane? Meya kai hannunta kayanmu harta daukarmin abu”
“Jalila Al’qurani fa ba Novel bane ko littafin hausa da zan kamata da kokawa in karba, gyaran daki nakemana tashigo ta ganshi ta dauka”
“Nana kingama dani dakika bari ta tafi dashi, amma tunda tace idan na dawo na je karba ki gayamata ta saurari dawowarta wa, tasan karona da ita ba dadi, zanzo in karba idan bata bayar dan Allah ba zata bayar dan dole, karma kikuma tada maganar tabaki zan dawo in karba, banda Jahilace me zatayi da Al’qurani metasani aciki? Inma tasani bashida amfani a gurinta ai”
“To nidai Allah yabaki hakuri, ni bayan haka wasu maganganu tazomin dasu dasam ban gane inda ta dosa ba?”
“Kamar yaya?” Jalila ta fada a kagauce
“Nikam Baby meye hadinki da Jalal ne?”
“Wane irin tambaya ne wannan Nana?”
“Jalila inkinga rashin mutuncin da Ilham ta dingayi a dakinmu sekinsha mamaki, tana gayamin wai na hada kaidake zaki kwace mata Jalal, wai taga abunda ban ganiba, Kina son Jalal ne, Naja tazo suka hadu sukayi tayi, ni abun yabani mamaki iya sanina ko shiri bakwayi dashi amma maganganunta sun ban mamaki “
Jalila tayi ajiyar zuciya tace
“Nana kyale ta aikinyi ne bata dashi, kinsan tun asalina yarinyar nan batayi min ba, shiyasa take neman masifa, nime zanyi da wani Jalal, ai Jalal se ita makakkiya itama din ba Auren ta zeyiba, ki manta da ita zan dawo ai daidai nake da ita ai”
Nana tace “Hmm Jalila kenan, inaji kaman kina boyemin wani abune, amma inba rami meyakawo rami? Shikenan dai sekin dawo din, ki gaida min Hanan dan Allah 🙏”
Nana ta kashe wayarta, Jalila ta kalli Hanan a salube,
“me Nana take nufi?” dan daga mata gira Hanan tayi tace
“Queen kenan, naga kin damu da abunda Ilham tayi, amma keda bakyasonsa meyasa kike son abunda yafito daga hannunsa haka har kikejin babu dadi?”
“Hanan bansan mezan gaya miki ki yadda dani ba wallahi, Hanan Al’qurani abune me girma, sannan inason sanin meye Jalal ya ajiye tsawon lokaci ni banganiba, sannan muddin ina raye Wallahi sena nunawa Ilham iyakar ta”
“to meye na wannan tada jijiyoyin wuya haka easy queen i know you can do it, amma meye next plan dinki akan Jalal, kina ganin tafiyarsa Dubai akwai Alkhairi kuwa?”
“To yatafi uwar Dubai mana, daga nan yatafi bangon duniya idan yanaso? Ke nagama abunda zan iya akansa kowa tasa ta fishsheshi, dama yace ina takuramasa kinga se yaje yayi abunda ya gadama, nima takaina nake, yatafi bayan duniyama yaje ya bude gidan giya in yanaso” takarasa fadin haka tana kokarin kwanciya
Hanan tace “karya kike tawajena, nasan halinki kaf Jalila yanzu kina jin wani abu ze sameshi zaki kuma tashin hankalinki, kya gama zagaye zagayenki ne”
Banza Jalila tai mata ta ja bargo ta shige, Hanan tai murmushi itama ta kwanta.
Jawwad yaje kiran da Mummy take masa, amma ya lurada wani kallon banza da Ilham take masa bebi takanta ba ya durkusa ya gaida Mummy dake zaune a palour,
Har kasa ya durkusa suka gaisa, Mummy tace “yawwa Jawwad dama nace kazone saboda Jalal, inason ganinsa amma nasan nidashi bazezo kiran danake masa ba, dan Allah Jawwad ka dinga yimasa fada, sati me zuwa daddynsa zezo akwai maganar danake so muyi nida shi da babansa, dan Allah idan daddynsa ya dawo zanmaka magana inaso ka kawomin shi “
Jawwad yace
“insha Allah Mummy zan masa magana, acigaba da hakuri ana masa Addu’a Insha Allah komai ze wuce, Alhamdilillah yanzu yafara rage wasu abubuwan”
“Hakane Allah yasa hakan nima ina masa addu’a”
Yatashi yai sallama yafita, Ilham tayi tsaki tace “Nifa Mummy gani nake wannaan Jawwad din ke kara ziga Jalal yake wani rashin mutuncin yake kara kina”
“Kinga nidai ba wannan ba, kokarina kawai inga abunda na shirya ya tabatta akan auren nan naku, idan kika matsa kika nuna bakyason Jawwad kinsan baze taba aurenkiba ko? Dan haka kishiga hankalinki”
Ilham ta zumbura baki ta tashi tabar palourn.
Zaman bauchi ya karbi Jalila, tayi kalau da ita, kusan koda yaushe tana tareda Anty fiddo kokuma gurin inna, susha hira taci dariya, gashi cousins din Hanan suma ‘yan shaftane mazansu da matansu, haka ake zuwa a cika babban palourn gidan aita wasa da dariya, samarin gidan da yawansu suna suna son Jalila amma fafur Hanan tace, ai Jalila tanada miji. akwai wani cousin din Hanan yusuf akayi bikinsa, komai da Jalila akeyi, kaikace ‘yar gidance dama can sunsanta, sunajin tsoron yusuf sosai saboda baya wasa ma sosai, anan gurin babban abokin ango ya like yace shi nan duniya Jalila yakeso, Yusuf yaji dadin hakan, dan haka yace “Aitunda daddy yace da Hanan da Jalila duk’ ya’yan sane, shima da Jalila da Hanan duk kannensa ne, ya yaba da halin Jalila dantafi Hanan nutsuwa”
Bayan biki yusuf yasamu daddyn Hanan, yagaya masa Abokinsa Ahmad yana rikon ‘yar baba
Daddy yai murmushi yace “indai’ yar baba ce inta amince sannan kun cika ka’idojinmu ai semu duba inkun cancanta abaku semu baku”
Yusuf yace “daddy kenan indai ana sanmu ai zamucika dukkan sharudanka” daga nan sukayi ta hira daddy agaban Mummy akayi tace “Amma danayi murna, dan Ahmad mutumin kirki ne zataji dadin zama dashi, amma ina tunanin yadda zata zauna da matar Ahmad, kasan ‘yar taka bata da hakuri’ ya’yannak ban san wadda tafi wata hakuri ba”
Daddy yace “Ai indai tana sonshi lafiya kalau zasu zauna, inmuka koma zanyiwa Abbanta maganar, indai basuyiwa wani Alkawari ba, Zanbawa Ahmad”
Yusuf yaita godiya kaman shi za’a bawa.
Daga Jalila har Hanan basu san me akeyiba Yauma, an taru a palour ana hira da daddare Daddy yake cewa abashi list din sunayen wanda ze samawa aiki, Jalila ba karamin birgeta family din nan suke ba, kansu a hade yake haka aka gama hira aka watse.
Jalila kullum tana tareda Inna, sannan Mummy Hanan duk ta dena mata wannan wulakanci datake mata abaya.
Jalila suna chatting da suleiman yake gaya mata, an tabattar da Alhaji Kabiru yana saida makamai da kwayoyi shida Jeje, ranar litinin za’a kaisu kotu, Jalila ba karamin farinciki tayi ba, taitayi masa godiya. Ta zauna tayi shiru tayi wani tunani, amma bata gayawa Hanan ba tasan damunta zatayi da tsokana dan haka tabar abun a ranta
Da safe Jalila bayan sungama breakfast taje tasamu Mummyn Hanan tace “Mummy dan Allah kan daddy ya fita inason inganshi”
Mummy tace “to shikenan zan masa magana” Hanan tace “queen me zakicewa daddy ne? Ina fatan bawata matsala?”
“Ba wata matsala inason inganshiine”
“to shikenan”
Mummy taiwa Jalila iso, taje palourn daddy , ta shiga suka gaisa yanata tsokanarta tana murmushi, se bayan sun gaisa tace
“babana gurinka nazo kamin wata Alfarma”
“Ina jinki ‘yar Baba fadi komene? Insha Allah in zan iya sena miki shi”
Jalila ta kwashi kusan Awa guda a gurin daddy sannan ta fito, ko Hanan bata gayawa Abunda ta tattauna da daddy ba.
Har yanzu Jalal baya walwala sosai, daddynsa yadawo Nigeria, yakan shiga cikin gida gurin daddynsa, amma babu ruwansa da Mummy balle wata Ilham, Iyakar Jalal dakinsa, sedai wani lokacin yakan fito amma baya nisa sosai, Jawwad ne ke takuramasa yadan fita dashi suzaga gari, Jalal yadena zuwa club amma yana shaye shayensa a dakinsa be denaba.
Hannah duk yadda zatayi taga Jalal abu ya gagara, dan haka ta yankewa kanta shawara ta karshe, ta shirya tsaf ta tafi gidansu Jalal, Jalal na cikin dakinsa a kwance besan me akeba, daddy yana gaggawa ze fita da yamma motar Hanna tai parking a kofar gidan, ta fito daga motar da wata irin shiga da bata kamaci dan musulmi ba, da sauri takaraso gaban daddy tace “barka da yamma”
Yace mata “yawwa barka” ya dauke kansa yana kokarin bude motarsa tace “Amma dan Allah Jalal fa?” seda gaban daddy ya fadi, kaddai ace Jalal yafara neman matane ya dake yace mata “lafiya me Jalal din yayi miki?”
“meyema bemin ba? Amma dan Allah yana cikine gurinsa nazo, inason ganinsa” kaidajin yadda Hannah ke magana kasan babu Alamun tarbiyya a tareda ita daddy yace
“Meye alakarki dashi dakike nemansa, baki bani amsa ba”
“Akwai alaka me girma tsakanina da Jalal, sanin Alakar bata da amfani a gareka, babu abunda sanin Alakar ze kara maka banda bacin rai da tashin hankali, dan haka bekamata ayi tone tone ba, amma ina neman Alfarmar ka dan girman Allah kasaka baki Danka ya Aureni, hakan ne kadai hanyar tsira da mutuncina”
Mummunar faduwar gabace takama daddy, hasashensa yazama gaskiya kenan, yanzu lalacewar ta Jalal harta kai ga fara neman mata Innalillahi wa inna ilaihi raji un juyawa daddy yayi da sauri ya rike kansa ya shige cikin gida yana hada hanya.
Hannah kam murmushi tayi tace “koda banganka ba Jalal, nayi abunda nasan dole ka nemeni, na fuskanci bakajin rarrashi kafiye taurin kai, gara in fito maka a Hannah ta.
Ilham na palour tana harabar gidan tana waya daddy yazo ya wuce rike da kansa, mamakine yakamata, yanzun nan fa yake sauri ze fita to shida waye, sauri tayi ta nufi gate ta leka, amma taga anja mota batagane waye ba.
Gida ta dawo taje tagayawa Mummy, da sauri Mummy ta fito ta nufi part dinsa yana zaune ya dafe kai akan kujera, zama tayi kusada shi tace
“meyasameka hakane? Habibi lafiya kuwa yanzufa kake cikin walwala kafita meke damunka ne?”
Dagowa yayi idonsa jawur yace “Khadija Jalal”
“meyasami Jalal din? Bashida lafiya ne?”
“ba wannan ba, ina kyautata zaton Jalal yafara neman matan banza” dan zaro ido tayi “Kamarya ya’akayi kasan haka? Kodayake ba abun mamaki bane ba, tunda duk wanda yake shan giya koya kwana a club ba abun mamaki bane amma gaskiya bana zaton Jalal yana neman mata amma”
“Enough!!! Baze yuwu ba khadija, iya sanina ďana ba manemin mata bane ba, ban san ya’akayi haka zata faruba, kinga yarinyar datazo gurinsa yanzu kuwa? Kinsan metace min ne? No baze yuwuba dole in dau mataki, Zina bala’i ce, dole inyiwa tufkar hanci”
Ilham dake labe a kofar dakin sedata kusa rusa ihu, da gudu ta tafi dakinta ta rufe kofa tana sintiri, nashiga uku idan Dagaske Jalal yafara neman mata ina na kama, menene makomata? Kan bala’i hakan na nufin lalacewar komai fa? Amma wacece tazo gurin nasa? Ina baze yuwu ba, idan har Jalal yafara neman mata bazamu samu komai ba gaba daya shirinmu ze lalace ne, dole inje inga umma a yau din nan jakarta ta dauka ta zuba kudi tayi waje da sauri tafita ta tari napep ta nufi gidansu.
A sukwane Ilham taje gidansu, ta tarar da mamanta a tsakar gida tana tankade, “Umma akwai matsala ajiye tankaden nan ki tashi”
A sukwane tace “ke lafiya kike wannan rawar jikin?”
“nikam ki ajiye tankaden nan kitaso akwai matsala”
Jan hannun mamanta tayi sukayi daki ta zauna a gefen gado tace “Umma akwai gagarumar matsala, mahaifin Jalal yace yafara neman mata, wai wata yarinya tazo neman Jalal, be fadi me tace masa ba, amma yace yana zargin yafara neman mata, idan haka ta faru mu menene makomarmu?”
“ki kwantar da hankalinki kitashi kikoma tun kafin su gane wani abu, ki bar komai a hannuna gobe da kaina zanje gidan malam, ya bincikamin tsawon shekaru mutumin nan yana mana aiki, bamu taba samun matsala ba dan haka bana tunanin za’a samu wannan matsalar “
” gara dai kije da gaggawa kar asamu matsalar wannan karon, dan ina cikin matukar tashin hankali “
” bakomai ki tashi ki tafi”
Sukayi sallama Ilham ta taho.
Gaba daya hankalin daddy yagama tashi, yarasa nutsuwa gaba daya, yana murna yana ganin Jalal yafara rage wasu abubuwan amma kawai ace wannan mummunan tashin hankali da abun kunya na gabato family dinsu. Ganin duk ya tashi hankalinsa yasa Mummy tasame shi tace
“Hayatee wannan damuwar ba iyace mafita ba, nasha gaya maka abaya Yakamata ayiwa Jalal Aure, Namiji ne me cikakkiyar lafiya dole ya bukaci abokiyar rayuwa, amma wakake tunanin zebawa Jalal Auren ‘yarsa a wannan halin nasa, shiyasa nace tunda Ilham ta nuna tana sonshi a haka kima’ yar uwassa ce, kayadda a hada Auren nan, shine rufin Asirin mu, kila ma kaga ya dena abunda yake”
Daddy yai ajiyar zuciya yace “bakin Auren Ilham da Jalal nake ba, ina gudun abunda ze biyo baya ne, kinsan halinsa inbayason abu, yace baya son yarinyar nan, tunda yace bayaso ko anyi Auren nan wahala zata sha”
“Haba Hayatee kafison yadakko maka magana atukuna, a wajene yake cewa bayaso, da anyi abun zakaji shiru sun zauna lafiya amma kayi tunani, ina tunanin ayiwa Jalal Aure shine mafita, tunda banajin ma yanada wata wadda yakeso giyarsa ce kawai ta dameshi, inaga yiwa Jalal Aure shine mafita”
“to shikenan zanga abunda Yakamata nayi, Amma hankalina tashi sosai”.
Bayan sallar magariba Jawwad yasa Jalal agaba da mita
“Gaskiya Jalal bana son wannan zaman gidan da kakeyi kadena walwala, kadena farinciki kullum a daki, bana son hakan, inaga zan duba mana wani business mufara kadena wannan zaman, dan haka zanyi tunani business zamu fara”
Jalal yai murmushi yace “Dama ina son yimaka magana, Daddy yacemin yasamomaka aiki amma kaki yadda katafi, karka damu dani Jawwad ka karbi aikinka ka tafi senafi kowa murna, Saura kuma muzo musha bikinka da Hanan, ko angon Hanan?”
Ajiyar zuciya Jawwad yayi yace “Jalal nina rasa mekemin dadi ma, Maama ta matsamin akan Auren Naja, kullum yarinyar nan setayi abunda zatajamin fada a gurin Maama, narasa yadda zanyi da ita”
“Kaine bakayi maganinta ba”
“Kamar yaya kenan?”
“Keje kasamu Abba ka gayamasa yanema maka Auren Hanan mana”
“Taya Jalal? Jalila tana sona idan na Auri Hanan ban kyauta ba Jalal”
“kana maganar kana son ta tana sonka amma meye makomarta agurin mahaifiyarka da danginta?”
Jawwad yai ajiyar zuciya yace
“Kasan wani abu makuwa?”
“A’a seka fada”
“Hanan tace min wai soyayyar ‘yan uwantaka ce tsakanina da Jalila, Akwai wani a zuciyar Jalila, amma kana ganin hakan ze iya yuwa?”
Jalal ya dan kalli Jawwad yace
“Hmm Maybe, nidai fatana kaje ka karbi aikin nan kawai da daddy yasamo maka in bahakaba nida kaine”
Jawwad yai murmushi yace “Jalal kenan sedai mutafi tare”.
Abbaa ya kira Jawwad dakinsa, gashi ga Mummy Jawwad ya shiga ya zauna yana fatan Allah yasa ba wani laifi yayi ba.
Abba yace
“Yayana na kaina, Maamanka tazomin da wani batu, shine nace yakamata ingaya maka kafin in aiwatar”
Jawwad yace
“to Abba na ina jinka”
“Yawwa Jawwad, Maamanka tace tanason hada Aurenka da Kanwarka Naja, kuma nan da sati biyu takeso akai kudin Auren, sannan ka karbi aikin da’aka sama maka, in anyi Auren se ku tafi can tare”
Duk wata jijiya ta jikin Jawwad seda ta dan tsaya na wucin gadi, gaba daya jikinsa yayi shock, cikin dakiya yace
“To Abbana, Allah ya tabattar mana da Abunda yafi Alkhairi gaba daya”
Maama tayi murmushi tace
“in ankai kudin banason asa fiye da wata shida”
Jawwad yace “to Maama Allah ya temakemu”
Abba yace “ina fatan dai ba’a matsa maka ba, inkana da magana ka fito kayi”
Jawwad yace “A’a Abba babu wata damuwa”
“to shikenan Allah yamaka Albarka”
Haka Jawwad yafito daga dakin jiki ba kwari ya tafi dakinsa ya kwanta
Jalal yayi mamaki jin shiru Jawwad bezoba yau, dan haka ya mike domin yaduba Jawwad, daddy ya kirashi a waya yace yana son ganinsa a cikin gida.
Cikin gidan ya nufa, ya nufi palourn daddy amma yana zuwa ya tarar da
Daddy, Mummy, dakuma Ilham turus yayi ya tsaya yana kallonsu daya bayan daya, yasan akwai wata kulalliya
Kara hade rai yayi ya shiga palourn ya zauna becewa kowa komai ba ya zauna, daddy ya kalleshi yace “son ka tashi lafiya”
“Alhamdilillah” daddy yai murmushi yace “Masha Allah, kayi breakfast ne?”
“A’a ina jiran Jawwad ne kuma bezoba”
“bari a hada maka anan kaci” daddy ya kalli Ilham yace “Ilham hadawa yayanki Abinci mana”
Jiki na rawa ta mike ta nufi dining din daddy ta hado masa kayan breakfast ta kawo ta ajiye, shidai be kulata ba ya zauna yafara cin Abincin sa, daddy suka cigaba da hirarsu shidasu Mummy, shidai Jalal bece musu uffan ba, yana kammala cin Abincin sa ya mike ze fita, daddy ya dakatar dashi ta hanyar cewa “Ina kuma zakaje? Zamuyi magana ne ai”
Dawowa yayi ya zauna yana kallon daddy, daddy yace “Jalal kaga zamanka haka baze yuwu ba, tunda ansamu degree daya da kyar, kaga shekarunka sun fara Ja daga kai har Jawwad zuwa yanzu yakamata ace ansama maka abokiyar rayuwa a matsayinka na namiji, amma bantaba jin kacemin ga budurwarka ba, ko akwai wata bansaniba “
Wani irin kallo Jalal yayiwa daddy sannan yace” dan Allah adena wannan zancen, in lokacin Auren yazo za’ayi, amma dan Allah for now a kyaleni”
“A’a Jalal babu batun a kyaleka, banason cigaba da ganinka a haka ba Aure, bakasan Aure shine cikar mutum ba, inma baka da budurwa ne ga Ilham tace taji ta gani tana sonka a haka, meye laifin Ilham? Dan haka nakiraka tunda kaida Ilham duk dayane”
“A zato na a baya munyi wannan Maganar ta wuce? Wannan tamkar maida hannun agogo bayane, nace bana sonta, bana sonta akan me za’a takuramin, kuma ai naga Aure ba wajibi bane, balle ace in banyiba nayi laifi, dan haka a kyaleni bana sonta bazan Aureta ba”
A fusace Mummy tace “Baka isa ba wallahi, da abun kunyar da kake shirin jawomana gara aimaka Aure, kokana so kobakaso Aure se anyi shi”
“Abun kunya na nawa kuma? Koke har yanzu abubuwan da nakeyi basu isheki kunya ba? Nagama magana ba wanda ya isa yamin Auren dole wallahi, duk duniya natasani wannan yarinyar natsani duk wani abu da yashafeta, Aurene bazan Aureta ba”
Ilham ta rushe da kuka tace “Nashiga uku Mummy, menayiwa Yaya Jalal haka?”
Mummy tace “rabu dashi, Aurene babu fashi, tunda yasan yafara biye biyen mata, har karuwai sufara biyoshi gida, rashin mutuncin sa ya wuce yaje ya samesu a can, se yafara kawosu gida, ai dole a dau mataki akansa”
daddyn Jalal yaso ya hana Mummy karasa maganar amma seda ta karasa, Jalal dake shirin fita ya tsaya cak ya juyo
“Niza kiyiwa sharri dan nace bana son wannan shashashar, Nine nakebin mata, kirasa dame zaki alakanta ni se wannan mummunan Aiki, to wallahi da in Auri Ilham gara a dauramin Aure da Akuya, Nagode da sharrin da kika yimin a matsayinki na uwata”
“Ba sharri tayi maka ba Jalal, gaskiyane” juyowa yayi inda daddy ke magana, nan da nan idonsa ya canza ya harzuka matuka yace
“daddy da bakinka? Kaima ka yadda zannemi matan banza? Ka yadda ni Jalal zan kawo karuwa cikin gidan nan? Ka yadda ni Jalal ina neman matan banza, lalacewata bata kai haka ba” daddy yace
“Ya isa Jalal, ba sharri akayi maka ba, ni yarinyar tasamu a waje tace gurinka tazo, ita tacemin Akwai alakar dake tsakaninku wadda bata kamata inji ba, kuma lallai insaka Aureta shine kawai hanyar tsira da mutuncinta da naka, ka gayamin meye hakan inba neman mata kake ba?”
Shiruu Jalal yayi ya marasa meze ce, mamaki gaba daya ya kamashi, a iya tunaninsa babu wadda zatayi masa haka, su Jeje ne kuma zuwa yanzu suna hannu kodai duk shirin Mummy ne haka? Amma a tunanin sa be cancanci daddy yayi masa wannan mummunan zargin ba, ba tareda yayi bincike ba ana alakanta shi da dabi’ar dayafi tsana a rayuwarsa wato zina.
“Shikenan daddy naji na gode, Jalal danka mashayi kuma manemin mata,
Daddy da ina neman matan banza da lalacewar da zanyi tafi haka, da ba tun yanzu ba matan banza sun dade suna zarya a gidan nan, dukda Jawwad yana rufamin asiri a abubuwa da dama bana tunanin ze yadda ya zauna da mazinaci, shikenan nagode amma kusani Wallahi bazan Auri wannaan shedaniyar yarinyar ba”
Mummy tace “dalla rufemin baki, kai har kanada bakin dazakace bakason Ilham? Ba rufamaka asiri zatayi ba, kanada bakin kiranta shedaniya ka…..
“Enough Mummy!!! Karki kara zagina waye silar komai, natsani Ilham natsani me sonta” yakarasa yana Zazzare ido, daddy yace “Jalal ya isheka haka, danme zaka dinga cewa ka tasani yarinya metayi maka haka? Lokaci yayi dayakamata kadinga dagawa mahaifiyarka kafa”
“Daddy kayanke min hukunci bakayi bincike ba, kasan bana maka karya, nidai fatana kayi bincike kadena zargina, daddy kanamin uzuri a abubuwa da dama ban taba zaton haka daga gareka ba, sannan maganar Ilham wani abune daba lallai in gaya maka meyasa nace bana sonta ba, duk ku kwantar da hankalinku Insha Allah a satin nan zanbar muku gidanku, in bar muku kasarma gaba daya ku huta”
Ya juya a mugun fusace yafito daga part din daddy, gaba daya jikin daddy yayi sanyi tausayin Jalal ya kamashi, ya juya ya kalli Ilham yace “Ilham mekika yiwa Jalal ne yake miki haka?”
Ilham cikin kuka tace “daddy ni bansan menayi masa ba, yakemin wannan muguwar kiyayya”
Mummy ta dinga rarrashin Ilham.
Jalal kam tunda yafito yaji wani abu ya tokare masa kirji, dakin Jawwad ya tafi yana zuwa yatarar da Jawwad kwance akan gado ido a rufe, Jawwad yana kwancene zuciyarsa ba dadi yarasa yadda zeyi da matsalar ke damunsa, jin Jalal ya shigo ne yasa Jawwad ya bude ido, ya tashi zaune ya dake ya boye tasa damuwar ya kalli Jalal yace “Lafiya kuwa naganka haka meya farune?”
Kasa magana Jalal yayi, sedai jijiyoyin kansa da suka mimmike idonsa jawur, se huci yakeyi kai dagani kasan akwai damuwa sosai.
Jawwad yace “ka gayamin mana meke faruwa?”
“Jawwad zan nemi visa, dole zan bar Nigeria a satin nan, kuma wallahi na tafi bazasu kara ganina ba”
“meyasa Jalal, meyasa zakace haka?”
“Jawwad nagama yanke hukunci, wannan karon karka cemin komai dan mutuwa ce kawai zata hanani tafiyar nan, zan bar Nigeria idan na tafi wallahi bazan kuma dawowa ba”.
A kwanakin nan sam Jawwad be gayawa Jalal shikuma tasa damuwar ba, sedai kokarin lallaba Jalal dayake yayi hakuri ammma fafur yaki se shirinsa yakeyi, sannan sam yadena shiga gidansu ya kashe wayoyinsa dan karma anemeshi.
Hanan da Jalila suna zaune suna hira da Inna a dakinta, Hanan tanata chatting ta dan dago ta kalli Jalila tace
“queen Haidar baya daga waya lafiya kuwa?” tai maganar a shagwabe
Jalila tace “kunfi kusa ai, nima bamuyi waya ba”
“nifa duk na damu a satin nan sam banji muryarsa ”
Inna tace “waye kuma haidar, da kike kula dashi haka”?
“Sirikinki ne, kwanan nan zezo kiganshi kyakyawa dashi in gayamiki yafi mijinki Alhaji kyau, kai kaf family dinku babu me kyansa”
Inna tace “ke tafi can, anya akwai me kyan mijina, ai Imamu mijin Mairona ce kawai na yadda yafi mijina kyau”
Jalila da sauri tace “Imamu kuma, shine mijin kanwartaki?”
“Eh shine shima dan uwanane, dan Autan su Imamu shine baban Hanan”
Jalila tace “Inna to wai ina suke yanzu ita kanwartaki”
Inna ta danyi shiru tace “bari yarinya ta, Mu ukune a gurin babanmu nida mairo da yayanmu magaji, ni na Auri Alhaji dan yayar Innarmune, itakuma mairo ta Auri Imamu, dan kanin babanmu ne, yana son mairo sosai, ‘yan fashine suka addabi garinmu, watarana suka shigo suka harbi wasu, sukayi Garkuwa da wasu, akayiwa wasu daga cikin matan fyade aka kora dabbobinmu sannan aka sakawa bukkokinmu wuta, kafin hakan tafaru yayanmu magaji ya saida wasu daga dabbobin gadonmu nida mairo yarabamana kudin, to lokacin da ‘yan fashi suka shigo garin mairo da mijinta basu dawo daga kiwo ba, A wannan harin aka kashe yaya magaji, nida Alhaji da matar Yaya magaji, da yaranta da nawa yaran muka gudu abun be ritsa damu ba, haka muka baro garinmu muka taho nan bauchi, lokacin duniya na kwance akabamu masauki, muka cigaba da rainon yaranmu, bayan wasu shekaru A hankali bayan wasu shekaru muka dinga haduwa da wasu daga cikin ‘yan uwanmu, duk inda mukaa hadu sesu sedawo nan gurin mu su zauna, a haka har mukayi wannan yawan, Amma har yanzu danake miki wannan zancen bansan inda mairo da imamu suke ba, ni ko bangansu ba inga zuri’arsu, Hanan tana matukar kama da ita, amma dana ganki senaga kunfi kama da ita, komai naki irin natane, Allah yasa ke irin zuri’arta ce” Inna ta fashe da kuka,
Jalila tace “Allah sarki inna, kiyi hakuri kinji Insha Allah zaki ganta ko ‘ya’ yanta, amma ni ban san kakannina ba inada kanan shekaru suka rasu, maybe da Yaya Jawwad ne ze iya sanin wani abun amma ni bansan komai akansu ba”
Suna cikin maganar Yusuf yayi sallama ya shigo, su Jalila suka gaiaheshi ya amsa, ya nemi guri ya zauna ya kalli Jalila yace “‘yar Baba kije palourn kasa, second floor kinada bako” gaban Jalila ne yai mummunar faduwa da sauri Hanan ta mike zaune tace “Bako kuma?”
“Kece Jalila?” Yusuf ya tambayeta shiru Hanan tayi tana tunanin waye wannan kuma, ya biyo takan Yaya Yusuf, jiki a sanyaye Jalila ta mike, Hanan ma mikewa tayi zata biyo Jalila, Yusuf yace
“ke dawo nan ki zauna, koke nace kije?”
Hanan tadawo ta zauna ta zumbura baki, tana nazarin waye kuwa wannan”
Jalila taje daki ta dakko hijjabinta har kasa tasaka, ta tafi a hankali ta tura kofar palourn ta shiga kanta a sunkuye tayi sallama.
“wa’alaikum salam warahmatullah” dan daga kai tayi ta kalleshi ido hudu sukayi tai sauri sunkuyar da kanta
Yace “karaso mana queen” Jalila a ranta too queen kuma iyayi, ta karaso ta zauna a kujerar da take facing dinsa,
“barka da dare”
“yawwa barkanki dai my queen fatan kina lafiya?”
“Am not queen Jalila sunana”
Murmushi yayi yace “to ai duk daya, koba haka Hanan take ce miki ba, kuma aini ya cancanta in fadi wannan sunan koba hakaba?”
Shiru Jalila tayi, “to ya gajiyar biki?”
“Gajiya tabi lafiya Alhamdilillah”
“Masha Allah, ni sunana Ahmad nasan kinganni a bikin Yusuf, kobaki ganni ba nina ganki kuma kinyimin Jalila, nagayawa Yusuf ya nemamin izinin zuwa gurin ki a gurin daddy, daddy yabani damar inzo, sannan yace inmuka cika wasu sharuda sannan kin amince ze bani ke” ya danyi shiru sannan yace “Jalila harga Allah kinyimin inasonki Aurenki nakeson yi tsakanina da Allah, amma bazan miki doleba se abunda kikace”
Shiru Jalila tayi tana wasa da yatsun hannunta
“queen kice wani abu mana” still ahiru tayi
“ko banyi miki bane? Ki gayamin ba komai, bazan miki dole ba”
Girgiza kai tayi alamar A’a yace “to gayamin abunda ke ranki”
Fafur Jalila taki magana yai murmushi yace “dago ki kalleni”
Noke masa kafada tayi kaman yanda yara sukeyi sannan tace “to ni me zance?”
“wow muryar ki da dadi Jalila, gaki shagwababbiya” murmushi ta danyi
Wayartace tafara ringing, ya kalleta yace “daga wayar mana”
Ta daga wayar tasaka a kunne Nanace tace “Baby ya kike dan Allah yaushe zaki dawo”?
“kai Nana wai yaushe zan dawo ba rana sena gama hutawa” Nana tace
“department dinku sukoma tun last week, nai shiru ban fadawa Abba kun koma ba, karyayi miki fada, sannan an kafe exams dinku yau”
“dagaske menasamu?”
“nidai nasamu upper credit, but Baby wallahi you are the most luckiest girl i ever seen in my life, kaf department dinku babu me points dinki, se zancenki ake, wasu sun sanki wasu basu sanki ba, lectures sunata a nuna musu ke”
“Alhamdilillah yanzu ina Yaya Jawwad kwana biyu baya daga waya?”
“Baby da banyi niyyar gayamiki ba, shiyasa naketa damunki ki dawo, Abba ya yadda Naja ta Auri yaya Jawwad, memakon yaya Jawwad yace masa bayasonta amma yayi shiru kinsan halinsa nan da kwana tara za’a kai kudin Auren sa gidansu Naja”
Jalila ta manta da wani Ahmad a gurin a razane tace “What, Nana dagaske kike dan Allah”
“Wallahi Baby dagaske nake, gashi yanata fama da Yaya Jalal shima wai ranar Asabar ze bar kasar nan, da se wani satin ze tafi, amma wani abun akayi masa a gidansu, yace wallahi inya tafi bazasu kuma ganinsa ba, ke yaya Jawwad yana cikin damuwa, gashi kusan kullum se Naja tasa anyi masa fada”
Mikewa Jalila tayi ta dafe goshinta tace “Nana am coming back this week Insha Allah, Idan har Abba yabari akayi Auren nan an rusa Rayuwar Yaya Jawwad gaba daya, kuma ina tausayin Hanan, zan dawo a satin nan Insha Allah, dole afasa Auren nan”
Sukayi sallama da Nana ta mike zata koma cikin gida Ahmad yace “Jalila lafiya kuwa? Naga kin shiga wani yanayi ko akwai damuwa ne?”
“A’a bakomai”
“Bari in kyaleki, nadawo na karbi lambarki zamuyi waya” gyada masa kai tayi ta fice da sauri.
Jalila na zuwa Hanan tafara yimata tambayoyi “Jalila wai waye Yaya Yusuf yace kinyi bako?”
“ke kyaleni dan Allah wani ne nina manta sunansa ma, Hanan satin nan, maybe nan da kwana uku zankoma Kano”
“Jalila meyasa? Saboda Yaya Yusuf?”
“A’a Hanan Akwai matsala ne, dole inkoma”
“Matsalar mene haka? Jalila kar mutan gidan nan su zargi ko wani lefi sukayi miki”
“bahaka baneba Hanan, Ankoma makaranta sannan ina bukatar zuwa gida”
Hanan tace “hmm ko dai saboda Jalal ne? Gayamin wani abune yafaru dashi ne?”
Cikin damuwa Jalila tace “Hanan dagaske Jalal yake in yabar kasar nan baze dawo ba, wai anyi masa wani abu a gidansu, fitarsa kasar waje hatsari ne” Jalila ta boyewa Hanan batun kai kudin Auren Jawwad kar Hanan ta damu.
Hanan taso ta tsokani Jalila amma ganin ta in serious mood yasa ta fasa tace “gaskiya yakamata kikoma bari daddy ya dawo se muyi masa magana”
Yusuf ne yayi knocking kofar dakin nasu sannan ya shigo da sallama ya kalli Jalila yace “Jalila yaya kun gaisa da Captain Ahmad?”
“Eh yaya Mungaisa”
“to bazamuyi miki dole ba, kigaya masa abunda ke ranki, inkinada wanda kikeso kigaya masa tun wuri”
“tana da wanda takeso fa, tana jin nauyin kane bata fada ba”
Yusuf yace “inkika kuma magana sekinyi tsallen kwado sau sittin a gurin nan, dake nake magana?”
Shiru Hanan tayi yacigaba da cewa “Jalila banason mu cutar dake gidan nan ba’ayi wa kowa dole, nayiwa daddy maganar, in ba kyasonsa ki gaya masa kinji”
Jalila ta gyada kai, yace to seda safenku.
Yusuf na fita Hanan tace “ke Jalila captain Ahmad ne dama, to tun wuri kice masa bakya sansa, har sunkai magana gurin daddy Yaya Yusuf baya wasa, wallahi dagaske suke, in Baba ya tambayeki kice be mikiba ba kya sonsa, kinada wanda kike so”
“Haka nace miki bana sonsa? Wanake dashi a yanzu danake so? To ni yayi min”
“karya kikeyi wallahi, Jalal shine kike so, ba wani aranki seshi”
Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!
Ina yinku ABDUL JALAL group irin sosai din nan fa 😍😍😍 inajin dadin Comments dinku, kuna Comments kana karamin kaimi typing duk bayan kwana biyu, kuna bari ina lalaci posting duk sati 😜😜😜
Share please
I want comments not stickers or just thanks
Daga alkalamin Aysher cool.