Hausa novels

Halysaah Page 49 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 49…Abdul ya zagayowa ya tsaya gabanta yana kallonta ya mika mata hannu yace “Give me what you are hiding” Sosai gabanta ya fadi tana kallonsa ta kasa cewa komai, tsawan da ya gigitata ya daka mata yana mata wani kallo, lkci daya hawaye ya cika idonta ta mika masa wayoyin da kudin hannunta, amsan su yayi yana kallon su, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, Calmly yace “Who gave you this?” Kasa dago kanta tayi hawaye na zuba idonta tana jiran jin saukan mari at anytime, juyawa yayi ya bar wajen ya nufi dakinsa yana rike da wayar da dollars din, Khaleesat ta bi sa da kallo har ya shiga dakin, taji kafafuwanta sun kasa daukanta tsabar yanda ta tsorata, da kyar ta karasa ta zauna gefen kujera tana jin bugun zuciyarta na karuwa, tana goge hawayen dake sauka idonta…. Abdul na shiga dakinsa ya zauna gefen gado ya ajiye dollars din yana jujjuya wayoyin hannunsa ganin iri daya ne with different colors, kuma duk a mace suke babu caji, Exactly irin second phone din da yake using ne, ya mike ya tafi yayi plugging din wayar Jay da chargern sa, sannan ya koma ya dau kudaden ya kiraga yaga 1k dollar ne, ya ajiye su saman gadon yana kallonsu, jin za a tada sallah a masallaci ya shiga bathroom dinsa, bayan ya fito zai tafi masallaci ya kulle Bedroom din nasa da makulli, har sannan Khaleesat na zaune parlor ta kasa motsi a inda take zaune, tana ganinsa ta mike tsaye a tsorace tana kallonsa, ko kallonta bai yi ba ya nufi kofa ya fita daga parlon, a sanyaye ta tafi dakinta hawaye na sauka idonta zata je tayi alwala ita ma. Abdul na dawowa masallaci bayan ya bude dakinsa ya shiga ya dau wayar Jay ganin har yayi caji ya kunna kansa, ya cire wayar jikin chargern ya dauko wayar Ajay ya jona, sannan ya koma gefen gado yana duba wayar tunda babu lock jiki, gani yayi ba Sim card a wayar, ya dai ci gaba da dube dubensa, babu inda bai shiga ba a cikin wayar yana bincike but bai ga komai ba don babu any form of Media a wayar, messages ma ko daya bai gani ba, bayan ya shiga Email yaga Business class flight ticket da Jay ya siya mata da zata dawo Nigeria, ya dinga kallon Ticket din for almost 30 seconds, sosai fa yayi mamaki ba kadan ba, fita yayi daga Email din ya shiga Gallery din wayar hoping zai samu hoto a ciki, a nan ne ya ga Hotunan Jay, wanda duk yawanci tare zaka gansu da Ajay, Zooming pic din Jay yayi yana kallonsa with full concentration, sai kuma ya koma kan Ajay shi ma ya dinga kallonsa baya ko kiftawa, at once ya gane da shi ne suka samu Encounter a Amurka, but sai ya ga Ajay looks familiar, where did he know him from? mikewa yayi da sauri ya dauko wayarsa ya shiga Instagram dinsa yayi Searching sunan da yake tunanin ya san sa da shi a Instagram, amma sai yaga account dinsa is locked, komawa yayi ya zauna ya kasa dena kallon hoton Ajay babu ko kiftawa, can ya kara duba hoton Jay yayi Zooming dinsa yana kallo, kawai bai san me yasa yaji yafi jin tsanar Jay ma akan Ajay, mikewa yayi ya dauko wayar Ajay don har ya ɗan yi caji, babu lock a wayar hakan ya sa ya shiga, nan yaga Ticket da aka siya mata from Kano to Lagos, iya shi kadai ya gani a wayar babu hotuna, babu WhatsApp, babu komai, hatta sim card babu a wayar, fita yayi daga dakinsa ya tafi dakin Khaleesat ya sameta tana sallah, tun da taga yanda ya tsaya mata a bakin kofa taki idar da sallan da take yi da wuri kamar me Tuhajjud, muryarsa taji cikin tsawa yace “Idan baki sallame sallan nan da kike yi continuously ba zaki ga abinda zai faru yanxu” Sosai jikinta yayi sanyi, haka nan ta daure ta sallame sallan tana ji kamar bango ya tsage ta fice daga dakin tsabar tsoronsa, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta hade rai taki kallon direction dinsa barin da ta ga both wayar Jay da Ajay a hannunsa, ya karaso cikin dakin yana mata wani kallo cikin daga murya yace “Wayoyin su wanene wannan??” Still taki kallonsa, wani tsawa yayi mata yace “Are you stupid? Are you Mad? Ina maki magana kina kallon wani direction din daban?” Sai a sannan ta kallesa, har sannan fuskarta a daure yak, amma Allah ya gani daurewa kawai take, yace “I am asking you whose phones are this?” A takaice tace “My Housemate and his Brother…..” Ya dinga kallonta babu ko kiftawa, she just realized she said her Housemate to him, ta kallesa a sanyaye, ganin kallonta yake yi baya ko kiftawa, ta sauke idonta a hankali tace “I mean….” Ya girgiza kai yace “No, you mean ur Housemate, dama Housemate dinki ne ranan da na je kika min karya? Dama gida daya ku ke tare da wannan katon banzan da na gani?” Gani tayi shiru fa ba nata bane, don shirun nata duka kawai zai ja mata, in ma maganar tayi ba hakan zai hana ya doketa ba in yayi niyya, ta wani hade rai duk da mugun faduwan da gabanta ke yi, a takaice tace “Eh, he is my Housemate, Nancy moved out of the apartment shi ne shi ya shigo, and i have no choice but to live with him, tunda bana son in dinga bothering dinka da Expenses, kuma naga in just few months za mu yi hutu, dama nufina idan mun yi hutu sai in ce maka ka canza min wani apartment din since a sannan ne zaka yi renewing house rent dina” Kallonta kawai Abdul yake yi babu ko kiftawa, ita dai ta kasa kallonsa gabanta na faduwa tana expecting ta ji saukan mari at anytime a cheek dinta, Calmly yace “So, shi ne kike zaune gida daya da shi ku ke rayuwa, ku yi sharing same kitchen, same parlor and same corridor, if coincidentally kin fito daki shi ma ya fito sai ku kusa karo da juna ko? Ki fito babu hijab ya gan ki haka, ki fesa turare ki zo ki wucesa yana jin kamshi, in ma ya kama ki zauna ku yi hira da shi, in kinyi girki ya diba ya ci” Sai a sannan Khaleesat ta kallesa tace “I don’t mind if you believe me or not… But shi baya kwana gidan, karatu kawai yake zuwa yi ya tafi don suna da gidansu a Amurka” Abdul ya dinga kallonta, sai a sannan ya tuna abubuwa masu tsadan da ya dinga gani a kitchen sanda yaje, tun daga kan bottle water, cikin nutsuwa yace “Shi ne dalilin da ya sa kika fara min wasu stupid attitude kenan? Kin samu wanda yake siya maki duk abinda kike so a gidan har ma ya ɗebe maki kewa, To bari ki ji, ko duk jikina kunnuwa ne bazan taɓa yarda babu wani intimacy da ya hada ki da shi, ke kika san me kike basa da yasa yake siya maki abubuwa masu tsada yake ajiye maki a kitchen, sannan har ya cire kusan 5000 dollars ya siya maki Business class ticket kawai don ki dawo Nigeria….” Nan da nan hawaye ya cika idon Khaleesat, ta mike tsaye tana kallonsa tace “Ko me zaka fada bazan ce maka ba haka bane, amma put this at the back of ur mind, ba kowa ke da halin son taɓa warce ba muharramarsa ba kamar ka, kuma shi bai dau kudin Business class ticket wata tsiya ba shi yasa ya siya min, akwai difference sosai between you and him” Kallonta Abdul ya dinga yi da mugun mamaki, bata ankara ba sai jin saukan tagwayen mari tayi a fuskarta, ta fashe da kuka tace “Iya mari kawai?? ka kasheni mana ka huta kawai Abdul….” Ya fizgota da karfi yana huci yana kallonta da idanuwansa da suka yi jajir yace “Ni kike comparing da wani ɗan iska matsiyaci can??” Cikin kuka tace “May be if i do that you will change ur terrible ways, he made me realize i am dating a monster because of his kind attitude toward me, babu komai tsakanina da shi amma shi din mutum ne me kirki da sanin darajan ɗan Adam da sanin ya kamata, he always make sure i am fine, baya barina da damuwa komin kankantar sa, kuma ko da kuskure bai taɓa saɓa min ba a duk zaman mu da shi a America, kyawawan halayyarsa da irin yanda yake interacting yasa naji i am fed up with ur attitude, all this made me realize you are enslaving me ba sona kake ba, why not treat me the way he is treating me idan har sona kake da gaske? Bani da daraja da mutunci a idon ka, kullum cikin duka da cin mutunci nake a wajenka tun sanda baka aureni ba, iyayena ma basu da mutunci a wajen ka, to menene yasa baza kayi releasing dina zuwa inda za a ga mutuncina da na iyayena ba kuma a san darajata? Is it my father’s fault da kaddarar sa ta zo a yanda take? Ku kan ku kun san bai ci kudin mahaifinka ba, bai salwantar masa da kayansa don son rai ba, ba ku tunanin ko ba ta sanadin mahaifina ba sai kun yi asaran kudaden nan tunda ku ma a kaddarar ku hakan take? Kuma meye zaka daga min hankali a kan su bayan kace baza ka sakeni ba kuma kowa yasan igiyar auren nan a hannun ka yake? Duk cikin rashin lissafin naka ne yasa kake kishi da su bayan ka ri ga ka aureni??” Turata yayi har sai da ta bugu sosai da bango sannan ya juya ya fice daga dakin kamar zai tashi sama. Wajen karfe dayan dare Khaleesat dake kwance taji an bude kofar dakinta, da kyar ta bude idonta da yayi mata nauyi tsabar kuka da ciwon kai, tana ta kwance a yanda take bata juya ba duk da bata ga ya kunna wutan dakin ba, duvet din jikinta ya sauke kasa ya jawota kusa da shi yayi kasa da murya yace “Kinsan da igiyata a kanki kike da effrontery din kawo min maganar wani katon banza can har kike comparing dinsa da ni? What wrong have i commit to you da kike ganin shi yana da halayya masu kyau wanda ni bani da shi” Khaleesat taji zuciyarta na mata wani zafi jin useless question din da yake tambayarta, tayi kamar bacci take taki motsawa, yayi kasa da murya yace “Khaleesat…” Still tayi kamar bata jin sa, duk da idonta a rufe yake she could feel the tears accumulating in her eyes, kiranta ya sake yi a hankali jin bata amsa masa ba ya juyota zuwa jikinsa yana kallonta cikin duhun, ya dora goshinsa kan nata yayi kasa da murya yace “But you know i love you so much Khaleesat, da bana son ki bazan yi wasting shekaru kusan biyar a kanki ba, i gave you the best of everything i can kema kin sani” Bata san sanda ta turasa ba tsabar wani tsanarsa da take ji a rai jin abinda yake cewa, ta mike zaune muryarta na rawa tace “Duk saboda kana sona kake dukana kake marina kamar jaka? Shi ma duk cikin so ne? Plss ka koma ka fahimci menene kalmar so….” Sauka ta fara kokarin yi daga kan gadon tana shesshekan kuka, ya rikota da sauri yaki barinta ta sauka, ta fashe da matsanancin kuka sosai tana jin zuciyarta na mata zafi saboda bakin ciki, ya rungumeta gam a jikinsa, a hankali yace “Kiyi hakuri, amma Allah ya sani ina son ki, in ma baki yarda ba i owe you no explanation tunda Allah shi ya sani, kuma today should be ur first and last warning Khaleesat…. I mean in ur life do not ever ever dare compare me with any stupid guy born of a woman, kar ki sake kawo min zancen wani ɗan iska ko shi wanene a kunne na, sannan bazan yi taking zaman da ku ka yi tare da shi and whosoever da kuma alakar ku personal ba because you are my wife now, duk wannan ya zama pass and shi ne looser, kuma har abada babu wata alaƙa da zai sake hada ki da shi don ubansa har duniya ta nade kuwa, ba wai ban ji zafin alakar da kika yi creating da su a America bane a raina, fadin zafin da naji ma is just an understatement wallahi, amma considering the fact that you are my wife yasa nayi letting bygone to be bygone, so let me keep using that to calm my self kar in masu abinda ke raina….” Wani mugun tsanarsa ne ke karuwa a ran Khaleesat jin kalmomin da ke fitowa bakinsa, wasu hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta tana tausayin kanta da irin monster din da Allah ya bata as miji, kokarin kwace kanta take yi a jikinsa zata sauka daga kan gadon yaki saketa yace “Ohk bokare min za kiyi don ina baki hakuri? But i said i am sorry, and i promise i won’t hurt you again, na dena dukan ki….” Ƙin ce masa komai tayi tana kuka a hankali, ya kwantar da ita kirjinsa yana shafa gashinta a hankali yace “Billah ina son ki Khaleesat, duk abinda kika ga ina maki saboda ina son ki ne, but kin ki bani hakkina saboda ke akwai wani plan din a xuciyarki, probably ma su suka koya maki haka” Daga kai Khaleesat tayi ta kallesa tsabar bakin ciki bata san sanda tace “Ai ba kowa ne bashi da aikin yi kamar ka ba” Shiru yayi yana kallonta babu ko kiftawa, ita kanta shirun tayi gabanta na faduwa don bata san sanda kalman ya fito bakinta ba, Instead sai ji tayi yayi kasa da murya kamar me rada yace “Where is the Lubricant?” Sosai gabanta ya fadi jin abinda yace, yana rungume da ita jikinsa ya bude bedside drawer kamar yasan nan din ta ajiye kuwa, ya laluba ya dauko, shesshekan kuka ta fara yi zuciyarta na bugawa, yayi kasa da murya yace “Kinsan tsinuwar Allah kike tara ma kanki kuwa?” Cikin kuka tace “To ai ba ni bace” Yace “To waye?” Muryarta na rawa tace “Wallahi ban sani ba” Cikin kwantar da murya yace “Promise me today will be different plss Baby” Ta kasa cewa komai hawaye masu zafi na sauka idonta ga faduwan da gabanta yake yi, gently ya fara cire kayan baccin jikinta yana kallon kwayar idonta cikin duhun dakin, a wannan dare Abdul bai yi bacci ba tsabar bacin rai, sai dai bai hantareta ba bai zageta ba, bai kuma doketa ba, haka ya mike ya fice kawai ya bar mata dakinta ya koma nasa, ya shiga bandaki ya sakar ma kansa ruwan sanyi duk da mugun sanyin da ake a garin, bayan ya fito ya saka Pajamas dinsa ya kunna karatun qur’ani a wayarsa ya kwanta amma ko rintsawa bai yi ba har asuba. Tunda Khaleesat ta idar da sallan asuba take zaune kan darduma bayan ta gama azkar dinta, gaba daya jikinta a sanyaye yake, zuwa yanxu kam sosai lamarin nan ya fara bata tsoro, ko baccin kirki bata yi ba daren jiya tsabar yanda abun ya tsaya mata a rai, kawai tayi deciding tayi amfani da abubuwan da Nenne ta kawo mata zuwa anjima, sai da gari ya waye sosai sannan ta mike tana tafiya a hankali ta fita daga dakin zuwa parlor, sosai gabanta ya fadi ganinsa zaune a parlon da cup din shayi a gabansa, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa ta tafi ta durkusa ɗan nesa da shi a hankali tace “Ina kwana” Maimakon ya amsa sai ji tayi yace “Meye nake perceiving a cikin kitchen kamar maganin gargajiya?” Khaleesat ta daga kai ta kallesa, shi ma kallonta yake fuskarsa babu yabo babu fallasa, rasa me zata ce masa tayi tana wasa da fingers dinta, a fusace yace “Bakya ji na ne?” Bakinta na rawa da kyar tace “Nenne ce ta kawo min” A takaice yace “Na menene?” Ta sauke idonta tace “Magani ne kawai, dama ta saba bani in dinga amfani da shi a gida” Mikewa yayi yace “Mu je ki bani su” Ta shi tayi kamar munafuka ta nufi kitchen din ya bi bayanta, ita kanta taji kamshin itatuwan da ta shiga kitchen din, ta bude inda ta ajiyesu ta dauko, ya mika hannu, ta karasa ta basa, yace “Ba a min amfani da irin wa ennan abubuwan a gida” Kai kawai ta gyada masa, fuska daure yace “Kin ji me nace maki? Kar ki sake amsa idan ta baki” A hankali tace “Na ji” Juyawa yayi ya fice daga kitchen din ya koma parlor ya zauna, ya ajiyesu nan kasan tiles, tana fitowa daga kitchen yace “Get ready za mu fita, kuma kar ki bata min lokaci” Cikin sanyin murya tace “Toh” Dakinta ta tafi, bayan kusan minti talatin sai ga ta ta fito cikin shiri, dai dai nan shi ma ya fito daga dakinsa rike da wayarsa da car key, yana gaba tana biye da shi suka shigo parlor, ya dau ledan magungunan da Nenne ta kawo mata ya nufi kofar fita daga parlon ita dai tana biye da shi a baya, a booth dinsa ya saka ledan magungunan, sannan ya zaga zuwa driver seat, ita ma ta shiga front seat, bayan ya gama warming motar ya fita daga gidan. A sanyaye Khaleesat ta fito daga Office din Dr Mariya with different thoughts running her mind, ta ɗan juya ta kalli Abdul da ke bayanta shi ma ya fito office din likitan, ƙin kallonta yayi, hakan ya sa ta ci gaba da tafiyarta slowly, sai ga Dr Mariya ita ma ta fito daga Office din zata masu rakiya zuwa parking space, hira suke yi kawai da Abdul suna tafiya a tare, ita dai Khaleesat na can gabansu, har dai suka fita daga reception din hospital din suka karasa parking space, Dr Mariya na kallonta tana murmushi tace “To amarya plss inji labari opposite of this kin ji? There is nothing wrong with you, In kinyi amfani da duk shawararin da na baki komai zai tafi dai dai in sha Allahu, hakuri kawai za ki yi it’s always like that dama, Allah Ubangiji ya bada zaman lafiya, in dai na samu lokaci zan zo har gida mu gaisa” a hankali Khaleesat tace “To Nagode Aunty, Allah ya kawo ki lafiya” Dr Mariya na murmushi tace “Ameen” Sai kuma ta kalli Abdul tace “To Barrister ku gaida gida, ina kuma tabbatar maka in sha Allah matsalar ta zo karshe tunda kaga mun dade ina magana da ita, kuma hopefully ta dau duk abinda nace mata” Yace “Thanks for your time Dr” Zagawa yayi ya shiga driver seat, Khaleesat kuma ta shiga front seat, ya tada motar suka bar hospital din, har suka yi nisa bai ce mata komai ba, ita ma dae shiru tayi tana ta tunane tunane, sae da taga unguwan da suka shigo tayi realizing gidansu ya kawosu, bayan yayi parking ya sauka motar, ita ma ta sauka, booth ya tafi ya bude ya ciro ledan da Nenne ta kawo mata, da mamaki tana kallonsa tace “Ina zaka kai wannan?” A takaice yace “Momy zan kai ma, naga tana dealing da irin abubuwan nan, she can use it if she want, ke dai baza kiyi amfani da su ba a gidana” Khaleesat ta marairaice masa tace “Noo pls, ni dai gwara kayi disposing dinsu don Allah” Fuska daure yace “Bazan yi disposing din su ba” Bata san dama haushinta ne fal zuciyarsa ba bayan Dr Mariya ta dubata ta tabbatar masa lafiyarta qlau babu wani abu da yake hindering passage dinsa, everything is normal, kawai hadin kai taki basa, Khaleesat ta sunkuyar da kai a sanyaye bata sake cewa komai ba, ya nufi entrance din gidan nasu, tana tafiya a hankali ta bi bayansa har suka shiga parlorn gidan, da mamaki Momy ke kallonsu tace “A’a, daga ina ku ke da safen nan, sannun ku da zuwa” Abdul ya zauna ya gaisheta, ta amsa tana kallon Khaleesat da ta zauna kasan carpet tana gaisheta, Momy ta amsa da fara’a sosai fuskarta tana welcoming dinta, Momy na kallon Abdul tace “Amma ba daga gida ku ke ba ko” Yace “Eh, daga asibiti mu ke” Da mamaki Momy tace “Asibiti kuma, waye ba lafiya?” A takaice yace “Bata ji dadi bane, amma da sauki” Momy na kallon Khaleesat tana murmushin karfin hali tace “Allah sarki, sannu Mamana, Allah ya kara lafiya” Sai kuma ta kalli Abdul tace “Ko wajen Dr Mariya ku ka je?” Yace “Eh” Mikewa yayi ya ajiye mata ledan magungunan kusa da ita yace “Kakarta ce ta kawo mata wnn jiya, ni kuma kin san bana son irin abubuwan nan na gargajiya shi ne na kawo ko zaki yi amfani da su ke” Momy tayi kuri da ido tana kallon ledan da mamaki, sai kuma ta dauka ta bude da sauri, lkci daya ta saita kanta tana murmushin karfin hali tace “Allah sarki, ai kam nasan halin ka baka san itatuwa, zan ko yi amfani da su dama nawa sun kare tas” Ita dai Khaleesat kasa dago kanta tayi, Momy was shock har cikin ranta amma tayi karfin hali take wayancewa, can ta kalli Khaleesat tace “Amma baki fara amfani da su ba ko” Khaleesat ta girgiza kai ba tare da ta kalli Momy ba tace “A’a jiya ta kawo min banyi amfani da komai ba” Momy tace “To to, hakan yayi” Ta kalli Abdul tace “In dai an samu wasu a dinga kawo min kawai” Mikewa yayi yace “Za mu koma Momy” Momy tace “Da wuri haka? To wai ka koma aiki ne?” Yace “Ban koma ba tukun” Momy tace “Toh shikenan, Allah ya tsare nima in sha Allahu ina nan shigowa in kawo mata turarrukan wuta da na jiki” Shi dai bai ce komai ba ya nufi kofa, Khaleesat ta mike tana yi ma Momy sallama, Momy duk fa a rude take ta gyada mata kai kamar kadangariya tace “To Mamata, sai na shigo, ku gaida gida, maza bi sa ku tafi” Daga haka Khaleesat ta bi bayan Abdul da har ya fita daga parlon, Momy ta dau wayarta har tana tuntube ta shiga dakin dake downstairs ta fara kiran Dr Mariya don family Dr dinsu ce for long, Dr Mariya na dagawa suka gaisa da Momy cikin fara’a, Momy tace “Yanxu Abdul ya zo min da matarsa yace daga asibiti suke, naga duk ba shi da walwala nasan yana da zurfin ciki bazai gaya min ko menene ba, shi ne na kira inji lafiya dai ko Dr? Ko juna biyu gareta? kinsan dama yace bai son haihuwa da wuri, in dai juna biyu ne da ita gwara in yi dubara in dawo da ita wajena don ni dai ina son ganin jikana, kar yaje ya bata wani abu da zai lalata cikin taje ta sha” Dr Mariya tayi dariya sosai, bata boye ma Momy komai ba tayi mata bayanin dalilin zuwansu Asibiti, Momy ta sauke wani irin ajiyar zuciya ba tare da tasan tayi hakan ba, sai kuma ta bige da cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, kinsan yarinya ce fa, duka duka Allah yasa tayi shekara ashirin, har da yarinta abun nata dae” Dr Mariya tace “Wallahi nima haka nace masa don dae in kwantar masa da hankali kar ya dinga jin haushinta, amma shekara ashirin ai ba yarinya bace Hajiya, aka ma er shekara sha biyar aure ta zauna balle er shekara ashirin, ni dai na bata shawarwari Allah ya sa tayi amfani da shi, kar tun yana hakuri da ita hakurinsa ya kare a fara samun matsala gaskiya” Murmushi kawai Momy take tana Allah Allah su gama waya da Mariya ta kira Godiya, daga karshe Momy tace “To Allah ya sa ta dau shawaran naki Dr, kuma zan yi ma yayarsa magana ita ma taje gidan anjima ta kara nutsar da ita in sha Allahu” A haka Momy suka yi sallama da likitan, Momy tayi wani dariya tana girgiza kai sannan ta fara dialing number Godiya, aikin miliyan biyu ai ba wasa bane, sun dade suna waya da Godiya a waya, daga bisanni suka yi sallama, Momy na ta murmushi ita kadai bayan Godiya ta sake jadadda mata Malamin yace lokacin ma da ya dibar masu za ayi sakin baza a kai haka ba, don gab ake da yin sakin cikin kwanan nan kuwa, Meemah da ta shigo dakin ta tarar Momy na waya ta zauna duk tana sauraron conversation dinsu har suka yi sallama tace “To shikenan Momy yanxu haka zai saketa ba mu ci ubanta ba na huce haushin abinda yayi min a kanta?” Momy tace “Ke wa ke ta wani cin ubanta? Ance maki shi ne a gabana sai kace wata yarinya? Ni dai in na samu Abdul ya rabu da ita an gama min komai, kuma hakan kadai ne a gabana yanxu ba shashanci irin naki ba, ke kinsan menene hada iri da talaka kuwa? Ke kiji matsiyaciyar kakarta har ta fara shige shigen malamai tana kawo mata asiri banda Allah yasa Abdul din ya gani, to karyarsu ta sha karya wallahi, cikin kwanan nan zai kora masu ita bayan ya saketa” Mikewa Meemah tayi ta fita daga dakin don kwata kwata ba haka ta so ba ita, so kawai tayi a bar ta tayi ma Khaleesat dukan mutuwa ko zata jin sanyin abinda Abdul yayi mata a kanta.*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

Back to top button