Hausa novels

Abban Sojoji Takun Karshe Book 3 Chapter 103 Complete Novel

*Father of soldiers*

*🔥TAKUN ƘARSHE🔥*


Am sorry,

tsoro ne ya kamata,Zuciyarta sai harbawa take yi da Æ™arfi da Æ™arfi,wani irin wahalallan yawu ta haÉ—iya,Sam takasa Motsawa,tabbas wani ne ya shigo cikin gidan tunda harta Ambaci sunan Daddynsu bai amsa mata ba,A Æ™opar É—akin ta tsaya cak kamar an dasa mata Aya,Saboda duhu ta ko’ina bazata iya hangen meke wakana ba acikin falon,tunanin kiran Abusufyan tayi,da sauri ta juya hannunta na kerma tana Æ™oÆ™arin tura Æ™opar É—akin ta shiga daga ciki,Ta jiyo ihun Oummansu dake a downstairs,A gigice Sehrish ta juya da gudun gaske ta nufi downstairs,cikin rashin sanin ina zata taka saboda duhu Æ™afafunta suka harÉ—e daga saman benen gaba daya ta rubza mashi,mirginowa ta dinga yi daga saman benen har ta faÉ—o Æ™asa ta Æ™ume goshinta,Sosai taji raÉ—aÉ—in buguwar da tayi amma a haka ta jure ta daddage ta mike,tana laluban hanyar zuwa É—akin Oummansu cikin duhun,Sosai take jiyo sautin koke koken da Oummansu keyi,Duk tabi ta ruÉ—e ta rasa ina zata dosa,
Da Æ™arfi ta soma kwala mata kira”Oumma!Oumma!!”tamkar makoshinta zai 6allo waje,duhu ya hana ta gano kopar É—akin,Bangon falon tabi ta dinga sanya tafin hannunta tana shasshafawa,da taimakon Koke koken da Oumman keyi ne ta samu ta ruÆ™o Handle É—in kopar É—akin,Da karfin Æ™arfe ta sanya Æ™afarta tare da Harba Æ™opar É—akin ta buÉ—e,Bata iya ganin komai ba saboda duhun da É—akin yayi an kashe Hasken É—akin kamar yadda aka kashe na Falo,
Shafa bangon tayi dayake tasan inda Switch É—in yake,Cikin sa’a ta kunno shi Æ™itt Haske ya gauraye ko’ina na É—akin,

Gabanta ne yayi wani irin mugun bugu rasss!ƙwayar idonta tamkar zata faɗo ƙasa saboda Tashin hankalin da sukayi arba dashi,
Ta ko’ina ya mamayeta,Æ™okarin rabata da kayan jikinta yakeyi,babu kunya babu tsoron Allah,Wani irin kukan kura Sehrish tayi bata dira a ko’ina ba sai asaman gadon,A hargitse ta Cakumi Wuyan rigar jallabiyar dake ajikinshi,da iya Æ™arfinta na Æ™arshe tayi wurgi dashi gefe guda,Ya gangara Æ™asan gadon,
Fashewa tayi da matsanancin kuka,tana kallon Oummansu wadda tuni ta jima da sumewa asaman gadon,
Jijjiga jikinta sehrish ta shiga yi tana Ambaton sunanta,Dakatawa tayi da yin kukan tare da wurga Æ™wayar idonta kan Mutumin wanda ke tsaye a bakin gadon,jallabiyace a jikinshi,kanshi kuwa Rawani ne,Ya sanya face mask a fuskarshi,”
Huci kawai takeyi tana kallonshi,
Hannu yasa tare da zame takunkumin dake a fuskarshi,Mummunane sosai bai da kyau ko miskala zarratin,irin mutanen da kallo guda zakayi masu kaji ka tsanesu,Sehrish bazata ta6a mantawa da fuskar wannan fasiƙin mutumin ba,
Ranta a matuÆ™ar 6ace tace”Mugu azzalumi!dama sai da raina ya bani cewa kaine!Ashe har yanzu kana bibiyar rayuwarmu!Wai uban mi muka tsare maka ne!Meyasa bazaka fita arayuwarmu ba!,”
Jinjina kai Ya sayyadi yayi yana kallonta batare da yace komai ba,sai da ta kammala balbaleshi da faÉ—a sannan yace”kin gama”?banza tayi bata tanka mashi ba,
“Bansan wacece ke acikinsu ba,Amma fitsarar da kikayi mun a yanzu ya tabbatar mun dacewa rishi ce ke,Dama tun kina yarinya kangararra ce ke,balle kuma yanzu da kika samu Æ´anci kika zama cikakkar budurwa,har kika samu bakin gayamun magana,Ban zo nan don inyi jayayya dake ba,Wurin uwarku nazo don ta bani haƙƙina na aure dake akanta…..”
Tunkan ya Æ™arasa maganar Sehrish ta Ambaci”innalillahi wa’inna ilaihirraji’un”dafe kanta tayi saboda jirin da take gani,Wani Æ™ululun baÆ™in ciki ne ya tokare mata makoshinta,
DaÆ™yar ta iya buÉ—e baki tace”Amma baka da kunya!Tunda nake banta6a ganin É—an akuya bunsuru ba,wawa jakki ba,kuma daÆ™iÆ™i irinka ba!Wai kai wani irin Dabbane…..”A fusace Sayyadi ya daka mata tsawa tare da furta”Kalas!karki kuskura ki Æ™ara jifana da waÉ—annan munanan kalaman!Ki iya bakinki in ba so kike na keta maki rigar mutunci ba awurin nan!Æ™aramar Æ´ar iska kawai,kin manta lokacin da kuke rayuwa a Æ™arkashin ikona?idan kin manta toh bari na tuna maki,”
Yayi maganar cike da sheÆ™iyanci yakai hannunshi tare da shafa gabanshi dake asandare yace”Ina fata kin tuna,”
Waro ido waje sehrish tayi yayin da idanuwanta suka cicciko tab da Æ™walla ta furta”Nashiga uku!”
Fashewa yayi da dariya kafin ya É—aura da cewa”kin tuna lokacin da nake damÆ™ar wuyanku in tasa ku gaba sai kun tsotsi gabana”?
Innalillahi wa’inna ilahirraji’un!fashewa tayi da matsanancin kuka na tashin hankali,Tsabar raÉ—aÉ—in tunawa da wannan Æ™azantar yasa ta fara yunÆ™urin yin amai ga Æ™irjinta da yayi mata zafi sosai,
Muryarta adisashe ta soma magana”Allah ya isa tsakaninmu dakai!Wlh Allah bazai ta6a barinka ba,Sai ya saka mana Cin zalin da kayi mana,in sha Allah tun agidan duniya zaka fara gir6ar abunda ka shuka,Ƙarshenka bazaiyi kyau ba Sayyadi,Sai kayi danasanin haihuwarka da Uwarka tayi acikin duniyar nan!Natsani ganin mummunar fuskarka fiye da yadda na tsani mutuwa,Munafuki,mugu azzalumi,fasiki,Sannan kuma matsoraci!tsabar bakin ciki ya hanaka sakat saboda ganin irin Canjin rayuwar da muka samu,Ni bansan wani tsautsayi bane yasa Oummanmu ta aureka ba,Nasan ba hakanan ka Æ™yaleta ba,domin kuwa duk wata mace me hankali da tunani bazata auri dabba,daÆ™iÆ™i,bunsuru irinka ba,Jahilin addini jahilin rayuwa,Kana yin amfani da iliminka wurin cutar da rayuwar al’umma, idonta arufe take zazzaga mashi masifa,
Goya hannayenshi yayi asaman Æ™irjinshi yana kallonta,maimakon yaji haushin kalaman da ta yada mashi,Sai ma yatsinci kanshi da jin sha’awarta,zuba mata kwartayen idanunwashi yayi yana bin jikinta da kallo batare data ankara ba,Kayan baccin jikinta shara shara suke,Subhanallah,

Sautin dariyar da taji ne yasa ta dakata da yin masifar,ta buÉ—e idanuwanta da sukayi jawuur dasu,Zuba mashi ido tayi tana kallonshi ganin yana dariya,
“Kin gama naki”?yayi maganar yana sakar mata wani shu’umin murmushi,
Shiru tayi batace mashi komai ba,la66anta duk sun bushe sun ƙame,ga ƙishin ruwa da take ji,

“sai yanzu nake danasanin barinku da nayi araye!naso ace tun lokacin da kuke a hannuna na tattaraku gaba É—aya na aika ku lahira,Amma Allah bai nufa ba,Duk yadda naso Sihiri na yayi tasiri akanku Amma hakan ya faskara,Na bibiyi rayuwarku tun lokacin da Mlm nura ya mayar daku wurin wata tsohuwa mai taurin kan tsiya……”
Tunkan ya Æ™arasa maganar Sehrish tace”hakan na nufin cewa,kaine kayi silar mutuwarta”?
shu’umin murmushin nan nashi ya saki tare dasa hannu yana gyara rawanin kanshi yace”Æ™warai kuwa!ni na kashe ta,saboda na nemi ta bani haÉ—in kai Wurin ganin na kawar daku,tayi mun gardama harda tofa mun kakin Majina ajikina,Wannan dalilin ne yasa nayi silar mutuwarta,duk da haka ban rabu daku ba,Bayan an kaiku Cell na tura inspector Esha donta tursasa maku akan ku amince Zaku amsa laifin ku kuka kashe ta,har kun amince sai kuma Ciwon Hosana ya tashi,Wanda hakan yasa Ƴan sanda suka kaiku Asibiti,Daga nan ne Allah ya haÉ—aku da Marshal Omar,har ya taimaki rayuwarku,Naji haushi sosai kamar na binne kaina lokacin,amma ba yadda na iya,Haka naci gaba da bibiyar rayuwarku,har lokacin da Omar yakai ku Kaduna gidan Yayanshi General Ishaq,Nan ma na biku don na kawar daku,babu wanda yasan duk wannan shirin nawa da nayi,Ni na tura matata wurin hafsat É—iyar Laila,ta bata zunzurutun kuÉ—i har miliyan shidda donta Zubar mata daku,daga nan na halaka ku,hafsa ta kar6i kuÉ—in amma bata aiwatar da abunda ta sanyata ba,a Æ™arshe ta buÆ™aci ta dawo mata da kuÉ—inta in ba haka ba zata yi Æ™ararsu………”
Duk cikin abunda ya sayyadi yake faÉ—a mata bakomai yafi É—aga mata hankali ba,fa ce Mutuwar tsohuwa,Ashe dama shi ya kashe ta duk don saboda su?Sosai ta fashe da kuka tana kallonshi hawaye wasu na bin wasu sam ta kasa furta komai,

Ko ajikinshi saima dariya da yake ta faman 6a66akawa kamar wani zautacce,
“Meyasa?meyasa duk kayi wannan”A fadace tayi maganar,jijiyoyin wuyanta duk sun fito ruÉ—u ruÉ—u dasu,
Tsagaitawa yayi da yin dariyar yace”É—aukar fansa nake yi,ko ince mukeyi!Laifi akayi mana wanda bazamu ta6a yafewa ba,gaba É—aya danginku a tafin hannunmu suke,duk wani motsi naku akan idonmu kuke yin shi,Nasan zaki yi mamaki,kuma zaki yi kokwanton ko Æ™arya nake yi…..”Hankali atashe sehrish take kallonshi,Ba Æ™aramin Caza mata Æ™waÆ™walwarta yayi ba,
“Nazo nan ne,Don in kashe mahaifiyarku bawai don in biya bukatata da ita ba,Sai dai kuma ganinki da nayi yasa na canza ra’ayina akan hakan,Surar jikinki ta yi matukar tafiya dani,Yanzu haka da nake magana dake,tsuma kawai nakeyi,kin matukar tayar mun da sha’awata,tunda nake ma ni ban ta6a jin sha’awar mace ba,Sai da nayi tozali da kyakkyawar surar Æ™irjinki,Nayi mamakin yadda kika Cika ta ko’ina,ba kamar yadda na sanki ba,Kai gaskiya Abusufyan ya iya raino,Naira ta zauna maki shiyasa kika canza,”
A ruÉ—e Sehrish take furta”Allahumma ajirni fil masibati wa’aklifni khairan minha,tsananin tsoro ne ya kamata,ganin ya sanya hannu yana Æ™okarin tattare jallabiyar dake ajikinshi,Tashin hankali!
..girgiza kai ta shiga yi tana fadin”karka kuskura kace zaka kusanto ni,Ni matar aure ce,”a ruÉ—e tayi maganar tana Æ™oÆ™arin saukkowa daga saman gadon’..
“Oh ashe ke matar aure ce,wannan ae ba wani abu bane dan naci amfanin gonar wani,”
Durowa tayi daga saman gadon tare da nufar Æ™opar fita daga É—akin,Aikuwa a zafafe Ya sayyadi ya biyo bayanta,kafin tayi wani yunkuri ya damÆ™i rigar baccin dake ajikinta,nan take rigar ta zame har izuwa mid back É—inta,Fashewa ta kuma yi da matsanancin kuka tana ambaton Sunan Daddynsu,Æ™oÆ™arin kwale mata rigar yakeyi gaba dayanta amma ta hana hakan,Ba zato ba tsammani taji yana goga mata abun gabanshi ta bayanta,Wa’iyazu billah,Daddagewa tayi da iya karfinta na Æ™arshe,Ta kai mashi naushi a tsakiyar cikinshi,Amma wani abun mamaki ko gezau baiyi ba,Kamar ta naushi Æ™arfe,kiciniyar Æ™wace kanta ta shiga yi daga hannunshi,Ji take kamar ta haÉ—iyi zuciya ta mutu saboda takaici,
Saukar harshenshi taji asaman fatar bayanta,kamar wani maye haka ya dinga lashe shi,
“Wayyo Allah na Oumma!na shiga ukku nabani na lalace!”cikin fitar hayyaci Sehrish ta samu hannunshi daya zagayo dashi ta gabanta,Ta daddage ta gartsa mashi cizo har saida ta fasa fatar hannunshi,raÉ—aÉ—in da yaji ne yasa shi yin saurin sakinta,A hanzarce ta sanya hannunta tana Æ™oÆ™arin buÉ—e Æ™opar É—akin,Sayyadi ya taÉ—iyo Æ™afarta gaba daya ta kife Æ™asa,kanta ya bugu sosai,fashewa tayi da matsanancin kuka tana bugun floor É—in da hannunta,Ta rasa ina zata tsoma ranta,jin motsinshi yasata yin saurin miÆ™ewa zaune tana ja da baya,
Cikin Shesshekar kuka take Ambaton sunan Daddynsu da sunan Oummansu don su kawo mata É—auki,
Hannayenshi ya sanya tare da tattaro jallabiyar jikinshi ya É—age ta sama har izuwa saman cikinshi ya naÉ—e ta,tsikar jikinta ce ta fara tashi,ganin uban cunkoson gashin jikinshi mara kyan gani,hannu yasa ya kwale gajeran wandon nashi,Rasss taji mummunar faÉ—uwar gaba,
Dariya ya dinga yi yana nuna mata abun nasa yayin da yake tunkararta tana ƙoƙarin ja da baya,
Koke koken da sehrish keyi ne ya fara kai mata ziyara cikin kanta,lokaci guda Kwakwalwarta ta fara tariyo mata kukan Æ´a’Æ´anta yayin da suke ambaton Sunanta,Oumma Oumma aduk lokacin da suka shiga wani hali,Allah ne ya farfaÉ—o da ita,Hannu tasa tare da dafe kanta wani irin raÉ—aÉ—i ta dinga ji yanayi mata,tunkafin ta buÉ—e idanuwanta ta soma ambaton Sunayensu Sehrish Hosana Jahad,wani ihu da sehrish ta kurma ne yasa ta yin firgit ta mike zaune daga saman gadon,Zazzare idanuwanta tayi akan sayyadi daya duÆ™ufa akan Sehrish,Ya sanya duka hannayenshi ya tallabo kanta yana Æ™okarin Kafa bakinta agabanshi,Hasbunallah!

 

Kukan kura abu tayi a fujajen ta diro daga saman gadon,a harzuÆ™e ta rarumi Side drawer É—in gadon,gaba daya ta kinkimota ta É—aga sama da gudun gaske,Bata sauketa a ko’ina ba sai akan sayyadi gaba É—aya Ta rotsa mashi ita asaman kanshi,wani irin jiri ne ya É—ebe shi ya soma tangal tangal zai faÉ—i,Rawanin kanshi tuni ya yi tsalle ya fadi kasa,
Tsabar raɗaɗin da yaji ne yasa shi sakin Wuyan sehrish,Jallabiyarshi ta sauko ƙasa daga naɗewar dayayi mata,Rawanin kanshi kuwa tuni ya wargaje aƙasa,wani irin jiri ya soma gani kafin ya dawo hayyacinshi,Ganin Abu yasa shi ɗaure fuskarshi tamau,idanuwannan sunyi jawur dasu babu ɗigon Imani akansu,Kallon kallo suka shiga yi,jinjina kanshi ya yi yana huci kamar wani mayunwacin zaki,gadan gadan ya tunkareta,gashin kanta ya damƙo tare da yin wurgi da ita,gaba ɗaya ta kife ƙasa,juyawa yayi ya koma kan Sehrish wadda ke yashe ƙasa a sume,naɗe jallabiyar jikinshi ya soma yi,zukunnawa yayi agabanta yana ƙoƙarin tallabo kanta,

Abu dake kwance a Æ™asa,ta É—aÉ—É—ago da kanta,yayin da hawaye ke ta sharorowa akan fuskarta,karaf idanuwanta suka sauka akan Sirinjin Allurar da Likita yayi mata É—azu da safe,Wani tunani ne yazo mata,matsawa tayi tare da miÆ™a hannunta,ta DamÆ™i sirinjin allurar,yunkurawa tayi ta miÆ™e,cikin sanÉ—a ta soma tafiya tana tunkararshi,motsin da ya ji abayanshi ne yasa yayi firgit,Juyowar nan da zaiyi don yaga me take Æ™okarin yi mashi,Ba zato ba tsammani,Abu ta daddage ta burma mashi Allurar acikin Æ™wayar idonshi,Zuruf ta nutse acikin Æ™wayar idonshi,Wata irin Æ™ururuwa Sayyadi yayi,Gaba É—aya yabi ya firgice ya gigice ya zauce,Wani irin raÉ—aÉ—in Azaba mara misaltuwa Yaji mai haÉ—e da zogi,Caccaka mashi allurar ta dinga yi,gaba daya ta tsiyaye mashi idanuwanshi duka biyun,sulalewa yayi kasa yana burgima,Wata irin Æ™ururuwa da ya soma yi gaba daya kwaratsin shi ya karaÉ—e ko’ina na cikin gidan,Abu ta shammace shi,ta naÆ™asa mashi idanuwanshi wanda ya kasance rauninsu ne,a Æ™ungiyarsu ta matsafa da zarar member ya rasa idonshi,duk wani sihiri na jikinshi zai rabu dashi ne,Ya dawo normal mutun kamar kowa,

Tsananin tsorone ya kama abu ganin yadda jikin ya sayyadi ke fitar da wani irin baƙin hayaki batare da wuta naci ajikinshi ba,kamar tsumma haka ya nannaɗe wuri guda,hannu tasa tare da toshe kunnuwanta,Saboda sautin kururuwar da yake yi tamkar  Ana buga ganga acikin kunnuwan nata haka take ji,sosai ta runtse idanuwanta,
Lokacin da ta buÉ—e su,Sai da ta tsorata,ya 6ace 6aat babu shi acikin É—akin sai dai Tsummar jallabiyarshi tare da rawaninshi,da kuma sharba sharban Silifas É—inshi,

 

*Boss Bature*

A hankali yake saukowa down stairs,jikinshi na sanye da Jeans tare da t.shirt fara,gaba ɗaya ya canza,komai nashi ya sauya,tamkar ba Sgr ba,kwata kwata babu annuri akan fuskarshi,ya ƙara haske sosai,ya kuma yi rama,

Jin takun tafiyarshi yasa suka ɗago suna kallonshi,Tsayawa yayi yana ƙare masu kallo one by One,Fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa,kullum ne sai sun zauna Zaman jiran dawowar junaid,babu yadda baiyi dasu ba akan su daina hana idonsu bacci Amma sun ƙiya,koda zasu yi baccin to sai dai ya ɗaukesu anan falon,Yayin da suke zaune zaman jiran dawowar junaid,

Ƙarasa saukowa yayi daga Saman stairs É—in Ya nufi wurinsu,tunkan ya isa yace’Bana hanaku zama anan ba”?
Shiru sukayi saboda basu da amsar da zasu bashi,
Fitowa azmee tayi daga kitchen ta tunkaro wurin da suke,Æ™arasowa tayi tana faÉ—in”Yawwa Rafayet,Dan Allah kayi Masu magana,tun É—azu nake fama dasu akan suci abinci amma sun Æ™iya,narasa yadda zanyi dasu,
ÆŠaure fuska jahan yayi tare da cewa’Dan Allah abarmu muji da abunda ya Dame mu,Idan muna jin yunwa zamu taso ne muci,”
Yana kai Æ™arshen maganar Fawan yace”Ni wlh komai ya fita raina,Nasaba cin abinci tare da baby junaid É—inmu,yanzu kuma babu shi,Taya ma zan iya Cin abinci?bayan bansan halin da junaid yake ciki ba,Shin yaci abinci ko bai ci ba,”ya Æ™arasa maganar tamkar zai fashe da kuka,
“Allah yasa basu cutar mana dashi ba,Junaid ya saba rayuwarshi acikin Æ´an uwanshi,hakanan wasu mugaye marasa imani sun É—auke mana shi,”Acewar Irfan,
Guntun tsoki jabeer yaja kafin yace”Ni babban takaici na,Duk yawanmu nan,arasa wa za’ayi garkuwa dashi sai junaid,Saboda bakin Hali irin na mutanan nan,wlh duk ranar da sukayi kuskuren da Asirinsu ya tonu sai sun É—anÉ—ani kuÉ—arsu,”

Kasa kunne Sgr yayi yana sauraronsu,tsananin tausayinsu ne ya kamashi,Ita kanta azmee jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba jin maganganun da sukeyi,Banga laifinsu ba,dole ne suyi kukan rashin junaid,yaron ne akwai shiga rai,Ya damu da kowa,kowa nashi ne,
“Wlh bazamu iya jure rashin junaid ba,Ya rafayet dan Allah idan sun Æ™ara kira,A sanar dasu cewa,Su dawo mana da junaid,Ni su É—auke ni,In yaso ma su ruÆ™e ni na har abada,”Ayaan ne yayi maganar,yayin da yake share hawayenshi,
“Yaya rafayet,dan Allah nima idan sun kira ace masu ga wani Æ™arin ma,”khaleed ne yayi maganar idonshi arufe Kamar maijin bacci,
“Wlh tun ranar da aka É—auke mana junaid,ban Æ™ara yin wanka ba,na Æ™untata rayuwata ne saboda Nima in É—anÉ—ani irin raÉ—aÉ—in da junaid ke ji a hannun waÉ—ancan Azzaluman mutanan”yana kai Æ™arshen maganar ya sanya tafin hannunshi tare da rufe fuskarshi yana kuka,abun ya ta6a masu zuciyarsu sosai,

Juyawa azmee tayi da sauri ta koma kitchen saboda kukan daya ciyota,

Cike da takaici Jahan yace”wai sun É—auke junaid saboda kuÉ—i.

 

“Is Enough!”tsit su kayi basu Æ™ara cewa uffan ba,
“Kafin nan da 3 minutes inaso inga kowa asaman dining chairs yana cin abinci”
Miƙewa suka yi ba don sun so ba suka nufi dining area,kowa yaja kujera ya zauna,wuri ya samu shima ya zauna,tare da ƙwalawa Azmee kira,

Fitowa tayi daga cikin kitchen ɗin fuskarta duk alamun hawaye,Serving ɗinsu ta shiga yi,daƙyar suke Cusa abincin abakinsu,
“Kunsan Allah!kaf sai kun cinye abincin nan,its better ku saki jikinku,”

Loma suka soma yi,Suna ci hawaye na zuba,kowa da abunda yake ayyanawa aransa,
“Babban yaya,kaifa?ba zaka ci ba?” Fawan ne yayi maganar,
Ɗaga mashi kai kawai yayi batare da yace ƙala ba,

Takun takalmi suka jiyo kamar ana tunkarosu,ɗagowa sukayi da idanuwansu suna kallon mai shigowar,Mommy ce jikinta sanye da Sleeping dress,ƙarasowa tayi ta samu wuri gefen Sgr ta zauna,
Hada baki su kayi wurin gaisar da ita Mommy barka da dare,
“Yawwa Sons,”ataÆ™aice ta amsa masu tare da kallon Fuskar Sgr dake a gefenta,
“My son,har Yanzu ba zaka daina sa damuwa aranka ba?ina fa sane da irin yarda kake rayuwa acikin gidan nan yanzu,Ba abinci ba bacci taya zaka samu natsuwar yin investigation akan Kidnappers É—in da Suka É—auke mun Romeo É—ina”idanuwanta cike tab da hawaye ta karasa maganar,
Calmly ya furta”Mommy,don’t worry about that,Addu’arki kawai nake buÆ™ata,”
“Kullum haka kake ce mun,why should i not worry?addu’a dama inayi maka,Ni so nake inga kana cin abinci kuma kana bacci”,

Bai amsa mata ba sai ma fawan da yayi ma magana”Fawan,Call Jahad for me,”miÆ™ewa fawan yayi jiki ba Æ™wari ya nufi bedroom É—insu Sehrish,
mayar da hankalinshi yayi kan Mommy
“She needs ur caring,tana cikin wani hali na buÆ™atar uwa atare da ita,Fawan zai kira maki ita,pls ki bata kyakkyawar kulawa,”yana kai Æ™arshen maganar ya miÆ™e da sauri yabar dining É—in,sam baison anayi mashi magana akan halin da yake ciki,
Girgiza kai kawai tayi,ita kanta jurewa kawai takeyi,

A bakin ƙopar ɗakinsu Fawan ya tsaya tare da sanya hannu yana kwankwasawa,
“Wanene,”muryar hosana ce yaji ta amsa mashi,
“Ya fawan ne,jahad ake kira,”
bude mashi ƙopar Hosana tayi tare da ɗan leƙo da kanta tana kallonshi,
“where is she”?
Nuna mashi cikin É—akin tayi da hannunta,Jahad ya hango kwance saman Darduma,
“Kamar bacci take yi ko”?
Jinjina mashi kai tayi”Eh,”
“Ta ci abinci”
“A’a,bata ci komai ba,”
.”Okey taso mun ita,”
Juyawa tayi ta koma cikin ɗakin zuƙunnawa tayi agaban jahad tare da sanya hannu tana bubbuga bayanta
“Jahad!jahad!”mutsu mutsu ta fara yi kafin ta yunkura ta tashi zaune,ta rame sosai tun daga kan fuskarta zaka lura da hakan,idanuwanta sun Æ™anÆ™ance saboda kukan da take sha,
“Hosana bana ce kada ki tashe ni ba,”
“Yaya fawan ne ke kiranki ae,”ta Æ™arasa maganar tare da miÆ™ewa ta koma saman gadonsu,
jiki ba ƙwari ta miƙe ta nufi ƙopar ɗakin,Fawan na ganinta ya ɗan saki fuskarshi,
“Ya fawan,”ta ambaci sunanshi,
“Babban yaya ne yace in kira mashi ke,”
Hannunta ya ruƙo ya jata suka nufi dining area,
Lokacin da suka Æ™arasa dining area É—in,kiranta Alex tayi”jahad,”Amsa mata tayi”na’am mommy,”da hannu Alex tayi mata nuni da tazo kusa da ita ta zauna,zagayawa tayi 6angaren da Alexandra take,taja kujera ta zauna,tana sauke ajiyar zuciya,
“Ya jikin naki,”? jahad tace”Alhamdulillah da sauÆ™i,”
“Good haka nake son ji,”
Da kanta tayi serving É—in jahad,ta shiga bata abincin abaki,dole Jahad ta saki ciki taci Abinci sosai,

*Boss Bature*

Ajiyar zuciya ta soma saukewa tare da Ambaton”ALHAMDULILLAH”mayar da idanuwanta tayi kan Sehrish dake sume a Æ™asa,da Sauri ta Æ™arasa wurinta zama tayi daga gefenta sannan ta sanya hannunta tare da janyo Sehrish ta É—aurata asaman cinyoyinta,lumshe idanuwanta tayi tare da buÉ—e su akan fuskar Sehrish,Slowly ta É—aura tafin hannunta asaman fuskar Sehrish tana shafata,kafin ta yarfar da Sumar kanta gefe guda,tayi hakan ne don taga rubutun dake a bayan wuyanta,Wanda tun suna yara Maman Sadeeq ta bata shawarar tayi masu shaida,Sehrish ta sanya mata SB ma’anarshi Sehrish buzuwa,Hosana ma akwai nata rubutun wuyan HB haka ma jahad,kowaccensu tana da shi abayan wuyanta,
“Ya Allah na gode maka,daka dawo dani cikin hayyacina,Adai dai lokacin da Æ´ata ke buÆ™atar taimako na,”tana magana hawaye ne shararowa akan fuskarta,waige waige ta soma yi tana kallon É—akin da suke ciki,Allah sarki lokaci guda ta fashe da kuka Saboda ta gane É—akinta ne na gidansu Abusufyan,Bazata ta6a mantawa da irin rayuwar farin cikin da tayi ba acikin gidan,Tunawa da mahaifinta Baba buzu mai gadi yasa ta Æ™ara sautin kukan nata,
“Zainab!Zainabu abu,”haka yake Æ™wala mata kira,idan yana nemanta,tayi matukar danasanin bijire mashi da tayi a lokacin da yake raye duk da ta auri za6inshi,bakowa tafi jin kunyar haÉ—uwa dashi ba,irin Abusufyan batasan da wani ido zata kalleshi ba,Ga kuma Hajiya Ameena,mutanen da suka yi mata halacci ta butulce masu,

Ruwan hawayen abu ne suka wanke mata fuskarta,wanda hakan yayi silar farfaɗowarta daga suman da tayi,Yunƙurin amai ta fara yi daga kwancen da take,da sauri abu ta ɗago da ita,nan take aman ya kwararo daga bakinta,tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito waje,hannu abu tasa tana ɗan bubbuga mata bayanta,Sosai ta dinga sharara aman anan ƙasa,ta galabaita sosai ga zazza6in da ya yi mata mugun kamu,
Miƙewa abu tayi da sauri ta fito daga dakin ta shigo palour,fridge ta hango da sauri ta nufe shi,buɗewa tayi tare da zura hannu ta ɗaukko bottle water jiki na rawa ta koma cikin ɗakin,A gaban sehrish ta zuƙunna a lokacin ta kammala kwarara Aman,cire murfin robar tayi tare da tarba tafin hannunta ta debo ruwan tana zuba mata shi abakinta tana kuskurewa,bayan ta gama kuskure bakin Abu ta kafa mata robar ruwan abakinta,Sosai ta shiga kwankwadar ruwan tana sha,sai da ta ƙoshi sannan ta janye bakinta,Har lokacin Sehrish bata dawo hayyacinta ba,jikinta duk ya saki babu ƙwari,
Ajiye robar ruwan abu tayi gefe tana kallon fuskarta,
Gam ta runtse idanuwanta,tana faman ciccije la66anta,
“RISHI”ta furta sunanta,
A hankali Sehrish ta É—an ware idanuwanta akan fuskar abu,wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta,ganin Oummansu agabanta,kuma da alama tadawo cikin Hayyacinta ne,
“Oumma,”ta ambaci sunanta tare da fashewa da wani sabon kuka,
Ita ma abun fashewa tayi da kuka,Cikin Shesshekar kuka take cewa”Laifina ne!komai ya faru arayuwarku ni ce sila,Ni naja maku….”
“Oumma ba laifin ki bane,ki daina É—aurawa kanki laifi,Allah ya rigada ya Æ™addara faruwar hakan”
“Rishi bakisan irin raÉ—aÉ—in da nake ji acikin zuciyata ba,bansan tsawon lokacin dana É—auka bana acikin hayyacina ba,bansan ya rayuwarku ta Æ™are ba,Nasan dole kunsha Wahala”
Sosai suke yin kukan babu mai lallashin wani acikinsu,
Sai da suka yi mai isarsu,Sannan suka tsagaita da yin kukan,
“Ina Hosana take?ina Jahad?duk suna ina?meyasa kike zaune ke kadai acikin gidan nan?Babu kowa atare dake?
É—agowa Sehrish tayi daga kwancen da take saman Æ™irjinta,cikin sanyin murya tace”Hosana da Jahad suna a Abuja wurin danginsu Daddy”
Cike da Mamaki abu ta maimaita sunan Daddy,
Sehrish tace”Eh,mahaifinmu nake nufi,Daddy Abusufyan atare muka zo kano,Tun da ya fita da marece bai dawo ba,kuma akwai security guards dake tsaron gidan,Amma bansan ya akai Ya sayyadi ya shigo ciki ba,”
Tunda Sehrish ta ambaci sunan Abusufyan jikin abu ya kara yin sanyi lakwas,shiru tayi na wani lokaci kafin tace”Kina nufin Abusufyan yana atare daku”?
É—aga mata kai Sehrish tayi”Eh,”
Abun yayi matukar É—aure mata kai,cike da mamaki tace”Taya akai kuka san cewa shi ne mahaifinku?Kuma ya akai kuka haÉ—u dashi”?har ya kai ku wurin danginshi”?daÆ™yar take magana saboda Ciwon kan da take ji yana É—an takura mata,
“Oumma,Labari ne mai dogon zango….,”kasa Æ™arasa maganar tayi sakamakon tashin Zuciyar da take ji,
“Sannu kinji,idan muka samu natsuwa sai ki sanar dani”
ta ƙarasa maganar tare da ruƙo hannayen Sehrish Cikin nata,suka mike tsaye suna fuskantar junansu,haɗa ido sukayi lokaci guda suka sakarwa juna murmushi,
“Kin girma sosai,komai naki ya canza mun,”duÆ™ar da kai kasa sehrish tayi tana dariya,
“Allah sarki hosana,Ashe da rabon zata rayu”?
“Sai ma kin ganta Oumma,Zaki sha Mamaki Allah,saboda hosana duk tafi mu girman jiki,”
wani irin farin ciki ne ya lullu6eta mara misaltuwa,

Sun jima suna tattaunawa atsakaninsu,kafin daga bisani Sehrish ta shiga toilet don tayi wanka,tunda ta rufo ƙopar toilet ɗin,ta sulale ƙasa jikin ƙofar tana kuka ƙasa ƙasa,Abunda ya sayyadi yayi mata ya tsaya mata aranta,yadda ya dinga goga mata Abunshi ajikinta,Da kuma harshenshi da ya sanya yana lasar mata bayanta Ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,runtse idanuwanta tayi sosai,wani irin ɗaci ta dinga ji acikin zuciyarta,lokaci guda ta fara jin ƙyanƙyamin jikinta,hada ƙaiƙayi miƙewa tayi ta soma tu6e kayan baccin dake ajikinta,

Lokacin da ta kammala wankan ta fito jikinta É—aure da towel,bata samu kowa a É—akin ba,Amma taga an gyara shi,komai ya koma yadda yake,hatta aman da tayi an kwashe shi da tarkacen Ya sayyadi,tasan cewa aikin Oummansu ne,

Jiki ba ƙwari ta wuce saman gado ta haye,tare jan bargo ta lullu6e jikinta,bakowa take jiran dawowarshi ba,fa ce Daddynsu,Tayi mamakin jimawarshi awaje,har wuraren 12,Allah yasa dai yana lafiya,

Kitchen ta shiga ta ɗauko Ashana,da sauri ta fito ta dawo harabar gidan,inda ta tattara Tsummokaran Ya sayyadi da ya bar masu,ba tare da taji komae ba ta Ƙyasta ashanar ta jefa ta asaman kayan nan take wuta ta soma ci ajikinsu,har sai da ta cinyesu abu na tsaye tana kallonsu,

Ajiyar Zuciya ta sauke tare da bin gidan da kallo,mutane ta hango a bakin gate ɗin gidan Sanye da kakin Sojoji,kowannansu a yashe ƙasa sai bacci sukeyi,Abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,ranta ne ya bata cewar Securities ne,Da alama Ya sayyadi ne yasa su yin baccin Dole,don ya samu hanyar shigowa cikin gidan,

Girgiza kai kawai tayi tare da komawa cikin falon,Bedroom ɗin ta shiga,tsayawa tayi abakin ƙopar ɗakin tana kallon Sehrish dake ƙumshe cikin bargo,jikinta sae kerma yake yi,
Idasa shiga cikin É—akin tayi har zuwa gefen gadon ta zauna,tare da Ambaton Sunanta”Sehrish,”
Muryata na kerma tace”Na’am Oumma,”
“Taya zan iya samun Daddynku?inaso nayi magana dashi,”
“Ina da waya,nabarta a É—aya daga cikin É—akunan dake a upstairs,”
Da sauri abu ta mike ta fuce daga ɗakin,Upstairs ta wuce,tana neman ɗakin da sehrish ta faɗa mata,Ɗaki ɗaya ta samu a buɗe,tun kafin ta shiga tajiyo ringing ɗin wayar tura ƙopar tayi ta shiga cikinsa,A saman gado ta samu wayar,hannu takai ta ɗauki wayar tare da duba screen ɗin
“My Boss Man,”shi ne sunan daya bayyana akan Screen É—in wayar,picking call É—in abu tayi tare da kara wayar a kunnanta,batasan wanene ba kawai ranta ya bata cewar Abusufyan ne,tayi tunanin zai yi mata sallama sai taji shiru,
Batare da ta kawo komai aranta ba,ta soma magana,
“Assalamu Alaikum,Oummansu Sehrish ce ke magana,dan Allah kadawo gida akwai matsala,Sehrish tana cikin wani hali,yanzu haka bata jin daÉ—in jikinta,duk ta tsorata saboda abunda Ya sayyadi yayi mata,
Sgr dake kwance asaman gadonshi,baisan lokacin da ya mike daga zaune ba,a kiÉ—ime yace”What?meya faru da ita ne?Waye ya shigo”?
Abu bata wayi muryarshi ba,ita dai kawai koma wanene so take akawo masu É—auki ko dan saboda halin da Sehrish take ciki,
“Ya sayyadi ne ya shigo cikin gidan,bamu san taya akai ya shigo ba,Ya so ya cutar da rayuwarta…..”gaba daya abu ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar dashi a Æ™arshe tace”dan Allah idan ka tashi dawowa,Ka biya koda chemist ne asamo mata maganin Zazza6i,ga tashin zuciya da take ji,Tunkan takai Æ™arshen maganar,Yayi rejecting Call É—in,
Hankalinshi yayi mugun mugun tashi,har wani jiri ya soma gani acikin idanuwanshi,a zafafe ya tunkari ƙopar fita daga bedroom ɗinshi,sai ga Marshal ya faɗo cikin ɗakin har karo suka kusan yi,
“Bro whats happening?Where are going?”
Zuciya ce kawai ke fusgarshi,
“Omar,Airport zani je,”
Damko damtsen hannunshi Omar yayi ganin yana ƙokarin wuce shi ya tafi,
“Haba Rafayet!Airport kuma at this time?Me zakayi acan ”
“Pls omar,leave alone,ka bani hanya in wuce,Zuciyana tafarfasa take yi,idan har ban kama wancan fasiÆ™in mutumin ba,hankalina bazai kwanta ba,”
A ruÉ—e Marshal yace”Wai wa kake magana akai?ko ka gano waÉ—anda suka kashe junaid ne”?
Girgiza kai yayi’A’a,ina magana akan wancan Bastard É—in dake a Kano,Yau ya taka har gidan da Abusufyan yake..wai har…’kasa Æ™arasa maganar yayi saboda raÉ—aÉ—in da yake ji acikin zuciyarshi,
Hankalin Omar ba karamin tashi yayi ba,tun kafin ma ya ƙarasa jin abunda ya faru ɗin,
“Rafayet,pls Calm down ur mind,Kayi mun bayani yadda zan fahimta,’
Mika mashi wayarshi yayi batare daya furta komai ba,
Kar6ar wayar Omar yayi, kaitsaye ya shiga call log nashi,
Kiran da Sgr yayi ma sehrish ya fara gani,”Calling É—in layin yayi,
A lokacin abu na acikin falo tana safa da marwa,jiran dawowar Abusufyan kawai takeyi,

Kiran na shiga wayar,da sauri tayi picking tare da zabga sallama,
“Am..sehrish,pls inason sanin meke faruwa anan ne,”?
Abu tace”ba Sehrish bace,Oummansu ce,”
Abun ya ɗan ɗaure mashi kai,jin tace Oummansu ce,a iya saninshi tana da ta6in Hankali,gaisar da ita ya fara yi cike da girmamawa tare da gabatar mata da kanshi a matsayin yayansu sehrish,abu ba ƙaramin daɗi taji ba,
Bata 6oye mashi komai ba,kaf ta kwashe abunda tasan ya faru ta sanar dashi,”
Jinjina kai Omar yayi,jikinshi har tsuma yake yi,daÆ™yar ya iya furta”Zan yi magana da Abusufyan É—in,Ki kula da Sehrish É—in kafin ya dawo gidan,”
amsa mashi tayi da toh,daga bisani su kayi sallama,
Zuba ma juna ido sukayi shi da Sgr,
“Bansan wani irin dabban mutun bane wannan,wai ma ina security É—in dake tsaron gidan ne?aikin me sukeyi ne da har suka barshi Ya samu damar shiga gidan?shi kuma Uncle bansan ya akayi har yayi dare haka ba awaje,”Omar ne yayi maganar ranshi a matukar 6ace,
“Last time ma,Ya ta6a yin irin hakan,Ya tafi ya barta ita kaÉ—ai acikin gidan,”Acewar Sgr,
Omar yace”ba don Oummansu na a kusa ba,da bansan mezai biyo baya ba,Amma naji daÉ—in jarumtar da tayi wurin ceton sehrish É—in,”
Kar6ar wayar Sgr yayi daga hannunshi,Layin Abusufyan ya kira,
Almost 3 times tana ringing ba’a É—agawa,
Sauke wayar yayi daga kan kunnanshi,
Omar yace “Allah yasa dai lafiya,hankalina fa duk ya tashi,abunda za’ayi yanzu Kawai gobe da asussuba su dawo gida kawai,nasan kafin lokacin may be Abusufyan É—in ya dawo,Zan cigaba da trying layinsa,”
Dakyar ya samu ya lalla6a Sgr ya fasa zuwa airport É—in,Amma fa abun ya tsaya Mashi aranshi,gefen gadonshi ya zauna,Omar ma ya zauna akusa dashi,
“Omar,kodai mun aikata wani zunubi ne da yasa waÉ—annan abubuwan ke faruwa damu ne?daga wannan sai wannan!
“Rafayet,ba laifin mu bane Laifin wasu ne aka É—aura mana,ni tunda nake arayuwata ban ta6a fuskantar tashin hankali irin na waÉ—annan ranakun ba,kuma ban ta6a tunanin cewa rana irin Wannan zata zo mana ba,”
“What’s the solution now?time fa yana Æ™ure mana,Daddy ma harya fara karaya da dawowar junaid,É—azu da safe da yazo bedroom É—ina,Tsare ni yayi akan in faÉ—a mashi gaskiya,Junaid zai dawo yaci gaba da sa rai,ko kuwa bazai dawo bane,A lokacin saina kasa buÉ—e baki inyi mashi magana,”Sgr ne yayi maganar
Omar yace”Wlh nayi regretting É—in 6oye mashi ainihin abunda ya faru,Duk da munyi hakan ne don mu ceto rayuwarshi,Amma kuma fa mun tabka kuskure babba,Don kuwa duk ranar daya gano cewa Junaid ya mutu,wlh ya gama yarda damu har abada,zuciyarshi zata karaya ne,Inajin tsoron wannan ranar,Rafayet,kodai mu sanar dashi gaskiyar lamarin ne”?
Shiru Sgr ya É—an yi yana nazarin maganar tashi,girgiza kanshi ya É—an yi tare da cewa”That’s not the solution Omar,koda ace zai sani,yakasance time É—in da muka kama waÉ—anda su kayi silar mutuwarshi,Mu gurfanar dasu agabanshi,before mu yanke masu hukunci akan idonshi,ina ganin kamar zaifi jin sauki acikin zuciyarshi,”
Sun jima suna tattaunawa a tsakaninsu kafin daga bisani,Kowannansu ya É—auro alwala,Suka daidai ta sahu tare da kabbara Sallah,

Ataƙaice

Abusufyan bai tashi dawowa cikin gidan nan ba sai wuraren sallar asuba,Bawan Allah ashe Bayan ya baro gidan su Maman Sadeeq akan hanyar dawowarshi gida aka turo mashi da saÆ™o cikin wayarshi cewa za’a kashe Ƴarshi da ya bari acikin gidan,Hankalin shi yayi mugun tashi,Ya kure gudun motarshi,idonshi ya rufe saboda tashin hankalin dayake ciki,Baisan sa’adda ya buge wani Tsoho ba dake Æ™oÆ™arin tsallaka titi,Tsohon yaji mummunan rauni dole ya tsaya don yaji bazai iya daukar alhakin guduwa yabarshi cikin mawuyacin halin da zai iya rasa ransa,mutane suka kama mashi tsohon yasa shi a motarshi suka wuce dashi asibiti,babu yadda ya iya,kamar ya fasa ihu haka yaji saboda tsabar baÆ™in ciki,duk da wani bangare na zuciyarshi na tunasar dashi akwae security guards a gidan,Bashi ya baro asibitin ba sai wuraren Sallar Asuba Ya dawo cikin gidan,Yayi mamakin ganin komai lafiya,Lokacin daya shiga É—akin abu kwance ya samesu rungume Saman gadon ita da Sehrish suna ta sharar baccinsu,Hankalinshi ya kwanta sosai ganin babu abunda ya faru dasu,

Falo ya koma ya zauna saman sofa,jikinshi duk amace,Ringing É—in wayarshi dayaji yasa shi zura hannu cikin aljihu ya É—auko wayar tare da duba sunan mai kiran nashi,Marshal Omar ne,
Picking call É—in yayi tare da kara wayar a kunnanshi,
“Omar me kake yi har yanzu bakayi bacci ba”?
On the other hand Omar yace”Uncle,Ina ka shiga ne anata nemanka,”?
Nan Abusufyan yake sanar dashi abunda ya faru dashi akan hanyar dawowarshi gidan,
“Yanzu na dawo gidanma,Na same su cikin koshin lafiya suna ta bacci,”
A nan Omar ya kwashe duk abunda Abu ta sanar dasu ya faɗa ma Abusufyan,A zabure ya miƙe tsaye jikinshi na rawa,
“Pls Uncle,ka kwantar da hankalin ka,Tunda ba abunda ya faru dasu,Abunda ya kamata kawai ku dawo gida yau yau É—in nan zamanku anan baida amfani,dama saboda ciwon Mahaifiyarsu ne Kuma ta samu lafiya,Yakamata ku dawo gida,Hankalinmu sai ya fi kwanciya,”
..jinjina kai kawai Abusufyan keyi sam ya kasa buÉ—e baki yayi magana,Allah kaÉ—ai yasan raÉ—aÉ—in da yake ji acikin Zuciyarshi,dakyar ya iya buÉ—e baki yace”Shikenan Omar,yanzun nan zamu shirya,’
“Allah ya dawo daku Lafiya,”
“Ameen”daga haka su kayi Sallama,
Komawa Bedroom É—insu yayi wuraren karfe 6 na asuba,da alama ko sallar asuba basu yi ba,sai sharar bacci sukeyi,
Zagayawa yayi gefen da Sehrish take a kwance ya zauna tare da zuba mata ido yana kallonta,Yayin da hawaye ke sharara akan fuskarshi,tsananin tausayinta ne ya kamashi,baiji daÉ—in abunda ya faru ba,ta wani 6angaren kuma yaji sanyi aranshi da Allah ya tsare mashi ita,ga kuma Mahaifiyarsu da ta dawo cikin hayyacinta ta silar abunda ya faru,
ShessheÆ™ar kukan da Abusufyan keyi ne ya farkar da Sehrish,buÉ—e idanuwanta tayi masu É—auke da bacci,Suna haÉ—a ido dashi tayi hanzarin mikewa daga zaune tana ambaton sunanshi”Daddy!yaushe ka dawo?meya faru kake kuka,”
“Daughter,Am sorry!am really sorry,duk laifina ne dana tafi nabarki ke kaÉ—ai acikin gidan,”
“Daddy,bangane akan me kake magana ba?nifa babu abunda ya faru dani,”tayi hakan ne don ta 6oye mashi gudun karya sanya damuwa aranshi,batasan cewa ya riga daya ji ba,
“Omar ya sanar dani duk abunda ya faru dangane da zuwan sayyadi cikin gidan nan,”
Mamaki ta shiga yi taya akai Ya Omar yasan abunda ya faru dasu?can kuma ta tuna da lokacin da Oummansu ta nemi yin magana da Abusufyan may be a wurinta yaji komai,
“Dan Allah Daddy,kada kasa damuwa aran ka tunda ba abunda ya faru dani lafiyata kalau,Sai ma wani abun farin ciki da ya faru,Oummanmu ta dawo cikin hayyacinta,Sanadin zuwan ya sayyadi,Kuma ta lalata mashi idanuwanshi,karkaso kaga yarda ya dinga kururuwa yana ihu,” Tayi maganar tana kwatanta mashi irin yarda Ya sayyadi yayi ihun,
Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba,dama tayi hakan ne don ta sanyaya mashi ranshi,

 

Yar Aikin Karuwai Book 1 Hausa Novel

 

É—aure fuskarta ta É—an yi ashagwa6e tace”Daddy banga kana farin ciki da abunda na sanar dakai ba”?
DaÆ™yar ya Æ™aÆ™aro murmushi akan fuskarshi yace”Ina farin ciki mana,Naji daÉ—i sosai,kawai dai nadamu ne akan Halin da kika tsinci kanki a lokacin da bana nan,”
É—aure fuskarta tayi”Why Daddy,bana ce ka kwantar da hankalin ka ba?komai ya wuce,Yanzu lokacin farin ciki ne,Ga ka, Ga Ni,ga Oummanmu kuma,Bari na tashe ta daga bacci kuyi magana,”ta Æ™arasa maganar tare da sanya hannu tana É—an bubbuga kafadar Oummansu,
Murmushi kawai Abusufyan ke saki yana kallonta,
“Oumma!oumma!ki tashi ga Daddynmu nan ya dawo,”
Kasa tashi abu tayi saboda kunyar Abusufyan da take ji,Ashe tun shigowarshi dakin ta farka,tana jinsu suna magana amma tayi likimo,

“Nasan cewa idonki biyu abu,bakison gani na ko”?Abusufyan ne yayi maganar ayayin da yake leÆ™en fuskarta,pillow ta sanya tare da rufe fuskarta dashi,
Murmushi suka saki atare shi da Sehrish,
“Inason magana dake,ki tashi daga zaune,”cike da jin kunyarshi ta cire pillow É—in tare da tashi daga zaune suna fuskantar juna,Ta kasa É—agowa su haÉ—a ido da Abusufyan,kunyarshi ta rufe ta,kamar tayi rami ta binne kanta,

“ZAINAB”ya ambaci sunanta da wata irin kasalalliyar murya,
daƙyar ta iya motsa lips ɗinta wurin amsa mashi,
“Na’am,”
Murmushi ya saki tare da É—aga hannunshi sama yana furta”Alhamdulillah!Alhamdulillah,Almost 3 times yana ambaton hakan,Cike da tsantsar farin ciki,
Sai faman sauke ajiyar Zuciya take yi,matsawa yayi kusa da ita tare da sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta yana ƙare mata kallo,
Siraran hawaye ne suka soma Zarya akan fuskarta masu É—umin gaske,
“Hawayen menene wannan”?
Cikin ShessheÆ™ar kuka tace”Kayi haÆ™uri,ka yafe mun,Na gane kuskuren dana yi,Naji jiki Abusufyan,nayi dana sanin butulce maka da nayi,Haƙƙinka ne yake ta bibiyar rayuwata,Ni ce silar duk wani abu daya faru a rayuwarmu nida Æ´a’Æ´ana….”ta Æ™arasa maganar tare da fashewa da kuka,Hannu tasa ta zame hannayenshi daga saman fuskarta,kafin ta Sauko daga saman gadon ta zuÆ™unna saman guiwowinta agabanshi,tana ci gaba da yin kukan….
“Tun da nake arayuwata,ban ta6a ganin mutun mai kyakkyawar Zuciya irin taka ba,duk irin girman laifin dana aikata maka,hakan baisa ka guje ni ba,Sai ma bibiyar rayuwata daka ci gaba dayi duk don kaga Ka taimake ni,Amma na kasa gane hakan,saboda tsabar baÆ™in kishin da nake dashi na yanke maka hukunci batare dana tsananta bincike ba……”
RuÆ™o hannunta Abusufyan yayi tare da É—ago da fuskarta yace”pls bana son muna tuna abunda ya wuce,Ni komai ya wuce a wurina Abu,tabbas naji zafin abunda kika yi mun Amma wlh banta6a ruÆ™e ki araina ba,kullum burina inga na taimaki rayuwarki saboda baki da kowa abu,Allah kaÉ—ai gare ki,Sai kuma Ni dana haÉ—a zuri’a dake,Ba zanso rayuwarki ta wulaÆ™anta ba,ko ba don haka ba Ke amana ce agare Ni,”

Zuba masu ido Sehrish tayi tana kallonsu fuskarta ɗauke da Murmushi,tsabar farin ciki kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha,
“Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin bayyana maka irin farin cikin da nake ciki ba,Abusufyan Allah kadai ne zai iya biyanka,”,addu’oi ta shiga yi mashi yana amsa mata da ameen,Kafin daga bisani Ya nuna mata gefenshi ta miÆ™e ta zauna,
“nasan kinyi kewar Æ´a’Æ´anki sosai,In sha Allah Yau É—innan zamu wuce Abuja,Zaki ga Hosana da Jahad,da kuma sauran Family É—inmu,”

Fira sosai suka shiga yi,Anan ta samu labarin irin wuyar dasu sehrish suka sha bayan 6acewarta,da kuma yadda akai suka haÉ—u da dangin mahaifinsu da shi kanshi Abusufyan din har kawo yanzu da suke bata labarin,Abu tasha kuka sosai tsananin tausayinsu ne yakamata,ta wani 6angaren kuma tayi farin ciki sosai Da Allah ya nuna mata wannan ranar da ranta kuma da Lafiyarta,

Batare da 6ata lokaci ba Suka kammala shirinsu na komawa Abuja,A jere Motocinsu suka fita daga cikin gidan,Motar Abusufyan na atsakiyan motocin security É—in gidan,Kaitsaye hotoro suka wuce domin yin sallama dasu Maman Sadeeq,
Sunsha kuka sosai,musamman Maman sadeeq da Abu,rungume juna suka yi kamar karsu rabu,babu wanda bai zubda Æ™walla ba acikinsu,kafin su tafi sai da Abusufyan ya damÆ™a ma Malam Nura key din gidansu dake a nasarawa G.r.a,Ya mallaka masu shi duk da haka sai da ya Æ™ara masu da zunzurutun kuÉ—i har miliyan 10,yace ya dauki miliyan bakwai yaba Baban Umari cikon miliyan ukkun,don bai manta da gudunmawar da akace ya bada ba wurin neman abu,anan take ya rubuta ma Malam Nura cheque,Duk da haka bai Æ™yalesu ba,Bayan haka kuma yayi masu albishir É—in cewa tare dasu Za’ayi aikin hajjin bana,Wayyo Allah saboda tsabar farin ciki,kasa bude baki su kayi don suyi mashi godiya,Kuka kawai sukeyi,abun da basu ta6a tsammanin zasu samu a rayuwarsu ba,Yau gashi silar taimakon da sukayi Allah ya É—aukaka rayuwarsu,
Sehrish kuwa Dama tayi alÆ™awarin zata taimaka ma Sadeeq ya gyara keken shi,maimakon kuÉ—in gyaran keken sai Gashi ya samu kyautar danÆ™areriyar Motar Abusufyan gaba daya ya mallaka mashi ita,kusan zaucewa Sadeeq yayi saboda tsabar farin ciki,sun jima a wurinsu suna bankwana,kafin daga bisani Sukayi masu Sallama,Anyi rabuwar mutunci sai kuma in Allah ya haÉ—asu wurin shagalin bikin Ƴa’Æ´an abu,

ÆŠaya daga cikin motocin security É—insu suka shiga Gidan baya Abu da Sehrish,Abusufyan yana agaban motar,A jere Motocin suka kama hanyar fita daga unguwar,

Su Maman Sadeeq na tsaye a kopar gida ita da Mlm nura,tare da sadeeq sai bye bye suke yi masu da hannu,yayin da hawaye ke zuba a fuskar kowannansu,

Sehrish sai lekensu takeyi ta glass É—in motar dake a zuge,har sai da suka 6ace ma ganinta tukunna ta hakuri da leken,Rayuwa kenan in akayi hakuri Komai mai wuce ne,

Hannu abu tasa tare da janyo Sehrish ta rungumota ajikinta,a lokacin har motocin sun haura saman titi,Sun miƙi hanyar barin garin da matsakaicin gudu,
Da zarar ta ɗago da idonta ta kalli madubin motar,Fuskar Abusufyan take gani yana sakar mata murmushi,Sunnar da kanta ƙasa tayi tana ƴar dariya,
Sehrish batasan wainar da suke toyawa ba,domin kuwa ta lumshe idanuwanta da alama bacci ya fara É—aukarta,
Sake ɗagowa abu tayi tare da kallon Mirror ɗin,suka ƙara haɗa ido dashi,
Kashe mata ido É—aya Abusufyan yayi,batasan lokacin da ta fashe da dariya ba cike da tsantsar farin ciki,
Shima dariyar yayi,kusan minti 30 bata ƙara dagowa sun haɗa ido ba,saboda baccin da yayi awon gaba da ita,
Wasa wasa shima bacci ya É—auke shi,dama duk basu samu isasshen Bacci ba a adaren Jiya,

Wuraren ƙarfe 2 na rana suka ƙaraso Abuja,Slowly motocinsu suka shararo izuwa cikin gidan,tun da Hosana tajiyo sautin shigowar motoci da gudun gaske ta fito daga cikin falon don taga su wanene,

Bayan sunyi parking É—in motocin,Abusufyan ya fito daga cikin motar,hosana na ganinshi ta Æ™wala mashi kira”Daddy”!wani irin farin ciki ne ya lullu6eta,da gudun gaske ta nufe shi tare da faÉ—awa jikinshi ta Æ™ankameshi sosai,tana dariya,
“Hosana,”ya Ambaci sunanta tare da É—ago da ita daga jikinshi yana kallonta,fuskarshi É—auke da murmushi,
ÆŠaure fuskarta ta É—an yi ashagwa6e tace”Munyi fushi daddy,Sai yau zaku dawo”?
Yana ƙokarin buɗe baki ya bata amsa,karaf idanuwanshi suka sauka akan Jahad wadda ta fito daga cikin falon tana tunkaro su,
Gabanshi ne ya faɗi rass!Ganin yadda kamanninta suka sauya tamkar ba ita ba,ta rame sosai ,tafiyar kanta ma daƙyar take yinta,
Ƙarasawa tayi gabansu ta tsaya batare da tace komai ba,idanuwanta na kallon ƙasa,
“Jahad!kinyi rashin lafiya ne”?É—aga mashi kai tayi alamar eh,
“Zazza6i nayi sosae amma naji sauÆ™i yanzu,”
Hannu yasa tare da janyota ya rungumeta ajikinshi,Kasa jurewa tayi aikuwa ta fashe mashi da kuka sosai,
Hankalinshi ya ƙara tashi,
“Jahad kukan menene”?
Cikin shessheÆ™ar kuka tace”bakomai Daddy,nayi kewarka sosai,”
hannu yasa yana É—an bubbuga bayanta yace”Am Sorry Daughter,pls ki daina kuka kada kisa nima na fara zubar da hawayen nawa,”
Dakyar ta tsagaita da yin kuka ta É—ago da kanta daga jikinshi tace”Daddy,ina rishi take?ina kuma Oumman mu?Hosana ta sanar dani cewa an ganta,”
Murmushi ya saki tare da sanya hannunshi ya É—an kwankwasa glass É—in motar,
BuÉ—e murfin motar Abu tayi tare da fitowa daga cikin Motar,Zuba mata ido su kayi suna kallonta kamar yadda itama take kallonsu,
Atare suka haÉ—a baki wurin ambaton sunanta”Oumma!”
Murmushi ta ɗan sakar masu,tare da buɗe masu hannunwanta don su zo ta rungumesu,Matsawa suka yi tare da faɗawa saman jikinta,ta haɗasu duka ta rungume sosai,fashewa sukayi da matsanancin kuka kamar ransu zai fita,musamman jahad da take cikin wani hali na buƙatar kulawarsu,
Itama abun kukan takeyi sosai,babu mai lallashin wani acikinsu,Fitowa Sehrish tayi daga cikin motar ta other side ɗin,jikinta a sanyaye ta zagayo ta wurin da suke,bayansu jahad ta fada ta rungumesu,abu ta haɗa da ita duka ta ƙanƙame abunta,

Tuni hawaye sun wanke fuskar Abusufyan,Yau burinshi Ya cika na ganin ya haÉ—a kan family É—inshi,wannan rana ce da bazai ta6a mantawa ba arayuwarshi,,

Suna cikin wannan yanayin sai ga Abbansu junaid tare da Alexandra sun fito daga cikin gidan,tsayawa su kayi suna kallonsu fuskar kowannansu É—auke da murmushi,
“Bismilla,Ku Æ™araso daga ciki mana,”Abba ne yayi maganar tare da yi masu nuni da hannunshi,
Kallonsu Abu yayi tare da yi masu gyaran murya yace”Koke koken sun isa haka,mu shiga daga ciki mana,”
Raba jikinsu sukayi dana Oummansu,ta ruƙo hannun jahad da hosana acikin nata,Abusufyan kuma ya ruko hannun Sehrish wurinsu Abba dake atsaye,
tunkan su Æ™araso Abba yace” masha Allah,Yau family É—in Abusufyan ya haÉ—u wuri guda,Ga Uwar Ga uban Ga kuma Æ´a’Æ´ansu,”ya Æ™arasa maganar yana dariya,
Alex tace “U’r Highly welcome, Abusufyan’s Family,Am glad to see guys “ta yi maganar tare da Æ™arasawa ta rungumo Abu ajikinta,hakan ba Æ™aramin daÉ—i yayi masu ba,

Sun jima a waje suna gaisawa kafin daga bisani suka koma babban falon gidan,Kowa dake acikin gidan sai da ya hallara A falon,Abusufyan ya shiga gabatar ma abu kowa,Sun yi farin ciki sosai,duk da tashin hankalin da suke ciki hakan bai hanasu yin Murnar dawowar Uncle É—insu ba tare da Oummansu rishi,Abusufyan ya lura da yanayin fuskokinsu,abun ya É—aure mashi kai,mutanen gidan duk sun rame sunyi duhu,bashi kaÉ—ai ba hatta Sehrish ta ankara da canzawar da mutanen gidan su kayi,Sai faman wurga ido takeyi taga ko junaid zai fito amma shiru babu shi,Ranta ne ya bata cewar ko sun fita tare dasu Babban yaya ne tunda bata gansu ba acikin gidan,

Basu tashi sanin halin da Family ɗin suke ciki ba,Sai da suka huce gajiyarsu,tukunna Abba ya sanar da Abusufyan shima ɗin don ya matsa mashi ne akan son ganin junaid,Hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,jin anyi garkuwa dasu Junaid,baima son lokacin da ya rufe Abba da faɗa ba saboda ƙin sanar dashi da sukayi,Don me zasu 6oye mashi abunda ke faruwa acikin gidan,abun ya ƙona mashi rai,Har cikin ranshi baiji daɗin hakan ba,har ƙwalla saida ya zubar,

Yinin ranar Abu na tare da Æ´an ukunta a bedroom É—insu,Sun sha firar yaushe rabo,har bacci ya É—aukesu atare saman gadon,basu suka farka ba sai wuraren Sallar Magriba,

Bayan kowannansu yayo alwala Jahad ta shimfiÉ—a masu darduma suka jera atare da Oummansu,a tsanake sukayi sallar har suka kammala,basu tashi daga saman dardumar ba,É—aga hannayensu suka yi sama suka shiga karanto addu’o’a abakunansu suna masu kara mika godiyar su ga Allah(S.W.A),

Allah Allah Sehrish take yi su kammala Sallar taja jahad gefe saboda ta tambayeta ina junaid yake sannan kuma ta bata Labarin Artabun da suka yi tsakaninsu da ya sayyadi,ita ma jahad ɗin a ƙagare take dasu ke6e ita da Sehrish,Don ta bata labarin mutuwar junaid,kota samu ta rage raɗaɗin dake acikin zuciyarta,bazata iya 6oyema Sehrish ba,duk da An gargaɗeta akan karta fadama kowa,

Basu suka samu lokacin kebewa da junansu ba,Sai bayan sallar Isha’e,kowa ya hallara a dining area,Suna cin abincin darensu,

Su biyu suka rage acikin bedroom É—insu,Zaune daga gefen gadonsu,kowa yayi tsit,na wani lokaci kafin Sehrish tace”Jahad,tun É—azu nakeso na tambayeki game da canzawar dana ga mutanen gidan nan sunyi,kowa ya rame yayi duhu,musamman ke kamar kin yi ciwo,”
Cikin sanyin murya Jahad tace”Labari ne mara daÉ—in ji Sehrish,Zan faÉ—a maki amma ina gudun na jefa ki cikin tashin hankali,”
“Kada ki damu jahad,ki faÉ—amun koma menene,in sha Allah zan jure bazan tashi hankali na ba,”
“Shikenan zan faÉ—a maki Amma kafin nan inaso ki yi mun alÆ™awarin cewa bazaki faÉ—a ma kowa ba”
..Sehrish tace”I promised you jahad,babu wanda zaiji abunda muka tattauna dake,”
Shiru jahad ta É—an yi yayin da take yin wasa da yatsun hannunta,
“Ina sauraronki jahad,”ta faÉ—i hakan ne don a Æ™agare take da ta ji abunda jahad zata sanar da ita,
“Sehrish!munyi babban rashi,wanda ya raunata zukatanmu,”
..tunkan ta ƙarasa maganar sehrish taji gabanta ya faɗi rasss,
AruÉ—e tace”Jahad kada ki ce mun junaid ya mutu……!”
Hawaye ne suka fara saukowa daga cikin idanun Jahad,bata 6oye mata komai ba game da mutuwar Junaid,Abun mamaki sai taga Sehrish na Zabga murmushi kamar wata zautacciya,
Bata karaya ba,cigaba da magana tayi”Babu wanda yasan ainihin abunda ya faru,daga ni sai su ya Omar sai kuma Jami’an Æ´an sandan da suke je wurin da kuma Sojojin dasu ya Omar suka je dasu,”
Dakatawa tayi da yin maganar tare da kallon Sehrish,wadda ke ta sakin murmushi,
Fashewa da kuka Jahad tayi tare da cewa”Sehrish meyasa kike yin murmushi?na faÉ—a maki ne don in rage raÉ—aÉ—in da nake ji acikin zuciyata,wlh da kinsan halin da muka shiga ni dasu Ya Omar da baki yi mana dariya ba,”tana kai Æ™arshen maganar ta Æ™ara sautin kukan nata,
Sai lokacin Sehrish ta tsagaita da yin dariyar,Sannan ta soma magana”Haba Jahad,taya zaki ce mun Junaid ya mutu farat É—aya in yarda?bazan Æ™aryata ki ba,mutuwa na akan kowa babu wanda yafi Æ™arfinta,Amma ni dai ban yarda cewa junaid ya mutu ba,tunda banga gawarshi ba,”tuni hawaye sun cicciko acikin idanuwanta,
Cikin Shesshekar kuka jahad tace”Taya za’ae kiga gawarshi!nace maki ko Æ™ashi ba’a samu ba daga sassan jikinshi,Saboda ya ruga da ya Æ™one Æ™urmus ya zama toka,”
“Jahad ni ban yarda ba,Allah Junaid É—inmu bai mutu ba,ki daina wahalar da kanki wurin faÉ—a mun,”
Rai a6ace Jahad tace”Wlh dole ki yarda Sehrish!meyasa zakiyi mun haka!Maimakon ki tayani jimamin rashin shi amma shine kike Æ™ara jefa ni cikin damuwa,”
Girgiza kai sehrish ta shiga yi tana faÉ—in’wlh bazan yarda ba,”tashin hankaline yasa Sehrish ta burkice mata,
“Ko kin Æ™i ko kin so dole ki yarda Sehrish,Junaid has gone forever,”
Miƙewa Sehrish tayi jiki ba ƙwari ta nufi toilet,Shigewa ciki tayi tare da jan ƙopar ta rufe,
Zuƙunnawa tayi ajikin ƙopar,sai lokacin ta fashe da matsanancin kuka kamar ranta zai fita,
“Allah sarki Junaid,Allah ya jiÆ™anka,bazan ta6a mantawa da halarcin da kayi mun ba…

Back to top button