Mejo Najeeb Page 47 By Autar Alheri
“Yace mizanyiwa farin ciki dady? Farin cikin tatafi tabarni tun ina jinjiri banma san da akwaita aduniya ba zanyi? Ko na ta bayyana bayan na mallaki hankalin kaina nagama Sham wahalar rayuwa? Humm tanasona ne dazanyi farin cikin dawowarta? Idan tanasona miyasa zata tafi tabarni? Dagani har sweet life bamuda hurumin farin ciki a wannan gaɓar domin kuwa dukan mu wofantardamu sukayi tun bamusan kanmu ba nafahimci hakanne tunlocinda wannan matar tabada labarin yadda akayi sweet life tazo hannunta, to wanne farin ciki zamuyi Dady? Sundai zo mungansu kuma munsan da akwai su a yau ɗinnan domin ko labarinsu ba’ataɓa bamuba dagani har ita, Ni nataso ina kallon cewar Hajiya umma ce mahaifiyata, ita ta taso tana kallon wata daban amatsayin mahaifiyarta, kenan koda rasuwane sukayi baza’asanar munaba ko adda’a muyi musu Dady? sabida hakan bamuda abinda zamuyi ayanzu Dady kawai ku barmu muyi tafiyarm….beƙarasa sabida marinda Abba yaje yimashi Dady yariƙe hannushi, wani irin kallon bakada hankali yakebin najeeb dashi yayinda Ammi da Hajiya Hannah harmada mama bintu keta famar rusa kuka.Kafin kowa yayi magana isseta tazo dasauri tatsaya gaban najeeb tana kareshi tare da jiyowa tana fuskantar Abba ta haɗe hannayenta duka biyu🙏alamar roƙo cikin kuka take faɗar “dan girman Allah Abba kayi haƙuri karka dakeshi wlh gaskiya yafaɗa akan iyayena amma Ammina batada laifi shibesan hakan bane shiyasa yake faɗar hakan akanta, sekuma tayi sauri juyawa tana kallon mejo idonta na zubda hawaye tace “yah najeeb tareda riƙo duka hanunshi biyu.. ɗagowa yayi kawai yana kallonta batareda yace komaiba, ganin hakan yasa tacigaba cewa “yah najeeb Ammi tana sanka ba’ason ranta tatafi tabarka ba wlh Allah shine shaida kuma nice shaida kaida kanka dakasanta ayadda nasanta baza buɗe baki kayi mata wani zancenba please karka hukuntamin uwa abisa laifinda bata aikataba dan Allah….wani irin kallo yakebinta dashi tunda tasoma magana hakama iyayen nata da duka sauran mutanen dakenan. Kafin najeeb yayi magana nazeer yarigashi ta hanyar faɗar “a’ina kikasan gwaggo lattey? Kuma ayaya kika santa dahar zakiyi wannan maganar dama kinsan kinada alaƙa da itane ? Naga ai komu bamusantaba kuma kema bakisanmuba se ayau.. “wannan amsar nice nan zanbaka ita ba Aminiya ba domin duk abinda Aminiya tasani akan Ammi nasanshi, cewar halima cikin jin haushin tambayar da nazeer ɗin yayi. Juyawa kowa yayi ana kallonta domin mutanen perlor sunkoma kamar katon duk inda akayi magana acan suke juyawa sanida dukkansu acikin duhu suke. Itako halima cikin takaicin abinda zata faɗa tafara basu labarin Ammi tun daga haɗuwarta tafarko da isseta tafara temakonta har izuwa Kaita asibiti dasukayi harkawo lokacinda suka dawo da ita gida maahh tabata magani. Seda takai ƙarshe kana tace kunji yadda akayi isseta tasan Ammi bawai dan tasan tanada wata alaƙar da itaba kawai tausayine datake dashi dakuma zuciyar imani, kana tajuyaga mejo “kaikuwa kaji abinda yasa tace itace shaida Ammi ba’ason ranta tabarkaba Nima shaidace akan hakan, sabida duk wanda yabar jinjiri yaro agida tun daga Niger yafito yana yawo akan titi cikin hali narashin hankali kasan cewa ba’abanza ne yafitoba sabida hakan godiya yadace kayiwa uban giji daya bata lafiya harka sameta cikin hayyacinta bawai kazauna kana complain ba, taƙarasa zancen cikin jin haushin su domin halima irin isseta ce basuda rigima amma fa basuda tsoro domin ko kaɗan waƴannan gardawan samarin basu tsoratataba harta ƙarasa maganarta, wannan abin datayi kuwa bakayimin ƙara burge general Aliyu tayiba…..mejo kuwa da idonshi suka cika tab da ƙwalla jiyowaya yayi ahankali yana kallon Isseta nason ta tabbatar mishida abinda halima tafaɗa, cikin kuka taɗaga mishi kanta kana tace “tabbas abinda halima tafaɗa gaskiyane akwaima har wanda taɓoye bata bafaɗa ba dan Allah kadena ganin laifin Ammin…bata ƙarasaba sabida wata irin wawuyar runguma da mejo yayi mata yana sakin marayan kuka meƙuna azuciya, wai mahaifiyarshi ce tarayu awulaƙance hakan cikin halin hauka, yanzu badan Allah yahaɗata da Maryam ba data kasance metausayi da yaya rayuwarta zata ƙare kenan? Waye yayi mata hakan? Miyafaru da ita wanda yakawo mata hauka? Duk shikaɗai yake yiwa kanshi wanan tambayar.Gabaki ɗaya mutanen dake wurin kuka sukeyi daga Alhaji abdussalam har Abba tunanin dasuke yi kenan miyakawo wa Maryama hauka? wacce irin rayuwa tayi kafin haɗuwarta da isseta? Gabaki ɗaya wurin ya kacame dakuka me ban tausayi duk wanda ya kalli Wannan ahalin yasan sunada ban tausayi. “Haƙiƙa ke alkhairice agareni Maryam kamar yadda maah tafaɗa na yadda da hakan tun bayanzuba tun lokacinda Allah ya bayyana minke a mafalki nagane cewar ashe kece yarinyar danake gani a mafalkina kina hana mansura da wannan yayar taki da kuma ƙawar Ummi cutar dani, nasha mamaki sosai alokacinda naga sune ke bibiyata da sharri kina taremun kuma alokacinne naga kinbani wani abun me mugun haske wanda nake binki nakarɓa kika hanani segaya kinbani da hannunki sedai kikace bazaki barmin shi dukaba domin kema kinason shi sedai muyi anfani dashi tare. Alokacinda kika bani abin naji sanyi sosai arai kuma naji natsuwa da kwanciyar hankali atare dani wadda bantaɓa jin irintaba arayuwa ta ashe mahaifiyatace ataredake itace zaki dawomin da ita, lallai maah tayi gaskiya datace mun komai Lokacine ze bayyana kanshi, sedai abinda yake ɗaurin kai wannan matar cikon ta huɗu nakasa ganin fuskarta kuma duk acikinsu itace tafi kowa so ta hallakani, please my sweet life idan kinsan ko wacece kigayamin ita please yaƙasara zancen yana shafa gadon bayanta domin duk wannan zancen dayakeyi ita kaɗai kejin abinda yake faɗa..”wani irin ƙuna Isseta takeji aranta tayaya zata fito fili tanuna Mishi cewar Hajiya umma ce keson hallakashi dawacce fuska ze kalli abun yama za’ayi ya yadda da ita.. please mamana kigayamin Dan Allah tatsinkayo Muryarshi…cikin sauri tagoge hawayenta kana tace “shikenan yah najeeb zangayama kuma ko bangayama ba zaka ganeta da kanka zangayama wasu abubuwa dazakayi idan kayi yadda nace dakanta zata bayyana agareka yanzu please kajegun Ammina kowanne lokaci zancenta bewuce tanaso taji ɗimin ahalinta ba dan Allah mijina kaje gareta, tafaɗa tana fidda shi daga jikinta… murmushi ya ɗan sakar mata tare da dungure mata hanci kana yataso ahankali yazo gaban Ammi yazauna kawai tare da zuba mata ido, aiko atake suka cika da ƙwalla yana tuna abubuwan da halima tafaɗa akanta beyi auneba yajita ajikinshi ta rungumeshi tana kuka…shima cikin sauri yaƙara rungumeta yana kukan. Hakan Abba yahaɗasu duka ya rungume shima yana kuka abin tausayi bame iya rarrashin wani acikinsu….sun ɗauki tsawon lokaci ahaka kafin suraba jikinsu dana juna cikin Muryar kaka tace “kayafemun yarona wlh bad..saurin rufe mata baki mejo yayi yana girgiza mata kanshi kafin yabuɗe baki daƙyar yace “please Ammi kidena faɗar komai dan Allah nine yadace nanemi afuwarki sabida na tuhumeki akan abinda kema bakisan yaya yakeba, dan Allah kiyafemun mahaifiyata… murmushi tasaki tare da shafar kyakkyawar fuskarshi tace Allah yayima albarka yaya abdoul…ido yaɗan waro shidasu sapwan haddama Abba….ganin yadda suka waro mata ido yada tayi murmushi tace “au kuna mamaki ne? Yaya abdoul mana part 2 duk wurinnan akwai mekamada shi kamarshi sekace antsaka kara. Se alokacin duk suka saki dariya me sauti hadda shi najeeb ɗin. Cikin sanyi murya Hajiya Hannah takira issetaAhankali tamiƙe tana ciza lips ɗinta sabida azabar datakeji gaya tsakanin inda take zaune da gunda Hajiya Hannah take akwai ƴar tazara. Cikin sauri mejo yamiƙe kamar wanda aka tsikara yaɗaukota ko Kunyar idon mutanen dake perlor bejiba, ajiyeta kusan Hajiya Hannah tare da cewa “Are you okay? Kai taɗaga Mishi hankali, tuni annurin fuskata yagushe karfi tabawa babanki karya shiga tayi iyak murmushi…b harmada mama bintu da kallo sukebin isseta domin dukkansu sun ɗora ayar tambaya akan wannan tafiyar Tata. Ajiyar zuciya Hajiya Hannah tasauke cikin rarrashi tace “Maryama kiyi haƙuri da abinda zakiji daga garemu wlh muma bawai hakan kawai muka rabudakeba akwai.. dalili Bara kiji abinda yafaru tun kafin haihuwarkima. Nan Hajiya Hannah tashiga bawa isseta labarin rayuwarta harkawo sanadin dayasa takawota gun mama bintu, daga ƙarshe tace “ina fatar zaki mana uzuri kiyafe mana dan Allah ƴata…rungumeta isseta tayi tana kukan tausayin mahaifiyar Tata tace “wlh bakomai dan Allah kidena bani haƙuri dama maah tagayamin duk abinda zanji ko zangani gaskiya ne sabida hakan nariga na yadda da ƙaddarata tunkafin tazomini. Wani irin farin cikine ya lulluɓe Hajiya Hannah wanda baze misaltuba.Anan dai kowa yafahimci kowa akasamu dedeto mekyau tsakanin ahalin biyu. Tuni akashiga raha da barkwanci tsakani ana gaishe gaishe da jadada sanayya ga juna, sunjima cikin nishaɗi yadda haddaka nayi bayin ɗazu nagankaba. ganindai anata hirar yoshe gamo ba’ada ba’asin yin abinda yakawosu yasa mlm Musa yin gyaran murya yace ‘ranka yadaɗe inada magana dudda cewar yanzu duka abun ahannunka yake. Cikin mama Alhaji abdussalam yace “wacce irin magana mlm Musa inajinka. “Yawwa ranka yadaɗe zancene akan auren Maryama dama nasan bintu ta sanar muku shine nace yanzu yaza’ayi kenan?? Kai aitunkamin mlm Musa yakai ƙarshe annurin fuskar Alhaji abdussalam yaɗauke cikin kakkausar murya “wannan auren shirme ne mlm Musa sam ban yadda dashiba kawai nemo mijin za’ayi yasakar mun ƴata domin Maryama tun da aka haifeta nayi mata mijin aure…! Tab ɗijam wata sabuwa akace inji ƴan caca.

