Hausa novels

Karfe A Wuta Chapter 106 By Ayshercool

106″I promise that, ina tare da kai ɗari bisa ɗari, komai tsanani da wahala, is enough yakamata ka huta haka, masifun nan sun yi yawa”Ya sauke ajiyar zuciya ya ce “Ina ga haryanzu sakamakon laifuffukana ne suke ci gaba da bibiyata”.Ta ce “A’a, Allah ba azzalumin sarki bane ba, kuma yana son bayinsa masu neman gafararsa. Wannan wata jarrabawa ce ta daban, kuma zamu cinyeta ita ma in sha Allah, sannu Vi” ya jinjina mata kai kawai bai sake cewa komai ba.Wayarta ta ciro, ta lalubo lambar Alhaji mu’azzam, ya ɗaga tare da yin sallama, ta amsa masa ta ɗora da cewa “yallaɓai ka ga abin da ya faru da Viper?””Wallahi ɗazu na gani Nabila, raina yayi mummunan ɓaci, na je Kano ne, amma anjima kaɗan zan shigo Abuja in sha Allah, kuma already na yi magana da ministan tsaro ma, za ayi bincike a kan lamarin””Wane bincike kuma, ana cewa wai sai an hukunta shi yayi harbi ba bisa ƙa’ida ba, ga harbi da aka yi masa, ni idan har haka aikin yake, kawai zai ajiye musu aikinsu, wannan wahalar ta isa haka””Ki yi haƙuri Nabila, na san halin da ku ke ciki, na kuma san wahalhalun da ya sha, duk kitumurmurar indabo ce, ina kyautata zaton an ce an sake shi ma, sai dai na zo kawai” tana cikin maganar wasu sojoji su uku suka shigo, da alama manya ne sosai a cikin rundunar tsaro, ta katse wayar.Joseph ne ya ƙame ya sara musu, sannan ya kalli Nabila ya ce “Ko zamu ba su wuri?” Ko kallonsa ba ta yi ba ta ce “Ba in da zani”.Ɗaya ya ce “Sannu Viper”Viper ya jinjina kai sannan ya ce “Thank you Sir”Nabila ta ce “Da gaske ne wai sai an hukunta shi saboda yayi harbi?”Suka kalleta gaba ɗaya, ɗayan ya ce “Muna tattaunawa a kan lamarin ne, an ce ba shi yayi harbin ba, Dss ne, kuma mun duba bindigarsa, yayi harbi da bullet biyar”Ta ce “Yanzu idan na ɗauki bindiga zan harbeka, ga bindiga a hannunka tsayawa zaka yi sai wani ya baka order zaka kare kanka?” Ba ta damu da mamakin da ya bayyana a kan fuskokinsu ba ta ci gaba “A matsayina na lauya nake yi muku magana, wadda ta san ‘yancinta, ni ba soja ba ce ba, kar ku yi expecting wata special girmamawa daga gare ni, na san ƙarshenta dai ace a kashe ni. Yanzu da an kashe mini shi, gawarsa kawai zaku kawo mini kuna yi wa gawar faretin banza da na wofi, babu lallai a samu hukumar ta sake bi ta kaina a matsayina na matarsa.Masu laifin da ya taimaka aka kama, ba ƙasa ya yi wa aiki ba? Harbin da aka yi masa bai isa ba, kuma sai an yi masa wani hukunci, ga suna an ɓata masa an kira shi da ɗan ta’adda amma ba ku ce komai ba”Viper ya ce “Nabila””Ka ƙyaleni Vi, sai dai a kashe ni, kun san abin da ya yi going through in his life, washegarin tarewata da aurenmu, ku ka ce lallai ya zo bakin aiki, yazo kuma yayi abin da ku ke so, kuma this is what he deserves, da haka za a saka koya wa matasanmu ƙauna da kishin ƙasa? Masu laifi na sharholiya masu kare ƙasa ana gana musu azaba, a kan laifi ƙanƙani, i will fight for his right” numfashinta sama yake yi sosai cike da ƙunar zuciya da takaici. Viper kuma ba shi da ƙarfin da zai hanata, saboda jirin da yake ji, da kuma jinin da ake ƙara masa.Ɗaya daga cikin sojojin, da Nabila ke kyautata zaton shi ne babbansu, sai ya yi murmushi, cikin harshen hausa ya ce wa Viper “Kai ka auro zakanya kamar kai, she’s lioness and fearless, i like her confidence.Madam, we are working on your husband issue, muna supporting ɗin sa, a kan ayyukan da yake yi, kin san mu bamu da hurumin kama mai laifi, sai dai muna hana yi wa ƙasa ɓarna.Mun yi haɗin gwiwa da wasu hukumomin, Viper shi ya gano gidan, kuma tare da shi aka je, a ƙoƙarin kama masu laifin, aka fara harbe-harbe.Kuma mu bamu fitar da report na ga abin da ya faru ba, and abin da viper ya yi bamu gama yanke hukunci a kai ba, kin ɗauki zafi da yawa ki yi haƙuri, Viper aikin sa ba zai iya ajiye shi yadda ya ga dama ba, ya san dokar aikin ai. Kuma zamu bincika duk wanda yake da saka hannu, wurin wallafa wannan labarin zamu baki dama, ki kai ƙararsa ki yi haƙuri”Joseph kansa da ya fara tsuma, bai san hukuncin da za a iya yi wa Nabila ba, wannan kwarmaton da tayi ba, amma abin mamaki, sai ya ga an ɓuge da rarrashinta.Hawayenta take gogewa, amma sun kasa tsayawa, saboda wani irin matsanancin tausayin Viper, da ya takura zuciyarta, ya wahala da yawa.Ɗaya sojan ma, rarrashinta ya din ga yi, yana kiranta da ‘yar sa. “Da kin san matsayin da mutane masu muƙamin Viper suke da shi a rundunarmu, da baki ce ya ajiye aiki ba, amma muna baki tabbacin, zamu san abin yi a kan sa”Suka gama maganganun da za su yi, da rarrashinta suka fita.Matsawa ta yi sosai jikinsa, sai bin sa take da ido.”Abla””Na’am vi” ya juyo a hankali ya riƙeta ya ce “Ki zauna a kusa da ni, kar ki je ko ina dan Allah””Ina tare da kai in sha Allah vi””‘yar madara ta tafi ta bar rayuwata da duhu, kin fara hasakata amma kina ta so kema sai kin bar ni, Please”Ta katse shi ta hanyar cewa “Vi dan Allah ka yi shiru, Allah ya baka lafiya na ɗaukeka mu tafi, Allah ya baka lafiya”Ya sake cewa “Amin, indabo azzalumi ne abla, an kama shi, amma na san sakinsa za su yi, na yi iya yi na, na bar wa Allah sauran”Nabila ta ce “In sha Allah kuma zai isar maka”Ta lallaɓa ta tashi, ta yi alwala ta yi salla, ta zo ta yi masa alwala,  ya gabatar da salla yana kwance.Wasu sojojin ne suka sake shigowa su biyu, ba su ce mata uffan ba, aka cire masa jinin da yake shiga jikinsa, kasancewar ya ƙare, suka ɗaga shi zaune, ya jingina da jikin gadon.Suka sara masa, sannan suka juya za su tafi.Viper ne yayi gyaran murya, suka tsaya suka waiwayo.Yayi wa ɗaya alama ya zo, ya tako ya ƙaraso, Viper ya nuna masa abincin da suka shigo da shi.Babu musu sojan ya buɗe kowanne ya ci, ya rufe. Da hannu ya yi musu umarni suka tafi.Nabila tana jejjera masa sannu, ya kalleta ya ce “Ga abinci nan ki ci”Ta ce “A’a sai dai kai na zuba maka ka ci”Ya girgiza kai ya ce “Na ƙoshi”Cikin damuwa ta ce “Ka ƙoshi kuma, vi kamar dai akwai wani abu kuma da yake damunka” ya ɗago ya kalleta.”Menene ka gaya mini mana””Ba komai” ya faɗa a taƙaice.Ta marairaice ta ce “Please, Vi menene ka gaya mini””Jikina ne kawai babu daɗi””Sannu, bari na zuba maka, ko kaɗan ka ci”Baya son ta ci gaba da takura shi da tambayoyi, dan haka ya daure ya din ga haɗiyar abincin, tamkar yana haɗiyar magani.Ya gama ta bashi ruwa, ta dubi hannunsa ta ce “An cire bullet ɗin ne?” Ya jinjina kai ya ce “Tun ranar aka cire”.”Amma yaya aka yi ka je gidan da kanka, har tsautsayin nan ya faru?”Ya ɗan numfasa ya ce “Tun bayan rasuwar Nura, da ya gaya mini in dw zan samu Simon, na je na same shi. Shi ne ya gaya mini in da gidan yake, da abubuwan da suke wakana a gidan.So ban yi wani abu a kai ba, har tsautsayin nan ya faru, so bayan nan na daɗe ina fakon gidan, ina da informers ɗina a kan gidan. Sai dai yadda ake gudanar da laifuka a gidan, akwai tsari da taka tsantsan ɗin da babu lallai a gane, tun da da haɗin kan wasu daga cikin jami’an tsaro ake abin da ake yi.Nayi magana da shugabannina, muka yi haɗin gwiwa police da DSS, sai da na tabattar da Indabo yana gidan, muka je operation, sai dai bayan mun shiga, wasu daga ma’aikatan gidan suka far mana da harbi.An kama Indabo Naja’atu ma tana gidan, da wasu manya a ƙasar nan, police sun tafi da su, amma bana tunanin za ayi wani dogon bincike, rahotannin da na samu, kamar an ce an sake shi ma, amma bani da tabbas.Ina takaicin mutum kamar Indabo ace ya ci bulus a kan abubuwan da ya aikata, amma babu komai””Wallahi ba zai ci bulus ba, dole ya girbi abin da ya shuka ko da me yake yawo””No, kar ki kuskura ki ce zaki yi wani abu, yanzu ma abin da ki ka yi, ikon Allah ne ya tsallakar da ke, kin san suwa ki ka tsaya a gabansu ki na faɗar maganganu kuwa? Bani da ƙarfin hana ki a lokacin, amma da sun yi yinƙurin yi miki wani abu, to da zan nemo ƙarfin duk in da yake na baki kariya, ko da kuwa hakan na nufin na rasa raina ne.Gidan soja ne nan, ba a misbehaving, idan ki ka yi dole na karɓi hukuncin da za ayi miki. I don’t know why you are so much lucky””I am lawyer, ‘yanci na sani, dan haka ba ruwana da dokar koma gidan waye, mijina nake son ya samu ‘yanci”Murmushin gefen baki yayi ya ce “Kamar gaske””Da gaske nake Vi””Na ji amma ban yarda ba”Alhaji mu’azzam ne yayi sallama ya shigo, suka amsa gaba ɗaya, ya ƙarasa suka gaisa da Viper.Cikin damuwa ya ce “Sannu Viper, ya jikin?””Alhamdilillah””Ashe abin da ya faru kenan, nayi magana da shugabannin naku ai, kuma ministan tsaro ya bayar da umarnin lallai su yi magana su wanke ka”Nabila ta ce “Alhamdilillah, har shi ma ya ji?””Eh tun kafin na zo muka yi waya ai, kuma zamu gurfanar da gidan jaridar da suka sanar da wannan labarin ƙaryar, dan na san biyansu aka yi suka yi hakan”.Viper ya ce “Wai da gaske an saki Indabo?”Kankarofi ya jinjina kai ya ce “Ai ba a bari ma an sanar da ainihin abinda ya faru ba gaba ɗaya. Amma tabbas an bayar da belinsu, Bunkure ce ba a saki ba, dama ita tuntuni kotu ta bayar da umarnin a nemo ta, duk in da take a gurfanar da ita a gabanta. Ka yi haƙuri na san abin da ka ke ji a ranka, amma ina mai tabattar maka da wahalarka ba zata tafi a banza ba, kana yi wa ƙasa hidima da ranka da jikinka, dan haka dole ayi maka wani abu na girmamawa””Bana buƙatar komai, dama babban burina in ga an hukunta indabo, tun da ba zan samu hakan ba, shikenan na haƙura””Kar ka yanke tsammani Viper, tabbas indabo yana da connection da manyan ƙasar nan, da suke aikata ɓarnar su tare, shiyasa baya taɓuwa, duk da Nabila tayi breaking record ta jijjiga shi, alhalin yana kan kujerar mulki, kin yi namijin ƙoƙari sosai, amma ka bar shi da Allah, kai fa ko iya haka ka tsaya ka ɗauki fansa, ka jira kaga yadda Allah zai yi da shi kuma”.Viper ya sunkuyar da kai yayi shiru, sai huci da yake yi.Nabila ta dafa kafaɗarsa ta ce “Vi, ka yi haƙuri dan Allah, kar ka sanya damuwa da yawa a ranka, kamar yadda wasu daga cikin mutane ba sa girbar tarin alkhairin da suka shuka, suke komawa ga Allah, su tarar da sakamakon su a can, haka wasu daga cikin waɗanda suke aikata ɓarna, ba sa girbar abin da suka shuka, sai a gaban Allah. Wata shari’ar sai a lahira ai”Viper ya jinjina kai ya ce “Haka ne”Alhaji mu’azzam ya ce “Haka ne zancenki, ni kaina nayi iya ƙoƙarina, na ga Indabo an hukunta shi, amma abu ya gagara, shiyasa na haƙura na zuba wa sarautar Allah ido, ka yi haƙuri Viper, mun san an cutar da kai, amma ci gaba da jayayya da dagewa lallai sai ka ga bayan indabo, zai ƙara complicating abubuwa ne kawai, lokaci ya yi da yakamata ka yi relaxing, ka huta ka nutsu ka yi enjoying life ɗin ka. Indabo kuma ka zuba ido, hakkin abubuwan da ya aikata, ba zai taɓa barinsa ya rayu cikin aminci da kwanciyar hankali ba, ko a yanzu ka kafa tarihi, kuma rayuwar gidan indabo ta watse, dan haka ka yi haƙuri”Viper ya jinjina kai, “Yauwwa, Ubangiji Allah ya yi maka jagora, ya kawo maka ci gaba na ban mamaki”Suka amsa da Amin.Viper ya kalli Alhaji mu’azzam ya ce “Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi””Bakomai kar ka damu”Ya sake kallon Alhaji mu’azzam ya ce “Ka tafi da ita wurin hafsa dan Allah, ta huta ta kwana a can idan ban takura maka ba”Alhaji mu’azzam ya ce “Wane irin takura kuma, ba takura ai dama yakamata ta kawo mana ziyara”Nabila kuwa ta ce “Yaya za ayi na tafi na bar ka, wa zai yi jinyarka?”Viper ya ce “Kar ki damu, babu abin da zan nema na rasa in sha Allah, ana kula da ni””Ni gaskiya ko na tafi ba zan iya nutsuwa ba, hankalina ba zai kwanta ba, ka bari idan ka samu lafiya na je gidan nata”Ya tsuke fuska ya ce “Zaki fara ko? Ba zan ce ayi abu ba ki yi, sai kin yi gardama ko?”Ta marairaice ta ce “Dan Allah vi, wallahi hankalina…. Kallon da ya yi mata ne ya sanya ta yin shiru, idonta na cika da hawaye.Haka tana ji tana gani, ta tafi ta bar shi.Gidan hafsa gida ne haɗaɗɗe mai matuƙar kyawun gaske, Hafsa na ganin Nabila ta rungumeta tana murna.Ta kalli Kankarofi ta ce “Yallaɓai, ina ka tsinto mini ita, ko ta biyo maigidan ne ban sani ba, ba ta gaya mini ba?”Ya ce “Ina fa, wani case ɗin ya kuma tasowa” nan ya gaya mata abin da ya faru.Jiki a sanyaye hafsa ta ce “Kai, Allah ya isa tsakaninmu da wannan azzalumin mutumin, Allah ya shiga tsakaninmu da shi, amma ya jikin Yaya Al’amin ɗin?”Alhaji mu’azzam ya ce “Jikinsa da sauƙi, duk da yana da ƙarfin hali, amma an harbe shi a kafaɗa”Cikin tausayawa ta kalli Nabila ta ce “Ki yi haƙuri kin ji ƙanwata, in sha Allah zai samu lafiya” Nabila kuwa ɗan kukan da take maƙalewa ya ƙwace mata, Hafsa ta din ga rarrashinta, ta kaita ɗaki ta yi wanka ta bata kaya ta saka.Ta ci gaba da rarrashinta, daga nan kuma suka shiga hira, a lokacin Nabila take bata labarin wasu abubuwan, tun daga haɗuwarta da Viper.”Ya sha wahala sosai da sosai, ina matuƙar jin tausayinsa, daga wannan sai wannan”Hafsa ta ce “Kin san da haka amma ki ka din ga bori wai ba kya son aurenku””Ina da dalilina mai ƙarfi na yin haka, amma koma dai menene ya riga ya wuce, Ubangiji Allah ya sassauta masa”Hafsa ta amsa da Amin tare da ci gaba da rarrashinta.A ranar aka fitar da sanarwar cewa, Viper ba ɗan ta’adda bane ba, domin yana aiki ne da rundunar tsaro ta ƙasa, kuma harbi ya yi shi ne a kan ƙa’ida, babu daɗewa za su fitar da rahoton ainihin abin da ya faru.Walid ya dawo daga kasuwa, bai samu dawowa gida da wuri ba, saboda ayyuka da suka yi yawa, kuma sai da ya biya wurin liti suka ɗan yi hira, suka zauna a joint tare, daga nan ya taho gida.Ya sha shagwaɓa da tuhumar dalilin daɗewarsa daga wurin amarya Shahida, kafin daga bisani ta gabatar masa da abincin sa na dare.Wayar Viper ya kira, bayan ya gama, ya ɗaga amma bai ce komai ba.”Mai zamani, wai ina ka shiga ne kwana biyu bana samun wayarka, hankalina ya tashi sosai, liti ma ya ce mini ba ya samunka”Ya sauke numfashi ya ce “Ina lafiya””Mai zamani””Mai laya”Walid ya ce “Akwai matsala, menene yake faruwa?”Viper ya ce “Nothing much, kar ka damu ya ƙanwata””Da akwai matsala, kuma ba ƙarama ba ce ba, kamar yadda ka ke faɗa, meyake faruwa?””Koma da akwai matsala, ba gashi kana ji na ba, babu wata matsala ba abin damuwa ba ne ba””Ka san ba abu ne mai wahala na yi sammako na taho Abujan nan ba, ka gaya mini menene?” Walid ya yi maganar a hasale.”Easy maza, harbina aka yi, amma ina samun sauƙi, kar ka ɗaga hankalinka”Walid ya ce “Innalillahi wa Innalillahi raji’un, kuma ka kasa gaya mini, ka ke cewa ba abun damuwa bane ba””Eh, bana son ɗaga muku hankali ne, dan Allah kar ka gaya wa kowa, kuma kar ka ce zaka zo, ba ni tabbacin hanya tana da kyau””Anya zan iya haƙuri ban zo ba, Viper kar ka ɓoye mini wani abu””Kai dalla ware ina gaya maka magana kana ja, zan saka maka ƙarfe ka kuma ƙoƙarin ƙaryatani, ja jiki dalla, mai laya” Walid bai san lokacin da dariya ta suɓuce masa ba ya ce “Na kiyayi mai zamani, tuba nake ka san ɗaukar ƙarfenka ba duk kai ba, na sallama tuba nake, Allah ya ƙara lafiya, ya ja zamaninka mai dogon zamani”Viper ma yayi murmushi ya ce “Sai da kai na wajena, ka gaida mini ƙanwata””Zata ji in sha Allah” suka yi sallama ya ajiye wayar yana murmushi.Ba a awa uku, sai Nabila ta kira Viper, ta tambaye shi yaya jikinsa.Har ga Allah ta so ta kwana tare da shi, amma ya koreta ya saka aka tafi da ita.Da kyar ta iya cin abincin dare, Walid ya kirata, yana yi mata mitar, meyasa ba ta gaya masa abin da ya samu Viper ba, ta gaya masa ba ta sani ba sai daren jiya, ita ma yau ta zo ta ganshi, amma ta tabattar masa da jikinsa da sauƙi.Ƙarfe uku da rabi, alarm ɗinta ya buga, ta tashi zaune, haka kurum sai ta kira lambar Viper, gani take yi kamar wani abu zai same shi, ga mamakinta kawai ta ji ya ɗaga.”Vi””Mmm””Baka yi bacci ba idonka biyu?”Ya ce “Mmm””To meyasa?””Ciwo” ya bata amsa muryarsa ƙasa-ƙasa.Ta miƙe tsaye ta ce “Ka gani ko, da ka bari na kwana tare da kai, atleast ina kusa da kai, na taimaka maka da wani abun, wurin harbin ne yake yi maka ciwo?””Mmm””Sannu Vi, Allah ya baka lafiya ya sanya kaffara ne” tayi maganar tana kuka.”Abla, stop crying, babu zafi sosai kawai na kasa bacci ne””A’a da zafi mana, ina jin zafin a zuciyata”Shiru ya yi yana tuna lokacin da jauhar take yi masa magiyar, ya daina zuwa in da za a cutar da shi, saboda ita take jin zafin a zuciyarta.”Ki na ji na?””Eh””Ki kwantar da hankalinki, ki daina kuka Please, idan ba haka ba, zan ba da umarni a hana ki ganina, har sai na warke””Yi haƙuri na daina””To shikenan, ki yi bacci mai daɗi”ya katse wayar.*****Bunkure ta din ga zuba ido, ta ga ta ina za ayi belinta, domin kuwa ba wuri ɗaya aka kaita da su Indabo ba, ita Kano aka yo da ita, domin ta fara Fuskantar tuhuma ta farko, da ake yi mata a kano, amma shiru babu alamar za ayi belinta, jami’an tsaro suka tabbatar mata da cewa a gaban kotu za a gurfanar da ita.Abokan aikinta da suka kai mata ziyara, suka tabattar mata da cewa an bayar da belin indabo, daga majiya mai ƙarfi, kuma ba a sanar da cewa an kama shi ba, ita ce kaɗai labarin kamata ya cika media.Abin ya ɗaure mata kai sosai da sosai, sai dai ta yi masa uzuri, ta ƙara masa kwanaki, ko zai waiwayota ya sanya a bayar da belinta.Washegari da sassafe Nabila da Hafsa tare da Alhaji Mu’azzam, suka tafi wurin Viper.Ko da su ka je, Nabila da Hafsa ne suka shiga, shi kuma Alhaji mu’azzam ya tsaya a wani office.Suka tarar an buɗe wurin raunin Viper ana dressing.Da sauri Nabila ta ƙarasa, ta zauna ta gefen sa tana yi masa sannu, cikin kulawa da tausayawa.Ya langaɓo kansa jikinta ya ce “Washh da zafi” sai ta sake rikicewa cikin tausayawa ta ce “Sannu Vi, dan Allah doctor ka yi masa a hankali”Likitan ya ce “Ba wani zafi, tun ɗazu nake durje ciwon, bai ce da zafi ba sai da ki ka zo”Viper ya ce “Abla zafi, da zafi yake yi mini” Hafsa kuwa riƙe baki tayi, tana kallon ikon Allah, da wani ne ya gaya mata zata ce an zabga mata ƙarya ne, kodayeke ba abin mamaki bane, ko a baya Jauhar yana sakin jiki da ita. Nabila kuwa ta sake rikicewa ta ce “Dan Allah ciwon nan ya wanku haka a ƙyale shi”Likitan kasancewar sa, bahaushe ne ya ce “Sai dai ya yi kukan jini, sai na cuɗe shi sosai”Marairaicewa Nabila ta yi kawai ta saka kuka, domin ramin da taga wurin harbin yayi, kuma a haka likitan yana cewa wai bashi da ƙan jiki, wurin ya ciko.”Ke da wasa nake yi fa, ba wani zafi kawai ina son in ga kina kula da ni ne””You are just pretending, amma na san da zafi”Yayi murmushi ya ce “Idan muka koma gida, ke zaki ci gaba da yi mini dressing ɗin fa”Ta girgiza kai ta ce “Ba zan iya ba, kuka zan ta yi” Viper yana kallo Hafsa ta silale ta bar ɗakin, bayan ta ajiye kayan abincin hannunta.”Zafin shigar bullet ɗin, bai kai zafin ƙiyayyar da ki ka nuna mini ba, ya taɓa zuciyata sosai”Ta marairaice ta ce “Am sorry Vi, dan Allah ka daina tunawa mana” dai-dai lokacin likitan ya kammala nananɗe masa hannun ya ce “Gashi nan maza ki haɗiye shi madam” Nabila ta yi murmushi, sai a lokacin ta farga Hafsa ba ta nan, ta ce “Kai, tare fa muka shigo da hafsa, tana ina?””Ta fita tun ɗazu, taga abin naki ba na ƙare bane ba” yayi maganar yana janyota jikinsa.Ta tura baki ta ce “Ni da suka din ga soyayya a gabana ya na yi, ko kunyata ba sa ji””Mhmm su su na can su na soyayya, ke ki na takaicin an yi miki auren dole”Tashi ta yi daga jikinsa, saboda da lafiyayyen hannun, yake ƙoƙarin fara lalubeta, ta ce “Bari na baka abinci ka karya, yaya ka kwana da jikin?””Jikina Alhamdilillah, yau zan fita ma na zagaya, na ji sauƙi sosai da sosai”Tana cikin haɗa masa breakfast, Alhaji mu’azzam ya shigo tare da Hafsa.Suka duba jikin Viper, Alhaji mu’azzam ya ce “Minista zai zo dubaka anjima in sha Allah”Viper ya ce “Ni ɗin?””Eh kai fa” ya kalli Nabila ta kalle shi.Ta ce “Yallaɓai, Viper ministan tsaro zai zo ya duba?”Alhaji mu’azzam ya ce “Ni ma ba ƙaramin ministan bane, ai komai sila ne Nabila, kuma idan Allah ya yi niyyar yi maka wani abu, ko da sai ka sha baƙar wahala, kan ka same shi, sai ya baka abin nan.Da gudunmawarsa ɗari bisa ɗari na din ga gudanar da wasu abubuwan, na taimaka wa rayuwarka.In sha Allah kukan da ki ke yi na sha wahala, zai zame masa alkhairi, dan na yi masa bayaninsa sosai da sosai, kuma mussaman saboda kai ya kira ya ce lallai ayi bincike a wanke ka, dan haka ka kwantar da hankalinka in sha Allah babu abin da zai faru da kai sai alkhairi, wahalar da ka sha, ba zata taɓa tafiya a banza ba in sha Allah”Shi dai Viper jin abin yake kamar ba gaske ba, bayan sun gama, Alhaji mu’azzam suka tafi, suka bar Nabila, da zummar da yamma za a zo a ɗauke ta.Viper zuciyarsa ya din ga kaiwa nesa, kasancewar sa da daga shi Nabila, saiti yana neman ya ƙwace masa, duk da a da yana iya sarrafa kansa yadda yakamata.Ya ja ta suka fita yawo, idan suka haɗu da na ƙasa da shi, su sara masa, idan na sama da shi ne, ya sara musu.Duk da gargaɗin da Viper ya yi wa Walid, amma sai da ya gaya wa Liti, abin da yake faruwa, ƙarshe sai da suka yi video call da shi, sannan hankalinsu ya kwanta.Sai da aka kwana huɗu, sannan Alhaji mu’azzam ya zo tare da ministan tsaro, kamar yadda ya sanar da Viper zai zo duba shi, ba kuma shikaɗai ba, har da babban hafsin soja na ƙasa, da wasu daga manyan shugabannin rukunin sojoji masu irin aiki irin na Viper.Yana zaune a kan gadonsa, Nabila na kan kujera, suka shigo, ta tashi tsaye tana kallon su, sai da ta gansu tare da Alhaji mu’zzam, sannan ta ɗan nutsu.Yana zuwa ya miƙa wa Viper hannu, sai da ya ɗan yi jimm, sannan ya miƙa masa suka gaisa.”Finally, yau gani ga Viper, ya ci sunansa Viper, yayi kalar mazaje” yayi maganar yana murmushi.Ɗaya daga sojojin ya ce “He’s very intelligent, and hardworking man, da taimakon team ɗin sa, mun daƙila hare-hare masu yawa, yana taimakawa rundunar tsaro sosai da sosai”Ya jinjina kai ya ce “Na ji daɗi sosai da sosai, duk da ta wani fannin mun aikata laifi, na cireka daga prison, aka yi maka horo na musamman, amma da wata ɓarnar gara wata, na ji labarin duk abin da ya sameka, hakan ya sanya na ƙara samun ƙwarin gwiwar saka hannu a taimaki rayuwar ka, duk da ka bamu wahala da farko, dan sai da na ce, idan zaka bayar da matsala gara a kasheka, amma Kankarofi ya dage, ya ce a bika a hankali.Ina jimanta abin da ya same ka, Allah ya baka lafiya, sannan zan san abin da zamu yi maka, mu ƙara ɗaga darajarka a gidan soja, you are brave man Al’amin, the entire nation is proud of you. Ka yi abin da ya dace, sauran kuma ko su hukunta masu laifin, ko su bar su, wannan kuma su da Allah ne, get well soon my man” yayi maganar yana dukan kafaɗar Viper.Alhaji mu’azzam ya ce “Ga kuma madam ɗin sa fa, his lioness wife, barrister Nabila, yarinyar da nake baka labari, mutuniyar Naja’atu Bunkure””Kai, to ai na ganta yarinya ƙarama””Eh yarinya mai kasada ba, su suka assasa lallai ayi wa Indabo kiranye, amma aka daƙile su, ai nan Abuja zata dawo, ku nema mata gurbi gaskiya, a din ga matsawa matasanmu, suna gwada mana tasu baiwar, hatta cheif judge ya san da ita, amma ita ba ta sani ba”Shugaban hafsin Sojojin ya ce “Tabbas ƙasarmu Nigeria tana da nagarttun matasa, wanda za a basu dama, zasu kawo gayar a abubuwa da yawa. Kamar history ɗin Viper da na duba, da tun tasowarsa, ya samu abin da ya dace, to da tabbas a irin ƙwaƙwalwarsa, da wataƙila shi ne a kujerata, ya zama matashi mafi ƙarancin shekaru da ya riƙe rundunar tsaro ta Nigeria, na yaba da basirarsa nesa ba kusa ba”Nabila ta ji daɗin yabon da Viper ya samu, bakinta har kunne, bayan fitarsu ba ta san lokacin da ta rungume shi ba, tana ta yi wa Allah godiya.Ta ce “Ka ga abin da na gaya maka ko? Dama lokuta da dama, Allah yana jarraba bawansa, kafin ya yi masa wata baiwa, Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya ƙara ɗaukaka Vi”Murmushi kawai ya yi mata, shi dai baya fatan ace za ayi masa wani babban matsayi, saboda yana da ‘yan adawa a cikin jami’an tsaron, gani suke kamar akwai wani fifiko na musamman da ake ba shi.Bayan tafiyar baƙin, shugaban sojojin yake cewa kankarofi, yana yi wa Nabila kallon sani, tana kama da wani tsohon ubnagidansa a sojoji, major Yusuf maitama.Kankarofi ya ce “Ai ‘yar sa ce” Ya ce “In dai jarumta ce da taurin zuciya, ba ta yar a ƙasa ba”Minista ya ce yana son a saka sunan Viper, cikin sabbin naɗe-naɗen da za ayi na sojoji, a yi wa manyan ritire.Shugaban ɓangaren su Viper ya ce “Amma sir, lokaci bai yi ba ayi masa wannan muƙamin fa””Eh a banza ma, ana saka waɗanda ba su cancanta ba, dan haka a saka mini sunansa, dan ya cancanta” ya ja bakinsa ya tsuke, domin kuwa kujerar da za a ɗora Viper, daga ita sai tasa.A daddafe Viper yayi kwana tara, ranar na goma ya ce a gidansa zai kwana, ya din ga zuwa dressing ɗin, ya gaji da zaman Asibiti.Nabila ma ta ji daɗin hakan, dan kuwa ta gaji da sintirin nan, babu wanda suka gayawa halin da ake ciki, a ‘yan uwa, duk Major ya samu labari, ya kira Viper ya din ga faɗa a kan meyasa ba su faɗa ba, Nabila ta kaee shi, ta ce masa basa son tayar wa mutane hankali ne.Allah ya taimake su, an daƙile yaɗuwar labarin ƙaryar cewar Viper ɗan ta’adda ne.Nabila tana ta yi wa Viper santin gidan, ɗan ƙarami mai kyau, hafsa har gidan ta rakata, ta tayata suka yi ‘yan gyare-gyare, komai akwai a gidan na furnitures da na buƙatu.Sai dai komai na maza ne, sai da hafsa ta tafi gida, ta aiko mata da wasu abubuwan.Nabila tana ta tsokanarsa, wai gidan gwauro.Ya kalleta ya ce “Gidan gwauro ko, zaki ga gidan gwauro, yau zan mayar da shi na magidanci”Sai kuma tayi ɗif, ta sha jinin jikinta.*GA MASU JIRAN DOCUMENT, ZA SU IYA PAYMENT YANZU, FEW PAGES YA RAGE, ONGOING PAGES NE 500 COMPLETE DOCUMENT KUMA 1K. VIA 0009450228AISHA ADAM JAIZ BANKSAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143

Back to top button