Hausa novels

Halysaah Page 32 By Khaleesat Haydar

Sai da Jay yaga Khaleesat ta ci pepper soup din me ɗan yawa sannan ya mike ya koma kusa da Ajay ya zauna, After a while Ajay yayi breaking din silence din da ya ziyarci parlon yace “Iya daukar nauyin karatun ta kawai yayi Aunty?” Aunty Farida zata yi magana wayarta ya fara ring, dauka tayi ganin Umma ce ke kiranta ta wayar makociyarsu Sha’awa, ta mike ta tafi dakinta don daga wayar, Ajay dai kallon Khaleesat yake kamar yanda Jay ke kallonta don har ta shanye pepper soup din, ta ajiye bowl din kasa tana kokarin disconnecting drip din hannunta ta yanda zata bar cannula din kawai, Jay ya mike yana kallonta yace “What happened? Do u want to ease ur self” Da kyar tana girgiza masa kai tace “I think i want throw up” Ya karasa cikin hanzari yayi disconnecting din mata, ta tashi ta wuce bandakin Aunty Farida da sauri tana toshe bakinta, sai ga Aunty Farida ta fito daga daki, ta kalli inda Khaleesat ke zaune ganin bata nan ta kalli kofar bandaki, zaunawa kan kujera tayi a sanyaye tana kallonsu tayi kasa da murya tace “Yanzu yayata ta kirani wai an zo an tafi da mahaifin Khaleesat” Da mamaki Jay da Ajay ke kallonta, Ajay yace “Kamar yaya kenan?” A sanyaye Aunty Farida tace “Baban Abdul din ne yasa aka je aka tafi da shi” Daga Ajay har Jay kallonta suke with confusion da kuma mamaki, fitowar Khaleesat daga bandaki ya sa Aunty Farida tayi shiru bata sake cewa komai ba, bayan Khaleesat ta kwanta kan 3 sitter din Aunty Farida ta juya tana kallonta tace “Ko zaki shiga daki a maida maki drip din?” Khaleesat ta gyada mata kai don ita ma ta gaji da kwanciyar kujeran, Aunty Farida ta mike tace “Bari in ma makociyata magana sai ta sa maki a daki” Daga haka ta fita daga parlon, after some minutes sai ga ta ta dawo da Neighbor dinta Bayerabiya, Khaleesat ta tashi ta koma dakin Aunty Farida, Bayerabiyar ta bi ta ciki ta sa mata drip din, ita dai Aunty Farida na zaune parlor tayi nisa tunanin da take har makociyarta ta fito ta tafi, Aunty Farida ta kalli su Ajay a hankali tace “To abinda yayata ta kirani ta gaya min kenan” Ajay yace “So suke a biya su kudin makarantar da ya dinga biya mata?” Aunty Farida ta girgiza kai tace “Ai ba iya kudin makaranta bane Junaid” Ajay yayi shiru yana kallonta, Jay yace “Bayan makaranta akwai wani abu na kudi da ya hadasu ne?” Aunty Farida tace “Kwarai kuwa…. Shekarun baya Malam Ali wanda shi ne mahaifin Khaleesat dreban babban mota ne, babu garin da baya zuwa da kaya a babban mota a fadin Nigeria, kuma motar tasa ce iyaka idan kana da lodi ya kai maka kayan ka har inda kake so sannan ka biyasa, har Nijar ya sha shiga da kaya daga nan Nigeria ta haka ma ya hadu da yayata Aunty Zahra’u warce ita ce mahaifiyar Khaleesat, don mu yan Nijar ne mahaifinmu har yanzu yana nan da ransa mahaifiyarmu ce dai Allah yayi ma rasuwa shekarun baya, to bayan ya auri yayata ya kawota Kano Nigeria ya ajiyeta cikin matansa biyu, bayan en watanni da auren shine na dawo wajen yayata tunda bata da kowa a Nigeria bata san kowa ba, nan rikona ya dawo hannunta a lkcn ina da shekara goma, tsangwama da kyara babu irin wanda ban sha ba a wajen kishiyoyin yayata, gashi bata iya ce masu komai tunda ita ma ba barin ta suka yi ba, mace ce me hakuri da kauda kai, in zanyi magana ma sai ta hanani, a haka ta samu makaranta ta saka ni tunda a can kasarmu ina karatu aka daukoni aka kawo mata, sai da tayi shekara biyar a gidan sannan Allah ya bata Khaleesat, Mahaifin Khaleesat na da rufin asirinsa sosai don haka bamu rasa komai a gidan ba sai zaman lafiya da kwanciyar hankali daga kishiyoyinta wani lokacin har da uwar mijin, jifa jifa mu kan kai ziyara Nijar gun iyayenmu da yan uwa da abokan arziki, bayan shekaru 12 da auro yayata a lkcn Khaleesat na da shekara bakwai sai abokan Mijin yayata da yan uwa suka dinga zugasa akan ya shiga siyasa ya nemi wani babban mukami zai samu tunda yana da jama’a sosai, kuma ba laifi yayi karatunsa, matansa ma suka dinga zugasa akan ya fito takara, yayata tayi kokarin ganin ta hanasa tunda bai rasa komai ba a sana’arsa ta dreban mota amma ya ki, haka nan ya daga babban motarsa ya siyar har da sabon gidan da ya fara ginawa a nan Ɗan Ladi na sidi, ya daga duk en kadarorinsa ya siyar ya shiga siyasa gadan gadan, duk matansa sai da ya biya masu Hajji suka tafi da mahaifiyarsa, ya kuma canza ma ko wacce kayan daki, ya ba kowa kudi a hannu, kusan mutane goma sha biyu ya biya ma Hajji a lkcn, banda matasan anguwa da ya dinga biya ma kudin makaranta, yayi ta facaka da kudi a karshe dai ya zo ya fadi zabe, duk wa enda suka dinga zugasa suka juya masa baya, Allah ya rufa masa asiri bai amshi bashin banki da wani abokinsa ke ta zugasa ya amsa ba kasancewar da zaben ya gabato bashi da kudi kuma a hannu, bayan faduwarsa zabe aka shiga yanayi na babu a gidan, cin yau da kyar na gobe da kyar ga yayata na da cikin yan biyu, dama gidan da yake haya me tsada tuni ya saki bayan kudin hayan sun kare muka dawo mariri gidan gadonsa da ya bari a walakance don saura kadan ya kyautar lokacin da yake campaign sai gashi gidan ya mana amfani ya rufa mana asiri, makaranta me tsada da yaran gidan ke zuwa duk ya ciresu suka dawo gida suka zauna babu karatu, iyayen basu yi dubaran mayar da su na gwamnati ba, duk muka shiga mawuyacin hali a gidan, sai sanda ya samu mota yake lodin kaya ya kai a biyasa, sanda babu mota kuma sai dai kowa ta ciyar da kanta a gidan, yana kuma fin wata da watanni bai samu ko da karamar mota ba, duk ka zo kofar gida zaka gansa a zaune babu abun yi shi ma duk ya fita hayyacinsa, tuni yayata ta siyar da kayan dakinta ta fara sana’a ina taimaka mata, ta kuma saka Khaleesat a makarantar da zata iya biya don Khaleesat ta taso da kwazo da hazaka ga ta yarinya ce me shiga rai ko don kalan fatarta, don a unguwan ma gidan buzaye ake kiran gidanmu, hatta Mahaifinta kiri kiri yake nuna yafi sonta a cikin sauran yaransa wanda hakan ya ja mata tsana da kyara a gun matansa da yan uwanta, ko sanda yake da mota a hannu tsaraba na musamman yake ma Khaleesat ko da bazai yi ma uwarta ba, ana haka yayata ashe duk cinikin da nake sai ta kwasa ta ba mijinta a boye ban sani ba, ga dai matansa duk da hali na babu da aka shiga a gidan basu bar yayata ba, kullum cikin hada mata tuggu da makirci ake wajen miji da uwarsa, cikin wannan yanayi yayata ta haifi yan biyunta wanda haihuwan da tayi na karshe kenan a gidan, a lkcn matsaloli har sun fi na da, jarin yayata ya karye kuma babu wani abu da zata siyar ta tada jarin, ga jegon yan biyu tana yi ga yunwa wani lkcn sai makota ke zubo abinci a kawo mata, iyayenmu a can Nijar ba masu karfi ba balle su taimaka mana, a haka na bi wata kawata zuwa nan garin Lagos tana siyar da abinci, kafin nan fa nayi aure har na fito, duka auren bai cika shekara daya ba, na auri wani abokin mahaifin Khaleesat, karayar arziki na samun Malam Ali na dinga fuskantar matsaloli gun mutumin da matansa uku wanda daga karshe ya sakeni dama ba saboda Allah yayi auren ba saboda kalan fata ta yayi, ina nan Lagos nake tallafa ma yayata da ‘ya yanta uku, don bana son karatun Khaleesat ya tsaya duk da ta samu Foundation sosai sbda makarantar da ubanta ya sa ta ma a sanda yake da rufin asirinsa yafi na sauran yan uwanta tsada, na zo Lagos da yan shekaru yayata ta kirani wataran wai gashi an ba Baban Khaleesat babban mota har zai kai kaya kudu, matsaloli sun fara warwarewa tunda har an biyasa kudin kai kayan kuma kudade masu tsoka gashi har ya siya kayan abinci masu yawa ya ajiye a gida, tace in Maza in dawo gida kawai dama ita hankalinta ba a kwance yake da zamana a lagos ina sana’a ba, a haka ta takurani har sai da na dawo Kano, a sannan Khaleesat na da shekaru sha shidda tana kuma gab da gama secondary don da wuri aka sakata a makaranta, na dawo da wasu kwanaki ranan muna zaune tsakar gida da yamma sai ga mahaifin Khaleesat an shigo mana da shi ranga ranga ko motsin kirki bai yi, wanda duk gaba daya mun zata yana hanyar kudu har ya kusa Lagos, ga dai shi babu ko kwarzanen ciwo a jikinsa kuma wa enda suka
kawosa suka ce ai daga asibiti ma aka taho da shi a can wajajen garin yarbawa, sannan kwanansa uku a asibiti aka sallamosa wasu mutane da suka shaidasa tunda dreba ne suka biya kudi aka sako sa a mota aka dawo da shi Kano, sosai hankalinmu yayi mugun tashi a wannan lokacin, sae da Malam Ali yayi kwana biyu a gida ana ta addu’a da neman taimako kafin ya farfado gaba daya har yana iya magana, nan fa yake sanar mana barayi ne suka kwace Trailer da kayan mutane a ciki bayan sun shaka masa wani farin abu, tashin hankalin da duk muka shiga bazai misaltu ba a lokacin, daga Trailern har kayan cikin trailern ya doshi miliyan dari da tamanin” Shiru Aunty Farida tayi tana goge hawayen dake zuba idonta, Jay that was shock ya kalli Ajay dake kallon Aunty Farida babu ko kiftawa jin zunzurutun amount din da ta kira, Aunty Farida na share idonta ta ci gaba tace “A ranan yan sanda sun kusa goma suka zo a motoci, a haka aka sa ma mahaifin Khaleesat ankwa ana jan sa kamar barawo aka fita da shi yaransa da matansa na kururuwa suna ihu, Khaleesat kadai ce bata motsa daga inda take zaune da littafi a hannunta ba sai hawaye kawai, duk aka cika kofar gidanmu babu masaka tsinke kai kace barawon gaske aka zo dauka, mun shiga tashin hankalin da baya faduwa a wannan rana, kuma duk mutanen da yayi ta biya ma Hajji a sanda yake da hali, da kuma mutanen da ya taimaka ma aka rasa wanda zai bi yaga inda ma aka kai sa, ashe daga kano Abuja aka nufa da shi, bayan dogon binkice aka gano trailern an yasar a wani gari an kuma juye duk kayan cikin trailern, dama me trailer daban, me kaya daban, adadin kayan cikin trailern kuma zai yi na miliyan dari, to ba kowa bane me kayan cikin trailern nan illa mahaifin Abdul, sam ba a yarda babu sa hannun Mahaifin Khaleesat a juye kayan cikin trailern ba, dama kuma yan unguwa na jin haushin ya samu lodi me yawa haka ya tafi kai kayan shi kadai ko yaron mota bai dauka ba, kuma ko wani dreba an san sa da yaron mota daya ko biyu, nan aka yi ta zuga baban Abdul akan kar ya yarda wai dama planning Baban Khaleesat yayi don ya taɓa yi ma wani mutum haka da dadewa yace barayi sun kwace kaya a hanya sai yafewa mutumin yayi, kuma wai don yaga Alhaji Musa wato mahaifin Abdul me kudi ne sosai shi yasa zai cucesa yace an sace kaya tunda yanxu ta kare masa bai da komai, kuma wallahi sharri ne ba haka Baban Khaleesat yake ba, bai cin kayan wani baya taɓa abu in ba nasa bane, beside bai taɓa sanin Baban Abdul ke da kayan ba sai da iftila’in ya faru sannan yaga me kayan, shi dai kawai ance masa ga Lodi zai kai lagos ya kuma amince tunda sana’ar sa kenan kuma kullum fatan samun Lodi yake, ko da babu zugin yan anguwa baban Abdul bai yi kama da mutumin da zai iya yafe kudinsa ba don kana ganinsa kasan bashi da mutunci bashi da kirki, sai da Mahaifin Khaleesat yayi wata uku bamu sa shi a idonmu ba kafin aka dawo da shi kano duk ya rame yayi baki ya dawo kamar ba shi ba, da kyar aka bari muka gansa a fursin da aka ajiyesa na nan kano, ranan duk bamu yi bacci ba bayan mun dawo gida, yayata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa don tun dauke mahaifin Khaleesat dama ta fara alalan siyarwa don mu rufa ma kanmu asiri saboda ɗan jarin da nake da shi nima duk ya karye bani da komai, kafin ma a dawo da mahaifin Khaleesat kano sau uku muna zuwa gidan Alhaji Musa a Nassarawa GRA domin mu basa hakuri ko zai dubi halin da muke ciki ya taimaka a sake mana Baban Khaleesat amma duk aka mana koran kare, na farko masu gadi ne suka kore mu, na biyu Matarsa ranan ta rako baƙinta ta gan mu tayi mana cin mutunci ni da yayata da Baaba Gaje ta sa aka kore mu, na uku kuma ɗan cikinsa Abdul wanda dama shi kadai ne namiji a ‘ya yansa, ana haka aka shiga kotu ko lauya baban Khaleesat bashi da tunda bamu da halin daukan Lauya, rana na farko da aka kawo Malam Ali kotu daga prison ni da Khaleesat da kishiyar yayata Mama Shatu ce muka je kotun don sauraron karan, to a ranan Abdul yaje kotun shi ma a matsayin daya daga lauyoyin mahaifinsa ashe shi ma Lauya ne, sarai na ganesa da na gansa a kotun don ranan karshe da muka je gidansu har ce ma masu gadi yayi in muka sake dawowa su rike mu yan sanda ne za su zo su tafi da mu, zaman kotu da akayi a wannan rana babu wani positive outcome da ke nuni da cewar da nasara a case din, kwata kwata babu alamun nasara tunda Malam Ali ba kowa bane, kuma ba shi da kowa bai da komi, bashi da wanda zai tsaya masa, haka aka dage shari’ar zuwa wani watan shi kuma za a maidasa prison cikin motar da ta kawosa ko belinsa anki badawa, Khaleesat ta dinga kuka sosai a haraban kotun tana kallon yanda aka shigar da babanta motar prison, nima ina rungume da ita ina hawaye, wanda wannan ne ya ja hankalin Abdul da fitowarsa daga kotun kenan zuwa kanta, ba shi ba hatta sauran jama’an wajen kallonta suke, Alhaji Musa babban mutum ne kuma me kudi wannan yasa har da yan jaridu a haraban kotun, wani ɗan jarida ya nufo mu yana tambayar me za mu iya cewa game da zaman da aka yi yau a kotu, budan bakin Khaleesat cikin kuka sai cewa tayi Allah ya saka ma babanta sharrin da aka masa, ina tunanin a nan ne Abdul ya fahimci er gidan wanda suke ƙara ce Khaleesat, duka duka shekarunta sha shidda a sannan amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta, ranan ma tsautsayi yasa ta fito babu Nikab duk da ba a shiga da Nikab amma duk inda zata bata fita babu Nikab, in ma bata sa ba uwarta zata tilastata ta saka, hatta nima bana fita babu shi haka Mahaifiyarta saboda bakin jama’a, kun ji inda Abdul ya fara ganin Khaleesat, a sannan kuma kawai motarsa ya shiga, sai wani Lauya me zaman kansa ya nufo mu, ya ja mu gefe yana kokarin calming din Khaleesat, nan ya tambayeni me ya faru, me ya kawo mu kotu, nayi briefing din masa komai nima ina kuka, ya tambayeni zuwa yaushe aka daga karan, na sanar masa, yace to in basa lambata in sha Allah anjima zai kirani yaga abinda za ayi akan case din kuma mu kwantar da hankalinmu, ko wayar bani da shi a sannan, instead sai na basa Address din unguwanmu Mariri, ita dai kishiyar yayata na zaune karkashin bishiya tayi tagumi, a haka muka bar kotu ranan rai babu dadi muka koma gida, bayan kwana biyu ranan da yamma wajen karfe shidda muna zaune tsakar gida ko wacce na fafutukar abinda zata dora ta ciyar da kanta da yaranta, don yanzu kowa takai takai a gidan, kishiyoyin yayata har sun sake ‘ya yan su maza kanana suna fita almajiranci suna ciyar da kansu, matan kuma a dora masu talla su tafi can bakin kasuwa, yayata dama ina taimaka mata muna sana’a a gida, kudin waec din Khaleesat ne dai muka kasa hadawa gashi saura kwanaki kadan a fara, kamar daga sama sai ga Mahaifin Khaleesat ya shigo gidan kamar an jefosa, Khaleesat ce ta fara ganinsa ta tafi da gudu ta rungumesa, duk muka mike tsaye a tsorace muna kallon ikon Allah baki bude, yayata tayi karfin halin tunkararsa tana tambayarsa daga ina yake haka, kar dai gudowa yayi daga gidan yari, Baban Khaleesat yace kawai shi dai ce masa aka yi an bada belinsa daxu da rana, sai gashi kuma aka daukosa aka kawo har gida aka ajiyesa, tsabar mamaki duk muka kasa cewa komai a tsakar gidan, yayata ta kama hannunsa hawaye cike idonta ta kai sa dakinsa don shi ma duk a firgice yake kana ganinsa kasan ba karamin wahala ya sha ba, sai a sannan yaran gidan suka fara ihu suna murnan dawowan mahaifinsu suna ta tsalle tsalle, sauran matan duk suka bi bayan yayata zuwa dakin Baban Khaleesat”

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it’s better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500

Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman

Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

Back to top button