Zakuna Biyar Page 8 By Princess Teema
Sun jima a wajen suna zaune, magana kuwa sai su fi mintina 20 babu wanda ya ce ƙala, can su ɗan yi hira, su sake yin shiru. A haka suka shari awanni uku a wajen, kafin Champion ya miƙe tsaye, dik in da kuke neman dakakkun jaruman maza waɗan nan sun kai, tsananin hora kansu suke yi fiye da yadda ake hora sojoji, dik saboda kwarewarsu, su basa yi wa ƙananan ƙungiyoyin ƴan ta’adda aiki, basu ma karɓar aiki a garaje, sai an yi saa, kuma wani lokaci fa har gwamnati suke yi wa aiki ba tare da gwamnatin tasan su ne IRON FIST ba.Akwai wani lokaci da wani daga cikin gwamna a Avaris ya nemi taimakonsu through wani abokinsa, ya basu kwangilar kashe wani sarki, a wannan ɓangare and sansu ne da fuskan ƴan Korea, dan abokin nasa ma ce mashi ya yi akwai wasu ƴan Korea manyan terrorists zasu yi wannan aiki. Mutun ɗaya ne daga cikinsu ya shiga Avaris ya kashe wannan sarki kuma ya fita ya dawo, tamkar wasu aljanu, dan haka fuskokinsu a duniya yana da yawa matuƙa! Su kaɗai suka san ainahin kamanninsu sai kuma alƙalamina!.Miƙewa ɗayan ma ya yi, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya buɗe curtains dake wajen ya shige. Shi kuma Campaion in da Seraph take ya kariso, yana zuwa yasa hannu ɗaya ya damki wuyan rigarta. Sama ya ɗagata sai kan shoulder ɗinsa. Ya nufi waje da ita. Hero zai biyosa ya nuna mashi hanya ya bi ɗayan guy ɗin, dan yasa idan ya biyota za’a samu matsala in ta farka.Kai tsaye room ɗinta ya nufa. Yana tura door ɗin ya tsaya kaman wani gumki, a cikin duhu ya hau jujjuya ash eyes ɗinsa da bani da tabbacin kwayar idanun gaskiya ce, dan na faɗa maku a baya komai nasu na boge ne!.Takawa ya yi a natse ya isa gaban light control dake manne kusa da bed, wajen da low light. Wutar ɗakin ya kunna, gabaɗaya haske ya gauraye ko’ina, a saman bed ya jefa Seraph tare da nufar toilet ɗinta. Jim kaɗan ya dawo hannunsa ɗauke da bowl, a gaban bed ɗin ya tsaya. A maimakon ya shafa mata ruwan a natse, sai ya kwarara mata shi a kan fuska!.A firgice ta tashi tana kiran sunan Mammy ɗinta. Yana ganin haka ya juya ya nufi toilet, bai yi mata magana ba bai kuma sake kallon in da take ba. Jim kaɗan ya fito, zai nufi waje ta diro ƙasa da gudu, a gabansa ta tsaya tare da riko hannunsa dake cikin terrorist hand gloves, muryanta na rawa, jikinta na kerma sosai saboda tsoronsa, dan dole kowa ya tsorata da ganinsu, bama kaga face ɗinsu complete ba, sai dara-daran idanu jajir, dik yadda aka yi suna shan wasu kwayoyi!. “Uncle, please take me to my mammy, I am scared of this house”…… Tana gama faɗar haka ta fashe da kuka gwanin ban tausayi. Kwace hannunsa ya yi ba tare da ya yi magana ba, ya raɓa gefenta zai wuce abinsa. Da sauri ta sake binsa, ta rikesa tana rokon ya kaita wajen Mammy ɗinta. Sau biyu yana kwace kansa tana sake rikesa, a na uku kam sai ya damko wuyanta da karfi, ya zazzare jajaye idanunsa a kan face ɗinta. Da muryansa da ba zaka iya gane wace iriya bace saboda nose mask ya ce. “Your mother is dead. Calm down, we don’t want nonsense here!!”. Yana faɗar haka ya ɗagata da wuyar da ya shake mata ɗin ya jefa saman gado daga in da yake tsaye…… Mutanen da kan iya harbin mutum a cikin jirgin kasa mai tsananin gudu ai saiti a kansu kuma ba’a magana.Yana jifa da ita bai sake kallon in da take ba ya yi wucewansa abinsa. Ji ta yi duniya ya tsaya mata cak, wai Mammynta ta mutu, sai ta ji kamar almara, shiru ta yi tana jin kanta a saman iska haka. Nan kuma ta fara tunano abubuwan da suka faru a gidansu, sai yanzu komai ya dawo cikin kanta, lokaci guda wasu zafafan hawaye suka fara wanke mata fuska, da gudu ta diro kasan bed ɗin, dan yanzu ta tuna komai.Bayansa ta bi ta fito waje. Babu kowa a parlon, ta manta da zaki a gidan, yau ko kasheta zai yi sai ya faɗa mata me dalilinsa na zuwa gidansu har ya ja aka kashe nata mammynta? Dan a yanzu tana ɗauka FT ne wannan. Shiga da fita ta fara yi a ɗakunan da ta gani kawai, dik in da zata shiga bata ganin kowa a ciki, daga karshe ta isa wajen staircase ɗan siririn nan, tana goge kwallah tana jan hanci. Ya manta bai naɗe staircase ɗin ba. Haurawa sama ta yi, a nan ta ga ashe wata duniya ce guda a saman.Ɗakin da ta fara cin karo da shi a parlon saman ta shiga. Nan ta ga uban computers da ba zata iya kirgasu ba, dik kuma suna kukkunne, kayayyakin aikinsu ne cike a ciki. Zazzare voilet eyes ɗinta a kan komai dake ciki ta fara yi, tana rarrabe idanunta. Can ta tsayar a kan wall na ɗakin dake gefe, hotuna ne kala-kala a cike a bangon. Tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki haka ta nufi wajen.A gaban hotunan ta tsaya tana kare masu kallo, wasu hotunan an sanya jar mark a kansu, da alama an kashe mutanen kenan. Can idanunta ya tsaya a kan wani hoto wanda aka sanyawa jar mark shi ma! Da sauri ta miƙa hannu zata ciri hoto sai kuma ta gagara. A fili ta ce. “For sure my mammy tana da irin wannan hoto! Tabbas tana da hoton mutumin nan! Waye shi? Meyasa hotonsa yake gidanmu kuma yake nan da jar mark? Kenan an kashesa?”. Tana neman waɗan nan amsoshi tin bata samu ba idanunta suka sauƙa a kan hoton mammy ɗinta cikin kayan aikinta, shi ma hoton an zana jar mark a jiki alamar ta mutu kenan! Babbar magana! Kenan dama su ne suka shirya kasheta ko ya ake ciki ne?. Nasan izuwa yanzu jama’a kanku ta kulle, ni ma dai kaina ya kulle, me alaƙarsu da Dr? Me alaƙa hoton wannan mutumi da Seraph ta gani yanzu da Mammy ɗinta? Dik yadda aka yi Dr tasan FT ko kuma shi ya santa, in ba haka ba ya aka yi yasan ita likita ce har ya je ta cecesa?.Kai mu ɗan ji labarin Dr ko da kaɗan ne, kila zamu ɗan samu wani haske.Dr ta jima tana rayuwa a wannan unguwa tare da abokan zamanta watau maƙotanta, daga ita sai ƴarta a gidansu, dik wanda ya san Dr zai ce maku ita kaɗai ya sani bata da mij ko dangii, ta reni Seraph cike da kulawa, tsantsar so da kuma kauna. Ita ke kaita school ta ɗaukota, ita take mata komai, ko wajen aiki idan zata je tare da ita take tafiya in ba school, bata yarda ta barwa kowa yarta ba.Seraph yarinya ce mai natsuwa da kwazo, ta taso cikin shaukin son shuke-suken furanni da kiwon tsuntsaye game da ƙananan kifaye a cikin ruwa. Shiyasa gidansu yake cike da shuke-shuken flowers masu ƙayatarwa, a gefe guda Dr tai mata katon glass tana kiwon ƙananan kifaye, ga tsuntsayenta a gefe suma tana kiwo. Yarinyar akwai son wasa da ruwa, dan tsab zata shige cikin ruwan kifi suna wasa tare, bata da hayaniya kuma bata zama kusa da hayaniya.One thing Dr ba musulma ba ce! Amma ba zaka taɓa gane hakan ba sai in faɗa maka aka yi, ta yi rayuwarta ne a tsakiyan musulmai, musulman ma ƴan Nigeria masu shegen shiga rai da iya mu’amala da mutane, shiyasa babu wani abu da musulmi zai yi wanda bata iya ba, harta Alqur’ani mai girma zata iya karanta kusan rabi, addu’oin musulmai kam babu wanda bata iya ba, kuma abin mamaki dik in ta shiga damuwa addu’ar musulmmai take karantawa, sai dai ALLAH bai nufeta da karɓar shahada ba har ta koma garesa. Haka Seraph ta taso ba musulma ba, yarinyar ta taso bata san waye mahaifinta ba, kuma bata taɓa tambayar mahaifiyarta ina daddynta ba, bata damuwa da son sanin ina yake tin da mahaifiyarta tana ɗauke mata dik wata damuwa, ta cika rayuwarta da ƙauna da kulawa. A haka suke rayuwarsu a wannan gida, Dr tana aiki ta rikesu da albashinta, ta shagwaɓa Seraph sosai. A takaice yadda suka rayu kenan, ainahin su waye su zai zo a gaba!…… My people na fara wani tinani! Ina daddyn Seraph? Meyasa kowa bai san shi ba? Dik daɗewar da ka yi da sanin Dr ba zaka taɓa sanin ina mahaifin yarinyar yake ba, wasu ma a gabansu Dr ta haifi yarinyar amma basu taɓa ganin ubant ba, sai suka ɗauka cikin shige ne kawai, kun san su ba wata matsala bace dan ka haifi ɗan shege, shi ne basu damu ba, amma wani lokaci suna tambayar kansu ya aka yi Dr take da kuɗi sosai fiye da kowa a unguwar? Albashinta bai yi kaɗan ya riketa ba kuwa?. To na fara wani tunani, anya kuwa FT ba shi ne mahaifin Seraph ba kuwa? Ku duba labarin da kyau! Ba’a taɓa ganin mahaifinta ba! Kila sai tsakan dare yake zuwa wajen Dr ko? Kuma ya ceci Seraph, sannan ya ce ayi mata komai da take so amma kada a bari ta sake kallonsa a duniya! Ku tina ya shiga gidan Dr kai tsaye, ya nuna mata sama kaman yasan nan ne ɗakin duba majinyatarta yake, ya fito da Seraph ta view, waye ya faɗa mashi akwai hanya ta wajen idan ba ya yi wa gidan farin sani ba?! A lokacin da ya je gidan ya nunawa Dr bindiga, ko kaɗan bata ji tsoron bindigar ba, hakan na nufin tasan bindiga sosai har bata tsoronsa! Wacece ita?! Kai ni ma da kaina kaina ya kulle, wannan hasashena ne na yi, kowa yana da damar yin nasa, alkalamina kawai shi yasan gaskiyar wannan sarkakiya!.To a takaice kun ji labarin Seraph, mu je kan labarinmu………. Ta jima sosai a tsaye a wajen tana karewa hotunan kallon ba tare da tasan kowa a ciki ba face hoton mamanta da wannan mutumi, can ta ga hoton wani dattijo a waje. Zazzaro voilet eyes ɗinta a kan hoton da kyau ta yi, lokaci guda ta ɗan ja baya, shiru ta yi tana ƙoƙarin tunano a ina tasan wannan mutumi?.Daga bayanta ta ji alamar motsi tamkar ana zuwa, hakan yasa ta bazama da gudu ta nemo wajen ɓuya, bata son su ganta. A bayan wasu drawers na tarin documents ta ɓuya, tana leƙosu a gefe. Champion and Scorpion ne suka shigo. A tsakiyar ɗakin suka tsaya, lokaci guda suka fara rarraba jajayen idanunsu a ɗakin, can ƙasa Champion ya ce. “Akwai wanda ya shigo room ɗin nan”. Da turanci ya yi magana, hakan yasa Seraph yin gaggawar sanya hannu ta toshe ɗan bakinta tana mamakin yadda aka yi suka gane an shigo masu!. Wucewa gaba Scorpion ya yi yana amsawa da. “I think so”. A gaban wata computer ya tsaya tare da cewa. “Maybe wancan yarinyar ce, the reason why na ce zamanta a nan zai haifar mana da matsala kenan! Let Lion back zai ɗauketa ne gaskiya ya kaita wani wajen ko boarding school”. Karisowa gaban nasa desktop computer Champion ya yi, suka shiga aikin da suka saba ba tare da ya sake yin magana ba, tamkar kurame a waje haka suke gudanar da rayuwansu, abin ma gwanin ban mamaki. Seraph na kallonsu suna ta fiffito da hotunan mutane a cikin computer suna sanya masu jar mark, wasu green, da alama list ɗin waɗan da zasu baƙunci lahira ake yi, aiki suke yi da jini a jika, kuma cikin zafa. Ai baki ta saki tana kallon Ikon God. Bata ankara ba sai gani ta yi sun miƙe kusan a tare alamar sun gama abin da suke yi, suka nufi fita, Champion ne ya datse door ɗin har da key ta waje, wai dan kada ta sake shigo masu ɗaki, bai san da ita ma a ciki ya gargame ba. Suna fita ta fito ta nufi kofa da gudu, sai kuma me? Ji ta yi a rufe, hankalinta ne ya yi mummunar tashi, ta hau buga kofar da karfi, sai dai ina, soundproof ce door ɗin, harta bangon ɗakin, in dai mutum yana ta waje ba zai taɓa jin abin da na ciki yake faɗe ba, ko da zai yi ta ihu ne.Dan haka ta yi iya bugawarta babu wanda ya iya jiyota, ga shi babu iska a ɗakin, dan ko view babu, in dai ka haura 30 mins a ɗakin to fa sai dai wani ba kai ba, su kansu da iskan Oxygen suke amfani idan suka shigo, in zasu fita su kasehsa, ita kuma bata san in da yake bama bare har ta kunna ta shaki numfashi. Zama ta yi a jikin kofar tana kuka hawaye sharɓe-sharɓe, dan karfin iskar da suka sake wa kansu bai gama tafiya ba, tana ɗan shaƙar numfashi kafin ya gama tafiya ta gane ALLAH da girma yake. ————————-🔥AZURE BARRACK.Washegari, yau takama ranar talata kenan. Yau su Arya basu da class sai practical, dan haka ba uniform za su yi using ba. Tin karfe bakwai suka shirya. Kamar kullum kun sani dressing ɗinsu iri ɗaya ne, white mini sket suka sanya zuwa ƙasan hips wajen saman gwiwa kenan, daga sama kuma blue top ce, sun tara gashin kansu sun ɗaure kashi biyu da blue rebon, sun gyara na gaban goshin nan nasu ya yi matuƙar kyau, sai tashin kamshin product na STARS LADIES LUSH suke yi, kafafunsu sanye da gladiator sandals masu shegen kyau wanda ya ƙara masu kyau matuƙa, sun ɗaura igiyar sandals ɗin har wajen gwiwa.Note, su Arya fa ba musulmai bane kuma ba kiristoci bane! Basu da addini, GAT bai yarda da kowani addini ba, dan haka su a haka suke rayuwansu, kome zasu yi lafiya lou ne, ku daina kallon rayuwansu kamar mu musulmai, ko cikakkun musulmai na ketare ma ya aka kare da su bare kuma waɗan da bama su da addinin!. A parlo suka isko daddynsu ya kamala shirinsa tsab yana jiransu. Angelina ta sanya ƙatuwar bluetooth a kunne tana jin sauti tana ɗan kaɗa kai, while ita ma V sautin soyayya da kalamai masu shegen daɗi a waƙa take ji, amma ita karamar bluetooth ta sanya.Breakfast suka yi cike da kaunar juna, daddy ya kama hannun V yana faɗin su je ya kaisu school. A shagwaɓe ta ce. “Daddy idan mun dawo daga school zan zo office ɗinka”……. Da sauri Arya ta amsa da. “Babu in da zaki je”. Ta faɗa tana harararta. Angelina ce ta sake cewa. “Sai son yawo, babu in da zaki je”. Mamaki ne ya kama GAT ganin cewa basu taɓa hana junansu zuwa office ɗinsa ba, ai suna zuwa time to time, to meyasa yau suke hana juna?. Angelina da Arya sun san cewa V zata je ganin Leo ne, shiyasa suka yi saurin dakatar da ita ba tare da sun dalilinsu na yin hakan ba, gara ma Arya ace basa shi ne,bita Angelie kuma fa?! Ita dai Manassa ko a jikinta. Kallon V daddy ya yi, suna nufar wajen mota ya ce. “Kin gaji da zaman gida ne?”. Kai ta gyaɗa mashi alamar e. “Okey sai kin zo”. Ya faɗa yana shafa kanta…….. A cikin zuciyarta Arya ta kuduri aniyar ba zata barta ta je ba, a cewarta ba zata barsu su yi soyayya ba dan kada su ja masu raini wajen maza!. Suna fitowa waje wasu jiga-jigan sojoji su huɗu da gudu suka nufosu, a gaban GAT suka tsaya tare da sara mashi, sun wani kame tamkar basa numfashi. Kai kawai ya jinjina masu, cikin zafin nama suka ɓalle masu door na motor, ciki ya shiga rike da hannu V, ya ɗaurata a saman laps ɗinsa, a front seat ya zauna, su Arya suka shiga gidan baya, da alama GAT ya fi kaunar V fiye da sauran yaran nasa.Wani katon soja madaka karti ne ya shiga driving seat. Ba tare da ɓata lokacin ba ya ja motar da gudun gaske suka nufi gate. Suna fitowa wasu comboi na motocin sojoji su uku, da wasu jip suka take masu baya, suka sanya motar GAT a tsakiya, take jiniya ta tashi tamkar zasu tafi filin yaki ne. Kai tsaye school nasu Arya suka nufa, sai hira suke yi wa daddyn nasu, watau idan da shi ne suna sakewa su yi hira sosai, idan ba da shi ba zaku ɗauka kurame ne.Har cikin school suka kaisu, cike da kauna suka yi sallama, dik sai da suka leƙo gabar motar suka bashi sumbata kafin su wuce, tsayawa ya yi yana kallonsu har suka shiga cikin class nasu su ukun, ita kuma Manassa ta wuce nasu sashen, sannan ne ya umarci a juya kan mota. Dik wanda yake tare da GAT a boys ɗin nan nasa sun san yana tsananin kaunar ƴaƴansa tamkar ransa!.Office ya wuce daga nan, dan yau suna da zaman meeting a kan tsaro, sati ya zagayo!. ———————🔥Jiki dik tsamin training daren jiya, haka suka tashi, suka yi wanka, yau dikkansu cikin sportwears suka shirya, sun ga Leo ya sanya ne sai suma dikka suka sanya. Vash da Zaysh ne suka fara ficewa, shi kuma Noor bed na Leo ya nufa, a kusa da shi ya zauna tare da cewa. “Good morning bro”…….. Bai amsa ba sai ya miƙe zaune yana binsa da wani irin kallo mai kama da na tuhuma. Da sauri Noor ya bi jikinsa da kallo kafin ya sake kallo Leo, shi dai bai ga wani abin tuhuma a jikinsa ba. “Bro lafiya?”. Ya faɗa a ɗan rikice, dan wlh idanun Leo rikita shi suke yi, ga su kalar sanyi zubin sleeping eyes, amma sai shegen kirita mutane……. Ganin babu alamar zai yi magana ne yasa Noor ɗan turo baki kaɗan kafin ya ce. “Ka iya gindayar da mutum kasa ya fara zargin kansa”…….. A yanzu shakuwa ce sosai ta shiga tsakaninsu a cikin wata ɗaya da ta wucen nan, sun zama tamkar ƴan uwan gaske. “What kind of dream did you have last night?”. In a cool way ya faɗa. Da sauri Noor ya sanya hannu yana rufe fuska, sai kuma murmushi ya kubce mashi. Wani irin kallo mai kama da harara Leo ya jefa mashi wanda yasa ya haɗiye murmushi, sai kuma ya ɗan shagwaɓe fuska. “Kai bro, I don’t know her, but she’s so pretty and cute”. Shiru Leo ya yi yana kara kare mashi kallo, yaro ya fara girma har da mafarkin mace, wai kyakkyawa ce, Noor ma ɗan duniya ne wasa-wasa. Jiya bayan sun dawo daga training na dare sai barci ya ɗauke sauran da wuri, shi kuma Leo sai da ya yi nafilfili sannan ya kwanta, bayan ya idar da sallar ne zai wuce sai ya ga Noor na mafarki, gabaɗaya sai numfashi yake yi sama-sama tamkar mai push-up ko wani abin mai wahala, har da haɗa zufa, ga bananarsa a miƙe zat. Kamar zai taɓa shi sai kuma ya ce kada ya katse mashi jin daɗi, shi ma da yake ɗan duniya ne wai kada ya katse mashi jin daɗi, shi ne ya kyalesa.”Sai yanzu zaka ji kunyata?”. Leo ya faɗa tare da yunkurawa zai sauƙo ƙasan bed ɗin, da sauri Noor ya biyo shi suka sauƙo….. “Bafa kunya na ji ba, amma bro fatan baka ga komai ba?”……. Girgiza kai Leo ya yi alamar yeah bai ga komai ba, daga nan bai sake yin magana ba. Kashe wayansa ya yi tare da ajiye wa, sannan ya ɗauki ɗan littafinsa, ya fara ƙoƙarin shinfiɗa gadonsa. Da sauri Noor ya taya shi suka shimfiɗa, ya ajiye wayansa a ƙasan pillow sannan suka nufi waje, dan lokacin sallah ta kawo kai, har an fara tada kabbara. Kai tsaye masallaci suka nufa, suna tafe kamar wasu kurame……. Bayan sallah sun haɗu a hall da suka saba tsayawa. A nan Captain ya zo ya samesu. Kamar kullum sai da yasa suka rera taken GIDAN SOJA kafin ya ce su nufi wajen da zasu yi weapon combat training. Ai Noor na jin haka ya matsa kusa da Leo, a ɗan shagwaɓe ya ce. “Bro ni ba zan iya rike bindigar nan in yi harbi ba, akwai wahala”.Kallo mai kama da harara Leo ya dalla mashi kafin can ƙasa ya ce. “But in the dream, you said you were strong enough to even harm a woman, right? Isn’t that what you claimed yesterday?”……. Da sauri ya ce. “Kai bro mafarki ne fa ba zahiri ba, ku ma ni ban yi komai ba”……….. Hannaye Leo ya zura a aljihu bai sake yi mashi magana ba, dan jiya Noor ya goge mashi hadda a mafarkin nan, wai har da sambatu. A tsakiyar hall da zasu gabatar da weapon combat training ɗin suka tsaya, koya musu amfani da bindiga da harbi cikin hanzari da tinani za’ayi. Dan Captain yasan basu gama iya sauya harsashi a kasa da minti ɗaya ba, kunga kuwa in basu iya ba akwai matsala, in suna tsaka da yaki bullet ya kare waye zai sauya masu? Musamman ace abokan gaba na harbo masu harsasai! Kunga ai dole su kware sosai.Nan aka kawo wasu ƙananan bindigu waɗan da ba kai tsaye na gaske bane, dan bullet ɗinsu ma yana cikin cover saboda tsaro. Nan Captain ya umarcesu da kowa ya ɗauki ɗai-ɗai. Bayan sun ɗauka ya kirga daga ɗaya zuwa uku ya ce kowa ya cire bullet dake cikin bindigar a second 30! Cikin zafin nama suka fara, Noor jikinsa har kerma yake yi wajen buɗe magazine ɗin bindigarsa, inda ake sakawa bullet ɗin kenan, ya ciro bullet ɗin ya ajiye a gefe, shi ne na biyun gama bayan Leo.Sai dai kuma tin daga kan manyan Generals dake kula da sashen horonsu har izuwa kan Captain da ake komai a gabansa sai da suka tsaya cak na ɗan dakiku a lokacin da suka ga abin da Leo ya yi. A lokacin da ya ɗauki bindigar da aka bashi, abu na farko da ya fara yi shi ne sai da ya fara rufe barrel na bindigar, bututun harbi kenan, sai da ya rufeta, sannan ya buɗe magazine inda ake saka alburushin ya cirota. Mamaki su Captain suke yi, domin kuwa Leo bindigar gaske suka bashi, kuma bullet ɗinta ba’ayi covering ba, sun yi ne dan su gwada shi, yana ɗaukar bindigar daga yanayin nauyinta ya gane komai real ne, shi ne ya fara rufe wajen harbinta kada ta kwace ta harbi wani, kwakwalwarsa tana da mugun gudu ne fiye da tunani, dik a ƙasa da second 20 ya yi wannan aiki!. Hakika sun shiga mamaki, dik yadda aka yi Leo ya san bindiga matuƙar sani, basu taɓa zatan zai gane komai na gaske aka bashi ba! Shi kuwa bai kawo komai a ransa ba, ya cire bullet ɗin ya ajiye a jefe cikin kwanciyar hankali.Captain sai da ya ɗauki ƴan mintina a ƙallah biyar kafin ya dawo daidai daga girgizan da Leo ya sanyasu. Sannan ya ce. “A ƙasa da 30 second ku mayar da bullet ɗinku, a ƙasa da second biyar ku ɗauki saitin harbi wa wancan board ɗin”. Tin bai kammala rufe baki ba suka fara, komai Leo yake yi cikin tsantsar natsuwa, a haka ya mayar da bullet ɗin, sannan ya mirgina daga in da yake, cikin zafa ya ɗauki saiti kamar da aka umarcesu. Ganin yadda ya yi yasa Noor ma mirginawa ya ɗauki saiti.Note, akwai abin da na mance ban faɗa maku ba, dik wani horon da aka yi masu ana maimaita masu shi ne har sai sun kware ya bi jikinsu, sai su fi sati suna maimata horo ɗaya, kunga ni kuma ba zan tsaya mu yi ta maimaita rubutun da muka yi ba, kun gane ai?!.Harbin tsakiyar board ɗin Captain yasa su yi, hakan yasa suka yi gagawar fara harbi, bullet ɗin kowa na da cover ne, hakan yasa ya fita salun alum ba wata ƙara sosai, shi kuwa Leo yana buga nasa sai da suka ɗan razana, dan ba cover. Dik wajen room 1 ne basu saɓa saiti ba, suka harbi in da aka buƙata, sai su Unays ke biye masu a saiti mai kyau. Captain ne ya ce. “Yanzu ku kaddara kuna tsaka da yaki bulle ɗinku ya kare, yanzu ku ciro bullet daga waist ɗinku, ku sanyawa bindigunku a ƙasa da one minute sannan ku cigaba da musayan wuta ba tare da ɓata lokaci ba”. Ya kai karshe tare da watsu masu bullet ɗaiɗai wanda zasu canza, sannan ya ce. “Minti ɗaya gareku”. Cikin zafin nama suka fara canzawa, wasu jikinsu sai rawa yake, wasu har da miƙewa tsaye, dan suna ganin a zaune buƙata ba zata biya ba. Dikkansu sun canza a ƙasa da minti ɗaya, amma room 1 sun canza ne a ƙasa da second 10 kacal saboda zafin nama da zafin jini irin nasu. Cikin zafa suka fara saita board ɗin suka yi harbi again. Sosai Captain ya ji mugun daɗi, haka ya sanyasu suka dinga maimaitawa har sai da ya ga sun mai da shi kamar ruwan shansu, sannan ne ya ɗaukesu suka nufi wajen da za su yi hand to hand combat training. Ba kullum yaƙi da bindiga ake yi ba, akwai in da faɗar hannu yake da amfani, musamman ga waɗan da ake son kamawa ba kashewa ba, waɗan da ake son bayanai daga bakinsu, so dole su iya faɗa da hannunsu a cikin wannan sati gabaɗaya, daga yau zasu fara.Sannan a nan aka koya musu dabarun ƙwace makami daga hannun abokin gaba. Sai da Captain ya fara koya masu yadda zasu daki abokin gaba, da yadda zasu karya hannu da kafafun mutane, shiyasa zaku ga wlh karyawa mutane hannu karamin aikin soja ne, sun kware a wannan sabga, to koya masu shi ma musamman ake yi, yadda zasu karya a take!Sai da ya gama koya masu wannan sannan ya umarce su suyi faɗa da junansu, wanda ya faɗi sai ya sake gwabzawa da wani har sai ya iya kare kansa, sai sun kware a iya jibgar wasu amma su kada su bari a jibgesu. Nan fa suka fara kallon juna, Leo bai zaɓi Noor ba, saboda yana tausaya mashi, yasan ma ba zai iya gwabzawa da shi ba, dan haka sai ya ce Juraiz ya zo su gwabza, dan ya gansa chocolate color, ga shi kakkarfa. Zaysh ya ɗauki Ameer, shi kuma Unays ya ce Noor ya zo su gwabza, har cikin ransa Leo bai so ba, dan ba zai iya ganin irin dukan da Unays zai yi wa Noor ba, dan yasan Unays ɗin ya fi karfin Noor, kuma yasan Unays bashi da tausayi, yanzu har cikin ransa yake jin Noor!. Captain na cewa start suka fara gwabzawa tamkar wasu mayunwatan zakuna, duka suka fara kaiwa junansu babu tausayi babu tausayawa, kowa ya iya allonsa ya wanke ne. Wani irin naushi da Unays ya kaiwa Noor a baki sai da bakin nasa ta fashe, take jini ta fara zuba, sosai Leo ya ji zafin haka, sai ya ji tamkar jikinsa aka nausa, a ransa ya ce bashi Unays ya ci, dik duka ɗaya da ya yi wa Noor sai ya biya shi. Amma shi kuma ga shi ya yi wa Juraiz mugun duka har ya baje a ƙasa yana numfashi sama-sama, kuma yake cewa zai ramawa Noor. Zaysh babu tausayi ya yi wa Ameer mugun duka shi ma, har ya fasa mashi baki, daga karshe ƙasa Ameer ya zube yana numfashi sama-sama. Ba karya Noor ya daku a hannu Unays duka mummuna ma kuwa, har sai da Captain ya shiga tsakaninsu, dan yaga Unays kamar ya mayar da abin gaske ne over, kun san dama yana jin haushin ƴan room 1, shi ne ya fara sauƙewa a kan Noor. Ba Leo kawai ba, hatta su Zaysh sun ji takaicin dukan da Unays ya yi wa Noor, jikinsu har tsuma yake yi na ganin yadda bakin Noor yake jini har ya kumbura!. Shi kansa Captain bai ji daɗin dukan ba, amma ya za’ayi? Dik cikin horo ne. Haka suna ji suna gani aka sake haɗa Noor da wani saboda doka ce in aka kada kai sai ka sake da wani. A nan ma Noor duka ya ci ba karya. Aka sake haɗa shi da wani, da team 1 suka ga fa za’ayi mashi mummunar illah sai Leo ya ce a haɗa shi da shi. Da sauri Captain ya aminta, saboda shi ma tausayin Noor ya gama cika shi. Da aka haɗasu sake jiki Leo ya yi Noor ya yi nasara a kansa, sannan shi aka haɗa shi da wani, dik dai abin da suke yi manyansu na kallonsu. A wannan horo dai ba’a tashi ta daɗi ba, dan bakin Noor a kumbure dam suka nufi wajen breakfast. Da kyar Noor ya iya cin abinci saboda yadda bakinsa take yi mashi zafi ga kumburi, sai da Leo ya mashi kalaman jarumta, sannan ne ya ci. Bayan sun gama karyawa aka ɗaukesu zuwa wajen da zasu yi guerrilla warfare training. A nan aka koyar da su yadda ake amfani da muhalli dan samun nasara a yaƙi.Kowa ya shiga cikin maɓoya, dan dole ne su ɓuya kuma su yi tafiya a kwance ba tare da an gan su ba, kamar kwantan ɓauna kenan. Sannan aka koya masu yadda zasu ɓuya su saje da ciyayi dan kare kai, da yadda in sun ɓuya zasu fito da bindigunsu su yi harbi. Dan dole suyi hari ba tare da sun bayyana kansu ba, shi ake cewa yakin sunkuru.Sai da suka yi awa guda a wannan horo sannan aka ɗaukesu zuwa wani tapkeken ruwa da aka yi shi musamman dan yin river crossing under attack training. A nan Captain ya koya musu yadda za su tsallake ruwa cikin gaggawa a yayin farmakin makiya, su tsallaka ana harbinsu da bindiga ta baya, dole su koyi kaucewa bullet a cikin ruwan. Kuma dole su iya yin iyo a cikin ruwa mai gudu, ana koya musu yadda ake ratsa ruwa ba tare da abokan gaba sun gan su ba, dole su natse cikin ruwa su rike numfashinsu suna tafiya har su haye. AIKIN SOJA BA NA RAGWAYE BANE MY PEOPLE’S, BA DIK KAI BA WLH! WAI DAN MA BAKU GANIN AZABAN A ZAHIRI, A RUBUTU BA ZAKU FAHIMCI AZABAR SOSAI BA, SAI KUN GANSU SUNA NISHI SAMA-SAMA TAMKAR RAI ZAI YI HALINSU A KAN IDONKU TUKUN NAN, A NAN NE ZAKU JI ZUƘATANKU SUN KARAYA, KUN TAUSAYA MASU.Duk wanda bai iya tsallake ruwan a cikin lokaci ba sakowa zai yi. Haka suka dinga fama, waɗan da akwai pool a gidansu sun yi kokari, amma an sha ruwa kam, an kuma ci azaba, sai numfashi sama-sama suke yi tamkar ba zasu kai labari ba, amma a haka suka jure.Bayan dikka wannan wahala sai aka kaisu in da zasu yi attack simulation, waje ne da aka shirya masu tamkar farmakin gaske, su kwaci kansu, unexpected suka fara jin farmakin. Cikin zafin nama suka fara fito da kwarewarsu a fili, abu na farko da suka fara yi shi ne rarraba kansu zuwa team by team dan su kwaci kansu su kuma yi wasa da hankulan abokan gaba, na biyu suka fito da dabarun ɓuya, na uku suka haɗa kai a wajen dan ganin sun yi nasara. Abin ya yi matuƙar bawa manyansu mamaki, like wow, suna da basira. Sai ma da Captain ya ga suna yi wa juna magana da ido a lokacin da suka ɓuɓɓuya a wajaje tantunan dake wurin, magana sosai suke yi da ido na yadda zasu yi su tsira, kai abin ya bawa Captain mugun mamaki, bai taɓa zatan kwakwalwarsu zata yi sauri basu dabara da mafita ba, sai ga shi kuma sun yi.Manyansu sun ji daɗi sosai. Daga nan suka nufi masallaci, bayan sun yi sallah suka yi lunch sannan suk nufi class. Yau an koya masu karfin gudun kowani bindiga, illarsa, dalilan da yasa yake kwacewa a wasu lokutan, goge dattinsa, cansa wasu sassa nasa, da faidar kowacce, kowacce lokacin da ya dace ayi amfani da ita.Sun ɗauki awa biyu a class ɗin kafin su fito su sake komawa wajen horon harbi, dai saiti shi ne babban abu a fagen yaki, in baka da saiti ma kana iya harbin kanka, dan haka dole ka kware sosai. Daga wajen saiti da yamma suka wuce wajen horon hannu, dan ƙara gwada kwanci, suka yi gym na yamma sosai zuwa karfe 7 suka tashi horo. Masallaci suka nufa, bayan sallar mangrib and Isha’i suka nufi rooms ɗinsu.Vash and Zaysh a tare suka jera zuwa yaronsu a maimakon su koma roon ɗin nasu. Noor and Leo kuma ɗaki suka koma, Leo ya je yana shafawa Noor magani a bakinsa da ta kumbura sosai. Sai sannu yake yi mashi, Noor sarkin son jiki tuni ya kwanta mashi a jiki har da kukan shagwaɓa, yau ya tuna da su Aunty Lusi, yadda yake yi masu ya hau yi wa Leo yau, shi kuma ya daure yana ta biye mashi, dan Noor ya shiga ransa matuƙa.A gefe guda kuwa su Arya bayan sun dawo da school sun yi lunch V ta ce zata tafi wajen daddy, da sauri Arya ta hanata ta hanyar cewa su je su buga basketball a wajen game ɗinsu. Ba dan ta so ba ta yarda, kuma babu rabon haɗuwarta da Noor nan kusa!.Arya ta raba masu team, suna sanya sportswear iri ɗaya kaunin milk color. Arya ta ɗauki basketball ɗin nasu suka nufi wajen wasanninsu. Katafaren fili ne da GAT yasa aka ƙawata masu shi, kayan wasanni ne kala-kala a cike a ciki, akwai wajen football, basketball, snooker, har wajensu whots akwai, kwallon kwando da komai dai.Raba kansu suka yi team biyu, Arya da Manassa, Angelie and V. Akwai wasu zaratan sojoji dake tsaron wajen wasan, suna tsaitsaye tamkar saƙaguna suna satar kallonsu Arya. Ga shi sportswear ɗin nasu guntun wando ke zuwa tsala-stala cinyoyinsu dake wani irin glowing, very soft. Daga sama rigar tasu mai ƙaramar hannu ce, kayan dai yai masu kyau sosai. Da suka fara ball ɗin dik in da suka yi idanun sojojin nan a kansu yake, musamman V da ko’ina yake cike dam, ai tana tashin kan mutane. Cikin nishaɗi suke wasanninsu cike da kaunar juna, Arya dai ta yi wa V wayau ta hanata zuwa ganin masoyi Leo. A can cikin barrack kuwa zama Vash and Zaysh suka yi a saman wasu kujerun dake arear wajen horonsu. Suna zama Zaysh ya ce. “Bro kasan akwai mata a training ɗin nan?”. Da sauri Vash ya amsa da. “Yeah, three days ago na haɗu da wata kyakkyawa a kusa da Senior staff side”.Shiru Zaysh ya ɗan yi kafin ya ce. “Ni kuma almost a month ago, mun yi karo da wata, kuma tin time ɗin ban sake ganinta ba”……… “Bar zancensu kira mana Ummie mu gaisa, na yi kewarta, jiya bamu yi waya ba”……. Watau idan kana da kyan hali kowa nemanka zai dinga yi!.Wayansa ya je ɗaki ya ɗauko ya dawo, yana kunnata saƙon Ummie na shigowa. “Koman dare idan ka samu lokaci ka kirani”. Shi ne abin da saƙon ya ƙunsa, haka kawai ya ji faɗuwar gaba, cikin zafa ya laluɓo numberta ya danna kira.A lokacin tana zaune saman kujerarta da ya gama shan wahala, dama ba wani qualityn kirki ba. Kiran na shigowa ta yi gaggawar ɗagawa, muryanta na rawa ta ce. “Hello”…….. Sai da ya ji kirjinsa ta buga kafin ya amsa da. “Ummie lafiya?”. Kuka ta rushe mashi da shi, da kyar cikin kuka ta iya cewa. “Zaynish na shiga uku, yayanka aure zai kara, ƴan uwansa sun ce ya kara aure tin da ni bana haihuwa”……. Ɗan waro idanunsa a kan face ɗin Vash ya yi, idan ransa ya kai miliyan to ya ɓaci, a duniya babu abin da ya tsana irin ya ga tashin hankalinta, yau da yana da dama babu wanda ya isa yasa mijinta ƙara aure, amma bashi da shi, innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Da kyar ya saita natsuwansa tare da cewa.”Ummie ki yi hakuri ki yi shiru mu yi magana kin ji?”……. Da kyar ta iya amsawa da. “Na gagara dannewa ne, Zay wai fa ƴar wannan gwaggon nasu masifaffiyar zai auro! Wannan yarinya mara kunya da ka taɓa wankawa mari lokacin da ta ce zata dakeni, ita fa suka ce ya aura! Wai ni me na yi masu ne? Meyasa suka tsaneni? Na yi wani laifi ne? Zay kada ka ɓoye mun, ka faɗa mun tsakaninka da ALLAH me laifina in gyara!”. Tana kuka tamkar ranta zai fita.Miƙewa tsaye ya yi, ya ɗan matsa gaba kaɗan dik da Vash baya jin yarensu, amma shi mutum ne mai son sirri da mugun zurfin ciki, yasan ko a yanayin maganarsa Vash zai fahimci wasu abubuwa. “Ummie baki da wata matsala, ki natsu, kin manta kece kike ce mun ALLAH na jarabbatar mutanen kirki ne? Kin manta kece kike ce mun a kowani hali nike ciki kada na manta da ALLAH ne? Yanzu ki rufe idanunki, ki ambaci sunan ALLAH sau uku a jere kafin mu cigaba da magana”……. Shi ma dauriya ce kawai yake yi, amma zuciyansa tamkar zai fasa kirjinsa ya fito waje.Cikin kuka ta amsa abin da ya ce, cike da yaki da yarda da ALLAH ta rufe idanunta ta ambaci sunan ALLAH sau uku a jere, take ta ji zuciyanta ya yi sanyi, dik wani raɗaɗi ya kau, nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sanya hannu ta goge hawayeta. A natse ta ce. “Nagode wa ALLAH da ya bani ɗan uwa kamar kai”. Ajiyar zuciyan shi ma ya sauke kafin ya amsa da. “Nafiki farinciki idan na tuna kece ƴar uwata”…… Kara nisawa ta yi tare da cewa. “To na yarda, yanzu dai ka bani shawara ɗan uwana”……. “To shikenan, yanzu dai so nike ki kwantar da hankalinki, ki natsu, sannan ki bani aron kunnenki”…….. Gyara zama da kyau ta yi, ta kara sauke ajiyar zuciya kafin ta ce. “Ina jinka rabin raina”. “So nike ki kara hakuri kan wanda kike dashi, ina ji a jikina wahalarki kaɗan ce ta rage, ki mai da komai ba komai ba, dik abin da za’ayi ki toshe kunnuwanki, ki rufe idanunki, kada ki taɓa nuna kamar kin san suna yi, ko ita yarinyar da zai aura kada ki taɓa nuna mata kamar kin damu, ki nunawa yaya kina supporting ɗinsa, zan tura maki kuɗi ku fara business, ki mai da hankali kan kasuwancinki, ki kuma cigaba da addu’a, ALLAH baya barci, kuma babu wanda zai baki haihuwa a duniyar nan face shi, tabbas kuma bai manta dake ba, amma dik da haka ki dage da addu’a, ki dage da tashi sallar dare, ki kai kukanki garesa, ki koma gefe ki huda ganye kina kallonsu, ina da tabbacin ALLAH zai dubeki da idanun rahama, sai warware mana dikkan matsalolinmu”. Sosai ta ji kwarin gwiwar kalamansa, amma sai ta ce. “A ina ka samu kuɗin da zaka bani in fara sana’a?”…… Bai ɓoye mata komai ba, ya faɗa mata kuɗin da Vash ya bashi, idan zai canza kuɗin ya turo mata sun kai 3M, jin kuɗin da bata taɓa ganin kwatansu bane yasa ta kiɗime, hankalinta a tashe ta ce. “Zay anya mutanen kirki ne kuwa? Kuɗi har miliyan uku zasu baka kyauta? Ni kam gaskiya ina tsoro, ka rabu da su to”. Dik ta rikice. Natsuwa ya yi ya kara yi mata bayani da kyau har ta fahimta, sannan ya ce zai tura mata 2.5 shi kuma zai bar sauran a hannunsa, ya ce ta samu sana’a mai kyau ta kama. Cike da murna ta ce mashi to zata sayi kayan gado da kujeru masu kyau ko da na 1m ne, dan ita ma ta sabonta ɗakinta kafin amarya ta zo.Na’am ya yi da wannan shawara tata, daga nan ya ce ta nemo account ta turo mashi zai tura mata, ta dai tsaya a kan sana’ar da zata kama sosai, kada ta yi wasa!. Ai mancewa da batun kishiya ta yi, ta dinga murna, har da dariya mai sauti, daga nan ya koma ya haɗata da Vash, suka gaisa ta dinga yi mashi godiya cike da murna, mamaki Vash ya dinga yi a kan meyasa take yi mashi godiya har haka ne? Dan ya ɗan hawa Zaysh ɗan wannan kuɗi da bai wuci na kashewansu a wuni idan suka so ba! Haka dai ya amsa da okey, daga nan Ummie ta yi masu addu’oin da ta saba, suka yi sallama, shi ma Zaysh suka yi sallama, ya koma ya zauna suka cigaba da hira da Vash. ———————🔥Haka rayuwar matasan sojojin nan ya cigaba da tafiya har suka ɗauke basic training na tsawon watani, a nan manyansu suka ga room 1, room 2 zuwa room 3 suka da kaifin ƙwaƙwalwa da kwarewa, dan haka sai aka fara basu horon jami’an na musamman, misali kamar a Nigeria ce jami’an NDA haka, su jami’ai ne da kwarewarsu ya zarce yadda ake tinani, dan shi horonsu ma na shekaru biyu ake yi masu, amma a Nigeria horon yana iya kai shekaru uku, sai dai su AVARIS a shekaru biyu jami’i ya zama kwararre, basa ɓata lokaci kuma basa ɗaukar wasa. Dan haka su Noor suka shiga fagen horon jami’ai na musamman da iya gwabzawa a ƙasa da ƙasa, ga karatun da suke karɓa tamkar a school, har yau Unays, Zaysh, Leo basa shiri, kuma har yau Leo bai yafe dukan da aka yi wa Noor ba, sauran jami’ai sun yi passing out a watanni shidda nan, su kuma an matsa da su gaba, wani wajen da aka kaisu ba mai iya samun damar ganinsu, ko fitowa basa yi, barci a ƙurarren lokaci tashi a farkon lokaci, komai an ninka masu ukun na baya. A ɓangaren su Arya ma hakan ce, sun dukufa a kan aikinsu babu kama hannun yaro, sun mayar da hankali sosai.To zan ɗan taƙaice training ɗin nan ne ba dan komai ba sai dan labarin yana gaba, manyan abubuwan da yakamata ku sani suna gaba ne, kada mu ja lokaci a horar da su! Dan tafiyar bama a fara ba! Shiyasa zan taƙaice maku shi amun afuwa!.A ɓangaren Ummie, cikin ikon ALLAH ta kama sana’a da kuɗin da Zaysh ya bata, ALLAH ya zubawa abin albarka, tana samu sosai, dan haka bata damu da auren da mijinta ya ƙara ba, an yi auren an luma kawo yarinyar gidan an haɗasu, ba kalar rashin mutuncin da yarinyar bata yi mata, amma ko kaɗan bata damuwa da ita, ta mai da hankali kan kasuwancinta, tana kuma yin waya da ɗan uwanta yana kwantar mata da hankali, har yanzu dai ciki shiru babu shi babu labarinsa, bata nuna damuwarta, tana dai cigaba da addu’ar ALLAH ya bata mai albarka!.Zaysh dik in ya samu wani kuɗi sai ya ƙara mata, yanzu tana da babban shagon sai da abayoyi, kishiyar tata bata da burin da ya wuce ta ga shagon ya durkushe, ta yi balal’in duniyar nan kan lallai mijin ya buɗe mata nata shagon, ya ce shi bashi da kuɗi, ita ma Ummie ba shi ya buɗe mata ba, ɗan uwanta ne, to shi ne take ta ƙulla makircin yadda zata yi shagon ya durkushe komai ya kare dan mugunta da bakin hali, kuma wlh Ummie bata rageta da komai ba fa! Har kyauta tana yi mata, kawai dai mugun hali ne. ——————–🔥Yau ta kama ranar Friday, sai shirye-shirye Ummie take yi, ranar Monday zata je kasar Avaris passing out na Zaysh, dan zasu fita, tin da ya tafi bata sake sanya shi a idanunta ba sai waya kawai, kunga kuwa sai murna ai yanzu.Kaya akwati guda ta shirya, kuma ita kaɗai zata tafi, dan mijinta bashi da halin biyan kuɗin jirgi, ita ɗin ma Zaysh na zai biya mata, ya ce kada ta taɓa kuɗin shagonta, shi ma kuma Vash ne ya bashi kyautar kuɗi ya ce ya yi shirin passing out ɗinsu, shi ne ya tura mata ta zo. Danginsa sai zaginta suke yi, wai yawo zata je, dama sun ƙala mata sharrin bin maza, wai idan ba bin maza take yi ba a ina ta samo kuɗin buɗe shagon nan nata?. Ita dai bata ce masu komai ba, suka ce ai sun san basu da komai, marayu ne, waye ya bata kuɗi?.Bayan mijinta bata faɗawa kowa ga wanda ya bata ba, ta koma gefe ta yi shiru tana kallonsu.Bayan ta kammala shirya akwatinta, ta rufesa kenan sai ta ji ana sallama a parlo. A natse ta amsa tare da miƙewa ta fito dan ganin wanene?. Cike da mamaki ta zaro idanunta a lokacin da ta ga mai daka mata sallamar. Muryarta har yana ɗan rawa wajen cewa…….
STAR LADY TAKU CE TA AMANA.🔥

