Uncategorized

Matar Makaho Part 20 Complete hausa novel

MATAR MAKAHO

Chapter 20

Bayan ta ya rike sosai ga wani irin ciwo da taji a maranta lokaci d’aya ta gigice tana salata tunda take bata taba jin ciwo irin na yau ba, Ambaton Allah kawai take a ranta gabaki d’aya ta had’a gumi, jin wani abu na zuba babu control ya sata tsorata ruwa ne yake dundula, salati ta sake hade da kwalawa khadija kira.

Khadija dake bacci kamar a mafarki taji muryar sumayya mikewa tayi ta nufi ban d’akin da sauri ta bude wazata gani? sumayya ce duke jikinta sai rawa yake gabaki d’aya ta had’a gumi a tsorace take tambayar ta haihuwa ne? sumayya bata samu Amsan bata ba, nuni kawai ta mata ta kira mata mota su tafi asibiti, ba musu khadija tad’au hijab tasa akan kayan baccin jikinta, ta ruga da gudu ta fita a falon, sakatan get in ta zare ta fita bakin kwalta, abinka da dare koh tsuntsu bata samu ba koh ina shuru, kuka ta sa da gudu ta dawo cikin gidan, kofar d’aya makwanciyar su ta wuce tana buga wa,  amma basu bude ba gashi kaf gidan babu mai mota koh mijin laila ma ba motar bane dashi.

Haka da dawo sashen su, tana shiga zuwa lokacin jikin sumayya ya kara tsanani sosai koh zama ta kasa har lokacin tana tsungune.

Da sauri ta d’auki wayar ta layin kalamu ta kira, sai da ta masa kusan 4 miss call kafun ya d’aga cikin muryar bacci yake tambayar ta lafiya?

Ai tana sanar dashi da sauri ya mike ya zura jallabiyar sa ya fitoh a d’akin sa, harya tura kofar falon su zai fita saiga nannen sa ta fitoh daga dakin  ta, tambayar sa tayi ina zaije a daren nan?

Sanar da ita yayi Auntin khadija ba lafiya tana labour, tambayar sa tayi mijin tafa,Amsa ya bata shidai bai taba ganin mijinta ba, yama ga alamu bata da miji, jin haka yasa nanne d’aukar hijab nata ta sanar da mijinta zasukai sumayya asibiti, suka fitoh tare dashi  mota kalamu ya fitar suka shiga sai get insu sumayya, fita nanne dashi sukayi zuwa ciki.

Zuwa lokacin sumayya tayi laushi sosai koh gane wake kanta bazata iyya ba, dayake dare ne nanne da khadija ne suka ririketa yayinda kalamu ya diauki akwatin ta, data jima da shiryashi a zaune, rufe musu kofar yayi suka tafi asibitin da sumayya ke awo.

Suna zuwa aka karbesu nanne na zaune a waje ita da khadija, kalamu keta hidima na sayyan abubuwan da aka bukata koh zama bai samu, har 4 na asuba sumayya haihuwa ya gagara, gabaki d’aya karfin ta ya gama karewa sai da aka kira Assalatu kafun haihuwa yazo gadan gadan, cikin hukunci Allah sumayya ta haifi yaran ta guda biyu wanda koh sanin wani iri ta haifa bata sani ba, tsabar wahalar da tasha, tadai san ta haihu sau biyu, Alluran hutu aka mata bayan an kimtsata a take bacci ya d’auke ta.

******************

Bugu d’aya Al’ameen ya d’auka a take Ammar ke sanar dashi anga wajen da khadija take,  suna Abuja.

Ai muhammad baisan lokacin da ya wantsalo daga kan kujeran falo, a take yayi sujjada akan tiles yana wa Allah kirari, goggo da mahmah dake zaune a kasan falo suna cin abinci da sauri suka mike suna tambayar sa lafiya?ai da sauri ya mike ya rungumi mahmah cikin farin ciki yake sanar da ita anga sumayya anga sumayya tana Abuja.

Ai sosai suka nuna farin cikin su goggo harda kuka, a take Muhammad ya fitar da waya ya kira abie ya sanar dashi akan yanzun nan zai tafi gidan su Ammar zasu wuce abuja.

Hanasa Abie yayi yace ya bari sai da safe sai subi fly zai sa a nema musu ticket sai su tafi tare da abie, ai a take goggo ma tace zata mahmah ma tace ita ma, dada dake kusa da abie tace itama baza’ayi ba ita ba, duk yanda abie da muhammad sukayi da tsofinnan su zauna a Taraba, su zasuje su dawo da sumayya amma kememen sukace kafar su kafar su abie, haka ba yanda abie ya iyya duka aka musu booking in fly tare da kiraye kirayen waya har nijar aka sanar dasu an samu wajen da suke, suma sun sanar dasu a cikin satin nan suna zuwa gabaki d’ayan su.

Washe gari tun sassafe suka bar Taraba muhammad koh bacci jiya kasawa yayi,   dada ma haka ta watsar da safina tace sai taje taga jikallen ta, Ammar ma tasa Abdul yayi a gaba tare zasu ya nuna musu gidan su kalamu.

Karfe 9 su muhammad suka dira a Abuja, dayake yana da aboki, tun a taraba ya kirasa akan suna zuwa, tarba suka samu daga wajen abokin abie shiyazo ya d’aukesu a Airport, direct gidan su kalamu suka wuce, Amma abin haushi basu sami kowa ba wai Suna asibiti, haka mai ganin ya sanar dasu Alfarman ganin baban kalamu abie ya nema ba musu, mai gadi ya shiga ga sanar dashi,  aiko sai gasa bayan sun gaisa ne sukace masa suna son sanin asibitin da kalamu sukaje in ba damuwa.

Ganin girman su da kudin su, gashi kamar ba lafiya ba, hakan yasa baban kalamu yace musu bara ya bisu asibitin, shiga mototi sukayi ya kira nanne ya tambaye ta asibitin da number room nasu, da mamaki yake tambayar ta koh lafiya jin muryar ta ya dishe-dishe alamu dai ba lafiya ba, koh tayi kuka, ya tambaye ta lafiya tace masa ba kome, kashe wayar yayi ya sanar dasu abie ga asibitin da suke.

Suna isa asibitin muhammad da gudu ya ruga bayan sanar dashi block inda suke koh kunyan su abie baiji ba da gudu yayi block in mutane sai kallonsa suke, da sauri sauri ya shiga d’akunan one by one yana dubasu, ana ukun ne ya shiga koh sallama babu ganin mace kwance akan gado ga yara sa’o’in juna zaune rike da jinjiraye a hannayen su, da sauri suma suka juyo jin mutun a d’akin babu sallama.

Ai da sauri khadija ta mike ta kwala ihu yaya!!!!!!!! Da sauri kalamu dake kusa da ita rike da d’ayar babyn da sauri ya cafke wance ke hannun khadija, don saura kad’an ta buga jinjira, da gudu khadija tayi wajen muhammad batayi wata wata ba ta rungumi d’an uwanta tana fashewa da kuka yaya, kaine koh mafarki nake?

Khadija nine nine khadija ina Aunty ki?

Allahu akbar yaya kalli nan tace tana nuna masa kan gadon da sumayya ke kwance har yanzun tana bacci.

Da sauri ya ware idanun sa yana kallon sumayya sai kuma ya juya ya kalli kalamu, ya sake kallon khadija?

Gyada masa kai tayi tana murmushi, shima murmushin yayi sai kuma ga hawaye, tare da matsawa kusa da gadon da sumayya take kwance, dukawa yayi akan gwuwar sa hannu yasa a hankali yana shafa fuskar sumayya,  dake kwance sanye da kayan asibiti, tayi kyau tayi fresh irin na masujego, wannan ce sumayyar tawa ashe haka take da kyau masha Allah?

Itace yaya kaga wa’innan jarirai nakane.

Da sauri ya juya yana kallon kalamu da sauri ya mike tsaye hannu yasa ya Amshi babies in yana kallon su, yarane mata masu tsananin kama da junan su tamkar An raba kunu a kofi, gasu masu tsananin kama dashi kome nashine a fuskar yaran, gasu farare tass, rungumarsu yayi ya fashe da kuka.

Toh ragon maza baka da aiki sai kuka, mahmah da suka shigo cikin d’akin tun d’azun, amma basu ma san da su ba.

Da sauri ya nufi mahmah yana ce mata, mahmah kalli yaran nan, wai yarana ne kallesu fa ga sumayya mahmah kyakkyawa fa sosai?

.

Sunkuyar da kai abie yayi yana mamakin surkin nan nasa yau koh dai ya mantasa a wajen ne, shima da sauri ya nufi wajen da yarsa ke kwance, zama yayi a bakin gadon yana shafa gashin kanta daya hargitse koh ribon babu.

Mahmah ce ta karbi baby d’aya dada ma ta karbi d’aya goggo kam baki kawai ta sake tana bin kowa da ido, kalamu kallon babansa yayi dake gefe, ya gaidashi, amsawa yayi yana tambayar sa mai jiki.

Matsawa kusa da abie muhammad yayi ganin sumayya ta fara motse, a hankali ta bude idanunta dalilin kukan da yaranta suka sake dukan su biyu.

Tana bude idanunta bata sauke sa akan kowa ba sai muhamamd dake kanta a tsaye, kamar a mafarki haka ta kalli abin da sauri ta mike zaune har tana kokarin zamowa kasa, da sauri ya tarota, bi a hankali sumayya jikin ki ba kirfi.

Ai jin abinda yace da sauri ta riko hannunsa gam tana kwalama khadija kira, Amsawa khadija tayi da sauri ta karaso wajen”khadija yayanki ke mini gizau na kamasa “

Aunty ba gizau bane yayane

“Yaya kuma khadija mijina fa baya gani yau kuma naga wannan na gani”?

Aunty ya warke ne.

Ai sumayya najin haka ta sake dariya cikin farin ciki koh damuwa da jikinta batayi ba ta rungume mijinta, don ita sam hankalin ta vaikai wajen mutanen d’akin ba.

Mikewa abie yayi dasu mahmah zasu fita a dakin su basu waje don sukam kunya ne zai kashe su.

Nanne dake toilet tana wanke kayayyakin sumayya daya baci, tun d’azun take jin surutai a d’akin mikewa tayi tsaye da boket na kaya a hannunta ta bude kofar toilet ta fitoh, Wai khadija da kalamu anya kuna da hankali kuwa mara lafiya na bacci kuke surutai da wa……bata karasa ba tayi turus ganin jama’ar dake shirin fita a d’akin dasuka juyo suna kallonta.

Dada ce ta kama salati tana tafa hanneye, wanake ganin nan?

Abie ma da sauri yace Hafsa??

Nanne kam bata wani nuna reaction ba,  dayake tun daren jiya data gane sumayya tasan tabbas zata ga su abie, duk da saurin da take tabar asibitin kafun suzo don ita batasan sumayya gudu tayi ba, haka ma batasan itace Aunty khadija ba sai daren jiya.

Nanne bata wani Amsa ba bare ma ta nuna tasan abie, sai tsayuwar da tayi tana kallon sumayya data sake muhamamd tana kallonta sosai irin kallon nan na kewa da soyayya, cikin kuka tace” ummi”?

Sai a wannan karo nanne tayi magana, Na’am momcy?

Da sauri sumayya ta sauka akan gadon tana takawa a hankali cikin dauriya tayi wajen mahaifiyarta fad’awa tayi jikinta tana kuka yau kam ta rasa ina zata sa kanta, murnan samun babies koh murnan ganin mahaifiyarta koh mijinta dole tayi kuka, ummi karan kanta hawaye ne ya cika a idanunta tana shafa kan sumayya ya isa haka momcy yi shuru kinga ba lafiya bane dake koma ki kwanta, tana maganar tana rike da hannun sumayya har ta kaita bakin gadon ta aje ta.

Waini yau hafsa nake gani ne koh gizau idanuna kemin koh mafarki nake ne?

Itace dada Abie yace yana dafe kansa cikin takaici da bakin cikin abubuwan da suka faru a baya.

Mijin hafsa ne yace, Hafsa kin sansu ne daman nina d’auka koh iyayen yarinyar nan ce? 

Baban kalamu ne da kakarsa wannan kuma Addansa ce ta nuna sumayya.

Daga sumayya har kalamu da Abie a tare suka jefowa Hafsa tambaya lokaci guda, baban kalamu wani kalamun?

Da sauri abie yace hafsa ban gane ba wanene kalamu.

Nuna masa kalamu tayi dake tsaye cikin shock na abinda nanne tace, yanzun wai sumayya Addansa, ta yaya kamar ya?baigane ba?

“Ummi kina nufin kalamu d’an uwa nane”?

Hafsa kina nufin wannan yaro, yaro nane?

Kallon sumayya da abie hafsa tayi jin tambayar da suka jefo mata, eh kawai tace tana kama hanyar kofa zata fita tare da kallon mijin ta, yauwa Alan guburo mutafi naga dangin ta sunzo zasu zauna a gunta.

Ah ah hafsa zuwan mu bazaisa ki daina hidima da yarki ba.

Ah ah dada zan tafi , Allah ya sauwaka momcy. 

“Ameeen ummi in zaki dawo a kawo mini sabulun wanka”

Toh momcy muje kalamu koh zaka zauna ne?

Ah ah nanne muje yace yana kallon abie da mamaki wai wannan ne babansa, shi abin ma yajisa wani banbara kwai.

Kokarin fita a dakin suke a hankali abie ya kama hannun kalamu daya wucesa zai fita a d’akin, kalamu bazaka ma abie magana bane?

Murmushi kalamu yayi sai kuma yaji hawaye ya taro masa, abie ashe kanason na maka magana, shine zaka kyamace ni ka kyautata rayuwar yar uwata, amma ka wofantar da nawa rayuwar ka barwa uwata ni, na zauna a matsayin agola a gidan da, bana ubana ba ya maye gurbinka ina Amfani da sunan sa koh a makaranta, bai taba nunawa duniya bashi ya haifeni ba koni bansan bashine mahaifina ba, sai yau akan me zan maka magana ni bansan wani uba ba sai ……..

“bai karasa ba sumayya ta mike ta wanke sa da mari cikin bacin rai ta soma magana, karka kuskura ka fara abinda zai dame ka wallahi kayi kad’an ka zagar min uba na barka,ni a haka nake son abina koma me zaimin bazan taba kinsa ba” sai kuma ta kama kuka.

Da sauri nurses dake falo suka shigo d’akin, akan surutun dake tashi, hakuri aka basu akan za’a kiyaye magana ne mai muhimmanci ake, ganin kalarsu yasa su barinsu a dakin.

Daker aka samu suka sassanta nanne ta koma gida dasu goggo yayinda mazan kuma suka koma hotel sumayya ma ita da dada kadai aka bari a hospital.

Washe gari aka sallame ta saboda kyaun da jikinta yayi, don haihuwar duk da yazo da gardama amma tana haihuwa shikenan.

Gidan nanne aka maidata bata koma gidan hayansu ba,sosai ake kula da ita muhamamd a rana sai yazo sama da sau hudu, sai da sumayya ta kwana hudu da haihuwa kafun suka koma shirye shiryen dawowa jalingo don anan ake son yin taron suna gashi yan nijar ma sunce suna shirin zuwa, duk yanda sukayi ta rokon nanne ta biyosu taki tace bazataki bin umurnin mahaifinta ba na raba kanta da zuriyar shugaba, saida mijinta ya nuna bacin ransa da nuna mata yaranta nada hakki akan ta, sannan kalamu bazaiji dadin hakan ba tunda shima so yake yaje yaga dangin babansa, daker dai ta Amince washe gari da sumayya ta cika kwanan biyar sukabi jirgi saijalingo.

Muhammad murza idanunsa yayi yace a gidan sa da babansa ya sai masa a Amazon sumayya zata sauka, ba musu duk da abie yaso ta koma gida Amma ganin hafsa da Al’ameen basason hakan.

Gidan sumayya ta sauka dayake babban gidane ga d’akuna shiyasa gidan ya d’auke su,  duka harda su hafsa falmata su babayo muhamamd goggo dasu mahmah, kalamu kam shugaba family house ya sauka kuma ba karamin farin cikin ganinsa sukayi ba.

Babu inda haihuwar sumayya bai bazu ba jama’a sai tururuwan zuwa dubata suke harda yan Abuja laila ma daga adamawa ta gangaro, a ranan yan nijar suka diro nageria gabaki d’aya yan uwan yusuf ne harda shi karan kansa ma, wannan zuwa harda lawiza da nabila, sosai gidan ya dad’a cika da yan uwa kota ina yan gidan shugaba ma tun a washe gari suna matan suka diro, yusuf a gidan sarki ya sauka dayake suma ana gobe suna suka zo, kai sumayya taga jama’a iyya jama’a ga wani irin lalle da aka watsa mata mai masifar kyau da ketson suna duka.

Yau take suna yara sunci suna NA’IMA da NA’IFA , tun Asuba yan gidan Adara suka diro su inna asabe inna lami Ana gindin murhu a sauke wanshan a d’aura wanshan, shanu uku aka yanka da rago biyu,  duk suna ta kan gyaran nama, ga abinci kala kala, gashi koh ina ka leka zakaga group group na mata kowa da angon su mai zafi,  wanda abie ya d’auki nauyi duka, yan nijar nasu da ban haka dangin adara, yan shugaba family house ga yan gembu, ashan gefe naga MATAR MAKAHO FAN’S  ansha anko na Atamfa mai ratsen flower green ana zazzaune ana dirkan shinkafa a manyan tireruka hhhhh.

Sumayya dake sanye da wani hadedden material gown wanda yasha dinki ga sarka na d’anyen gwal da sarki ya bada aka kawo mata, sarkane da dankunne sai warwaro ga agogo mai zafi na mata duka, tasha heavy make-up sai d’aukan hotuna suke da kannen Ammar dake sanye da Ankon su, khadija da kalamu dake zaune a gefe suna cin shinkafa.

Muhammad da Ammar harda su ramadan zulkiflu gidado badaru duk yanzun sun chanja kamar basu ba, suna zazzaune a kofar gida a rumfar da aka kakkafa abinci suke ci mairai da lafiya.

Tun daga nesa suke jin ihun yara da mutane suna rugawa a guje, da sauri suka mike gabaki d’ayansu suna kallon abinda ke faruwa.

Mutum suka gani kamar mace ne koh na miji bazasu gane ba, kadangaru manne a jikin sa tana gudu suna binsa wasu na jikin ginin unguwan suna rugowa suna binta sosai kota ina kadangaru ga wasu runduna na binta a baya, sai wata mata dake gefenta rike da sharbebeyar bulala tana kad’a mai kadangarun suna tafiya a haka.

Da sauri su muhammad suka ruga cikin gida da gudu har ana rige rige, ganin wajen da suke suka nufo.

Suna shiga suka rufe kofar gidan da karfi suna ji sai bugawa matar take akan don Allah abude mata, kiri kiri su muhammad sukaki budewa har abin yaja hankalin matan dake compound sosai, dada dake rike da jinjira zata kaiwa kawayen ta dake falo a zaune ssga dayar, itace taji hayaniya aje jinjiran tayi ta fitoh compound, ganin su muahmamd da jama’ar tsakar gidan a tsaye yasata karasawa bakin get in tana tambayar dalili, kafun ma su muhammad suyi mata bayani tuni tasa hannu ta zare sakatar get in, ihu Ramadan ya sake tsabar rikita yare ma ya fara.

Dada na budewa idanunta ya sauka akan matar dake rike da bulala kwalalo ido tayi cikin mamaki tace  wanake gani anan kamar Nafi………….

kafun ma ta karasa maganar ta idanunta ya sauka akan wance ke tsaye mammanne da kadangaru ga bataliya a kasa, ai ihu dada tasa ta ruga ciki da gudu, da sauri inna lami tazo  zata rufe get aida sauri wannan matar ta banke kofar ta kora mai kadangaru ta shigo, itama  shigowa tayi, ai ana ganinta, ihu ne yake tashi abinka da mata atake masu Aljanu Aljanunsu ya soma tashi, gidan suna gabaki d’aya ya rikice ya zama gidan tsere kowa gudu yake yana burmuwa falo wasu kitchen masu Aljanu kam sun zuzzube..

Duk masu Aljanu sun zuzzube a kasa,  muhammad da gudu yayi falon cikin gidan duk da yaga tashin hankali a cameroon Amma wannan tashin hankalin tabanne koh mutum baida Aljanu indai yaga kamila sai tsikar jikinsa ya mike, yana shiga falon yaga an watsar masa da jinjiraye akan kujera,  kawayen dada tuni sun ruga daki da sauri ya ciccibi yaransa ya manna a kirjinsa yanemi gefen daining ya tsaya yana jijigasu.

Ta gefen sumayya kam bayan d’akunan gidan suka nufa mahmah dake dana da jiki, gudu take kamar kazan Agric irin sunyi naman nan, kowa fa gudu yake abin dariya abin tausayi a take ramadan ya kira yusuf ya sanar dashi,  Ammar ma abie ya kira don su harga Allah abin ya basu tsoro especially ganin yanda kadangarun makwanta ke biyowa ta gini da gudu suzo wajen kamila, gasu bataliya guda.

Ba’a d’auki lokaci ba saiga Abie ya shigo shikaran kansa abin ya masa tsoro, Amma sai yayi ta maza ganin nafisa, babban get in ya wangale galala gabaki d’aya ana kallon cikin gidan, nuni yama nafisa dasu fita waje su tsaya, ba musu ganin get a bude ta kora mai kadangaru suka fitoh bakin get suka tsaya suna hangen cikin gidan.

Daidai lokacin yusuf da mijin nafisa suka iso a tare, don shima wani abokinsa dake unguwan ne ya kirasa akan yaga kamila da nafisa sai gudunsu mutane kiyi.

A get yusuf ya sauka suka nufo inda abie ke tsaye, yana ma nafisa masifa akan sun shigo sun dagawa jama’a hankali, ita kuma sai hakuri take basa akan tazo tana son ganin muhammadsumayya da hafsa taji labarin duk suna gidan nan.

Daker aka shawo kan abie da wasu mazajen unguwan akan yayi hakuri aji meke tafe dasu, rukiya yusuf yayi ma masu Aljanun suka farfado, matan da suka gugudu ma duk aka tarkatosu, sumayya kam d’ankwali ya fadi koh takalmi babu, muhammad har lokacin yaransa na hannunsa,shimfid’a manyan taburmaye akayi a gefe guda hudu, gefen maza daban na mata daban kowa aka ajesa, wasu da dama kam sun gudu gida wasu kuma na cikin d’akuna, sun rantse bazasu kara yarda su kara kallon kamila ba, haka masu Aljanu duk an hanasu fita.

Zama akayi sarki kam kujera aka kawo masa ya zauna, yasa aka shigo da nafisa kamila kam a wajen get akace ta zauna saboda kadangarun ta.

Yusuf ne ya kalli nafisa, baiwar Allah lafiya kikazo kika d’agawa mutane hankali da wanshan abin?

Kuka nafisa tasa a hankali ta kalli mijinta, sam bataso yau ta sanar da sirrin ta a gabansa ba tsoron kar auren ta ya mutu gashi batasan inda zata shiga ba.

Wai ba magana ake miki bane kinsan waye a gabanki kuwa, sarkine da kansa ki kama kanki baya magana biyu?

Kayi hakuri nasan yau koh naki koh naso sai gaskiya tayi halinta, shiyasa na gwammaci kunyar duniya data lahira, gwara na nemi yafiyar su koh Alhaki zai barni.

Shuru kowa yayi ya zubawa nafisa ido don jin me tazo dashi.

Abubuwan da suka faru a shekarun baya da suka wuce, nidai sunanan nafisa Abdullahi kamar yanda wasu suka sani macece maison abin duniya gabin bokaye, bayan nayi aure da mijina saboda halayena ya rabu dani, lokacin na haifi yarinyata kwalli d’aya da Allah ya bamu mai suna kamila, duk yanda naso na koma gidan mijina sam yaki amince wa hakan yasa na shiga islamiyya saboda a lokacin bana zuwa boko sam, mun hadu da safina ne A makarantar islamiyya muka kulla kawance, a lokacin don ance hali sai yazo d’aya ake abota, kawancen mu yayi karfi a lokacin safina ke sanar dani bata da buri saina auren Abdulsalam Amma goggon ta(dada) bata bata goyi baya ba.

Ni kuma jin haka yasa na bata shawara muje gun wani malami danaji labarin sa, nima so nake na koma gidan mijina ba musu safina ta samo kudi muka kama hanya har Ardo-kwala wajen wani hanshakin boka.

Bayan munje da bukatan mu yake sanar damu Auren safisa da Abdul bazai taba yuwa ba, mundin yana tare da hafsa don soyayyar su na daban ne kuma mai karfi, dole rabasu shine zai iyya taimakawa ta samu Abdul salam.

Babu musu mukace mun Amince a rabasu, nima na shaida masa bukatana nason komawa gidan mijina aiko cikin sati d’aya baban kamila ya dawo yace shi kaf duniya saini, na koma gidan mijina aiki yayi kyau sai dai aikin safina shuru  baici ba, haka muka koma wajen bokan nan yake sanar damu saimun kawo idanun jariri, kafun mu iyya dishar da soyayyar dake tsakanin su,yaji kwata-kwata baya ganin farin hafsa sai bakinta, sannan bazai iyya rabasu ba sai safina ta had’a da kirsa.

Babu musu na samo wasu rikakakun yan daba muka biyasu suka sato mana jinjiri,  haka ba tausayi aka kwakule idanunsa a take ya mutu koh shurawa baiyi ba, muka kaiwa boka ido yayi aiki aiko koh sati ba’ayi ba rashin zaman lafiya ya wanzu a tsakanin ma’auratan nan, yayinda na baiwa safina shawara ta shiga sacewa mutanen gidan Abubuwa daga karshe ta likawa hafsa.

Aiko shawarata taci don cikin wata d’aya akayi hakan kuma aiki yayi Abdul ya sake hafsa.

Bayan nan muka koma wajen boka ya mana wasu aikin gabaki d’aya ya rikitar da dada da yan uwanta akan sai Abdul ya Aure safina kuma duka aikin bokane.

Bayan auren kuma safina tazo da bukata akan tanason a raba sumayya da Abdul don ta fahimci yana tsananin son yarsa, shawara na bata akan basai mun koma wajen boka ba ita ta d’auki mataki da kanta, amma abin mamaki har Kashe mata aure dukan sumayya yajawo wannan dalili yasata tayi sanyi ganin babu yanda ta iyya da sumayya.

A lokacin da sumayya takai shekara 14 sai gabaki d’aya hankalin safina ya tashi ganin irin kyaun data tashi dashi, gashi koh a gidan su farin jinine da ita gashi kowa na dangi baida magana sai sumayya, kome sumayya hakan yasa safina fara kishi da sumayyar.

Kasa hakuri tayi muka koma wajen boka akan a raba tsakanin sumayya da ubanta,  dayan gidan su suji sun tsaneta yanda zatayi rayuwa cikin kaskanci, Amma boka yace hakan bazaiyu ba sai an diga magani a idanun yaro matashi mai tashen balaga kuma ya kasance tauraren sa nada karfi, wannan zance da mukaji yamatukar d’agawa safina hankali don ita tana da tsoro ba kamar ni ba.

Nikam jin haka sai wani tunani ya fado mini na Al’ameen dake likewa yarinya ta, kwata kwata bana sonsa da yarinyana,gashi nayi iyya kokari na babanta ya rabasu yaki itama duk irin lallama da dabara da zan mata ta rabu dashi Amma taki, hakan yasa na kirawo wa’innan yan daban da suka taba sato mana jinjiri na basu hoton muhammad dake wajen kamila na d’auka, na musu kwatancen makarantan su a ranan suka kama muhammad bayan sun bugar dashi suka daukesa har Ardo-kwala wajen boka,  sai da akayi sati baya cikin hayyacinsa, ana masa wankan magani da digawa a ido, kafun aka mayar dashi bayan gari aka jefar.

Wannan shine dalilin makantan Al’ameee, ta karasa maganar tana kuka, jama’ar dake wajen salati suka buga, Muhammad kam gabaki d’aya jijiyoyin kansa su  mike bacin raine karara a fuskarsa wanda kallo d’aya zaka masa kasan ran maza ya baci, mikewa dada tayi tsaye habba nafisa mai muka miki? yanzun da haden bakin safina aka aikata wannan mummunan aiki, Sai kuma ta fashe da kuka take surutai ya fara tashi kowa yana furta Albarkacin bakinsa.

D’aga hannu sarki yayi tare da bada umurni kowa yayi shuru, aiko shurun akayi ya bawa nafisa dake kuka damar ci gaba da bayaninta.

Bayan an gama aiki kuma yaci, sai dai sam bai kama Abdul ba iyya yan gidan ne sukaji basa kyaunar sumayya sam, sai kuma Abdul ya d’agata ya maidata hostel wanda hakan ya rage musguna mata da ake, kuma hakan baiwa safina Dadi ba, taso abar sumayya a gida taci kwakwa.

Duk yanda mukayi babanta ya rabu da ita abin ya gagara karshe dai haka mukayi hakuri aka cigaba da rayuwa, kamila ma taki muhammad a lokacin ganin ya makance.

Lokacin da sumayya ta zama cikekkeyar budurwa hankalin safina ya tashi hassada take da sumayya karta samu mijin dayafi ubanta kudi, koh wani mai mulki kwata kwata so take taga sumayya ta kaskanta a rayuwa wannan dalili yasa muka koma wajen boka daman sumayya nada wani hali na raina wa mutun ArZiki, aiko da halin nan nata aka samo mafita wajen mata magani yanda samari zasuji basa sonta kwata kwata wanda majority zasuce halinta ne ya ja mata.

Bayan nan sumayya ta rasa manemi sai dai ba’anan gizo ke saka ba, sumayya na samun kudi sama da safina don tana aiki, ga kaunar da mahaifinta ke mata, shawara na bata muje wajen wani bokan aiko munsamu wannan aiki da wanshan ya kasa wannan yace zai mana amma da sharadi, shine sai an nemi makahon yaron da mukama asiri, mu had’asa aure da sumayya wannan ne zaisa ta fita a zuciyar Abie,yanda mukasa muhammad yana kallon baki, haka su dada ke kallon bakin sumayya, kuma duk adadin sex da zasuyi,  haka aiki zai kara karfi tamkar muna bawa shuki ruw, tsanar ta a zukatansu zai karu, amma aiki zai lalace mundin aka rabasu misali d’aya na wani kasa d’ayan na wani kasa aiki zai karye.

Ba musu muka abince daman safina ta shanye kowa a gidan, kowa tsoron ta yake sai abie kawai baya shayin ta, wannan dalili yasa ta samu su babuji da dada ta tilastasu akan aurar da sumayya kuma ita ta sama mata miji ba musu suka amince jiki na bari.

Mu muka nemi mamman dayaje ya samu muhamamd akan shine uban sumayya, zai basa auren ta amma dayake Al’ameen nada tunani sai yaki Amince wa, karshe dai wajen Bappa suleman akaje don munji labarin yanada son kudi, mamman ya sake masa kudi masu yawa akan zance, wanda gaskiya lamari sharri muka ma suamyya akan tayi ciki saurayin da zata aura ya fasa, a taimaka a had’ata da muhamamd ba musu ya amince da zancen.

Bayan auren sumayyya da muhammad magani yaci Abdul ya tsane yarsa, duniya kaf babu wanda yaki jini irinta, muma sosai muka sakawa rayuwar sumayya ido duk wani motsenta muna sane dashi.

A lokacin An jima da sakar mini yata kamila wance ta koma makaranta tana ci gaba da karatunta da bata samu tayi ba, kusam ta dawo rayuwar muahmamd wanda bansan da labarin ba saida  taje gidan Adara aka mata duka, a lokacin raina ya baci kuma na jama kamila kunne akan ta rabu da rayuwar yaron nan in tanason kanta da lafiya, amma bata daddara ba ita da kawarta suka je mutum biyu wajen boka………………………………………har sanadin haka ta samu wannan matsala na kadangaru wanda na tabbata Alhakine yake bibiyata.

Munyi neman duniya wa bokan nan don mu biyasa koh mu basa hakuri ya rabu da ita,  Amma ina bamu gansa ba duk malaman da muka kira shuru ba sauki, a lokacin na shiga tashin hankali ita kuma safina a lokacin take jin dadin ta, naje wajen ta akan ta taimaka mini akan zancen kamila koh da kudine don kaf abinda muka tara ya kare a wajen jinya amma haka safina ta murza ido bata tuna irin hallaci dana mata ba ta hanani koh biyar, ni kuma abin yayi matukar bata mini rai hakan ne yasa na d’auki kayan dakina na sayar na biya yan dabanda suke mini aiki tsawon shekaru, akan su kashe mini muhamamd yanda aikin safina zai lalace sannan nima na huce takaicina akansa, tunda ata dalilinsa rayuwar yata ya shiga garari, don haka kowa ma ya rasa.

Aiko yan ta’andan nan sun bani tabbacin batar muhamamd wanda zancen yaje har kunnen safina, kuma ta zargi nice wanda har gida tazo mukayi fad’a kasha kasha, ta tafi ban sake bi takanta ba, sai kawai labarin rashin lafiyar safina ya riskeni, da kuma dawowar muhammad gida.

Shine nazo neman yafiyar ku don Allah ku yafe mini sharrin shaid’an ne?

Ai kece shaid’aniyar in kam, munafuka wallahi bazan taba yafe miki ba har abada kin cuceni kin rabani da matata kin muzguna ma rayuwar yata, Allah ya isa tsakanina daku kuma bala’i yanzun kika fara gani.

Jin abinda abie yace yasa dada mikewa tsaye da hannu tayi pointing in mutanen gembu, maza maza su tashi su tafi gidan shugaba su tattari safina a yau innan su maidata wajen dangin uwarta babu ita babu safina har Abada, ita tana ta bauta mata ashe shaid’aniya ce.

Baban kamila mikewa yayi yanzun nafisa har kisan kai kike? toh kiji daga yau bani bake kuma bara kiji na sakeki saki biyu daman babu igiya d’aya a tsakanin mu, ki tattara yarki ku kara gaba koh gidana karki koma don bakizo da kome ba, bazan iyya zama daku ba, kuka nafisa tasa da sauri ta rike kafar baban kamila tana neman yafiyar sa tunkudeta yayi ya kama gabansa.

Duk yanda yusuf yaso wajen yayi shuru abu ya gagara ganin yan gidan Adara sun rufarwa nafina da duka, waya Ammar yayi wa ofishin yan sanda cikin kankanin lokaci sukazo daker aka kwace nafisa anso tafiya da ita, Amma yusuf ya hana yace a barta kodon Albarkacin kamila dake d’auke da wannan matsala taje duniyace, haka ta mike daker tana koran kamila suka bar unguwan gwanin tausayi.

Hafsa a ranan kuka tasha bana wasa ba kuma itama ta basu labarin, bayan rabuwarsu akan cikin bai zube ba, jinine ya zuba kuma mahaifinta yace sai an zubar da cikin Abdul salam, baza’a haifa masa a gida ba ganin yanda ransa ya baci yasa kanwar mamarta  d’aukar ta ashan ta haifi kalamu bayan haihuwar sa ne  matar cousin nata kabeer  ta rasu, bayan shekara d’aya da mutuwarta sai ya nemi ya auri hafsa kuma ba musu findon ta amince dayake kowa yasan halin ta macece mai nutsuwa, kuma bayan auren su ta rike yaran kabeer hannu bibbiyu, wannan dalili yasa sa rike d’anta itama kamar nasa hatta su babayo basa nuna wa kalamu ba yan uwansu bane harya girma, bayan kalamu ta haifi yara uku shamsiyya(tayi aure a maiduguri) falmata da musa (auta) duk yaran hafsa ne da suka haifa da kabeer.

Sosai abie ya nuna nadamar sa kuma ya nemi yafiyarta tare da sanar da ita insha Allah gobe gobe xasu je maiduguri har wajen mahaifinta ya nemi yafiyarsa wannan umurnin yusuf ne kuma hardashi zasu.

Washe gari haka aka tattaru duka aka wuce maiduguri duk yanda akayi sumayya ta zauna saboda yanayinta amma ina tace da ita za’aje taga kakan ninta da kanwarta shamsiyya,  ba yanda aka iyya haka aka tattaru harda Ammar suka wuce maiduguri.

Da isarsu suka sauka a gidan sarki yayinda Ammar ya nemi Alfarmar su muhammad su bisa gidan Uncle nasa su kwana, bazasuji dadi ba in sukasan yazo Maiduguri ya kwana a wani wajen, ba musu ramadan da muhamamd suka bisa jin yace musu babu kowa a gidan daga uncle nasa sai matarsa da yarsu babba.

Unguwane mai kyau suka shiga cikin wani gida madaidaici mai kyau,sunyita sallama Amma shuru ba’a amsa ba, hakan yasa Ammar nufar kofar falon ganin kamar a bude,  aiko yana turawa yaga kofar ta bude, bismillah yama su muhammad ba musu suka shiga da sallama, amma shuru.

Macece zata kai shekara 44 zaune akan sallaya a falo ta fuskanci gabar rabin fuskar ta kawai suke iyya hanga zaune take tayi tagumi kana ganinta kasan tayi zurfi a tunani.

Girgiza kai Ammar yyi saboda wannan abin ba sabo bane agunsa, abune da ya saba da ganinta a haka, da sauri ya nufi wajen da take ya tabata Aunty!!!!!

Da sauri ta dawo hayyacinta, ta dubesa a dakile tace Ammar yaushe kazo?

Yanzun nazo  kina sana’ar taki ina zakisan na shigo?

Shuru ta masa alamu dai batada yawan magana, koh ince damuwa ya maidata haka.

Ganin ta masa shuru yasa sa tambayar ta, aunty ina mom?

Basanan Ammar kai kad’aine?

Ah ah Aunti babba nida abokai nane, yace yana nuna mata su Ramadan dake tsaye, yayinda shi  kuma muhammad ya zuba ma fuskar matar ido yana kallonta, kallo irin na tsana, koh shekara dubune bazai manta da wannan fuskar ba.

Ai tana kallonsa jikinta ya soma rawa da sauri ta mike tsaye sanye da hijab, tana nunasa da hannu sai kuma ta yanke jiki zata fad…………..

Back to top button