Hausa novels

Halysaah Page 81 By Khaleesat Haydar

Yau laraba Khaleesat suka zana exam dinsu na karshe for the semester, suna zaune da Safiyyah a haraban department dinsu Safiyyah tace “Yanxu ranan Friday din za ku tafi Nigeria ke da Housemate?” Khaleesat tace “Haka dai yace amma ban sani ba” Safiyyah tayi tagumi tace “Wallahi nayi da na sanin hadani da Yaya Musty da aka yi a kasar nan, daga ce masa zan kira Babana in ce zan taho hutu Nigeria ya fara surutu wai me zan je inyi bayan ba hutu me tsayi bane, ina ruwan Musty in ba gudun biya min kudin jirgi yake ba, gashi yanzu kema tafiya zaki yi ki barni ni kadai raina a garin nan, wallahi ko me zai faru bazan yi hutu a garin nan da er iskar matarsa da bata son kwanciyar hankalina ba” Khaleesat tayi murmushi tace “Na zata ai kun yi settling disputes dinku ke da ita” Safiyyah tace “Wa?? Don kinga na dena kawo maki korafinta? Gajiya nayi kawai in gaya maki, amma tana nan bata fasa abubuwanta ba ashe ba ciki gareta ba kwanaki da nace maki kamar tayi ciki…” Khaleesat tace “Toh Allah ya kyauta, kilan idan kika lallabasa zai bar ki ki tafi Nigeria din” Safiyyah tace “Shi fa ta aljihunsa yake, kudin jirgin da zai biya min ke daga masa hankali, alhalin ni babana nace zan kira ya turo min kudi bance ya biya min ba, Yanxu kenan Ajay kawai za ku bari a kasar nan?” Khaleesat tace “He is leaving today, don ma yayi rescheduling Flight ticket dinsa da tun Monday zai tafi ai” Safiyyah tace “Kin ji ko? Wato duk tafiya za ayi a bar ni ni kadai a garin nan kamar mara galihu, wallahi bazan yarda ba, wannan ai sai Depression ya kama ni kafin ku dawo” Dariya kawai Khaleesat tayi bata ce komai ba, truly hutun babu tsayi sosai kuma banda she is missing her mother da sai tace Housemate ya tafi kawai ya bar ta a kasar saboda Safiyyah, amma a yanxu kam ji take kamar ta jawo Friday don tayi missing Ummanta so much, kiran Jay ne ya shigo wayarta tayi picking call din ta kai kunne, bayan sun gama waya ta kalli Safiyyah da tayi shiru kana ganinta kasan hankalinta ya tashi za a bar ta ita kadai a Maryland, Khaleesat tace “Mu je Housemate dina yana jiran mu…” Safiyyah ta sauke wani ajiyar zuciya ta kara rafka tagumi tace “Ki je kawai ni zan zauna nan inyi tunanin rayuwata, In ba rashin gata ba menene wannan, in zauna a Maryland in ci uwar me? Wallahi bazan zauna ba bakin ciki ya kasheni, ko duka kudin account dina ne gwara in siyi ticket in gudu, sai dai Mustapha ya tashi rana daya yaga babu ni, yayi ta iko da ni sai kace wata matarsa daga dai ina zaman cin arziki a gidansa” Khaleesat tayi murmushi tace “Kilan ma wasa yake maki amma duk kika daga hankalin ki, ni dai ki tashi mu tafi…” Safiyyah tace “Kiyi tafiyarki kawai ni ina nan bazan je ko ina ba” Duk yanda Khaleesat ta so Safiyyah ta tashi su tafi Housemate yayi dropping dinta a gida Safiyyah taki bin ta, haka nan Khaleesat ta kyaleta ta dau Backpack dinta ta tafi inda Housemate yayi parking yana jiranta, bayan ta shiga motar ta kara gaishesa, ya amsa yace “How was the exam Halysaah?” Tace “Alhamdulillah” Yace “Safiyyah bazata tafi gida bane ban gan ku tare ba?” Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace “Eh wai bazata ba, she is angry saboda yayanta yaki barin ta tafi hutu Nigeria” Jay yana murmushi yace “Shi zai biya mata kudin ticket din ne?” Khaleesat tace “Nima ban sani ba” Jay yayi igniting motar yace “Indai zai bar ta sai in siya mata flight ticket din, probably bai sa kudin Flight dinta a Budget dinsa for this month ba, beside kilan yayi considering hutun bai da tsayi” A hankali Khaleesat tace “She is so sad about it” Jay ya dau wayarsa yace “Let me call her” Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take har ya gama waya da Safiyyah, komai nasa burgeta yake, yana daga idonsa tayi saurin sauke nata idon, yayi kasa da murya yace “Me da me kike bukata da zaki tafi Nigeria da shi?” Khaleesat ta girgiza masa kai cikin sanyin murya tace “Ba komai, recently kayi min shopping ai” Yace “But zaki yi ma mutanen gida tsaraba” Tana murmushi tace “A’a ba abinda zan siya” Yace “To ni zan siya masu” Ta langwabe kai tana kallonsa tace “Don Allah kar kayi, expenses din yayi yawa pls” Bai sake tankata ba, tasan kuma sai yayi tunda yace zai yi, ya kalli agogon wrist dinsa don anjima zai yi dropping Ajay a airport, bayan kusan minti biyu ya kalleta calmly yace “How about coming back to Maryland as a bride?” Khaleesat ta daga idanuwanta ta kallesa don sai da gabanta ya fadi jin abinda yace, ya sakar mata murmushi a hankali yace “How about that?” Sunkuyar da kanta tayi don bata ma san me zata ce ba don kunya, yayi kasa da murya yace “Halysaah” Ɗan murmushi Khaleesat tayi ta kauda kai kawai, yace “Say something” a hankali tace “Ni ban san me zan ce ba” Yana murmushi yace “To a matsayin amarya zaki dawo in sha Allah” Khaleesat dai taki yarda ta juyo ta kallesa, shi ko bai fasa kafeta da ido yana ta kallonta ba, a haka Safiyyah ta iso gun motar, ta bude back seat ta shiga da sallama kamar mara lafiya, Jay ya amsa ya kalleta yayi murmushi yace “Cheer up Safiyyah, yayanki zai bar ki in sha Allah, duk yanda ku ka yi da shi sai ki min magana ta WhatsApp” Safiyyah tace “To Yaya Jawwad” Khaleesat sae kallon Safiyyah take tana murmushi ganin yanda ta nutsu irin tana cikin damuwa din nan, ta gefen ido Safiyyah ta harareta, Khaleesat tayi dariya tace “To ni me nayi maki?” Jay yayi driving motar suka bar wajen. Wajen karfe uku Khaleesat ta sauko downstairs tana kallon Housemate dinta dake parlor don wayarta ya kira, ya juya ya kalleta yace “Are you sleeping?” Ta girgiza masa kai, yace “Ohk get ready let go drop Ajay at the airport” a hankali tace “Toh” Sannan ta juya ta koma sama, bayan ɗan lokaci ta sauko cikin shiri, ganin baya parlon ta fita waje ta gansa yana jiranta a garage, kulle apartment din tayi ta karasa ta shiga motar bayan ya bude mata front seat…. Suna isa gidan nasu Jay yayi parking a waje ya bar ta a motar ya shiga cikin gidan, after a while suka fito tare da Ajay, bude front seat din tayi ta sauka ta koma back seat, Ajay ya bude booth ya saka hand luggage dinsa, sannan ya shiga gaban motar, Jay ma ya shiga driver seat, sai da Jay ya fara driving Khaleesat ta ɗan kalli Ajay don yi yayi kamar bai san tana cikin motar ba, tace “Ina yini” Yana fastening seat belt dinsa yace “Good” After some minutes ride Jay yayi parking a inda zai cire kudi, yana kallon Ajay yace “Let me get some cash” Ita dai Khaleesat kallonsa kawai take, ya juya yana dubanta yace “I am coming” Ta gyada masa kai ya bude motar ya sauka, ta daga ido tana kallon Ajay ta madubin gaba suka hada ido, ta tallabi chin dinta tace “Are you going to kano or Bauchi?” Ear pod dinsa ya ciro ya toshe kunnensa, ta wani kallesa, after some seconds ta ɗan buga seat din da yake zaune tace “Ina tambayar ka ne” Ya juya ya kalleta yace “Baki da hankali ne?” Ta langwabe kai tace “To ai nasan kana ji na, i am just asking a harmless question” Yace “Mind your business” Daga haka ya juya, tabe baki tayi ta matsa zuwa can karshen motar ta zauna, Jay ya dawo bayan ya cire kudin ya shiga motar, har suka isa airport ba wanda yace komai cikin su, Ajay ya bude motar ya sauka ya zaga ya bude booth ya dau jakarsa ya dawo ya daga ma Jay hannu, Jay yace “Journey mercies bro” Ajay yace “Thanks” Ita dai Khaleesat ba abinda tace, Ajay ya ɗan kalleta sannan ya juya ya nufi cikin airport din, Jay ya kalli Khaleesat yace “Dawo gaba Madam” Murmushi tayi ta bude motar ta sauka ta koma front seat, yace “Me yasa baki masa Allah ya kiyaye ba” Khaleesat tace “Ohk, na ma manta” haka suka bar airport din, eatry ya tsaya ya siya masu abinci don baya son ta ba kanta wahalan girki, daga nan suka koma Apartment dinta, ko abincin Khaleesat bata ci ba ta tafi ta kwanta a dakinta don bacci take ji. Wajen karfe bakwai na dare Khaleesat ta bude kofar dakinta tana kallon Jay dake tsaye bakin kofar, yace “Are you still sleeping?” Ta ɗan yi murmushi tace “Na tashi” Yace “Knocking dina ya tashi ki dai, nasan ko sallah baki yi ba?” A hankali tace “Zan yi” Yace “Ohk kiyi sallah ki sakko downstairs ki dau abincin ki, idan ya so sai ki ci gaba da baccin ki” Tana murmushi ta gyada masa kai, Bayan ta idar da sallan magrib ta sauko downstairs, tun da suka dawo daxu da ta tafi sama ta kwanta sai yanxu ta sauko kasa, kallo daya yayi mata ya ci gaba da kallon TV da yake, taga yayi mata micro waving abincin nata ta dauka da bottle water tana kallonsa tace “Thank you” Without looking at her yace “Are you going upstairs with the food?” Ta gyada masa kai tace “Uhm” Yace “Alright, sai da safe kenan?” Ta ɗan kallesa, sai kuma ta gyada masa kai, shi ya ma fi so taje tayi ta baccin da ta sauko downstairs ta zauna inda yake, upstairs ta koma bayan ta ci abincin a dakinta ta dau wayarta ta duba ko Aunty Farida tayi mata message amma taga bata hau online ba, ta jira har lokacin Isha’i yayi, tayi sallah sannan tayi wanka tayi shirin bacci ta kwanta. Washegari da safe wajen karfe goma saura Khaleesat ta sauko downstairs, kallon Housemate dinta dake kwance idonsa lumshe a parlon tayi, har yayi wanka ya shirya, ta kalli makullin motarsa alamar ya ma fita ya dawo, taga ya bude ido a hankali yace “Good morning Halysaah” Ta zaro ido don ta zata bacci yake yi, sai kuma tayi murmushi tace “Good morning” Yace “I got us breakfast, ga naki saman Centre table” Tace “Kayi breakfast din?” Ya gyada mata kai, tace “Ohk” zagawa tayi zuwa inda ya ajiye mata breakfast din, Ya mike zaune yana shafa gashin kansa yace “I am going out, dama ina jira ki tashi ne, should i drop you at Safiyyah”s place? Cause i don’t want you to be home alone” Khaleesat tace “Mun yi chatting da ita daxu tace zata zo nan da karfe goma, kilan tana hanya, she is coming to help me wash my hair” Kallon kanta yayi duk da akwai hula a saman kan sannan ta daura dankwali yace “Kin rage gashin ne?” Dariya Khaleesat tayi bayan ta tuno yanda yace ta rage gashin kanta da dadewa and he was serious about it, tace “Eh na rage” Yace “Da gaske? Ta gyada masa kai tana kallonsa, yace “To in gani” Sunkuyar da kanta tayi tana Murmushi taki ce masa komai, yace “Ko baza ki nuna min ba” Ta ɗan kallesa tace “To saboda me zan nuna maka?” Yace “So that i can confirm ko da gaske kike” Ita dai bata fasa murmushin da take ba, can ta ɗan yi baya da hulan kadan tace “Ka gani?” Yana kallon gashin gaban kanta that’s so Curly and black, a hankali yace “Ban gani ba” Dariya tayi tace “To ai shikenan” Yace “Baza ki nuna min ba dai kenan” Shiru tayi tana kallonsa kamar yanda ya kafeta da ido, after some second ta cire hulan kanta duk gashin suka sauka har kusan gadon bayanta, mikewa Jay yayi yana kallon gashin with astonishment, it was very black, full and long, hannunsa ya kai kan gashin yana feeling texture dinsa, he couldn’t believe this is her real hair, Khaleesat ta zaro ido ta koma baya da sauri ganin abinda yayi, kiris ya rage ta fada saman Centre table din bayanta yayi saurin rikota yana kallonta babu ko kiftawa ya kai forehead dinsa saman nata murya can kasa yace “You’ve got a very beautiful hair Halysaah, I love it…” Gaba daya Khaleesat ta daburce tana kokarin kwace kanta aka danna bell din gidan, that was when he realised and quickly let go of her, dukawa tayi da sauri zuciyarta na bugawa ta fara neman hulanta, shi kuma ya nufi kofar parlon ya bude, Safiyyah ce tsaye bakin kofar ta gaishesa tana washe baki ya amsa yana mayar mata da murmushin ya juya, makullin motarsa kawai ya dauka ya fita daga gidan, Safiyyah ta zauna kan kujera tana kallon Khaleesat da mamaki tace “Ya na ganki duk kamar a daburce, shi ma Housemate din naga yake kawai yayi min, kuma har ya fita” Khaleesat ta mike taki yarda su hada ido da Safiyyah tace “Ban gane a daburce ba, ba kince da Aslam zaki zo ba, me yasa baki zo da shi ba” Kitchen Khaleesat ta nufa Safiyyah ta bi ta da kallo har ta shiga ciki, Sai kuma ta bi parlon da kallo tace “Uhmm abi did i interrupt anything?” Bayan Khaleesat ta fito kitchen din da plate a hannunta da cup din shayi still taki yarda su hada ido da Safiyyah ta fara bude breakfast din da ya siyo mata, Safiyyah tace “Goben ne tafiyar taku?” Khaleesat tace “Ehh in sha Allah” Safiyyah tace “Ni ya Musty yace in bari next week dukanmu ma za mu tafi Nigeria din da gantalalliyar matarsa” Khaleesat ta fara cin fries din da ta zuba a plate ta kalli Safiyyah a karo na farko tace “Sakko mu ci, sai yanxu zan yi breakfast” Safiyyah tace “A’a ni nayi tun daxu” Khaleesat bata sake ce mata komai ba ta ci gaba da cin fries dinta, Safiyyah sai kallonta take a ranta kuwa cewa take yaushe Housemate ya lalace haka har yake neman gantalar mata da kawarta da ko hannunta bata yarda namiji ya taɓa, sam bata gane wannan birkicewar da kawarta tayi ba, kaddai kiss dinta yayi, dama taga kamar lip gloss a lips dinsa, what if har da romance, ta kalli Khaleesat tace “To kallo ku ke a parlon ne ku ka kashe Tvn da na zo?” Khaleesat ta wani kalleta, sai kuma tace “Ni fa wallahi yanxun nan na sakko downstairs tun da gari ya waye, baki ga breakfast dina akan Centre table ba sai yanxu na dauka, i am just coming down now” Safiyyah sai kallonta take ganin a duburce take duk bayanin nan, can ta kyabe baki ta sauka kusa da ita zata fara cin fries din ita ma, Kamshin turaren Housemate ne ya daki hancinta daga jikin Khaleesat, Safiyyah tayi tagumi tana kallonta amma bata dai ce komai ba, can ta dau fries din ta fara ci, a ranan Safiyyah bata yarda ta koma gida ba ta kira Ya Musty ta lafta masa karya wai Khaleesat na kwance bata da lafiya, har da ba Khaleesat wayar yayi mata sannu, ita kanta Khaleesat taji dadin kwanan da Safiyyah zata yi a gidan because she is still shocked at what happened in the morning…..

Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah Ur evidence
07087865788

Hakika duk wacce ta Bari aka barta abaya ita taso domin mu mata da ado da kwalliya aka sanmu. Assalamualaikum, barkanmu dai Yan uwana ma masu albarka, ayau na zo maku da batun sababbin kayan da na kawo Mana masu matukar kyau da kuma inganci,oum eman collection 🤝😍, takawo maku jakunkuna da takalma,hadi da abayas da kuma sarkoki masu matukar kyau da kuma sauki,07018872587 Ena amare da uwayan gida masu capacity’s toh duk wacce ta yarda da tacika mace da wacce takeso ta zamo ma abociyar kwalliya toh ta garzayo gunmu domin hadewarki cikin ado da kwalliya kedai nemeni a wannnan number domin kisami kayayyaki masu kyau da kuma quality akan kudi kalilan hajiyata 07018872587 ngd 🤝 ado da kwalliya shine takenmu

Back to top button