Ruwan Zuma Page 31 Hausa Novel
(31) Washe gari da safe Laila tayiwa Haydar breakfast yaci kad’an ya tashi zai tafi ta kira sunanshi ya amsa ya juyo yana kallonta. “Har zamu fara irin haka?�? Ta tambayeshi. “Na kafa dokata kin karya Laila, a maimakon ki bani hak’uri ki nuna mini hakan ba zai sake faruwa ba sai kika tsareni kina mini wasu tambayoyi naki.�? “Amma meyasa zaka k’i d’aukan wayata? Kasan damuwar dana shiga kuwa? Na d’auka kai d’in ma tafiya kayi ka barni.�? Hawaye ya taru a idanunta. Tausayinta yaji sosai, yayi saurin isa gurinta yana goge mata hawayen daya zuba a fuskarta. “Kayi hak’uri da d’aukan wayarshi da nayi. Ya kirani sau biyu ban d’auka ba sai ya mini text cewa kunyi magana ka tafi cikin fushi. I called him back domin inji meya faru sai yace in nemeka saboda he was worried.�? Runtse idanunsa Haydar yayi yana tunanin ya zai yi da Alhaji Abdul ya fita a rayuwarsu. “Nayi ta kiranka ka k’i ka d’auka, na dafa maka abinci ka k’i ci Haydar. Kaima kasan haka kawai bazan d’auki wayarsa don mu gaisa ba. I’m sorry.�? “It’s ok ya wuce.�? Ya rungumeta a jikinsa yana jin zafin k’irjinshi na raguwa. “Kayi hak’urin.�? Ta d’ago kanta tana kallonshi. “Nayi. Kema kiyi hak’uri. And I hope you’ll forgive me.�? “Don Allah karka sake mini haka, akwai d’aci, ban ji dad’i ba wallahi. Zuciyata tana mini zafi sosai.�? “Bazan sake ba Insha Allah.�? Rabata yayi da jikinshi ya dubeta da kyau yace, “Kiyi blocking d’inshi Laila. I don’t trust him.�? “Tun jiya ma nayi.�? “Good girl.�? Dukan k’irjinshi tayi yayi dariya yace, “Ko bad girl ne?�? “Zaka yi latti.�? “Zo muje d’aki kiji wani abu.�? Hararanshi tayi kana ta sunkuya ta wuce ta gefenshi ta isa bakin k’ofa ta bud’e mishi tace, “Zo ka tafi kafin kayi latti.�? “Idan na k’i fa?�? “Sai ka zauna.�? Kissing d’in goshinta yayi ta mik’a mishi key tana cewa, “Yau bana son fita shago, Sabrin zata kula da komai.�? Kar6a yayi kana ya tafi tana d’aga masa hannu. Yana isa kai tsaye ya wuce office d’in da yake, bai jima da zama ba Alhaji Abdul yayi kiransa ya tashi ya tafi. “Morning Sir.�? Ya gaisheshi ba tare da ya zauna ba. “Sannu Aliyu Haydar. Ya ake ciki? Ka kar6i aikin?�? “Na kar6a amma ba don na cancanci kujerar ba.�? Wani irin tafi Alhaji Abdul yayi yana murmushi, hannunsa ya d’aura saman desk d’insa yace, “Yayi kyau. Kamar yanda na fad’a maka jiya, yau zaka samu Manager ya nuna maka aikinka, sannan muna da meeting after 2pm.�? “Amma kafin k’arfe biyu muke tashi a aiki, ya kamata na koma gida bayan nan.�? “Yanayin aikinka will require a lot of sacrifices Aliyu Haydar, karka manta kaine Assistant Manager na Lu’a Ventures.�? “Hakane.�? “You are dismissed.�? Alhaji Abdul ya d’auki wani file yana dubawa. Haydar ya juya yayi taku uku kana ya juyo ya dubi Alhaji Abdul wanda ke aikinshi cikin walwala yace, “Kafin in tafi akwai maganan da zamu yi.�? Alhaji Abdul bai d’ago ido ba ya kad’a mishi kai alamar yana jinshi. “I want you to stop calling my wife, saboda a yanzu ita matar aure ce ba bazawara ba. Idan kana da matsala dani kayi kirana ba wai ka fad’a mata ta mini fad’a ba, she’s my wife not my mother. A k’ark’ashin ka nake aiki kuma bana tunanin kiran matata na cikin contract d’in da nayi signing.�? Diff annurin dake fuskar Alhaji Abdul ya d’auke yana kallon Haydar tamkar zai fashe tsabar 6acin rai. Har ya bud’e baki zai yi magana sai kuma ya fasa ya sauk’ar da kanshi k’asa, ajiyar zuciya yayi sannan ya d’ago yace, “You are right again. Za’a kiyaye hakan.�? Haydar yana jin hakan ya fita daga office d’in yana jin sauk’i a zuciyarsa, idan ya takawa Laila birki shima Alhaji Abdul na buk’atar a taka masa saboda kar ya sake gigin kira masa mata a waya. A ranar aka bawa Haydar office d’insa, sai dai ya lura yanayin aikin nasa na buk’atar jajircewa saboda kusan komai na aikin company a kanshi yake wanda ya rasa gane dalilin hakan, ko dai dama Assistant Manager yafi kowa aiki? Bai bar office d’in ba sai bayan la’asar ya dawo a gajiye, daga bakin k’ofa Laila ta tareshi dalilin taji shigowar motarshi. “Wanka zanyi Laila. Na gaji da yawa.�? Ya fad’i hakan yana mik’a mata sabuwar laptop d’in da aka bashi na aiki wanda zai iya tafiya da ita gida. “Sannu fa, ai daga ganinka na gane yau ka gaji. Mu isa.�? Bayan yayi wanka ya ci abinci yake fad’a mata abunda ya faru a office. “Daga k’arin matsayi kinga har na fara dawowa late kuma a gajiye.�? Laila dake massaging kafad’unsa tace, “Sakali d’an Ammi.�? Muntsinin k’afanta yayi tayi saurin d’agewa tana duba gurin, “Muntsinina kayi fa.�? “Saboda kin rainani ne.�? Dariya tayi mai sauti kana ta sauk’o ta zauna a gefenshi tana kallonshi cikin ido. “Ya?�? Ya tambayeta yana warware gashinta data tufke guri d’aya. “Kawai ina mamakin wai da gaske kai mijina ne. Ban ta6a tsammanin hakan zai faru ba.�? Murmusawa yayi ya jawota jikinshi yana shiru bai ce komai ba. Can ta gyara kwanciyarta tace, “Yau Abul ya kirani.�? D’agata yayi daga jikinshi ta juyo tana ganin mamakin dake shimfid’e a fuskarsa. “Meyasa baki fad’a mini ba tun daya kiraki?�? “Saboda ina son sai ka huta.�? “Ya yake? Ina yake? Yana nan lafiya kam?�? “Lafiyanshi kalau, sai dai da kaji muryarshi zaka san yana cikin kayan maye ne. Bai fad’a mini inda yake ba, kuma har gobe yana kan bakanshi na cewa sai na kashe aurena kafin ya daina shan kayan maye.�? Ta k’ara kwantar da kanta kan Haydar ta jawo hannunshi tana wasa da yatsunsa. Shiru yayi na wasu sakanni sannan yace, “Why are you calm Laila? Bana son kina 6oye abunda ke zuciyarki yana cinki a rai, talk to me kinji?�? “Haydar kullum k’ara girma nake yi, sannan ban san yaushe ranar mutuwata ba tunda ba’a bani guarantee zan kai tsufa ba. Meyasa zan damu a kan abunda ba zan iya canjawa? Meyasa zan kasa walwala don Abul yaga daman lalata rayuwarsa? Yayi hakan ne don ya bak’anta mini ya cusa mini bak’in ciki da tashin hankali, kuma yayi sa’an hakan amma a yanzu na watsar da komai na barwa Allah. Addu’a kad’ai zan iya mishi tunda bashi da niyyar daina munanan d’abi’unshi. Ko a yau Allah ya d’au raina bani da kaico domin ina da Sabrin, ko ita d’aya zata mini addu’a ya kuma bini har cikin kabarina. Shi kuma Allah ya shiryeshi yasa ya gane hanya.�? “Ameen. In Allah ya yarda komai zai zo ya wuce kamar ba’a yi ba.�? “Hmm, barin shaye-shaye abu ne mai matuk’ar wahala Haydar. Ni dai na barwa Allah komai.�? “Kin fad’awa Mas’ud?�? Ya tambayeta yana jawo wayarshi wacce take ringing. “Na fad’a mishi yace zai kai ayi tracking number, nace zai yi wuya domin Abul yasan me yake yi.�? “Hello Ammi.�? Magana ta fad’a mishi yana amsawa kana suka yi sallama. “Ammi rigima.�? “Lafiya dai?�? Ta tambayeshi. “Wai wata mata ce da ‘yayanta suka zo neman taimako shine ta d’auki kayan abinci ta bata. Yanzu tana fa’da mini cewa bata da kayan abinci ne.�? Murmushi Laila tayi kana tace, “Wannan ai ba rigima bace, taimako ne. Wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimakeshi.�? Gyad’a kai Haydar yayi kana yace, “Karki hana Mas’ud gwada tracking number Abul, domin ba’a sani ko za’a dace ba.�? “Mu bar maganan. Ka tayani addu’a kawai.�? “Ina tayaki Laila, domin farin cikinki shine nawa.�? Bayan kwana biyu ranar alhamis Laila ta tashi da fara’a, Haydar na lura da ita sai dai bai ce komai ba har yayi breakfast yayi shirin fita. A bakin k’ofa ta tsaya kamar kullum zata mishi bankwana ya kasa hak’ura yace, “Hajiya irin wannan walwala kamar kinyi tsintuwa.�? Ya shafi sajenshi yana binta da kallo yana murmusawa. “Tsintuwar nayi.�? “Kawo mu raba.�? “Kai za’a raba kenan? Saboda kai ne tsintuwar da nayi.�? Kyakkyawar murmushi yayi har hakwaranshi na bayyana yace, “Naji dad’ina ni Haydar. Ko dai yau kar in fita aiki ne?�? Dariya tayi tace, “Ban ce ba. Umm… kasan me?�? “Sai kin fad’a.�? Sassauta muryarta tayi tana kallon cikin idanunshi tace,“I think I’m ready.�? “For?�? Ya tambayeta don bai gane ba. Murmusawa tayi kana ta k’ara tsayinta ta rad’a mishi magana a kunne ya zaro idanunshi kad’an yana binta da kallon mamaki had’e da farin ciki. “Are you sure?�? “I guess so.�? “Laila kenan. Guessing ma kike yi? Hakan na nufin baki shirya ba kenan. Karki takura kanki, zan jiraki zuwa koyaushe ne. Trust me.�? Da haka ya d’aga mata hannu ya shiga mota ya tafi aiki. K’arfe sha biyu na ranar Hajiya Shatu ta sauk’a a gidan Laila. “Nan gidan goggon su Ilham nazo shine nace bari in shigo mu gaisa, da fatan dai mijinki baya nan.�? “Ya fita aiki tun tuni. Ya yaran?Kwana biyu ban ji labarinsu ba.�? “Suna can suna fafatawa da matar ubansu.�? “Ke dai karki basu goyan bayan su mata rashin kunya domin ita d’in matar ubansu ce. Idan kuma kika nuna musu hanyar raina na gaba dasu to ki sani nan gaba kanki zai dawo.�? Laila ta mata hannunka mai sanda domin tasan Hajiya Shatu na goyan bayan ‘yayanta suna yiwa matar ubansu rashin kunya da fitsara. “Ke dai a bar maganan kawai, amma wani abunda take musu dole suyi magana. Yaro da gidan ubansa amma a hanashi walwala? Ai ba zai yiwu ba! In dai basu ji dad’in gidan ba to wallahi itama k’aryanta taji dad’insa.�? “Allah ya kyauta.�? Laila tayi addu’a kawai domin tasan da wuya Hajiya Shatu ta gane me suke gudan mata. Bayan sun d’an yi hira akan Abul Hajiya Shatu ke cewa, “Hajjaju naga kin k’ara haske da walkiya, ko dai har kin guntsa ne?�? “Allah ya shiryeki matan nan. Dama ni haka nake babu abunda ya karu ko ya ragu a jikina.�? “Wannan kuma ki fad’awa na goye. Ai ko makaho ya laluma zai tabbatar kina shanawa.�? “Hmm baza ku gane bane. Amma ina cikin damuwa game da Abul na sabon d’abi’arsa.�? “Hakane kam. Allah ya shirya shi Hajiya. Muna tayaki addu’a.�? “Ameen Ya Rabbi. Nagode.�? Laila ta amsa kana ta canja musu hiran. Bayan Hajiya Shatu ta tafi ta shiga kitchen tana waya da Sabrin wacce ke cewa tayi kewanta. “Ke dai kina nan kamar ‘yar goye. Ya shago?�? “Ana ta fama, batun turaren wutan ne yasa na kiraki. Kince yau za’a saka a mota, ya iso ne?�? “Ban san ko sun saka ba amma ko ya iso ke zasu kira saboda numbernki na bayar tunda Abul baya nan.�? Sabrin tayi shiru na wasu sakanni Laila tace, “Hello.�? “Ina nan Mama. Wannan karon bai kirani ba, ko dai wancan karon ya samu labarin na fad’a miki yana gidan Micheal ne?�? “Bana tunanin ya sani. Idan kayan ya iso ki fad’a mini akwai nawa da zan ware.�? Da haka suka yi sallama. Da yamma bayan Haydar ya dawo ya samu Laila bata nan ta fita, kiran wayarta yayi ta fad’a masa tana makwabta amma gata nan zuwa. Minti biyu da haka ta shigo ta samu ya shiga wanka. Kayansa daya saba watsarwa ta tattara ta kai gurin ajiye kayan wanki sannan ta fito masa da k’ananan kayan da zai saka. Bai jima ba ya fito yace, “Har kin dawo uwar yawo?�? Dariya tayi mai sauti tace, “Yau kuma nice uwar yawo?�? Murmusawa yayi kana ya fara shiryawa tana binshi da kallo. Sai daya gama shirin ya dubeta a lalace yace, “In kyau nayi sai ki fad’a ba wai kiyi ta bina da ido ba.�? Tashi tayi fuskarta d’auke da murmushi had’e da kunya tace, “Baka da dama. Mu je kaci abinci.�? Yana cin abincin suna hira yake cewa, “Kinji wai za’a rufe schools, kasuwanni da duk wani gurin aiki ko?�? “Haka nake ji a labarai wai har an rufe Lagos tunda cutar tafi yawa a can.�? Ta amsa cikin jimami. “Allah ya karemu ya kuma dakatar da ita tun kafin ta yiwa mutane illah.�? “Ameen Ya Allah. Amma wanda basu saba zaman gida ba zasu wahala.�? “Tunaninki kenan?�? Ya tambayeta yana dariya. “Gaskiya na fad’a ai.�? Ta murmusa tana kwashe kwanunkan zata kai kitchen. Bai tayata ba ya tashi ya koma falo ya jawo Laptop d’inshi ya kunna kana ya d’auki wayarsa ya kira Ammi suka gaisa. “Yau kam baza ki ganni ba Ammi. Yanzu dawowa na daga aiki sannan akwai wani abu da ake jira in duba in turawa Company. Insha Allahu gobe kafin na wuce aiki zan shigo in dubaki.�? Bayan sun gama magana ya ajiye wayar ya maida hankalinshi kan Laptop d’in yana karanta wani abu. Laila dake gefenshi taji haushi ba kad’an ba domin ko kallonta bai yi ba. Minti biyar da haka ta mintsineshi a hannunsa ya juyo da mamaki a fuskarsa yana kallonta. “Mena miki?�? Gyara zamanta tayi taci gaba da kallon tv fuskarta babu fara’a. Shafa gurin yayi yana nurmushi don yanzu ya gane laifinsa. Sai dai bai kulata ba yaci gaba da aikinshi dalilin an bashi lokacin da ake buk’atar ya tura aikin. Bugeshi tayi kamar bata sani ba taci gaba da kallonta. Murmusawa ya k’ara yi yace, “Wallahi idan na gama aikin nan I will deal with you Laila. Kici gaba.�? Yayi kwafa yaci gaba da aikinsa. Minti uku da haka ya gama aikin ya tura musu, kafin ya kashe Laptop d’in yaji ta k’ara mintsininshi ya juyo yana cewa, “That’s it! Come here.�? Hannunta ya kamo duka ya had’a guri d’aya ya fara mata cankulkuli tana rok’onshi Allah da Annabi ya bari. “No, ai baki ga komai ba. Ba ni kike muntsina ba?�? “Na daina. Haydar ka daina, wallahi zan suma.�? “Muna da ruwa zan yayyafa miki ki farfad’o.�? Sai daya tabbatar ta jikkata sannan ya barta ya koma ya zauna yana kallonta tamkar bashi ya gama mata mugunta ba. “Zan rama.�? Shine kawai abunda ta fad’a ta tashi ta wuce d’aki domin ya birkita mata kwalliyarta. Dariya yayi ya kwashe Laptop d’in ya bita d’aki don yaji laifin daya aikata. Kwana uku da haka kullum Haydar baya dawowa gida sai bayan la’asar, watarana kuma sai kusan magriba zai dawo wanda hakan baya yiwa Laila dad’i. Sai dai bata ta6a k’orafi ba saboda tasan neman na rufa musu asiri yake yi, ba wai wani gurin yake zuwa ba. Da dare suna zaune a falo tare da Mas’ud wanda ya kawo musu ziyara suna kallon News. A nan ake sanar da cewa an shiga lockdown a jihar Kano dalilin cutar Corona ta yawaita. “Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.�? Laila ta dafe k’irji tana kallon ikon Allah. Haydar ya dubeta ya kad’a kai yana murmushi domin tun ba yau ba ya lura tana tsoron cutar ba kad’an ba. Ido ya yiwa Mas’ud shima ya kalleta yaga yanda ta kasa zama daidai bakinta a bud’e, hannunta a kan k’irjinta cike da tsoro. “Wai haka take da tsoro dama?�? Haydar ya tambayi Mas’ud yana k’unshe dariyarsa. “Kad’an ka gani.�? Mas’ud ya mayar masa da martani sannan ya gyara zamanshi fuskarsa ta zama so serious ya dubi Laila yace, “Kalti abun nan sai addu’a fa.�? A nan ta juyo ta kallesu zuciyarta na kad’awa tace, “Mas’ud ko dai tashin duniya ne ya zo?�? Haydar yayi dariya mai sauti har yana rik’e cikinsa, Mas’ud ma dariyar yake son yi amma ya gimtse domin muguntar da yaso shiryawa Haydar. “Alamomin tashin duniya kam tuntuni muna gani Kalti. Wannan d’in ma watak’ila yana ciki domin Annabi Muhammad SAW yace idan alfasha da fasadi ya yawaita to a saurari cututtukan da za’a rasa gane maganinsu. Ga HIV, ga Cancer har yau babu maganinsu sai dai a sha ayi sauk’i. Ke dai ku kiyaye. Gobe kuje kasuwa ku sayi duk abunda kuke buk’ata sai ku zauna a gida kamar yanda Gwamnati ta umurta.�? Wannan magana ba k’aramin shigar Laila tayi ba, ai kuwa ta dubi Haydar da yake murmusawa irin ko a jikinshi nan tace, “Ka ganshi ko? Har yanzu bai yarda cewa cutar nan gaskiya bace. Daga gobe babu inda zaka sake zuwa sai an tabbatar we are all safe.�? “Sai mu gani in d’aureni zaki yi.�? Ya bata amsa kana ya dubi Mas’ud wanda sai a lokacin ya fara dariya yace, “Kai kuma ka kyauta. Sai yanzu na gane manufarka.�? “Me kuma nayi? Don na baku shawarar yin taka tsantsan? Kuma gobe kar ku manta ku sanya takunkumi wato Face Mask kafin ku fita.�? Ya mik’e tsaye yana dariyar mugunta. “Kana ji ko?�? Laila ta harari Haydar yayi rolling idanunsa bai ce mata komai ba. Mas’ud ya mata sallama amma hankalinta na kan TV tana ganin yanda ake bayanan symptoms na Covid-19. Haydar ya raka Mas’ud waje inda motarsa yake yana kyakyata dariya. “Kai mugu ne Mas’ud, wallahi baka kyauta mini ba. Yanzu hankalinta k’ara tashi zai yi ta hanamu sakat a gidan nan.�? “Zaka gode mini nan gaba. Ga face mask ka kai mata.�? Ya damka mishi kwalin ya kunna motarsa ya tafi yana dariya. Haydar yana komawa falo Laila ta tsayar dashi daga bakin k’ofa tace, “Bani hannunka in d’iga maka hand sanitizer.�? “Are you kidding me Laila? Mas’ud na raka waje fa.�? “I don’t care. Kafin ka shigo ka ta6a mabud’in k’ofa ko baka ta6a ba.�? “Yes, na ta6a.�? “Bani hannunka.�? Tsayawa yayi yana kallonta, yanda ta had’e fuska babu wasa yasa ya mik’a mata kwalin face mask d’in yana cewa, “Gashi Mas’ud yace a baki.�?“Allah sarki Mas’ud, shi burinsa yaga bana cikin had’ari. Idan na d’iga maka sai ka shafa a jikin kwalin saboda watak’ila akwai cutar a jiki.�? “Fuck me!�? Ranshi ya fara 6aci ya ajiye kwalin a k’asa ya mik’a hannunsa ta d’iga masa ya shashshafa tana gyara masa yanda zai yi. “Saura kwalin.�? Ta masa nuni dashi. “Laila bazan iya shafawa kwali abu ba. Dama kece zan iya bin duk ilahirin jikinki in shafa miki amma banda wannan.�? Ya nuna kwalin tamkar zai yi ball dashi. “Baka da kunya.�? Ta fad’a tana harararsa kad’an. “Dama ban ce miki ina da ita ba.�? Ya ratse ta gefenta zai tafi. “Ka dawo ka goge abun nan.�? Hand sanitizer hannunta ya kar6e ya ajiye a k’asa ya rik’o k’ugunta yace, “Mas’ud was just messing with you ne. Yayi hakan ne don hankalinki ya tashi ki hanamu sakat, kuma gashi har kin fara tun kafin aje ko’ina.�? “Babu dai inda zaka je.�? Ta bashi amsa tana kallon kwayar idanunsa. Saketa yayi ya koma falo tana kiran sunansa wai yazo ya shafawa kwalin sanitizer. “Bazan iya ba Laila.�? Kwafa tayi kana ta tura kwalin gefe da k’afarta tana cewa, “Ai ance idan cutar tayi 9hours a jikin surface tana mutuwa da kanta. So zuwa gobe da safe zan iya d’auka.�? Da haka ta d’iga kad’an a hannunta ta shafawa k’afanta inda ta ture kwalin. “Seriously Laila?�? Haydar ya sake baki yana kallon ikon Allah. “Prevention is better than cure.�? Washe gari tare suka fita ta ajiyeshi a office ita kuma ta wuce gurin sayayya domin tace bata yarda dashi ba. Kafin azahar aka fara kora mutane gida, dama tuni Laila ta gama sayan duk abunda zata saya, office d’in su Haydar ta isa ta kirashi a waya yace mata yana zuwa ta jirashi. Ta kai awa d’aya da rabi tana jiranshi sannan ya fito, kafin ya iso ta fito daga motar da d’iga mishi Hand Sanitizer ya shafa babu musu amma ya lura ranta a 6ace yake. Sai da suka shiga mota suka fara tafiya sannan yace, “Gimbiya laifin me nayi?�? “Babu.�? “Akwai dai. Irin wannan had’e fuska nasan nayi laifi.�?“Ya wuce.�? Ta haka ta hau titin da zai kaisu gida yace, “Mu koma inda kika yi shopping zan sayawa Ammi kayan abinci. Ni sai yanzu hankalina ya tashi da wannan lockdown d’in. Ya zan yi da Ammi da bata da kowa sai ita d’aya? “Na kai mata duk abunda zata buk’ata. Sannan na samu makwabtanku sun bata wata ‘yar budurwa wai Meenat da zata zauna da ita.�? “Thank you, idan mun je gida sai ki mini lissafin kud’in in baki. But ya aka yi iyayen Meenat suka iya barinta ta zauna da Ammi?�? “Bana buk’atar sisinka, nima Ammi uwace a gurina. Ka san yarinyar kenan?�? D’an muskutawa yayi kad’an kamar mara gaskiya yace, “Kin manta unguwarmu d’aya ne?�? “Haka fa.�? Laila da bata kawo komai a ranta ba taci gaba da tafiya har suka iso gida Haydar na waya da Ammi. “Ammi da zarar na samu dama zan zo na dubaki domin wannan lockdown d’in bai mini ba. Kina nesa ina nesa wa zai kula da ke?�? “Da kake zuwan kai kake kula dani? Ji mini shiririta! Idan dukan sojoji kake so ka fita daga gidanka. Mu nan ko k’ofar gida bama lek’awa balle har mu fita daga unguwar mu je wata.�? Laila dake gefe tayi dariya domin a hands free ya saka kiran. Harararta yayi kana yaci gaba da magana da Ammi tamkar wani k’aramin yaro. “Na lura idan kana gaban Ammi yaro d’anye shataf kake dawowa kamar wanda aka yaye jiya.�? Laila ta tsokaneshi tana zama a kan kujera bayan ya gama wayar. “Zan dinga fita aiki 3days per week. A nan kuma zan samu hanyar zuwa gurinta.�? “Allah ya bada sa’a ya hana had’uwarka da sojoji.�? A ranar shi da kanshi ya musu girki suka ci suka zauna kallon labarai wanda ya zama sabon d’abi’ar Laila. Zaune yake a k’asan Carpet ya mik’ar da k’afafunsa, Laila kuma ta d’aura kanta kan cinyarsa yana tura hannunsa cikin gashin kanta tana lumshe ido, a gefe guda kuma waya take yi da Sabrin tana k’ara jaddada mata matakan tsaron gujewa cutar Corona. Bayan ta gama wayar ta sak’ala hannayenta a bayanshi ta tura kanta kan cikinshi tana numfashi a hankali. Yanayin kwanciyarta a jikinshi ya sanya masa wani irin yanayi wanda ya saba ji a kullum in yana zaune kusa da ita. Sai dai me zai yi? Hak’urin daya saba yi shi zai yi saboda ba zai ta6a mata dole ba, yasan zafin da rad’ad’in yiwa mace dole, don haka bazai ta6a yadda ya aikata hakan ba. “Haydar.�? Ta kira sunanshi wanda hakan yasa yaji kamar hura mishi iska take yi a fatar cikinshi dalilin bai sanya riga ba, wanda dama shi haka yake baya son saka kaya. “Na’am.�? Ya amsa yana k’ok’arin rabata da jikinshi amma ta k’i sakeshi. “I’m ready.�? Ta d’ago idanunta tana kallon yanda fuskarsa ta sauya cikin k’ank’anin lokaci. “Are you sure?�? �?100%.�? ‘Dagota yayi ta zauna suka fuskanci juna yace, “Why?�? “Ina tsoron kar duk mutuwa zamu yi, watakila this is the only chance da muke dashi na kasancewa tare.�? “Laila babu mai mutuwa sai lokacinsa yayi, sannan da yardar Allah babu abunda zai samemu har cutar nan ta tafi. And you are not ready yet.�? “And…�? Ta fara magana sai kuma ta tsaya. “And???�? Ya tambayeta. Mayar da kanta tayi kan cikinsa ta 6oye fuskarsa tace, “And I need my husband.
Mum Fateey 👌



