Mijin Marigayiya Page 57 Hausa Novel
Tace ‘Um, babu madara a nan dama idan nayi canjin kudin makaranta ne nake siyo mana kuma yanzu ka ga ina hutu shi yasa bani da kudi.’Takaici ya cikashi, yanzu da ransa da lafiyarsa madarar shayi ace sai Afaf ta tara kudin makarantar da yake bata ta siya sannan zasu sha. To wai ina kansa ya shiga hakan take faruwa a gidansa? Tunda yake a rayuwarsa bai taba ganin Khadeeja ta hana yaranshi wani abu da ya siyo ba, sai dai ma ya san lokutan da take sayen abu da kudinta su ci ita da yaran. To wai yaushe ma Khadeeja ta bar gidan?Ba a fi wata takwas ba fa da rabuwarsa da Khadeeja amma gidan duk ya zama haka? Ita da take zama cin abinci a tsakiyar yaran balle a ce ta boye wani abu ta hana su.Ya bi fuskar yaran da kallo gaba dayansu babu wadda take da cikakkiyar walwala, tabbas yanzu ne zasu ji nauyin maraicinsu. Shi kanshi sai ya ji kwalla tana neman kwace masa, sai da yayi da gaske sannan ya mayar da kwallar. Ya dubi Nasreen yace ‘Nas dauko min kofi nima na sha shayin.’Ta tashi ta shiga nan kichin din kasan ta dauko masa tsohon kofin tangaran ta kawo masa da sugar a ‘yar roba. Ya kalli kofin duk ya dafe ya dubi Nasreen din da ta ajiye kofin yace ‘Kije sama ki dauko min wani kofin mai kyau.’Tace ‘Abba Anti Naja fa tace kada mu hau kuma wallahi idan na hau zagina zata yi in nayi magana tace na mata rashin kunya, sai dai ko yaya Afaf taje ta dauko.’Haka ya karbi kofin ba don ya so ba ya hada bankin shayi ya sha tare da ragowar burodin da suke ci. Sai da ya gama sannan ya tashi ya haye sama domin ya shiryo ya fita aiki.……..Ta ji dawowarsa tunda ya shigo da motarsa, sai dai da ta ji shiru ta saka rai ya tsaya a wajen yaransa don ya kara jin abubuwan da zasu gaya masa a game da ita. Don haka a parlor ya sameta tana ta cika tana batsewa ita a dole kada yayi mata fada. A gajiye yake sannan bashi da karsashin hayaniya da ita, don haka ko inda take bai kalla ba ya shige daki ya fara shirinsa.A shirye tsaf ya fito dauke da jakarsa, tana nan zaune a inda ya barta. Ya dauke kai ya nufi kofa bayan ya amsa a dawo lafiyar da Rukayya tayi masa.Ta mike ta nufoshi fuska babu walwala tana cewa ‘Ga abincinka can zaka fita baka yi breakfast din ba.’Ya kalleta a fusace ba tare da ya daina tafiya ba yace ‘Abincin da kike hana yarana? Ni na koshi ki kirawo ragowar ‘yan uwanki ku cinye.’Ta bude baki zata yi magana sai dai kafin tace wani abu ya ci rabin kafar benen, tana nan tsaye kamar zata hadiyi zuciya ta jiyo ficewar motarsa daga gidan.Dole itama ta shirya ta fice ta tafi wajen aiki domin a hakan ma ta san sai an harareta tunda ta makara.Kansa a cike yake saboda rashin bacci ga damuwa, don haka yana shiga office din ya rufo kofar ya kwanta a kan 3-seater din da take wajen.Yana rufe ido ya fara nadama; ya aka yi ya saki Khadeeja? Ya aka yi ya bari har ta gama idda bai mayar da ita ba? Tunda dai ai da ya mayar da ita ya san bata da wani zabi dole ta zauna da shi tunda ba zata saki kanta ba. Tunda yake da Khadeeja bai taba ganin wata damuwa game da yaransa ba, gashi wata takwas kacal da ta barsu gidan yana neman ya gagareshi. A da yayi zaton Naja zata fita kulawa da su musamman yanda yaga tana nuna kauana garesu kafin ya aureta; to me ya canza mata ra’ayi har aka kai inda basu da damar da zasu ci abinda suke so a gidan ubansu? Lallai dole ya dau mataki.Haka ya wuni a office din cikin rashin sukuni; yana tunani halin da yaransa suke ciki a gida sannan kuma ga shi zuciyarsa taki ta kyaleshi da tunanin Khadeeja. Tabbas da Khadeeja tana nan da babu yanda za ayi ya wuni a office yana tunanin halin da yaran suke ciki. Domin ya tabbatar duk halin da suke ciki to itama tana cikin wannan halin a tare da su. Ya tuno lokacin da tace ba zata yi musu girki ba yanda suka gaya masa gari suka sha kuma garin ma tare da ita suka sha. Yayi dariya a fili; tabbas Khadeeja tana da rigima amma ta iya rigimarta. Ya tabbatar babu yanda za ayi taci kaza ta bar yara da bakin shayi. Haka ya zauna yana aiki yana tuno rigimarsu da Khadeeja yana murmushi shi kadai. Bai taba zaton zai yi kewara rigimar Khadeeja ba amma yanzu tabbas kewar rigimar tata yake yi.Karfe daya da rabi daidai suka idar da sallah a farfajiyar office din su. Yana shiga office dinsa ya auna a kan kujerarsa ya turata baya kadan yana juyawa ya dauki wayarsa wadda take kan tebur din ya lalubo lambarta ya dannan mata kira, ya kara a kunnensa bayan da ta amsa yace ‘Hello.’Bayan sun gama gaisawa yace ‘Kina ina ne?’Da mamaki a muryarta tace ‘Ina office mana, akwai wata matsala ne?’Murya a sanyaye yace ‘No, babu matsala kawai dai ina son ganinki. Zan iya zuwa office din yanzu?’‘Umm! Akwai matsala ne?’ Ta sake tambaya.Yayi ‘yar dariya ‘Babu matasala fa, akwai dai maganar da nake so muyi. Zan iya zuwa, minti talatin kawai ya isa.’‘Ok, ina jiranka duk da dai na kusa tashi.’Ya ajiye wayar ya mike ya dauki mukullan motarsa ya kama hanya.…….Yana sane yaki ya kirawota da ya sa don so yake ya shiga ya sameta a office din nata, don haka bayan ya ajiye motarsa sai ya fito ya shiga gidan talabijin ya tambaya. Ba tare da bata lokaci ba aka nuna masa office din nata.A hankali ya kwankwasa kofar, daga ciki muryarta ta bashi amsa ‘Shigo a bude kofar take.’Ya tura kofar ya shiga da sallama.Tana zaune a kan kujerar zaman mutum daya wadda take gefe guda, da jakarta a gefenta tana ta danna waya; da alama ta gama shirin tafiya gida. Bayan ta amsa sallamarsa ya mayar da kofar ya rufe sannan ya karasa yayi kansa mazauni a kujerar da take kusa da wadda take zaune a kai. Bai san dalilin da yasa ganinta ya saka shi jin dadi ba amma dai ya san ya ji dadin ganinta. Cikin girmamawa ta gaisheshi kamar babu wata damuwa a tsakaninsu.Bayan ya amsa tace ‘Allah ya sa dai ba wata matsala don tunda kace zaka zo nake ta tunani.’Yayi murmushi yace ‘Babu wata matsala, kawai dai ina son ganinki ne.’Ta dan yi gajeren murmushi tace ‘Uhm, to gani.’Yayi dariya yace ‘Kamar dai kina korata.’‘Ba korarka nake ba, kawai dai ina son na tafi gida don wallahi na gaji.’Ya gyara zama; yarasa ma ta inda zai fara domin ganinta ya goge masa duk zantukan da ya tsaro zai zo ya gaya mata. ‘Yara suna kewarki.’ Ya fada bayan ya gama nazarin ta inda zai fara.Nan da nan murmushinta ya kara fadi, tace ‘Allah sarki ni da Hammad ma muna kewarsu. Don ma Yaya Habib yana zuwa gidan Mommy yana gaishemu.’Ya girgiza kai domin Habib bai taba gaya masa yana zuwa wajen Khadeeja ba, bai ma taba yi masa maganar Khadeejan ba tun bayan da suka rabu.‘Ya Hammad? Baya kukan makaranta?’ Ya tambaya.‘Baya yi, ka san ya hada wayon yayyinsa gaba daya.’ Ta fada tana dariya.Suka yi shiru na dan lokaci; ita duk ta kosa domin so take ta tafi gida yayinda shi kuma ya gyara zama yana kwaso hira.Suka yi shiru na dan lokaci, jimawa kadan yace ‘Khadeeja.’‘Na’am.’ Ta amsa tana kallonshi.‘Wai me yasa kika ce na sakeki?’ ya tambaya yana tsareta da ido.Ta sunkuyar da kai tana murmushi, ta dago ta kalleshi suka hada ido sannan ta sake yi masa wannan murmushin nata wanda yake dauke da ma’anoni daban daban tace ‘Right question at the wrong time; amma dai zan baka amsa…
