Uncategorized

Matar Makaho Part 11 Complete Hausa Novel

 

MATAR MAKAHO

Chapter 11

Cikin gida yabi sumayya, yana kiranta amma koh juyawa batayi ba, har suka shiga kofar su

Ke sumayya bake jinane, koh me? sai magana nake kin mini banza.

“Na fasa zuwa kaban key na bude d’aki”?

Akan me kika fasa zuwa, koh ince me akai miki, nadai san lafiya muka fitoh?

Ba kome kawai dai na fasa ne, tace tana tunanin ta fad’a masa abinda Ammar ke mata, wani zuciyar kuma ya gargade ta,   kartayi ta jawo wata rigimar kuma abanza.

Ke sumayya koh ba magana nake miki bane, nace menene dalilinki na fasa zuwa ?    

“Nikam nafasa nace maka kuje kawai”?    

Akan wani dalilin?

“Kaina ciwo yaka kuje kawai”

Ai shikenan nima na fasa zuwa, bara nakira, khadijan ta dawo,yakarasa maganar da kokarin juyawa

“Da sauri ta rike masa hannu”nifa ba ina nufin ku fasa zuwa bane,bafa”   

Ni kuma in bakije ba bazanje ba

“Shikenan muje”    

Haka sumayya tanaji tana gani tabi muhammad suka fitoh waje, ido ta d’aga ta kalli Ammar

Sunkuyar dakai Ammar yayi, tunda yaga fitowar su bai sake d’aga ido ya kalleta ba

Shiga motar sumayya tayi,  muhammad ma gaba ta bude masa ya shiga, ita da khadija a baya.

Ammar motan yaja suka cillah titi,sai millionaire sweet khadija kam sai bin gidajen unguwan take da ido, kamar wata wawuya,  tana d’aga ido, suka had’a da Ammar ta mirrow hararanta yayi ya kauda fuska 

A kofar wani makeken gida sukayi packing Ammar ya danna hon, da gudu maigadi yazo ya bude musu get, kusa hancin motarsa yayi zuwa ciki.

Suna packing Ammar ne ya fara budewa ya fita da,sauri ya zagaya ya bude ma muhammad bangaren sa hannunsa ya kama,  yatai maka masa ya sauko

Sumayya ma budewa tayi ta fitoh ta tsaya, tana kallon khadija dake ta kalekale koh fita takasa “khadija menene haka bazaki fitoh bane”?

Da sauri ta fitoh tare da d’an sosa kumatun ta najin kunya.

Cikin gidan suka shiga, sumayya kam, koh d’aga ido batayi ta kalli waje sau biyu ba , gaban ta kawai take kallo, don ita wannan gida baikai ta masa kallon hauka ba

Suna isa kofar falon Ammar yasa hannu ya bude,shiga sukayi bakin su d’auke da sallama

Wa’alaikumu salam oyoyo laleemon bee warugo, wata bakar mata hajiya kyakkyawar gaske, kallo d’aya zaka mata kasan ita ta haifi Ammar,sai wasu yan mata guda biyu,   da saurayi zaiyi sa’an khadija, duk suka mike ganin su sumayya sun shigo cikin falon.

Murmushi d’auke a fuskar muhammad ganin yanda mutanen gidan suka taresu da mutunci,yauwa hajiya jam bandu, noi shumre yan julijam?

Jam sai jam,muhammad?tace tana kallon sumayya dake tsaye, bismillah sumayya on jod’a mana?

Ba musu sumayya tazauna akan d’aya daga cikin kujerun falon Ammar ma waje yanunawa muhammad ya zauna sai khadija da tuni ta dade da zama abinta.

Gaisawa sukayi da hajiya, kannen Ammar suka gaidasu,Kayan ciye ciye aka jera musu a gabansu, dangin nama da kayan ci. 

Ammar ne ya aike kannen sa suka d’auko abincin da suka kawo a motar,sosai mamarsa taji d’adin ziyaran nan, abincin ma atake suka zuzzuba suna ci, sosai hakan yama sumayya dadi ganin basuda wulakanci koh jijidakai sam.

Har yamma suna gidan sosai khadija ta sake sai hira take da yan matan, muhammad ma hira yake da Ammar da Abbas sabanin sumayya da hajiya keta janta da hira, itakam daga eh sai ah ah .

Kai Aunty sumayya tsaya maimuna ta d’auke mu hoton sallah, khadija tace tana matsowa kusa da sumayya don tun d’azun hotona suke d’auka, ba musu sumayya ta mika wayarta iPhone wa maimuna ta dauketa da wayan.

Da mamaki maimuna kanwar Ammar ke kallon wayan, da sumayya ta mika mata,  koh su basu rike waya mai tsadan wannan ba,  sai wannan da yayansu yace rayuwansu abin tausayi, Amma ita bata ga tausayi anan ba mata kamar balarabiya, ga aji, dajiji dakai,  ga sutura mai tsada irin wanda mom in su ke sawa, Karba tayi 

khadija da sumayya suka gyara ta fara d’aukarsu hoto

Ganin maman Ammar tabar falon, yasa sumayya tashi ta kamo hannun Al’ameen ta jashe zuwa d’aya kujeran suka zauna, dafa kafad’arsa tayi “maimuna d’auke mu pls hoton yayi kyau

Ai da gudu khadija ta dawo bayan kujeran ta tsaya, daman 1siter ne Al’ameen azaune akai, sumayya a hannun kujera, ita kuma ta tsaya a bayan kujeran, d’aukarsu hoto maimuna take duk da muhammad ba kallo yake ba, Amma dai hoton yayi kyau, saidai ba camera yake kallo ba 

TikTok maimuna ta shiga ta kunna waka,  tana musu vedio sosai yayi kyau, fa’i ma shiga tayi da Abbas kannen Ammar, duk sun shiga vedio abu da iphone ga background, ba karamin kyau sukayi ba, Ammar ne kawai bai shiga ba.

Sai dare maman Ammar ta barsu suka tafi bayan sunci abincin dare, da suka tashi tafiya turare da zani ta baiwa khadija, sumayya kam sarka mai kyau ta bata fari, sosai sukayi godiya.

Tunda suka kama hanyan dawowa, sumayya ta lura akwai abinda ke damun mijinta,  ganin yanayin sa ya sauya sosai.

Bayan sun dawo gida, har gida Suka raka khadija,ruwa ta iba takai band’aki ganin yanayin Muhammad, kamar ba lafiya, gabaki d’aya yayi laushi kamar bashi ba”yayan khadija nakai maka ruwa, koh zakayi wanka”?

Toh,kawai yace yana mikewa,wankan ya shiga koh towel bai d’auka ba, saida sumayya ta kai masa 

Bayan ya fitoh wanka d’aure yake da towel, daga kagan sa, kasan ba lafiya,a hankali yake tafiya yana dafe da kirjin sa, yashigo d’akin.

 da sauri sumayya ta bisa da kallo,dayake yanzun basa shakkan juna, sosai bakaman daba,yasaka ta tube kaya a dakin, towel nata ta d’aura ta fita, ban d’aki ta shiga tayi wanka,  fitowa tayi ta shiga dakin da mamaki take kallon Al’ameen, ganinsa har lokacin zaune koh kaya baisa ba yayi tagumi.

Al’ameen dake zaune ji kawai yayi sumayya ta kamo hannunsa,A hankali tayi magana “yayan khadija lafiya”?

Janyota kawai yayi gabaki d’ayanta ta fado kansa, a hankali ya sa hannu ya dad’a mannata a jikinsa.

” yayan khadija bansa kaya ba”? 

Na sani sumayya ai naji jikin ki d’aure da towel.

“Meke damunka”?

Zuciya ta ke dokawa da karfi, sumayya inaji a jikina akwai wani babban Al’amari dake tinkaro ni.

” kamar ya”?

Sumayya zuciyar kowa na bugawa, sannan wani sa’in mutun najin zuciyar sa na luguje,  Kamar yaji tsoro,koh baida gaskiya,koh yayi laifi.

“Hakane”

Amma ni wannan bugun zuciyar bana tsoro koh fargaba bane.

“Name kenan, bangane ba”?

Lumshe ido yayi yana kara manna sumayya a jikinsa,irin wannan lugujen na ringaji lokacin da mami na zata bar duniya, Aranan haka na wuni da lugujen zuciya.

Haka ranan da zan makance, ma irin bugun nan na ringa ji, haka ranan da salim zai bar duniya,sumayya inaji a jikina akwai abinda zai faru dani duk da bansan gaibu ba.

“Subahanallah insha Allah ba abinda zai tinkare ka sai Alkhari”

Insha Allah….Sumayya!

“Na’am yayan khadija”

Don Allah sumayya, yau ki bani hakkina, sosai nakejin wani irin matsanacin bukata, tun da yamma………….

Ta bangaren hajiya kami, kamar yanda boka yace, haka ta d’auke mujiya har cikin gidansu, bayan ta saka kejin a buhu, a d’akin ta ta ajesa a karkashin gado, kamar d’a haka take masa jinya, A washe garin ranan da sumayya zata fara period, a daren ranan, Alarm kamila tasaka a wayan ta, da misalin karfe 2 na dare ya tashe ta, mikewa tayi a hankali ta bude kejin zata d’auki mujiya.

Da wani irin mugun sauri taja baya tare da zaro ido…..mujiya ne tayi mushe, bakinta har rawa yake ta d’auki waya, lalubo number Harira tayi, ta kara wayan a kunne

Ta bangaren Harira kam,tana tsaka da baccin ta,don a silent ta saka wayar sam bata san ma, wata kamila na kiranta ba

Jifa kamila tayi da wayan,jin Harira bata d’auka ba 

Washe gari da sassafe koh karyawa,kamila batayi ba ta ciccibi mushen mujiyan nan, tayi gidan Harira,don wallahi ta kudurta A ranta bazai yuba, bazata kashe kudi abanza ba, sai an biyata kudin ta, haka kawai ita ba muhammad ba, ita kudin ta ya tafi

Koh sallama babu ta shigo falon Harira, tana kwala mata kira.

Da sauri mijin harira ya d’ago, yana kallon kamila, lafiya baiwar Allah? 

Lafiyar kenan, ina Harira?

Kafun ma yayi magana, harira ta fitoh daga d’aki cikin mamaki jin muryan kamila da sassafen nan, kamila lafiya?

Lafiyar kenan, kika gannin nan,wallahi kinji na rantse bazanyi asaran kudina ba, kin sanni bani da mutunci tam.

Da sauri Harira ta kamo hannun kamila,  sukayi wani d’aki dake cikin falon, ganin mijinta a zaune a falo, kamila ke kokarin tona mata tsilili

Ke kamila bana son iskanci kinji koh, zaki  zo mini gida da sassafe,agaban mijina kina kokarin zubar mini da mutunci.

Au mijin da kikace kin shanye ne,  har zakiji tsoron yasan wani abu a game dake?

Ji hauka toh don ka asirce, mutum sai akace ka fad’a masa ka masa asiri ?ji mahaukaciya

Ke duk ni ba wannan ba,mujiya ta mutu,  tana boot na mota na,ki wuce mu koma inda muka karbo she, yaban kudina in yasan bai iyya aiki ba, mena karbamin kudi(daman wannan halin kamila ne indai akan kudin tane bata da mutunci)

Ke da sassafe,  koh karyawa banyi bane,  zan kama hanyar mutum biyu,toh baki isa ba,  don uwarki ni, xaki tsaya kina bawa umurni.

Ganin Harira tad’au zafi, daman ita bata iyya fushi ba sam, yi hakuri Harira raina ne ya baci,  don Allah ki taimaka,mu koma wajen mutumin nan.

Ki jirani nayi wanka, na karya saimu tafi?

Ok kawai tace tana zama,abakin gadon d’akin ta zabga tagumi.

Sai kusan 9 suka d’auki hanya, gabaki d’aya kamila sai masifa take, akan malamin bai iyya aiki ba

Bayan sun isa,aje masa kejin mujiyan,  kamila tayi a gabansa 

D’aukar mujiyan yayi ya kakkala, yanka cikinta yayi ya fitar da layan,warwarewa yayi atake,  yaga rubutun sunan sumayya ya kone murus,  kamar wanda aka saka kalanzir da petur aka banga masa, d’aga ido yayi ya kalli kamila.

A gaskiya raba Wa’innan ma’aurata baban matsalane, don asirin da aka musu mundin aka rabasu, xa’a iyya samun matsala aikin wasu warware wa zaiyi,gashi sun rike ibada sosai,koh wajen kofa da Aljan zai kusance su sun tushe sa,makiyansu na tare dasu,  tabbas suka gane akwai mai kokarin bata musu shiri,zasu iyya ganin bayanki don su mutuwa koh Rayuwa,agunsu don cika buri ba kome bane.

Ina mai baki shawara,kamila ki hakura da kokarin rabasu,kidai nemi wani hanya da zaki malleke sa, Amma banda asiri tunda kika ga nayi iyya kokari na ba’a dace ba toh ki hakura.

Wani irin na hakura,sai dai kace baka iyya aiki ba, kuma maganar kudina, Amaida min tunda aiki baici ba.

Keeeeeeee!!!! dakata,  bamason rashin kunya a wajen nan,inba haka ba wallahi zamuyi maganin ki, nan ba wajen shirme bane, kuma kudi inya shigo baya fita

Ganin tana kokarin magana,yasa Harira matse mata baki

Buge hannun Harira kamila tayi,don gabaki d’aya ranta ya gama baci,sosai zuciya ya ibeta,kai bokan banxa, bokan wufe mai karyan aiki,yana cin kudin mutane,wallahi baka isa kace zaka dakeni ka hanani kuka ba,  kudina ne sai ka bani,tunda aiki na baka,  kuma aiki baiyi kyau ba,kai harka isa kace zaka min abinda Allah bai mini ba?

O’ kinsan da hakan ne,kikazo guna yau saina nuna miki aikin, nakan dutse gaskiya ne, wani irin maganganu yayi take kadangaru dake manne a jikin kokon,guda goma suka ruga da gudu zuwa jikin kamila, ai kam da sauri suka manne mata a jiki, daman dogon riga da d’an karamin gyele ta yafa, biyar sukayi kasan dogon rigan suka mamakale mata a cinya wasu sukayi cikinta wasu kan breast inta, suka makale wasu kam gashin kanta suka shiga suka kwanta.

Ai wani irin ihuuuu Harira ta sake, da gudu tayi waje, kamila kam wani rin tsalle tayi ta bugu da kasa hade da kurma ihu, tana bawa nakan dutse hakuri,amma ina koh kallon ta baiyi ba,jin kadangarun manne a jikinta,  kamar sun samu jikin gatanga, yasata yarda d’an kwali da takalmi da gyele,da gudu ta ruga tayi waje tana ihu, jinsu sai yagushinta suke, b’anb’arawa tayi da gudu harta wuce, Harira data dade da fita,cikin gari ta fitoh tana ihu tana kokarin kwabe riganta Allah yasa akwai brz da dogon wando 

Ai jama’a salati suka d’auka, ganin kadangaru mammanne,a jikin kamila gashi duk inda ta wuce sai wasu kadangaru dake wajen,sun bita da gudu,ai itama saita kwasa a guje suma suka bita gayya guda a baya 

Duk mai imani inya kalli kamila saiya tausaya mata, wasu kam sai Allah kara suke mata jin tana sambatun, mugun abinda taso aikatawa hakan ya faru da ita

Harira batabi dakan kamila ba,duk tabi ta tsorata motar taja sai jala.

Tana isa gidan su kamila ta wuce direct, tana kuka ta sanar, da iyayen kamila abinda ya faru, sosai hankalinsu ya tashi,  hade da tsinewa Harira,su sunsan yarsu batasan wajen boka ba Harira ne ta kaita

A take suka tasa keyar Hariya zuwa mutum biyu, suna isa ake sanar dasu ai kamila tayi daji,don gudu take kadangaru na binta, da gudu iyayenta suka nausa hanyar da aka nuna musu kamila tabi. 

Kamar wasu zararu haka suka fasa daji, suna neman kamila,Acan gindin wani bishiyan kuka,suka ganta zaune sai ihu take tana kama kadangarun dake jikinta tana hurgarwa,  da gudu zasu dawo su like mata, gabaki d’aya katangaru ne a mammanne a jikinta, wasu suna manne da jikin bishiyan da take kai, saboda basu samu fili ba abin gwanin tausayi gabaki d’aya ta zareeee.

Maman ta kam kwala kara tayi, tayan ke jiki ta fadi, da gudu baban ta yayi wajen da niyar kamo yarsa, duk da kadangarun sun matukar bashi tsoro, amma haka yayi ta maza

Ai kadangarun nan,na kallon baban kamila na tahowa da gudu suka zabura, sukayi kansa 

Ganin kadangaru sun juya garesa,yasa sa b’anb’arawa da gudu yakoma baya,suma koma sukayi inda suke kamar da

Ganin Halin da maman kamila take ciki, yasa Harira da baban kamila,d’aukarta yayi suka fitoh cikin gari da ita,asibitin mutum biyu suka kaita, bayan an bata gado,waya baban kamila yayi ya kira maman sa, da yan uwansa ya sanar dasu abinda ke faruwa, Harira taso fecewa,Amma baban kamila yace ina, kafarsa kafar Harira in Harira taga tabar mutum biyu toh da kamila za’abar garin………….

Da sauri ta d’ago kanta jin yanda yayi maganar a matukar sanyaye,  kamar wanda zai nemi Alfarma itafa halaliyar sace,amma ga yanda yake had’ata da Allah, yayi matukar kokari, yanzun ana neman kusan wata uku da auren su, koh ma fiye da haka, ba tare da ya taba tilasta ta akan hakkinsa, kullum ya bukace hakan, zata saka masa kuka, koma hakan koh baya so yake kyaleta.

Jin batace kome ba yasa sa lalubar fuskar ta,In baki Ra’ayi kiyi hakuri sumayya,na hakura.

Da sauri ta kamo nasa fuskar hawaye na cika mata ido, “yayan khadija  hakkin kane fa?kaima da kanka ka fad’a, kaga kenan ni bani da damar hana ka, tunda naka ne, duk abinda zaka bukata a gareni mallakin kane, na amince kayi duk abinda kake so dani, ta karasa maganar da fashewa da kuka.

Jin ta fara kuka yasa muhammad, da sauri yace, sumayya kiyi hakuri nama hakura, shikenan tashi kisa kayanki mu kwanta.

“Ba kuka nake ba”    

Hannu yasa ya shafo kumatun ta, toh me kike, kuma menene a fuskar taki?

“Kayi hakuri”     

Fuskar sa ya had’a da tata fuskar, baki min kome ba sumayya.

“Toh insa kaya koh haka xamu kwanta” ?

Shikam ba karamin dariya sumayya ta basa ba harya kasa hakuri, saida ya dara, hhh menene haka kuma sumayya?

“Toh ba tambaya nayi ba, koh tambaya laifine”?

Ah ah ba laifi bane, yace yana d’aura fuskarsa a kafadar ta, yana goga mata gemunsa. 

A hankali sumayya ta manne masa gam a jiki, hannu tasa ta kama gashin kansa,  jin kamar zai zautar da ita, jin bakinsa akan wuyan ta.

Ahhhh, yace yana kamota, d’agota yayi gabaki d’ayan ta, yana lalube harya hau gadon, kwantar da ita yayi ya hau kanta,  bakinsa ya jona cikin nata, sosai yake tsotsar bakin ta, jikinsa sai rawa yake.

Sosai sumayya ke tare da farga ba, don yanayin muhammad kawai yau zai tabbatar maka, da gaske yake son Angon cewa.

Washhh Ashhhhh sumayya tace, lokacin da taji muhammad ya yaye mata towel in jikinta, shima tuni ya watsar da nasa daga ita harshe babu sutura a jikinsu…….

Zafafan Romance Al’ameen yake wa sumayya, da zafi zafi don A lokacin bazaka taba tunanin koh baya gani ba, aikin dake gabansa kawai yake.

Sumayya dake kwance rumtsa ido tayi,  jin Al’ameen na ware mata kafa, bakinsa d’auke da Addu’an saduwa da iyali

Kara ta kwala da karfi, tare da ware ido, jin wani Al’amari mai girma daya ratso rayuwarta, a karon farko hannunta dake free, ta d’aga a zabure ta cakumo gashin kansa.

Da karfi ya fizgo Hannunta, daga gashinsa ware hannun yayi ya danne da jikin katifa, sosai ya kara bada himma akan abinda yake, bai taba d’aukar zaiji wani d’adi ba tunda Abbajon sa ya barsu,  wahalar rayuwa bai barsa ya tuna akwai wani dadin da zai iyya d’and’ana wa, maka mancin wannan dadin ba, sai gashi yau sumayya ke shayar dashi.

Sumayya kam gumi ta had’a sosai, duk da an fara yayyafi, Amma daga ita har muhammad zufane ya jikasu, sosai sumayya ke kuka tana goga kanta da jikin pillow, ba zafin da Al’ameen ke d’and’ana mata bane yafi ratsata, wani irin sarawa taji kanta nayi kamar wance ake fisgar gashin kanta da karfi, haka takeji a kanta kuka tasa, don abin ya hade mata biyu, ga azaban da Al’ameen ke gana mata  sosai, kanta ke bugawa ji take kamar kwakwalwarta zai fita, sai salati take tana murza kan da filo.

Ta bangaren Al’ameen kam, yau ba’aji ba’a gani am amsa sunan MAKAHO yau, don koh kukan sumayya baji yake ba,  hankali..sa na gefe, damuwar sa kawai yaji abinda yake gabansa.

Sumayya jin wasu irin bugawa da kanta keyi akai akai jijiyoyin kanta takeji kamar zasu tsinke, koh gani bata iyyawa yanzun sosai, duk da a duhu suke Amma duhun da take kallo yanzun yafi karfin duhun  d’akin.

Sosai bakin ta ya bushe, sai shakuwa take, tana kiran ruwa da muryarta da baya fita sosai.

Amma ina muhammad baisan tanayi ba abinda yasa agaba yake fama.

Jan numfashi sumayya tayi da karfi jin wani irin wahalallen shakuwa, ya gudu da numfashin ta duka, sakewa tayi jagab ta koma jikin filo, 

Muhammad bai farga da halinda sumayya take ciki ba sai da ya gama samun nutsuwa, A hankali ya zare jikinsa a nata, aiji yayi kamar an watsa masa Allurai a idanun sa, soki yakeji a cikin kwayan idonsa, sunfi d’ari rumtsa idon yayi da karfi, yana kiran sunan Allah jin wani irin barkono da soki na cakansa, tunda yake bai tabajin azaba irin wannan ba, kansa ya had’a da jikin gado da karfi ya buga ji kake gauuuuu ………..ya sulale kan katifar baya motse.

Har Asuba muhammad da sumayya suna sume, basu farfado ba, babu wanda yasan halinda suke ciki, sai mahallincin mu, 

A Hankali sumayya ta fara motse, a hankali take kokarin bude idanunta, sai kuma ta maida su ta rufe da sauri, jin wani irin nauyi daya mata, sai da tafi minutes 10 kafun ta sake bude idon, a hankali harta budesu duka, ware idon tayi tana kallo dishi dishi har idanunta suka sauka akan muhammad, dake yashe a gefe ga goshin sa a fashe.

Cikin matukar razana ganin sa kamar wani matan ce, haftowa tayi da kuzari zata mike, kara ta sake tana Ambatan sunan Allah, ta koma ta kwanta jin wani irin rad’ad’i dake ratsata, ta kasa

A hankali ta mike zaune, tana cije lebenta, ta fara rarrafawa zuwa garesa, matsowa tayi sosai ta tattabasa jin baya motse, yasata sake kara”innalillahi wa’inna’illahi raji’um nashiga uku, don Allah muhammad karka tafi ka barni wayyo nashiga uku, wayyo mijina na bonu,ganin kamar suma yayi, sai kuma ta rarrafa da sauri taja blanket in ta rufe masa jiki, da rarrafe ta sauka akan gadon,  towel inta dake yashe a kasa ta d’auka ta d’aura.

Firij ta wuce ta d’auki ruwa, haka ta rarrafa ta iso bakin gadon ta saitin da yake, hannu tasa ta bude bakin goran, ta tsiyaye ta wasa masa a fuska, Amma ina shuru muhammad bai tashi ba, kuka ta sake tana bulbula masa ruwan sanyin a fuska, Amma koh motse baiyi ba,”wayyo muhammad wayyo mijina, na shiga uku Allah ka taimake ni”

A matukar gigice ta saka kunnen ta a kan kirjinsa, jin zuciyarsa na bugawa, yasa hankalin ta kwanciya don ta gane suma yayi.

Tunawa tayi da number maimuna kanwar Ammar, a wayan ta koh ta kirata ne? ta had’ata da Ammar koh Zai taimaka mata mijinta ya tashi tunda itama, tana bukatn taimako, gashi bata san wazata kira ya tallafa musu ba.

Da rarrafe ta isa kusa da wayan d’auka tayi jikinta sai bari yake, ta kira maimuna tanajin ta d’aga tace”Assalamu Alaikum”

Wa’alaikumu salam Aunty sumayya ina kwana?

“Lafiya maimuna don Allah Ammar na gida”?

Lafiya kam aunty sumayya, naji muryan ki a dishe?

” nace miki Ammar na gida”?

Ah ah wallahi yau yabar gari da asuba lfy?

Kashe wayar in sumayya tayi, don bata da lokacin maimuna.

Da sauri wani tunanin yazo kanta, ta rarrafa ta isa wajen kayan sa, budewa tayi tana ciro masa kaya, in yaso sai ta saka masa, ta fita ta kira keke su tafi asibiti, duk da ba lafiya bane da ita, koh da rarrafe zata fita ta taimake rayuwar mijinta.

Kayan sa ta bude ta, dauko jallabiya tayi ta aje, tasa hannu zata d’auki gajeren wandon sa, taji hannunta ya taba wani abu mai karfi kamar gidan agogo, hannu tasa ta zaro abin, haka kawai taji hankalin ta bai kwanta da wannan karamin akwatin ba, hannu tasa ta bude.

Da sauri ta rufe Idanun ta ganin wani irin haske daya kashe mata ido,A hankali ta sake bude ido ta kurawa sarkan ido, yayi haske yasa ke  mutuwa farine sosai, mai kyau sai zanen zaki dake tsakiyar gaban sarka, sosai sarkan ke sheki yana komawa normal.

Jiki na bari ta rike sarkan, indai bata manta ma Al’ameen yace baban shi ya basa sarka, koh dai wannan ne sarkan? menene dalilinsa na cirewa? a wuyansa, rarrafe tayi ta isa garesa, sarkan ta d’auka ta d’aura masa a wuya.

Ai sarkan nan na shiga wuyan Al’ameen, ya wani irin haske sosai sai kuma ya koma normal bai sake hasken ba.

Da rarrafe sumayya ta fita a kofar dikin”subhanallah”tace ganin har rana ya fitoh don lokacin ana neman, kusan karfe 8:00 na safe koh sallan asuba basuyi ba,da rarrafe ta shiga kitchen kittle ta jona a soket, tana zaune a wajen ya tafasa juyewa tayi a boket, ta sake saka wani saida ta juye kittle uku,sannan ta fara kokarin mikewa,don d’aukar boket in ta juye a band’aki, Amma ta kasa, kuka kawai ta sake, ta koma ta zauna.

Muhammad kam tunda sumayya ta fita a d’akin ya farka, sosai idanunsa ke masa zoge kamar an kwakule masa su,tun d’azun yana kwance don duk jikinsa a sake yake.

Da sauri ya mike zaune jin kukan sumayya ta window, sai yanzun tunanin abinda ya faru ya fado masa,take yaji tsikar jikinsa ya miki, hasbinallahu wani’imal wakin, yace yana mikewa zaune, dafa kansa yayi da karfi jin wani irin rad’adi a inda ya buge, a haka dai ya lallaba ya mike zaune, jin baida sutura a jiki yasa sa fara laluben gadon, ji kawai yayi hannun sa ya taba wani abu damshe damshe, ga karnin jini.

Da sauri ya mike, sauka yayi ya d’auki wando a cikin kayansa ya saka, yana dafe da kansa har lokacin idanunsa a rufe suke.

Sumayya!!!sumayya!! Menene?yace yana karaso wa kusa da ita.

Ai barin kukan sumayya tayi, ta zare ido ganin Al’ameen akan kafafunsa, hannu tasa ta kamo nasa hannun”na kasa tashine, ga rana yayi bamuyi wanka ba, gashi ina son kai ruwa band’aki na kasa, gashi ka suma hankali na ya tashi”tana maganar tana kuka.

Rungumar ta muhammad yai da karfin gaske,  A hankali ya bude baki daker, kamar yanajin tsoron magana, sumayya ina sonki, sumayya ina tsananin kaunar ki, bazan taba mantawa da daren jiya a rayuwa ta ba, har abada kece cikon farin cikina, ina fatan har in koma ga Allah, karna miki butulci matata.

Kara rungumar sa tayi sosai, taji wani sanyi a ranta da tausayin mijinta”nima babu abinda zance maka sai dai na mana fatan gamawa da duniya lafiya, mijina har abada bazan taba barin kaba harsai ranan da na daina numfashi in Allah ya yarda.

Toh bakice kina sona ba?

“143”

Meyake nufi?

“Kayi tunani mai zurfi, wanka nakeso nayi nayi sallah, rana yayi ka kaimin ruwa bayan gida”

Toh yace yana saken ta, boket na ruwan zafin ya d’auka, yana tafiya har lokacin idanunsa zafi suke masa, kuma bai bude suba.

Bayan ya aje ruwan, dawowa yayi ya ibi na sanyi a wani boket in daba.

Sumayya dake zaune har lokacin a dakali”ga baf  a kitchen ka kaimin ban d’akin”tace masa

Haihuwa kikayi ne wai gimbiya?

“Mutuwa nayi”

Insha Allah ba yanzun ba, yace yana d’aukar boket in, kaiwa yayi band’aki yana fitowa,  sumayya dake kan dakali ya ciciba yayi bayan gida da ita, ajeta yayi.

“Toh ka fita mana, waima menene naga ka rufe ido yaukam kaki budewa”?

Idanun ciwo suke mini, yau kamar borkono a ciki.

Uhmm kawai sumayya tace tana had’a ruwan wanka, duk yanda taso muhammad ya rabu da ita ki yayi shiya taimaka mata tayi wanka, ya d’auko mata wani towel in, ta d’aura ruwa ya cika a buta ya bata tayi Alwala.

Shima wankan yayi ya fita a d’akin har lokacin idanunsa a tamke, yayi Alwala yashiga d’aki,  zuwa lokacin sumayya tayi sallah tana zaune tana lazimi.

Bayan ya idar da sallan, a hankali yasa hannu ya shafo sarkan wuyansa da mamaki ya kalli sumayya, gimbiya yanaga sarka a wuyana kuma,  ke kika d’auko koh?

Da mamaki sumayya ke kallonsa, yau kuma gimbiya ta zama kenan”eh nina saka maka,  kace babanka ne ya baka sannan baka sakawa, akan me”?

Sumayya naki saka sarkan nan ne, dom sau biyu ana kokarin fizgesa a wuyana,shiyasa na daina sawa.

“Kamar ya ban gane ba”?

Wallahi barayi mana, kaje kasuwa xaka saida abu anki saya, Amma barayi na kokarin sata.

“Allah ya kyauta , wai bazaka bude idon bane”

Ba musu yad’an fara kokarin, bude idon a hankali a hankali harya budesu duka.

“Ya illahih”sumayya tace lokacin da idanunta ya sauka akan kwayar idon muhammad, yayi jajazur kamar jini zai digo, inka ga idon zaka d’auka koh buga masa shi akai jini ya taru.

Sumayya menene naji kina salalami?

“Ba kome, yayan khadija kaga idanunka kuwa”?

Taya zan gani, bayan ba gani nake ba, me idon yayi?

Wallahi kamar jini zai digo jajazur”

Kuma Nima rad’adin da nakeji sosai fa.

Allah ya kyauta, bara naji sauki sai muje asibiti, Amma dai yanzun, kaje chemist ka siyo mini magani rage rad’adi, kaima saika sayawa kanka naga, har wajen ya kumbura”?

Gaskiya ne, kannawa ciwo yake wallahi, gashi ma yunwa nake ji, kema nasan kinaji bara na had’a duka nasai mana.

Nikam bazanci kome ba, ka biya shago kawai ka d’auko mini lemo, bakina d’aci, ka tura a kira khadja tazo tad’an gyara mini kofar, nikuma bara nayi sauri na fitar da zanin gadon ya baci sosai”

Toh ki zauna kawai tunda tafiyar taki batayi kyau ba, bara na jika zanin gadon inna dawo zan wanke? yace yana fita a d’akin bayan ya d’auki zanin gadon, waje muhammad ya fita bayan yakai zanin gadon band’aki, tsallake titi yayi, yaro ya samu ya aika gidan goggo, a kira masa khadija, shikam ya wuce chemist in jambusko.

Yana isa chemist yasamu layi dole ya zauna har akazo kansa, maganguna ya saya harda wanda zai diga a ido, yabi shagon sa lokacin har shagari ya bude, d’aukowa sumayya lemon yayi, yasai abinci duka yana rike da laidodin a hannunsa har lokacin idanunsa rad’adi suke masa.

Yazo tsallaka titi kamar daga sama yaji mota yayo kansa gadan gadan da gudu ya fara kokarin kauce wa, Amma ina saida suka cin masa, kamar zasu kadesa, amma suna zuwa kusa dashi suka ja birkiii

Sosai ya tsorata sai kiran sunan Allah yake, wasu kattai hannun su d’auke da bindigogi, suka fitoh a motar duk sun rufe fuskokin su da mask……..πŸ€

Kamo muhammad sukayi, suka d’aga sa sama suka tura a mota sai ihu yake yana ataimake sa, amma ina mutane kowa gudu yake kar a had’a dashi, muhammad naji aka turasa a mota suka ja….

Khadija data tsallake titi, ganin yayan ta yasata tsayawa tana jiransa ya tsallako su karasa gidan tare,kamar a mafarki take ganin abinda ya faru da d’an uwanta, ihu tasa ta ruga a guje ta tsallaka titin kafun ma ta isa garesu tuni sunja motar sunyi gaba, kuka ta sake sosai tana a taimake yayan ta sai a lokacin jama’a suka fara dawowa. 

Sosai surutu ya tashi a unguwan anata bawa khadija hakuri wance ke kuka kamar ana tsikaran  ranta da tsinke, wasu kam maida zancen yanda ya faru suke, khadija dake duke tana kuka taji an dafa ta, d’agowa tayi da sauri tana kallon sa.

Lafiya khadija mai ya faru naga mutane na tare a bakin titi, gaki kina kuka kuma?

Wayyo shagari yayana barayi suka sace,  duk sun rufe fuskar su da mask, tana maganar tana kuka.

Innalilahi wa’inna ilaihi raji’um yanzun fa yabar shago, ya d’auki lemo, yake sanar dani yau bazai fitoh ba na zauna a shagon, saida ya fita naga ashe ya manta bai d’au maganin daya shigo dashi a hannun sa ba, shine na biyo na kawo masa, yana maganar hawaye na zuba, 

Khadija mikewa tayi, har tana ganin jiri jiri shagari yana rike da ita da taimakon sa suka koma gidan goggo, don bazata iyya zuwa gun sumayya ba a halin yanzun da take cikin nan .

Assalamu Alaikum,shagari yayi sallama a kofar gaggo.

Wa’alaikumu salam, lafiya me zan gani meya samu khadijan?

Zaunar da ita shagari yayi a hankali, shima ya zauna akasan koh kujera bai nema ba tsabar tashin hankali, khadija na kuka shi kuma yana hawaye duk da yana namiji Amma b’atan muhammad ya shiga jikin sa.

Kun zauna kuna kuka bazaku fad’amin abinda ya faru ba, gabaki d’aya kunsa raina sai tsinkewa yake?goggo ta fad’a jikin ta na rawa har zani na kuncewa.

Goggo wallahi oga Al’ameen ne, wasu sukazo suka d’auke sa?

Kamar ya suka d’auke sa bangane ba?

Eh ina ga kidnap ne fa.

Kidnappers kuma wani irin yan garkuwa da mutane, kuma muhammad ina yaga kudin da yan garkuwa zasu sansa, sai kuma ta fashe da kuka, na shigesu ni Amina, ya Allah ka taimake wannan bawa naka ka tsaresa a duk inda yake, Albarkacin Annabi da Alkur’ani.

Ameeen goggo, shagari yace yana dafe kansa koh mutuwar mahaifin sa baiji tashin hankali irin  nayau ba koh don baban nasa ya rasu baiyi wayo sosai bane sai Allah.

Goggo Aunty bata sani ba, ina tsoron kar wani yakai mata labari tazo ta d’aga hankalin ta, gwara dai ke, ki sanar da ita goggo.

Hakane khadija ki daina kukan ya isa haka,  addu’a yake bukata ba kuka.

Dole nayi kuka goggo, shikad’ai nake dashi,  nake gani hankali na ya kwanta, yau an waye gari bansan halinda zai shiga ba.

Kiyi hakuri khadija, bara naje gidan yayan naki, na samu sumayya.

Toh goggo, kawai tace tana cigaba da kukan ta, shagari ma mikewa yayi kamar ruwa ya cisa yayi waje.

Ta bangaren sumayya kam bayan fitan muhammad, kwanciya tayi haka kawai takejin faduwar gaba, for no reason, har bacci ya d’auke ta. 

Goggo tunda ta fitoh gidan ta, sai zulumin ta ina zata fara sanar da mace an sace mata miji, amma dai gwara ita ta fad’a mata dataji a wani wajen, tana shiga gidan koh bi takan kofar yan uwan ta batayi ba,cikin kofar sumayya tayi tana kwala sallama.

Sumayya dake tsaka da bacci ne, ta farka jin sallama ake,  Amsa wa tayi, ta sauka a kujeran a hankali tana dingishi don yanzun dai Jikin da sauki tunda, ta shiga ruwan zafi.

“Laaa goggo sannu da zuwa, bismillah goggo ki shigo”

Ah ah sumayya kedai bari zan zauna a wajen,  ban kujera kawai.

Kitchen sumayya ta shiga zata d’aukowa goggo kujera, da ido gaggo ta bita koh ita yarinya ne ta fahimce meke faruwa.

Hawaye ne ya shikawa goggo ido, duk yanda taso daurewa kasawa tayi.

Sumayya kam sosai jikin ta ke rawa, wanda batasan dalili ba, tana ajewa goggo kujeran itama a bakin dakali ta zauna tayi shuru.

Sumayya!!

“Na’am goggo”

Kin dai san a rayuwar d’an Adam tana tafiya ne, tare da jarabawa koh?

“Kwarai kuwa Goggo” tace tana kara gyara zaman ta, don tasan tabbas akwai abinda ke faruwa

Sumayya ina so ki kwantar da hankalin ki,  kuma ki rungume kaddara a yanda tazo miki,  ina son kiyi hakuri da abinda zan sanar dake sumayya, ki kwantar da hankalin ki addu’a kad’ai ya dace kiyi.

“Meya farune goggo”?

Sumayya ki kwantar da hankalin ki, tace ganin sumayya harta mike tsaye jiki na rawa tana kallon ta.

” goggo meya same shi?tabbas nasan abune ya faru dashi, tun d’azun wallahi zuciya ta tsinkewa take”ta karasa maganar da fashewa da kuka.

Sumayya kiyi hakuri wasu da bamu san suwaye ba, suka zo suka tafi dashi,ki kwantar da hankalin ki in ma masu garkuwa ne zamu jira kiransu, insha Allah babu abinda zai f…….

Goggo bata karasa magana ba, dalilin ganim sumayya ta zube tim akasa,da gudu tayi kanta tana girgizata tana kuka. 

Jin kuka akofar sumayya yasa inna asabe lekowa, wanake gani kamar Amina meya samu MATAR MAKAHO kuma?

Wallahi inna muhammad aka sace, shine na sanar da ita kinga sai kawai ta yanke jiki ta fad’i.

Toh ai saiki kamata muje asibiti, ashe abinda modi ya sanar dani gaskiya ne, wai an kama MAKAHO banda haukan kidnopas ina su ina kama nakashashe?koh d’an kudi da aka ga yad’an samune oho.

Inna ki taimaka mini bara na zuba mata ruwa, da gudu goggo tayi d’aki,ruwa ta ibo a firij  tazo ta watsa mata, amma sumayya bata tashi ba, cicibarta sukayi ita da inna asabe zasu fitar da ita waje sai ga khadija.

Innalilahi inna meke faruwa?

Khadija jeki rufe musu kofa kizo mu tafi asibitin kiyi sauri.

Toh goggo tana kuka ta nufi kofar yayan ta,  rufewa sumayya d’aki tayi da kofa tabi bayan su goggo.

FMC suka kai sumayya, suna zuwa aka bata gado,khadija shagon yayan ta ta wuce saboda rashin kudi a hannun su, shagari dubu 10k ya baiwa khadija, yace na cinikin da yayi yaune.

Ta bangaren kamila, bayan yan uwan babanta sunzo aka kaisu sukaga kamila, sosai suka tausaya mata ba kad’an ba, masu magani aka nema kowa yazo ya gwada, abu ba sauki kadangaru fa sunki barin kamila.

Harira taso koma wa jalingo, Amma sam baban kamila yaki, mijin ta yayita kira tun tana masa karya harya gaji yazo da kansa,  yaji ba’asin zaman ta a kauye. 

Sosai yasha mamaki lokacin da baban kamila ya masa bayanin abinda matar sa ta jawowa yarsu, baice kome ba ya juya ya koma jala.

Bayan maman kamila ta farka, tace atafau sai an maida kamila gun nakan dutse, suje su basa hakuri in ma kudi za’a basa a basa, ya bar musu yarinya ta huta.

Anyi yanda za’ayi aja kamila amma an kasa saboda kadangaru sunki daga an tinkaro ta zasu hayayyako ma mutum. 

da aka ga haka sai aka samo bulala ana kora kamila dashi kamar saniya ana mata barazana tana gudu, in zatabi hanyar da bashi suke soba sai wasu su tarota, a haka gwanin tausayi akayi gun nakan dutse da ita,  Amma ina suna zuwa aka ga koh kokon sa yau babu filine shatt ba kome.

Haka suna ji suna gani kamila tayi ta fama da kadangaru, ga watan azumi gashi sun rasa ya zasuyi su dawo da ita jalingo.

Karshe dai  motar akori kura, aka samu aka kora kamila tahau baya, da kadangarun ta mammanne a jikin ta, Aka ja motar sai jalingo.

Sai ayau Harira ta samu dawowa gidan ta,   jikin ta har rawa yake ta shigo gidan, da mamaki ganin mijin ta zaune da yaranta, suna bud’a bakin azumi.

Assalamu Alaikum

Ba tare da ya d’ago ba ya amsa mata,  wa’alaikumu salam.

Rikice wa tayi ta rasa ma me zatayi ta zauna a falon ne, koh ta shiga d’aki, tashi tayi ta shiga d’akin ganin kallon banza da mijin ke mata.

Tana shiga d’akin ya taso ya bita, kee Harira sai yau kika dawo?

Eh sai yau wallahi aka samu aka fitoh da ita.

Yayi kyau karbi wannan,yace yana mika mata takardan dake kan mirrow ta.

Jiki na rawa tace menene wannan baban Amir?

Takandar sakin kine, kije bazan iyya zama dake ba, yanzun ma jira nake ayi sallah aure zanyi.

Saki, aure?

Kwarai ma kuwa na baki nan da awa biyu ki tattara kayan ki kibar mini gida now now…

Don Allah kayi kahuri, baban Amir kayi hakuri na tuba, wallahi bazan sake bin koh mai tofi,  kayi hakuri karka sake ni wallahi bazan iyya koma wa gida a yanzun ba .

Au nan in gidan ubanki ne da bazaki iyya koma wa ba?

Sosai harira tasha mamaki, yau mijin tane ke zagin ubanta, mutumin da koh d’aga ido bayayi ya kalli tsakar idon baban ta tsaban kunyan sa dayake ji.

Koh bazaki fita bane? yace cikin tsawa.

Mikewa tayi ta fara tattara kayan ta, tanayi tana kuka tana dana sanin sanin kamila,  gashe a dalilin neman mata auren wani gata ta kashe auren ta ..

Kamila kam har akayi sallah tana fama da kadangaru, yan unguwan su ba wanda baiji abinda ya faru ba,  wasu suzo gulma wasu suzo musu jaje, mamar ta haukane kawai batayi ba, duk malamin da aka samo abu yaki sam har akayi sallah jiki yaki sauki kadangaru kam basu barta ba.

Ta bangaren muhammad kam, tunda suka sasa a mota sai had’asu da Allah yake, su taimaka su barsa matar sa ba lafiya yanzun ma magani yaje sai mata, sumai hakuri, amma ba wanda ya kulasa, da suka ga surutun sa yayi yawa, gam suka likawa bakinsa.

Shidai yana zaune yanaji sai tafiya ake dashi sosai, kafun yaji motar ta tsaya, d’aya daga cikin sune ya bude masa baki, suka jasa waje aka fitar dashi daga motar, ajesa sukayi a kasa, suka aje masa plate a gaba, 

kai muhammad d’auke abincin gaban kan nan kaci, tafiya ne a gaban mu.

Don Allah kuyi hakuri ku maidani, wallahi matata bata da lafiya na barta koh karyawa batayi ba.

Kai muahmmad banace kaci abincin gaban kaba, koh bakaji bane?

Ai da sauri ya fara cin abincin, jikinsa na bari.

Kasan me mukeso dakai muhammad?

Ah ah sai kun fad’a ya basu amsa abinci cike a  bakin sa, don ya tsorata ainun, tura abinci kawai yake.

An bamu kwangilar kashe ka, Amma mu bazamu iyya kashe ka ba, don shekarun baya mune tsilar makantar ka, wanan karon bazamu iyya d’aukar ranka ba, bakaji ba, baka gani ba, ana buwayan rayuwar ka.

Innalilahi kune daman wa’inda kuka zubamin abu a fuska, na makance?

Ba zuba maka abin bane ya makantar dakai muhammad, tafiya mukai dakai a wancan karon ma.

Toh me nai muku kuma, waya saku?yana maganar yana kuka.

Kai mana shuru,abinda muke so dakai yanzun shine xamu fitar dakai daga NIGERIA,  Bama son ka kara taka kafar ka a wannan kasar, kaje can kayi rayuwar ka, yafi maka Alkhari sama da zaman ka a kasar nan.

Toh don Allah ku bari na d’auki matata da kanwa ta, saimu tafi tare wallahi na muku Alkawari bazamu sake taka nigeria ba.

Kaiiii kana wasa da ranka koh? ana maka gata kana kokarin sa kanka a matsala, an gaya maka koma warka gida yanzun baka bata mana aiki bane, don haka barin kasar nan dakai ya zama dole mundin kana son rayuwa mai tsawo

Don Allah ranka ya d….

Bai bari ya karasa ba yace, rufemin baki wawan banza kawai, kome mata mata  ai akwai mata da yawa a duniya, in sake jin ka am bace Hakuri anan saina sumar dakai nosense.

Shuru muhammad yayi, agun suka kwana washe gari suka kama hanya, wanda shi ba gani yake ba bai san ma ina ake jansa ba.

Lokacin da aka zo tsallaka border da muhammad ana tsallaka nigeria wani irin ihu ya sake yana birgima a cikin motar, ji yake kamar ruwan zafi aka watsa masa, sosai yake salati yana kuka jin jikinsa na tafarfasa. 

Abin mamaki mutanen basu wani damu ba,  kuma abin bai basu mamaki ba, d’aya daga cikin sune ya masa Allauran bacci a take jikin sa ya sake.

Ta bangaren sumayya sai da ta kwana biyu kafun ta dawo hayyacin ta, tunda ta farka sunan muhammad kawai take kira sai kuka,  zaune take akan gadon asibiti An d’aura mata sabon ruwa a hannu, inka ga sumayya saika tausaya mata tsabar rama da tayi, 

Likita ce ta shigo d’akin, sumayya ta kalla ta sake kallon goggo dake zaune a gefe, ga khadija ma zaune tayi tagumi gabaki d’ayan su wujiga wujiga suka koma, abin tausayi.

Sannun ku yamai jikin?

Da sauki likita, goggo ta Amsa mata.

Masha Allah, sumayya kam tana da mijine?

Eh likita tana da miji.

Ok koh zan iyya ganinsa?

Kuka sumayya ta sake mai tsanani, tana dafa kirjinta jin zafin da yake mata.

Subhanallah sumayya ki kula da lafiyar kifa, kina kokarin d’aurawa kanki wani ciwon kuma akan wanda kike dashi.

Dole nayi kuka Dr mijina aka sace shikaran jiya da safe.

Amma kun kai report wajen yan sanda kuwa?

Ah ah waye muke dashi, da zai kai mana report, yan sandan ma in kaje sai sun nemi wani abu agun ka, mu ina muka ga abinda zamu basu.

Duk da haka gwara kukai report yafi, sannan ina son kuban waje zanyi magana da sumayya?

Ba kome likita, goggo tace tana fita, khadija ma tashi tayi tabi goggo har lokacin bata daina kuka ba inta tuna yayan ta.

Sumayya hawan jini kika samu ya kamata, ki nutsu kisa tawakkali a ranki kiyi hakuri insha Allah mijin ki zai dawo.

Dole nayi kuka Dr mijina shine kad’ai farin cikina daya saura mini, sannan a waye gari ban gansa ba dole na shiga damuwa.

Kiyi hakuri, sannan ya kamata kima mahaifiyar ki magana ta ringa xuwa miki da ruwan zafi, kina zama a ciki saboda yanayin jikin ki kinji Allah ya sauwaka.

Ameeen nagode likita, sumayya tace tana kallon likitar bazata wuce sa’arta ba koh ta bata yan tsiraran shekaru.

Ta bangaren muhammad Sai da sukayi sati suna tafiya a motar, kafun suka iso kasar da suka shirya kaisa.

Suna shiga kasar da suka yanke zasu aje sa, d’aya daga cikinsu ne ya kalli ogansa, oga anya wannan yaron, bazaice zai dawo kasa ba kuwa, ka sansa akwai fahimta ni inso samune mai zai hana a masa yanda zai manta da kome,  na d’an wani lokaci.

Bazai yuba hakkin yaron nan ya mana yawa,  mu barsa haka wannan karon bazan sake cutar da yaron nan ba.

Shikenan oga amma naga hakan ma,  taimakon sa muke son yi, don mun masa hakan ba kome bane.

Gaskiya ne oga, d’aya daga cikin su yace

Kai ban Amince ba ku aje yaron nan mubar kasar nan, kar a kamamu jirgi ma zamu bi,  bada mota zamu koma kamar zuwa ba.

Haka suka aje muhammad suka kara gaba.

Kamar Awa d’aya da tafiyar su muhammad ya farka, A hankali ya motsa hannunsa sai kuma ya fara kokarin bude idanusa a hankali, ya bude su yana kallon sararin samaniya, ai da sauri ya mike zaune, mafarki yake koh gaske jikin sa har rawa yake yasa hannu ya murza idon sa da kyau don kara tabbatar wa kansa abinda yake gani, gaskiya ne koh A  mafarki yake…….

Mafarki yake koh gaske, da idanun sa yake kallon duniya, wanda rabon sa daya gani yanzun ana neman shekara 13, Allahu Akbar Tsarki ya tabbata ga Allah, Alhamdulilah Alhamdulilah, shine abinda yake maimaitawa

Mikewa yayi da sauri yana bin koh ida da kallo, kamar wani dolo, shi ganin abin yake kamar mafarki ne, an jima zaici gaba da ganin duhu,sai bin wajen yake kamar daji, haka ya ringa takawa a hankali yana tafiya cike da Al’ajabin abinda ke faruwa yau dashi,  shine da kallo?

Hango gonaki yayi a shimfide, gwanin sha’awa na kayan labbu, ga kogi babba yana gudana da gudu yayi saitin kogin da saurinsa ya shiga ruwan, don wallahi azababben kishi yake ji, ai yana shiga kogin ya tsoma hannun sa cikin ruwan ya iba yasha, ya sake tsoma wa ya iba yasha, kamar wasa yaji ruwa yana jansa daga bakin gaba, har tsakiya sai kokari yake ya fitoh amma ina abin yaci tura, salati ya fara yana innalilahi, wasa wasa ruwa ya fara nitsar dashi sai kokowa yake da ruwan, duk  kokarin sa na fita, abu ya gagara, daman shi ba ruwa ya iyya ba, ina makaho ina rafi, koh lokacin tasowar sa baiyi yayin bin yara kogi ba.

Sosai ruwa ya hadiye sa har wuya, sai kokari yake Amma ruwan yafi karfinsa, zuwa wani lokaci, shuuuuuuuu yaji ya burme cikin ruwa,  da sauri yayi tsalle yafitar da kansa, sai kuma yaji ya sake komawa, kamar wasa Al’ameen ya fara shan ruwa, sannu sannu har yaji ruwan yaci karfinsa, tun yana gani dishi dishi har yaji bayanan , 

Gid’ado ne tsaye da shanun sa, daya koro bakin gaba susha ruwa, kamar wasa yaga shanukan sa, na kuka a bakin gaba, Alamu dai wani abin suka gani.

Da sauri ya karaso wajen don yayi tunanin kada ne, koh wani mugun abu, tsayawa yayi turus yana bin abinda yake gani shida dabbobin sa, mutum ne, kwance baya motse kamar gawa, da sauri ya kad’a shanunsa har ya juya zai tafi don gudu rigima, daman ba shiri suke da manoma ba kar ace shiya kashesa, ya shiga uku.

Sai kuma ya sake dawowa, haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta da tafiya yabar gawan ba, nade kafar fantalelen wandon sa, na kiwo yayi ya shiga ruwan, jawo Al’ameen yayi, kiiiiiiiiii ya fitar dashi a ruwan, ajesa yayi a kan tabon bakin kogi. 

Kurawa fuskar Al’ameen ido gid’ado yayi tabbas wannan ba kabila bane, duk da fuskar tayi irin na fulani,Amma ba fulani husul  bane, kyaun sanan akwai mix,ganin Hakan yasaka sa ciccibar Al’ameen, ya d’aura a bayan wuyansa yayi Rugan su dashi.

Tun daga mahadin rugan su ake binsa da kallo, ganinsa d’auke da gawa a wuya, kowa ya tare sa, cemai yake shima a ruwa ya gansa, sosai wasu ke zagin sa meye na kawo musu gawa salon ya jaza musu bala’i,  Amma shi sam bai damu ba tafiyar sa kawai yake.

Isarsa gida ya tarar da mahaifinsa zaune a gindin bishiyar tsada a tsakar gidan su, sai innar sa dake gindin murhu tana girki. 

Assalamu Alaikum

Waalaikum…….sai kuma ta dakata, bata ma karasa amsa sallamar ba, hadde yan boni, gid’ado dun dume, miyiyata do ha bahoma?(me nake ganin nan a bayan ka)

Shuru yayi yana kallon ta, ganin yanda gabaki d’aya tabi ta gigice, bappan sa dake zaune a gindin bishiya ne, yayi saurin tasowa jin abinda inna kece wa.

Gid’ado d’obo?bappan sa ya tambaya, yana nuna Al’ameen dake kafadar gidado. 

Bappa, kuyi hakuri bara na sauke sa sai in muku bayani, duk cikin fulanci suke maganar.

Wani irin mu kwantar da hankali?kawai ka ciccibo mutum baya motse a kafad’ar ka, ka shigo mana ruga akan me?

Don Allah inna a wad’a muyal, nima ganin sa nayi a bakin gaba, alamu dai ruwane ya jasa,  koh aka yardashi, gidado yace yana kallon matarsa data fitoh daga d’aki, d’auke da tsohon ciki tana nufosu.

Kwantar dashi gid’ado, in yaso koh sallah Amasa tunda naga kamar musulmi ne, bappa yace.

Sauke sa gidado yayi, sosai bappa ya kurawa fuskar muhammad ido, yana nazari sai kuma ya d’aga ido yakalli gidado, Ai ohmayai(ai bai mutu ba)suma yayi.

Da sauri gidado ya kara maimaitawa suma bappa?

eh, yi sauri ka d’auko mini kwaryar magani a bukka, yana maganar yana dukawa kusa da muhammad, danne masa ciki ya farayi, take ruwa ya fara fita, ta bakin sa duk da baiyi motse ba, amma dai ruwan na fita sosai,  bappa ya mammatse masa ciki.

Matar gidado kam kujera ta samu ta zauna a hankali daker, sai ga gid’ado ya fitoh bukan bappa, da sauri ya ajewa bappa magani a gefe, bappa da lenki mai.

Maganin bappa ya d’auka a kwarya, yana shashafa ma Al’ameen a fuska, da wuya yana masa Tofi,yana gamawa ya d’aga ido ya kalli gidado, husumo ayara ha sudu(ka daukesa ka kaisa d’aki)

Wai bappan gidado ban gane a d’auke sa akai sa d’aki ba, yadaga ganin mutum bamusan daga ina ba, mugune koh nagari?kawai mu d’auko mu aje a cikin gidan mu, ni gaskiya ban yarda ba.

Talatu kena bani mamaki wallahi, yanzun ace mutun baya cikin hayyacin sa, ina kikeso mu kaisa?

Koma ina a kaisa, amma dai gaskiya banda cikin gidan nan, taima ma mugune.

Koh mugune, mu Allah zai dubi zuciyar mu, insha allah bazai basa ikon cutar damu ba,  bare ma wannan yaro baiyi kama da mugu ba,  daga ka gansa kasan akwai jinin fulani a jikin sa.

Lantana matar gidado kam, mikewa tayi ta shiga d’aki ganin fad’an bappa da inna baya karewa in gari ya waye .

Kai gidado d’auke sa ka kaisa d’akin kusa da gindin murhu.

Toh bappa, yace yana ciccibar sa yakai d’aki,  shanu kansa dake binsa a baya tunda ya d’auko Al’ameen har gida, suya kama ya d’ad’aure a turke…….

**************************

Ta bangaren sumayya yau satin ta d’aya a Hospital, har da kwana d’aya, Amma jikin dai za’ace Alhamdulilah, da sauki kad’an duk da baiyi kwari ba, sosai likitoti ke kula da ita,  hatta Dr tana iyya bakin kokarin ta, ganin sumayya ta samu lafiya, Amma taki kwantar da hankalin ta sam.

Khadija ma yau sati guda, rabon ta da makaranta,suna faman jinyan sumayya,  Goggo ke zama a asibiti, ita kuma ke musu girki a gida ta kawo musu, duk da sumayya baci take ba, sai yan aikace aikacen gida duk ita keyi.

Kamar yau ma, khadija ce ta kammala girki a kofar sumayya, zuzzubawa tayi a kula, tasa a kwando ga flask a hannun ta, ta fitoh gidan Adara, tsallaka titi tayi ta nufi shagon yayan ta, shagari ta samu zaune yayi tagumi gabaki d’aya yaron ya shiga damuwa ainu na b’atan Al’ameen, duk da shike kula da shagon yanzun, amma sai yanajin shagon kwata kwata baya masa dadi.

Assalamu alaikum.

Wa’alaikumu salam, khadija zaki wuce hospital in kenan harkin shirya?

Eh na gama girki.

Ok yace yana mikewa, laida ya d’auko ya zuzzuba ayaba da kankana mai yawa, ya  rufe shagon, kwandon hanun khadija ya kamar ba, ya bar mata flask in yana rike da laidan kayan marmarin a d’aya hannun, suka kama hanyar  FMC da kafa, don shagari duk da muhammad baya nan, amma baya masa Almubazza ranci da kudi, asalima tattalin sa na yanzun yafi nada, hatta kudin asibiti duk Abinda aka bukata shiyake biya, ya hana sumayya kashe koh sisi.

Sunzo sharan kwanan doruwa, kawai suka ga anyi packing moter a gabansu, khadija kam koh duban motar batayi ba, kokarin kaucewa take ta gefe, ta wuce abinta, dayake shagari bai wani waye Ammar ba, yasa bai ma saurare saba yabi bayan khadija.

Ke yar kauye, mai tafiya bata kallon gaban ta.

Da sauri khadija ta d’ago jin muryar Ammar,ina kwana?tace.

Kin Amsawa yayi ya dubeta, ina zaku kuma da abinci haka.

Asibiti, ta basa Amsa.

Waye ba lafiya?

Aunty sumayya .

Subhanallah, yayan naki nacan ne?nima yau na dawo da asuba, shine nace bara na biyo gunsa.

Shuru khadija tayi bata basa Amsa ba, sai kaucewa da tayi taci gaba da tafiya.

Da sauri ya fitoh a motar, yabi bayan ta, keee ba magana nake miki bane?kina tafiya?

Kala batace ba, tana ta tafiyar ta.

Hannun ta Ammar ya rike, da sauri ta juyo tana kallon sa, sakemin hannu?

Naki na saken, ina miki magana kina manna mini hauka, ina wasa dake?

Kuka khadija ta sake masa da karfi, ai da sauri Ammar ya sake mata hannu, ya juya yana kallon shagari, dake tsaye yana kallon su, fuskar sa A hade, haka kawai yaji ya tsani Ammar, ganin yanda ya wani rikewa khadija hannu.

Kai meke faruwa ne?Ammar ya tambaye sa.

Fuska a hade yace, An sace oga ne shiyasa daka mata maganar, ina yayan ta,  take kuka.

Sai a lokacin Ammar ya gane shagari, watoh shine wanda muhammad yace zai d’auko su zauna a shago, abu na biyu daya basa mamaki kuma wai an sace muhammad, sai kace kaza, ban gane an sace saba?

Eh an sace sa, haka kawai wasu a mota sukazo suka d’auke sa, a bakin titi

Tsabar razana har tuntube yayi, yau kwana nawa kenan?

Sati d’aya.

Amma har sati d’aya, police basu d’auki wani kakkauran mataki ba?mutum ya bata kamar wani kaza koh d’uriyan sa babu?

Koh report bamu shigar ba, Shagari ya basa Amsa.

What?? ba’a kai kara ba, akan me?

Sumayya na asibiti, ni kuma tsoro nake ji,  shiyasa ba wanda yakai.

Amma ai koh baku kaiba, nasan labari zaije wa yan sanda, tunda kuna kusa da station, yaci su subibiye Lamarin.

Shuru suka, masa.

Ku shiga muje asibitin, yace yana karban flask in da khadija ta dongorar,  yasa a mota.

Shagari ma shiga yayi ya zauna a gaba, har lokaci tana tsungune a kasa, hannu kawai Ammar yasa ya fizgota, ya jefa a bayan motar, ya zagaya driver sit ya zauna, yaja motar suka nufi Hospital.

Suna shiga hospital in, dashi da shagari ne suka d’auko kula da flask, harda laidan,  khadija kam an kaikaya mata inda yake mata kaikayi, kuka har lokacin yinsa take, duk yanda shagari keta bata baki tayi shuru,  amma ina. 

Keeee wallahi in na sake jin koh tarinki, a asibitin nan saina saba miki, banason shirme tun d’azun, sai cika min kunne kike nayi shuru,  yanzun mun shigo asibitin ma bazaki rufe bakin bane? saikin tara mana jama’a.

Shuru khadija tayi, harga Allah wannan Ammar in kamar mai Aljanu haka yake, zafi zafi sanyi sanyi.

Shagari kam gaba ya kara, dayake yasan d’akin da sumayya take, bai saurare tahowar suba, yayi tafiyar sa,  yana maijin haushi a ransa.

Shiya fara shigowa d’akin, da sallama.

Amsa masa sumayya tayi, wance ke zaune daga ita sai dogon rigan kanti, kanta koh d’ankwali babu, tana zaune a bakin gadon, rike da wayarta, hawaye nabin kumatun ta.

Ina wuni Aunty,  ya jiki?

Kai kawai ta d’aga masa, ta mika hannu ta d’auki d’an kwalinta, dake gefen gadon ta yafa a kanta.

Zama shagari yayi yana bin d’akin da kallo,  ganin baiga goggo ba.

Assalamu alaikum, Ammar ne yayi sallama a bakin kofar d’akin.

Amsa masa shagari yayi, ba tare da ya d’ago yaga bakin kofar ba.

itama sumayya bata d’ago ba, sanin wake sallamar, don ta shaida mai muryar.

Shigowa Ammar yayi, idanun sa ya sauka akan sumaya, dake zaune gabaki d’aya ta chanja, ta rame sosai sai haske data kara a yan kwanakin nan, har yayi yawa,tayi fari kamar ka tabata jini ya fitoh.

A hankali ya tako har inda take, hannu yasa ya amshe wayar, sai a lokacin sumayya ta d’ago ta dube sa, hade da mika masa hannu,  Alamun ya bata wayar ta.

Matsawa yayi gefe, ya kurawa screen in wayar ta ido, hoton tane da suka d’auka, ita da muhammad ranan sallah a gidan su.

Sumayya ya kamata kima kanki fad’a, wannan abinda kike kara cutar dakan ki kike,  kuka bashi ne magani ba, koh mafita, kin zauna kina kuka, gaki ba lafiya bane dake, ki dubi yanda kika koma fisabililahi.

Gaya mata kam D’an nan, haka nake fama da ita, bansan me take gani a wayar nan ba, ta tura khadija ta d’auko mata, shikenan tamai dashi madubi, tana kallo tana kuka, goggo data fitoh a toilet na d’akin ne take maganar.

Hoton mijin tane a ciki mama, Ammar yace yana latsa wayar sumayya, dake hannun sa.

Au shiyasa take kuka?/lalle sumayya baki jiran kanki, kiga yanda kika zama gabaki d’aya kin koma, kashi da rai sai haske da kike tayi kamar mai ciwon far d’aya.

Kyaleta mama,  hotunan duka zan goge.

Kuka sumayya ta sake, jin abinda Ammar yace wai zai goge hoton muhammad a wayar ta”ka bani wayata karka goge na rokeka don Allah”

Ah ah bafa zan baki ba, in gaya miki,  tunda zaki tasa wayar a gaba kina kallo kina kuka.

“Allah nayi Alkawari zan daina” tana magana tana kuka

Toh yanzun me kike in ba kukar ba?

Don Allah ka bata wayar ta, sai kuka take tana maka magiya, kana wani ja mata rai, khadija ce tayi maganar cikin jin haushi ganin iyayin da yake ma Auntin ta.

Wani kallo Ammar ya watsa mata, jin maganar da take masa kamar sa’arta.

Bata sake magana ba, aje abincin tayi tana kallon sumayya, in zuba miki Aunty?

“Ah ah banaci”

Wani irin bakici?sumayya yau kwanan mu tara a asibiti, abinci kirki baki ciba ya za’ayi kiyi lafiya.

Shuru sumayya tayi, ta koma ta kwanta bata kara magana ba, don ta fahimci bazasu gane abinda ke damun ta ba.

Ammar kam kallon khadija yayi ya sake kallon, Goggo,meke damunta , sukace mama?

Damuwa ce d’an nan, hawan jinine ya kamata, maimakon ta nutsu ta samu lafiya, Amma ina sai kara kwantar dakan ta take A gado.

Allah ya bata lafiya,  in ba damuwa mama,  ina so zan fara bincike akan case in batar Al’ameen, in muna bukatar cikekken bayani zan tuntube ku.

Ba kome yaro mun gode, Allah ya saka sai dai ban gane kaba?

Abokin muhammad ne.

Au koh dai kaine Ammar, da yake sanar dani ka bude masa shago?ai munga abin Arziki Allah ya biya ka.

Ameeen mama.

Sai a lokacin shagari da khadija, suka san Ammar ne ya bude ma Al’ameen shago.

Fita Ammar yayi bai bawa sumayya wayar taba, ita ma bata sake magana ba.

Ta bangaren Al’ameen kam har dare bai dawo hayyacin sa ba, gidado yayi ta zuwa dubasa yafi a kirga Amma shuru.

 sai da gari ya waye, ya farka jujjuyawa yayi sai kuma ya bude idanun sa,  da sauri ya koma baya da mamaki, ganin yarinya budurwa zaune a gaban sa kyakky……………..πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€πŸ€

Back to top button