Halysaah Page 123 By Khaleesat Haydar
HALYSAAH PAGE 123 ….Ajay na kallon football wajen karfe sha dayan dare kiran Mai martaba ya shigo wayarsa ya rage volume din TV din ya sauke kafafuwansa kasa daga kan kujera sannan yayi picking call din, cikin ladabi ya gaida Sarki, bayan sun gaisa sarki ya tambayesa Khaleesat, yace “Tayi bacci ranka shi dade” Sarki yace “Ohk, goben za ku tafi UK for Hadiyah’s Convocation which is on Tuesday?” Ajay yayi shiru, can yace “I thought Wednesday ne ranka shi dade….” Mai martaba yace “A’a, Jawwad din bai tura maka Invitation din bane?” Duk da bai tura masa ba Ajay yace “Ya tura, ban kula bane da date din” Mai martaba yace “It’s Tuesday not Wednesday” Ajay yace “Toh Allah ya kai mu lafiya ranka shi dade, nasan ba lallai ka samu daman karasowa ba ko?” Mai martaba yace “Za a wakilce ni, beside Hajja ma gobe za su tashi zuwa England din in sha Allah, Kai ma ya kamata kai da matar ka should leave tomorrow ba sai ranan talatar ba” Ajay yayi shiru at first, sai kuma a hankali yace “Abba i think ba sai na je da ita ba, she will stay with her friend kafin in dawo” Mai martaba yace “Ko saboda me?” Shiru Ajay yayi, Mai martaba yace “To ku je tare, she will get to meet most of ur relatives da basu san ta ba, there is no point leaving her behind shi yasa nasa ayi mata Visa” Ajay ya sauke idonsa yace “Toh Abba, we will go together in sha Allah” Mai martaba yace “Good, Walid ma tun shekaranjiya ya tafi England din” Ajay yace “Ehh he was here yesterday, amma ya tafi yau” Mai martaba yace “Really, America ya tafi dama?’ Ajay yace “Eh nan ya zo” Mai martaba yace “Wani irin tafiya ne wannan yayi? Shi da zai tafi England that is just 7 hours from Nigeria me ya kai sa America tafiyar kusan awa sha shidda?” Ajay yace “May be he have something to accomplish here, but ya tafi England din daxu da safe” Mai martaba yace “Ohk then, take care” Ajay yayi masa sallama sannan Mai martaba ya katse wayar, ajiye wayar yayi ya jinginar da kansa jikin kujera yana nazarin ta yanda zai fara tafiya England da Khaleesat, shi ma ba da son ransa zai je ba balle ya wani je da ita, mikewa yayi kawai ya kashe kayan kallon ya wuce sama. Safiyyah da ta rike haɓa tana kallon Khaleesat da mamaki tace “To hakan yana nufin kishi yake da ni kenan ko me? Banda haka me yasa zai hanaki zuwa wajena bayan tare ya gan mu? Ji min mutum, Ko don saboda yasan ni Team Housemate ce? To dole ne sai na goyi bayan cin amanar da yayi yake nufi ko me? Ni dama tun asali kowa yasan Housemate nake yi shine nawa, kuma bazan taɓa canza ra’ayina ba, har gobe bazan dena cewa ba a kyauta ma Housemate ba an ci amanarsa an cucesa, shekaranjiya ma naga ya saka status wai amaryarsa zata yi convocation a Oxford, caption dinsa ne yasa jikina kuma yayi sanyi qlau” Khaleesat ta daga ido tana kallonta, Safiyyah ta taɓe baki tace “Ko meye na wani sa wife dinsa a caption bayan kowa yasan wife dinsa ce ba sai ya gaya mana ba, ni dai kaddai fa ace har yayi move on ya bar ni nan da jiye masa takaici kullum ina babatu, su fa maza ba tabbas gare su ba, zuciyarsu ba shi da tabbas yanxun nan sai su canza in suka samu wata daban, tun da naga ya sa kalmar wife din nan a status jikina yayi sanyiiii, kinga alamar ya dirji amarcinsa yanda ya kamata kenan har da referring dinta to as his wife a status dinsa, to ai shikenan” Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba tana jin zuciyarta na mata zafi, Safiyyah ta taɓe baki tace “Duk da dai shi ma Ajay din ba mutumin banza bane mutum ne me shegen class da personalities masu kyau, kuma dama can yana burgeni yanda baya daukan wargi yanxun nan kana raina masa hankali zai kai maka naushi ya hada maka jini da majina, ba irin mijin Surayyah da Housemate ba masu ba namiji ɗan uwansu hakuri, tun daga nan suka sire min wallahi naga inaaa ba gwarzaye bane” Khaleesat ta kalli wayarta jin shigowar sako, sai kuma ta kalli Safiyyah a hankali tace “My driver is around Sophie, sai gobe” Safiyyah tace “Ni dai ki kwantar da hankalinki ki dena damun kanki wallahi, tun da Allah yayi Housemate ba mijinki bane don gashi can har ya rungume er matarsa to kema a gaskiya zan baki shawara kiyi hakuri ki fara kula mijinki duk da ɗan rainin hankali ne shi amma to ya za ki yi? Nasan shi ma wallahi daurewa kawai yake yana pretending amma ya gama macewa a kanki, yana zaune gida daya dake yana kallon ki matsayin halaliyarsa da wannan shape din naki da glowing skin har ya isa yace baya jin komai a ransa? Ai sai dai ya yaudari kansa wallahi, kawai daurewa za ku yi ku sauke hakkin juna a wuce wajen” Mikewa Khaleesat tayi without answering her fuskarta daure ta dau jakarta tace “Bani textbook dina zan tafi gida” Safiyyah tayi er dariya tace “Ranan da zai nuna maki ke halaliyarsa ce may be you will come back to ur senses that day, bar ganin yana kyaleki, ba dai namiji bane? wataran ko yace zai kyaleki bazai iya ba a sannan ne zaki dawo hankalin ki” Takaici yasa Khaleesat ta juya kawai tayi tafiyarta ta bar wajen, cikin bacin rai ta nufi inda driver ke parking yana jiranta. Khaleesat na isa gun motar ta bude back seat zata shiga, still tayi tana kallonsa, yana zaune driver seat ya saka Black glasses irin no respect din nan yana kallon gabansa kamar bai san ta bude motar ba, ta ɗan taɓe baki ta rufe back seat din ta bude front seat ta shiga motar, Without looking at him kamar ana tilasta ta tace “Good evening” Bata ji ya amsa ba ya ja motar suka bar wajen, ba hanyar gida taga ga nufa da ita ba, ita dai tana ta kallon hanya wondering where he is taking her to, sai da suka yi tafiyar kusan awa daya sannan yayi parking a wani babban Mall, ya kashe motar ya sauka, ganin bata sauko ba yace “Don’t waste my time” Bude motar tayi fuskarta babu walwala ta sauka, yana gaba tana biye da shi suka shiga wajen, Abayoyi masu tsadan gaske da dogayen riguna ta dinga gani, ita dai tana biye da shi a baya, without looking at her yace “Pick the ones u need” Ta daga kai ta kallesa, yana duba agogon wrist dinsa yace “Do not waste my time” Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, can ta daga wani Abaya da take ta kallo tun da suka shigo wajen, tana ganin price dinsa bata san sanda ta mayar da sauri ba, taga ya dau Abayan yana dubawa, ita dai kallonsa kawai take, ya duba size din, daga haka bai sake bin ta kanta ba ya ci gaba da duba Abaya da tsadaddun dogayen riguna yana daukan wanda yaga yayi kyau, sai da ya dau riguna biyar duk masu shegun tsada a wajen, don mamaki ma abun ya bata, yayi payment suka fita wajen ya shiga wajen takalma da jakunkuna designers, ta buda ido sosai tana kallonsa, nan ma duk shi ya zabar mata kala uku uku har tayi mamakin ta yaya yasan size din takalminta ga riga ma da ya siya yasan size dinta, sosai jikinta yayi sanyi ganin prices din items din da yake dauka ba na wasa bane, bayan yayi payment suka fita daga wajen takalman kuma duk shi ke rike da kwalayen da aka zuba masu kayan, ta wani zaro ido ganin wajen designers jewelries zai shiga, ita dai a hankali take tafiya tana bin sa a baya, nan ma set din jewelries lafiyayyu uku ya daukar mata ita dai tana ta kallon ikon Allah, taga ya kara mata da zobuna biyu duk designers, sai wristwatch, zoben ne ma ya bata ta gwada without looking at her, daga nan ya biya kudaden suka fita daga wajen, inda ake siyar da hair accessories irin na turawa ya gani ya shiga wajen tana dai biye da shi cikin sanyin jiki, hadaddun ribbons din gashi ya siya mata iri iri bayan ya biya suka bar wajen sannan suka fita babban Mall din gaba daya, she don’t even want to start calculating the amount he spent in just this shopping cause the money was huge especially when converted to Naira, millions masu dama kenan fa in anyi lissafi, bayan mota ya bude ya ajiye kwalayen kayan hannunsa sannan ya bude driver seat ya shiga, ita ma ta shiga gaban motar ta kulle, sae da suka kusa gida after almost an hour and 15 mins ride sannan ya tsaya wani eatry ya siya abinci takeaway biyu, daga nan kuma suka wuce gida wajen karfe bakwai na dare…. A nan parlor Ajay ya bar mata kayan a takaice yace “Get ready za mu yi tafiya gobe karfe biyar na asuba, iya wa ennan kayan zaki tafi da” Yana kai wa nan ya wuce sama ta bi sa da kallo, a hankali ta dau package din kayan gaba daya ta wuce sama ta kai daki, kara fitowa da kayan daya bayan daya ta dinga yi tana duba su, ya subhanallah… they were soo beautiful and unique, the designer bags and shoes where more than gorgeous, har cikin ranta suka yi mata kyau sosai, gashi ya iya zabe ya ma fi wata macen iya zaban kaya, ta gwada takalman taga kamar don kafanta aka halitto su, ta zaune gefen gado ta fito da jewelries din su ma tana duba su, they were screaming nothing but luxury, ta gwada 2 rings din dake ta kyalli ta ɗan yi murmushi sai kuma murmushin yayi fading daga fuskarta ta cire su a hankali ta ajiye bayan ta tuna zoben da Housemate dinta ya siya maya, lokaci daya duk mood dinta ya canza, ɗan farin cikin kayayyakin da take yi yayi disappearing at once daga ran ta, tafi minti sha biyar zaune kafin daga karshe ta mike a hankali ta goge hawayen dake makale idonta ta nufi banɗaki zata yi alwala, sae da tayi sallan magrib sannan ta fita daga dakin, ta jima tsaye corridor as if contemplating on what she is about to do, at the end kawai ta karasa ɓangarensa tana tafiya a hankali ta bude kofar ta shiga kamar munafuka, yana zaune parlor ta samesa yana duba wayarsa, taki barin su hada ido ta tsaya jikin kujera a hankali tace “Thank you so much for the wears, Allah ya kara budi” Bai daga kai ya kalleta ba, bayan few seconds taji yace “Thank God instead” Still not looking at him tace “Okay” Daga haka ta juya ta fita daga parlon ta kullo masa kofa, sai bayan da ta koma daki ta fara tunanin kaddai fa convocation din Hadiyah za su je gobe, sosai gabanta ya fadi bayan wannan tunanin ya zo mata rai, lokaci daya jikinta yayi mugun sanyi taji ƙafafuwanta sun mata nauyi sun ma kasa ci gaba da daukan ta, anya zata amince ta bi sa kuwa? da kyar ta karasa edge din gadon dakin ta zauna kamar warce ruwa ya cinye tunani iri iri na yawo a ranta, after some minutes ta jawo wayarta cikin sanyin jiki zata kira Safiyyah ta gaya mata.Karfe hudu dai dai na asuba Ajay ya bude kofar dakin da Khaleesat take ya kunna wutan dakin yana kallonta, bacci take ta rufe har kanta da Duvet, ya karasa kusa da gadon ya sauke duvet din yace “Kee” firgit ta bude ido ta mike zaune da sauri tana komawa baya, sai kuma ta fara duba hulanta a kan gadon zata rufe gashinta, juyawa yayi ya fita daga dakin, ta jawo wayarta tana duba agogo taga karfe hudu da minti biyu, ajiye wayar tayi ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki…. Kafin karfe hudu da minti hamsin Khaleesat har ta gama shiryawa dama tun daren jiya ta hada duk sabbin kayan da ya siya mata a box dinta ta shirya, tana tsaye gaban madubi tayi oiling dogon gashinta tana combing dinsa zata daure da daya daga ribbons din da ya siya mata jiya, sai kallon baƙin gashin nata take ganin kamar ya kara yawa ma, banda sheki babu abinda gashin yake, bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri ta kalli kofar tana daure tulin gashin nata waje daya cikin hanzari, kallo daya yayi ma gashin yace “Ke Malama you are wasting my time, ko bakya duba agogo ne” Ta ɗan turo baki ta dauke kanta tace “Ni sai nayi sallah tukunna” Tana fadin haka ta ci gaba da abinda take, can ta juya ta kalli direction din kofar taga ya bar wajen, biyar da kusan minti goma ta fito daga dakin da box dinta da handbag ta sauka downstairs, high waisted palazzo ta saka with matching top sai karamin veil dinta da handbag tayi kyau sosai ba kadan ba duk da babu abinda ta shafa a fuskarta sai eye pencil da ta sa a idonta, yana zaune parlor alamar ita yake jira, jin footstep dinta ya juya ya kalleta sai kuma ya dauke kai, kara kallonta yayi kamar zai yi magana sai kuma dai ya fasa ya mike ya nufi kofar parlon ta bi bayansa tana jan trolley dinta, driver na tsaye jikin mota yana jiransu, yana hangota ya tafi ya amshi box din hannunta sannan ya bude mata back seat ta shiga bayan sun gaisa da shi, kallon Ajay dake zaune gaban motar tayi, murya can kasa tace “Good morning” Bai ce komai ba, hakan yasa tayi tunanin bai ji ba ta sake gaishesa a takaice yace “Same” Wani kallo tayi masa ta dauke kai, driver ya shigo motar ya tada suka bar gidan…. Karfe biyu saura suka sauka Ingila Ajay yayi masu order din Indrive da zai kai su har gida, sai bin sa da wani kallo take don he is not even helping with her box, iyaka hand luggage dinsa kawai ya dauka, driver din motar ya dau akwatin ya sa a booth ta bude motar ta shiga don tuni Ajay ya shiga kamar ba tare suke ba, Suna isa gida Khaleesat dai ta tsaya bakin apartment din da taga Ajay ya sa driver ya ajiye akwatin ta, ya gama wayar da yake sannan ya danna bell din apartment din, not long after aka bude kofar apartment din, step sis dinsa Baby ce ta bude kofar tana ganinsa ta rungumesa tace “Oyoyo Yaya….” Yace “How are you?” Tace “Am fine, welcome” Juyawa tayi ta kalli Khaleesat, ya dau box dinta ya mika mata yace “Can’t you greet?” Baby tace “Ina wuni” Daga haka ta amshi akwatin Khaleesat ta shiga ciki, ya juya ya kalli Khaleesat dake rakube gefe daya bayan ta amsa gaisuwar Baby, ya hade rai yace “Baza ki shiga ba Malama” Shiga parlon tayi sannan ya bi bayanta ta cire takalmanta nan bakin kofa, Aunty ce zaune parlor sai Ummi uwar Hadiyah da Gimbiya Firdausi, Mami ma na zaune parlon da Hajiya Nafisa, Khaleesat sai da gabanta ya fadi sosai ganinsu gaba daya, duk suka daga kai suna kallon ita da Ajay, kasan carpet ta duka a hankali ta gaishesu tana kallonsu gaba daya, Ajay ya zauna kan kujera ba tare da ya yarda ya hada ido da su ba ya gaishesu shi ma, just Hajiya Nafisa da Ummi sai Gimbiya Firdausi ne suka amsa gaisuwansa babu yabo babu fallasa, Mami dai ko kallon inda suke bata yi ba, ita kuwa Khaleesat dama babu wanda ya bi ta kanta suka ci gaba da labarin da suke a parlon, ko ya hanya babu wanda ya tambaye su, jikin Khaleesat yayi sanyi sosai ta daga kai ta kalli Ajay dake danna wayarsa kawai, bude kofar parlon aka yi sai ga Jay ya shigo yana gyara face cap dinsa, Khaleesat dake durkushe kan carpet bata san sanda ta karasa zaunawa a kan Carpet din ba bayan sun hada ido da shi, within few seconds ya dauke idonsa daga nata, ita kuwa bata fasa bin sa da kallo ba ko kiftawar kirki bata yi, Ajay dai bai yarda ya dago kansa ba tunda ya lura Jay ne ya shigo parlon wayarsa kawai yake ta dannawa, a hankali Khaleesat ta gaida Jay har sannan tana kallonsa, Jay ya zauna without looking at her yace “Lafiya lau, sannu da zuwa” Mami na kallonsa tace “Baka zo kayi breakfast ba yau Jawwad and ur phone isn’t reachable” Yace “A restaurant nayi” Mami tace “To Lunch fa?” Yace “Sai anjima” Baby ce ta shigo parlon rike da wayar Aunty ta nufeta tace “Momy u have a call” Aunty ta amshi wayar, Jay na kallon Baby ya nuna mata Khaleesat yace “Take her upstairs Baby” Baby ta kalli Khaleesat tace “Ok let go” Khaleesat ta sauke idonta ta mike ta bi bayan Baby da ta kai ta sama zuwa dakin da su Hadiyah suke, Hadiyah na kwance kan gado sai Maryam da Khadijah sisters din Walid, da Shahuda yarinyar Gimbiya firdausi ta biyu, sai Iklima yarinyar Hajiyah A’isha, ga kuma Bilkisu yarinya Hajiya Sumayya gaba dayansu cousins ne a dakin, kuma duk Shahuda ce babba sai Maryam Kanwar Walid, duk suka juya suna kallon Khaleesat kamar sun ga Alien ta shigo, ita kuwa ji tayi kamar an saka mata chain a kafa tsabar yanda ƙafafuwanta suka yi mata nauyi ganin zuka zukan matan dake dakin gashi duk sun zubo mata ido suna kallonta daga sama har kasa, tayi karfin halin karasawa cikin dakin ta zauna kasan carpet ta gaishesu gaba daya, Hadiyah dai sai kallonta take a walakance kamar taga bola, Shahuda na yatsine fuska ta kalli Baby tace “Wacece wannan kuma Baby kika shigo mana da ita?” Baby ta taɓe baki ta karyar da kai tace “I think Ya Ajay’s wife, yanxu suka zo” Shahuda ta mike zaune a hankali daga kwancen da take tana kare ma Khaleesat kallo daga sama har kasa, can tace “Dama wannan ce matar tasa? Ikon Allah, ashe zabiya ce” Tsaki Hadiyah ta ja tace “Don Allah mu ci gaba da maganar da muke, what were we even saying before we were interrupted?” Maryam na kallon Baby fuska daure tace “To ke uwar wa yace ki kawo mana ita nan? Duk dakunan dake sama ki rasa inda zaki shigo da ita sai wannan? Ko baki da kai ne? Dama akwatin ta ne wancan kika shigo mana da shi daki?” Baby ta bude ido ta langwabe kai tace “Ya Jawwad ne fa ya ce in kawo ta Aunty” Hadiyah ta mike zaune jin abinda Baby tace, fuska a murtuke tana kallonta tace “Yace ki kawo ta ina? Ina kika gansa yace ki kawo ta nan, yaushe ya zo? Dalla dau akwatin can ki fitar mana da shi daga nan, kinga nan yayi kama da inda za a kawo bare” Ita dai Khaleesat kallon direction daban take babu ko kiftawan kirki tana jin duk abinda suke cewa, Iklima ta juya tana mata wani matsiyacin kallo tace “Keee duk nan da kike gani jinin sarauta ne babu wani bare, babu ordinary blood don haka can you kindly get out of here? They are other rooms ba wannan kadai bane daki a gidan nan, ko kuma ki tafi Garage dama babu komai a ciki….” Khadijah tace “Can you imagine don rainin wayo ma wani wajen daban take kallo ana mata magana ko er uban wacece ita oho, bari ki ji duk nan babu sa’an ki wallahi, mu ba class din ki bane ta ko ina, don haka get out of this room” Baby na kallon Khaleesat tace “Sun ce ki tafi wani dakin you are not welcome in their midst” Mikewa Khaleesat tayi a hankali bata dai ce komai ba, Baby ta kalli yayyin nata tace “Ko in kai ta dakin Granny kawai?” Shahuda ta jefa mata wani harara tace “Are you stupid? What is Granny’s relationship with her da zaki kai ta dakinta? Ordinary person kamar ta zaki kai ta dakin Granny ko baki da kai ne, pls take her out before i loose my temper” Baby tace “Oh ohk, bari in kai ta dakin da ku ka ajiye boxes din ku to” Daga haka ta dau akwatin ta nufi kofa Khaleesat na biye da ita, Hadiyah ta bi ta da wani matsiyacin kallo kamar yanda Shahuda ma ta bi ta da kallon tsana don mutuwa ne kawai bata yi akan son Junaid ba amma daga karshe wai Khaleesat ta samesa a sama kusan a banza ba wani wahala tana er matsiyata da ita shine zata zama matar ɗan sarki me jiran Gado, Iklima ta rike haɓa tace “Dama ita ce Ya Jawwad ya so ya aura ya hadata da ke Hadiyah?” Hadiyah ta hade rai sosai tace “Plss bana son wannan maganar Iklima, keep quiet if you have nothing good to say” Shahuda ta koma ta kwanta tana jin wani irin bakin ciki a cikin ranta mara misaltuwa, gani daya da tayi ma Khaleesat taji duk duniya babu wanda ta tsana kamarta, Khadijah tayi dariya tace “Ko yaushe ma aka aurota da zata fara cuso kanta cikin abun da ya shafi gidan sarauta, who is she to intrude in our affairs? Who even invite her to this Convocation? Wallahi sai tayi da ta sanin zuwa taron nan, next time duk abinda ake a familyn gidan sarauta bazata yi marmarin sake zuwa ba balle ta shigo cikinmu, dama ace ba ordinary person bace da sauki, amma ke ba er kowa ba ki wani ce zaki shigo cikinmu ana mamaki magana ma kina kallon wani waje daban, to mun sa kafar wando daya da ita kuwa” Iklima tace “Wallahi she will regret coming to England” Hadiyah dai kokarin kiran Jay kawai take da wayarta fuskarta daure amma baya shiga. Dakin da Baby ta kai Khaleesat babu kowa ciki sai akwatunan wasu daga yan matan, a hankali Khaleesat ta zauna kasan carpet bayan Baby ta fita, lokaci daya hawaye ya fara sauka idonta kamar an bude pampo, daya bayan daya maganganunsu suka dinga dawo mata kai, Baby na sauka downstairs Jay dake zaune parlor har sannan ya kirata sannan ya mike ya fita waje ta bi bayansa, tuni dama Ajay ya bar gidan bayan da Baby ta raka Khaleesat sama, Baby na kallon Jay bayan ta bi sa waje tace “Gani yaya” Yace “Hope you gave her a separate room?” ta gyada masa kai yace “Ohk akwai abinci a gidan ai?” Ta ɗan karyar da kai tace “Akwai, fried rice Ummi suka dafa mana da chicken and Salad, very delicious” Yace “Ok now ki je ki xuba abincin ki kai mata da ruwa” Buga kafa tayi ta rungume hannu kamar zata yi kuka tace “Yaya na gaji da hawa stairs fa, sai ni ce kawai za ayi ta aika a gidan nan” Yace “C’mon Baby, be a good gal and do what I ask you” Ta langwabe kai a hankali tace “Ohk” Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma daga nan yayi tafiyarsa gidan da ya sauka which isn’t far from this House kuma duk gidajensu ne, Gimbiya Firdausi da Hajiya Sumayya ma can suke kwana da yayar mahaifin Hadiyah, Baby tayi yanda Jay yace mata ta kai ma Khaleesat abinci da ruwa sannan ta koma wajen uwarta ta kwanta jikinta, hira su Aunty suke amma gaba daya hankalin Aunty na kan Khaleesat da aka kai sama, abincin da Baby ta kai sama ma bata san ita zata kai ma ba ta zata yayyinta ne suka sa ta debo masu abinci da baza a kai ba, ita dai Khaleesat ko taɓa abincin da Baby ta kawo mata bata yi ba saboda bakin ciki gashi ta kasa daina kuka, she was so hurt da abinda suka yi mata, daga karshe haka ta tashi ta shiga bandakin da ta gani kusa da dakin ta dauro alwala ta dawo ta bude akwatinta ta dau hijab ta saka ta tada sallah…. Baby ta fito waje saboda kiran da Ajay yayi mata ta nufesa a inda yake tsaye tace “Gani yaya” ya mika mata ledan hannunsa yace “Take this food to her” Baby ta wara ido tace “Sau nawa za a kai mata abinci, Bayan ya Jawwad ya sa na kai mata abinci da ruwa daxu” Ajay yayi shiru jin abinda tace, can yace “Ohk, but still ki kai mata wannan ma” Tace “To ni ina nawa fa?” Ya hade rai yana kallonta yace “Ina wasa da ke ne?” Tayi yake tace “No Yaya” sannan ta amshi ledan ta juya ta koma cikin gidan, shi kuma yayi tafiyarsa can daya gidan, Baby na shiga parlor da abincin Aunty ta kirata ganin leda a hannunta, ta tafi har kusa da Aunty tace “Ga ni Momy” Aunty tace “Meye wannan a hannun ki?” Baby tace “Ya Ajay ne ya bani abinci in kai ma wife dinsa” Aunty ta karɓe ledan ta ajiye kusa da ita tace “Tafi ki ban waje” Juyawa Baby tayi ta tafi ta zauna ta dau wayarta ta ci gaba da kallon Cartoon din da take. Khaleesat na kwance saman Carpet bayan ta idar da sallah da kusan minti talatin har sannan ta kasa daina hawaye, ko kallon abincin da Baby ta ajiye mata bata yi ba, text message ne ya shigo wayarta ta dau wayar tana dubawa taga Ajay ne ya turo mata message yace “You need anything?” Taji wani sabon hawayen ya zubo idonta, reply ta mayar masa tace “Eh” Sai ga wani message din nasa yace “What?” Ajiye wayar tayi tana goge hawayen dake zuba idonta bata mayar masa reply ba, bayan minti biyar sai ga kiransa ya shigo wayar, Sai da ya kusa katsewa tayi picking ta kai kunne tayi shiru, yace “Ke kika saka min katin zaki yi shiru? What is that you need?” Shesshekan kuka ta fara yi ta kasa ce masa komai, Calmly yace “What happened?” Ta ma rasa me zata ce masa kawai ta fashe da kuka, shiru yayi yana sauraronta for few seconds, can yace “Come outside” Bata ce komai ba, calmly yace “Kin ji me nace maki?” A hankali tace “Uhm” Daga haka ya katse wayar, goge idonta ta dinga yi duk da hawayen yaki tsayawa, after some minutes ta mike ta tafi bandaki ta wanke fuskarta ta fito, tana tafiya a hankali ta sauka downstairs, kanta a kasa ta nufi kofar fita waje ba tare da ta yarda ta kalli inda su Aunty suke ba, su Aunty da Mami da sauran matan dake parlon duk suka bi ta da kallo har ta fita ta kullo kofar, waige waige ta dinga yi a neighbourhood din ganin bata gansa ba, after almost 2 minute ta hangosa walking toward her, ta sunkuyar da kanta har ya iso inda take tsaye sannan ta daga kai tana kallonsa, yana kallon kwayar idonta da yayi ja yace “Me ya faru?” Ta girgiza masa kai sai ga hawaye na silalowa daga idonta, bai sake cewa komai ba yana kallon wani direction din, bayan few seconds ya nuna mata wani roadside chair yace “Zauna can” Ba musu ta tafi ta zauna wajen da yace, ya karasa cikin apartment din, kallo daya yayi ma su Aunty ya wuce sama without saying anything to them, Aunty dake cin abincin da ya ba Baby ta kai ma Khaleesat ta bi sa da wani kallo, haka ma Ummi da Mami, dakin da su Hadiyah ke ciki Ajay ya bude, gaba daya suka juya suna kallon kofar, one by one suka dinga gaishesa ganin shi ya bude kofar, duk yayi masu kallo daya ya fice daga dakin without bordering to answer their greetings, ya bude wani dakin yaga Hajja tana bacci sai Hajiya A’isha dake dakin, gaisheta yayi bayan ta amsa ya kullo dakin, ya bude last room din yaga box din Khaleesat da handbag dinta sai wayarta, shiga ciki yayi ya dau akwatin da handbag din ya saka mata wayar cikin handbag sannan ya fita daga dakin, tun da ya sauko downstairs su Aunty suka bi sa da kallon mamaki har ya fice daga parlon without looking at them, duk suka kalli juna irin kallon mamaki, Ummi ta gyada kai tace “Tabdi, dauketa zai yi a gidan yake nufi ko me?” Gimbiya Firdausi dai tayi shiru tana kada kafa a hankali fuskarta dauke da wani expression ita ma na mamaki, Aunty ta rike haɓa tace “Kun ga wani ikon Allah kuma” Ummi tace “To ku ka san me ta kintsa masa?” Gimbiya Firdausi tace “Ku kyaleni da shi” Ita dai Mami bata tofa nata ba don bai shafeta ba, Ajay na komawa inda Khaleesat take zaune ta bude ido sosai tana kallonsa da mamaki, ya ajiye mata akwatin ta da handbag ya zauna leaving much distance between them, sosai jikinta ya kara sanyi ta dinga kallonsa babu ko kiftawa, wani bakin jinin yake son kara ja mata gun danginsu, wayarsa ya ciro yana duba hotel din da zai yi reserving, after a while ya gama making reservation din hotel din da yayi selecting ya biya kudi sannan yayi order din Indrive that will take them there, da kyar Khaleesat tace “Amma bai kamata ka dauko akwatina daga cikin gidan ba…..” Wani kallo ya jefa mata yace “I will give you a dirty slap” a hankali ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, after waiting for almost 15 mins sai ga Indrive din ya karaso, Mikewa yayi ya dau handbag dinta ya ajiye mata kusa da ita ya dau akwatin ya kai Ride din, ta bi sa da kallo sai kuma ta mike jiki a sanyaye ta nufi motar ita ma, Front seat Ajay ya shiga bayan drivern motar ya saka akwatin a booth din motar, ita kuma ta bude back seat ta shiga, bayan tafiyar kusan minti talatin suka isa hotel din da yayi booking, without much wasting of time in the hotel reception tunda ya riga yayi reservation online suka yi lodging din hotel room din, gefen gado Khaleesat ta zauna a dakin har lokacin jikinta a sanyaye yake bata taɓa tunanin abinda zai yi ba kenan, ya shiga bandakin dake cikin dakin ya dauro alwala ya fito don lokacin la’asar har ya wuce, mikewa tayi ita ma ta tafi ta dauro alwala, ko da ta fito har ya tada sallah, ta dau wani hijab din nata a box ta saka ta tafi bayansa ta tsaya zata bi sa sallan…..*
