Uncategorized

Kishi Da Aljan Chapter 4 Complete Novel

Be gama fita daga cikin ɓacin ran da sarauniya Aziza ta barshi a ciki ba yaji ana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin na shi

Yi yayi kamar ba ze buɗe ƙofar ba, 

duk a tunanin shi ko kunnen shi ne ke jin hakan.

Seda yaji muryar Abbah na kiran sunan shi tukun yai azamar buɗewa.

Kanshi a ƙasa ya buɗe ƙofar, bece komi ba se sadda kanshi da yayi saboda irin kallon da Abbah ke binshi da shi

Bayan kallon shi da yayi na ƴan mintuna Abbahn yace

“Me ya sami idon ka?”

Be ɗago ba, yace

“Bacci na tashi ne Abbah”

Ba dan Abbahn ya yarda ba yace

“me ya samu wayar ka itama na kira baka ɗaga ba?”

A hankali Abdul ya kalli Abbahn yace

“Ban gani bane Abbah”

Juyawa Abbahn yayi sannan yace

“ka same ni a palour na in ka kintsa”

Da “to” kawai Abdul ya iya amsawa shima ya juya cikin ɗakin

Toilet ɗin shi ya shiga ya watsa ruwa a gurguje,

Sanda ya fito daga wankan ya iske an ciro mishi kaya daga cikin kayan shi an aje a bakin gadon shi suna ta zuba ƙamshi,

 a gefe kuma ga brush da lotion ɗin da yake shafawa a aje

Se kuma agogo a gefe, se daga ɗayan gefen kuma takalmi ne an goge shi tas se ɗaukar idanu yake

Komi dai da Abdul ya saba amfani da shi wajen shiryawa an aje mashi shi.

Koda Abdul yai arba da kayan, tsaki yaja yace

“aikin banza, ƴar wahala kawai”

Be bi ta kan kayan ba, ya buɗe walldrop ɗin shi ya ɗakko wasu kayan ya saka, 

ya ɗauki turare ya feshe jikin shi da shi, ko agogon ma be ɗauki wanda aka aje mi shin ba, wani ya ɗauka ya ɗaura, tsabar takaici haka ya haƙura be shafa mai ba tunda dama guda ɗaya ne da shi, kuma takaici ya hana shi ya ɗauki wanda aka aje domin shi.

Wayoyin shi ya ɗauka ya saka a aljihu, sannan yai hanyar fita daga ɗakin

Gab da ze ƙarasa ficewa daga ɗakin yaji muryarta tace

“Bazan taɓa gajiya da hidimar ka ba Azizun Aziza, zan ta lallaɓa ka har in ɗau cikin ƴaƴan ka, kaga daka nan nasan baza ka taɓa juya min baya ba”

Bece komi ba, be kuma nuna yaji me tacen ba, 

sema ƙarasa ficewa da yai daga ɗakin ɗauke da addu’ar fita a bakin shi.

Direct wajen Abbah ya nufa,

Yana shiga ya iske shi zaune, ummie na gefen shi ta na yanka mishi Apples yana ci

Sallama yayi ya ƙarasa shiga ciki, ummie ya gaisar sannan ya ce

“Gani Abbah”

Wata ƙatuwar envelop dake aje can gefe Abbah ya nuna mishi yace

“Malam Hamza zaka kai wa, sannan kace ina miƙo gaisuwa ta kafin nazo”

Da hannu biyu Abdul ya ɗauki envelop ɗin, har ya juya ze fita Abbahn ya sake kiran shi ya dawo

“Kar ka je mishi da wannan ɗingilallun kayan, kaje ka saka manyan kaya kafin ka tafi”

Da “to” kawai Abdul ya amsa bayan ya musu sallama ya fita.

Ɗakin shi ya koma, sannan ya cire kayan jikin shi ya sake buɗe walldrop ɗin shi

Da mamaki Abdul ya waro idanun shi waje  yana kallon kayan shi da sukai ciɗu-ciɗu da datti, 

har wani tsami-tsami suke yi tsabar dauɗa

Sororo ya tsaya, tsabar malolon baƙin ciki da ya cika mishi rai ya sa shi kasa tunanin komi,

Ya daɗe tsaye a gaban wallɗrop ɗin yana kallon yarda kayan suka sauya daga wankakku gogaggu e zuwa masu datti.

Har ya fara maida kayan shin da ya cire, idanun shi suka kai kan manyan kayan dake aje a gefen gadon shi har yanzu,

Ba wani tunani na biyu, haka ya ƙarasa ya ɗauki kayan ya saka, ya ɗora hula a kai sannan ya ƙara fesa turare akan wanda aka saka mishi a kayan

Yana cikin fesa turaren yaji dariyar ta daga bayan shi

“hhhhh, na gaya maka dama, be kamata ka rinƙa musu da duk wani abu da nace maka ba, 

kaga ko banza ka wahalar min da kanka,   kuma kayi sahu biyu”

Tsaki me sauti sosai Abdul ya ja, 

Ɗaukan envelop ɗin da Abbah ya aike  shin yayi, sannan ya rifo ɗakin ya nufi inda motar shi ke a ajiye a wanke tas itama se ƙyalli take, yana gani yace

“ƴar wahala kawai”

Jawo ɗakin yayi yana ƙoƙarin rufewa, sarauniya Aziza tace

“ai ka bari na tafi tukun kafin ka kulle ƙofar ko?”

Ta ƙara da “jeka kawai zan rufe, me zaka ci kafin ka dawo?

Be tanka mata ba be kuma ƙara taɓa ƙofar ba yai gaba abinshi.

Yana tafe yana jin ana take mishi baya har ya je ze buɗe gate, 

kafin ya kai ga taɓa gate ɗin aka buɗe mishi,   

ko a jikin shi ya koma ya shiga motar shi ya fice a gidan

Ta mirrow ya hango an tura gate ɗin kamar yarda aka buɗe mishin.

Tafiya kaɗan ce ta kai shi layin gidan malam Hamza

A ƙofar gidan yayi parcking, 

Ya jima zaune a cikin motar ya kasa fita, wani nauyi yaji kanshi yai mishi, ga wata kasala da ta rufe shi har wani bacci-bacci ke ƙoƙarin kama shi.

Seda Abdul yayi da gasken gaske sannan ya iya yunƙurawa ya fito motar da ƙyar ɗauke da envelop ɗin a hannun shi

Jingina ya sake yi da jikin motar, a zuciyar shi yake jin kamar ma ya juya kar ya shiga

Ya daɗe anan ɗin ma kafin daga baya ya ƙarasa kusa da soron gidan

Leƙa kanshi yayi yai sallama sannan ya ɗan dawo baya,

Be kai minti ɗaya a tsaye ba kalid ya fito bayan ya amsa sallamar

Kallon Abdul yayi ya miƙa mishi hannu suka gaisa,

Abdul yace

“Malam fa?”

Kalid ɗin yace “yana ciki, yanzu ze fito sallah”

Rufe bakin shi kenan, Malam Hamza ya fito, yana ganin Abdul fara’ar fuskar shi ta ƙaru, yace 

“idon ka kenan Abdul’aziz?, gani yayi wahala”

Kan Abdul a ƙasa yana shafa ƙeyar shi murmushi ɗauke a fuskar shi yace 

“Aiki ne ya ɓoye ni Abie”

Murmushi kawai malam Hamza yayi yace

“to mu ƙarasa masallaci muyi salla se a gaisa”

Su ukun suka juya suka nufi masallacin dake manne da jikin gidan malam ɗin, bayan Abdul ya maida envelop ɗin cikin mota shima ya bi bayan su.

Tunda sukai tozali da malam Hamza(Abie) ya dena jin juyin da kan shi ke mishi,

Alwala ya ɗaura anan bakin masallacin.

 sune a sahun gaba aka kabbara sallah, 

Mlm Hamza na a ta raka’a biyu, bayan ya gama karanta fatiha, ya shiga sura, yayi ɗan nisa a cikin surar da ya jaa ya kakare.

Dai-dai nan Zainab tana daga wajen windon masallacin da ke manne da harabar cikin gidan nasu taji kakarewar Abie

Ya maimaita ayar kusan so biyu, da dai taji be ƙarasa ba, ta ɗan daga murya kaɗan yarda ze iya ji ta gyara mishi.

Karaf muryar Zainab a kunnen Abdul dake sahun farko, a zuciyar shi yace

“ME MADARA”.

Har wani lumshe idanu yake jin sautin muryar ta

Da sauri Abdul ya kori sheɗan ya maida hankalin shi ga sallar har suka idar.

Da yake yau Abie yana hutu bashi da masu ɗaukan karatu yasa be wani jima a masallacin ba ya wuce gida

A babban soron gidan na shi suka zauna shi da Abdul, se kuma Abubakar da ɗa ne na biyu shima a wajen Abie, kuma abokin Abdul ne sosai, 

yana yin aikin junan su ne yasa haɗuwa tai musu wahala

Envelope ɗin da Abbah ya aike shi da ita ya ajiye a gaban Abie, kan shi a ƙasa yace 

“Abbah yace a gaishe ka, kuma yana nan shigowa shima”

Murmushi Abie yayi bayan ya amshi envelop ɗin ya aje a gefen shi na dama, 

Kallon yarda Abdul ke ta zufa yake kamar wanda yai ƙarya aka turke shi a gaban alƙali

Abie yace

“ina amsawa, shidai baya gajiya da ɗawainiya”

Shafa goshin shi yayi ya ɗan share zufar, 

be dai ce komi ba se murmushin yaƙe da yake ta zabgawa, 

jin shi yake a ƙuƙƙule ta ko’ina a jikin shi,

Allah-Allah yake ya bar wajen Abie,

So yake ya tashi daga wajen, amma ji yake kamar an ɗaure shi, ga kuma azalzalar da zuciyar shi ke mishi na ya bar wajen

Daga can ya ƙara tsinkayar muryar Abie na tambayar shi

“Ya aikin naka?”

Kafin  Abdul ya ba shi amsa suka fara jiyo kukan mujiya daga can wajen soron

Da mamaki a fuskar Abie ke kallon direction ɗin inda yake jiyo kukan mujiyar, 

Haka Abubakar ma, 

Abubakar ɗin ne ya miƙe da sauri yace “bari a kore ta Abie, mujiya da tsakar rana”

Dakatar da shi yayi, yace 

“Rabu da ita, shi ga gida a haɗo ma Abdul ruwa yasha”

Ba musu Abubakar ya juya ya shiga gidan ya barsu su biyu a soron.

Abubakar na shiga ciki, Abie ya tashi da kanshi ya leƙa, 

ido hudu sukai da kyakkyawar farar mujiyar,

Ƙatuwa da ita.

Kusan seconds suna kallon juna, kafin daga bisani mujiyar ta tashi ta bar wajen a guje, 

Akan idon Abie, mujiyar ta ɓace ɓat.

Abdul na zaune dunkum, besan wainar da ake toya wa ba

tunda ya fara  jin kukan mujiyar hankalin shi yai nisa, nutsuwa yai sosai yana sauraron sarewar da ake mishi me shiga zuciya da saukar da damuwa

Har Abie ya dawo ya zauna, be sani ba, kiran sunan shi yayi nan ma shiru,

Shima se yai shiru yana zuba mishi nashi manyan idanun inda anan Zainab ta gada,

Kallon shi yake tare da nazartar yanayin da Abdul ɗin ke a ciki, da kuma ganin da yai wa mujiyar nan da tabbas yaga alamu tattare da ita na ba mujiyar bace

A hankali cikin nutsuwa Abie ya sake kiran Abdul, shi kuma a dai-dai nan ya dena jin sarewar nan,

Buɗe idon shi yayi da suka kaɗa sukai ja ya kalli Abie yace

“Ni zanzo in koma Abie”

Kallon shi Abie yayi da ɗan damuwa a fuskar shi yace

“Meke damun ka Abdul?”

Sunkuyar da kanshi ƙasa Abdul yayi, yace

“Bakomai Abie” amma a can ƙasar zuciyar shi ji yake inama ze iya faɗa mishin.

Murmushi kawai Abie yayi yace

“Se dai in ba zaka faɗa min ba, 

amma duk wanda hankalin shi ze kau besan me ake ba na ɗan wani ƙanƙanin lokaci, 

to tabbasa da dalili, amma tunda ba zaka faɗa min ba, shikenan, Allah yai mana maganin abun da ba zamu iya ba”

Ba dan ran Abdul ya so ba ya amsa da “amin Abie”

Abie ya ƙara cewa

“kuma ka dage da azkhar Abdul, na san ka a kwanakin baya ba ka da wasa sam, sedai yanzu ne ban sani ba tunda ka gujeni ka dena zuwa ballanta na in san damuwar ka”

Still murmushi Abdul yayi, be kuma ce komi ba se shafa ƙeyar shi da yake ta yi.

*********

Gaskiya Mama ba zan je gidan Iya ba yau, in na tafi waze kular min da jariran nan?

Mama tace “kin gaji da samun ladan kenan?”

shiru zainab tayi tana ci gaba da shafa bayan ɗaya daga cikin magunan,

kamar warda ta tuna wani abu, ta miƙe ta shiga ɗakin ta, 

tayi wankan ta dama tun ɗazu, 

hijabin ta brown kawai ta ɗauka se wata jaka warda a ƙalla zata ɗauki kaya kala biyu ko uku ta ajiye anan gefen gadon ta.

Fitowa tayi ta ɗauki kwalin da magunan ke a ciki tace

“mama bari in shigar da su ɗaki, kar inzo na tafi ayi ruwa ya salwantar min dasu”

“koke fa” cewar mama da ta miƙe ta shiga kitchen

Zainab na shiga ɗakin, ta buɗe wannan jaka da ta ɗakko ta kwashe magunan ta tas ta saka su a ciki ta zuge zip ɗin, ta bar musu kaɗan inda iska zata rinƙa shigar musu.

Seda ta fito ɗakin ta leƙa taga mamar na sabgar gaban ta, ta koma ɗakin da gudu ta ɗauki jakar ta fitar da ita ƙaramin soron gidan ta ajiye, sannan ita kuma ta koma ciki.

Ƙaramar pose ta ɗauka se wayar ta da ta saka a ciki, se kuma madara data ƙulla a leda itama ta saka a ciki ta fito, ta nufi inda take jin motsin mama, tace

“Na shirya mama zan tafi”

Mama tace “ko kefa zainabu na, a gaishe mana da iya da kyau”

Kuɗin Napep ta bata wanda ze isheta zuwa da dawowa 

Tana zuwa soron ta ɗauki jakar ta, seda ta duba taga lafiyar su tukun ta rufe tai gaba abun ta.

Tafito dai-dai Abdul na sallama da Abie, 

Da zazzaƙar muryar tai musu sallama tana tsaye daga bayan su, 

Abie ne kawai ya amsa,

Abdul kam kamar wanda aka ingiza ƙeyar shi cikin mota, shigewa yayi, gaba ɗaya sallamar ta tana mishi amsa kuwa a kunne

So yake ya waiga, amma wuyan shi ya ƙame ƙam a inda yake, 

Yayi yayi ya waiga ɗin amma ya kasa,

 anan take sarewar nan ta fara tashi, nan da nan jikin shi ya mace kasalar gaske ta rufe shi

Har Zainab ta gama yi ma Abie sallama ta tafi Abdul be sani ba, 

Shiru Abie yayi yana ƙara nazartar yanayin Abdul ɗin da bema san yana kallon shi ba, 

Kusan minti biyar ya ɗauka kafin sarewar ta ɗauke, hankalin shi ya fara dawowa jikin shi.

Bayan ya nutsu, ya kalli Abie dake tsaye har yanzu yace murya a sanyaye

“Zan ƙarasa gida Abie”

Murmushi Abie yayi ya shafa kan Abdul yace “kace ma Abbahn ka ina son ganin shi duk sanda ya samu lokaci”

Da “InshaAllah” Abdul ya amsa, sannan yaja motar shi yai gaba, yana ta kallon hanya ko Allah ze sa ya ƙara tozali da fuskar ta.

ko da Abdul ya je gida bece ma Abbah ko mi ba game da saƙon Abie, 

Sedai saƙon gaisuwar shi da ya isar

Ta ɓangaren Abie kamar yasan Abdul baze isar da saƙon shi ba, 

Bayan sun gama karatun dare ya ɗauki waya ya kira Abbahn da kanshi yace

“Naga saƙo Alhaji Bukar, Allah ya ƙaro baɗi me albarka”

Da ladabi Abbah ke amsa Abie, akwai girmamawa me ƙarfi a tsakanin su

Tunda Abie yaji suna gab da sallama amma Abbah be mishi maganar zuwa ba ya ƙara tabbatar da zargin shi akan Abdul.

Gyaran murya Abie ya sake yi yace

“Alhaji Bukar, nace in ba damuwa ina son ganin ka a gidana, akwai muhimmiyar maganar da nake so muyi da kai akan Abdul’aziz”

Cikin ladabi Abbah yace

“Ko yanzu kace inzo zan zo Allah gafarta malam”

Murmushi Abie yayi, sannan yace

“Ah, dare yayi yanzu, mu barwa gobe in Allah ya kaimu”

Abbah yace “Allah ya nuna mana, kafin in wuce office da safe zan shigo inshaAllah”

A haka sukai sallama cike da girmamawa.

Gaba ɗayan su suna zaune ana cin abincin dare, 

Abdul ne kawai babu a wajen

Ummie ta kalli Rukayya da itama zaman ta kenan tace

“Ruky, je ki kira min yayan ku”

da “to” ta amasa, sannan ta tashi ta fice

Ta ƙofar kitchen Ruky tabi, tana tafe tana amsa call ɗin saurayin ta, gaba ɗaya hankalin ta na ga wayar da take har ta ƙarasa ɗakin Abdul ɗin dake rufe.

ƙwanƙwasa ƙofar tayi kusan so uku tukun Abdul ɗin ya amsa da

“waye”?

Ruky tace “Nice yaya Abdul, ummie ce tace ka zo”

“gani nan” kawai ya ce yaci gaba da goge jikin shi da towel

Memakon Ruky ta juya ta koma ciki tunda ta isar da saƙon, amma ta samu waje ta zauna tana ci gaba da amsa call ɗin ta.

Abdul na tsaka da goge jikin shi, yaji an karɓi towel ɗin hannun shi ana goge mai jiki

Gaba ɗaya jikin shi ya hau karkarwa, yana nonnoƙewa, ga wani irin nauyi da harshen shi yayi mishi, magana yake son yi amma ya kasa, 

Da ƙyar da yardar ubangiji ya samu maganar ta fuzgo ta fito da ƙarfi yace

“meye haka!”

Yarda maganar ta fito da ƙarfi yasa gaba ɗaya lungun ɗakin na shi ya amsa, har Ruky dake zaune tana waya taji

A ɗan tsorace ta miƙe ta ƙarasa bakin ƙofar Abdul ɗin ta sake ƙwanƙwasawa tace

“yaya Abdul kai da wa?”

Shiru taji be bata amsa ba, se maganr shi da take jiyowa da ƙarfi kamar wanda hankalin shi ya fara tafiya, yana cewa

“Nace ki sakar min towel ɗina, ana so dole ne, wallahi ki fita harka ta, ki rabu dani na gaya miki”

Cikin tsoro da mamaki Ruky ta tura ƙofar ɗakin ta shiga,

Gani tai yayan nasu na ta bin towel yana faɗin “ki bani abu na”

Towel kuma na ta zagaya ɗaki shi kaɗai ba wanda ya riƙe shi.

Wani razanannen ihu Ruky ta buga, ta zube nan a ƙasa sume.

Kamar saukar aradu suka jiyo ihun Ruky, da guda ummie da Abbah suka miƙe su kayo waje

Fauza da Amal ma suka taso, har rige-rigen fita suke, 

kai tsaye side ɗin ɗakin Abdul suka nufa, tunda an san nan aka aiketa

Kafin su ƙarasa ɗakin yaci nasarar kama towel ɗin, yana ta zuba uban haki, kallon Ruky yake ko ƙiftawa babu, tunani yake a yaushe ne ma ta shigo ɗakin be sani ba.

Kara tambayar kan shi yayi yace “badai ta ganni daga ni se gajeran wando ba”?

Be gama tambayar kanshi ba ummie ta banko ƙofar ɗakin a firgice, 

Hankali tashe Abbah na ya shigo.

A tsorace ummie ta kalli Ruky, sannan ta kalli Abdul da gaba ɗaya shima ya ruɗe.

A haukace tayi kan Abdul ta finciko shi tace

“uban me kayi ma ƴar mutane?” ba tambayar ka nake ba ka bini da idanu?

Abdul be ce komi ba se kallon Ruky dake kwance yake, 

Ƙara kallon kanshi yayi, sannan ya tuna daga shi fa se gajeran wando,

Da sauri ya juya ya ɗauki jallabiyar shi dake gefen gadon shi ya saka

Fashewa da kuka ummie tayi ta koma kan Ruky da Abbah ke ta fama yaga ta farfaɗo,

Cikin kuka ummie tace

“wallahi tallahi in nagane wani abu kai ma ƴar mutane bazan ƙyale ka ba”

Ba wanda yace mata komi, suna dai ta ƙoƙarin su ga numfashin ta ya dawo,

Abdul kam kamar mutum-mutumi, abu biyu zuwa uku ne suka haɗe mishi,

Me maganar ummie ke nufi?

Sannan yaushe Ruky ta shigo ɗakin?

Da sauri shima ya tsugunna a saitin da Ruky ke kwance a sume, a kasalan ce yace

“ku matsa in duba ta”

Yarda yayi maganar a kasalance, zargin ummie ya ƙaru.

Cikin fushi ummie ta miƙe ta saka hannun ta biyu ta hankaɗa Abdul da iya ƙarfin ta.

Caraf kafin Abdul ya kai ƙasa aka tare shi, cak ya tsaya da ƙafafun shi,

Tashin hankalin da suke a ciki ne ya hanasu lura da yarda Abdul ya cake cak a ƙafar shi

Irin wannan hankaɗar in ba abinda ya tare ka dole ne ka sha ƙasa.

Kafin ummie ta koma kan Ruky, akai wurgi da ita gefe itama, ji kake “ƙumm” ta bige kai da gefen kujera.

Fauza da Amal ne suka ɗagota, bakin ta ya mutu murus, se zazzaro idanu take

Taimakon gaggawa Abdul ya ba Ruky, Abbah na tsaye a kan su Ruky ta dawo hankalinta

Tana buɗe idon ta tana tuna abunda ta gani, wani ihun ta ƙara bugawa ta miƙe zumbur tana neman ƙwace riƙon da Abbah yai mata,

Faɗi Abbah yake 

“Ki nutsu mana, me ya faru? me akai miki?”

Inaaa,

 kwata-kwata Ruky bata jin abinda Abbah ke faɗa, Abdul kawai take nunawa tana ci gaba da ihun ta.

Ummie kuka, Fauza da Amal ma suka ɗauka, gaba ɗaya sun cika ɗakin da iface-iface

Gaba ɗaya idon Ruky sun firfito waje tsabar tashin hankalin Abinda ta gani

Da ƙarfi Abbah ya daka musu tsawa, yace

“Bana ciki da shashancin banza, da kukan ta zamuji ko kuwa da naku kukan mara dalili?”

Fuuu, haka ummie ta wuce bayan ta finciki hannun Ruky daga wajen Abbah tai waje da ita

Ɗakin ya rage daga Abbah se Abdul, se kuma Fauza da Amal da kukan su yai ƙasa ba kamar ɗazu ba.

Kallon Abdul Abbah yayi yace 

“ka same ni yanzu a ciki”  ya maida idon shi kan fauza da Amal yace “ku kuma ku shige muje”

Wucewa sukai gaba, Abbah yabi bayan su, har yasa ƙafar shi a waje ya juyo ya kalli Abdul da idon shi ya kaɗa yai jaa, jijiyoyin kanshi sun fito sun yi  ruɗu-ruɗu, 

ƙaɗa kanshi kawai yayi yana ƙara jin tausayin ɗan nashi a can ƙasan zuciyar shi.

Dirshen Abdul ya zauna, yana dafe da kanshi yai shiru yana sauraran bugawar da zuciyar shi keyi

A hankali ya ɗora hannun shi a saitin zuciyar shi yace

“meke damuna?”

Be kai ga cire hannun shi daga ƙirjin shi ba yaji tace

“KAYI HAƘURI, NI WASA NAKE MAKA FA”

Rintse idonshi yayi da ƙarfi jin yarda maganar ta yasa tsiga jikin shi tashi

“BAKA CE KOMI BA MASOYI?”

Be ce komin ba, be kuma nuna yaji me take faɗa ba.

Tunawa da yayi Abbah yace ya same shi a ciki, yasa ya miƙe yana gyara maɓallin gaban jallabiyar shi.

Da ƙarfi aka maida shi ya zauna,

A hankali ya fara jin hannun ta na yawo a jikin shi, tun daga kanshi har zuwa ƙeyar shi da ta wajen wuyan shi take shafawa.

A saitin kunnen shi ta fara mishi magana

“BANA SON IN MAKA DOLE AZIZ, YA KAMATA KA GIRMAMA BUƘATA TA, 

NA KULA DA KAI TUN BAKA SAN KAN KA BA, NA BAKA ABINCI A LOKACIN DA BAKA DA WANDA ZE BAKA, NA TEMAKA MAKA A MAKARANTA NA BUƊE MAKA IDANU KANA GANI DA GANE KOMI HAR KA ZAMA ABIN TINƘAHO”

Cikin tsawa Abdul ya katse ta, yace

“Na roƙeƙi da kiyi min hakan? me yasa baki ƙyale ni ba a lokacin?”

Hucin iska yaji a kunnen shi, kamar an hura mishi iska a kunne, tace

“MU BAR MAGANAR MASOYI, 

ALFARMA NAZO ROƘA A WAJEN KA, NA SAN KUMA ZAKAI MIN”

Bata jira cewar shi ba taci gaba

“ALFARMAR ITACE, KAR KA YARDA DA DUK WATA MAGANA DA ABBAH KO WANCAN WAWAN MUTUMIN DA KAJE WAJEN SHI ZASU CE MAKA, SANNAN INA ƘARA NEMAN WAJEN ZAMA DAGA GARE KA”

Wawan tsaki Abdul ya ƙara ja sannan ya yunƙura da ƙarfi ya fice ya bar mata ɗakin.

Sanda ya shiga ɗakin an samu da ƙyar Ruky ta dena zabure-zaburen da take

Amma tambayar duniyar nan Abbah ummie sun mata taƙi cewa komi

Tsayawa yayi ya kalli iyayen nashi fuska ba yabo ba fallasa yace

“Ummie kina zargina da aikata mummunan abu ne?, ni sam na kasa gane me kike nufi da kalaman bakin ki”

Da ƙarfi ummie ta yunƙuro, tayo kan Abdul da ko ɗar be ji ba, ta nuna shi da yatsa tace

“ihun me yarinyar mutane tayi? me kai mata?”

Rai ɓace Abbah yace “Bana ce ki bar maganar nan ba Asiya?”

A hankali Abdul yace 

“Ban mata komi ba, kuma bazan taɓa mata komi ba, tun farkon zuwan ta gidan nan bata taɓa burge ni ba, dan haka yanzu ma ba zata taɓa burge nin ba”

Da mamaki Abbah da ummie ke kallon Abdul yarda ya tsaya yana gaya mata magana, abun da be taɓa aikawa ba a rayuwar shi gare su.

Har ya juya ze fita ya waigo ya kalli Abbah yace

“Ka yafe min Abbah, banyi dan na ɓata maka rai ba”..

COMMENT AND SHARE FISABILILLAH

ALLAH KASA ANNABI YA CECE MU.

MASU MIN LAƁE A GIDA INA KALLON KU🙄

TALLAH! TALLAH!! TALLAH!!!

INA AMARYA, INA KUMA UWARGIDA KUZO GA SIRRIN KAMA MIJI A HANNU, SINADAREN GIRKI BA ABUN WASA BANE, KUMA NAMU BA IRIN NASU BANE.

MUNA SEDA

GINGER AND GARLIC SPICES

CURRY(AKWAI NA JELLOF RICE DA FRIED RICE) CINNAMON

THYME

TUMERIC

CHICKEN AND MEAT

DA NA PEPPER SOUP

MUNA SEDA NA SATCHETS KANANU DA MANTA SANNAN AKWAI NA ROBA, DUK AKAN FARA SHI ME SAUƘI, MUNA SEDA ƊAI-ƊAI SANNAN MUNA BADA SARI

ZAKU IYA SIYA TA WANNAN NUMBER

08137256112 KO 07046637375

SE KUN ZO, KARKU BARI A BAKU LABARI.

Back to top button