Gyaran Jiki
Idan kuna son fata ta yi laushi da sheki ku samu wadannan abubuwan kamar haka:
✓ Man zaitun
✓ Lalle
✓ Kur-kur
✓ Madara
Zaki hade wadannan kayan hadin guri daya, sai ki kwaba su ki shafe jikinki da fuskarki, zakiyi wannan hadin kafin ki shiga wanka. Idan ya bushe a jikinki sai ki murje sannan sai ki wanke jikin, jikin yana yin kyau yayi sheki.
Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata
Gyaran Jiki 2
Wannan hadin shi ake cewa kafi TURGEWA, ku samu wannan abubuwan kamar haka;
✓ Kur-kur
✓ Dilka
✓ Zuma
✓ Kwai
✓ Lemun tsami
Ki hade su guri daya ki samu ki kwaba kamar yadda ake kwaba lalle, amma yafi kwabin lalle ruwa, sai ki shafe fuskarki. Idan kuma har da jiki kikeso, sai ki shafa harda jikin Bayan (1hr) sai ki shiga wanka zaki ga yadda jikinki zai goge.
Karanta>>> Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.
Gyaran Jiki 3
Idan kuna son fata ta yi laushi da sheki, ku samu:
✓ Lalle
✓ Kwanduwar kwai guda 3
✓ Manja cokali 3
✓ Kur-kur
Sai ki kwaba su guri daya ki shafe jikinki zuwa (1hr) daya, sai ki yi wanka da ruwan zalla da ruwan dumi ki shafe jikinki da ita sai ki kuma yin wanka.
Karanta>>> Tsumin Matan Aure Na Musamman Domin Inganta Zaman Aure
Kyaun Fuska
Idan Kina Son fuska ta yi kyau ki samu wannan abubuwan Sai ki hade su guri daya ki kirba su cikin turmi, ki mulmula ki rinka wanke fuska zaki ga yadda fuskar ki zatayi
1. Dettol
2. Sabulun Ghana
3. Garin zogale
4. Farar albasa
Karanta>>> Maganin Karin Hips Mai Sauki Ga Mata
Gyaran Fuska
Wanna hadin wanda ya kesa fuska tayi haske da annuri ta kore kurajen fuska, samu bawon kankana a rinka goge fuska da shi yana gyara fuska tayi sumul.
Karanta>>> Amfanin Kubewa Musamman Ga Ma’aurata
Gyaran Fata
Ku samu wadannan abubuwan kamar haka;
1. Lemun tsami
2. Bawon kwai
3. Kur-kur
Zaki hade su guri daya ki daka su sai ki rinka wanka dashi fatar mace zata goge tayi kyawun gaske.
Karanta>>> Ina Mata Masu Fama Da Rikecewar Al’ada Ga Magani Da Izinin Allah
Gyaran Fata
Ki samu wadannan abubuwan kamar haka;
1. Ganye magarya
2. Sabulun salo
Zaki daka ganyan magarya sai ki zuba a cikin sabulun salo ki rinka wanka dashi, yana gyara jiki.
Karanta>>> Dalilin Daya Sa Matan Hausawa Ke Tsufa Da Wuri Da Zarar Sunyi Aure
Gyaran Fata
✓ Ganyan magarya
✓ Man zaitun
✓ Man habbatussauda
Ana daka ganyan magarya a zuba cikin man zaitun da man habbatussauda shi ma yana gyaran fata.
Karanta>>> Maganin Toilet Infection Da Kuma Rashin Sha’awa Ga Mata
Gyaran Fata
Ki samu
✓ Lalle
✓ Garin ridi
Ana amfani da lalle kafin ki shiga wanka sai ki kwaba ki zuba garin ridi ki shafe jikinki zuwa (1) hr sai kiyi wanka.
Karanta>>> Sirrin Mallakar Miji Ba Boka Ba Malam
Gyaran Gashi
Ki samu
✓ Man zogale
✓ Man kwakwa
✓ Man zaitun
Zaki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki.
Karanta>>> Ingantaccen Matsi Da Bashi Da Illa, Kuma Da Kanki Zaki Hadashi.
Gyaran Gashi
Samu wadannan abubuwan kamar haka,
✓ Man zogale
✓ Ganyan magarya
✓ Kanunfari
Sai ki hade su guri daya ki rinka shafawa a kanki yana sanya tsayin gashi ya kuma yi laushi
Karanta>>> Maganin Kurajen Gaba Da Kaikayin Gaba Na Mata
Gyaran Kafa
Baki ba zuwa wajen wanke kafa madarar kinyi amfani da wannan hadin, ki samu wannan abubuwan kamar haka
✓ Man shanu
✓ Man kwakwa
✓ Man ridi
✓ Man alayyadi
Idan kafa tana tsagewa ko tana kaushi da daddare zaki hada wadannan mayamayen guri daya ki shafa a kafa Idab zaki kwanta bacci daddare sai ki daure da Leda da safe ki wanke da ruwan dumi ki shafa man zaitun da man ridi.
Karanta>>> Yadda Za’a Yi Amfani Da Kanunfari Wajen Magance Ciwon Sanyi
Maganin Ciwon Sanyi
Duk macen dake son ni’ima ta tabbatar mata, koda yaushe ta kasance cikin ni’ima to lallai ya zama dole ta magance matsalar ciwo sanyi.
Karanta>>> Amfanin ‘ya’yan kankana 7 a jikin Dan Adam
(Toilet Infection)
Domin magance wannan matsala ki samu wadannan kayan kamar haka;
✓ Hulba
✓ Bagaruwa
✓Habbatussauda
Ki hada hulba da bagaruwa guri daya, ki dafa idan ruwan ya sha iska sai ki zauna a ciki, kuma ki samu man habbatussauda kiyi matsi dashi.