Hausa novels

Gargadar So Chapter 37 By M Shakur

Kusan 5min Khaleel da Baba sukai ahaka sannan yadaga kanshi daga kafadan Baba yakalli Baba yace “kahuta? Kadena damuwa”? Gyadamai kai Baba yayi yace “nahuta Ibrahima” sauka Khaleel yayi yadauki crutches din yabashi Baba ya karba suka fito tare, Ammi bata wajen hanyar dakin sukayi Khaleel yaci tura dagadan nesa Baba yajuyo yakalleshi yace “bazaka shiga ba” dan sosakai yayi saikuma ya dauke kai ahankali yace “uhmmm kunyan nakeji” dariya Baba yayi irin na manya dinnan jin maganan dayayi yace “kunya? Wai kunyan Ammi”? Dasauri Khaleel yajuya yana gyadamai kai yace “bye Baba sai munzo anjima” kafin Baba yayi magana har yayi kofa su Salman dake wajen suka budemai kofa yafice suka bishi Baba yace “jama’a wannan yaro akwai shiga rai, Ya Allah inama Hawwa na kwadayinsa sosai, Allah inhar alkhairi ne auren nan kasa ya tabbata yau” yayi maganan a yana shiga cikin dakin da murmushi kan fuskanshi yayi inda Hawwa take dake bacci anmata allurai da dama, Ammi na zaune ta buga tagumi ganninshi yasa Ammi takalleshi da damuwa akan fuskanta, Baba yajuyo yaja kujeran plastic chair ya zauna cikeda farin ciki yace “kidena damuwa Zainabu kiyi addu’a inhar Ibrahima rabon Hawwa ne kuma mijinta ne yau za’a daura mata aure” dasauri Ammi ta kalleshi tace “waye kuma Ibrahima Malam”? Labarin Khaleel yashiga bata all abubuwan daya sani, tai shiru Allah yasani yanda taga Khaleel yayi da Baba taji ya burgeta, banda haka Ni’ima said some disturbing about Hawwa, ita mace ce, sannan ita uwace, ko yara irin su Ramla sunsan sha’awa yanzu, Hawwa ba yarinya bace, babu bawa da baida sha’awa, tanaso Hawwa tai aure ta sami natsuwa da kwanciyan hankali, ba maza Hawwa kebi ba, bata iskanci so dole ne a irin shekarunta taji yana bukatan namiji, tabbas Hawwa na bukatan natsuwa, abun yamata, 50/50 Ammi keji azuciyanta, one side na zuciyanta ya goyi bayan auren sabida abubuwan da Ni’ima tafada especially bukatun Hawwa kafin yarsu tafada halaka, kota kauce hanya amata auren, zuciya ba kashi bane tsokace duk yanda takai da karfin imani shedan zai iyacin galaba akanta wata rana idan takasa hadiye sha’awar, another bangaren zuciyanta kuma zaiso ayi bincike akan koma waye Ibrahiman but idan aka tsaya bincike kafin agama yaron yagudu ko yace yafasa fa? Cus abinda ke faruwa kenan dazaran sunzo su gudu, yagudu yaushe Hawwa zata kara samin wani yafito ga Ni’ima ta tasata agaba? Sotake tai aure tai nisa da anguwan ta huta da bakin cikin Niima, she kind of reason with Baba sabida yanda samari ke guduwa gwara su kama Khaleel dinnan as earlier as possible, zata taya Hawwa addu’a Allah ya albarkaci auren ya kauda fitina su sami fahimtan juna, amman dai tai auren Hawwa na bukutan natsuwa kafin tafada wani hali, ganin tai shiru tana tunani yasa Baba yace “kin yarda Zainab? Dan banso mukara fada yanzu komi yawuce, ni da kene iyayen Hawwa, banda mu batada kowa, ada nai kuskure dana dinga bala’i dake, gayamin abinda ke ranki dan hukuncin nan tare zamu yankewa yarmu” murmushi Ammi tayi jin yanda Baba ya girmamata yabata matsayi yakuma karramata, anatse tace “na yarda Malam, nakuma aminta idan Alkhairi ne Allah yasa su dawo adaura idan ba alkhairi bane kuma Allah ya musanya mana yabata miji da gaggawa” Baba yace “Ameen Ameen” yana murmushi suka cigaba da hira, abinci aka kawo musu akace an riga an biya kudin abincin duk sukaci Ammi takira Ramla tace kartai girki, tabama Baba wayan Hawwa tace “Malam kira wajen aikinta ka sanar dasu tayi hatsari” Baba yace “nemomin number kaman DIG naji tana kiran Ogan nata duba kiciromin number” Ammi ta karba tana ciromai.WAIWAYE BAYA KADAN..!Ana fitar dasu waje har parking space aka kaisu aka tsaitsaya akansu kaman barayi, Salman yace “you have 10secs to leave this hospital else we hand you over to police and press charges against the both of you, we have cctv camera in every corner of this hospital starting from patient room” kallonta Baban Yaseer yayi yanda take kallonshi tana haki, ranshi ya baci iya baci da abinda tamai, baitaba sannin this is who Ni’ima is ba sai yau, cikin kakkausan murya yace “daganan kiwuce gidanku, namiki iyaka da gidana zankira mai gadi na shaidamai kada ki shiga gidan nan, kije na sakeki saki daya!” Faduwa gabanta yayi sosai zatai magana kawai yabude motan yashiga yawuce tabishi da kallo kirjinta na bugawa, Salman yadaka mata tsawa. “Madam leave our hospital!” Jikinta har rawa yake ta wuce ta shiga tata motar ta kunna tabar asibitin.School nasu Yaseer yawuce direct ranshi na suya ya daukosu yace zasu danyi tafiya na 2week, sukaje gida yahada kayansu tundaga kansu Ipad yasasu a mota kawai sukai Kano gidan iyayenshi sukaje yakaima mahaifiyarshi yaran sunata murna yace suyi kwana biyu yasayo musu komi washe gari yabar Kano da sassafe danso yake yaje yaga Baba he made up his mind zai auri Hawwa yanzu, he wants to make her his wife.****

Back to top button