Hausa novels

Halysaah Page 181 By Khaleesat Haydar

HALYSAAH PAGE 181…Wajen karfe tara na safe Malam Ali ya shigo dakin Nenne da sallama, Nenne tace “Yanxu nake shirin zuwa in same ka a parlon ka don yau na tashi cikin matsanancin damuwa Ali” Zaunawa yayi kan Carpet din dakin yace “To Allah ya sa lafiya dai Nenne” Nenne tace “Ina fa lafiya Ali, yanxu haka za mu zuba ido kamar marasu makabuli mu bar yarinya a gidan sarauta ba gaira ba dalili shekaru sun doshi biyu kenan? Ko dai mun sallama masu Khaleesat din ne Ali? Su kansu kallon shashashan iyaye za su dinga yi mana wallahi a yanxu dai, to tare da su zata zauna har abada kenan ko kuma dama wanda ya mutu yana dawowa ne balle mu ce zaman jiran marigayi take? A ina aka taɓa haka ita ba ‘ya ya gareta ba balle jikoki a gidan? Gaskiya abun ya fara damuna babu inda ake haka a duniya, kar mu zama yan iskan iyaye gwara ayi abinda ya kamata mu sa Bala yaje ya kamo mana ita ya dawo da ita gidan nan, in ma daureta za mu yi mu daureta, gashi talakawan unguwan nan da na ja zuwa jikina nake da na sanin haka yanxu sai tsegumin mu suke wai mun sallama ma masarauta er mu, kilan jira muke sai an raba gadon marigayi ta amso kasonta sannan ta dawo, ni tsorona ma kar masarautar ma su yi zaton dalilin da yasa muka bar masu ita kenan a gidan muka yi shiru, ka duba wannan lamari Ali babu inda ake haka wallahi, ga dai Zahra’u kullum cikin kuka tana son er ta a kusa da ita” Tun da Nenne ta fara magana Malam Ali yayi shiru yana sauraronta har ta kai karshe, jin shirun nasa yayi yawa tace “Ba shiru zaka yi ba Ali ya kamata ka zama uba jajirtattce kasan yanda zaka dawo da er ka gabanka, kar a mana kallon marasa lissafi mana” Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace “Yanxun nan muka gama waya da Sarki shi ne ma dalilin da ya sa na shigo nan” Nenne ta zaro ido tace “Sarki da kansa? Ahaf kaga su ma sun gaji da rashin lissafin mu, wato ya kira yace a zo a dauketa ko? Yanxu ina amfanin haka, baka ji yanda naji kunya ba tsamo tsamo, akan Khaleesat aka fara mutuwar miji da zata haukata kanta haka ta maida mu iyayen banza? Allahn da ya fi ta sonsa ne ya dau kayansa, wannan ai kafirci ne rashin danganar da taki yi, duk musulmin kwarai an san sa da tawakalli da ɗaukan ƙaddara mummuna ko kyakkyawa, yanxu ba sai su ga bamu bata ilimin addini bane tunda gashi bata san dangana ba, mu dai ta cuce mu wallahi, sai ka kira Bala yaje ya daureta ya taho mana da ita kawai tunda mahaukaciya ta maida kanta, sau nawa ana dawowa da ita gidan nan ta faki ido ta gudu, to su ma sun gaji shi yasa ya kira ka” Malam Ali yace “Ni ba maganar Jiddah yayi min ba Nenne” Nenne tace “Maganar me yayi maka to?” Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace “Wai gobe juma’a zai aiko wakilai a daura masa aure da Farida, in kuma can Nijar za aje daurin auren to sai aje, kiran da yayi min kenan yanxun nan” Sai da Nenne ta mike tsaye tsabar gigicewa hannunta na karkarwa tace “Wace Paridar?” Malam Ali yace “Farida dai da kika sani” Nenne na gwalo ido tace “Wai Paridah Kanwar Zahra’u matar ka?” Malam Ali yace “Kwarai kuwa” Nenne ta fashe da kuka tace “Allahu Akbar, wai kana nufin sarki da kansa ko kuma dai wani yake nema ma aurenta?” Malam Ali yace “Cewa fa yayi zai turo a daura masa aure da ita gobe, kuma ki ce wani Nenne, shi ne zai aureta, baki ga kai tsaye kawai har ya yanke gobe a matsayin ranan daurin auren ba babu wani dogon magana, ai Sarautar kenan, kuma bamu isa mu ce a’a ba….” Nenne ta gwalo ido tace “Ka ji Malam Ali da wata magana kamar wawa, dama uban waye zai ce a’a? Ai babu shegen dake ja da maganar sarki” Nenne bata sake sauraronsa ba ta fice daga dakin da sauri ta tafi dakin Umma tana kwalo mata kira, Umma na zaune dakinta da Aunty Farida har ta mike zata fita sai ga Nenne ta shigo kamar an jefota, sai kuma ta fashe da matsanancin kuka wanda Umma sai da ta tsorata duk tunaninta abu ne ya samu Khaleesat, Aunty Farida ma ta mike cikin tashin hankali tace “Lafiya Nenne, me ya faru?” Nenne ta duka ta dafe gwiwowinta cikin kuka tace “Wallahi Sarki ne da kansa ya kira Malam Ali yanxun nan” Nenne na fadin haka Umma ta fashe da kuka cikin tashin hankali tace “Innalillahi wa Inna ilaihi raji’un, me ya samu Khaleesat din Nenne? Ita ma mutuwan tayi?” Ita kanta Aunty Farida jikinta rawa yake tsabar rikicewa tace “Abu ne ya samu Khaleesat din Nenne?” Nenne ta mike tace “Wacece Khaleesat kuma?”

Back to top button