Hausa novels

Mijin Marigayiya Page 29 Hausa Novel

Sai karfe biyu na rana take da lecture amma haka ta shirya da wuri lokacin da Mustapha ya shirya zai tafi office tace ya wuce da ita ya kaita gidan Mommy, in ya so daga can sai ta wuce makarantar ta kuma dawo gida. Haka kuwa aka yi.Tunda ta shiga gidan Mommy ta karanta damuwa a fuskarta, ta dai kyaleta har Baffa da Nabila suka gama shirinsu suka fice. A nan parlor din inda suka barsu Mommy ta zuba mata ido na dan lokaci, har ta ji a jikinta Mommy din kallonta take. Tana juyowa kuwa suka hada ido; ta danyi dariya tace ‘Mommyy.’Itama tayi dariyar tace ‘Ya aka yi ne? kamar dai kina da damuwa. Ko kuma ba kya jin dadi ne?’Ta jijjiga kai tace ‘Mommy Mustapha aure zai yi.’Ta dan zaro ido ‘Aure? Ikon Allah.’ Sai kuma ta saki fuskarta ta cigaba ‘Ko da yake wannan ba abin mamaki bane ai don haka kada ma ki sakawa kanki damuwa.’Ta sunkuyar da kai cikin damuwa tace ‘Mommy nima ba damuwa nayi ba, kawai dai yayanyin abun ne.’‘Ban gane ba.’Nan ta sanar da ita wadda zai aura sannan ta sanar da ita a inda taga labarin auren da kuma irin sakonnin da Afaf take turawa Najan da kuma yanda take fama da Afaf din a ‘yan kwanakin nan.Duk da Mommy bata yi mamaki ba amma dai ta ji babu dadi, musamman yanda Afaf ta zama ‘yar rahoton Naja. Tace ‘Ikon Allah, to shi me yasa yake boye miki auren?’Tace ‘Wallahi ban sani ba, ko da wasa bai taba gaya min ba kuma danginsa ma babu wanda ya gaya min. Amma kin ga yaran har sun sani, tunda gashi har ana gaya musu za a zo a gyara min zama.’‘Lallai mutum sai a barshi.’‘Dama na gaya miki Mommy tunda naga gidan da ya saya nace miki gidan nan ba na mace daya bane, kin ga maganata ta tabbata.’Sukayi shiru na dan lokaci, jimawa kadan Mommy tace ‘To da ce mata aka yi baki zauna daidai ba da take cewa zata gyara miki zama ko me? Amma kafin ta gyara miki zama ke ce zaki bi dare ki gyara zama ta hanyar addu’a, idan gari ya waye kuma ki dora da sadaka.’Ta sunkuyar da kai tana koakrin boye kwallar da ta gangaro a kwarmin idonta; wannan kalmar ta za a gyara mata zama ta tsaya mata a rai. Domin dai kalma ce da zata iya daukan kowacce ma’ana. Amma kamar yanda Mommy ta fada hakan zata yi tunda ta san bata da gatan da ya wuce Allah.Haka suka cigaba da hira Mommy tana ta bata baki kuma tana yi mata alkawarin daga nan ma zata dinga yi mata addu’a kuma da sadaka, ta tabbatar mata ba za tayi nasara a kanta ba.Da wuri Mommy ta sauke abinci saboda Khadija taci kafin ta tafi makaranta, tana daga kitchen din ta kwalawa Khadeejan kira. Tana shiga kitchen din ta fara gatsina fuska tana cewa ‘Mommy wannan wane irin kifi ne kika dafa me azabar karni? Allah ya sa dai ba da shi kika yi abincin ba.’Mommy ta kare mata kallo na dan lokaci sannan tace ‘Wane kifi da aka dafa tun jiya da daddare aka cinye, ni shinkafa da wake ma na dafa.’Nana da nan fara’arta ta karu, ta dauki plate ta matsa tana mikawa Mommy tana cewa ‘Yauwa Mommy zuba min na fice don wallahi kitchen din nan karni yake.’Ta karbi plate din tana cewa ‘Cikine da ke ko?’Ta kalli Mommy da baki a bude, suka dan zubawa juna ido sannan ta rufe bakin tace ‘Anya kuwa Mommy, tunda dai ni ban ji wani sauyi na azo a gani ba.’Ta zuba mata abincin ta mika mata tana cewa ‘To ki dai bincika tukunna kafin kiyi saurin cewa a’a, don tunda kika shigo nake kula da ke gaba daya ma na dauka abinda ya kawo ki kenan.’‘To ban sani ba gaskiya Mommy, amma zan duba yau din nan kuwa.’Bayan ta gama cin abincin tayi sallah sanna ta fice ta kama hanyar makaranta. Sai da ta tsaya a chemist ta sayi abun pregnacy test sannan ta wuce. Ta riga ta san su Rahma suna jiranta a hostel don haka kai tsaye can ta wuce, tana ajiye jakarta a dakin ta fice ta fada toilet. Tana tsoma abin nan a fitsarinta ya nuna radau positive; wato tana dauke da ciki. Tayi murmushi tana ji kamar ta daka tsalle saboda murna, nan da nan idonta suka ciko da kwalla saboda jin dadi. A take kuma jikinta yayi sanyi da ta tuna cewa Mustapha ne yayi mata ciki kuma shine yake shirin auro matar da ta ke ikirarin zata shigo ta gyara mata zama.Ta sunkuyar da kai ta saki takardar a kasa sannan ta fito daga bandakin cike da damuwa.Yanayin da ta shiga dakin ya tabbatar musu da akwai matsala, don haka tun kafin ta Zauna farida ta mike ta tareta tana cewa ‘Ya na ganki haka, lafiya dai ko?’Ta zauna a kan gado Rahma kamar wadda aka jefa, ta kalli farida suka hada ido sannan ta saki murmushe wanda yake hade da takaici tace ‘I am pregnant Farida.’Nan da nan su Rahma da Amina da ke zaune suka dako tsalle suka fada jikinta sun ihu. Sai da suka fahimci ita bata taya su ihun kamar yanda suka saba sannan suka tsaya suna kallonta.‘Girl, wannan ai abun murna ne na ga kamar ke baki ni dadi ba.’ Amina ta fada tana rike da hannun Khadeejan.Ta sunkuyar da kai ta zare hannunta ta goge kwallar da ta fado daga idanunta. Ta basu labarin auren Mustapha da kuma abinda ta gani da ma yanda yake boye mata.Tace ‘Ban ma san wanne zan yi ba; murna ko bakin ciki? Ni da za a zo a gyarawa zama ina zan mike kafa na fara haihuwa; haihuwar da ni ban ma tabbatar zai yi murna da ita ba. A yanzu ma gaba daya kai na ya kulle. Mommy dai tace kada na kuskura nayi masa maganar kara aurensa, na barshi har sai ya zo da kansa ya ya gaya min, a lokacin sai ayi duk wadda za ayi. Amma wallahi ban sani ba ko zan iya jurewa. Gaba daya ma yanzu ban san matsayina a wajen Mustapha ba, kuma ga ciki.’Suka yi shiru na dan lokaci.Amina ce ta katse shirun nasu tana cewa ‘Gaskiya mutumin nan dan wulakanci ne, haba!’Rahma tace ‘Amma gaskiya ina bayan Mommy, ki barshi kawai kada kiyi masa magana in ya so idan ya zo zai gaya miki da kansa sai ki yi masa wankin bargo tunda dai babu abinda zai sa ya fasa wannan auren da yayi niyya.’Tace ‘Hakane.’Nan suka daui lokaci suna bata baki, sannan daga baya Farida da Rahma suka fice suka tafi lecture din suka barsu a dakin itada Amina wadda ta tsaya ta tayata zama don tace ba zata iya zuwa lecture din ba.Duk yanda take cikin damuwa da yanda take so ta yiwa Mustapha tijara game da yanda ya boye mata maganar aurensa da Naja haka ta hakura ta danne zuciyarta. Domin ita kanta ta kasa ganin maslahar yi masa maganar; tunda dai itace baya so ta sani gara ta rabu da shi ta gani ko za a dauro auren ne a kai amarya sama jannati saboda kada ta sani. Cikin da take dauke da shi ma kasa gaya masa tayi, domin bata ga alamar yana farin cikin kasancewarta matarsa ba. Gaba daya ma cikin ya zo mata a wani lokaci ne da take jin cewa da bata same shi ba zata iya hakura da haihuwa a gidan Mustapha har sai ta fahimci inda auren nasu ya sa gaba. Ko da yake dai ta san ana cewa idan namiji zai kara aure matarsa da take gidan sai ta yi matukar hakuri; to tabbasa ta ji a jikinta cewa lokacin nata hakurin ne ya kama yanzun…

Back to top button