Gargadar So Chapter 123 By M Shakur
Zama yayi Mom tabude flask na kosan dasauri yadauki daya yakai baki asanyaye dan baida energy yace “it smells good Mommy” yakai bakinshi Mom tashiga zubamai kunu, hakanan kosan na shiga bakinshi kawai it reminds him of Hawwa again yayi shiru ya dakata da taunawa, ganin ya tsaya yadena taunan yasa Mom tace “ba dadi ne”? Girgiza mata kai yayi baice komiba sai kawai yacigaba da ci, Mom ta zauna kusa dashi tana juya kunnun ta a spoon takai bakinshi tana bashi yasha why does it taste like Hawwa made this? Rabon dayaci abinci dayama bakinshi dadi tun ranan daya tafi office around after twelve sai yau dayabi Sam party, taba wuyanshi Mom tayi tace “Alhamdulillah temperature ya sauka sosai, idan kagama saimuje hospital ko?” Dan turomata baki yayi gabaki babu abinda kemai dadi yace “ni yaro ne zaki wani bini hospital they will send the result to Dad” Murmushi Mom kawai tayi ganin first of all he’s hurt and not in good mood tace “to shikenan yarona uhmm cigaba da cin abincin ka” baki yabude mata tadebo kunu a spoon zatakai bakinshi ta gefen idanunshi yafara ganin kaman yaga Hawwa wai idanunshi gizo sukemai ne yadai daure yaki motsi gently Hawwa tafito daga kitchen din tazo wajen kirjinta na bugawa kawai saita kara kneeling awajen batare dataji kunyan Mom ba ko yan aikin dake kitchen ahankali tace “go……g…good morning Husby” Kaman Khaleel baisan mutum na wajenba yakalli Mom batare daya sha kunun datake bashi ba, voice nashi ba dadi yace “did she make this food?” Yatsine fuska Mom tayi tace “ban sata ba taje takama aikin daga hannun masu yi tahau yi” mikewa Khaleel yayi cikin kakkausan murya yace “this should be the first and last time za’a bani abinci made by her Mom!” Wani irin katsewa zuciyan Hawwa yayi tana wajen aduke tana kallon Khaleel sai kawai yadauki tissue ya share bakinshi ahankali yace “bye Mom” yajuya zai tafi karaf Hawwa takama hannunshi tarike dasauri yajuyo ranshi a masifan bace, tashi Hawwa tayi ahankali takalleshi kaman yanda yake kallonta da tsana akan idanunshi gabanta faduwa yake sosai, bakinta dake rawa sosai tashiga budewa zatai magana but zuciyanta ma ba karfi kawai tafashe mai da wani sassanyar kuka yakalli hand dinshi data rike yace “sakeni! Let goo off my hand!” Kin sakinshi Hawwa tayi tana kallon kwayan idanunshi ganin yanda rayuwa juyi juyi ne, da fa ita Khaleel ke rikewa haka tadinga bala’i tana gaggayamai magana tana cewa yasaketa kawai saitaji she’s regretting everything more, cikin murya mai bala’in rauni batare data sakeshi ba tace “Husbyyyyy I want to talk to you! Please give me just a minute, dan Allah” dauke idanu daga kallonta Khaleel yayi yace “for the last time let go off my hand and kada bakinki yakara kirana da that name my name is Ibrahim Khaleel” Kirjin Hawwa bugawa kawai yake da tsoro da fargaban ganin mijinta ya tsaneta muryanta babu ragowan kwari tace “I love……” “Ke!” Khaleel ya fizge hannunshi daga nata ya nunata da yatsa idanunshi na kadawa saikuma ya matso dab da ita ta yanda dagashi sai ita zasuji maganan yace “don’t you dare say that word cus it makes me even hate you more! Na tsaneki!” Baya Hawwa tayi kaman zata fadi dasauri ta dafa chair Khaleel ya watsamata mugun kallo yawuce yayi kofa abinshi.Khaleel na fita yashige motanshi yana sauke ijiyan zuciya.Momy da fadansu kaman tana kallon tv haka abin yake mata tana xaune abinta a dinning tana kallo tawani harari Hawwa dake zaune akasan falon tana goge fuska sai kawai ta wuce dakinta abinta.Khaleel na zaune cikin mota wayanshi yahau ringing Baba ne hakan yadaga Baba yace “kazo gida ina nemanka” ahankali yace “toh” har unguwansu yaje ya gyara buyuran rigansa yafito daga mota Baba namai murmushi sai kawai yakama hannunshi suka shiga xaure dayayi shimfida ya zauna shima ya zauna, Baba yace “ya jikinka?” Anatse yace “naji sauki Baba” Baba yace “yau result dinka zai fito ko”? Gyadamai kai yayi yace “amman inaso Dady na ya karbo I told Dr yabashi result din” murmushi Baba yayi cikeda so yace “zamuji alkhairi in sha Allah” yayi shiru hakan yasa Khaleel yace “Baba menene?” Cus yaga yanayin shi, anatse Baba yace “maisa kake shaye shaye Ibrahima?” Dasauri Khaleel ya kalli Baba saikuma ya sunnar da kanshi kasa kunya na kamashi sosai, ahankali aba yace “jiya mahaifinka ya sanar damu” Baba yayi shiru yace “ko kadan bakai kama da mai yiba Ibrahima yaran arziki basa shaye shaye kuma nasan kai yaron arziki ne dan haka nace saina kiraka namaka fada, inaso ka bari kaman yanda mahaifinka yace bayan kayı aure karage yi, inaso ka cigaba ahaka kama daina gabaki daya, sabida Allah sannan sabida lafiyan jikinka, inaso kazama mutumin arziki kamili yanzu kai ba yaro bane, kanada mata da yarinya duk rayuwan banzan nan abarma yara kaji, akwai mutum biyu yanzu da hakkinsu na kanka dole kazama namiji kafita daga sahun yaro ko yaron Mamanshi kadawo namiji tsayayye kaji” gyadamai kai Khaleel yayi Baba yace “inaso ka rike kanka, kaji tsoron Allah ka gyara rayuwanka kanunama matarka kasan mai kakeyi kayı haka zakaga bazata taba rainaka ba kajini”? Anatse Baba yace “inasonka ne Ibrahima saisa nake maka fada, inaso kazama mutumin arziki a better person, na hana Hawwa aiki but kai inaso ka dinga zuwa naka aikin dazaran ka gama samun lafiya kaji” gyadamai kai Khaleel yayi, Baba yadanyi shiru chan yace “Hawwa batason Baban Yaseer wlh, bata taba sonshi ba kuma bazata taba sonshi ba wlh” lumshe idanu Khaleel yayi, ahankali yace “I know! Nasan dalilin dayasa tai magana kawai kalman yacimin……” saikuma yayi shiru yadan sauke ijiyan zuciya yace “Dady yagayama min everything da maganan da sukayi, yan sandan da aka tura hospital din sun karbi wayansa sun tabbatar min yajeyi stalking Matana yakeyi, ga hotunanta tundaga sanda tafito daga gidana ma, da every move nata” Gyadamai kai Baba yayi yace “rayuwan nan zomu saba ne zomu shirya, Hawwa tayi ba daidai ba amman yanzu tasan tana kaunarka kayakuri kaji, Ibrahima ina sonka da diyata sosai tayi kuskure ka gwada mata tayi sabida nan gaba kada ta karayin makamancin sa, amman kada ka tsaneta yarinya ce kasan mata da kalan tunanin su gasu da tapka shirme, kayakuri” gyadama Baba kai yayi ahankali, Baba ya shafa fuskanshi, dan kallonshi Khaleel yayi for the first time sai yayi dan murmushi kadan yace “thank you Baba namaka alkawari zan gyara halayena kamin addu’a kaji Baba” Baba yace ina maka yarona, Khaleel yatashi yace “zan tafi” Baba yarakashi har waje yatafi.




