Hausa novels

Gargadar So Chapter 47 By M Shakur

Bugawa kirjin Hawwa yayi sabida yanda murmushi taga yamai kyau da sauri ta dauke kanta tayi folding hannuwanta a kirji tace “ewww Allah ya kyauta you don’t even belongs to league na men da Hawwa fancy, babu abinda zanyi da womanizer, drunkard and a playboy like you!” Shiru Khaleel yayi yana kallonta kaman mai nazarin wani abu saikuma yatashi daga bakin gadon jakan daya gani a tsakar dakin yadauka yace “we will see about that if this womanizer, drunkard and what’s even the last one dakika fadi Kulu”? Aharzuke Hawwa tace “nace maka ba sunana Kulu ba” dan murmushi kadan yayi baice komiba yawuce kofa, Hawwa data kara kulewa sabida yanda taga ya maidata mahaukaciya tace “ina zaka da jakana? Zaka kara da sata akan qualities din naka ne”? Tsayawa yayi saikuma ya juyo ya kalleta yabude baki zaiyi wata magana kawai saiya daga mata gira daya yamata dan iskan murmushi yabude kofa yafito dasauri Aminu yazo zai karbi jakan yace “kawo Ya Ibrahim nadauka”girgizamai kai Khaleel yayi yace “no dauko sauran saika sameni a mota awaje” yawuce Ammi tabishi da kallo kawai taji yafara kwanta mata arai itama ta tashi tashiga dakin Aminu ya kwaso sauran kayan yafito, Ammi takalli Hawwa data kirne fuska tace “lafiya naga ranki abace” dasauri ta gyara fuskanta tace “bakomi Ammi” hannu Ammi tamika mata tace “tashi mutafi gida to” ahankali ta sauko daga gadon Ammi narike da hannunta suka fito Khaleel na tsaye tareda Aminu yagansu sun fito duk yanda yaso yadena kallon Hawwa data haderai tadauke kai yakasa daga Ammi har Aminu saida sukaga kalan kallon da yakema Hawwa kaman zai hadiyeta da idanu, har wajen motan sukazo Hawwa tace “ina keken Aminu”? Dan sosakai Aminu yayi zaiyi magana Khaleel yace “I’m taking you home dakaina” yasa hannu yabude musu bayan mota yace “Mom shiga” ahankali Ammi ta shiga shikuma Aminu ya zagaye shiga gaba abinshi Hawwa ta kalli Khaleel da idanunta dahar sunyi ja, Ammi ta leko ta window ganin yanda take hararan Khaleel tace “shigo mana Hawwa” danne komi tayi sabida Ammi ta shiga taki rufo kofan yadanyi murmushi yasa hannu yarufe yashiga gaba ya kunna motan he can’t even remembers d last time dayayi driving haka yaja motan su Salman na binsu abaya cikin wata Lexus.Aminu sai hira yakema Khaleel, adan hankali yace “me kake karantawa a school” Dasauri yace “computer science engineering but nagama project nakeyi” gyadamai kai Khaleel yayi baisan kodan shi baida siblings bane but he kind of love siblings nata barinma yanda yaga suna sonta and suna sonshi ahaka har gida parking yayi Hawwa tabude tafito azuciye Baba yace “oyoyo oyoyo” kawai ya rungumeta yace “mara lafiya yaya jikin eh patient” dan murmushi tama Baba yace “naji sauki” da gudu Ramlat tafito tana zuwa tai wajen Khaleel tace “Ya Khaleel oyoyooo sannu da zuwa good morning” kallon Ramla yayi kowama na wajen yayi saikuma yayi murmushi, sosai Hawwa ta tsare shi da idanu he looks so good dayana murmushin, he just loves yanda suka nuna suna sonshi, cikeda wasa yace “Ram……” dasauri tace “Ramla sunana” gyadamata kai yayi yace “nice name” zatai magana Ammi tace “ke kibar mutane su huta” Baba yace “zoka zauna Ibrahima” dasauri Hawwa tasaki hannun Baba tawuce ciki abinta su Ammi da Ramla suka bita sai Baba da Aminu suka zauna awajen, Baba ya kalli Khaleel yace “sannu da kokari Ibrahima Allah yabaka lada nagode da komi” dan sauke kamshi kasa yayı Baba yace “yau zan sanar da Hawwa zancen auren ku” ahankali yace “Ibrahima Hawwa matarka ce yanzu kaine keda iko da ita bani ba, Alhamdulillah tasami lpy an salla mota daga asibiti ko yanzu kace zaka tafi da ita ban isa nace a’a ba” Baba yasake shiru yace “inaso ka sanar dani yaushe kakeso ta tare? Kanaso ayi taro ne? Zanso na gayyaci yan uwan marigayiya mahaifiyarta dake kauye da nawa yan uwan, yanda akai auren mudan sanar da mutane bıkın suzo wannan shine ra’ayi ma amman kai me kakeso?” Shiru Khaleel yayi baitaba biki ba as far as public is concerned haryau anamai kallon mara aure ne dan ba’a taba sanar da bikinshi waje ba, hakanan kuma ya kalli Baba ya kalli siblings nata kawai sai yaji he wants to throw wedding for them, sister su batai aure da wuri ba is only right he lets them celebrate her, and one last final point is kodan ya kular da Hawwan yanuna mata he can actually get duk kalan macen dayakeso yasamu aduniya yanaso yayi biki ayi su dinner yayi kissing nata in public yatabata bayanda zatayi, wani, Kayataccen murmushi yayi yace “Baba inaso ayi biki, nan da 3weeks” Dasauri Baba yace “dubamana date Aminu” calendar Aminu yashiga yana duba date yace “July 24th kenan Baba ranan asabar” ahankali yace “Baba I will handle everything zan kawo katin biki da komi” yakalli Aminu yace “kome akeso kamin message” Dasauri Aminu yace “banda number ka” kiramai number shi Khaleel yayi yayi saving sannan yatashi yace “Baba natafi” Baba yamai murmushi yace “bye my son”.

Back to top button