Uncategorized

Wace Ce Ita (Who Is She) Chapter 50 Complete Novel

 

WACE CE ITA⁉️ (WHO IS SHE⁉️)

Unique Barakancy

                                  FIFTY📍

      Shiru tayi batace komai ba…..

Ganin shirun yayi yawa mami tace;;

     “Muna sauraranki baby tee”…..

Shiru ne ya sake biyowa baya yayinda zuciyoyin wasu ke bugawa, ba Deen kadai ba har khaleel dayasan ba’a daura ba hankalinsa a tashe yake jin tayi shiru……

Da mamaki umm ta kalleta tace;

     “Why are you taking time to respond, ko abinda kika fadamin ba gaskiya bane?”…..

     “Gaskiya ne!”….

Ta fada tana sunkuyar da kai…

     “Then answer us!”….

Dagowa tayi suka hada ido da deen da yake mata pleading look, sai mata signal yake akan tace eh, dauke kai tayi tace;

      “Ba’a daura ba!”……

Ai deen ji yayi kamar ya shaketa tsabar takaici, ta gama ce masa ta yarda zatace an daura all of a sudden ta chanza baki without second thought, seriously he felt betrayed, duk sai yaji zaman parlourn ma ya ishe shi, ba dan yanasan komai ya faru a idonshi ba daya tashi yayi tafiyarsa, dole ya zauna ita kuma sai ya tabbatar yaci ubanta da kyau idan suka hadu, saita gayamasa dalilin yaudaransa datayi…….. 

Gyaran murya abby yayi yace;

     “Toh Alhamdulillah munji daga bakinta dukda nima nasan ba’a daura auren ba saboda wakilci da suka nemi in musu wanda nayita jan abun saboda banaso suyi aure batareda amincewar iyayansu ba, ashe ya’yana ne bansani ba”…… 

Gyada kai dad yayi yace;

      “Masha Allah! Haka muke fata dama, ina amfanin yara suyi gaban kansu?”…..

      “Gaskiya ne, toh nidai inaso zan bawa khaleel auren fatima dan na masa alkawarin tsaya masa akan haka tin ba yau ba amma saida amincewarku duka!”…..

       “Na amince! Allah yasa ayi damu!”….

Mami ta fada tana murmushi……

Gyada kai dad yayi yana murmushin amincewa yace;

     “Ameen ameen”…..

Kallon umm Abby yayi yace;

     “Baki ce komai ba boddi?”…..

Wani irin bugawa kirjin deen yayi kamar shi aka tambaya, umm ce last hope dinshi akan kin yuwuwar aurennan, idan tace ta amince ai ya shiga uku, kallon Umm yayi yanata addu’ar Allah yasa su hada ido ya mata signal ko Allah zesa tace bata amince ba deep down kuma yasan be isa ya sata yin abinda batayi niya ba, saidai sam ko inda yake bata kalla ba……..

     “Ban amince ba!”…..

Deen ya jiyo muryar umm kamar a mafarki tace hakan, gyara zamansa yayi yanajin kamar an zare masa wani abu daya tokare masa kirji, ze iya cewa tinda yake umm bata taba abinda ya burgeshi ba irin wannan…..

Da sauri kowa ya dago ya kalleta suna mamakin jin furucinta dan basu taba expecting haka daga gareta ba duba da irin kokarin da shi khaleel yayi har tonawa mahaifinsa asiri yayi sannan a gabanshi aka ciwa mahaifinsa mutunci amma dukda haka rokonsu yake a bashi baby tee…..

       “Baki amince fa kikace boddi?”….

Abby ya tambaya dan ya sake tabbatar da abinda tace….

      “Kwarai!”…

Ta fada ba alamun wasa…. 

Abinda basu sani ba kuma shine da gangan tayi hakan badan bataso a bawa khaleel ba sai dan son ganin reaction dinsa da ita baby tee din, shin dagaske tana sonsa data bisa wata kasar a daura musu aure ko kuwa a giyar hauka tayi hakan?…..

Ai kawai sai ganin khaleel sukayi ya rarrafa ya tafi gaban umm, hawaye ne suka shiga zubo masa yayinda yakejin wani zafi a zuciyarsa, ko bacci beyi jiya ba saboda damuwa data masa yawa, ba karamin karfin hali yayi jiya ba na ganin halin da daddy yake ciki, yes yasan cewa daddy me laifi ne amma hakan bazesa ya manta irin soyayyar daya nuna masa ba, ga momma itama ya manta when last sukayi waya dan ko ya kira bata dauka kuma duk saboda tace ya rabu da wifey ya ki, wifey din da yake tinanin itace only hope dinsa ake nema a hanashi itama, inaa zuciyarsa bazata iya dauka ba…. 

Hannayensa biyu ya hade alamar roko hawayen na zuba a idonsa yace;

     “Dan Allah dan annabi umm ki taimakamin, idan kika hanani fatima nasan rayuwata tazo karshe, nasan abinda mukayi bamu kyauta ba but it was the only way out a lokacin saboda daddy ya ki daura mana aure, in baku bani auranta ba mutuwa zanyi, dan Allah ki taimaki rayuwa wallahi ina sonta tsakani da Allah”…..

Ya kareshe da fashewa da kuka…..

Sosai ya bawa umm tausayi ta kuma gane duk abinda yake fada is coming directly from his heart, amma ta girgiza kai tace;

     “Kayi hakuri khaleel na riga na mata miji ba tin yau ba”……

Baby tee na jin haka itama ta rarrafa gaban Umm, dafa kafafuwata tayi kamar zatayi kuka tace;

    “Umm dan Allah ki amince, ni wallahi shi nakeso”…..

Ba umm ba harta Deen da yake ganin ta yaudareshi tace ba’a daura ba beyi tinanin zata iya cewa tana son khaleel a gaban kowa ba…..

Dauke kai umm tayi kamar bata jita ba, sai kawai ta fashe da kuka itama, suka hadu sukaita rusa kuka ita da khaleel suna rokon umm akan ta amince, deen ko ji yake kamar yaje ya hadasu duka ya zane, shi khaleel din nema yafi bashi mamaki yanda yake kuka kamar mace, yanzu ita coward dinnan takeso ta aura? Ace kana grown up man ka tsaya kana kuka akan mace, wannan shine abun duka ba sanda, ita ko baby tee dama baya sata a lissafin mutanen dan haryanzu gani yake batasan me yake mata yawo akai ba…..

Tausayi suka bawa mami sosai harta kasa shiru, ta kalli umm tace;

     “A taimaka mana a amince umm, ko nima sai nazo na duka na tayasu kukan ne?”……

Cikin tausayi Abby shima yace;

     “Wlh kuwa boddi na dan Allah a duba lamarin”……

      “Ya kamata kam tinda suna son junansu”..

Dad shima ya fada…..

Murmushi umm da duk take sauraransu tayi sannan tace;

     “Na amince! Allah yasa hakan shi yafi alkhairi!”…..

Deen na jin haka da sauri ya zabura yace;

     “Toh ni ban amince!”….

Harararshi mami tayi tace;

     “Da wa yake bukatar amincewarka?”…..

Bata rai yayi yace;

    “Toh kuna nufin kun basa ita kenan? Haba mami!”…..

      “Insha Allahu, me za’a fasa da yardar Allah tinda itama tanaso”…..

     “Wannan me ta sani akan soyayya? Ya ma zaayi ku biyemata?”…..

      “Wannan kuma kai ta shafa”…..

Cije lips dinsa yayi yana tuno da plan b dinsa, kamar yasan za’a samu matsala shiyasa yazo a shirye, in wanchan beyi working out ba sai a koma wanchan…

      “Toh haka ake bawa mutum aure ba’ayi tests ba?”…..

Deen ya fada yana murmurshi ganin ya samo yanda ze dankesu cikin ruwan sanyi dan tsarin bappa ne ba’a taba bada aure sai anyi tests both mace da namiji….

Saida gaban khaleel ya fadi jin wannan furuci na deen, addu’arshi daya Allah yasa ita ba irin shi bace….. 

Cikin gamsuwa umm ta gyada kai tace;

     “Hakane, gobe sai aje ayi”…

Budar bakin deen yace;

     “Ba sai sunje asibiti ba, their genotype is both SS, technically be kamata suyi aure”….

 Kafin kowa yayi magana baby tee tayi saurin fadin;

      “Naji ni inason sa a haka”…..

Throw pillow din dake kusa dashi Deen ya dauka ya saita daidai dan bakinta ya jefa mata sannan a tsawace yace;

        “Dalla yi mana shiru manya na magana kina wani sa baki, inji kin kara cewa kina sonshi wallahi saina fasa miki baki fitsararriya kawai!”……

Mami ce ta dakatar dashi da fadin;

       “Sai me dan tace tana son sa? Karka kuskura ka kara mata tsawa dama!”…

Dad ne ya kalli Deen cikin rashin yarda da abinda ya  fada yace;

       “Ya akayi kasan genotype dinsu?”…

Shafa kansa yayi yace;

     “I’m a Doctor dad, I have treated both of them before!”……

       “Baka taba treating dina ba kuma ni ba SS bane!”….

Khaleel ya fada yana jin haushin deen……

     “Probably kana dan yaro lokacin kuma wallahi kai SS ne!”….

     “Kai kuma kana me a lokacin?!”….

Deen zeyi magana kenan umm ta dakatar dasu da fadin;

      “Enough! Gobe kawai suje suyi test duk wani required tests, abar zancen haka”….. 

Duk wannan abinda ake sameer na zaune yana jin kamar yayi kuka, so yake yace dan Allah shi su bashi sai yaga kamar ma basusan da zamansa a gurin ba, dama deen ne hope dinshi amma tsoron mishi magana yake, sai yayi tagumi yana tinanin ta yanda ze billowa al’amarin a fasa daurawa da khaleel a daura dashi……

Mami ce ta fara mikewa baby tee tabi bayanta da sauri dan sai a lokacin taji kunyar abinda ta fada a gaban kowa, ga Deen da bataso ta hadu dashi dan tasan haduwarsu bazatayi kyau ba, tana sane tace masa ta amince saboda tasan inba haka tayi ba sai yasan yanda yayi yasa kowa ya yarda ba’a daura ba tinda ta kula bayasan auren, itako tanasan darling khal dinta ……

Tashi umm tayi itama zata bar parlourn Abby ya mika mata ledar dake hannunsa yace ta bawa baby tee, karba tayi ta juya tashige, kamar jira deen yake ya tashi ya bi bayanta shima….

Tare suka shiga bedroom dinta, sai a lokacin ta kula dashi dan batasan yana biye da ita ba…..

Batace mishi komai ba ta zauna a bakin gado tana saka ledar da abby ya bata a cikin bedside drawer, tsugunawa Deen yayi a gabanta ya tallafe habarsa yace;

      “Umm meyasa kika amince?”…..

     “Because he deserves her!”….

Ta bashi amsa kai tsaye…..

Girgiza kai yayi yace;

    “He doesn’t deserve her! Kin manta abinda mahaifinsa yayi ne? Da shi kansa ma, idan kana son mutum tsakani da Allah ai bazaka daukeshi ku tafi wata kasar a daura muku aure batareda izinin iyayenku ba!”….

     “Nasan da wannan saif amma abinda nake so ka duba shine ko mahaifinsa da yake nufarta da sharri ya inganta rayuwarta ta wani fannin atleast ya bata ilimi, even though his intentions were not good amma badan shi ba da Allah kadai yasan a wani hali zamu tsinceta, shi kuma besan family member dinta ba tinda mahaifinsa ne ya kawota kaga basu da second option illa hakan da sukayi, nasan hakan is wrong but if you can put yourself in their shoes zaka gane sunyi hakanne saboda son da suke yiwa juna”…..

Numfasawa yayi yace;

     “Maybe shi yasan abinda yake amma baby tee is still very young for all this, trust me bata san menene soyayya ba haryanzu, dan Allah umm kubar zancen nan abarta tayi focusing akan karatunta”……

      “Saif ta riga ta nuna itama tana san auren to ya zamuyi? Kabari kawai a mata abinda takeso”….

     “Okay I’m not against tayi aure anymore, damuwata shine banaso ta auri khaleel!”….

Questionably umm tace;

      “And why?”….

Shafa gemunsa yayi yace;

     “Saboda na mata miji!”…..

Dariyar da bata shirya ba tayi tace;

    “Ai baka fadamin kayi adopting dinta ka zama ubanta ba, toh wa zaka aura mata?”….

     “Wani bawan Allah ne, far way better than this so called khaleel din!”…..

Umm bata bashi amsa ba sukaji sallamar mami baby tee biye da ita a baya…..

Wani irin kallo mami tayiwa deen tace;

     “Dama ina nemanka, na kula da take takenka akan aurennan, wai meye matsalarka ne?”

Bata rai yayi yace;

     “Fisabilillahi mami all this is too soon, yaushe ma akayi reuniting da ita da har za’a mata aure? For God’s sake she’s just 19 or something shine zaku wani mata aure, ko ku ba haka bappa ya muku ba, duk saida kuka gama degree dinku even older than her then, shine ita za’ayi rushing dinta”….

Yana fadin haka yabi ta gefensu ya fice, binshi da ido sukayi gabadaya with shock, har mami zata bi bayansa umm ta ruko hannunta tace;

     “Karki bishi yaya, barni dashi zanyi maganinsa! Sai ya fadamin wanda yace gobe goben nan za’a daura mata aure”…..

     “Allah ya kyauta”…

Kawai mami ta fada tana dawowa ciki sosai….

Nunawa baby tee drawer umm tayi tace;

     “Ki bude akwai sakonki a ciki”…..

Budewa tayi taga wata medium sized bakar leda, zarota tayi ta budeta, wayoyi ne a ciki guda biyu da latest Samsung da latest iPhone sai AirPods da headphone harda SIM cards sai wata yar takarda a gefe, ajyewa tayi ta fita da sauri tuno da wayar umm data dauka sanda zasu gudu da khaleel, kasa ta sauka ta shiga daya daga cikin bedrooms din da take tinanin ta ajye jakarta a ciki, tana zuwa kuwa taga jakar, tana bude jakar taga wayar a ciki, dauka tayi ta koma sama da sauri, tana shiga dakin umm ta mika mata wayar, kallonta umm tayi da mamaki tace;

     “Dama ke kika dauka dagaske?”….

Sunkuyar da kai tayi tace;

    “Eh nice but wallahi I don’t mean stealing it, dama zan dawo miki dashi”….

     “It’s okay, wannan abby ne ya kawo miki, kisa SIM cards din a ciki sai ki jona a chargy”….

Ba musu tayi hakan, bayan ta jona su duka ta shiga karanta note din dake ciki, a fakaice tayi squeezing note din tana kokarin fita ta yar umm ta dawo da ita da fadin;

     “Menene a hannunki?”…

Da kame kame tace;

     “Bbbb..aabu komai”….

     “Hand it over to me!”…

Mika mata tayi da sauri tana kallon gefe…

Budewa umm tayi ta karanta content din ciki, ta dago ta kalleta tace;

      “You can’t change the fact that he’s your father ko da yayi hakan da gangan dagabaya ya tuba barema ba a cikin hayyacinsa yayi ba, ki shirya before that time!”….

Mami ce tace;

     “Wai meya faru ne?”….

Mika mata takardar umm tayi tace;

      “He’s inviting her for a launch shine takeso tayi declining by throwing the piece away”….

Karba mami tayi tana fadin;

     “This is not right daughter why would you decline your father’s offer?”……

Ciki ciki tace;

     “Ai zanje”….

Karanta abinda ke ciki mami tayi…. Sai kuma tayi dariya ta kalli umm tace;

     “I would be glad if you come along with your mom! Hahaha to kinji fa yace ta tawo da mamanta, sai ki shirya kuje”…..

Daure fuska umm tayi tace;

      “Ba wani zuwa da zanyi, ita dai daya zamewa dole zansa taje”…..

      “Da dai kin daure kinje ko Allah zesa baby tee tayi settling dinku”…

Mami ta fada cikin tsokana….

Dauke kai umm tayi taki kulata, haka mami ta karaci dariyarta ta fice…..

       Deen na sakkowa yaci karo da sameer a inda kowa ya tashi ya barsa, yana zaune sai zufa yake, kana ganinsa kasan akwai abinda yake damunsa, kallonsa Deen yayi ya tabe baki yace;

     “Kai dama kananan haryanzu?”….

Kamar wanda aka zungura yace;

     “Kai nake jira boss”….

    “Tashi muje”…

Mikewa yayi yabisa a baya, garden Deen ya nufa sameer na biye dashi, guri suka samu suka zauna sannan strictly Deen yace;

     “Ina jinka”….. 

A raunace sameer yace;

     “Yanzu shikenan an bawa khaleel ita? Ni banma san haka takeda kyau ba sai da naganta yau”….

A fusace Deen ya juyo kamar ze dakesa yace;

     “Me kace?”….

Sameer be gane gatse ya masa ba yace;

      “Cewa nayi she’s too beautiful, dan Allah ka taimakamin in sameta, God ji package dan Allah”…..

Ai kawai  sameer shafa bakinsa yayi yaji jini, ashe tin kafin ya dire Deen ya sauke masa naushi a baki, da mamaki ya shafo jinin yana kallon Deen, so yake ya tambayesa abinda ya fada offensive a cikin maganarsa daze masa haka amma ya kasa saboda yanda bakinshi ke masa zugi harji yake kamar baze iya sake magana a duniya ba, murza idonsa yayi yanabin ciyawun da yake akai da kallo, sai a lokacin ya gane Deen cillashi yayi ma, ko kafin ya gama tantance yanayin da yake ciki kawai yaga mutane akansa, daukanshi sukayi chak sukayi gurin deen dashi, wani mugun kallon Deen yayi wa sameer yace;

      “Ku kaishi ku ajye min shi a inda kuka ajye ubansa! Ku kuma tabbatar ya jiku da frog jump kafin nayo kansa!”….

Sama sukayi da sameer yanaji yana gani aka sashi a mota sai barack din sojoji”…..

   Mami dakanta ta shirya baby tee cikin wani lilac caribbean fitted high waist skirt sai long sleeve top daya zauna mata sosai kamar dan ita aka halacci kayan, light make-up mami tayi mata daya kara fito da kyawun kyakkyawar fuskarta me tafiya da imanin duk wanda yayi tozali da ita, lips dinnan yasha lip gloss sai sheki yake, gashin idonta kuwa kamar wacce tasa eye lashes saboda mascara da mami tasa mata, sai kwalli da eye liner daya kara fito da kyawun  idon kamar ka saceta ka gudu, sosai kayan suka amshi jikinta kowani curves na jikinta ya fito kadama hips dinta da butt dinta suji labari dan karyar lafiyayyen namiji ya ganta a haka ya kwana lafiya, karyar mutum kuma ya mata kallo daya ya dauke kai, har gel akasa a gashin ta gaba sannan ta yane kanta da karamin mayafin kayan, tirare mami ta fesa mata ta hau yi mata hoto sai kodata take wai duk familyn shuwa babu me kyanta, ita yarta tafi ta kowa….

Umm na zaune tana kallon duk abinda suke saidai ko uffan batace ba, ita mamaki ma mami take bata yanda take biyewa baby tee, mami da kowa yasan boss ce bata wani shiga sabgar yara amma yanda take biyewa baby tee kai kace kawarta ce…… Kallon baby tee Umm tayi aranta tace ‘fata barakallahu ahsanul khaliqeen’ dan ko ita data haifeta tasan Allah yayi kudurarsa anan, sai kuma ta kalli mami tace;

     “Bazata chanza mayafinnan ba kuwa? Kamar jikinta na nunawa ko?”….

      “Waye ze ganta bayan kinsan a vip section Muhammad yake zama a restaurant? Maybe ma ba’a restaurant zasuyi launching din ba, it can be in his house”…..

      “Hakane, Allah ya kiyaye hanya”…

Umm na fadin haka taja bakinta tayi shiru…..

Saida mami ta rakata har stairs sannan ta dawo gurin umm…..

     “Har kin dawo daga rakiyar kenan?”…

Umm ta tambaya tana dariya….

      “Eh dawo”…

     “Toh sannu, yauwa yaya kinyi waya dasu bappa kuwa? Inata kira bana samunsu”….

    “Naga message dinsa dazu, sun samu network issue ne a maiduguri, ni so nake mu fara shiri ma akan welcome party din da zamu yiwa baby tee, kinsan kuma su anna da gayya nasan bazasu tawo su kadai ba”….

   “Yeah hakane, gashi kuma ina tinanin zanje UK jibi but under probability”…..

     “Me zakije kiyi kuma, gaskiya ko menene ki ajyeshi for now”…

Murmushi umm tayi tace;

     “Rai fa ake magana akai yaya, just pray komai ya tafi daidai if not I have to go”….

    “Toh Allah yasa, kinga bappan ma yana kiranki”….

Mami ta fada tana mikawa umm wayarta, karba tayi ta dauki wayar da sallama…..

       Saida ta fara zuwa fridge ta dau ruwa tasha sannan ta nufi kofar parlourn, murdawa tayi ta bude daidai shi kuma ya murda kofar ze shigo, Ido hudu sukayi da deen da ya hau binta da wani shu’umin kallo!!!…..

Domin Sauke Littafin Sai Ku Dannan inda aka saka Download Now!

Back to top button