Kannywood

Daga Karshe Jarumar Fim, Mercy Aigbe Ta Tabbatar Da Shiga Musulunci

Wani bidiyo na jarumar Nollywood, Mercy Aigbe tana mai sake gabatar da kanta a sabon addininta ya yadu

An yi hira da ita ne a wani taron Ramadan da jarumar ta shirya tare da mijinta wanda ya samu halartan manyan jarumai

Bidiyon wanda tuni ya yadu ya haifar da cece-kuce a tsakanin masu amfani da soshiyal midiya.

Mercy Aigbe ta sa masu amfani da soshiyal midiya yamutsa gashin baki bayan bayyanan wani bidiyonta da ya yadu.

Ku tuna cewa jarumar da mijinta, Adekaz sun gayyaci abokai, abokan sana’a da yan uwa zuwa taron Ramadan.

Bayan nasarar da ta samu a taron, an yi hira da jarumar inda ta tabbatar da cewar ta bar addinin kirista zuwa na Musulunci. A bidiyon, an iya gano jarumar tana sake gabatar da kanta da sunayenta da suka hada da na Musulunci.

Kalamanta:

“Sabon sunana shine Hajia Meenah Mercy Adeoti. Meenah.”

Jama’a sun yi martani

mz__seunfunmi:

“Wannan bai dameni ba sunan da na san ki da shi shine mercy aigbe.”

openspeaker_1:

“Idan suka rabu daga baya fa??? Kada ta je ta bi boka faaaa.”

benny_lee04:

“Soyayya na shirin gamawa da mercy.”

official__jessie:

“Muna nan gaba daya lokacin da idanun mutumin nan za su bude.”

 

Back to top button